YAR AGADEZ
{Page 16}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
A hankali yake rocking dinsu yana dan jijjigasu kafin yaji chanji daga yanayin saukar numfashinta wanda hakan yana nuni da cewar tayi bacci. Daukarta yayi ya kaita kan gadonsa har ya juya zai tafi sai yaga alamun hijab dinta kamar ta takura mata, cire mata hijab din yayi sannan ya sunkuyo yayi mata dan karamin peck a goshinta karasa kashe fitilun yayi zuciyarsa cike da tausayinta.
A hankali ta bude idanunta nan ta fara juye juye, tana ganinshi ya taho gunta sai ta dan tsorata ita tabata yayi jya dafa hannunta "Calm down a Hoodah, babu abinda zan maki kinji?" A hankali ta sauke ajiyar zuciya ya xauna kusa da ita yana sanye da towel yana kallon face dinta da hawaye har ya taru "Hoodah kukan me kikeyi?" Ya fada cikin sauti mai taushi mai kuma kwantar da hankali, ji yake kamar ya bude kirjinsa ya sata a ciki yakeji, shiru tayi ta kasa magana, matsowa yayi dab da ita ya zauna yana goge mata hawayen fuskarta "Do you still trust me? Komai zai faru a gaba zaka yi trusting dina?" Bai bari ta karasa ba yayi hugging dinta hade da shafa gashinta, "Look at me Hoodah..." ya fada yana scooping fuskarta da hannuwansa biyu a hankali ta sauke idanuwanta cikin nashi "I trust you dear, I will never let anything happen to our relationship again, and I promise you Hoodah zan gano ko wacece take neman tarwatsa farin cikinmu, it's fine kinji?" Kuka ta fashe dashi "Thank you Sultan, nagode I feel relieved now..." dan Murmushi yayi mata "Tou kukan na menene kuma? Sai kace ance maki na mutu?" Ya fada yana hugging dinta, shi kanshi mamaki yake ya kasa tsaida kansa daga faruwar hakan, "How can I not trust my wife? Na maki alkawari daga yanzu I will always be by your side, kuma bazan sake bari a hada mu ba." Ta yi murmushi ita tama kasa magana mamaki kawai yake bata yadda Sultan ya chanza gaba daya kamar bashi ba, "Tashi ki shiga bathroom kije kiyi wanka, zan dauko maki duk abinda kike bata a dakinki, and forget about cooking na mana breakfast..." ba zato ba tsammani kawai sai jin hannunsa tayi ya daga ta cak har suka sauka kasa, tsaye tayi kamar an dasata ita gaba daya ji yake jiyoyin jikinta basu aiki tayi tsaye kamar wata dogari sai kawai ta tsaya tana kallonshi, "Hoodah kafin nayi counting 3 ki tafi ki wuce bathroom kiyi wankan nan, 1,2..." bai ida rufe baki ba ta zunduma da gudu bata tsaya ko ina ba sai bathroom dinsa, saida tasa key ta rufe ta tsaya tana maida numfashi, amma meyakon ta fara wankan sai kawai ta durkusa ta rizgi kukanta a nan bata taba tunani ba ko a mafarki Sultan zai zama caring haka ba, ashe dama haka yake bata sani ba? Abinda ya mata yau ya ta6a mata zuciya. Tana shiga shi kuma ya gama gyara dakin tsab baka taba cewa namiji ne ya gyara shi haka tas, yana gamawa ya sa kaya sai ya wuce dakinta ya dauko mata duk abinda yayi tunanin zata bukata da kayan da zata sanya. Koda Hoodah ta fito ta gama shirinta tsab bata ganshi ba, tana fitowa ta ganshi yana jera plates bisa dining yana ganinta ya saki murmushi itama ta mayar masa, hannunta yazo yaja ya zaunar da ita ya shiga serving dinta abinda ya girka masu wato doya da minced meat sauce sai hot coffee, ba karamin enjoying abincin nan tayi ba, ya mata dadi sosai, suna gamawa ta sauko hijab dinta yaja hannunta suka tafi gaida su Abbi. Bata taba tsintar kanta cikin farin ciki ba irin yau ba, he's a blessing to her.
Throughout ranar yau data yi spending da Sultan he's the sweetest man ever, riritata yake kamar kwai, dan wani lokaci saidai ta tsaya tayita kallonshi har sai ya mata snapping hannu sannan ta daina kallon nashi, idan ya tambayeta kallon me take mashi saidai tayi dariya tace "So nake na tabbatar idan da kai nake zaune anya Sultan kaine kuwa?" Bai iya yace mata komai saidai yayi dariya don shima kansa mamaki yakeyi. Tun daga ranar suke zaune lafiya kalau cikin kulawa da juna saidai fa ba wanda ya fahimci me zuciyoyinsu ke ciki. Shi da mai martaba gaba daya babu abinda sukeyi sai bincike sosai don gano waye ke haddasa masu fitina a tsakaninsu waye ke masu wadannan abubuwan.
******
An shude watanni, cikin watannin nan Ashraf yanata healing a hankali duk da dai ba gaba daya ba amma ya ragu sosai all thanks to Yasir, saidai fa ko fita baya yi sai Yasir yayi da gaske kafin ya fita.
Yana kwance cikin dakinsa kullum saidai kawai yaje ya gaida Hajiya mahafiiyar Yasir da safe shikenan, kannen Yasir kuwa su biyu suke kawo masa abinci kulllum, suna matukar tausaya masa gidan gaba daya dan haka suna kokarin ganin sun tsamo shi daga dilemma da ya afka ciki, ya danyi adjusting to environment din, wani lokaci haka zai kura ma bango ido abubuwa da yawa suna rushing back cikin kwalwarsa yana tunanin abubuwa da yawa da suka faru a baya, baya tunanin zaya gushe daga cikin ransa har abada har bayan ransa, wani lokaci haka zaka tsince shi yanata murmushi ko kuma yana goge hawaye, yasan dai tunda ya rasa Hoodah toh bazai taba samun wata rayuwar da yayi ta farin ciki a baya ba, saidai kunci da bakin ciki, a hankali yaji knocking kafin ma yayi magana yaji an murda kofar an shigo a hankali, Zarah ce tsaye bakin kofa rike da tray din abinci, stool ta jawo ta aje mashi kusa dashi, sannan ta tsugunna tana kallonshi cike da tausayawa "Yaya Ashraf barka da dare? Ga abincinka nan inji Hajiyah tace don Allah ka daure kaci abinda kake so ne tayi maka da kanta, don Allah kaci tace na dawo anjima na kwashe na kai mata taga ko kaci..." tunda ta fara magana yake kallonta bai ce uffan ba ya kai akalla second kamar ashirin sannan ya kalleta "Nagode Zarah." Yayi murmushi har cikin ransa, "Basai kayi godiya ba yaya Ashraf, ka riga ka zama dan gida yanzu." Ta fada tana murmushi, ta kuma ce masa "Try and be strong duk da is not going to be easy, nasan da ciwo kuma duk naji labari daga gurin yaya Yasir yadda kuke da Hoodah da duk abubuwan da suka faru abu baiyi ba dadi ba, amma kasani kowa da tasa kaddarar wannan itace taku kaddarar yaya Ashraf..." shiru yayi na yan dakikai "It's not going to be easy amma kasani kaifa namiji ne, ita kanta Hoodah baza taso ta ga yayanta cikin wannan halin ba, wata kila ita ta dauki kaddara ta cigaba da rayuwarta, kai me zai hana ka yin hakan?" Wani kwalla ya goge "I will be fine, it will surely take time, but gradually ko?" Tasaki murmushi "Yes sure, kadai ci abincin nan please ko in zuba maka?" Ya girgiza kai "A'a Zarah karki damu, thank you." Ta mike tana murmushi "You are welcome kaci fa zan dawo na duba." Yayi murmushin shima "Zanci." Daga haka ta sa kai ta fita daga dakin.
Yasir ya shigo parlon Hajiya tana zaune kan kujera ya zauna kasa kusa da ita "Ina wuni Hajiya?" Tace "Lafiya lau Yasir." Yace "Gani Hajiya naji ance kina nemana?" Tace "Eh hakane, abinda yasa na kiraka shine inason muyi shawara da kai." Yace "Toh Hajiya." Ta gyara zama "Wannan yaro Ashraf wato abokinka dinnan, a gaskiya ina matukar jin tausayinsa, kuma ni gani nake wannan zaman kadaicin da yake yana kara contributing to kara damuwa a gareshi, sheyasa na zauna nayi tunani naga me zai hana mu hada shi aure da Zarah?" Yasir yayi murmushi "Hakika Hajiya ba ke kadai ba nima abin ya dameni sosai da sosai, nayi iya yina na ganin na tsamo shi daga cikin wannan halin da yake ciki amma abun yaci tura, gaskiya naji dadin shawarar nan taki Hajiya, kuma bana tunanin za'a samu matsala daga ko wane bangare, Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi, hakan ma karamin rage masa damuwa zaiyi ba." Tace "Sosai ma dan haka kaje kayi shawara dashi." Yace "InshaAllah zanyi." Tace "Shikenan tashi kaje." Daga haka ya mike ya shige ciki.
*********
2 days later....
A gigice ya bude idanu, ba inda jikinshi baya kadawa zufa kuwa gaba daya ta wanke masa jiki, ya saba mummunan mafarkai amma na yau yasha bam bam, bazai iya cewa ya kalar mafarkin yake ba amma dai ya tsorata matuka, Hoodah ta bude idanu itama a tsorace ta kunna bed side lamp tace "Sultan lafiya? Meyafaru? Ko mafarki ka sakeyi marar kyau?" Ta tambaya tana dan taba fuskarsa data jike jagab da zufa, duba time Hoodah tayi taga karfe biyun dare, addu'a ya shiga jerawa jikinshi na cigaba da kadawa Hoodah na tayasa addu'ar duk da tazo bakinta. itama zuwa yanzu ta fara tsorata, "Sultan menene?" Ta sake tambaya a tsorace, saida ya dan dawo daidai ya furta yana maida numfashi "Wani mummunan mafarki nayi marar kyau." Tace "Wane iri?" Yace "I can't say, bansan ya zan fassara sa ba," ta dora kanta bisa kirjinsa "It's okay InshaAllah, everything will be ok." Yayi mata murmushi, nan ta tashi taje ta debo masa ruwa ta kawo masa ya fara sha, yana cikin sha dinne sukaji kururuwar mutane da hayaniya, da sauri Hoodah ta kalleshi jin ana jijjiga kofarsu kamar za'a ballata, Hoodah batasan lokacin data bude ba, dogawara sun kai bakwai tsaitsaye sai zufa ke keto masu, "Ranki yadade, Sarki da Sarauniya...!" Cup din Sultan ya saki take ya tarwatse kasa, Hoodah ta juyo sai yanzu ma kwalwarta tayi registering abinda suka fada masu, kallo daya tayi masa ta lura kamar hankali baya jikinsa, "Meyafaru dasu?" Ta tambayesu, "Sai dai kuzo ku gane ma idonku." Suna fadan haka suka juya da sauri suka bar wurin, a hankali ta taka kusa da shi wani irin bala'in shock ne kwance kan fuskarshi, kofar ya kura ma ido bako kyaftawa gaba daya kwalwarsa ta chunkushe, Hoodah itama kanta batasan yadda zata misalta abinda takeji ba, glass din da ya tarwatse kasa Hoodah ta tattara gudun kar a ji ciwo don dukkansu bamai takalmi a kafa, dispenser taje ta debo masa ruwa ta sa masa a baki gaba daya ya zuke ruwan nan kafin ya saki wata ajiyar zuciya, sulalewa yayi kasa gani yake kamar abinda suka fada mashi karya ne gani yane wasa ake masa, dan marin kansa yayi yaji ko shin har yanzu mafarki yakeyi bai farka ba? Hoodah itama sulalewa tayi bisa gwiwoyinta kusa dashi ta kura mashi ido, tunda ya sulale a gurin da kyar ko numfashin kirki bai iya yi, sai da yaji muryar Hoodah tana fadin "Sultan kazo mu tafi..." ta fada tana dragging dinshi wai ya tashi, sai yanzu Sultan ya dawo hayyacinsa tunani yake meyafaru? Meyafaru da iyayensa? Mutuwa sukayi? How? When? Where? Ya za'ayi su tafi su barshi a take? Shin basu san rayuwarshi is incomplete bane without his parents? The people he love beyond everything and everyone, they're his entire life, saukar hawaye daidai kumatunsa yayi daidai da furtawarsa "I need to go and see... nasan ko me nake tunanin ya faru dasu ba haka bane, they're ok, they can't do this to me ko Hoodah?" Take yaji wani tausayin kanshi ya dirar masa, wani gunjin kuka ya saki wanda ya razana Hoodah itama take ta fashe da kuka, sun kai minti hudu a haka kafin Hoodah tayi karfin halin mikewa tsaye kamar yar maye tana tangadi, cikin karfin hali ta soma jan hannun Sultan "Tashi muje Sultan, let's go and see for ourselves." Gyada kansa yayi ya mike tsaye da kyar kafin ta kamo hannunsa suka fita daga gidan. Tun daga wajen sashen zuciyarsu na wani irin harbawa ba kamar Sultan da yake jin kamar zata huda kirjinsa ta fito, hannunsu rike cikin na juna suka kutsa kai ciki, wani irin sakin hannun Hoodah yayi ya karasa cikin parlon da sauri hawayenshi suka tsaya cak, Abbi da Ummi suka gani kwance kasa tsakiyar parlor dogarawa sun zagaye su da wasu wanda baya gane ko su waye, steps uku ya kara baya baya ganin jini na fita ta goshinsu da cikinsu, Hoodah na karasowa kusada su a gigice ta rufe bakinta da hannuwanta biyu, wata irin kara ta saki ta zube nan jikinta na kyarma....!
No comments:
Post a Comment