Tuesday, 8 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 07

 YAR AGADEZ

 

         

              {Page 07}



Tunda suka kama hanya Hoodah bata bar shar6ar kuka ba, maganganun Kaka kadai ke mata yawo cikin kai kafin a taho da ita lokacin da take mata nasiha daga ita sai Hoodah a cikin daki. "Kiyi kokari wajen girmama mijinki Hoodah, a koda yaushe ki zama mai sauarensa a duk abinda zai ce maki, mun baki tarbiyya daidai gwargwadon ikonmu, in har kika zamo mai yawan kyautata masa na tabbatar a hankali soyayyarki zata dasu a cikin zuciyarsa, yi nayi bari na bari kar ki, ki cigaba da kwalliya kamar yadda kika saba yadda ko kallonki yayi zai ji dadin zabin iyayensa, ki zamo mai tsafta da gyara muhalli karki dubi daga inda kika fito, ki tabbatar kina masa kwalliya ki zama attractive, ki zamo mai kamshi a koda yaushe nasan kina son kamshi amma ki kara kan wanda kike dashi a nan, ki masa girki, kinsan way to man's heart is his stomach, ki zamo babbar aminiyar mijinki daga abota akan zamo masoya, ki fidda Ashraf daga cikin ranki tunda yanzu kinga ke matar wani ce, kece zakiyi grooming dinshi yadda kikeso ki tabbatar kece mace ta farko da zai nema wajen shawara. Mijinki public figure ne, yarima ne wanda zai iya zama sarki nan gaba ke kuma ki zama sarauniya, kingane me nake nufi, ki tsaya dashi duk dadi duk wahala rayuwa ba yadda bata kamawa yau gareka gobe ga waninka, don haka ki kaunace shi, ki rirrirace kamar sabon jariri, ki girmama iyayensa da yan uwansa da duk wani wanda zai ra6e shi, iyayensa suma naki ne ki saki jiki dasu wajen neman shawara duk sadda wani abu ya shige maki duhu...." kuka take a hankali Kaka ta numfasa "Ki zamo mai riko da addini, sallah da azkhar ki nemi tsari daga dukkan wani sharri, Allah yayi maki albarka ya baku zaman lafiya mai dorewa..." Wani hawaye masu dumi suka gangaro mata yanzu ita duk abubuwan nan da Kaka ta fada mata anya zata iya? Idan shi baiyi treating dinta yadda ya kamata bafa ita ya zatayi? Ta dinga kuka cikin jirginnan ta kasa controlling kanta, Aunty Rahanatu dake gefenta ta kamo hannunta cikin nata tayi squeezing, ta dago a hankali sai ta fada bisa ita ta dinga kuka kamar an aiko ta, Aunty Rahanatu batayi gigin hanata kuka ba haka ta barta tayita kukan kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa, d'an shafa kanta takeyi alamar rarrashi....

Bayan sun sauka dama an aiko da motoci sunfi kala biyar wanda zai daukesu daga airport, haka aka dinga sakin kirari a haka suka shiga mota aka wuce dasu gidan Sarkin Niamey. Da isarsu dama kowa su yake jira nan da nan aka tarbe su tarba ta musamman aka masu iso, amarya aka ja har bangarenta wanda yake bangare ne dake ke6e shi kadai na daban, kowa sai da yayi mamakin haduwar gidan don ba karamin kyau yayi ba, mahaifiyar Sultan tasa aka dinga shigo masu da abinci, su kaza, tsire balangu wannan tire dinsu daban daban banda salad, aka aka dunga jida ana shiga bangaren amarya dashi, nan da nan gidan ya sake kacamewa da baki shiga kawai ake ana fita kamar ana hankado su, nan suka cicci Abinci suka sha drinks sai kuma sukayi sallah, suna gamawa aka jawo amarya don taje gaido surukan nata.... har fadar Sarki aka kaita inda suka karbe ta hannu bibbiyu suka sa mata albarka, ana gamawa aka maida amarya ta sake yin wanka ta fito nan aka shirya ta Budan kai. Amarya tasha golden lace mai kyalkyali wanda akayi mata harda veil na bisa kai, bayan an gama shiri aka fito da ita inda aka gyara za'ayi event din yayi kyau sosai nan aka fara gudanar da Budan kai.

"Takawarki lafiya yar sarki jikar sarki kuma Gimbiyar mata, sarauniyar kyau, doguwar mace alkyabbar mata, shugabar mata kyakkyawa mai dimple Gimbiya mai siffan larabawa ko ba'a sanki ba sai an tambayi wacece ke..." Ba abinda Hoodah keyi sai murmushi kanta cikin veil, "Masha Allah...!"" Shine kawai abinda suke fadi, can sai ga cousins din Yarima ne sun kai su bari suka je inda Gimbiya take a hankali sukayi lifting mayafinta, take aka fara mata liki ana zubar da ruwan kudi, sannan sai ga aunties din Yarima suka fiddo turare suka dinga fesa mata, suka dinga welcoming dinta into the family, duka bayan an gama wannan aka damka wa dangin ango amarya inda sukace sun dauki amana... daga nan makada suka fara nasu aikin suna cigaba da praising Gimbiya Hoodah!

"Sarauniya Hoodah, yar gaban goshin mai martaba, farar mace alkyabbar mata, sun buga dake sun barki, takawarki lafiya yar sarki jikar sarki, Allah yaja zamanin uwar gida sarautar mata...." Nan da nan wurin ya rikice da guda da kide kide da raye raye na ban mamaki! Bayan an natsu na kamar minti sha uku haka sai kuma taji an fara cewa "Ga yarima nan isowa shida tagawarshi! Ga ango nan shigowa yanzu muna so kowa ya samu wuri ya zauna! Dan sarkin Niamey zai shigo...." Take ya shigo yasha wasu kaya masu kama dana indiyawa sunsha aiki sai kyalkyali yake, gefensa yana tare da abokansa sun kai biyar, bayansa dogarawa ne ke ta faman take masa baya... take suka fara da cewa "Yarima na Gimbiya, Sultan na Hoodah! Ango na amarya! Kun zauna an tashi, Gimbiya Hoodah matar Yarima Sultan, Dan sarki jikan sarki, mulki yafi kudi, Allah yaja zamanin masu sarauta...." cike da kasaita yake tafiyar har aka kaishi mazauninsa wato kusa da amaryarsa Hoodah. Bayan ya zauna. Nan Sarauniya Hajiya Batul itama akayi mata iso da kirari nan da nan ta fara gudanar da kyauta ta musamman da zasu bada itada sarki. Bayan an ci an sha sai aka cigaba da gudunar da shaglin biki ba karamin dukiya aka kashe ma wannan sabga ba, kaji kuwa sai da sukayi kamar zasuyi magana banda tsire da ragunan da aka gasa. Ba su suka gama bikin sai gab da magrib nan aka kare kowa ya kama gabansa, Hoodah dakinta aka maida ita nan mutane sukayita tururuwar zuwa ganin amarya da kuma dakin amarya....

Nan aka soma watsewa tashi akayi aka kara kimtsa ma amarya dakinta aka sanya turaren wuta. Hoodah ce zaune har kusan karfe sha daya babu ango babu dalilinsa, itama kanta ba son zuwansa take ba dan gaba daya kirjinta in banda bugawa babu abinda yakeyi, wani tsoro da fargaba ne ya darsu a ranta. Can cikin dare misalin sha biyu na dare taji alamun bude kofa dama ta kasha fitilun dakinta ta fara bacci sama sama...

********

Khairy ta kalli samudawan dake gabanta kusan su uku suna tsaye bayan wani kango ko wane fuskarshi kadai abun tsoro ne tace tana huci 

"Wannan aikin da zaku aiwatar bana son kuskure... ku tsaida hankalinku kuyi shii yadda ya dace yadda nikuma zanji dadin biyanku yadda ya kamata..." daya daga ciki mai suna damisa ya dakatar da ita yana busar sigari, yace "Toh malama sai ki fara bada rabi kinsan banida mutunci kan kudi, zan iya yin komai..." tace "Haba zan bayar yanzu ga wannan..." ta damka mishi abu cikin envelope, ogan ya karba yana tabawa saida yaji da dan kauri sannan ya bushe da dariyar mugunta "Kisa a ranki anyi a gama kawai..." Khairy tayi murmushi tana kada kai "Kuna iya tafiya, idan kun kammala ku neme ni a nan..." daga haka tayi gaba zuciyarta fes.

********

Jin motsin bude kofa tayi, tayi zaton ko Yarima ne ya shigo, a dan tsorace ta kalli kofar, ta mike a hankali tana fadin "Sultan?" Jin shiru ya sanya ta fara kokonto ji tayi an damke mata kafafu an matse an kunna fitilan daki, ganinsu ya gigitata ya kuma razanata matuka, take jikinta ya fara rawa ganin katti gabanta sun rufe fuskarsu da mask, "La....fiya? Me kukazo yi mun?" Ta fada tana tunanin inda bayinta suka tafi bataji alamun motsinsu ba, wani irin damka sukayi mata take Hoodah ta fara shure shure, amma tunda daya ya zabga mata wani irin gigitaccen mari taji gaba daya tunaninta ya dauke, take ta fara ganin biyu biyu ji tayi an wullata kan gado da mugun karfi, ta dafe kanta tana kokarin mikewa tsaye amma ina she's weak haka ta koma ta fada shakaf kan gado tun tana ganin biji biji har idanunta suka rufe ruf......


Kuyi hakuri da wannan😛😛

No comments: