YAR AGADEZ
{Page 15}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Haka ta kwanta tana ta faman tunanin little Affan, yayi karami ace yana experiencing wannan abubuwan, subhnallah kuma mahaifinsa wanda shi ya cancanta ya zamana yana gefensa yana share masa hawaye wannan wane irin uba ne? Anya shine ma ya haife shi kuwa? Abinda matar nan ta fada mata gakiya ne ko kuwa? Kodai wani 6oyayyen al'amari ne tattare da abin? Indai har gaskiya ne bai dace ma ace ya ta6a haihuwa ba, astagfirullah ita wacece da zatayi judging abinda Allah ya hukunta? Da kyar bacci 6arawo ya sace ta. Washe gari ta kai kimanin minti 30 tana wanka, gaba daya ta rasa mafita ta rasa meye abinda ya kamata tayi, tana son ta taimaka mata amma wani bangare na zuciyarta baya so. Kamar kullum sai ta fada ma Sultan zataje yawan shakatawa, har fa fita sai ya kirata "Wai bakya gajiya da zuwa wurin nan ne? Kullum sai kinje?" Dariya ta kakalo "I promise wannan ne zuwan da zanyi na karshe zan dauki time banje ba..." yace "It's fine, but do you need someone to take you?" Tace "No, I will be ok thank you." Gyada mata kai yayi "Alright be safe..." daga haka tasa kai ta fita zuciyarta na harbawa, inda suka saba haduwa yau ma a nan ta iske matar na zaune tana zaman jiran Hoodah ta karaso, idanunta jawur alamun taci kuka murmushi ta kakalo ganin Hoodah, sallama Hoodah tayi mata ta amsa "Ya jikin Affan? Wurin wa kika barshi?" Tace "He's better Alhamdulillah, na barshi da nannynshi." Hoodah tace "zamu iya tafiya? Amma gaskiya bazan shiga hotel ba, sai dai ki masa magana ya fito waje..." matar tayi yak'e ta tashi suka fito parking lot, mota suka shiga ta jasu, tafe suke babu wanda ya tanka cikin motar amma ji take kamar abinda take ba daidai bane, tana ji kamar bata kyauta ba, gani take wannan shine worst mistake da zata aikata, parking sukayi gaban makekiyar hotel din matar tace "Muje?" Hoodah tayi shiru gabanta na faduwa, "Muje ina? I thought I said am meeting him outside? No kije ki kirashi I can't go inside..." matar ta numfasa sai ga hawaye shar shar tace cikin shesheka "Taya xan fara ce masa ya fito? Bakisan halin Aliyu bane wallahi bazai fito ba, amma indai har kina ganin kamar cutar dake xanyi kawai mu hakura mu koma, am seriously telling you and ke da kanki kikayi niyyar taimaka man I want my baby to survive..." Hoodah tayi shiru gabanta na harbawa tana sauraren sheshekar matar "Don Allah ki daina kuka, bawai ban yarda dake ban, kawai dai zuciyata ce bata amince man da in shiga ciki ba I don't know why!" Matar sai ta kifa kanta a steering wheel ta dinga sheshekar kuka "Babu komai, a haka ma nagode da niyyar taimaka man da kikayi, I don't mean to make you feel uncomfortable, bari naje na gwada kiran nasa nagani... amma alfarma daya xakiyi mun, muje bakin receptionist sai na masa magana a nan ya sauko..." tace toh ta fito daga motar suka cigaba da tafiya a natse duk Hoodah is uncomfortable sai kalle kalle take, can tace "Kar kice na cika complain amma gani nake kamar ana kallonmu..." matar ta juyo ta dafata "Toh ko dai ki tsaya a waje? Idan baki iya shiga." Hoodah tayi smiling back "A'a it's fine muje kawai." Nan ta shiga ciki ta bar Hoodah tsaye. Tun Hoodah nasa rai zata fito har ta fara gajiya da jira, toh dama akwai steps a wurin sauka nan tana cikin tafiya kawai sai tayi taga taga zata fadi, wani dake gefenta yayi saurin tarota.....
Shi kuma a bangaren Sultan tunda Hoodah ta bar gida ya kasa samun nutsuwa, a hankali ya fito ya dinga binsu ga mamakinsa sai yaga sun tsaya a hotel, nan ya fara tunanin meya kawo Hoodah hotel wacece wanann da suka zo tare? Kawai yana fitowa daga mota sai ga Khairy kamar an korota, "Sultan!" Cak ya tsaya ya juyo yana ganin Khairy yace "Khairy me kikayi a nan?" Ta matso daf dashi "Mama ce ta aikeni nan kawai ina fitowa sai naga matarka da wata mata sun shiga cikin hotel, toh a hankali na dinga binta ina zuwa sai naga asha da wani ne suka hadu..." yace "Mey? Me kikace? Yoh must be joking." Tace "I am sorry Sultan but that's the truth, believe it or not gaskiya matarka tana bin maza... karka ce kishi nake ko wani abun, ni da idona na ganta..." ya runtse idonsa gam gam yana girgiza kai "No! Karya kike Khairy kishi ke damunki amma Hoodah bata bin maza..." Khairy tace "Oh really, why don't you go inside and see it for yourself!" Kasa tsayuwa yayi nan yaji kamar zai fadi, rigarshi Khairy ta damko ta dinga jansa kamar wani gunki haka suka shiga cikin reception din, yana fara hawa steps daidai lokacin da Hoodah ta kusa faduwa wani ya tarota, tsayawa yayi yana kallonta take ya fara wani girgiza kai ya fasa kara "Hoodah!!!!" Yayi gigitaccen kara kamar wani zaki, ita kuma lokacin ta kusan fadowa tana kokarin rike stairs kar ta fada masa amma ina ta kasa controlling hakan, wata irin zabura tayi ta jiyo a gigice, kafin ta ankare sai ganin Sultan tayi ya nufo ta gadan gadan wane kura ta ga nama, wata irin damka ya kai ma kugunta ya dinga janta suka fita hotel din don mutane nata kallonsu, cikin motarsa ta tullata har sai da kanta ya bige da karfen motar ta rike kan hawaye na taruwa cikin idonta, gefe ya shigo ya kunna motar ya tada ta da karfin balai yaja su wane zai kifar dasu, "Na yarda da maganar da ake fada a kanki yau na tabbatar!" Muryarta na rawa tace "Me kake nufi?" Ko amsata baiyi ba ya kara wutar motar kamar zaiyi accident, a tsorace take kallon shi jikinta babu inda baya rawa, yana isa gida ya finciko ta ko tsayawa baiyi ba sauraron kowa ya nufi sashensu, yana zuwa ya wullata kasa yasa ma kofar key, "Sultan wai lafiyanka?" Ta fada tana kokarin mikewa tsaye tuni hawaye sun wanke mata idanu, finciko hannunta yayi ya matse gam gam yana kallon cikin idanunta "Tambayata ma kikeyi?" Ya fada kamar zai fasa mata dodon kunne Hoodah tace itama a tsawace "Dole na tambayeka! Naga alamar kamar kwalwarka ta samu matsala!" Kara matse karfin rikon da yayi ma hannunta yayi "Naganki dawani kato a cikin hotel sannan kizo kina tambayata meye faru da kwalwata?" Hannu tasa tana kokarin cire rikon da yayi mata cikin kuka tace "This is the second time Sultan zargina kake? Baka yi trusting dina ba? Sultan what the hell is wrong with you? Subhnallah don kawai kaganni da wani bai ci ace ka zargeni da aikata abinda ba daidai ba, trust me da wata naje taje ciki ta dawo kawai nazo faduwa...." daga mata hannu yayi "Bana son jin komai daga bakinki Hoodah! Akace maki ni wawa ne bansan me nakeyi ba?" Hoodah tace "Oh haba? Now I get it! Dama dai kiris kake jira ka fara mun abinda ba daidai ba! In banda haka meyasa bazaka tsaya kayi bincike ba? Ka gano idan na aikata hakan?" Idanunshi jajir jijiyoyinsa a waje yace "Ni mamakin da kike bani sai wani cewa kike bakiyi komai ba, bayan sau biyu ina kama ki dumu dumu amma still you're denying the fact!" Hannu tasa take karfi yazo mata ta fincike masa hannu daga jikinta tace "Toh bari kaji Sultan! Nagaji! You know what? I don't care anymore am tired of all this!" Ta fada tana nufar hanyar dakinta "And where do you think you are going?!" Saida ta kai dakinta ta juyo tace "My room, kuma babu abinda ka isa kayi!" Tana fadan haka ta shige daki nan yaji anata knocking "Sultan ka bude mana kofar nan!" Da sauri yaje ya bude nan sarki suka tsaya suna kallonsa "Lafiya? Me kuma ya faru? Ina Hoodar?" Ummi ta fada tana sa kai ciki, knocking dakin Hoodah tayi ta kai minti biyu sannan tazo ta bude, Hoodah na ganin Ummi kawai taje ta rungumeta gam ta saki kuka mai ban tausayi "Ummi I think someone else is setting me up! Inaga akwai wanda baya son zamana cikin gidannan ..." Ummi ta dago ta tana share mata hawaye "Meya faru?" Ta fada tana kamo hannunta ta zaunar kan kujera mai martaba ma ya shigo ya zauna shima yace "Meya hadaku fada tun farko?" Sultan yace "A hotel na kamata dawani kato..." daga masa hannu yayi "Ba kai na tambaya ba yata na tambaya ita nakeso tayi man bayani dalla dalla..." kwafa yayi ya fice daga gidan wane zai tashi sama, share hawayenta tayi ta dago daga kan cinyar Ummi sannan ta basu labari daga farko har karshe, mai martaba ya numfasa "Tabbas wannan set up ne daga ji ma, amma kema Hoodah kinyi ganganci meyasa kika bita kuma meya hana ki fada ma Sultan gaskiya tun farko?" Tace "Wallahi nima bansani ba! Kawai na tsinci kaina da son taimaka mata shine fa, amma bayan nan babu wani abu wallahi." Ummi tace "Toh wai wacece wannan da take son hanaku zaman lafiya? Sau biyu fa kenan! Amma karki damu zamu gano ko waye kuma wallahi idan na gano I won't spare her! Share hawayenki inshaAllah Allah zai bayyana mana gaskiya." Ta share hawayenta sai yanzu ta soma fahimtar komai dalla dalla.
Bayan mai martaba sun fita nan Hoodah ta dinga safa da marwa a dakinta tana tunani "Waye wannan yake nemana da sharri? Meye hadina da shi? Me na masu? Waye?" Nan ta dinga tafiya tana tunani zama tayi gefen gado "Tunda yanzu na fahimci komai, I won't rest sai na gano ko waye wanann yake tarnishing image dina yake kuma hadani da Sultan, mark my word sai na gano ko ke wacece no matter what it takes I won't spare you!"
Tana nan zaune a haka har aka kira sallar magrib jiki a sa6ule ta tashi ta shiga bathroom ta watsa ruwa hade da alwala tana fitowa ta saka loose gown. Can bayan isha'i taji shigowar Sultan garam haka aka buga kofar dakin aka shige kamar zata balle, a hankali ta fara tunanin yadda rayuwarsu ta sauya cikin kankanin lokaci da irin kulawar da suka ba junansu amma yanzu lokaci daya ansamu wata shegiya ta tarwatsa masu farin ciki, tafi minti talatin sannan ta mike a sanyaye ta nufi dakin nasa, jikinta babu inda baya rawa, tana shiga ta tsaya kofar dakinsa tana kalle ganin babu kowa, nan tayi tsaye lost in her thoughts kamar daga sama taji takun tafiyarsa kusa da ita, wani irin mugun firgita tayi da tilas tari ya sarketa, bai ce komai ya juya ya fita ashe ruwa ya debo mata ya mika mata ta sha da sauri amma fa fuskar nan kamar an aiko mashi da sakon mutuwa, ta kula yayi wanka ya chanza kaya "Meya kawo ki dakina?!" Ya fada cikin daga murya, muryar nan babu taushi ko kadan. Ta dago da rinannun idanunta tana kallonshi, kafin ya ankara sai hawaye ya runtse idanunsa ya zauna kan kujera, ganin haka yasa Hoodah ta zame ta zauna kusa dashi tana tunanin maybe zata samu sassauci, kallonta yake babu ko kyaftawa ita kuwa kuka take tamkar ranta zai fita, kasa ta sauko don tayi alkawarin bazata taba barin gurin ba sai ya daina fushin nan da yakeyi, tayi missing kulawar da yake bata kwana biyu da suka wuce, ya dandana mata zuma mai saurin kama zuciya. Dan kwanciya tayi bisa cinyarsa ta lumshe idanu "Sultan ya kamata ka fahimceni kai kasan wannan ba halina bane is a set up don a rabamu, nasan bamu zaman lafiya bama son junanmu da farko, amma wallahi ban taba aikata abinda kake tunani ba please..." tausayi ta bashi matuka kamar ya durkusa ya rungume ta amma ego bazai barshi ba "Tashi ki fitan man daga daki!" Rufe idanunsa yayi da san ya manta abubuwan da suka faru 2days ago, it's a beautiful moment a happy one, "No bazan tafi ba har sai kace kayi trusting dina, sannan sai kayi hakuri nasan nima inada laifi da na tafi ban fada maka ba, kayi hakuri wallahi ba laifina bane matukar tausayina ne yaja mun amma nayi learning lesson, I was just trying to help her she told me to talk to her husband, yaronta yanada cancer batasamun kulawa daga garesa, I even offer to help her nace ta fada mun nawa ne kudin aikin yaronta tace indai inaso na taimaka kuma nayi niyya sai dai nayi magana da mijinta da ke zaune a hotel, kayi hakuri don Allah, nidai kawai so nake kace kayi trusting dina that's all that matters to me, ko da zaka dakeni ko kace ka tsaneni as long as zaka yi trusting dina I don't care, please Sultan don Allah..." ganin ko kallonta baiyi ba yasa ta zagayo da hannayenta duka biyun a waist dinsa ta makalkale wani irin shock sukaji su duka, juyowa yayi ya kalleta kafin yabi hannunta da kallo dake zagaye dashi!" Shiru yayi kafin yace "I hate you! Nace ki tashi ki fitar man daga daki! Abinci ma karki sake bani zan dinga fita inaci! And lastly koda wasa karki kara taba jikina!" Ya fada yana ture hannunta daga jikinshi ko second daya bai kara a dakin ba ya tashi ya fita ya buga kofar da karfin bala'i. Wani abu Hoodah taji kamar madaci ya tsaya mata a makoshi, sai yanzu ta tabbatar da duk kukan da take a baya ba kuka bane takaicin data kunsa dazu ba komai bane ba compared to na yanzu, duk wata kafa dake zuciyarta saida ta toshe sannan ya bude mata kofofin bakin ciki da damuwa mai tarin yawa. Kuka ta saki mai cin rai a nan, nan ta kwanta a kasa tayita kuka kamar ranta zai fita, tun tanayin kukan har bacci ya fara fizgarta, sannu a hankali bacci ya sureta a nan inda take.
Ashe Sultan yana parlor kwance shima a nan bisa kujera bacci yayi awon gaba dashi, can cikin dare fitsari ya ishe shi, ko lura da ita baiyi ba kasa sai da yafito daga bathroom ya hango ta can kamar xata shige cikin kujera ta kudundune da hijab dinta sai faman ajiyar zuciya takeyi, samun kansa yayi da rage mata sanyin ac sannan ya rage mata fitila, karasowa yayi a hankali inda take ya dafata a firgece ta farka "Kayi hakuri kace ka yar...." sai a yanzu ya lura da kuka takeyi cikin bacci, tana bude idonta ta ganshi kawai sai tayi hugging dinshi ta fashe da wani irin kuka, "Kace kayi trusting Sultan, azzalumai ne suke so su rabamu, zaka nemo su? Ka hukunta su?" Kuka take har can kasan ranta, wani irin tausayinta yaji yana shigarsa, a hankali yayi hugging dinta back yace "Kiyi shiru ki daina kuka kinji? Zan sa a nemo su bazan bari su kara hadamu fada ba ki koma baccinki yi shiru."
No comments:
Post a Comment