YAR AGADEZ
{Page 11}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Yafi minti biyar yana kallon saukar numfashinta yana kuma kare ma fuskarta kallo, wani irin yawu ya hade ji kake k'utt ya juyar da fuskarsa gefe yana tunanin mafita, don shidai baisan mey zaiyi ba yanzu cire mata zaiyi ko kuwa? Tunani ya tsaya yi cikin sanyin jiki ya nufi wardrobe dinta, yana budewa yaga kayanta tsaf tsaf dasu, wata pink nighty ya hango bangaren kayan bacci cotton mai zanen katuwar teddy tayi hugging heart hannunta dan siriri, tsawon rigar iya gwiwa, sai ya samu kansa da daga rigar yana kallo... karasawa yayi bakin gadon yanayin daya ga Hoodah ya tabbatar masa da bacci ya dade da daukar ruhinta, irin baccin nan ne da mutum keyi idan yana zazzabi, shawara ya yanke a kan ya fara zare mara skirt din jikinta hakan kuwa akayi ya gyara mata kwanciya rigingine ya hade kafafunta ya shiga jan skirt din, prefect skin color dinta yake kallo chocolate color mai haske sosai, sai gashi yala yala da take dashi na jiki ya kwanta lub lub, ya dade a haka kafin ya runtse idanunsa yana sauke numfashi "For Ummi's sake..." yafada cikin sa ma kansa kwarin gwiwa, zaiyi ne bawai don she mean something to him ba sai don tana cikin wannan halin, baisan mai zai fara yi ba hannun zai cire ko hook din zai fara zarewa? Wayyo Allah! Ji yake kamar ya daura hannu saman kai yayita ihu, gashi bayinta basu nan ballantana su taimaka masa wayyo yau yaga ta kansa shikam, tsaye yayi kamar zai fashe da kuka, ganin tsayuwar bazata yi masa ba yana 6ata ma kanshi lokaci a banza, siririn tsaki ya saki wani irin weakness yakeji yana dirar ma ruhinsa baiki ace yaje ya kwanta yanzu ba, zama yayi gefenta yana sauke numfashi ya tallabo kanta da bayanta yaji skin dinta wani irin bala'in taushi kamar jariri sabuwar haihuwa, wannan anya ta san wahalar rayuwa kuwa? Komai na jikinta lugub, da kyar ya samu ya cire hook din bra din, ya zagayo hannunshi a hankali ya zare mata hannun bra din so ya ke ya gama ya wuce wurin. Ashe baisani ba wannan shine babban kuskuren da zai tafka! Yana janyo bra din komai na jikin Hoodah ya bayyana, gabanshi ne yayi wani mummunan faduwa ya dan saki kara yana runtse idanunsa "Innalillah....!" Ita kuma Hoodah wani relief taji yana cire mata ta saki wata irin nannauyar ajiyar zuciya har salon numfashinta ya chanza take ta sake masa jikinta gaba daya ya sake sakin kara gwanin ban dariya yana runtse idanunsa, yau shidai yaga rayuwa! Da sauri ya dauko rigar baccin ya sanya mata yana gamawa ya saketa da sauri ya mike tsaye yana wani shesheka kamar wanda yayi gudun fanfalaki, ko tsayawa gyara mata kwanciya baiyi ba yayi wurgi da bra din saman gado ya fita a guje daga dakin kamar wanda aka biyo za'a kashe, direct dakinshi ya shiga wanda yake gefen dakin Hoodah yana shiga ya nufi bathroom da gudu ya sakar ma kanshi shower ya dade tsaye a nan yana zare ido kamar munafuki, a hankali yaji hankalinshi ya fara dawowa jikinshi, saidai fa har yanzu taushin jikin Hoodah bai daina ji a hannunsa ba. Yana fitowa ya zauna gefen gado kwalwarsa ta daina ja ya kai kimanin kusan minti arba'in yana zaune da tagumi, can dai ya mike a kasalance gaban mirror ya shafa mai ya fesa turare ya dauko kayan baccinsa ya sanya yama manta ko isha'i baiyi ba gashi ta wuce dama yayi alwalla kawai ya tada sallah yana gama azkhar ya hau gado yana kalle kalle, a haka ya kwanta yau yama manta ko saida safe baiyiwa su Abbi ba, kwana yayi yana juyi ba abinda yakeji sai taushin jikin Hoodah bai ta6a tsamannin haka take ba, her figure, her structure astagafirullah kamar ita ta kera abunta, da tunanin Hoodah yau ya kwanta wanda hakan ba karamin haushi yake bashi ba, why yake tunaninta? Ya saki tsaki, har Hoodah ta isa ta rikita masa lissafi har nawa take? A haka ma bacci takeyi inaga idonta biyu? Ya salam yau shidai yaga ta kansa....
********
Khairy cike da bacin rai tace "Wai me Sultan ke nufi? Ya naji shiru har yanzu bai korata ba? Kuma har yanzu banji wani mummunan labari ba ya fito daga gidan sarki, by now yaci ace sunga videon duk wannan shirin da nayi indai har bai korota ba ya tashi a banza kenan? No impossible! Bazai yuwu ba! Khairy never fails! Don haka a shirye nake da sake zage damtse da shirya wani makircin da tuggu! Idan har wannan aikin baiyi tasiri akan yarima ba toh ya zama dole na sake daukar wani mataki akan wannan tsinanniyar matar tasa! Zan kara bada kwana biyu idan naji shiru zanyi tattaki koda na 6adda kama ne sai naje, idan naga komai lafiya lau toh ina mai tabbar ma kaina da cewa zan sake wani shirin, Ni Khairy Usman na dauki alkawarin cewa, sai na tarwatsa Hoodah, sai nayi destroying dinta, sai na keta mata haddi! Sai na kuma daukar fansar abinda tayi man, bana asara duk abinda nakeso sai na samu...." ta kece da wata irin muguwar dariya tace tana shafa hoton Sultan dake hannunta "Welcome to hell Hoodah, kin kawo kanki da kanki babu mai cetanki sai Allah! Let the game begin!" Ta sake kecewa da dariyar mugunta sai kace wata witch.
*********
Sanyin safiya ne ya tada Hoodah, ko da asuba bata farka ba sai yanzu Allah ma ya taimake ta hutun sallah take, jiki a sanyaye ta mike kamar wacce akayiwa duka ta wuce bathroom tayi brush, ta wanke fuskarta, ta fito tana tafiya kamar marar lakka ta zauna shakaf kan gado, jikinta ta kalla a razane taji ko bra bata dashi, batasan lokacin data mike zumbur ba! Tana kare ma kanta kallo ta mirror kuka ta fashe dashi kamar an aiko ta, "Na shiga uku! Kar dai Sultan ne ya cire mani bra?!" Ta furta a rude tana dudduba jikinta, Shikenan taga ta kanta yanzu Sultan yaga jikinta kenan? Haka tayi tsaye ta kasa ta6uka komai, can dai a sanyaye ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta kimtsa kanta da dakinta sai kamshi ke fita daga jikinta kamar koda yaushe, yadda ta bar parlon jiya haka ta tarar dashi... gyara ko ina tayi yayi fes ta kunna burner ta sa turaren wuta, ta kunna ac, ta rufe curtains, tana kitchen tana hada tea aka yi knocking da sauri ta fito ta leka ta whole din kofar sai ganin Sarki da Sarauniya tayi tsaye, ware fararen idanunta tayi da sauri taje daki ta dauko mayafinta ta fito da bude kofar da sauri kanta kasa, sukayi sallama suka shigo suka zauna ita ma ta zauna kasa ta gaishe su da ladabi suka amsa, Sarki yace "Yaya jikin naki? Da fatan kin samu sauki?" Ta gyada kai "Alhamdulillah." Sarauniya tace "Toh MashaAllah, daman munzo ganin jikin naki sanann abunda ya faru rannan inaso ki manta dashi kamar ba'ayi ba sannan kiyi hakuri da yadda mukayi treating dinki..." ta dago da sauri tace "Basai kun bani hakuri ba Ummi, nagode da kulawa..." Abbi yace "Madallah da y'a ta gari Allah yayi maki albarka..." tayi murmushi "Ameen, bari na kawo ruwa." Ta fara kokarin mikewa tsaye Batul ta tsaida ta "Karki damu sai kace wasu baki? Bari mu tafi Allah ya kara lafiya." Suka mike a tare ta rakasu har waje ta masu sallama sannan ta juyo ciki. Daki ta tafi ta maida mayafinta ta nufi kitchen ta karasa hada tea dinta ta fito ta kunna tv, series dinta na jiya taga anayi, cike da jin dadi ta fara kallo tana sipping tea dinta a hankali, tana cikin kallon taji sautin bude kofa, kafin ma ta juya sai ta gansa har ya karaso cikin parlon, kai tsaye wurin tvn ya nufa ya kasheta gaba daya, bata tsaya tambayarsa dalili ba kuma haka ma batace dashi komai ba, sai ma tace "Ina kwana?" Ta dan russuna alamar girmamawa, muryarta har wani rawa rawa takeyi, tama ki yarda su hada idanu, wani siririn tsaki yaja "Daga yau ban yarda ki sake kunna koda socket ba sai da izini na, is my house sai abinda nace za'ayi do you understand?" Wani kallon banza yake binta dashi yasa tayi saurin kai kanta kasa tana wasa da cup din hannunta "Naji..." tana fadin haka ta mike tana maganar zuci "Ji man mutum kai sai kace kayan kallon ba nawa bane yake wa mutane wani iko da su mtsw." Kitchen ta wuce ta sauke dankalin dake kan wuta ya soyu, ta kwashe egg sauce a warmer dankali ma ta xuba ta wuce kan dining ta jera komai ta kai plates da kayan tea, bata ma jira abinda zai fada mata ba ta fara serving dinshi yana zaune hakimce yana latsa waya, tura masa tayi gabansa ta debi nata ta koma can tsakiyar parlor inda bazai hangeta ba saboda kejeru, kujerun ma dakakkun royal chairs ne, tana zama kawai sai ta fara kuka amma fa ko kadan bamai sauti bane ba, baima jita ba har ya gama ya mike zai shiga dakinsa ya hango ta tana goge hawaye wani tsaki yaja wai don ya hanata kallo shine take masa kukan munafunci? Har ya wuce kuma sai ya tuna magaganun Ummi ajiyar zuciya ya sauke yazo daidai inda take zaune ya durkusa ya kureta da ido da sauri ta dago kai tana dagowa suka kalli juna ido cikin ido haka kuma yayi da zubowar hawaye bisa kumatunta, wani abu yaji ya tokare masa kirjinshi yayi masa wani irin sukar da harda saida ya runtse idanunsa yace "Ya Rabbi!" ita kuwa Hoodah yadda kasan an bude tap haka ta cigaba da rizgar kuka wane an aikota kuka takeyi bill hakki har can cikin ranta, karshe ma data ga abin nayi ne kawai sai ta kifa kanta bisa kujera ta cigaba da rera kuka, shi kuma Sultan zugui yayi yana kallonta don shi sam baiga abun kuka a nan ba. Da ya gaji da tsugguni dan kansa sai ya zauna dirshen ya cigaba da kallonta kamar ya samu tv baice kala ba, amma dai sai yau ya lura kamar tana tare da damuwa kala kala, ko da yake irin haka is better mutum yayi kuka kar hawan jini ya kama shi yasan dai Hoodah bata tare da depression. Ganin ta rage kukan nata yasa ya gyara xama yace "Feeling better?" Gyada kai tayi kamar wata yarinya tana faman share hawaye, ita kanta mamakin Sultan takeyi sai kace ba dazu ya gama yi mata masifa ba? Amma yanzu jishi yana wani kwantar da murya kamar bashi ba, ba tare da yayi koda murmushi ba don ma kar tayi tunanin yawani sauko, a hankali ya mike yana zura hannu cikin aljihunsa both hands, "Good, dama na kyaleki ki ne ki gama kukanki don nasan bai dace ba mutum yana pouring heart dinsa out a tsaida sa ba, amma hakan ba yana nufin na chanza abunda na fada ba yana nan daram no tv kina jina?" Yadda yawani daure fuska sai ka rantse bashi bane yayi mata magana dazun nan ba, ta dukar da kanta tana gyada kai zuciyarta na harbawa har mugun da tasani a fuskar shi ya dawo sabo, tace "Naji..." juyawa yayi ya sa kai ya fita ita kuma ta bi da kallo har ya fice, ajiyar zuciya ta sauke yadda kaddara ta fada mata lokaci daya, take kuma ta tuna Ashraf nan nan hawayenta suka dawo sababbi wanda suka fi nada zafi da kunci da bakin ciki... sake dukar da kanta tayi kan kujera ta fashe da wani irin matsaanancin kuka mai ban tausayi....
No comments:
Post a Comment