YAR AGADEZ
{Page 13}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Wani irin mugun tsaki yaja har saida ya kada ma Hoodah yan hanji, "Wallahi tallahi in baki daina mani wannan kukan munafuncin ba sai na lahira yafiki jin dadi, in banda munafunci kinsan abinda kika aikata amma ki kasa bada hakuri and accept your damn mistake, amma da yake taurin kai ya maki yawa, sannan I don't know wani mistake din ya kawo ki gidana, what do you want from me? Nasan dai ba dukiya ba! Ba kuma sarauta ba! Are you after my life? Do you want to kill me? Talk to me!" Ya fada yana wani irin girgiza ta da karfi fuskarsa jawur wanda hakan ba karamin kidimar da Hoodah yayi ba, bare ma aje ga maganganun da ya fada mata ba karamin girgiza ta sukayi ba, "Ki fada man nace what do you want from me? Ko ance maki bansan halin stepmom dinki ba ko wani asirin tayi man aka kawo ki gidana?" Ko rufe baki baiyi ba hannayenshi dake saman kafadunta suka fado kasa kallonta ya tsaya yi, nan yaga wani irin zallar bacin rai da tsantsar tsanarshi a idanunta, take yaga Hoodar da yasani ta bace bat wata sabuwa ta bayyana with no sign of respect, "Kayi kadan! Ko kadan baka kai matsayin da za'a mallake ka da asiri ba, kai waye kai da za'a aikata shirka a kanka? Kai nan har tunani kake kana da wani matsayi a duniya da za'a soka a bika har a sabawa mahallicinmu? Me kake takama dashi? Mulki? Sarauta? Kudi? I am far more better than that! Abinda kawai yasa nake maka shiru kana taka ni yadda kaga dama shine na farko kai mijina ne ko ba komai ance nayi maka biyayya dukda ba sonka nake ba! Na biyu ina respecting kakata wadda itace ta rokeni akan nazo na zauna dakai kar na sa6a maka! Kai wallahi ba sarauta ba ko ni almajira ce babu wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi tsoronsa! Duka duka nawa kake? Who the hell do you think you are? Bana living life donni wata tsiya ce in fact I hate being royal! Yadda kake mutum nima haka nake yadda kake da kafafuwa da hannuwa da baki da ido da kunne nima duk haka neke dasu! Zuciyar da ke bugawa a kirjina daya ce kaima taka ce daya ce tak! Idan ka isa kana kuma tunanin kanada wani matsayi a idon duniya da kuma Allah, don Allah ka chanza halitta ingani ya kasance kai kadai ka fita daban ka fita unique a duniya that is idan har ka isa! Kuma da kake maganar munafunci I am all acting naga dai we are married ko? Kai ko kunya bakaji ba ace kana kiran matarka mazinaciya yaushe ka kamani da idonka inayi? Kai baka mayi tunanin ya akayi ma har aka dauki videon ba? Daga gani kasan shiri ne! Kuma da kake maganar stepmom dina tana bin bokaye da malamai wallahi ta fiye man a kanka sau dubu! Duk wani isarka da mulkinka are nothing compared to her in my life! Indai wannan wahalallen auren ne agabana da bamu kai haka ba! Ni nan ba zaman ka nake ba zaman kakata nakeyi da Abbana! Kai bari kaji fa wallahi tallahi inda naso tun ranar da aka kawoni cikin gidannan sai nasa ka duka kasan gwiwowinka kana rokona sai nasa ka zama bawana na dinga juya ka son raina! Nima fa inada matsayin da zan dinga juyaka amma banyi ba saboda baka gabana, kallon banza ma baka isheni ba, sannan bari kaji wallahi babu boka babu malam sai na hargitsa duk wani tunaninka saina kwance duk wani notin da ke kanka." Hawayen ma kwata kwata sun daina tsiyaya, bakin cikin data kwasa tun ranar data shigo gidan ta sauke mashi san ranta kafin tayi hanyar bathroom din. "Idan ka gama tsayuwar ka fitan man daga daki ka rufe man kofa... kuma ka aje man wayata bisa gado, kuma idan naga dama sai na fada mata duk abinda kake man kaga idan zaka kwana lafiya gobe da sai na nuna maka matsayina nima!" Tana gama magana ta shige bathroom tasa key, tana shiga ta zube kasan bathroom din ta dinga rizgar kuka bata ma damu dayana cikin dakin ba itadai bakin cikin dake cikin ranta take fiddawa.
Sultan yafi minti araba'in tsaye inda ta barshi yana jin sautin fitar kukanta, yadda kukan ke fita daga ji na bakin ciki ne da kunci dake cikin zuciyarta. Gaba daya Sultan sai ya rasa meke mashi dadi wani irin guiltiness da dana sani ne ya fara dirar masa cikin ruhinsa, zai iya cewa yafi kowa sanin dadin uwa amma yau ya bude baki ya kira wacce ta dauka a matsayin uwa mai bin bokaye da malamai, meya aikata haka? Jiki a sabule ya fita daga part dinta ga kuma magaganun Ummi wanda take fada mashi rikon maraya yadda yake take wani guiltiness ya sake rufe shi barin garin yayi gaba daya, sai da yayi kusan awa biyu sannan ya dawo cikin garin Niamey, haka yayita yawo yama rasa ina zaije, sai can ya dawo gida. Direct dakin shi ya shiga yayi wanka.
Ita kuwa Hoodah tafi awa daya cikin bathroom tana shar6ar kuka saida ta gaji dan kanta ta watsa ruwa ta fito, tana fitowa ta chanza kayan bacci ta haye gado, a hankali bacci barawo ya sace ta haka tayi bacci tana sauke ajiyar zuciyar kuka.
********
Da safe Sultan yana tashi sai ya tsinci kansa da son zuwa dakin Hoodah, yau dai yasan ba lallai bane ya samu breakfast amma to his surprise yana fita yaga abinci jere saman dining, gidan sai kyalli yake ko ina fes fes ga wani irin kamshi na musamman na fita daga gidan yaji turaren wuta ga freshener yana tashi, sai yaji ta bashi tausayi, zama yayi kan dining din sai yaji yanaso tayi serving dinsa, gashi ya tuna yace kar ta kara bari su hadu idan yana nan. Yana gama cin abinci ya tashi ya fita daga gidan, rasa inda zaije yayi gaba daya abin duniya ya ishe shi ya dame shi.
********. 1 MONTH LATERAL
Tun abinnan da ya faru tsakaninsu babu abinda ya chanza masifar yau da daban ta gobe daban abu kadan zaiyi ta hau shi da masifa kamar wata uwarshi, amma duk da haka tana dan shakkarsa, gaba daya dawo wani solo6iyo ya daina ta6uka komai.
Da daddare ranar wata litinin ne tayi masu indomie mai shegen yaji, haka suka ci abincin nan har tari ya dinga yi na yajin abincin gashi ba damar yayi magana yanzu ta hau shi da fada. Yanzu ya daina hanata kallo kunnawa takeyi ko yana so ko baya so tayi kallonta son ranta, bayan sun gama cin abincin ne ta tatttara ta tafi dakinta ta kwanta. Can da daddare wurin karfe biyu na dare ciwon ciki ya tasheta tun kwana biyu da suka wuce take jin alamun shi, azabar kadan kadan kamar wasa, can kamar a mafarki ta farka tana ta uwar zufa ko ta ina, nan ta fara juye juye tana mirgina, can dai ta mike tsaye ta kwanta ta kife, ta tsugunna kasa, duk abinda zatayi a banza kamar ana karo shi, ganin numfashinta na bazaranar daukewa sai yasa ta rarrafa ta nufi wurin kofar Sultan a galabaice ta isa kofar ta fara bubbugata da karfin bala'i. Shi kuma Sultan dama yajin da yaci ya ishe shi da kyar ya samu bacci ya dauke shi, wannan uban knocking ya tashe shi ya bude kofar da sauri yana budewa sai ya ga Hoodah durkushe kasa dirshen dafe da cikinta, siririn tsaki yaja "Ka lafiya me kike man a kofar daki?" Ya tambaya a hankali ba cikin masifa ba, wata uwar harara ta watsa mashi "Aww tambayata ma kakeyi? To marata ke ciwo... komin banza dai ba wanda zan fadi mawa sai kai ay ko?" Ta fada cike da tsiwa, wani azaba taji ya turnuke ta batasan lokacin data saki kara ba ta cakumo wandon shi ta makalkale mashi kafa dan dole ya durkushe kasa ya rungume ta shi tsoro ma ta bashi, wani tight hug ya bata hakanan yaji yana bukatar wanda zai rungume yama manta shaf ciwon ciki takeyi, wani ciwon ya sake turnike ta ta saki kara tare da sakin wani wahalallan nishi tace "Na shiga uku wayyo Abba zan mutu!" Ta fada wane za'a zare mata rai, a hankali ya zare jikinshi daga nata yana kallon fuskarta yadda ta jike da zufa tsabar azaba ta cije le6e ta dafe cikinta ta rike shi gam gam, "Yanzu me kikeso na maki? Kinga dai am not a doctor Hoodah..." cikin sanyin murya yake maganar yana kallonta ita kam idanunta a rufe suke ita dai burinta baifi ya lafa mata ba. "Ohh wai tambaya ma kakeyi? Kai ka taba jin ance menstrual pain nada magani? Ko don ba jikinka ciwon yake ba, ka wani tsaya kana kallona ko pain reliever ay ka bani ko?" Kallonta yayi baki sake "Oh wai dama menstrual pain ne? I thought ulcer ce due to yajin da kika ci jiya Allah ya baki hakuri uwar masifa, ke bakisan rana ba bare kuma dare..." yana gama fadan haka ya mike ya koma dakinshi ya rufe kofarsa. Kwanciya tayi a nan ta gama juyinta bakin kofa kafin ta bude kofar dakinsa ta shiga, dan tsabar iskanci na Sultan ulcer ce zata sa man ciwon mara? "Amma wallahi kai dan rainin hankali ne, yanzu yaji ne zai sa man ciwon mara? Kuma da kaji ba ciwon ulcer din bane meya hana ka tashi ka bani magani? Kai dama ba tausayi gareka ba kama san meye ciwon mara kuwa? Toh wallahi ko ka nema man maganin rage pain ko kaji sammaci daga wurin Ummi, na lura don kaga ina rufa maka asiri kafi wulakanci..." tana fadin haka ta durkusa kasa rike da ciki yau ita kam ta bani ciwon yau yafi na kullum. Jin an ambaci Ummi yasa Sultan sakin wani dan guntun tsaki kafin ya tashi tsaye, closet dinsa ya nufa ya dauko first aid box, pain killer ya ballo mata guda biyu ya mika mata, "Gashi nan kije kisha kuma ki fitar man daga daki, na lura munafuncinki yana nema ya wuce gona da iri..." ya fadi haka yaga taki karbar maganin, wani tsaki yaja ya koma kan gado ya juya mata baya ya rufe idonsa "Toh wai haka ake shan magani babu ruwa ba komai?! Ko na maka kama da yar kwara da zan banki magani ba ruwa? Wallahi ka kiyayeni Sultan..." saida taji wani d'ar data fadi mashi haka don ita bawai ta daina tsoronshi bane gaba daya. Guntun tsaki ya kara ja shidai burinshi ta bar mashi daki, mikewa yayi a fusace ya fita parlor ya dauko cup ya debo mata ruwa yana dawowa ya wani mika mata shekeke, "Ansa ki karba ki sha dan Allah dan Allah kar ki sake takura man bacci zanyi, out." Ya nuna mata kofa, batayi musu ba ta karba tasha maganin, ga mamakinsa sai yaga tana gama sha ta aje cup din ta kwanta kasan carpet din dakin, ba irin maganar ba baiyi mata ba amma fir taki tashi ta fita, da ya isheta ma sai ta rarrafa ta isa bakin gadonsa ta hau taja bargo ta kwanta. "karka cika ni da surutu nasamu yayi sauki, ka kashe fitila don ni bacci zanyi." Idan kaji yadda take maganar sai ka rantse da Allah dakinta ne, galala yake kallonta baki bude "Ke wai bakida hankali ne? Hoodah a dakina kike fa bazaki tashi ki koma naki dakin ba zakizo nan ki dinga mun iko a nawa dakin? Tashi da Allah ki tafi." Ya fada yana jawo mata bargon, rikewa tayi gam tana harararshi, "Saida safe Sultan, at least be nice koda sau daya ne, kaga banason kana tabani kuma ni ba iya tashi zanyi da kaina ba, idan har kaga bakason kwana nan din kana iya komawa parlor, bye." Kallonta ya tsaya yi anya yarinyar nan batada ta6in kwalwa kuwa? Shi dariya ma ta bashi, ashema bataso ya ta6a ta shine ta kwaso jiki tazo masa daki? Yanzu kuma gata a kan gadonshi inda yake kwanciya? Fitila ya kashe ya koma dayan side din ya ja bargo ya lullu6e ya kwanta. Ko kwakkwaran motsi ya kasayi saboda tsoron kar ya ta6a mata jiki. Can cikin dare Hoodah ta gangaro gefenshi ta rungume shi ta kwantar da kanta bisa kirjinsa a haka ta cigaba da baccinta, da sauri ya bude ido yana zare su kamar munafuki sabon kamu, wani irin zabura yayi kamar ya kurma ihu, karshe dai a haka ya hakura ya rufe idonshi har bacci yayi gaba dashi...
No comments:
Post a Comment