YAR AGADEZ
{Page 30}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Dama ance duk abinda ka shuka tou shi zaka girba, Doctor din ne yayi kanta yana kokarin bata hakuri akan wannan kaddara ce kuma ay cuta ba mutuwa bace...kallonshi ta tsaya yi tana girgiza kai idanunta kuwa jajir wane garwashi ta daga masa hannu "Kar ka kuskura kazo inda nake! Nasan wannan result din ba gaskiya bane, bana dauke da wannan cuta don haka ban yarda da kai ba..." Mikewa ta fara kokarin yi Doctor din yace "I know da wahala ka yarda saboda wannan cutar ba abu bane me kyau, sannan ita survival rate dinta is zero percent amma idan har Allah yaso sai kiga kin warke, the best thing da zakiyi shine medication da gaggawa, in ba haka ba zata cigaba da kara yaduwa ko ina, hakuri zakiyi kizo ayi referring dinki to team of doctors don su fara baki taimakon gaggawa..." Wata irin tsawa ta daka masa "Tou ay sai kazo ka kasheni ingani! Komai zaka fada bazan taba yarda inada wannan cuta ba don haka kaga tafiyata!" Tana fadan haka ta fice daga office din, Doctor din tsaye yayi yana binta da kallo, adaidaita ta tsaida inda ta fada masa sunan unguwar su nan ya kaita, yanzu ita talauci zata koma tsundum? Saukinta ma tanada yan kudade a account dinta zata fara amfani dasu kafin tasan nayi, bakin lungun gidanta ya sauketa nan tabi unguwar da kallo ganin a can inda take ko kare gareta bazata kawo shi wannan unguwar ba, babu abinda ke tashi sai warin kwata, dod'e hanci tayi ta biya shi kudinsa sannan ta nufo ciki tun a bakin kofar gidansu taga dogarawa suna sauke mata kayanta babu abinda suke sai cilli da akwatinanta, da sauri ta karaso tana fadin "Kayan nawa ne aka wulakanta min su haka?" Babu wanda ya tanka mata a cikinsu sai bayan sun gama watsa mata kayanta tatas sannan suka kalleta "Mai martaba yace baya son ganin ko tsinkenki a gidansa sheyasa ya bamu umarni da mu kawo maki kayanki, bayanson ki sake taka masa koda kofar gida ne," suna gama fadan haka suka shiga mota suka tafi, kasa kwakkwaran motsi tayi, ta juma a tsaye kafin ta tako a hankali ta bude kofar gidanta wacce duk sha wahalar duniya, tana budewa ta dinga daukar kayanta tana shiga dasu bata damu da yadda yan unguwar ke kallonta ba, bayan ta kai ta shige ciki tana kare ma gidan kallo, anya zata iya rayuwa a cikinsa yanzu kuwa? Wannan gidan ko karenta bata iya kawowa, gidan wani dan kut dashi daga tsakar gida sai daki daya sai bandaki da kitchen sai kuma zaure, zubewa tayi kasan gidan tana zubar da hawaye, wayarta ta dinga jin alert tana dubawa taga transactions kala kala kamar an mata hacking account, kara dubawa tayi taga da gaske an yashe ta tas, hannu ta dora bisa kai ta fasa wani irin ihu kafin ta saki kuka mai cin rai....
Haka Karimah tayi hakuri ta cigaba da rayuwa cikin gidannan batada kudi gashi da kyar ma take samun cin yau dana gobe, yan unguwarsu kyamarta suke yi don bayan yan kwanaki sai ta fara ganin wasu kuraje na fito mata a jiki masu ruwa da wari, ga cikinta dake kumbura kamar wata mai ciki wata tara, gashi batada kudin zuwa asibiti abinci ma da kyar take samu ta ci sau daya a rana.
3 Months Later...
Daga dakinta ta fito tana faman jan kafa cikinta ya girma ya kumbura kamar wanda aka aje yaya goma a ciki, a bakin kofar dakin ta tsaya tana kokarin maida numfashi sabida yanzu ko taku biyu tayi sai ta dunga jin kamar zata suma, ta kai kusan minti goma tsaye tana numfashi sama sama, yau dai taga alama numfashin bata baida niyyar daidaita don kullum ta kanyi kamar minti goma zuwa sha biyu kafin ta samu numfashin ya dawo amma yau abin ya faskara, a dalilin haka ne zufa ta dinga tsatsafto mata ta ko ina anya ba mutuwa zatayi ba?Ta tambayi kanta, ganin dai abun bana karewa bane yasa taja jiki tana jin kamar cikinta zai fado tsabar yadda ya kumbure, bandaki ta shiga tayi wanka ta fito a tsakar gida ta zauna saboda wani irin zafi keda akwai a cikin dakin ga kurajen jikinta duk suk chabe suna mata kaikayi, jingina tayi da bango tare da numshe idanu nan da nan baccin wahala ya dauketa... tana kwance sai tayi mafarkin wai tana tafiya cikin daji a tsorace tana kalle kalle sai kyarma takeyi, wai sai tafiya takeyi hanyar dajin baya karewa ga wani bala'in duhu ga kishirwa tana ji, can dai sai taga wani pampo ta tafi da sauri har ta kusa zuwa wurin sai kawai taji kafarta zata fada cikin wani katon kabari wanda yake a bude, wasu hannaye masu zara zaran akaifa taji sun chafko mata kafa take ta fasa wani irin gigitaccen ihu, haka taji ana ta janta cikin kabarin nan har suka kai can cikin ramin mai zurfin balai, kawai suna zuwa sai kawai taga wata mata ta fito mata da fararen kaya duk jikinta haske ne daga kanta zuwa kafarta, a tsorace take ja baya ganin Ammin Hoodah, takowa tayi kusa da ita tace "Kadan daga cikin abubuwa da kika shuka ne suka fara tasiri akanki! Kin kasheni kin dauka kinci bulus? Kin zo kin bi bokaye kinbi malamai kinbi yan bori! Kin azabtar man da ya! Kin asirce sarki! Hahahaha! Tou kadan daga cikin abubuwan da kika fara shukawa ne kike girba!" Bat ta bace, kalle kalle ta farayi a tsorace. Tana tsaye sai ga wasu zombies sun taho kansu karkace badai kyan gani masu kama da aljannu, nufar ta sukayi gadan gadan suna fadan "Ki tuba ga Allah! Ki nemi yafiya ga wadanda kika cutar! Ki tuba kafin lokaci ya kure miki! Ki tuba, ki tubaaaa....."
Suna gama fadin haka suka wani daga ta sama suka sake jefa ta cikin wani rami dake cikin kabarin, wata irin muguwar faduwa tayi ji kake tim! Kanta sukayi kuma gadan gadan suna fadin "This is your home in baki tuba ba!" Suka fada suna nuna mata wata wuta dake tashi mai shegen zafi, wadda tafi ko wace muni ce ta wani irin caka mata akaifa wata irin kara ta saki tana tura jikinta baya a tsorace, wata irin farkawa tayi jikinta babu inda baya kadawa zufa kuwa kamar an mata wanka, numfashi take ja tana faman zare ido "Sun kamani! Sun kamani!!" Abinda kawai take iya fada kenan tana faman goge zufa...
*******
Zarah ta riko mata hannu wasu sabbin hawayen na taruwa cikin idanunta tana girgiza kai itama haka Khadija ta tsaya tana kallonta cikin ido kafin Zarah tace "Kinyi gaganci da kika bari soyayyar wanda nakeso ta kama maki zuciya, meyasa kika bari zuciyarki ta yaudareki? Tou ki bude kunnenki da kyau ki saurareni da kunnen basira, Yaya Ashraf is mine and mine alone, babu abinda kika isa kiyi, ita soyayya ba'a forcing mutum yayita... ke baki isa kizo ki tursasa mashi dole sai ya soki ba, ko yanzu nasan am step ahead of you saboda ni yake so bake bake ba kisa wannan a ranki, ni yanzu hankali na a kwance yake saboda nasan bakya daga cikin kalar matan da Yaya Ashraf yakeso, sheyasa tun tuni nake nuna maki mace anasonta kamila mai al kunya, natsatsiya mai kamun kai ke ki fada man a ciki wanene kike dashi? Bakida ko daya baki iya komai ba sai hauka da shigar banza wallahi har mamaki nake yadda ma muka fito ciki daya dake, kwakakwata baki biyo halina ba, sannan magana ta gaba ni bazan taba yin fada dake akan saurayi ba bana fatan Allah ya nuna mun wannan ranar, kedai da kikaji zaki iya tou sai kije kiyi am not your mate, maganar yaya Ashraf kuma babu yadda zakiyi nan gani nan bari sai dai hange daga nesa, don haka ki kama kanki ke macece kar ki yarda kizubar da kimarki akan wani namiji." A fusace Khadija ta fizge hannunta daga na Zarah idanunta cike da hawaye ta shiga nuna Zarah "Kome zaki fada kije ki fada Zarah I don't care, yes baya sona for now amma zai soni a gaba, I told you sai na kwaci soyayyarsa kina ji kina gani, don haka sai ki shirya..." tana gama fadan haka ta juya ta fita nan Zarah ta tsugunna ta fashe da kuka mai ban tausayi....
**
Kafin ta kwankwasa sai taga kofar ma a bude take, a hankali take taku saboda tray din dake hannunta har ta aje shi saman table kafin ta dago tana kare ma dakin kallo, gyara dakin tayi tas tana tsakar linke bargo ya shigo motsinshi taji, fuskarsa alamun yana cikin damuwa ya zauna gefen gadon duk kokarinsa akan ya mata murmushi kasawa yayi, itace ma ta sakar masa murmushin "Abinci na kawo maka, amma naga alamar kamar kana cikin damuwa, please kaci abincin...." murmushi ya kakalo "Allah sarki kin kyauta kuwa thank you." Tray din ya jawo gabanshi yana budewa "Sannu kinji? Allah yayi maki albarka.." wani irin sanyi taji a cikin ranta, murmushi tayi kafin tace "Ameen." Kallon shi take yadda ya fara cin abinci cikin nutsuwa, kallonta ya dago yana yi ya kasa jurewa sai yace "Wai Zarah meyake damunki? Na lura gaba daya yau bakya cikin walwala meyafaru tell me?" Tsayawa yayi da cin abincin yana kallonta "Dan Allah kar ki boye man koma menene kinji?" Ta kakalo murmushi "Gajiya ce kawai kasan yau general cleaning mukayi ma gidan, is just stress that's all..." yayi shiru yana nazarinta "Tunda na fahimci kina cikin damuwa Zarah gaba daya nima sai najini cikin damuwa, kuma baza kice stress na saka damuwa ba, kinga yadda kika zama kuwa yau? Kin fada kin zama wata kala..." tayi murmushi kafin ta tsiyaya mashi juice din data kawo mashi cikin glass cup "Ciwon so ne yake damuna na kosa na zama mallakinka kowa ma ya huta." Yayi dariya kafin yasha juice din "Kinji ki da wani magana, sai kace wacce za'ayi kwace? Tou nida ke wa ya kamata ace ya kamu da ciwon so? Kinsan yadda nake sonki kuwa?" Yar dariya tayi alamun jin kunya tace "Babu wanda zai mun kwace... nagode da son da kake mun." Tsayawa yayi yana kallonta "Ina so in bar kasar nan, ina ya kamata muje honeymoon bayan munyi aure? Saboda ni akwai mutanen da bana son gani yanzu gara mu gudu mu bar masu kasar..." dariya ta fashe da shi "Jishi don Allah kamar wanda ake kora ko ake masa wani mugun abu?" Yar dariya yayi yana kallon yadda take dariya kyanta na kara bayyana, ajiyar zuciya ya sauke "Zarah ina sonki, son da bansan adadinsa, I don't know how when where? But your love in my heart is deep..." karar abu sukaji suna daga ido sukaga Khadija tsaye tana binsu da kallo tray da cup din data dauko sun tarwatse a kasa, har glass ya fadan mata a kafa, da hanzari Ashraf da Zarah suka mike sukayi kanta take Khadija tace a shagwa6e "Yaya Ashraf am hurt...naji ciwo yana man zafi..." Zarah ta riko ta da sauri don ta fahimci attention din Ashraf kawai take so, janta takeyi da sauri tana tirjewa har cikin parlor, wani irin wurgi Zarah tayi da ita kan kujera sannan tace "What do you think you're doing?" Khadija tayi murmushi "What you think! Wai kin dauka wasa nake maki maganganun dana fada maki jiya? You must be joking!" Tayi wata dariya, Zarah tace "Ko me zakiyi bazaki taba cin nasara ba, our love is pure so dama ki kwantar da hankalinki Allah zai baki wanda ya fishi..." Mikewa Khadija tayi da hanzari "Babu wani wanda ya fishi, ke bari in fada maki, I told you before saina kwace Ashraf kota dadi ko ta tsiya! Ko aure aka daura maku saidai a kwance shi wallahi...!" Zarah batasan lokacin data dauke Khadija da mari ba tana nunata tace "So ba hauka bane, ki dawo cikin hankalinki tun wuri tun kafin wankin hula ya kaiki dare!" Dafe kuncinta Khadija tayi kafin ta dauko hannu zata rama taji ance "If you dare lay a single finger on her Khadija you'll regret ever been born!" Duk da yadda zuciyar shi ke mashi kuna haka nan ya daure ya fara magana cikin nutsuwa "Yau na tabbatar rawar kanki bata amfana maki da komai ba Khadija, bansan haka kike marar hankali ba sai yau! Duk naji conversation dinku tou bari kiji in fada maki Zarah nakeso baki isa kiyi forcing kanki a kaina ba! Ke dabbar ina ce da zaki fara kishi da yar uwarki? Har kike ikirarin sai kin aureni koda hakan na nufin ki kashe mata aure? A cikin dabobbi ke bansan wace specie bace kin taba ganin yan gida sun auri mutum daya? Are you mad? Duk wani abu da kike ji a game dani kiyi gaggawar fiddashi daga ranki in ba haka ba kece zaki wahala a banza a wofi! Hope kin fahimta...!" Shiru dukkansu sukayi. Zuciyoyinsu na bugawa, sai kawai ganin Khadija sukayi ta zube kasan gwiwowinta tare da riko wandon Ashraf ta fashe da kuka "Ko kasheni zakayi Ashraf Ina sonka! I still love you..." Cikin karaji Zarah tayo kanta gadan gadan tare da fincikota ta fara kokarin rabata daga jikin Ashraf hawaye na faman zarya a idanunta, Ashraf kuwa tsaye yayi kamar gunki komai nashi ya tsaya cak da aiki wannan wace irin masifa ce haka?
Kuyi hakuri da wannan ba yawa😆😆
No comments:
Post a Comment