Thursday, 10 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 10

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 10}




To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Daya daga cikin kuskuren daya tafka shine daya bari Hoodah ta kufce ba, da kuma ya tafi ya bar family dinsa, ya bar yan uwansa da masauratarsa, tushensa, asalinsa da kuma zuciyarsa!

(Emotions, loads and deep emotions)...shine kawai abinda Ashraf ke ayyanawa a ransa, ya tsaya tsayin daka tare da family dinsa duk rintsi duk wahala duk abinda yafaru ya dinga dawo masa crushing his weak heart gaba daya yayi breaking down, dalla dalla, guilt, bakin ciki, fargaba ya dinga bin ko wane lungu da sako na jikinsa, bai taba tunani ko a mafarki cewar zai taba rasa Hoodah ba duba da yadda suka taso cike da hope na mallakar junansu amma rana daya tak komai ya ruguje kamar glass din da ya tarwatse kasa yayi breaking into pieces haka relationship dinsu ya tarwatse wanda baya tunanin zai gyaru, heart dinsa tana tare da ciwo kuma warkewarsa ba nan kusa ba, ba abinda ya zama sai prisoner din kansa da kansa tunda ya baro Agadez! Akwai shakuwa! Akwai farin ciki! Akwai kwanciyar hankali! Da kuma soyayya! Kwalla ya taru cikin idanunsa a yayin da yake tuna wasu abubuwa da dama, abinda yakeji yafi karfin rubutu... Wani abu ya tuna shekarun baya da suka shude...

"Yaya Ashraf...!" Yar kimanin shekara bakwai ce ta fito tana tafiya hannunta dauke da lollipop guda biyu, a hankali ya juya yana ganinta ya saki murmushi yace "Na'am Hoodah habibty...!" Ya durkusa daidai ita yana kallon cute fuskarta da dimple dinta wanda ke kara mata kyau idan tayi smiling, tace "me kakayi a nan??" Baiyi replying dinta ba sai ya tsaya yana kallon fuskarta yadda take tsotsar lollipop dinta... miko mashi lollipop din tayi dake dayan hannun nata wanda bata fasa ba tana murmushi sosai wanda ya kara bayyanar da cute dimple din nata, yayi murmushi "Wannan fa? Nawa ne?" Ta gyada kai "Nawa ne Abba ya bani shine na aje maka daya....." yayi murmushi "Wow habibty, amma fa gaskiya ni daya ya min kadan saidai ki hada dana hannunki wanda kika fara sha kibani..." shiru tayi jin abinda yace tana kallon lollipop din nata ta kasa cewa komai, gimtse dariyarsa yayi ganin yadda ta boye lollipop din nata bayan hannunta ta mika masa dayan "Wannan ne naka, wannan nawa ne..." ta fada tana turo dan karamin pink bakinta, sai yayi alamun fushi ya mike tsaye yace "Shikenan na gane rowa zakiyi man toh bazan ma sha ba gaba daya jeki shanye kayanki...." wai shi nan harda tafiya kamar gaske da sauri tayi wuff ta kamo masa hannunsa harda dan kwallanta ta hade lollipop din da nata da nashi ta mika masa "Toh na koshi gashi ka shanye duka..." baisan sadda ya saki dariya ba ya duka tare da dagule mata hanci "Wasa nakeyi habibty, da inada wani ma dana kara miki, amma ki bari zan siyo maki da yawa ki dinga tafiya school dashi..." ta wani daka tsalle tace "Thank you yaya Ashraf you are the best best best ever!" Yayi dariya "And you are also the best Habibty..." haka ya dawo daga duniyar daya lula lokaci zuwa lokaci yake goge kwallan dake gangaro masa, this feeling really hurts damn! Knocking yaji a kofa ashe an kai minti kusan ashiri ana knocking mikewa yayi yana kara goge hawayen idanunsa ya nufi kofar tare da budewa, Abokinsa ne Yasir wanda yake zaune a gidansa tare sukayi university abokinsa ne na kut da kut. Turus Yasir yayi bakin kofa da mamaki yace "What's wrong with you? Are you okay?" Ashraf yace "Yasir!" Ya daka masa tsawa yana mai rike hannuwansa duka biyun hawayen na cigaba da zuba daga idanunsa, da sauri Yasir yayi hugging dinshi take ya fashe da kuka kamar wani karamin yaro, "Yasir..." yace cikin muryar kuka "Ashraf please tell me what's wrong?" Runtse idanunsa yayi har ga Allah so yake ya manta da ita yasan ita yanzu matar wani ce bai kamata yana tunaninta ba amma ya rasa ta wace hanya zaiyi hakan, "I...i....ba....zan iyaba....!" Yasir yace "Menene?" Jikinsa na wani kadawa yana wata irin zufa yace "Ka taimaka man Yasir! Please help me!."

*********

Yadda yake rufe mata baki da hannunshi ba karamin razana tayi ba gashi ya matse hannayenta duka ya harde su wuri daya, girgiza kai tayi tana wani irin zillewa tanata kokarin maida hawayen idanunta hakan bai hana Sultan kara mata karfin rikon da yayi mata ba, ba karamin cikin tashin hankali ta shiga ba ita gaba daya yanzu tsoronsa takeyi. Daga karshe data kasa rike hawayen kawai saita hakura ta sake su suka cigaba da zuba freely kamar da bakin kwarya, janta yayi ya xaunar da ita kan kujera, wani irin tsoro ne marar misaltuwa yake shigarta har yafi wanda taji ranar da mutanen nan suka durar mata! Suna tafe inda zai zaunar da ita sai yaga numfashinta na sama sama tana wani irin gunjin kuka hade da shesheka irin kukan nan inka zuciya kake sakinsa, shifa kukan munafuncin nan ke baya so in har tana masa wannan kukan wahalar shi zata sha a banza. Wurgar da ita yayi saman kujera sannan ya taka daf da ita, girgiza mashi kai kawai takeyi hawaye kuwa kamar ana tunkudo su, ganin ya nufota gadan gadan sai tsoro ya dirar mata ko dai shima irin abun nan zaiyi mata da aka shigo mata, kodai shima irinsu ne? Sai ta fara kyarma take ta fasa wata irin razananniyar kara "Wayyo Abbana! Na shiga uku Abba ka cece ni! Dan Allah dan annabi kayi hakuri! Dan girman Allah! Wayyo Abbana na shiga uku!" Turus yayi cike da mamaki yana kare mata kallo "Meye haka? Bakida hankali ne? Wani abun kikaji nace zan maki? Me zanyi da kazamin jikinki?! So disgusting!" Ya fada yana mai juyar da fuska feeling hurt, wata irin tsawa ya daka mata mai razarnawa jin bata daina masa ihu ba duk ta cika masa kunne, take ta hade kukan nata sai dai yaga tayi shiru bata kara motsi ba idanunta na kallon sama, a tunaninshi duk cikin iskancin nata ne data tsiro dashi kwana biyu, tsaki yaja ya wuce dining ya zuba abinci bai kara bi ta kanta ba, can dai yace "In kina son zaman lafiya dani better confess ki bani hakuri a wuce wurin, amma na lura shegen taurin kai ne dake!" Saida ya gama cin abincinsa to his surprise yaji abincin yayi mugun dadi ashe ta iya? Yana gamawa yabi da pineapple and mango juice sannan yayi wani balancing ya fiddo wayarsa yayita chatting dinsa yana latse latse hankalinsa a kwance. Can ya saki guntun tsaki "Ina zaman zamana aka kakaba man wannan mugun aure, auren nan ko auren kaddara auren wahala! Mts!" Tsaki ya kuma ja cikin takaici ya mike zai shiga daki yaga tana nan yadda ya barta, yaga dai alamun ko kafarta bata motsa ba har ya kai cikin daki sai kuma ya dawo yana fadin "Wannan wane irin sabon iskanci ne haka Hoodah?" A kanta ya tsaya hannayensa harde yana kallon fuskarta wanda hawaye duk ya bubbushe mata, "Ke tashi kije kiyi clearing kan dining... wane irin sabon salon iskanci ne kika tsiro dashi haka?" A tsawace yake maganar amma ga mamakinsa sai yaga ko motsi batayi ba, "Lallai yanzu kuma raini kika tsiro dashi kenan?" Ya fada yana kada key din hannunshi "Zaki tashi ko kuwa one last chance! Wallahi karki bari raina ya kara baci!" Still dai shiru ko motsin kirki batayi ba, sai a sannan ya lura da yadda numfashinta ke tsaye cak kirjinta baya motsi, take hankalinshi yayi matukar tashi! Dukawa yayi ya kamo hannunta sai yaji shakaf hannun ya koma ya fadi, innalillahi wa inna ilahir rajioon! Zuciyarsa ta buga, cikn rudu ya kai hannunsa saitin hancinta yaji numfashinta bai fita, yar da key din hannunsa yayi a guje yayi fridge ya dauko katuwar kwalbar swan tsabar rudu baima san a bude ya bar fridge din ba, yana zuwa ya bude ya fara yayyafa mata a fuska, sam baiyi tunanin suma tay ba don shidai bai ta6a ganin anyi suma a haka ba, daya ga yayyafawan bazaiyi ba kawai sai ya juye mata shi gaba daya amma ina shiru kakeji Hoodah bata dawo ba, cikin rudu ya fara neman wayarsa a cikin gidannan yama manta shaf tana cikin aljihunsa, haka yayi ta watsi da pillows din parlorn ya daga wannan ya maida, ya bude can ya rufe, wata irin zufa ce ke keto masa can ya laluba wayarsa sai gashi ya ganta a take ya kira family doctor dinsu, nan Sultan yayi masa bayani abinda ke faruwa nan ya fadi mashi me zaiyi kafin ya karaso. Abinda Doctor din yace mashi shi ya fara yi mata, nade hannun rigarsa yayi with both hands ya fara daddana kirjinta amma duk a banza, can dai ya dage iya karfin yayi mata wani irin danna take tari ya sarke ta, baisan lokacin daya furta "Alhamdulillah." ba, ya wani saki ajiyar zuciya ya zauna dirshen kasa yana maida numfashi feeling relieved, tana ganin shi gefenta sai ta nemi ta kara birkicewa saboda gabanta ne ke cigaba da faduwa ba kakkautawa, Sultan ya lura tabbas tsoro takeji matuka, yasan idan mutum ya suma ba'a motsa shi in ba haka ba attack din zai dawo. Mikewa tayi da kyar tana dudduba jikinta taga me yayi mata? Ajiyar zuciya ta saki sai ga hawaye shar shar ta fara kokarin tashi tsaye ta kasa ga wani weakness dake kwasarta, ji take kamar zata kara suma. To her surprise sai ganin Sultan tayi ya koma da sauri kusa da ita, zatayi magana kenan kawai taji an janyo ta a hankali anyi hugging dinta yana saitata "Listen, karki tsorata nothing will happen to you, ki natsu Doctor yana hanya..." yadda yayi maganar cikin kwantar da hankali yaba Hoodah mamaki, sai tayi lamo ta samu kanta da kasa motsin kirki don ita bawai zata iya motsawa daga wajen ba she's weak, a kirjinsa ya kwantar da ita sun kai kimanin minti goma sai ga doctor ya iso sallama doctor yayi kawai Sultan sai ya tsinci kansa da zuwa daki dauko mata hijab, yana sa mata hijab din sai yaje ya bude ma Doctor din kofa ya karaso ciki, nan yayi yan duba dubensa ya fada ma Sultan cewa idan mutum ya suma ba'a jijjiga shi ko a zuba masa ruwa mutum ya farka hakan yana kara guddumuwa akan suman, "She had a panic attack! Ya kamata ka zauna ka tambayeta meke damunta, she should avoid it at all cost." nan ya bata wasu magungunan yace "Wanann zasu rage mata panic din don haka kar tayi wasa dashi ta dage tasha na kwana bakwai ne..." nan Sultan yayi masa godiya ya tafi, koda ya dawo isketa yayi ta bingire kan kujera tana ta bacci, tsaye yayi yana kallonta ya jima a haka yana shi kanshi baisan dalilin kallon ba, sai can yasaki ajiyar zuciya ya daga ta ya jinginar da ita bisa kafardarsa ya kaita daki, kwantar da ita yayi yace "Hoodah..." wani yar yaji daya kira suna nata,  ta dan bude ido kadan tace "Uhmm?" Ta amsa da kyar, hijab din ya cire mata ya lura sai zufa takeyi, sannan ya dinga ta6ata alamun ta tashi "tashi ki canza kayannan jike suke kar kiyi mura... ko so kike ki mutu ne?" A kasalance ta mike dankwalin kanta ta zame take gashinta ya warware ya baje bisa bayanta, hannu ta daga kamar wata yarinya ita sam ta manta da wa take ita bama muryar maza takeji ba ita duk a tunaninta Kaka ce. "kaka cire mun rigar please wallahi bazan iya ba na gaji..." cike da shagwaba Hoodah ke maganar tawani turo baki tsabar baccin da takeji... kallonta kawai ya tsaya yanayi innocently take maganar, sai kayi tunanin wata yarinya yar shekara goma ce, ganin dai da gaske bacci takeyi a haka dole yasa ya matso dab da ita, ajiyar zuciya ya sauke yanzu ya zai cire mata rigar nan? Kuma bazaiso ya barta haka ba sanyi yana iya kamata, daure fuska yayi yace "For the sake of Ummi," kafin ya fara cire mata rigar harda runtse idanu, Hoodah na jin an cire mata riga tayi wani luuuu ta fada kan gado ta cigaba da baccinta, tace "Thank you..." daga nan ko motsi bata kara yi ba sai numfashinta ya fara fita a hankali mai nauyi alamun bacci takeyi mai dadi. Sukuku Sultan yayi baki sake yake kallonta yau shikam yaga ta kanshi ya jawo wa kansa, gashi Doctor yace kar a bari komai ya takura mata har yanzu numfashinta bai dawo daidai ba, yanzu ya zaiyi ya cire mata bra fisabilillahi?!

No comments: