YAR AGADEZ
{Page 28}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
2 DAYA LATER
Stool Khadija ta jawo ta zauna gaban mirror wacce ke faman shafe shafe a fuskanta, wannan yarinya tana son makeup sai kace wata fashionista! Khadija ta daga ido ta hangota ta madubi tana kokarin shafa lipstick ta dakata tace "Lafiya kika kura mun ido haka? Ko na maki kyau ne?" Zarah tayi murmushi "Kyau? A haka? Duk kinbi kin painte fuskarki, Khadija kwalliyar nan tayi yawa, by the way you looked beautiful without makeup." Khadija ta turo baki "Kaji man bakin ciki! Zarah in har kwalliyar nan ta maki kyau kawai ki fada kema sai ayi maki ay." Zarah tace "No thank you please." Khadija ta cigaba da makeup dinta Zarah ta kuma cewa "Wai shin fita zakiyi ne?" Khadija tace "Yes salon nake son zuwa..." Zarah ta kwalalo idanu "Salon kuma? Malama kinsan karfe nawa ne yanzu? Karfe biyar fa harda rabi kice zaki tafi salon are you okay?" Khadija tayi dariya "I am perfectly fine! Salon kuwa zanje yanzu InshaAllah." Zarah ta tabe baki "Kekam kina bukatar addu'a gaskiya, kuma wai sai kinyi makeup kafin kije salon?" Khadija ta juyo a fusace "Wai kekam ina ruwanki? Haba ki kyaleni mana!" Shiru Zarah tayi ta cigaba da abinda takeyi. Bayan duk ta gama kimtsawa kai kace wacce zataje wani dinner party, turare ta feshe jikinta dashi ko ina har kamshin yayi yawa, chewing gum ta dauko ta watsa baki ta suri wayarta ta juyo ta kalli Zarah "Bye." Zarah tace "Wa zai kaiki? Ke zaki tuka?" Tana taunar chewing gum tace "Nah." Saukowa tayi bisa bene duk ta cika wurin da karar takalmi, hango Ashraf tayi bisa kujerar parlor yana faman danne danne a waya, ta gabanshi taxo ta wuce amma ga mamakinta ko dago kai baiyi ba bare ma ya kalleta, dakin Mummy ta wuce tana zaune kan gado da littafin hadith tana nazari Khadija ta shigo, gefenta ta zauna Mummy ta dago tace "Ina xakije haka kika ci wannan uwar kwalliyar?" Khadija a shagwa6e tace "Salon..." Mummy tace "Salon? Karfe 5:45?" Wayarta ta kunna ta kalli time ta dago tana kallon Mummy "Please Mummy wallahi kaina yana bukatar gyara, na dade ban gyara shi ba ji nake kamar bazan iya kai gobe dashi ba a haka..." Shiru Mummy tayi can tace "Ok karki dade kice wa Yasir idan yana nan ya aje ki mana." Ta turo baki "Baya nan fa yaa Yasir, sai yaya Ashraf kawai ke gidan." Mummy tace shi yasan gurin ne?" Khadija tace "Sai dai na masa kwatance," Mummy tace "No problem dauki key din motata bisa madubi kice nace don Allah ya taimaka ya kaiki." Da sauri ta mike ta dauko key din ta fice parlor yana inda ta bar shi dan sunkuyawa tayi tace "Yaya Ashraf ina wuni? Yaya Ashraf Mummy tace don Allah wai ka kaini salon." Bai ce mata komai ba kawai ya mike ya fice waje, kallon mamaki ta bishi dashi kafin a hankali tabi bayansa, waje ta iske shi tsaye harde da hannaye wurin mota yana ganinta ya kara hade rai, ta karaso ta mika masa key din, ko kallon inda take baiyi ba ya bude motar yace mata "Jeki kira Zarah ta raka ki." Hade rai tayi tace "Tace maka zata je ne?" Ya gyada kai "Zataje mana, kawai kije ki kirata." Shiru tayi kamar bazataje ba can dai ta juya kamar zata tashi sama ta nufi ciki, ta kai akalla minti sha biyar can sai gata ta fito itada Zarah wacce ke sanye da ash hijab abinta ba karamin birge shi tayi ba, gaba daya ya dinga binsu da kallo yana gani differences sosai tsakaninsu a halayya, tsarin rayuwa, nutsuwa da kuma kyau. Karasowa sukayi Zarah tace "Yaya Ashraf gani." Yace "Wai unguwa zaki raka Khadija." Tace "Don Allah ka rabu da ita kalli time fa yanzu ana iya kiran sallah muna can, yanzu salon dinne bazata iya hakura saida safe taje ba?" Tsaki Khadija ta saki da harara "Wai ina ruwanki? Ba Mummy tace inje ba dai?" Ashraf yace "It's okay ku shigo muje." Nan Khadija ta fara kokarin shiga gaba Ashraf yace "Koma baya Zarah zata shiga gaba ay itace babba." Ba karamin kule ta yayi ba yau, hade rai tayi ganin haka yasa Zarah tace "Bakomai fa zan shiga baya ni." Hade rai yayi yace "Nace ki shiga gaba ko?" Bude gaban tayi ta shiga Khadija ta shiga baya yana ayyanawa a ransa sai ya sauke mata rawar kan nan nata da wannan tunanin yaja motar suka bar gidan.
*****
Tana kitchen tana fama da girki kamar daga sama taji an rungomota ta baya, kamshin turarensa da taji shi ya tabbatar mata daya iso, fara ture shi tayi daga jikinta shi kuwa ya makalkaleta hade da rufe ido, "Sultan girkina zai kone please let me go." Peck yayi mata a wuya "Tou ya kone din, sai na girka mana wani." Shiru tayi, sai don kansa ya sake ta hade da juyota tana fuskantansa, kallonta yake cikin ido yana rike da waist dinta yace "Habibty, tun daga bakin kofa nake jin aroma na abincin nan na tashi, it sure gonna taste delicious." Tayi murmushi "Mhmm, tun kafin kaci har ka fara cika baki?" Ya rungume ta yace "Kome kika dafa dole yayi dadi indai daga hannunki ya fito." Tayi murmushi "Thank you, but first of all, go and freshen up then you can meet me at the dining later." Shagwa6e fuska yayi "Tou bazaki tayani ba?" Ta dan ware idanu "Girki nake fa amma next time." Yayi dariya "Naki wayon..." dariya yayi ya wuce daki zuciyarsa fes fes, Itama Hoodah cike da nishadi ta kammala girkinta, bayan yafito a haka suka kare cin abincin su suka tafi suka kwanta.
Kiran sallar farko ya tada Hoodah daga bacci wacce ke kwance a jikin Sultan ya nadeta da hannunsa, daga ido tayi ta kalleshi take kunya ta kamata tuna irin kukan data sha jiya, kallonshi ta tsaya yi bata taba kare masa kallo haka closely ba sai yau bacci yakeyi hankalinsa a kwance, bak'in sajensa take bi da kallo wanda ya nannade sai sheki yake kai kace na larabawa, yadda ya burgeta sai taji ta kasa hana kanta take ta dora hannu a kai ta dinga shafawa a hankali, wani irin santsi taji hade da taushi, haka ta cigaba da shafa shi, a hankali ta bi idanunsa dake rufe da kallo yadda lashes dinsa sukayi zara zara kamar a kitsa, tunani ta farayi wai ita dashi wama yafi tsawon lashes? Tayi nisa wurin kallon nasa ashe batayi aune ba ya tashi ya kura mata ido, "Da alama wata tana admiring kyawuna." Gabanta ya wani buga da sauri ta runtse idonta gam gam cike da kunya da sauri ta dauke hannunta daga kan fuskarsa yayi wuf ya riko mata hannun "Ay wallahi baki isa ba kuma, bazaki dauke hannunki ba sadda kika ga dama ba kuma," ya fada yana mayar mata da hannunta a wurin, "Ki barsu a nan Habibty." Kokarin tashi zaune ta farayi "Za..nyi salla...h." Ta fada tana kokarin janye hannun nata at the same time, yayi murmushi "Nima ay sallar zanyi, tare zamuyi sallar ma habibty." Hannunsa ya dora bisa hannunta yana motsa shi daga bisa sajensa "Naga alama wurin yana maki dadin ta6awa." Kunya duk ta kama Hoodah tayi maza tace "Kallo fa kawai nakeyi." Ta sauke ajiyar zuciya sai kai kace wacce tayi gudu don gaba daya yadda ya tsare ta da idanunsa sai taji bazata iya jurewa ba, tashi daga bisa gadon ta fara kokarin yi da sauri Sultan ya riko mata hannu, "Ina xakije?" Yace tare da kara rike mata hannunta cikin nashi yana murzawa shiru tayi tana sauraren bugun kirjinta, can tace "Uhm babu kawai xanje bathroom, I need to go please!" Murmushi yayi yace "Babu inda zakije mrs Sultan, ke kika tashe ni daga bacci, kuma kika fara ta6ani sannan yanzu kice zaki gudu kuma?" Rufe ido tayi cike da kunya ya saki dariya ya mike tsaye ya kamo hannunta ya kaita har cikin bathtub ya kunna mata warm water, ba zato ba tsammani kawai sai ganinshi tayi ya shige wankan shima kusa da ita ay bata san sadda ta fasa ihu ba, dariya yayi suka yi wankan tare duk da ta kasa sakin jiki dashi, hade da alwalla. Da kansa yasa mata kayanta ya samata hijab, shima kayan ya sa yaja su sallah, saida suka gama sukayi addu'oinsu ya kalleta yace "Good morning my beautiful princess." Tayi murmushi ta rufe quranin data gama karantawa ta aje shi mazauninsa sannan tazo gefensa ta zauna hade da dora kanta bisa kafafarsa tace "Morning to you too my handsome prince." Hannunta taji ya kamo ya manna ma kiss sannan ya mikar da ita tsaye yana dago fuskarta "Look at me Hoodah." Ta kalleshi yace "I love you, you are the person who exactly knows how to put a smile on my face, kece mutum ta farko da nake so na fara gani da safe haka ma kece ta karse da nakeso na gani kafin nayi bacci, ever since I fell in love with you Hoodah rayuwata ta sauya, i will always be there for you no matter what." Hugging dinshi tayi sosai tace "Babu words din da zanyi amfani dashi wurin nuna farin ciki hade da godiya ga Allah (SWA) daya mallaka man kai a matsayin mijina I am really thankful." Zuciyar sultan kamar zatayi boasting tsabar farin ciki resting kansa yayi bisa shoulders dinta yace "I love you Hoodah, I promise to love and be with you duk rintsi duk wahala, and this time around am not going to break my promises InshaAllah." Gyada kai tayi hawaye na kawo idonta, jawota yayi ya cire mata hijab dinta yace "Let's sleep." Kan gadon suka haye ni kuma na fito na basu waje....
******
"Ranki shi dade gaskiya nifa babu wata kasar da xan kara zuwa! Ni aure zanzo inyi na gaji da wannan kazantacciyar rayuwar da kika dora ni a kai, kiyi hakuri amma gaskiya bazanje ba!" Wani wawan riko Karimah tayi mata ta maidota ta gabanta kafin ta faska mata wani irin wawan mari, ranta a bace take kallon baiwarta wacce ta maida yar gayu tayi clean, har an kai lokacin da Zubaida zata kalli kwayar idonta ta fada mata magana? Kodai maganin da take amsowa ya fara daina aiki ne? Don a yadda sukayi maganar yace ko wani namiji yace yana sonta asirin zai karye shekara da shekaru tana wannan harkar sai yanzu wannan kazamar baiwar zata kawo mata cikas. Batasan ya zatayi ba gashi nan da kwana uku ya kamata ta tura Zubaida Paris yanzu ya zatayi? Zubaida batasan lokacin data fara kuka ba, "Nasan kin bani rayuwa kin tsamo ni daga cikin talauci a lokacin da nake tsamo tsamo a cikinsa, amma nagaji! Rayuwa ce me cike da kazanta da tarin zunubi! Rayuwa ce abar kyama ko nasani ko bansani ba nasan tabbas idan na dore akan wannan rayuwar babu abinda zai hana ta kaini zuwa jahannama, Umma ki hango yau da ace kinada ya ko da ake transferring dinsu daga wannan mace zuwa wata ko daga wannan namijin zuwa wani, kasa zuwa kasa ba don komai ba sai don alfasha da matan banza ko mazan banza! Ya zakije a ranki?" Kafin ta rufe baki Umma ta kara wanke ta da wani wawan marin, idanun baiwar Allahn nan har sun rine kumatunta yayi sawun mari, "Ke har kin isa ki alakanta nawa jinin da wanann maganar? Duka duka yaushe na dauke ki daga tsummar rayuwarki?" Abinda Umma ta fada kenan karshe ma sai ta fara dukan Zubaida, kuka take bawai zafin dukan ba sai don irin kunar da zuciyarta ke mata, wato ita bazataso ayi ma nata ba amma ita takeyi wa yayan mutane? Amma ji yadda ta dage tana dukanta? Ita wace irin alfasha ce ke bata aikata ba? Wallahi inda ace yau mai martaba zai gano kadan daga cikin abinda takeyi toh da ko kara second daya baxaiyi da ita a cikin gidansa ba... Dan halak din kuwa sai gashi ya shigo da sauri ya karaso yana fadin lafiya? "Sarki wai yau ni Zubaida ke fadawa magana, ni Zubaida take zagi ta uwa ta uba wai na mayar da ita baiwa ita ba baiwa bace da gatanta na dauko ina sata bauta!" Sai ta fashe da kuka, cikin tsananin bacin rai sarki ya damko Zubaida ya dauko yatsunsa biyar ya shatata mata a kunci, sannan yasa hannu ya shako mata wuya, babu abinda Zubaida keyi face girgiza kai tana gunjin kuka "Ke har kin isa ki fadawa matata haka? Idan kin mata bari na tuna maki cikin kazantarki na dauko ki na mayar dake mutum shine yanzu har wuyanki yayi kwari ya isa yanka ko?" Girgiza kai ta cigaba da yi tana kuka sosai tana kokarin cire masa hannu daga wuyanta da ya shake "Ranki ya dade wallahi ba gaskiya bane, sam banga laifinka ba Allah ya baka yawan rai! Sorry to say amma bakasan da wace irin mace kake tare ba, she's evil! She's wicked! She's a witch! She's a Murderer! And full of dirt!" Wani marin ta kara jin ya sauke mata, ko gezau batayi ba bata kuma bari ya fara magana ba ta tsaida shi "Ka tsaya ka saurareni! Ko mey zakace kace amma ka tsaya in gama magana! Kai kasan wace irin rayuwa tabani? Da kuma dubannan yan mata? Ta maida ni lesbian! Duk tafiye tafiyen da nakeyi ita ke tirsasa man! She sells me off to wives of ministers, senators, governors.... bani kadai ba duk wata da ka aje haka take maida su, ta saida mana mutuncinmu all in the name of son kudi and luxury! Bata tsaya a nan ba ta kashe matarka mahafiyar Hoodah kisan gilla...." wani irin wawan ihu da Umma ta kurma ta fara dora hannu bisa kai tana nuna kanta "Sarki kaga abinda mutum zai iya yi ko? Dan adam! Ka dauko shi daga rana ka maida shi inuwa amma shi sai ya tunkuda ka rana tsundum! Sarki a gabanka take alakantani da masu Wanann halayen?" Kuka Umma takeyi tana maganganu ta inda take shiga bata nan take fita ba, nan sarki ya fara binsu da kallo, daka ganshi kasan he's in shock ya kalli Zubaida ya kalli Umma ya rasa maganar wa zai dauka a cikinsu....
No comments:
Post a Comment