Sunday, 6 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 04

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 04}



Tashinsa kenan daga bacci aka kwankwasar kofarsa yayi bismillah ya mike tsaye ya zura bedroom slippers dinsa ya nufi kofar yana budewa daya daga dogarinsa mai suna Sani ne tsaye da wata envelope a hannunsa ya zube kasa yana fadin "Rankaya dade barka da kwana! Ga wannan sakon aka ce na kawo maka." Yasa hannu ya karba yana jujjuya takardar sannan yace da Sani "Wannan fa?" Sani yace "Banida masaniya rankaya dade." Sultan yace "Kana iya tafiya..." daga haka Sani ya mike ya tafi inda Sultan ya juya ciki da tunani kala kala... Zama yayi a daya daga kujerun dakin sannan ya warware takardar a hankali ya soma karantawa kamar haka: 

"Assalamu Alaikum mai girma yariman Niamey! Da fatan kana lafiya? Allah yasa haka ameen. Bazan tsaya wani dogon bayani ba saboda banida bakin zan maka wata magana, amma inaso kasani ban taba tsammanin zan rubuta wannan takardar a gareka ba saidai banida za6i don kai kajawo! A tunanina soyayyarmu ta ginu acikin zukatanmu sannan ina ikirarin da kakeyi na cewar bazaka ta6a iya rabuwa dani ba? Ashe duk karyar banza ce! Naji labari a gari na cewar zakayi aure, nayi mamaki matuka kuma na karyata hakan! Saidai yanzu banida damar kara saka doubt cikin raina don na tabbatar da zancen nan haka dinne! Shekara kusan shidda muka dauka muna soyayya amma rana daya ka rusa mana farin ciki ban taba tunanin haka daga gareka ba, ya zama tilas nayi hakan amma kasani bazan ta6a yafe maka ba! Ka cuceni ka yaudareni! Bazan ta6a kar6ar uzurinka ba! Zanyi kokarin ganin nayi moving on amma kasani kamar yadda ka rusa farin cikina haka kaima kayi bankwana da zaman lafiya da ma ko wacece zaka auro! I don't care who the fuck she is I must destroy her mark my words! Though it will be slowly but painful amma daga karshe sai nayi winning! Kar kayi gigin zuwa inda nake don zan iya halakaka! Nagode da abinda kayi man na barka lafiya! Daga wacce ta tsaneka Khairy Yusuf!" Squeezing gashin kansa yayi yana huci idanunsa sunyi jajir wane garwashi, bai ta6a tsintar kalaman da sukayi masa zafi ba irin kalaman Khairy ba, ya tabbatar Khairy duk abinda ta fada bil haqi iyakar gaskiyarta ta fada ya fahimce ta amma meyasa ba zatayi masa uzuri ba? Meyasa ta zabi ta ci mutuncinsa sannan ta wulakanta sa? A hassale ya mike kamar mai shirin zuwa dambe ya fice daga dakinsa da isarsa fadar mai martaba sai yayi kansa gadan gadan yana huci "Kayi nasara!" Abinda kawai ya furta kenan, da hanzari Sarki ya mike yana fadin "Kai lafiya? Are you okay?" Yace cikin damuwa, a zuciye yace "Ka daina mani wannan tambayar! Na bayar da zuciyata da ruhina ga wacce nakeso amma saida kasan yadda kayi ka rabamu! Wow bravo! Clap for yourself you deserve an award for that!" Hannunshi ya kamo ya damke da karfi yana huci shima yace "Ka manta dawa kake magana ne? Kana magana da sarkin garinnan kuma mahaifinka! Don haka kar ka sake bude baki ka fada man maganar da bata dace ba! Am your father don't you dare disrespect me!" Hannunshi yake kokarin fizgewa yana fadin "Let go of my hand! Ka sakar mun hannu! Baka cancanci ka zama mahaifina ba saboda abinda kayi man don haka ka sakeni!" Ya fizge hannunsa ya fita daga fadar kamar zai tashi sama!

******

Sallama tayi harabar mai martaba yana ganinta ya mike da sauri yana fadin "Kaka meyasa kika taso da kanki? Ay da kin kirani nazo....." zama tayi gefensa tace "Kar ka damu magana nazo muyi dakai...." ya sallami guards dinsa sannan yace "Lafiya ko?" Tace "Lafiyar kenan....Abban Hoodah..." yace "Na'am..." tace "Meyasa kakeso kayiwa yarka auren dole? Ka tuna fa ita kadai Allah ya baka, bayan haka marainiya ce, baka ganin akwai daukar alhaki a cikin lamarin nan kuwa?" Yace "Bangane me kike nufi da akwai daukar alhaki ba? Banida right din da zan zaba mata miji sai ya zama daukar alhaki?" Tace "Ba haka bane kana da iko amma kuma ka dubi girman Allah da ma'aiki ka janye batun auren nan da yarima, kuma ka tuna fa Ashraf jininka ne meyasa kake gudunsa? Har ka gwammace ka aura mata bare akan jininka?" Yace "Ban taba tunanin rana mai kama da yau zatazo ba, ranar da zakiyi questioning right dina! A matsayina na mahaifin yarinya na zaba mata miji and that's final...." ta dakatar dashi "Hoodah ta maka biyayya taji maganarka kai meyasa baza kaji maganata ba? Sai na matarka?" Yace "Karki sako matata cikin maganar nan Kaka ba ruwanta..." tace "Dama ay haka zakace amma bana maka fatan kayi dana sanin matakin daka dauka akan yarka!" Yace "Kuma maganar Ashraf kin manta dana ne? Ina son sa kamar yadda nakesona nawa...." ta dakatar dashi da hannu "Karya kake! Baka sonshi, da kana sonshi da bakayi masa haka ba ka nuna baka so ya auri yarka!" Yace "Shikenan bazan musa maki ba, amma nidai am doing this for Hoodah's happiness and maganar Ashraf am not selfish Allah yasani a cikin raina ban taba daukar Ashraf a matsayin bare ba..." tace "Amma kuma ka nuna ba kai ka haife shi ba ko kana so ko ba kaso ko ka yarda ko kar ka yarda ka nuna masa banbanci don haka kaje kayi abinda kaga dama kawai addu'a zan biku dashi Allah ya yaye maka abinda ke damunka... a matsayinka na sarki kana nufin you are always right and not wrong, ina nufin baka iya making wrong decisions kai kullum you are always right, bazai yuwu ba kuma baka fi karfin ka nemi shawara ba ko ka karbi kuskurenka ba, kaima haifanka akayi hakan baya nufin you are weak a'a yana nufin kaima mutum ne kuma dan Adam yana kuskure. Kasani nina haifeka kuma bazan fasa fada maka gaskiya ba duk wanda aka ce bayada magaya gaskiya toh ya shiga uku, don haka na fita hakkinka a matsayina nan uwa, rokona daya kawai ka duba abubuwan dana fada maka nagode...." daga haka ta mike ta gyara daurin zaninta sannan ta fice daga harabar ta barshi ya kasa koda kwakwaren motsi.

********

Tunda take bata taba tsammanin akwai ranar da zatazo ace an fasa aurenta da yarima ba, inda haka bata faru ba da yanzu saura wata hudu kacal bikinsu amma wai an wayi gari anyi canceling bikinsu... zaune suke itada Sultan hawaye na shatata daga idanunta, "Meya kawo ka wurina? Ba na ce karka kuskura kazo inda nake ba mayaudari kawai... Gaskiya ne zancen da nakeji cewar aure zakayi zaka aura wacce tafini matsayi zaka aura yar sarkin agadez!" Ya numfasa "kiyi hakuri gaskiya ne zancen da kikeji saidai wallahi...." daka masa tsawa tayi "Dama abinda nake so naji kenan kuma ka riga ka fada da bakinka! Bana son sake jin komai kuma!" Mikewa tayi da kin son kara kallon fuskarsa ta ruga da gudu tana gunjin kuka taso ace akwai wuka a hannunta da ta caka masa kowa ma ya rasa, "Na tsaneka na tsaneka Sultan kuma bazan ta6a yafe maka ba!" Ta tsaya bakin kofa ta fada masa haka sannan ta shige ciki ta barshi nan baki sake yana kallon kofar. Tafe take tana maganar zuci. Yanzu a dalilin wata wai Hoodah shine dalilin daya sa nake cikin wannan pain din, tunda take bata taba fada ba a rayuwarta amma yanzu ta kudiri she will fight wacce zai auro kuma bawai dambe ba a'a zata kwato yancinta... dakinta ta fada kan gado tana ihu hade da zage zage, can mahaifiyarta ta shigo a guje jin ana fasa abubuwa tana shigowa taga dakin kaca kaca tayi watsi da komai na dakin. "Ke Khairy meye haka!?" Nan ta fara kokarin kwace wani vase dake hannunta tana neman ta buga shi ga bango, da kyar tayi nasarar kwacewa nan suka hau kokawa tana so ta zille daga hannunta ta cigaba da aikata aika aika, nan maman ta dage ta wanke ta da mari sai a sannan ta tsaya cak daga kokowar da takeyi tana kallon wuri daya, zamewa tayi kasa ta dukar da kanta tare da rufe fuskarta ta fashe da wani irin kuka... "Mama an yaudare ni, yarima ya yaudare ni aure zaiyi Mama, shikenan yanzu aure na dashi anyi canceling baza'ayi ba, macuci! Mugu! Azzalumi...." Mama ta daka mata tsawa "Wai ke meye haka? A kan namiji kike wannan abun? Wallahi dama ki daina wahalar da kanki ki dauki kaddara, kiyi hakuri komai kika ga ya faru haka Allah ya hukunta ki kaddara yarima ba alkhairinki bane...." ta dago da jajayen idanunta tana kallon Mama tace "Indai har bazan same shi ba shi toh itama bazata same shi ba dukkanmu sai dai mu rasa ko ta aure shi bazan barta ta zauna lafiya ba sai na tarwatsa farin cikinta na rama abinda tayi mun...." Maman ce ta make mata baki "Kul na kuma jin kin sake fadin haka Khairy babu kyau kinji ko, nasan ba'a kyauta maki ba amma dai kiyi hakuri komai mai wucewa ne kuma Allah yana tare da masu hakuri...." Shiru tayi amma can kasan ranta tasan cewar sai ta rama ko ta wane hali ne....



Kuyi hakuri da wannan jiya na fita ne😅😆

No comments: