YAR AGADEZ
{Page 08}
Dariya suka bushe da ita dayan mai kirar samudawa ana kiransa da katako ne ya kunna camera ya saita ta yadda zasu aiwatar da komai yadda aka umarce su! Nan suka fara recording inda Damisa ne yayi pretending kamar yana kissing Gimbiya da yake ya ba cameran baya ita kuma Hoodah tana kwance unconscious ya sanya baza'a gane idanunta rufe yake, ya kai akalla minti sha biyar a haka sannan ya sauka suka kashe cameran suka kalli juna alamar sun kammala abinda ya kawo su sannan da sauri suka dinga fita suna tsallake bayin da ke kwance shame shame a kasa suna sharar bacci, a waje ma gaba daya bawanda ya gansu yawanci duk anyi bacci. Sai can wajen karfe 1am Hoodah ta farka, a hankali ta bude idanunta tana budewa take ta tuna incident din daya faru da sauri ta mike ta nufi bathroom ganin basuyi mata komai ba ya sa ta saki nannauyar ajiyar zuciya, sai kuma ta fara tunanin meya kawo su toh in ba fyade suka zo yi mata ba? Nan ta dinga tunani kala tana tsaye gaban mirror duk a tsorace take, kamar daga sama taji an dafata kirjinta yasake bugawa, ta fasa wani irin gigitaccen ihun da sai daya sa Yarima yayi baya a guje har yana neman faduwa, ita kuma runtse idanunta tayi gam gam tana makyarkyatar sanyi ko ina na jikinta yana kadawa, kaduwa mai ban mamaki! "Ka taimaka man, kar ka cutar dani! Karka tabani!" Yarima yayi kasake yana kallonta cike da mamaki, kuka takeyi sosai tana adduar Allah yasa suji tausayinta su kyaleta toh meyasa suka dawo? Still tsoro ya hanata bude idanunta taga ko wanene bata fatan ta sake hada idanun dasu. "Hoodah...! Lafiya? Mesame ki?" A hankali ta daina kyarmar da takeyi tayi kuri idanunta a rufe tana saurare kodai kunnenta ne baiji da kyau ba!!? Daf da ita ya isa tare da kamo hannunta ita kuma kamar tana jira tayi sauri ta makalkale shi jikinta na cigaba da kadawa wane mazari ko ina na jikinta ya dau zafi... Yarima yayi hugging dinta back yana fadin "Shhhh.... Kiyi shiru ni bangane me kike nufi ba Hoodah, ni ne zan cutar dake? Zazzabi kike ne naji jikinki akwai zafi, yama akayi na ganki ke kadai bayinki suna kwance suna bacci! Is that how to do their jobs?!" Ya fada da karfi! Ganin yanayin kukan da takeyi yasa Sultan yaja ta har cikin daki sannan ya kwantar da ita ya lullu6e mata jikinta da har yanzu bata bar rawar sanyi ba sannan ya shiga rarrashinta.... ya kai minti uku sannan ya mike yace "Bari na kawo maki koda juice ne sai na baki magani kisha kiyi bacci ko?" Tana jin haka ta wani mike da sauri tana rike hannunshi tana kalle kalle "Kar ka tafi ka barni ni kadai tsoro nakeji..." ta fada hawaye na surnano mata, kallonta yayi yace "Yanzu zan tada bayinki su zauna dake kafin in dawo kinji? Zauna a nan yanzu zan dawo babu abinda zai faru..." yana fadin haka ne yana zaunar da ita kan gado nan ta yarda ta zauna tana hade hannayenta wurin daya zuciyarta na harbawa. Yana fita parlor ya wani daka masu tsawa suka mike a gigice a kuma rude ko wace tana neman mikewa tsaye, "Yanzu ku ashe Gimbiya batada lafiya shine kuka kwanta a nan kuna sharar bacci bakusan halin da take ciki ba? Abinda aka dauko ku kuyi kenan?!" Ya daka masu wata watsar, a tsorace suka durkusa suka dinga bashi hakuri don su basu tabayin bacci haka mai nauyi ba, nan dai sukaita bada hakuri da kyar ya hakura sannan yace "Yanzu zan dawo ku shiga wurinta tana jin tsoro ne..." daga haka ya sa kai ya fita, yakai minti kusan ashirin sai gashi ya dawo da cup da magani a hannunsa, suna ganinshi duk sai suka fito daga dakin suka kulle kofar, nan ya iske ta ta shige cikin bargo tana jin alamun shi tayi sauri ta bude idanunta ta mike zauna, kan drawer ta gefen gadon ya zauna ya mika mata juice din ya balla mata maganin sannan ya bata ta sha, sai kuma yace "Kici kaza kafin ki koma ki kwanta nasan kina tare da yunwa..." ta girgiza kai da sauri tace "Na koshi..." ya wani daure fuska "Dama ay ba tambayarki nayi ba umarni ne na baki..." ya fada yana bude ledar kazar yago mata cinya yayi ya mika mata fuskar nan tasa tamau ta kalli fuskar shi sai ta karba da sauri tana ci a hankali, tare suke ci yana tirsasa mata da kyar ya samu ta danci sannan ya kyaleta yace ta kwanta, tana kwanciya nan da nan bacci barawo ya saceta, gyara mata bargon yayi shikuma ya fada bathroom yayi wanka ya fito ya shafa cream ya sanya kayan baccinsa ya haye can gefen gado ya kashe side lamp yayi addu'a ya rufe idonsa.
A hankali Hoodah ta bude idanunta ta ga haske fayau ta mike da sauri tana duba lokaci, da hanzari ta mike ganin ko sallar asuba batayi ba, alwala tayi ta fito ta tada sallah bayan ta idar tayi wanka ta fito ta shirya, kayanta masu ado da kwalliya, tayi kyau sosai sai dai daka kalleta kasan ba'a cikin nutsuwa take ba, bayinta na ganinta parlor suka shiga gaisheta ta amsa fuska sake sannan suka take mata baya har bangaren sarki can ta iskeshi shi da matarsa Batul suna karyawa, nan ta gaishe su suka amsa fuska sake sannan Sarauniya tace "Ashe bakida lafiya? Dazu ay munzo bangaren naki muka tarar kina bacci, da fatan jikin naki da sauki?" Ta danyi murmushi "Allah sarki, eh da sauki sosai Alhamdulillah..." Sarki yayi murmushi "Toh madallah, ki koma bangaren naki ki huta yanzu zansa a kawo maki kalaci kuma ki tabbatar kinci..." ta gyada kai a hankali ta mike ta nufi sashen nata, tana komawa kuwa ba'a wani jima ba sai taga ana shigowa da abinci kala kala, bayan sun gama kawowa suna niyyar fita sai ga yarima ya shigo yasha kaftan sai kamshi ke tashi daga jikinsa, ta kalleshi a hankali sai tace a ranta "Wannan anya ba jinsin larbawa bane kuwa?" Ya karaso cikin dakin yana fadin "Kin tashi? Ya jikinki?" Ta danyii murmushi "Dasauki alhamdulillah nagode da kulawarka..." yayi murmushi "It's my duty..." nan ya zauna gefenta ya hada masu shayi ya mika mata cup daya ya zuba mata chips da kwai da sausage sai kidney sauce, ta kalli plate din a dan tsorace tace "Ko a rage Abincin?" Yace "Dalili?" Tace "Ya min yawa..." yace "Toh ba sai muci tare ba?" Tayi murmushi kurum, a haka suka ci abinci har suka kammala...
******
Safa da marwa takeyi a inda suka saba haduwa sai faman duba time takeyi she is restless, ajiyar zuciya ta sauke trying her best to calm down, takai kimanin minti arba'in can sai gasu sun iso inda take ta wani daka masu tsawa "Ya mukayi daku? Sai yanzu kuka ga damar zuwa? Tun yaushe nake jiranku a nan!?" Damisa ya wani huro hanci fuskar nan a yamitse ba kyan gani yace "Wa kike ma ihu a nan? Ni sa'anki? Hattara!" Shiru tayi tana kallonsu Katako yace "Mun kammala maki aikinki, sai ki cika sauran kudinki sannan mu baki video!" Ta wani daka masa hara tana mika masa envelope din, fizgewa yayi ya yageta ya zaro kudin, kirgawa yayi a natse sannan ya kalleta "Ya naga dubu 100?" Tace "Sata kakeso inyi? Kasan a yaya nasami kudinnan?" Yace "Ina ruwana? Ba dubu dari uku mukayi dake ba?" Tayi crossing hannayenta tace "Banida su!" Ya daka mata tsawa "Ke karki raina mana wayau mana! Na rantse da Allah zan tattake camera dinnan a gabanki kuma babu abunda zaki iya yi a kai!" Ya dakko ta zai wullata kasa kenan ta fasa ihu "Wait! Tsaya! Dan Allah tsaya! Karka fasa! Zan baku wallahi zan bada complete...!" Ta fada tana zuge zip din jakarta ta fiddo dayar envelope din har guda biyu ta mika masu, dariya ya kece da ita irin ta mugayen nan abokanansa na tayasa ya dauki second goma sannan ya daure fuska tamau ya fizge sauran kudin hannunta ya shiga kirgawa a natse ganin sun cika yasa ya kunna sigari ya hura mata a fuska yana mata kallon rainin wayau.... "Toh gashi..." ya mika mata cameran, da sauri ta karba tare da kunnawa tana kalla, dariyar jin dadi tayi "And nothing is going to save you from this humiliation am getting you into Hoodah! Tun farko ke kika shiga gonata da baki shiga ba da duk haka bata faru ba! Kece kika rabani da masoyina kika tarwatsa farin cikina dan haka welcome to hell Gimbiya Hoodah..." ta fada tana jujjuya cameran, Damisa yace "Dama ay ke ba mutunci gareki ba ba'a ta6oki bama ya aka kare ballantana kuma an taboki, jahilai ne kadai ke maki kallon mutuniyar kirki amma mu da muka san wacece ke....!!" Ta daga masa hannu "Rufe man baki a nan!" Ta fada tana nufar hanyar fita. Duk suka bushe dariya a take.
**********
ONE WEEK LATER.
Da yammancin ranar wata asabar Yarima da Gimbiya suka fita yawo, aka raka su cikin gari, idan ka gansu baka ta6a cewa cewa basu son junansu tsabar yadda suka dace da juna, amma kowa ta ciki na ciki kawai dannewa sukeyi, tunda akayi aurensu basu taba fada ba suna respecting juna, sunyi exploring garin an zagaya da Gimbiya har kusan yamma, haka suka dawo saidai tunda suka shigo fadar mai martaba suka iske dashi da Sarauniya tsai tsaye kowane cikin bacin rai, turus sukayi bakin kofa mai martaba yayi tafi da karfi duk bayin da dogarawan suka fita da sauri, Yarima yace "Abbi lafiya?? Ummi meyafaru?" Kauda kai yayi yana kallon wani gefe Ummi ce ta tako daf da Hoodah tana mata wani irin kallo sannan tace cikin bacin rai, "Ashe haka kike? Meyasa kika bata mana suna! Kinsan nan gidan wanene! Nan gidan fuskar mutane ce meyasa kika zabi ki tozarta mu ki ci mana mutunci sannan ki wulakanta mu....!?" Hoodah a razane tace "Ni kuma Ummi?Menayi?" Abbi yace "Bakisan me kikayi ba? Yanzu dan baki son dana shine kike nema ki tozarta kanki ki tozarta shi? Har kiyayyar da kike masa ta kai haka?" Cike da confusion Sultan yace "Wai meyake faruwa ne? Ku fahimtar damu...." Abbi ya mika masa wayar Ummi wanda aka turo da wata unknown number danna masa play yayi ya fara kallo, runtse idanunsa yayi yana girgiza kai "Anya Ummi? Wannan ba Hoodah bace bazata ta6a aikata wannan abun ba!" Ya kara kallon videon ashe anyi editing sosai ansa mata jikin wata wacce batada kaya jikinta sai aka bar fuskar wacca ake gani sosai, Ummi tace "Toh fuskar take ce?" Juyawa yayi yana kallon Hoodah wacce ke tsaye kamar an dasata a wurin, a hankali yake taku har ya isa dab da ita ya damko mata hannunta ya sa mata wayar ciki, hawaye ne suka fara zuba daga idanunta tana kyarma ta dago wayar tana kallon screen din hankali tashe tana girgiza kai, "Ban aikata ba wallahi ban aikata ba..." Sultan yace "Toh wannan wacece Hoodah? Ki fada man gaskiya kinga sai a wuce wurin wallahi idan kika fada man zan iya yafe maki..." ta dago tana kallonsa sannan ta kai dubanta ga Sarki da Sarauniya wadanda suka kauda fuskarsu daga kallonta da sukeyi. "innalillahi wa'inna ilahir rajioon!" Take ta fara recalling incident da ya faru da ita daren ranar da aka kawota, "Ya akayi sukayi controlling dina? Meyasa zasuyi man haka? Menayi masu? Su wanene suka aikata mun wannan abun?" Gaba daya ta jera ma kanta wadannan tambayoyin amma babu amsa, duniyar gaba daya taji ta fara juya mata, ji tayi an damko ta take ya dinga janta kamar wani zaki fuskar nan jawur alamun bacin rai, Sarki suka dinga kiranshi amma ina har sai da ya kai sashensu ya kulle kofar, ya turata ta jingina da bango, sannan ya matso dab da ita yasa hannunsa biyu ya dafa bango yana kallon cikin idonta! girgiza kai takeyi hawaye wani na kara wani, Sultan yace "Ashe tsanar da kikayi man zatasa ki aikata wannan mummunan abun?" Ya nuna kan gado "A bisa gadon mu na sunna kika aikata alfasha Hoodah, why!? Why did you do this to me? Why?!" Ya fada yana girgizata da karfi, "Ya za'ayi kayi tunanin zan aikata wannan abun? Never in my life ban taba aikata makamancin haka ba, why don't you believe me I was unconscious I don't know what happened...." tsoro da fargaba sune suka mamaye zuciyarta don yanzu burinta bai wuce ace ya fita ya bar mata dakin ba, a hankali ya zauna kan gado ya dafe kai "Innalillahi wa inna ilahir rajioon....!" A hankali ta zube kasa gabanshi tace "Ka kalli cikin idona idan har inada gaskiya zaka gane, amma kar ka zargeni akan abinda bakada tabbas a kanshi...." ya dago kai yana kallonta idanun nan jajir "Zargi kikace? Ba maganar zargi anan, nagani da idanuna me kuma zaki fada man?" Ta share hawayenta duk da ba tsayawa hawayen yake ba "A lokaci da dama abinda muke gani ba shine yake faruwa ba..." wata irin iska me zafi Sultan ya furzar ya runtse idonsa, "This is what you want right? Ayita jan zance? Da yanzu kin fada min gaskiya an wuce wurin amma na lura baki son zaman lafiya dani..." kuka ta fashe dashi jikinta har kyarma yakeyi "Allah yaga zuciyata, ban aikata abinda ake zargin na aikata ba, framing dina akayi bansan dalili ba, ban san menayi ba...." Tsaki yayi mai sauti kafin ya mike tsaye, "You should be ashamed of yourself, na tsaneki na tsani mai irin halinki, gashi kin man karya bazaki fada man gaskiya ba you lied to me, I saw everything and you still have the guts to lie!" Yana gama fadan haka ya bude kofar fita ji kake garam!Wani irin kuka ne ya kufce mata sulalewa tayi ta kwanta shame shame a kasa har sai da tayi mai isarta, takai awa daya a haka har sai data gaji don kanta tayi shiru idanunta sunyi luhu luhu sun kumbure, da kyar taja jikinta ta shige bathroom ta watsa ruwa ta dauro alwala fito ta shafa mai, wata riga ta sanya ta material doguwar riga ta tada sallar magrib.
A 6angaren Sultan kuwa bayan ya fita daga wurin Hoodah bai zama ko ina ba sai dakinshi na da, kan gadon ya fada ji yake kamar ya fashe da kukan bakin ciki, "Why would Hoodah do this to him? Why?" Ya tambayi kansa amma ba amsa....
No comments:
Post a Comment