YAR AGADEZ
{Page 09}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Washe gari koda Hoodah ta farka ta kimtsa tayi wanka ta shirya tsaf, saidai fa kusan zaman minti 20 tayi cikin dakinta tana jero addu'oi tana fatan kar ya sake shigowa inda take don ita ko kaunar ganinsa batason yi, a hankali jiki a sanyaye tayi shahada ta dan leko kadan taga ba kowa don ta cewa bayinta su bata wuri ita kadai zata kwana gidan yau, don haka parlon babu kowa sai masu aiki daya na jera abinci kan dining daya kuma na goge tv stand, duk suka dago suka gaisheta da sauri ganinta tsaye tsakar parlor ta amsa a mutunce, bata ga alamar Sultan ba ko ta tambayi inda yake? Bayan sun kammala aikinsu suka tattara suka fita, dining din ta karasa don wata irin wahalalliyar yunwa takeji kamar tayi hauka. Ta zauna kenan tana tsakar serving ma kanta abinci taji an bude kofa, da sauri ta juya ganinshi tsaye bakin kofa directly idanunsa cikin na juna, yayi bal'ain yi mata kwarjini sanye yake cikin white shadda mai kyalyali marar nauyi ta amshi jikinshi tayi masa kyau ainun. Take tasha jinin jikinta yadda taga ya wani murtuke fuska dole ya sakar mata da wani irin tsoro da fargaba sai kace taga dodo. Wani siririn tsaki ya saki na jin haushin iyayenshi don su suka tursasa masa yazo duba ta, tabbas suna fushi suma saidai fa bazasu fasa duty dinsu na amanar da aka basu ba na kula da yar mutane, tunda sassafe Ummi ta hankado keyarsa don tasan d'an nata bai iya fushi ba ko kadan idan yayi fushi yakan kasa controlling emotions dinsa, don haka da lalla6a da nasiha ta samu ya yarda zaizo din, abinda tace dashi yana kai kawo cikin ranshi "Sultan bazamu taru mu zama marassa tunani ba, tabbas Hoodah bata kyauta ba amma kuma wani abu da ya bani mamaki bayan daka jata kun tafi sashenku sai kawai naji ba dadi, naji gaba daya jikina bai bani Hoodah zata aikata hakan ba, bansan dalili ba amma nidai haka nakeji, toh yau da safe sai na wayi gari na nemi fushin da nakeyi da ita na rasa, Yanzu abinda nakeso dakai shine ka daure ka tashi ka tafi wajen yar mutane, please go and check on har nasan ba sashen ka kwana ba, amana ce a wurin mu, bazanso ayiwa tawa yar abin da akayi mata ba...." ya dago yana kallon Ummi "Haba Ummi, bakiga me ta aikata bane da zaki ce haka? To nidai gaskiya bazan iya danne zuciyata ba na cutu she tarnished our reputation! It really hurts!" Ummi tace "I know, kayi hakuri komai mai wucewa ne, nidai just go to her do it for Ummi..." gyada kai yayi ya mike ba don yaso ba ya nufi sashen nasu...
Da sauri ta dauke idonta daga kanshi ta dukar da kanta kasa feeling hurt kwalla cike idanunta, a hankali ya tako inda take da kyar kamar ya koma yakeji, wani mugun kallo yake watsa mata ita kuwa idonta na kan plate din dake gabanta wanda ko spoon daya ta kasa ci sai wasa take dashi. Ji yake kamar ya shake ta ya huta amma dai albarkacin Umminsa ya sa yazo ma inda take. "Ba'a koya miki gaisuwa bane? Ko har yanzu rashin kunyar taki bata sake ki ba!?" Yafada cike da masifa, murya na rawa Hoodah ta furta "Kayi haku...ri, ina kwana?" Meyakon ya amsa gaisuwar tata sai kawai yaja tsaki sannan yaja kujera daya ya zauna yana karkada kafa, ita dai sai binshi take da ido, sunfi minti goma a haka babu wanda yayi magana a cikinsu can Hoodah ta mike tana share hawayenta tana kokarin kar hawayen ya zubo mata amma dai ta daka ganta kasan daurewa kawai takeyi abu kadan za'ayi mata ta fara kuka. Juyawa tayi ta bashi baya tana faman goge hawayenta, sai data maida kukan da kyar sannan cikin karfin hali ta juyo tace "Me zan zuba maka?" Jikinta har wani rawa yakeyi, ko dagowa daga kallon wayarshi da yakeyi yana latse latse balle ma tasa ran zai amsa mata baiyi ba, hade hawayen nata tayi, kawai ta bude warmers ta shiga zuba masa casserole din da yasha kayan lambu da sausage, bayan ta gama zuba mashi ta tura mashi gabanshi ta hada masa tea ta mike masa, sai da ya dankara mata harara sannan ya karba, tana kyarmar jiki ta mika masa ashe bata lura ba bai kama cup din da kyau ba sai ji kawai tayi cup din ya sa6ule daga hannunta ya fadi kasa duk tea din ya fantsalar masa a farin kaya, wani irin shock ya kama shi yana dudduba jikinshi baki bude, a fusace ya mike yana huci, Hoodah ta fasa wani irin razanannen ihu tayi baya tama dauka dukanta zaiyi yadda ta ganshi, "Ke dakikiyar ina ce? Ke yarinya ce da zaki sakar man cup a kasa ya bata mun jiki? Kuma kukan me kikeyi haka? Kin cika man kunne kamar wadda aiko ma da mutuwa! Zakiyi man shiru ko sai na sa6a miki yanzun nan? Stupid kawai!" Wata irin tsawa ya kuma daka mata wadda tasa don dole Hoodah ta hadiye kukan da takeyi amma jikinta babu inda baya rawa, hannuwanta duka biyun tasa ta rufe lips dinta gam gam tana shesheka a hankali "Am sorry please...." ita dai burinta kawai taga ya fita bata son ganinshi wani irin shakkarshi takeyi yanzu...
"hold your sorry to your filthy self, banason munafunci Meyasa jiya kika kasa bani hakuri sai yanzu xaki wani kama bani hakurin karya, toh kisani wani kalar tausayi da wani kukan karyar da kikeyi man bazai sa na sauko ba har sai kinyi admitting laifinki kin kuma bani hakuri sannan mu dawo normal rayuwa! Kisa wannan a ranki na tsani abinda kika aikata yadda nakejin tsanarki a yanzu bana tunanin akwai irinta a duniya, daga yanzu babu wata baiwa da zata sake yi maki aiki a cikin gidan I dont care about your status ke zaki cigaba da aikin da sukeyi that's your punishment! Ki tabbatar kar na dawo na tarar da wannan cup din daya fashe kasa baki tattara ba sai na lahira yafi ki jin dadi, sakarya kawai idiot dakikiya!" Yana kaiwa nan kawai yayi gaba abinshi ya shige daki ji kake garam! Tanaji yasa ma kofar key ya rufe ta gam gam da karfin bala'i.
Durkushewa tayi kasan tiles din parlon ta saki wani irin kukan da tunda tazo duniya bata ta6a yin irinshi ba, kalamansa ba karamin impact sukayi mata ba sun ta6ata sosai, wai idan bazai iya zama da ita ba ya saketa mana, ko ta ta6a cewa tana sonshi? Toh dole ne? Ashe dama baida tausayi haka? Ashe duk wannan sanyin muryar dawani kirkin da yake mata ashe duk na munafunci ne? Kuka takeyi bil hakki ta dade a haka kafin a hankali taja jiki taje kitchen ta dauko broom da packer tazo tana dafe kai saboda yana sara mata, a hankali ta tattara gurin tana fama share hawaye saida ta gyara shi tsab sannan ta maida kitchen din. Shi kuma Sultan koda ya shiga daki bathroom ya nufa ya cire kaya ya watsa ruwa fuskar nan a murtuke kamar tashin duniya, yana gamawa ya sa kai ya fita yaje ya sallami bayinta yace Hoodah tace kar su kara zuwa aiki for a while har sai ta neme su da kanta. Side din Abbinshi ya nufa yana haraba da mutanenshi kota su bai bi ba kawai ya samu Abbi take Abbi yace su basu wuri na minti kadan, yana isa kamar wani karamin yaro sai ya fashe da kuka mai cin rai, "Abbi yanzu ka rasa wacce zaka aura man sai mazinaciya? Abbi so nake ka bani dama na rabu da ita inaso na sallameta bazan iya cigaba da zama da ita ba bazan jure ba Abbi, am tired Abbi..." Abbi ya dafa shi "Sultan bansanka da rashin hakuri ba da tausayi ba, dan me zaka rabu da ita? Yanzu idan kanwarka ce haka ta faru da ita xakaso mijinta ya koro maka ita? Bazaka so ayita mata uzuri ba? Sannan gaskiya kabani kunya a matsayinka na namiji namijin ma jarumi wanda nake sa ran zaka gajeni wata rana ka rika zubar da hawayenka a banza ba..." da sauri ya goge hawayen nasa yace "Ba haka bane Abbi, raina ne ya baci fa, kuma ni Abbi meyasa aka man aure da ita kasani fa Khairy nakeso na aura kaje ka hadani da ita, dole saini?" Abbi ya numfasa "Komai kaga ya faru da mutum mukkadari ne daga Allah, I know you like Hoodah koda kadan ne, and kunyi bonding a yan kwanakin da suka gabata kafin wannan abun ya sameta..." ya zaro idanu waje "So kuma Abbi? Me zanso a jikin wancan yarinyar? Allah ya kyauta nikam..." dariya Abbi ya kyalkyale dashi "Sultan kenan, karfa kazo kayi dana sanin abinda kake fada mun nan gaba kazo kana mana kuka saboda kaunar Hoodah... kuma don Allah ka daina cewa ka tsaneta especially a gabanta babu dadi, nima kaina abubuwan dana fada mata jiya nayi regretting kasan idan mutum yayi fushi babu abinda bazai iya fadi ba, zamuje nida Batul mu bata hakuri har sashenta, inaso mubi komai a sannu, nasan gaskiya zata fito inma ta aikata inma bata aikata ba duk Allah zai bayyana mana inshaAllah, don haka ka danne zuciyarka ka daina mata mugunta saboda abinda ya faru..." numfasawa yayi "Wallahi I hata her I hate everything about her now amma saboda kai zan daina InshaAllah..." godiya Abbi yayi mashi da bashi baki da kuma tunatar dashi akan zamantekawar aure, shidai jinshi kawai yake amma baiyi niyyar aikata abinda yace mashi ba, "kuma naji labarin ka korar mata bayi meyasa Sultan? Bafa daga gidan banza ta fito ba yadda kake dan sarki itama haka yar sarki ce, kuma tunda ka koresu na tabbatar wata rana da kanka zaka nemo su, amma Bakomai bazan tirsasa maka sai ka dawo dasu ba, tashi kaje Allah yayi maku albarka..." tur6une fuska yayi ya amsa da Amin sannan ya mike tsaye, daga nan wajen Ummi ya shiga don yana so ya fita ne, itama dai shigen irin abubuwan da Abbi ya fada masa kusan itama shi ta fada masa, har mamaki yayi yadda akayi suka sauko lokaci daya a take jiya kamar zasu kashe Hoodah amma wai yau har sune suke cewa ya daina hantararta?
Sultan dai bai dawo gida ba sai can bayan sallar magrib, yana shiga ya iske Hoodah cikin shigar da bai taba ganin tayi ba wato riga wando na jeans sai tasa wata farar top ta shan iska, ta sa pillow gaban tv tayi rub da ciki ta dan daga kafafuwanta sama kafar nan tasha jan lalle yayi maroon gwanin ban sha'awa, gaba daya hankalinta naga tv tana kallon wani series daga gani tana jin dadin kallon da takeyi har wani smiling takeyi tana kallon, har ya taka yaje daidai inda remote yake batasani ba saida remote din ya kubce masa a hannu ya fadi ne ya tsoratar da ita ta saki wata irin kara tana juyowa sukayi ido biyu dashi, hawayen daya gani a idanunta ne ya kular dashi, abun haushin bai yi mata komai ba kawai zata fara mishi kuka daga yada remote ikon Allah! Hannunta duka biyun ya matse wuri daya sannan yasa dayan hannun nasa ya hade lips dinta na kasa da sama ya rufe su hakan ya dakakar da ita daga ihun da takeyi na tsoronshi, "Wallahi kika kuskura hawayen nan ya zubo sai kinyi regretting kuma ki zubar dasu in gani..." ya fada yana tsareta da idanu. Kallonshi takeyi cike da tsoro da kuma fargabar da bata ta6a tunanin zata ji ba a tsawon rayuwarta ba....!
No comments:
Post a Comment