Thursday, 24 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 24

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 24}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Cak ya tsaya yana kallonta jikinsa kaf babu inda baya kadawa, abinda yake gani cikin idanun Hoodah ba karamin tsoro yaji ba da alama dai ta matukar zuciya, fushin da yagani bawai abu bane da zai iya kawar dashi lokaci daya yana bukatar lokaci. "Hoodah please listen to me, don't blame me for everything that has happened zuciyata zata iya daukar komai amma banda fushinki, will you listen? Wallahi bansan meya shiga kaina ba Habibty kamar wanda ake controlling haka na koma... like I have no control over me anymore."  Gaba daya ya rasa ma abinda zai ce mata anymore. Ko kula shi batayi ba ta fara kokarin sauka daga kan gadon, ta wani fizge drip din dake hannunta take ya fara digar jini ko damuwa batayi ba ta wani cire oxygen din very painful, saidai duk wani external pain din da take ji bai kai ciwon da zuciyarta ke mata ba ta shafe komai. "Ba sai kabani hakuri ba Sultan, I don't care anymore, idan kaso aljana ma zata iya controlling dinka I don't care." Tana gama fadin haka ta dafe gadon don biyu biyu take gani ta zura takalmanta ta fara tafiya tana hada hanya hawaye kuwa kamar an kunna pampo. Wani irin wawan riko yayi mata da tilas sai data fada jikinshi, ganin yadda take kokarin fizge jikinta daga gareshi tana wani irin gunjin kuka, yasa a tsorace ya kara riketa gam gashi daga gani ko karfin arziki bata dashi "Ina kuma zakije with this condition Hoodah? Can't you see you're sick and weak?" Ya fada cikin confusion don zuwa yanzu yama rasa abinda ke masa dadi ya rasa ta cewa "Zan tafi duk inda Allah ya kaini, meye amfanin zamana a asibiti? Ciwon da nakeji a jikina bai kai ciwon daka dasa man a cikin zuciyata ba Sultan, you hurt me deep it's damn painful, and kar ka damu I will be ok by myself you don't have to worry." Tana gama fadin haka tawani fizge jikinta daga nashi ta bude kofar fita baki daya a guje kamar wacce aka koro, cikin hanzari Sultan ya bita amma da alama dai Hoodah ta gudu tama fita daga asibitin, kudin asibiti ya biya yayi masu bayanin cewar Doctor ya maida marar lafiyar a gida zata karasa jinyarta a can, da gudu ya fito kamar wanda aka ce yazo yaga gawar Hoodah, nan fa ya hau dube dube babu inda bai duba ba kaf asibitin nan babu alamun Hoodah, har dai waje ya dinga bi yana dubawa amma bata nan, nan ya hau mota cikin hanzari ya hau titi, cikin sa'a ya hangota bisa mashin cikin go slow in banda kukan fitar rai babu abinda takeyi kuka take iya karfinta har mutanen dake bisa ababen hawa suna binta da kallo, babu damar da zai sauka haka ya dinga bin mashin dinnan, wani lokaci su bace masa ya bar ganinsu sai anzo wani junction din suke sake haduwa, ya dinga kallonta hawaye cike a idanunsa ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya surota daga kan mashin dinnan, kukan da takeyi ba karamin affecting dinshi yake ba haka yakejin kukan nata har kasan ransa, ji yake har wani sukanshi yakeyi cikin rai gaba daya hawayen nasa ma ya kasa rike su nan suka dinga saukar masa yana hade wani abu kamar madaci, ganin da gaske Hoodah duniya zatabi kamar yadda ta fada yaga an ajeta cikin wani daji, tana sauka taga babu wasu kudi a hannunta nan ta bar mai mashin tsaye yana jira ta bashi kudinshi, mamakinsa bai wuce yar sarki ba a haka saman mashin? Anya lafiya kuwa? Ita kuma a hankali ta juya ta fara tafiya cikin dajin nan gefen mai mashin dinnan Sultan yayi parking ya fito ya biya shi kudinsa, cike da tsoro da kuma fargaba ya fara binta a hankali kar dai ace kashe kanta zatayi? Take ya dinga binta a tsorace, wani wuri yaga ta tsugunna hade da rungumo gwiwarta, kuka takeyi irin wanda ke girgiza dan adam, ya kusa minti goma yana kallonta tana wannan kuka ita duk a tunaninta ita kadai ce a wurin, tasan yanzu ko tsafi takeyi bata isa ta koma gida ba, tasan halin Umma sarai ita yanzu ko fuskarta ma bata son gani, tasan idan ta koma to tabbas babu abinda xai hana Umma kashe ta, ganin kukan nata yayi yawa gashi bawani isassar lafiya gareta ba yasa Sultan ya matso kusa da ita sosai, bai tsaya wata wata ba kawai ya sureta tana shure shure tana dukan kirjinsa shi kuwa bai damu ba kawai ya bude mota ya saka ta a ciki, da sauri ya zagaya ya shiga ya danna lock driver ya jasu, ko tanka shi batayi ba don gani take ma yi masa magana bata baki ne, abubuwan da yayi mata ba karamin ciwo sukayi mata ba, gaba daya zuciyarta ciwo takeyi, tun tana ganin hanya sama sama har baccin wahala ya kwashe ta. 

Bata kara sanin inda kanta yake ba saidai ta farka tagansu cikin garin Niamey, bude ido tayi taganta cikin wata motar daban nan tafara kallon garin kamar yaune zuwanta na farko, da mamaki ta fara bin garin da kallo ganin har dare yayi da alama ma har isha'i angama, har suka iso gida babu wanda yace koda uffan ne a cikinsu, parking driver din yayi, yayi unlocking dinsu, Sultan ya fito ya zagaya ta gefenta ya bude mata kofa yace ta fito, wani irin mugun kallo ta watsa mashi ko gezau batayi ba ba ma tada niyyar fitowa, "Hoodah magana fa nake maki? Nace ki fito mu shiga gida." Hawayen da suka taru a idanunta ta maida "A lokacin da babu abinda nake so face zama gidannan me kayi man Sultan? Fitar dani kayi as if I mean nothing to you, don haka yanzu bana bukatar zama a gidanka, nasan banida inda zanje amma kuma bazan zauna gidannan ba anymore ka kaini hotel." Kallon mamaki ya bita dashi  "Hoodah nan fa gidan mijinki ne! Bakida inda yafi nan a halin yanzu, ki fito kishiga nace," tabbas zasu iya kwana a haka yanayin yadda yaga tawani kafe, "Kai bakaji kunyar cewa gidan mijina ba? Ashe dama zaka iya zama da wacce ka tsana! Wacce bakayi trusting ba kace mai bin maza, mazinaciya! I am indecent ko? Wato ka auro karuwa." Wani irin wawan numfashi yaja "Hoodah kar ki kara kiran kanki da wadannan munanan kalamai...." bai karasa magana ba ta tari numfashinsa "Saboda me? Saboda ina tsoronka? Har ka manta me kace mun? Lokacin da Umma tace maka nayi ciki meyasa ka yarda? Har kake ikirarin you can't accept it? Wai me ka daukeni ne Sultan? Yar iska? Ko karuwa? Ko kuwa rashin yarda dani ne yasa ko me akazo aka fada maka akaina sai kayi saurin yarda? Na fada maka ka kaini hotel ko in sauka inje in hau taxi."

Abinda ya lura dashi shine Hoodah meant every word she said, bai kara ce mata komai ba kawai ya sureta ta cak ya shige da ita ciki nan driver din gidan shine ya zo dama tuni ya fita daga motan kafin su gama ya fito masu da akwatinsu ya bama dogarawa suka shiga da shi ciki, bai ajeta ko ina ba sai cikin dakinta, kallon dakin yayi take wasu memories suka dinga dawo masa, itama dakin take kallo take sai hawaye, nadama marar iyaka Sultan yayi duk da yanada tabbacin abubuwan da ya aikata bada saninsa bane wani abin kamar baida control a kansa ne, kasa tsayawa yayi cikin dakinta yadda gabansa ke bugawa kawai sai ya juya ya fita daga dakin bai kara tanka mata ba. Ta jima a zaune tana share hawaye sannan ta mike tana tafiya da kyar saboda weakness ta shiga bathroom tayi wanka, tana fitowa ta kimtsa cikin kayan bacci marassa nauyi nan taji cikinta na kugi ta mike ta nufi kitchen a nan ta iske shi yana soya sausages gefe kuma indomie ce ya dora har ta kusa tsanewa daga shi sai singlet da boxers, tana shigowa ta wani hade rai ta kauda kanta gefe don ita ko ganinshi bata son yi balle ma har taji soyayyarshi ta kara yin tasiri a cikin ranta. Tana ji yana mata magana akan ita yake ma abinci amma ko kallon inda yake batayi ba, wanke kettle tayi ta zo ta zuba ruwa a ciki ta kunna ta hada custard ta fita. 

Haka suka cigaba da rayuwa kullum sai Sultan ya shigo dakin Hoodah yafi a kirga amma ko sau daya ba zataji tausayinsa ba balle ma har ta daga kai ta kallleshi, ko a parlor suka hadu it's either ta latsa waya, ko tv ko kuma ta kirkiri baccin karya. Satinsu biyu da dawowa amma tunda suka dawo magana bata ta6a hada su ba, in ba gaisuwa ba Hoodah bata tanka masa, babu irin roko da magiyar da bai mata ba amma duk a banza, kullum bai fi kalma uku ke hadasu ba daga ina kwana? Ina wuni? Sai kuma sai da safe. Gaba daya Hoodah ta dawo gidan kamar wata stranger tace toh meye amfani ta cigaba da nuna mashi kulawa bayan bai yarda da ita ba? Sannan babu abinda yafi mata ciwo yadda yace ta hada kayanta kiri kiri ya nuna baya bukatar cigaba da zama da ita tace toh ay ba amfanin ma ta cigaba da kula shi, abinda kuma yafi mata ciwo fiye da komai lokacin da Umma ta alakantata da mai cikin shege wai he can't accept it? Wato kawai tana fada har ya yarda kenan? 

Kullum aikinta kenan daga kallo, latsa waya, tunani, azkhar sai bacci. Ta daina girki ta daina cin abinci, in taga dama ta sha custard ko tea, ko yoghurt su kadai take sha, komai ya siyo ya kawo mata in zai shekara rokonta taci bazata ci ba sai dai ya hakura, ko kallon banza ma bata mishi ballantana ma yasa ran zataci. Tunda suka dawo kuwa yama daina fita haraba, duka duka baifi sau uku yaje ba. 

Yau ma kamar kullum tana zaune kan dining ta hada custard tana sha a hankali duk ta kara ramewa tayi wani fau da ita, Sultan ne ya shigo da ledar take away a hanunsa har wani duhu yayi shima duk ya rame, tana ganinshi kawai ta mike ta dauki cup dinta da niyyar shigewa daki taji ya riko mata hannu, rabon daya tabata tun ranar daya nemi yayi hugging dinta ta rufe ido ta karta masa wani irin rashin mutunci, yanzu ma wani irin juyowa tayi a fusace tana jefa mashi wani warning look hade da fizge hannunta cike da tsantsar masifa amma kafin ta kai ga magana taji yace "Hoodah ina sonki, san da bansan adadinsa ba, bansan ya kike so inyi da raina ba please ki daina fushin nan da kikeyi ki yafe mun Hab...." kalmomin kasa fitowa sukayi a sanadiyar wani wawan tsaki dataja harara ta watsa mashi ta wani shige daki ta buga kofar da karfin bala'i ji kake garam! Har dan firgita yayi data banko kofar kuma ta danna mata lock, shikenan yau yaga ta kansa yasan bazata yafe masa ba ya riga yasani, tsaye yayi a wurin kamar an dasa shi yana bin kofar da kallo cike da mamaki gashi kuma ya kasa wani kwakkwaran motsi, shifa ganinta kawai yakeso yayi baice dole sai tace tana sonsa ba, ta tsaya ma ta sauraresa ta kuma gasgata son ta yake mata, wai shin dama haka soyayya take? Ashe dama haka soyayya take da ciwo? Take wani irin bakin ciki ya mamaye masa rai, tun lokacin daya fahimce ya kamu da sonta amma ya kasa yarda shine yayi tunanin ya dauke ta daga gidanshi yayi zaton zai daina jin abinda yakeji in bata kusa dashi, amma daga ranar da ya maida ita gida rayuwarsa ta tsaya masa cak, ya lura rashin gani nata shine mafi azaba daya taba dandana a ransa mafi muni ma kuwa, a haka dai ya daure kuka ne kawai baiyi ba komai ya chakude

masa cikin rai. First ganinta da yayi bayan ya maida ita gidansu ji yayi kamar an sauke masa wani irin katon dutse a cikin zuciyarsa take yaji bata masa nauyin da take masa da bata tare da shi, bai taba jin dukan zuciya kamar yadda yaji a lokacin, baisan abinda yayi holding dinsa back ba lokacin da Umma take dukanta dama kana jin kakasa kwakkwaran tunani wani lokacin? Gashi yanzu sun dawo karkashin inuwa daya amma ko kallon arziki Hoodah batayi masa ba, he needs her more than anything else in the world wani dan guntun kwalla ya goge kafin a hankali ya taka yaje bakin kofar dakinta....

No comments: