Monday, 21 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 21

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 21}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Da kansu suka ja mata rigarta kasa sannan suka mikar da ita tsaye, kuka take harda shasheka daya ya kece da dariya "Ba dai ice cream kikeso ba? Gashi nan mun baki." Suka sake kecewa da dariya gaba dayansu, fizgo ta sukayi suka cillata cikin mota, haka suka tada motar motsin kirki Khairy ta kasa yi  in banda kukan fitar rai babu abinda takeyi, hayaniya sukeyi cike da nishadi cikin motar "Kai ay amma fa mutumina ka cika wayau wato wai ta bimu kwadayin shan ice cream sai gashi mun bata hot tea!" Wata irin makirar dariya suka sheke da ita, yace "Allah mutumina nake gaya maka na dade ina kwadayin yarinyar nan kasan dole saida wayau da dubara in kana son cinma burinka!" Suka kwashe da dariya gaba dayansu, wani irin bakin ciki ne ya lullu6eta, ji tayi sun tsayar da motar kafin ma ta ankare taji sun jefar da ita tana kallo suka tada motar suka tafi suka bar ta cikin kasa, ita yanzu ya zatayi? Ina zata saka ranta? Wannan wace irin kaddara ce haka ta afka mata? Ko a mafarki bata ta6a tunani ba! Dama haka duniyar take cike da marassa imani? Hawaye ta cigaba da zubarwa, tabbas tasan dare ya lula can tsakiya wani sanyi da taji yana ratsata, yanzu tasan in ta koma gida ubanta Mama zataci, babanta kuwa ay kasheta kawai ma zaiyi! Da kyar ta mike ganin wani rumfar shago tana tafiya da kyar ta lallaba ta isa wurin ta zauna, nan take kuka ya dawo mata sabo, zuciyarta kuwa kamar ana tafasa ruwan zafi takeji kuka take bil hakki har tana cijewa har ji take wani wahalallen zazzabi ya rufeta kamar yadda yayi ma ruhinta da baibayi, kwantawa tayi bisa dakalin shago don kuwa ko motsin kirki bata iya yi a nan bacci yayi awon gaba da ita baccin kuwa babu abinda ke cikinshi sai tarin bakin ciki da takaici.

Sanyin asuba ne yayi nasarar tada Khairy daga wahalallen baccin da takeyi, tana bude ido wani dafin bakin ciki ya daki zuciyarta nan take hawaye suka sake zubo mata, hakkun a wajen shago yau ta kwana shagon ma tana tunanin na saida kayan dinki ne. Bakin titi ta nufa tana tafiya da kyar ta samu machine ta hau gidan wata kawar ta mai suna Zaliha ta nufa, daidai bakin gate ya ajeta saukinta ma tana aje kudi cikin bra dinta nan ta zaro wasu yan chanji ta mika masa, kwankwasawa ta soma yi can mai gadi ya zo ya bude yana ganinta ya fara murmushi don yasanta sosai kawar Zaliha ce ta secondary school, bata ko jira ta gaishe shi ba tayi ciki da sauri ta kofar baya tabi don tasan basu kulle ta tana bude kofar taci karo da Zaliha tsaye da cup din ruwa wanda kallo daya zakayi mata ka hango baccin dake idanunta, a tsorace ta dago tana kallon Khairy "Innalillahi Khairy kece?" Ta fada dafe da kirji idanu a waje, sulalewa tayi a kasa tana wani irin gunjin kuka "Zaliha sun cuceni! Sun gama dani! Na shiga uku!" Kuka take kamar ranta zai bar jikinta, a hankali Zaliha tayi hugging dinta ta tadata tsaye ganin kukan Khairy bazai kare ba yasa taja hannunta suka tafi dakinta ta zaunar da ita kan gado tace "Khairy kiyi hakuri don Allah! Wallahi Bangane me kike nufi ba? Zazzabi kike ne? Naji jikinki da zafi. Bari naje dakin Mami na dauko maki magani in kika samu bacci anjima sai muyi magana."  Tana fadan haka ta mike ta fita daga dakin can sai gata ta dawo da cup din ruwa da magani a hannunta, bayan tasha maganin ne Khairy ta kwanta, har lokacin bata daina kuka ba ita kadai tasan bakin cikin da take ji, a haka har bacci ya sureta.

Sai can wajen 11am ta farka tana bude ido wani bakin ciki ya dabaibayeta, ashe bacci ma rahama ne? Saidai fa every second of her sleep bakin ciki ke cikinsa da tarin takaici. Da ta tuna yadda sukayi mata sai ta fara wani sabon kukan, dama haka duniyar take ba kowa ke son ganinka cikin farin ciki ba? Cusa kanta tayi cikin cinyarta tana gunjin kuka, a haka Mamin Zaliha ta shigo "Wai Khairy ce taxo da sassafe? Lafiya kukan me takeyi haka?" Zaliha tace "Wallahi bansani ba Mami, tun dare ta shigo gidannan tana wani irin kuka da kyar nasamu tayi shiru na bata magani shine tasha ta kwanta, Khairy don Allah ki fada mana meyafaru?" Cikin kuka Khairy ta soma magana "Mami ashe haka wasu mutanen suke? An wulakantani Mami, haka zan kare babu mai aurena ko? Nasan idan Mama ta gane korata zatayi Babana kuma ya tsine min." Dan rungume ta tayi Mamin alamun rarrashi "Khairy ki saurara kinji? Waya gaya maki babu wanda xai aure ki? Yanzu dai ki fada mana meyafaru? Komai yayi zafi maganinshi Allah." Ta tsaida kukan nata "Da misalin karfe sha daya na dare akwai wani guy da na taba haduwa dashi ya nuna man shi corper ne zuwa yayi ashe cutata zaiyi, kullum muka hadu sai yace man sai na bishi shan ice cream, jiya daya zo na bishi dashi wasu friends dinsa su uku suka taru suka yi min fyade, fyaden cin mutunci suka tullani cikin daji da suka gama suka wullani bakin wani shago suka gudu...." kuka ne yaci karfinta takasa ci gaba wani sabon zafi takeji da radadi a cikin ranta, rarrashinta Mamin ta cigaba dayi kafin Khairy ta cigaba "A bakin shagon nayi baccin wahala don wallahi ko hauka nake bazan fara komawa gida ba, Mama kuwa dama tsine min zatayi sai nasha shi ba iyaka hade da zagi, na gaji da rayuwa dama mutuwa nayi da wannan abun...." Mami tace "Kul na sakejin kin fadi haka..." Khairy ta cigaba "Inaga abinda na shuka ne na fara girba tun yanzu..." Mami ta dago tana kallonta tace "Me kika shuka?" Ta share hawayenta "Mami ay dai kinsan yadda nake da Sultan ko Yarima?" Mami ta gyada kai "Ba yayi aure ba kar dai har yanzu baki hakura dashi ba Ummalkhairy?"  Ta gyada kai "Ban hakura ba ina sonsa Mami, kuma bana jin zan iya hakura, toh shine na dinga kulla makirci kala kala babu abinda banyi ba don ya rabu da ita baiyi ba, wannan abun daya faru dani sak na aika a mata irinsa daren da aka kaita amma sai basuyi mata fyaden ba, sai suka yi recording bayan nan nayita kokarin tarnishing image dinta wai fa don dai ya tsane ta ya rabu da ita amma a banza karshe ma sai yaci man mutunci yace ya tsane ni bazai aureni ba..." ta karasa tana kuka Mami ta numfasa "Tabbas kinsan in har akace hakki toh an gama komai, tabbas hakinta ne yake bibiyarki kuma inaso kisani baki kyauta ba tou shi kishi hauka ne Khairy? Da haka zaki kwaci soyayya? Yanzu da kikayi haka kinyi nasara? Kinga dai tun ba'a je ko ina ba kin fara kwasar kashinki a hannu, kuma muddin baki nemi gafararta ba toh ina tabbatar maki da yanzu kika fara haduwa da bakin cikin duniya kafin ki hadu dana lahira! Dan haka tun wuri ki nemi gafarar wadanda kika cuta saboda basuda hakki a kanki sai kiyi tunani."

Sai bayan sallar azahar Mami ta kwashi Khairy a mota xata maida ita gida ana shiga layin gidan ta fara zufa ihu ne kadai ya rage ta kurma, suna tsayawa Mami ta juyo tana kallon Khairy duk yadda ta tsure sai ta bata tausayi matuka, itadai kawai zata taimaka mata ne "Kinaji Khairy? Ki kwantar da hankalinki, nan ba gidanku bane? A nan fa aka haifeki kika girma?" Nan Mami da Zaliha suka fito daga motar suka jawota da lallashi da ban baki suka samu da kyar tace zata shiga tana tafiya kamar wacce aka ma duka don har yanzu jikinta ko ina ciwo yake mata, suna shiga gidan suka iske Mama bakin kofa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba masifa ce take zazzaga ma Baba kamar wani dan cikinta wainan dole sai ya tashi ya tafi neman Khairy kamar zata cinye shi danye wai ya tashi ya shiga gari neman Khairy, ita kuwa Khairy najin an fadi sunanta take yan hanjinta suka hautsine, "Na rantse da Allah zama bai ganka cikin gidannan ba, namiji dakai sototo wai kai a dole kana cikin damuwa alhalin yarka bata kwana gidannan ba! Itama shegiya gantaliyar banza da wofi na rantse da Allah idona idon Ummalkhairy dan idan na damketa sai dai kila yan sanda ne zasu amshe ta a hannuna, dan ubanta ni zata jama abun kunya cikin unguwa? Ace wai wai katon banza ne ya dauketa cikin mota, gidan ubanwa taje? Na rantse maka da Allah....!" Mama bata karasa magana sai ga Khairy ta kutso kai ta shigo jikinta kamar mazari sai kyarma takeyi cike da tsoro "Ke! Zo nan dan ubanki! Gidan ubanwa kikeji? Gidan wane kato kika kwana? Wane dan iskan ne ya daukeki? An fada man anganki kinbi saurayi cikin dare! Na rantse da Allah yau cikin biyu za'ayi daya, kodai masu wankan gawa su amshe ki hannuna ko kuma yan sanda su kwace ki su mika ki can wurin malaman asibiti dan ubanki!" Kukan kura Mama tayi tayo kanta gadan gadan ta wani shako wuyan Khairy kamar zata kasheta, bata ma lura tare take da su Mami ba ita kuwa sai masifa take yarfa mata, a guje Mami tayo kanta ta shiga kokarin raba su....

Da kyar ta kwace ta tana ta faman bata hakuri da kyar da ji6in goshi ta yadda ta hakura suka kaisu parlor suka zazzauna, ta gefen Baba suka wuce bayan sun gaishe shi shidai kanshi a duke ya kasa dagowa alamun kunya, bayan an natsu "Kamar yadda kuka gani tare muke da Khairy, kiyi hakuri Khairy bawani wajen banza taje ba, tare suke da yar wajena gata nan Zaliha aikensu nayi shine suka tafi yayanta Zalihar mafarin kenan da aka ce anganta cikin motar saurayi, amma dan Allah dan annabi kiyi hakuri dalilin rashin dawowarta gida jiyan naga sunyi dare sheyasa nace su tsaya su kwana gidana da safe sai in maidota har gida kuyi hakuri dan Allah." Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Mama ta sauke "To to ay babu damuwa indai hakane mun gode Kwarai da gaske Allah ya bar zumunci." Baba ya gyara zama yace "Mungode Hajiya Sakina, amma nidai nayi fadan nayi fadan akan yawon yarinyar nan bataji, kullum ina mata fada amma kamar baya shiga Kunnenta zagayowa yakeyi ta bayan kunne, amma babu komai tunda jiya ma tana tare dake ay alhamdulillah mungode da kulawa Allah ya bar zumunci." Tace amin nan suka gama tattaunawa daga karshe Mamar ta mike itada Zaliha suka tafi, har bakin gate ta rakasu sannan ta juyo ciki.

*********

Cikin ikon Allah tunda aka fara ma Sultan magunguna da rubutu yana sha aka dage bil hakki sai gashi ya warke tas, saidai tunda ya dawo daidai yaji baya son ganin Hoodah tsanarta yakeji har baisan ganinta for no reason. 

Ranar wata Thursday sunyi fada sosai har tana tsoron fita parlor su hadu tana daki zaune har karfe goma da kusan minti hamsin, ga yunwa na addabarta ji take kamar ranta zai fita tsabar yunwa ita tsoronta bai wuce su hadu ba idan ta fita, saida da taga har 12 kuma batajin motsin kowa ba sai kawai tayi shahada ta fito kitchen, tea kawai ta hada tayi frying eggs ta zauna parlor tanaci haka nan takeci bawai don dadi ba, ita dai kullum addu'arta Allah ya saka mata cikin gaggawa duk wanda ke son ganinta cikin bakin ciki tana addua'r ya dawwamar dashi cikin kunci har abada. Da rana bai dawo ba sai kawai ta dafa indomie har dai wajen goman dare babu alamun shi, nan ta fara jin tsoro kodai shaye shayenshi ya koma? Tace no ay Kawu na prison ta ya zai cigaba? Nan parlorn bacci ya dauketa can sai wajen daya na dare taji alamun an shigo, zumbur ta mike ta nufi inda yake taga babu alamun maye a tattare dashi, "me kikeyi a nan? I told you several times ki fita harkata wai ke mayyar ina ce? Na tsane ki Hoodah! And for the last time ki fita harkata in ba haka ba sai na farfasa maki baki!" Cikin wani irin kuka take girgiza kai zuciyarta na tafarfasa "Toh wai dole ne zama dani? Nima na tsaneka na tsaneka in baka iyawa ka rabu dani mana!" Cikin wata irin razananniyar kara ya furta "Bazan rabu dake ba! Zama dake yanzu ma na fara!" 

Babu irin kukan da Hoodah batayi ba tasan yana daga cikin dakinsa yana jinta amma ko alamar zai bude kofa baiyi ba, karshe ma bubbuga kofar takeyi akan ya bude kofar ya sauwake mata don gaskiya ita ta gaji da wannan wahalallen auren yau dadi gobe babu, tun tana jin alamar motsinshi a cikin dakin har ta daina, nan ta silale bakin kofar tasa tun tana kukan har bacci yayi gaba da ita. Da asuba sai dai taji motsinshi ko kafin tace wani abu har ya tsallake ta ya fita daga gidan, tunda taga ya fita da wayarshi a hannu tasan bazai sake dawowa ba sai dare yau ma, haka ta wuni cikin gidannan tun tana kiran wayarshi bai dauka har ya koma yana rejecting, gashi bata taba tunanin soyayyar da take ma Sultan tayi zurfi haka ba abun har ya fi karfinta ma.

Wasa wasa har sunyi sati daya a haka tun yana kwana cikin gidan har ya daina a cewarsa baya so yana haduwa da ita baya son ganin koda fuskarta, tasan dai babu inda zaije ya kwana daya wuce sashensu Ummi, tun tana kuka har ta hakura ta fawwala ma Allah lamarin ta koma addu'a sosai ba dare ba rana, duk yar kibar da tayi ta zube ta koma kamar a hure.

Suna cikin sati biyu a haka ne ranar taji motsinsa a parlonta, da sauri ta fito ko dankwali bata sa ba, sai ta iske shi dauke da trolley din kayansa ga kayansa a saman kujera ya watsa, kallo daya ta masa take hawaye suka fara zarya, kana ganinshi kaga wanda yake cikin matsananciyar damuwa amma duk da haka baiyi lalacewar da Hoodah tayi ba. Ko kallon inda take baiyi ba, "Ki hada kayanki na kaiki Agadez...." wani irin duka da kirjinta yayi sai kayi tunanin ce mata akayi ya rasu a hankali ta kama bangon dake gefenta ta rike har wani jiri take gani, sai can taji ya furta "Zanje nayi 10 days a can." Ko jira yaga halin da take ciki baiyi ba kawai ya suri bag dinshi ya fita daga gidan gaba daya sai dai taji ya bude mota....

No comments: