YAR AGADEZ
{Page 05}
Kwance take kan cinyar Kaka a hankali Kaka tana shafa dogon gashinta wanda ya baje bisa bayanta, tanada gashi asalin na buzaye mai tsawo da sheki, lumshe idanu tayi kafin Kaka ta soma magana "Kiyi hakuri da duk abunda yake faruwa na tabbatar maki dukkanmu nan ba wanda ya tsara hakan sai Allah (SWA), ba Jalal ba, ba Sultan ba balle kuma Ashraf... Akwai dai sila amma Allah shine ya kaddara hakan a gareki..." Hannun kaka ta kamo tace "Kiyi man wata alfarma guda daya Kaka..." tace tana gyara rikon da tayi ma Kaka "ki daina ambaton sunansa a gabana na tsane shi..." tace feeling hurt already, Kaka ta daga ta zaune suna fuskantar juna sannan tace "A'a Hoodah karki sake fadin haka, kalmar tsana bata kamace ki ba hakika kalmar tayi miki tsauri da yawa...." Ta girgiza kai "Toh me kikeso ince Kaka? Nace ina sonsa?" Kaka tayi murmushi tana shafar fuskarta a hankali "Ko me mekika ga ya faru yana dalilin faruwa InshaAllah..." Hoodah tace "Ko kusa Kaka tunda nake ban ta6a dandana heartbreak ba sai wannan karon, Abba ya dasa man wani ciwon zuciya wanda warkewarsa ba nan kusa ba, Kaka ba'ayi man adalci ba...." tace wasu sabbin hawaye na neman zubo mata, da sauri Kaka tasa hannu tana share mata hawayen, zuciyarta babu dadi sam. "Zuciyar mace tanada matuqar rauni, takan kamu da soyayyar mai kyautata mata da bata kulawa, ba daya bane da zuciyar namiji idan har ita mace tana son abu, abu ne mai sauki ta hakura dashi, amma namiji ba hakan bace shi a nashi bangaren ba lallai bane yaso wacca bayaso amma wasu sukan sauya a hankali su so wacce basu so din... Hakika namiji zai iya auren mace hudu kuma ya basu kulawar data dace amma can karkashin zuciyarsa akwai wacce yafiso a cikinsu, kamar yadda na fadi maki a baya Allah ne kadai yasan dalilin dayasa yayi hakan, kedai naki hakuri Allah yana tare da masu hakuri, na tabbatar idan kika auri Sultan zaki samu farin ciki koba yanzu ba. Tabbas yanzu baya sonki amma akwai yuwuwar ya soki wata rana, ba namijin da zai ganki yace bakiyi masa ba, gaki kyakkyawa, ga gashi tubarkallah ga kyan hali da sanin ya kamata, ga hakuri da addini, gaki yar babban gida babu abinda kika rasa don haka ki kwantar da hankalinki Gimbiya da izinin Allah zakiyi alfahari da zabin mahaifinki koba yanzu ba kinji yar albarka?" First time ever Hoodah ta danji sanyi a ranta sannan ta saki murmushi a hankali kanta na kasa. Kaka tayi murmushin itama, ban taba fada maki ba amma auren mahaifiyarki da Abbanki yarjejeniya ce da wani makudan kudi da ya kamata Jalal ya biya don kare masauratarsa daga kawo hari. Can garin su mahaifiyarki wanda mahaifinta shine mai garin garin, garin yana daya daga cikin gari mai matukar girmama sarautarsu basu dauki abun wasa ba, masauratu da yawa sun so su dawo karkashinsu amma basu amince ba. Yin yaqi ba shiine mafita ba don lokacin army dinmu na nan basu da wani karfi. Gashi lokacin masarautar tana cikin mummunan hadari, lokacin ne Mahaifinki ya dinga neman shawarwari har daga karshe suka yi yarjejeniya aka bashi Safinah a matsayin wannan deal din, yayi alkwarin zai kare masarautar da kuma Safinah na nuna jin dadinsa don dama ansan mahaifin Safinah mutum ne mai matukar saukin kai da sanin ya kamata, bazan taba mantawa ba ranar da za'a daura masu aure Abinda Abbanta yace da Safinah. (Zaki zama safe tare dasu yata na maki wanann alkawarin kiyi man wannan saboda masarautata, ni mahaifinki ne kuma I want the best for you) ya kamo hannunta cikin nashi, tana zubda ruwan kwalla tace dashi "Zan aure shi Abbu, zanyi duk abinda kakeso indai bai sa6awa addininmu ba InshaAllah na maka alkawari..." Cikin jin dadi yace "Allah yayi maki albarka Safinah, na tabbata bazaki bani kunya ba..." abinda yasa na baki wannan labarin shine Inaso kiyi koyi da mahaifiyarki kinga dai yadda ta amsa kudirin mahaifinta kuma batayi nadama ba sun gudunar da rayuwarsu cikin jin dadi da soyayya kafin waccan matar tazo ta ruguza komai..." ta numfasa "kinga dai ta yadda akayi auren amma a hankali soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu...." Hoodah ta numfasa sannan tace da Kaka "Toh ita Umma ta yaya akayi ta hadu da Abba har ya aureta?" Kaka tayi murmushin karfin hali sannan ta dora "Hakika Karima itace ta kamu da soyayyar Jalal, lokacin da farko baya kaunarta har ta kai ta dinga kawo masa ziyara, karshe ta shiga ta fita har ya amince zai aureta tofah tunda ta shigo gidannan ta tarwatsa farin cikin gidannan, gashi dai Allah bai bata haihuwa ba duk kuwa dabararta, don a cewarta tana so ta haifi namiji don ya gaji ubansa, amma dai shiru ba labari, koda Safinah ta samu cikinki Jalal ba karamin murna yayi ba don ya dade Allah bai bashi ba, a lokacin ne ita kuma Karimah bakin cikin duniya yabi ya haye mata ta dinga neman yadda zata kashe dan cikin Safinah Allah bai bata iko ba, har dai aka haifeki bata daina bin hanyoyin da zata rabaki da duniya ba, amma da yake shi Allah ba'ayi masa dubara sai gashi kin rayu har ma kin girma cikin hukuncin ubangiji, saidai fa ba karamin tsanar Safinah tayi ba gata muguwa ce bama Safinah ba gidannan ta addabi kowa kuma abin takaicin ma Jalal baya ganin laifinta duk abinda zatayi bai ta6a daukar mataki ba, duk abinda tace ayi shi za'ayi abinda ta hana toh ya hanu kenan, harta dai abinda za'a girka saida izinita don dai fa ta kuntata wa Safinah, amma da yake Allah ya zuba mata hakuri bata ta6a complain ba." Kuka sosai Hoodah takeyi na tsananin tausayin mahaifiyarta "Ki daina kuka Hoodah, abinda kawai nakeso ki gane shine ki kar6i kaddara mai kyau ko marar kyau Allah shi yasan daidai shine ya kaddara hakan...." cigaba da kuka tayi Kaka na faman share mata hawayenta, can dai ta tsaida kukan nata tace "Allah sarki Ammina taga ukubar rayuwa, tabbas ranar da Allah zai tashi kama matar nan toh ta kiyayi karshenta, na gode ma Allah da bangani ba da bazan taba mantawa ba da halin da Ammina ta shiga ba..." Kaka tayi murmushin karfin hali "Hakane, kuma na tabbatar Sultan mutumin kirki ne kuma nan gaba zaki bani labari da kanki lokacin kin kamu da soyayyarsa...." Kaka ta fada cikin yar dariya....
*******
Ashraf yana tsaye bakin kofar dakinsa ya zurfafa cikin tunanin abubuwan da suke faruwa da rayuwanshi cikin yan kwanakin nan... A kullum burinshi ya zama yana yawan kyautata wa Abba wanda na kasanshi zasuyi alfahari dashi... ajiyar zuciya ya sauke, amma meyafaru idan har wannan yayan yayi hurting kanwarshi daya kamata yayi protecting. Take ya fara recalling abinda ya faru shekarun baya da suka shud'e.
"Ammi!" Yaro dan kimanin shekara goma shabiyu ne ya shigo dakin yana sanye da farar kaftan da hular data shiga da kayan a guje ya shigo ya dawo daga Islamiyya hannunsa dauke da jakkar littatafansa, Ammi na rocking Hoodah wadda ke lumshe idanu a hankali alamun bacci ya fara surarta, da yake islamiyyar boarding ce tunda aka haifeta bai ganta ba sai yau don haka da mamaki shimfide saman fuskarsa ya shigo idonsa na kan kyakkyawar jaririyar dake kwance, Ammi ta juyo tana kallonshi fuskarta dauke da murmushi tace "Na'am Ashraf." Yana isowa daidai inda babyn ke kwance yace "Ina kika samu baby?" Ya kuma lekawa yana kara kallonta har yanzu bai bar mamaki ba, Ammi tayi dariya sosai bata ce dashi komai tana dai kallonshi yadda yake ma babyn kallon mamaki can ya kuma cewa "She's beautiful Ammi, kanwata ce?" Ammi tace "Eh kanwarka ce Ashraf she will call you yaya Ashraf...." wata kayataciyar dariya yayi jin an ce kanwar shi ce sai yaji kaunarta ya shige shi yana jinta har cikin ransa, yana murmushi ya kuma kallon Ammi yace "I like her already, Ammi ki bata kulawa sosai yadda zata girma muyi wasa tare..." Ammi ta shafa kansa tana murmushi "Karka damu Ashraf amma kaima inaso kayi man alkawari guda daya tak..." yace "Anything for my Ammi." Tace "Inaso ka kula da kanwarka ko bayan bana nan..." da sauri yace "Ina zakije Ammi?" Tayi murmushi tana shafa fuskar shi "Babu ko ina kawai dai ina so ka kula da ita sosai..." yayi murmushi shima yace "Na maki alkawari Ammi, amma Ammi zaki sake siya man wani babyn amma namiji nakeso wanda xamu dinga fita wasa tare...". Dariya ya ba Ammi tace "Ay ba siyan baby ake ba Ashraf, Allah ne yake badawa zan dai tayaka addu'a ya sake bamu wani namijin next time..." yace "Promise?" Ya bata dan karamin yatsansa sai ta sakala nata ciki tace "InshaAllah." Haka ya cigaba da kallon babyn yana taya Ammi raino. Dawowa yayi daga duniyar tunani yana share kwallan dake zuba daga idonshi yace "Kiyi hakuri Ammi da alama dai ban cika kadan daga cikin alkawarin dana daukar miki ba."
No comments:
Post a Comment