Tuesday, 29 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 29

 YAR AGADEZ



                 {Page 29}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



This page is for you Hafsat Kabeer your comments are always on point🔥❤️😅thank you🥰🥰



Wasu marukan ya sake sauke mata kafin ya fara maganar a fusace yana nunata da yatsa, "Wallahi kinyi karya! Kuma kazantar rayuwarki tayi kadan! Ke har kin isa ki bude baki ki kalli matata ki jefeta da wadannan munanan kalamai mafi muni? Kaskantacciya irinki ke har kinyi isar da zaki kalli matata ki kirata mai kisan kai? To wallahi baki isa ba kinyi karya don haka maza maza ki tattara kayanki da duk wani abu da kikasan dashi kikazo gidannan ki fice ki bamu wuri, wawuya butulu shashasha kawai!" Kafin sarki ya ida rufe baki Zubaida ta nufi wajen da kayanta suke, babban akwatinta ta dauko ta bude ta dinga jefa kayanta ciki, yanda zuciyarta ke tafasa da kuna kamar ranta zai fito tsabar bakin ciki, hakanan ta daure tama kasa tsaida kukanta don ta lura da wata dariya da Umma ke mata irin ta victory dinnan, bayan ta rufe akwatin ta dauko hand bag dinta ta saka wasu abubuwa da zata bukata, sauraren zagin da sarki ke mata takeyi kamar ta fasa ihu, tazo zata fita bakin kofa kenan taji ya tsaida ta "Tsaya malama! Ina zakije da wannan katon akwatin? Ko hand bag din dake hannunki a nan gidan kika sameta, da kayan dake ciki, abinda kawai kikazo dashi gidannan wasu tsummakora ne kwaya uku kacal tsabar talauci!" Wata dariyar takaici tayi ta juyo ta hada ido da Umma, "Ka tambayi matarka ita tasan duka kayan dake ciki da kudina na siya, i mean kudin da matan governors suke biyana ladar aikin da nake masu all thanks to your wife tasan manyan mata, i have the luxury by my self, and by the way Hajiya Karimah zan dauki motata da aka bani bayan na dawo da Japan don idan na sa kafa na fita bazan sake dawowa garinnan ba har abada, ranka ya dade rana da zuwa da duk zaka tuno da maganganun dana fada maka a lokacin ne na maku nisa ballantana ka nemi gafarata, all the same na yafe maka saboda ba laifinka bane tana juyaka ne son ranta amma akwai ranar kin dillanci, bissalam." Ko juyowa batayi ba ta fita daga dakin hawaye kuwa kamar an bude pampo, haka taje inda ake aje key din motoci ta dauki nata kafin ta fice daga gidan gaba daya.

Bakin wani daji tayi parking tana fitowa ta duka a nan ta fasa wani irin ihu ita matsakarta shine bakin paintin da Karimah ta goga mata, a hankali ta fara kuka tana dana sanin haduwarta da Karimah, ta kuduri zata gyara rayuwarta InshaAllah. 

Sarki kasa ta6uka komai yayi ya fito daga dakin duk ransa a dagule, tsayuwa yayi a balcony yafi minti talatin yana tuno da maganganunta, fita yayi daga balcony din ya nufi dakinsa direct ya rufe ya nemi privacy daga dogari, a ransa sai yake ganin kamar fa gaskiya Zubaida take fada don tafiye tafiyen da takeyi na menene tana baiwa? Yanzu daya koreta ina zataje? Kamar an dasa shi a wurin haka yayi jugum ya kasa kwakkwaran motsi. 

*****

Zarya takeyi cikin dakinta sai kai kawo takeyi ta rasa inda zata saka ranta abubuwan data fada a gaban sarki sunfi komai daga mata hankali, kawarta ce mai suna Larai tace "Haba Sarauniya Karimah ban taba tunanin zafin ranki ya kai har haka ba har kije ki aikata wannan abun ba, yanzu wane irin warning ke ban maki a kan wannan yarinyar ba? Tou yanzu danaje malamin cewa yayi in har kika bari tayi tozali da danginta asirin mu ya karye bama wannan kadai ba harda wannan kika yi wa sarki, asirinki tonuwa xaiyi tas, yanzu abunda mukayi ta mance ita wacece da ta tafi ta gano asalinta fa? Tou Wallahi sai kisan nayi nidai banida asara ke kika jiyo ma kanki." Tunda ta fara harkar nan bata taba ganin wanda ya kawo mata nasara ba kamar Zubaida yanzu in ta rasa ta ya zatayi? Don dole tabawa Larai kudi masu tsoka akan ta tsaida mata wannan gobarar dake neman tashi da ita, "Nasan InshaAllah ma babu abinda xai faru! Bazata hadu da kowa ba, ba kince Chad take ba? Tou nasan hankalinta bazai taba bata can ba saidai cikin Agadez ko Mali dai zatayi tunani ko tabar kasar gaba daya, yanzu nikam ya zanyi da her excellency? Sai kirana takeyi akan lallai lallai gobe in turota." Hankalinta duk ya gama tashi, wani irin tsakin takaici Larai ta saki, "Mts wannan ay duk mai sauki ne, kawai kice mata yarinyar ce batada lafiya, ta turo maki kudin jirgi da komai xaki turota da taji sauki." A haka sukayi sallama nan take Umma ta kira matar ta shaida mata, sam bata nuna rashin jin dadinta ba nan take ta turo wa da Umma da makudan kudade wai a kaita asibiti da kuma sauran kudin magani hade da siyayyar kafin tazo. Daya daga yaranta dake Mali ta tura ma ta tura ma hoton Zubaida wai a bincika mata ita. A bangaren Zubaida kuwa tunda ta bar gida gararamba takeyi ta rasa inda zataje a cikin mota take kwana, kuka kuwa babu irin wanda batayi ba ko kango ne gidansu zata je ta zauna a haka, saidai ta shiga wannan eatery taci abinci ta shiga waccan. Da daddare wajen 8pm ta tsaya wata eatery ta siya abinci amma kasa ci tayi ma, da kyar taci loma biyar ta mike ta biya ta fita cikin mota ta koma ta zauna don a nan ne gidanta. Nan tazauna ta dunga bin mutanen da kallo yadda suke annashuwa, wasu families ne wasu harda yara, wasu saurayi da budurwa wasu friends, take taji damuwa ta dawo mata cikin rai sabuwa fil take ta fara kukan bakin ciki.. duk tunaninta bai wuce inda zata samu matsugguni ba, tasan dai bamai taimakonta a wannan marra, idan tace ta kama gida ma bata tsira ba dama kowa kallon yar iska yake mata. Batada madafa haka zalika batada kowa a halin yanzu sai Allah, ana haka taji an haske tada fitila gabanta ya yanke ya fadi bata ta6a jin tsoro ba irin na yau, motar tayi parking ta gabanta, duhu bata ganin mai fitowa nan Zubaida tayi tsuru tsuru, knocking glass din window din akayi kamar bazata bude ba can dai ta bude, glass din ta sauke gaba daya a take sukayi ido hudu da yayarta Sadiya, wani irin kallon tsoro suka bi juna dashi, Sadiya ce ta fara girgiza kai tana kara damke hannun mijinta dake cikin nata, wannan ba Zubaida bace, Zubaida batada kudi, batada mota, Zubaida bata shigar yan gayu, tasan a matsayin baiwa aka kaita agadez gidan sarki how come? "Sadiya lafiya?" Mijijnta ya furta sai a lokacin hankalinta ya dawo jikinta kuka ta fara yi iya karfinta "Sadiq Zubaida ce! My one and only sister, ita kadai nakeda, amma anya wannan itace Zubaida? Taya ta xama mai kudi?" Bata jira amsar shi ba kawai taje ta bude motar inda Zubaida ke zaune kamar an dasata a wurin babu abinda ke motsi a jikinta, wasu fresh memories ne suka dawo mata kamar ana kunna mata tv tun daga lokacin da aka tura ta a matsayin baiwa har yanzu datake a gaban Sadiya har time din da suna yara ta hango cikin kanta, ta shekara ba iyaka tana kokarin tuna ko ita wacece amma yanzu tashi daya memory dinta ya dawo, mikewa tayi a hankali ita kuwa Sadiya cikin kuka ta fada jikinta sai a lokacin Zubaida ta saki wata atishawa mai karfi kafin tabi jikin Sadiya luu... da kyar Sadiq ya lallaba Sadiya kafin ya samu ta kama mashi Zubaida suka sata a mota, duk abinda ke cikin motar Zubaida sai da suka dauko shi ya kuma biya daya daga ma'aikatan wurin suka tuko masa motar. Tunda suka kama hanya Sadiya ke razgar kuka ya dade dajin labarin Zubaida wajenta kusan kullum sai tayi kuka akan itadai Zubaida bata san halin da take ciki ba tana so ta ganta, duk wani labari akan Zubaida ta masa so yasan how close they're, a lokacin da aka rabasu ta karfi aka tafi da Zubaida ita kuma Sadiya aka kaita aikatau, su marayu ne basuda uwa basuda uba. Bayan sun isa gida Sadiya ta kama ma Sadiq suka shiga da ita gida, tanaji ya gama shigo da kayan amma ko motsi Sadiya batayi ba, sai bayan kusan minti talatin Zubaida tafarka babu abinda bata gani ba cikin idanunta kuka ta fashe da shi saboda ta dauka duk mafarki ne, "Aunty Sady...." sunan da take kiranta dashi kenan, da kyar Sadiq ya lallabasu suka daina kukan nan, Sadiya ce tasa Zubaida ta shiga tayi wanka tasa kayan bacci, ta rama sallolinta sannan suka zauna don bada labarin bayan rabuwa "Wace irin rayuwa kikayi living? Naga kinyi aure kin auri mai kudi?" Sadiya ta gyada kai, "Bayan an kaini aikatau Allah ya hadani da mutanen kirki matar gidan na masifar sona ke in takaice maki labari dai itace ta hadani aure da danta..." Zubaida tace "Allah sarki kinyi sa'a fa, amma dama nan aka kawoki aikatau na dauka kina Chad?" Tace "Nan aka kawoni...."

She can't believe Aunty Sady tayi aure harda ciki, "Zubaida what happened to you? Don Ba Zubaidar dana sani bace ba." 

Numfasawa tayi "Ana kawoni  a matsayin baiwa na manta wacece ni Aunty Sady... Nadai san bayan nazo ta bani juice nasha tou daga lokacin na manta wacece ni, sunana kawai nasani amma bayan nan I don't remember who i really am...." tiryen tiryen ta fara ba Sadiya labari duk kasashen data je da kalar rayuwar da tayi, harda kayan data siyo kowane kala biyu take siya she just felt something is missing a part of her.... kuka sukeyi rungume da juna har karshe inda Sarki ya koreta, kuka sukeyi kamar ransu zai fita, sunsan ba komai bane ya jawo masu sai rashin iyaye amma sun dauke shi a matsayin kaddara, tun suna kuka har abun ya koma labari sunyi,  sometimes suyu dariya sometimes suyi shedding tears, karshe Zubaida ta kori Sadiya ta tafi wurin mijinta, share hawayenta tayi ta shiga bathroom ta wanke fuskanta kafin tazo ta kwanta cike da tunani kala kala...

*******

A hankali friendship dinsu ya rikede ya koma soyayya, tun lokacin da itama Khadija ta fahimce soyayyar Ashraf ya mata katutu a cikin ta fara neman hanyan da zata ja hankalinsa gareta, kuma a iya fahimtarta ta fahimci soyayya suke yi da Zarah, kullum sai ta rufe kanta cikin daki taci kukanta ta koshi, gashi ta kasa controlling kanta kishi take neman yi da yar uwarta ta jini wacce itama tayi nisa a soyayyar Ashraf, Zarah sam batasan me zuciyar Khadija ke ciki ba tadai fahimci idan ta gansu tare suna fira take mood dinta zai chanza koma ta tashi ta bar wurin. 

Wata rana da yamma Zarah ta dawo daga gidan friend dinta tana shigowa tsakar gida ta hango Ashraf zaune shida Khadija wacce ke faman son yi fira dashi amma da alama hankalinsa baya kanta kwatakwata, murmushi ta kakalo tace "Yaya Ashraf tun daxu fa nake ta faman yi maka magana amma ka gagara kulani, wai me nayi maka?" Hannu ya daga mata alamun ta dakata "Can you please keep quiet? Ina duba abu a nan ne kuma idan kina mun magana kina distracting dina." Wani kululun abu ya tokare mata makoshi, takun Zarah sukaji Ashraf ya daga ido ya kalleta "Assalamu Alaikum..." ta fada fuskarta dauke da kyakkywan murmushi, shima murmushin yayi mata yace "Wa'alaiki salam Fatima Zarah...." ledar dake hannunta ta aje bisa center table din dake tsakiyarsu ta fara kokarin fiddo abunda ke ciki, "Donut na siyo maku kuma glazed ne kaji dadinsa kuwa?" Yace "Da gaske? Thank you babe." Bude box din tayi tace "Am coming." Ta nufi ciki, can sai gata ta fito da cups da kwalin juice a hannunta, tana zuwa ta aje cups din guda uku ta zuba ma kowa nasa ta zauna tana kallon Ashraf "Yaa Yasir ya fita ne?" Yace "Ya fita zance tun daxu." Tayi dariya "Tou meyasa baka raka shi ba? Ya kamata ay kaje kaga masoyiyar tasa ko?" Shima dariyar yayi "Kinsan kishin Yasir kuwa? Ay bazan fara binsa ba..." tace "Har ya kaika?" Yace "Yama fini, saidai idan akanki ne tou fa nafisa kishin nan..." Khadija wacce keshan juice sai kawai suka ji ta fara tari alamun ta kware Zarah tayi saurin bubbuga mata baya "Subhnallah Khadija are you okay? Bari a kawo ruwa sorry." Tsaida ta tayi "A'a am fine bari na shiga ciki na sha...." ta fada tana kallon Ashraf wanda ke mata sannu ta mike tayi ciki sauri, ta window din dakinta ta tsaya tana binsu da kallo zuciyarta na tafasa kamar garwashi, wani irin nishi ta farayi ganin yadda Ashraf din ko kallo bata ishe shi ba yake bin da Zarah da kallon soyayya, kasa jurewa tayi take ta silale a tsakar dakin jikin bango ta hade gwiwarta ta saki wani irin kuka, "Innalillah wai meke shirin faruwa dani? Am I in love with my sister's boyfriend? It can't be! I can't do this to her, she's my sister I don't want to hurt her, amma kuma ina sonsa ni fa tawa zuciyar? Bazan iya controlling kaina ba, ya zanyi?" Kuka take bil hakki kamar wacce aka aiko ma da sakon mutuwa, ta kai awa daya a haka kafin ta mike ta shiga bathroom tawanke fuskanta ta fito, kamar daga sama sai ga Zarah ta shigo fuskarta ta kasa daina murmushi dauke kai Khadija tayi tana jin wani irin bala'in kishi na turnike ta, dafata Zarah tayi "Tarin ya tsaya? Meyasamu idonki Khadija? Did you cry?" Girgiza kai ta shiga tana share hawaye tace "Zarah tambaya nakeso na maki?" Zarah ta zauna gefenta tace "Ina jinki what's going on?" Khadija tace "Wata friend dina ce take tambaya na wai she's in love with a guy, tou Akwai sister dinta itama same guy dinnan takeso, shine take tambaya me zatayi shin ta bar ma yar uwarta saurayin ko kuma she should go for him?...." shiru Zarah tayi kafin ta numfasa "Wannan shi ake kira kwamacala, but in my own opinion they should let the guy decide a cikinsu wa yakeso, wacce baya so a cikinsu sai ta hakura dashi..." Khadija tace "Ni friend din tawa tace man bazata iya hakura dashi ba idan har ta rasa shi zata iya mutuwa..." Zarah tace "What if ita yakeso? Sai dayar ta hakura..." Khadija tace "Tace man dayar yakeso ba ita ba, and she can't lose him...." Zarah tace "Tou gaskiya I don't know, banida  amsar tambayar nan taki Khadija, abu daya zan iya cewa saidai daya zata iya sacrificing ta bar ma daya, tunda sisters ne..." Khadija tace "Put yourself in her shoes Zarah ke zaki iya yin haka?" Gaban Zarah ya wani buga tace "What do you mean? Meyasa xan alakanta kaina dasu? Ay mu bai faru damu ba so stop asking me that question Khadija, you're my blood sister bazaki taba son abinda nakeso ba, haka nima kuma bazan so abinda kikeso ba...." Khadija tace "Am saying what if a misali nake maki just answer me yes or no?" Zarah tace "Please stop it Zarah, this is not a joke..." Khadija ta mike tsaye "Amma yanzu kika gama cewa daya ta bar ma daya Zarah, now ke meyasa kika kasa amsa man tawa tambayar don nayi comparing dinsu dake?" Zarah tace "Saboda am not in their shoes, please stop it Khadija..." ta fada tana mikewa tsaye kirjinta na dukan tara tara... "Am in love with yaya Ashraf Zarah..." wata irin juyowa tayi tana  bin Khadija da kallo daka kalli kwayar idon Zarah kasan ba karamin girgiza tayi ba, "Me kika ce? You're in love with who?" Khadija tace "Yaya Ashraf, I love him so much don Allah ki taimakeni ki bar mun shi bazan iya rasa shi ba..." wani irin wawan duka kirjin Zarah yayi kasa tsayuwa tayi ta zube kan gado tana girgiza kai, da sauri Khadija ta zube gabanta tana zubar da ruwan hawaye "Ki taimakeni Zarah, nasan cewa kina sonshi kema, but wallahi nima am madly in love with him...." ta fada tana dafa kafafun Zarah, wani irin hawaye suka zubo ma Zarah, a hankali ta cire hannun nata ta mike tsaye da sauri tana goge hawaye "I wish zan iya hakura in bar maki shi but I can't Khadija, tun farkon zuwansa gidannan na kamu da kaunarsa duk da cewar lokacin he's heartbroken amma still na jure na raini soyayyarsa a cikin raina sai yanzu da ya fara accepting dina kawai sai kizo kice in bar maki shi Khadija? How is that even possible? I can't wallahi....I really can't am sorry..." tana gama fadan haka ko tsayawa kara kallon Khadija dake durkushe a kasa tana kuka batayi ba dakinta dake gefen na Khadija ta shiga tasa key da sauri ta silale a kasa, wani irin kuka ta fashe dashi mai ban tausayi "Why Khadija? Meyasa kika bari zuciyarki ta kamu da son masoyina? Kinyi ganganci gashi nima ina sonsa bazan iya hakura dashi ba, ya fara accepting dina I started enjoying his company, He's beginning to be happy around me, meyasa zaki bari zuciyarki ta yaudareki Khadija?" Kuka take harda shesheka yanzu wazata fadawa damuwarta? Gashi Mummy tayi tafiya kuma ko tana nan tasan zatace ta hakura ta bar mata shi, zatace ay kanwar tace, then what of her? A hankali taji ana bubbuga kofar dakinta "Zarah don Allah ki bude min kofar nan muyi magana, idan baki bari munyi magana ba zan rabu dake inje in kwaci soyayyarsa in rabaku don haka ki bude!" Zarah najin haka ta tsaida kukan da takeyi ta mike tsaye da kyar ta bude mata kofa, kallon Khadija tayi ta koma  kamar wata mahaukaciya kwalli duk ya bata mata fuska, rike shoulders din Zarah tayi pleading her tana kuka kamar ranta zai bar jikinta, "I love him Zarah, I love him so much, tun ina boyewa har yanzu na kasa banso na kasa jurewa ba amma ya zanyi? Abun yafi karfina! You are my only hope? Remember da muna yara? Kinsha bar man abubuwa kici girma kin tuna? Ko a school you always took care of me you loved me so much, yanzu ma meyasa bazaki iya bar man ba?" Hawaye suka cigaba da kwarara daga idanun Zarah "That was before Khadija, yanzu ba daya bane, I have no control over this, kiyi hakuri baya sonki ni yakeso, ke kadai ke sonsa shi baya sonki in return..." wani irin kuna zuciyar Khadija keyi kamar an zuba mata garwashi "Ki daina fada man baya sona it hurts! Na lura bazaki bar man shi ba ko? Do you want us to start a war?" Da mamaki Zarah ke bin Khadija da kallo "What are you saying Khadija? Bai kamata a kan saurayi kina fada mun haka ba! You're my sister for goodness sake, I beg you ki bar maganar nan ki aje makaman yakinki wannan fa ba doguwar magana bace! I told you he has accepted me mun fara relationship ta yaya kike zaton rana daya ya fara sonki? Karki bari soyayya ta rufe maki ido alakar dake tsakaninmu ta lalace a banza...." Khadija ta tsaida ta "Tou in bakiso ta lalalce ki rabu da Yaya Ashraf..." ta girgiza kai "I can't Khadija, I wish I could dana hakura amma kisani soyayya ba abu bane mai sauki da za'a ce ka cire ta a ranka rana daya ba...." daga mata hannu tayi "Well then, idan bazaki iya hakura ba then let the war begins! I can go to any length to get him and to love me you know I can do it, don't underestimate me Zarah, tunda bakiso ayita ta lalama then am ready to fight this war with you, mark my words sai na auri Yaya Ashraf no matter what it takes!" Tana gama fadan haka ta juya a fusace zata bar dakin da sauri Zarah ta riko mata hannu wasu sabbin hawayen na kuma taruwa a idanunta tana girgiza kai idanunta cikin na Khadija itama haka Khadija ta tsaya tana kallonta cikin ido, kafin Zarah tace....

*******

A 6angaren Umma kuwa tun ranar data kira Larai sukayi magana ta nufi gidan wata kawar huldarsu, a nan ta iske an kawo wata tsaleliyar budurwa tou yau aka kawo mata ita har gida, dalilin kenan data tabbatar da cewar sarki baya nan ya tafi farauta cikin daji, kuma ya kan dade a can wani lokaci har awa uku zuwa hudu bai dawowa, tunda taga tasamu dama sai kawai suka baje a dakinta suna sharholiyarsu, bayan kusan awa daya suna cikin alfasaharsu kawai taji an banko kofa, a duniya bata taba zaton zataji tashin hankali irin na yau ba, ganin da sarki yayi mata cikin Wanann siga ba karamin kidimata yayi ba, take ta fara kyarma tana mai tunanin kalaman malaminta "Sarauniya Karimah koda wasa karki bari ya kamaki cikin wannan siga, dan ke kinsan aikin da mukayi mashi shekara da shekara idan yau duniya zata taru a kanshi tace ga abinda kikeyi ina mai tabbatar maki bazai taba yarda ba! Ke ko ke da bakinki kika fada masa ba yarda xaiyi ba balantana ma a fada masa amma da zarar idanunsa suka gane masa zahiri toh illahirin asirin da kikayi ya karye har abada, sannan da sharadi zaki iya haukacewa ko ki kamu dawani deadly ciwo saboda ke kinsan aikin nan na aljannu ne karki bari ki ketara masu doka wallahi ki kula!" Da sandar dake hannun sarki, da wani littafi dake hannunsa yana nazari da kanshi sarkin tare suka fadi rigib kasa a bakin kofa, idanushi akan Umma ko kyaftawa baiyi, da sauri itada yarinyar suka suturta jikinsu kafin yarinyar tayi sum sum ta fice daga dakin, kamar wacce kwai ya fashe mawa a jiki haka ta silalo da rarrafe ta zo inda yake zaune rigib kasa hawaye kawai ke fitowa daga idanunta, "Karimah meyasa? Meyasa zakiyi man haka?." Ya fada hawaye na zuba daga idanunsa ji yake kamar ranshi zai fito ya huta da wannan bakin cikin da takaicin... giirgiza kai ta farayi ta fara bashi amsa "Jalal tun kafin na aureka nakeyi, bansan ya zanyi in daina ba na kasa hana kaina, kayi haku...." wani mugun kallo yake mata "Mena tare maki? Duk wani hakkinki dake kaina ina kokarin saukewa, ki rasa wanda zakibi sai mace yar uwarki? Dama abinda baiwarki take fada rannan gaskiya ne? You ruined their life, why did you do this to me? Why?" Da akwai yadda mutum zai fiddo zuciyar shi fa yau Jalal sai ya fiddo tasa komai ya tsaya masa cak, "Now tell me did you kill my wife?" Hannu ta kai zata tabashi yayi saurin janye jikinshi "Just answer my question did you kill her yes or no?" Da hanzari ta fara daga kai "Nina kashe ta years back, wallahi kishi ne kawai bawani abu ba, saboda kai nayi don ta bar man kai...." wani irin wawan mari ya dauke ta dashi hagu da dama cikin zafin nama ya shako mata wuya "So you're a monster as my daughter always told me, amma da yake bakin alkadarinki yana yawo a kaina na kasa gane komai, I always overlooked your mistakes and forgave you! Ashe da bakar muguwa nake zaune, kin rabani da matata mai kaunata tsakani da Allah ke ba sona kike ba, you are just after my sarauta and money!" Mikewa yayi har hannunshi kyarma yakeyi idanunsa jawur wane garwashi yace "Karimah kije na sake ki saki uku, ki tattara duk wani abu da kikasan naki ne ki bar man gida, na baki awa daya kacal ki kwashe kayanki ki fice man daga gida! Idan na dawo na iske shi cikin gidannan duk abinda nayi maki ke kika ja, bazan hukunta kiba amma kisani na bar komai a hannun Allah shi yasan yadda zaiyi dake!" Kuka take har wani shidewa takeyi tana wani irin ihu kai kace sabuwar mahaukaciya, fita yayi bai ko kara kallonta ba zuciyarsa na kuna, Karima na nan tsugunne inda ya barta tana kuka kawai sai jinta tayi tsamo tsamo cikin jini, da sauri ta mike ganin yadda jinin ke kwarara ba karamin tsoro taji ba "Innalillah wa inna ilahir rajioon, meke shirin faruwa dani? Kardai maganar malamin nan daya fada har ya saka man cutar?" Ganin jinin da gaske ba tsayawa zaiyi ba yasa ta samo pad ta saka ta gyara wurin da kyar take jan kafa sai binta da kallo mutanen cikin gidan sarkin sukeyi, bata damu ba itadai burinta taje asibiti, da isarta ta samu ganin wani Doctor ta masa bayanin abinda ta gani kuma tace masa ta wuce menopause sheyasa tayi mamakin ganin jinin, tests ya rubuta mata kala kala taje tayi da scans, bayan tayi ta dawo tana fuskantarsa gaba daya hankalinta a tashe yake ya soma warware takadar, kana hango tashin hankalin da Doctor din ya shiga yana bin takardar da ido, gabanta ya wani buga tace "Me aka gani a ciki?" Shiru yayi na dakiku kafin a hankali ya fura "Am sorry Hajiya result ya nuna mana kina dauke da Cervical cancer, tumor ce ta kasanki sheyasa ma kika fara bleeding, ta dade tare da ke baki farga ba sai yanzu data fara showing signs and symptoms...." mikewa tayi tana girgiza kai hawaye na shatata daga idanunta "No no it can't be, not me...." wani irin ihu ta kurma take ta zube kasa....

No comments: