Sunday, 27 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 27

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 27}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Shima same kallon data yi masa ya bita dashi sannan yace "Yawwa." Yana gama fadan haka ya bude mota ya shige yabarta nan tsaye, glass dinta ta maida Yasir ya zagayo yana mata wani mugun kallo yace "Wai ke yaushe zakiyi hankali? Gaskiya ki chanza hali." Yana fadan haka ya juya ya shige mota, kafada ta make alamun oho sannan ta bude mota ta shiga itama, nan ya tada motar suka bar airport din. Bayan yayi parking ko rufe motar bai ida yi ba Khadija ta bude motar ta fito da gudu tayi cikin gida, "Mummy!" Ta kwala mata kira tun daga bakin kofa aikuwa da sauri Mummy ta taso nan tayi hugging dinta, cike da murna Zarah ta fito itama jin hayaniya tace "Oyoyo mutan Turai!" Nan sukayi hugging juna, janta sukayi cikin parlor ta zauna tana cire jacket dinta tana wani fifita da hannu, "Mummy Nigeria zafi akeyi haka?" Mummy tayi murmushi "Sannu baturiya, kedai nan don kin saba da weather din can sheyasa amma ay babu zafi yanzu haka damina ta fara kawo kai." Shiru tayi ganin su Yasir sun shigo bakin kofa ya aje mata akwatinta yace "Ke bazaki iya tsayawa ki fito da akwatinki ba saboda kin rainawa mutane hankali ko?" Ashraf ya dafata "It's ok kaga ay tana murnar ganin Mummy ne dole ta manta akwati." Yasir yace "Toh idan kin gama sai kizo ki shiga dashi ciki." Yamutsa baki tayi alamun shagwaba "Kai yaaya na gaji fa." Tsaki yayi ya wuce dakinsa Ashraf na biye dashi a baya, Mummy ta mike tana fadin "Halinki dai na nan Khadija da lalalaci aikuwa dole ki dauke kayanki. Sai ki tashi kije ki watsa ruwa ga abinci nan kici." Tana fadan haka itama ta wuce dakinta, Khadija ta turo baki Zarah tayi dariya, Khadija tace "Yawwa wai wannan waye yake zaunen mana a gida?" Zarah tayi murmushi "Har kin manta yaya Ashraf? Wanda da suna karatu waje tare? In suna Niger ma ya kanzo nan garin har yayi kwanaki ya tafi? Yana da jinin sarauta kawunsa ne sarkin agadez...." shiru tayi alamun tunani can tace "Ohh na tuna sa, ay na dade ban ganshi ba sheyasa na manta fuskansa." Zarah tace "Sarkin mantuwa, tou yanzu dai ki tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci." Mikewa tayi tace "Don Allah ki taimaka ki hau mun da akwatina sama." Zarah ta maka mata harara "Wa? Wallahi baki isa ba uwar lalaci, ni inda nice yi mun zakayi ne? Ba saidai in mutu ba?" Zarah tayi dariya "Please please dear." Rolling eyes Zarah tayi tace "Naji." Ta fada tana mikewa ta nufi akwatin nan Zarah ta mata godiya ta kwashi tarkacenta ta hau sama, ruwa ta watsa ta fito Zarah na bisa gado tana latsa waya, shiryawa tayi cikin matsatsun kananan kaya, shekeke Zarah ke binta da kallo tace "Ke meye haka?" Khadija tace "Mey?" Zarah tace "Kalli shigarki nan fa Niger ne ba turai ba, ki chanza wannan shigar taki gaskiya batayi ba," ta wani hade rai "In chanza me? So kike inta fama da atamfa kayan zafi? I can't!"

Dariya taba Zarah tace "Ay bance dole sai kinsa atamfa ba, you just have to adjust nan Niger ne ba UK ba, kuma fa kinsan munada bako nan gidan bai kamata ya fara ganinki a haka ba, sam bai dace ba ga ya mace musulma." Tsaki ta saki tana gyara zaman rigarta tace "And so? Ni nace yazo mana gida? Kawai saboda shi sai in takura ma kaina? Sam bazai yuwu ba wallahi, this is bullshit! Idan har yaga shigar da nake zata takura masa yana iya kauda fuskarsa, hope u understood?" Zarah ta girgiza kai "Ke kam dai bakida mutunci Khadija, wai ina amfanin wannan mugun halin naki? Sai kace ke kadai kika taba karatu a kasar waje? Shikenan daga zuwa turai sai kibi ki chanza halayenki ki koma fitsararriya?" Wani mugun kallo ta watso ma Zarah "Toh sannu natsatsiya! Ni kinga yunwa nakeji bari na sauka kasa..." tana gama fadan haka ta fice tana tafiyar kasaita, girgiza kai Zarah tayi ta mike don dauro alwalla.

Yau dai gaba daya a dining suka zauna don cin abinci, Zarah ce karshen fitowa tana saukowa sukayi ido hudu da Ashraf sai ji tayi gabanta ya buga, daurewa tayi ta karaso ta zauna tana murmushi ta gaishe da kowa ta zauna gefen Zarah wacce ke kokarin bude warmer din dake gabanta, sai data bude gaba daya sai ta tsaya shesheke tana bin abincin da kallo, can tace "Mummy a rasa abinda za'a dafa mun sai shinkafa? Kinfa san na dade ban cita ba ta yaya kikeso in fara cinta a yanzu?" Mummy tayi murmushi "Khadija kenan, toh me kikeso a dafa miki in ba shinkafa ba?" Ta wani yamutsa fuska ita a dole yar gayu tace "Mummy nifa can na saba cin abincinsu sheyasa sai nake ganin shinkafan ta mun wani kala na daban..." Yasir yace "Ke! Rufe mana baki a nan! Mummy kike fadawa meyasa ta maki shinkafa? In banda rainin wayau in bazaki iya mata godiya ba ay ba'ace dole sai kin ci ba ko? Wai ke meye haka? Gaba daya halinki sake yin worst yakeyi ko wane hutu kikazo...!" Bubbuga kafa ta farayi tana kukan shagwa6a, nan kowa wurin ya bude baki galala yana kallonta, can ta mike tsaye "Wallahi bazanci shinkafar nan ba! Zanje nayi order din KFC ko Pizza!" Mikewa Yasir yayi a hasale zai tsaida ta Mummy ta daga masa hannu "Rabu da ita Yasir...." zama yayi yana jin kamar ya tashi ya bata shegen kashi kila zata natsu, Zarah ta mike ta fara masu serving fried rice da peppered chicken sai salad gefe da yaji kayan hadi, bayan ta zuba masu ta tsiyaya ma kowa zobo nan itama ta zuba nata ta fara cin abinci, every second take dagowa ta kalli Ashraf wanda baisan abinda takeyi ba. Bayan sun gama cin abinci suna kan dining din basu tashi ba Mummy ce kawai bata nan, sai ga Khadija ta shigo niki niki da ledoji a hannu, a bisa dining ta dire su ko kallon kowa batayi ba ta bude kazarta da katon robar pepsi ta zauna ta fara ci, Yasir ya mike Ashraf ma ya mike yana mamakin hali irin na Khadija, Zarah ce kawai ke bata tashi ba ta zuba mata ido tana cin kayanta, gefenta laptop ce ta kunna wani series tana kallo, Zarah ta numfasa "Yanzu tsabar karya kice baki iya cin shinkafa? Uban me kike ci a da kafin ki tafi uk din?" Tabe baki tayi "Wai nikam meyasa kika fiya sa ido ne? Sanin da kikayi mun a da tou yanzu na chanza nace bazan iya cin abincin nan ba ko dole ne?" Zarah tace "Da kyau, komin tsiyarki dai nan ne tushenki, muna nan dake zaki dawo kina neman abincin namu dole kici ba!" Tana gama fadan haka ta mike ta fara clearing wurin.

****

One week later....

Ashraf ya saki jikinsa sosai da Zarah sun zama friends duk da ita a bangarenta ba haka ta dauke shi ba tana matukar sonsa, amma dai Ashraf shi kawai ya kasa bude heart dinsa gaba daya amma dai suna friendship sosai, Khadija kuwa a nata bangaren rashin mutuncin yau daban na gobe daban, gaba daya halinta bai ma Ashraf ba, miss grumpy ma yake ce mata gashi ta tsani sunan, in kuwa ta bushi iska ta bar gidan yawo take tafiya Yasir yayi zagin yayi fadan amma duk a banza. 

**

Zarah tana zaune parlor tana cin apple at the same time tana kallo Ashraf ya shigo parlon yana kallonta yace "Wai bakya gajiya da kallon series dinnan ne?" Tayi murmushi "Bana gajiya dashi, ga apple bismillah." Daya ya dauka yana ci a hankali suna fira jefi jefi, Khadija ce ta shigo da sallama, tana sanye sa doguwar riga sai ta dora hola, kujerar da Zarah ke zaune akai ta zauna tana fuskantar Ashraf, kwana 2 sunyi noticing yadda ta chanza rawar kanta ya sauka sun rasa meya chanza ta haka gaba daya, Zarah tace "Wai meyake damunki Khadija?" Yamutsa fuska tayi ta dauko apple daya taci sannan tace "Me kika gani uwar sa ido?" Zarah tayi dariya "Kwari ma kuwa, naga kinyi sanyi ne." Ta kalli Ashraf da hankalinsa ke kan tv ta sauke ajiyar zuciya, "Tou babu abinda ke damuna sa idawa." Dariya taba Zarah tace "Haka akeso ay miss grumpy." Harara ta watsa ma Ashraf "Kagani duk kai kaja man wannan sunan yanzu gashi nan Zarah tana kirana dashi." Yayi murmushi "Tou ba gaskiya take fada ba miss grumpy?" Hade rai tayi "A'a bawani gaskiya wallahi."

*****

Da asuba bayan Ashraf ya gama sallah sai kawai yaji baya son komawa bacci fitowa yayi waje, shakar iskar asuba mai hade da ni'ima da kamshi dadi yayi, zama yayi a garden ya jingina da kujera ya lumshe idanu, "Good morning yaya Ashraf." Bude ido yayi ya ganta tsaye cikin kayan bacci riga da wando purple color sai tasa hula, "Good morning miss Grumpy!" Dan bata rai tayi "A'a am not nikam." Yayi murmushi "Toh how are you?" Tace "Alhamdulillah you seem to be enjoying the cool breeze today." Yace "Yes is a good feeling." Ta dade tana kura masa ido kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Tou bari na shiga cika bacci zanyi." Ok yace mata kafin ta fara tafiya a hankali tayi ciki.

Da rana Yasir da Ashraf sun dawo daga wata unguwa suka nufi kitchen jin hayaniya, Zarah da Khadija ne tsaye suna girki, Yasir ya leka ganin jollof rice ya sa yace "Tou mutan turai har kin fara cin shinkafar ne?" Zarah ta kyalkyale da dariya harda dukewa tace "Na nawa kuma? Ay yanzu karyarta ta kare saidai kuma idan komawa tayi can." Hade rai tayi tana cigaba da abinda takeyi, Yasir ya matso kusa da ita yace a hankali "Mufa mun gaji da ganin grumpy face dinki ya kamata ki saki ranki malama." Kara hade rai tayi ta kalli Ashraf da ya harde hannu yana binsu da kallo, "Zarah please miko mun curry." Ta fada hade da juya fuskarta gefe tana sauke ajiyar zuciya ita kadai tasan yadda zuciyarta ke harbawa, Zarah ta tsare ta da ido ganin yadda take sauke numfashi sannan ta kura ma Ashraf idanu har wani murmushi take saki, gaban Zarah yayi wani mummunan faduwa kar dai tunanin da takeyi akan Khadija gaskiya ne? Kar dai son Ashraf takeyi? Ji tayi ta kasa tsayuwa da sauri ta bar kitchen din har tana hada hanya, gaba daya suka bi Zarah da kallo....

No comments: