YAR AGADEZ
{Page 06}
Kamar kullum tana zaune suna labari itada Kaka akayi sallama Jamila ce daya daga cikin bayi ce ta shigo ta durkusa kasa tana fadin
"Barka da hutawa Kaka, Barka da hutawa Gimbiya, Gimbiya wai kizo Yaya Ashraf yana son ganinki...." tayi shiru can tace "Kice masa ina zuwa." Tafi minti sha biyar batada niyyar tashi Kaka tace "Me kike jira Hoodah? Kije ki same shi mana." Tace "Zanje..." Kaka tace "Toh tashi mana yana can yana jiranki. Ko kina gudun kada Karima ta ganku tare ne?" Ta gyada kai a hankali, Kaka ta dafata "Babu matsala tashi kije don yanzu na tabbatar tana can daki tana zuga bacci." Tashi tayi a hankali ta fice daga dakin Kaka ta nufi inda tasan zata same shi, da isarta sai ya bita da kallo har ta karaso ita dai kanta na kasa, tana zuwa ta samu wuri ta zauna ta gaishe shi ya amsa fuska sake, yayi murmushi yace "Kwana biyu kina guduna ko? Meyasa?" Ta fara inda inda "Abinda.... ya... yasa... na....na...." ya numfasa "Meyasa Gimbiyata...?" gabanta ya dan buga tace "Babu komai fa." Yace "lafiya dai ko?? Kina jin tsoron Umma ne?" Ta girgiza kai da sauri tana kalle kalle yace "Shikenan tashi ki tafi...". Ta mike da sauri har tana hada hanya zata bar gurin kawai taji tayi karo da mutum, Saurayina tayi taga taga zata fadi Gimbiya tayi saurin tarota a tsorace, Da sauri Ashraf ya mike inda Sarauniya ta tsaya tana kare masu kallo, "Mey kukeyi a nan? Kuma a tare?" Duk sukayi shiru Karima tace "Ohh a gidannan ban isa na bada doka ba sai ku karya mun? Sau nawa zan maimaita maganar nan? Nace kar ku sake ke6ewa tare amma da yake kunnuwan qashi ne daku ko kuma kun raina ni ban isa daku ba?" A hankali Ashraf ya tako dab da ita sannan yace "Hoodah kanwata ce ta jini ko babu soyayya tsakanina da ita akwai alaka mai karfi tsakaninmu, ke baki isa ba kice zaki karya bond din dake tsakanina da ita, duk fiffiko nan naki da wani nuna isa da gadara da kike takama dashi bai isa yasa naji tsoronki ba, mun maki biyayya iya biyayya amma da yake bakida imani....." bai karasa ba Karima ta dauke shi da wani irin wawan mari ta daga hannu zata kara dauke shi da wani marin saidai taji an rike mata hannu gam bata karasa marin ba, ta dago a fusace sai ganin Hoodah tayi tana mata wani irin kallo idanunta jawur, "Duk abinda zakiyi kar ki sake daga hannu kice zaki mareshi no matter what..." wullar da hannun tayi taja hannun Ashraf da har yanzu shock din marin bai sake shi ba tayi hanyar fita, har ta kai kofa Karima tace cikin daga murya "Bari kuji na fada maku bazaku taba yin aure ba indai ina bisa doron kasa ina rayuwa, na haramta maku yin aure don haka kuje ku gama soyayyar taku a banza, sannan dani kuke zancen sai na nuna maku wacece ni a yau dinnan, tuggu da makircina zan nuna maku tasirinsa a yau, tana gama fadan ta juya itada bayinta tayi hanyar harabar mai martaba tana matsar kwalla... da isarta kawai sai ta zube gabansa ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, da sauri sarki ya taso yana tambayar lafiya? Ita kuwa sai ta kara sautin kukanta, dagata yayi ya zaunar da ita yana rarrashinta sai data tsaida kukan nata kadan sannan tana shesheka tace "Tunda nake a rayuwata ban taba cin karo da jarabawa ba irin ta yau, ka duba fa kagani mai martaba yaran nan ni ce nayi dawainiya dasu, da cinsu da shansu, sutura da sauransu duk ni nayi, amma yau sunyi girman da har ni zasu daga hannu su mara, daga ita har Ashraf daga wai nace masu su daina shige ma juna kaga yadda na iske su dazu? Kamar zasu shige cikin jikin juna wai da sunan soyayya yanzu shikenan daga nace basu kyauta ba yanzu nayi laifi kenan? Ashe ban isa dasu ba saboda ban haifi nawa ba ko?" Ta kara fashewa da sabon kuka, sarki ya mike a fusace yace "Ay wannan bake suka raina ba kadai har da ni suka raina, Kai Sadiqu jeka kira man su yanzu yanzu kace suzo su sameni a fada..." da sauri dogarin ya ruga ba'a dau lokaci ba sai gasu sun shigo a tare suna shigowa sarki ya shako ma Ashraf wuyan riga yana jijjiga sa "Yanzu kai wuyanka har yayi kwari haka? Ka daga hannu ka wanka ma matata mari? Ko baka dubi matsayinta gareni ba ay ka duba dawainiyar da tayi daku!" Cike da rashin fahimta yace "Abba wallahi ban mareta ba ta ya za'ayi in mareta? Ita ce fa ta....." Karima ta fashe da wani sabon kuka tace "Kagani ko Mai martaba? Wai karya zaiyi man Wallahi karya yakeyi tambayi jakadiya...." Hoodah ta kalli Karima cike da mamaki tace "Umma...?" Abba yace "Yi man shiru a nan marar kunyar wofi, tunda kukayi wa matata wannan dibar albarkar toh dole na dauki mataki a kanku!" Sadiqu kuje ku rufe man su a dungeon yanzu sai gobe yi war haka za'a bude su..." Ba abunda Hoodah keyi sai faman zubar da hawaye zuciyarta na tafasa wane garwashi suna ji suna gani aka kulle su sai kace wadanda suka aikata kisan kai. Tunda Kaka taji labari ba irin magiyar da batayi ba da fada amma fir ya ki sauraronta... Aikuwa Kaka ta dauki fushi dashi can kasan ranshi yasan bai kyauta ba amma ya kasa ta6uka komai yana tsoron Karimah.
Kafin safe duk sun zama wata kala ba kamar Hoodah duk ta kode, bai sake su ba sai wajen karfe 2 na rana da sauri Kaka ta nufi wajen Hoodah wacce ke tafiya da kyar da isar Kaka sai kawai Hoodah ta zube kasa da sauri aka sureta akayi dakin Kaka da ita inda aka kira Doctor ya shiga bata taimakon gaggawa da kyar aka samu ta farfado tana farfadowa sai ta fashe da kuka sosai, nan Kaka ta bata ruwa ta sha sosai sannan ta taimaka maka tayi wanka sai data tabbatar ta gashe mata jikinta sannan ta fito da ita, she's still in shock abinda Abbanta yayi mata ko a mafarki bata ta6a tunani ba, wai meye shiga kanshi ne haka? Wasu hawaye masu dumi suka gangaro mata, Kaka ta sa aka debo mata abinci taci kadan shima saida kaka ta tilasta mata, Kaka ta zauna gefenta tace "Kiyi hakuri Hoodah nice nace maki ki tafi wurinsa da bance kije ba da duk haka bata faru ba, ki yafe mun..." da sauri Hoodah tasa hannu ta rufe ma Kaka baki tana girgiza kai idanu sha6e sha6e da hawaye, "Ba laifinki bane Kaka, babu mai babban laifi irin Abba..." tafada tana share hawaye kaka tace "Hakika Jalal yayi nisa baya jin kira baban abun tashin hankalin shine ko maganata ma bayaji sai na wannan tsinanniyar matar tasa..." Hoodah tace "Itada Allah Kaka duk abinda ka shuka shi xaka girba..."
LATER THAT SAME EVENING
Hoodah na dakin Kaka still tana bacci kamar daga sama Kaka taga Jalal bakin kofa da hanzari ta mike a fusace ta isa bakin kofar tace "Lafiya? Waye haka? Waye kai? Me kikayi mun a kofar daki macuci kawai..." yayi shiru shi kansa baisan kwakkwaran dalilin daya kawo shi ba kawai dai abunda yasani ya aikata ba daidai ba, dukar da kansa yayi kasa yace "Nazo in duba Hoodah ne..." da sauri tace "Wace Hoodar!?" Yace cikin kwantar da murya "Yata mana Kaka ki taimaka ki barni na duba ta..." Kaka tasa hannu ta tare bakin kofar tana fadin "Ya kuke da Hoodah? Ay bakada wata sauran alaka da ita maza ka juya ka koma wurin wacce kafi so tun muna biyu da kai..." yace "Don Allah kaka kawai halin da take ciki zan gani." Kaka tace "Ka damu ne? Mugu kawai kaje dai kayita biyewa waccan matar taka ta kaika ta baro, ni matsa bani wuri..." ta ture shi ta rufe kofarta da key, ya juma a nan yana knocking amma fir Kaka taki bari ya shigo, yafi minti talatin tsaye nan tun yana sa ran zata bude har ya gaji yajuya ya koma kamar wanda kwai ya fashewa a jiki, yana isa fadarsa ya hadu Karima tana fadin "Ranka ya dade lafiya?" Daga mata hannu kawai yayi ya juya yayi komawarsa daki, ta6e baki tayi ta kama gabanta. Haka sarki ya kwana yana juye juye bai ta6a feeling guilty ba irin na yau gaba daya ya rasa natsuwarsa, gashi saura sati biyu kacal a daura auren Hoodah da yarima amma gaba daya ji yake auren kamar a fasa saidai bazai iya tunkarar Karimah ba da maganar nan dole saidai ya hakura.
Washe gari da misalin karfe sha daya na safe daya daga dogarin sarki ne ya rugo a guje yana zuwa ya fadi kasa yana kwasar gaisuwa sannan yace "Ranka ya dade! Na nemi Ashraf sama ko kasa ban ganshi ba, sai wannan takardar na tsinta..." ya fada yana miko masa ita ya karba ya jujjuya ta ya mika masa "Karanta mana." Nan ya warware ya soma karanta masu: "Assalamu Alaikum Abba, da fatan idan kayi arba da wannan wasika tawa zaka fahimce ni, na tafi na barku bazan iya cigaba da zama tare da ku ba, kayi man komai na rayuwa ka kula dani na gode Allah saka da alkhairi saidai a bisa abubuwan da suke faruwa ana ganin a dalilina ne Gimbiya bataso tayi aure sheyasa na nisance ku gaba daya yadda zaka samu ka aurar da yarka cikin kwanciyar hankali. Inaso kuyi mun alkawari bazaka fadawa Hoodah ba don bana so ta tada hankalinta akan wannan, kuma ina nan lafiyata lau so karku damu, na barku Lafiya Ashraf..." squeezing takardar yayi yana kallon Sarauniya da take masa wani kallon banza tace "To shine me don ya gudu? Zakabi kawani tada hankalinka? Ka barshi yafi ruwa gudu mana ya dade..." ta fada tana wani jujjuya ido, nan Sarki yayi shiru ya kasa koda cewa uffan, tsoronsa idan Kaka ko Hoodah sukaji maganar nan yasan akwai kura, nan ya fara tunanin yadda zai bullowa al'amarin can yace da mutanen wurin "Maganar nan ya tsaya iya nan! Kar na kuskura najita a waje duk wanda ya tambayi Ashraf kuce nina aike shi wani waje shikenan..." kowa ya amsa da toh ya juya ga Sarauniya "This is a serious warning Karimah ki kiyaye..." yana gama fadin haka ya tashi ya fita. Haka kuwa akayi aka fadawa su Kaka can cikin ranta taji dadi "Gara ma ya bar garinnan ya huta ma rayuwarshi sarki ya kyauta daya tura shi wani wuri..." ita kuma Gimbiya fushi tayi cewar meyasa zai tafi bai fada mata ba? Tace lallai zai dawo ya sameta.
Tunda abinda ya faru da Abba yayiwa su Hoodah ta kasa sakin jikinta da Abbanta dari dari take dashi gaba daya ta tattaro kayanta ta dawo dakin Kaka da zama, duk wani shirye shiryen amarya Kaka ce ke fadi tashi, gaba daya yanzu Hoodah ta daina damuwa da maganar aurenta ta fawwala wa Allah komai ta saki ranta daidai misali hakan ba karamin dadi yayiwa Kaka ba. Tun ana saura sati daya daurin aure gidan ya fara daukar harami gaba daya an cika da yan uwa da abokan arziki dama wanda ba'a gayyata ba, ba wanda xai ga Hoodah yace wai auren dole ne za'ayi mata.
Ana jibi daurin aure ne Hoodah taci kukanta a bandaki ta wanke fuskarta ta fito, ranar ne kuma aka kawo lafe akwati goma sha biyar ko ita kanta Sarauniya bata zaci haka zasu kawo kayan ba don ba karamin mamaki tayi ba. Gaba daya gidan ya kacame da hayaniya, angwaye har sun iso tun safiyar ranar daurin da dangin ango, sun samu tarba ta musamman inda akaita dawainiya dasu sunji dadin hakan.
Yadda Sarauniya Karimah ke hidima sai ka rantse zaman lafiya ake da ita sai wani nan nan take da Hoodah, ita abin mamaki ma yake bata, Kaka tace "Duk abinda zatayi ki rabu da ita taje tayi... wannan rawar jikin da takeyi ba don Allah bane." Duk cikin shagulgulan biki baxasuyi bidi'a ba daga daurin aure sai walima.
Ranar daurin aure amarya tasha kyau cikin tsadaddun leshi hadade sai kamshi na musamman ke tashi daga jikinta. Makeup dinta light akayi mata wanda yayi mata very simple. Safiyar ranar da misalin karfe biyu aka daura auren Hoodah da Sultan akan sadaki dubu dari biyu, ana gama daurin aure aka dinga daukar hotuna in banda yake babu abinda Hoodah keyi don ita har ta gaji da daukar hotuna. Dakin kaka yawanci duk yan uwan Hoodah ne a ciki sai kawayenta yawanci wadanda sukayi makaranta tare dasu ne suka zo mata biki.
Washe gari aka fara shirin daukar amarya ta jirgi za'a dauka saboda nisan wurin anyi selecting wadanda zasu tafi kai amarya, saida Kaka tayi mata nasiha sosai sannan shima Abba ya dora da nashi ya dade yana mata nasiha kafin daga karshe tayi hugging dinshi tana gunjin kuka.
Haka suka tafi zuwa Niamey wanda ta jirgi ne zai kaisu awa biyu kacal.....
Tafiya take yi tsakanin dakin, daga wannan corner zuwa wata, kawar tace mai suna Abidah ta riko ta tace "Wai lafiya kike tafiya ke kadai kamar wacce keyin safa da marwa? Me akayi miki?" A mugun fusace ta juyo tana huci, "Meye ma ba'ayi man ba? Yaudara! Cin amana! Da kuma Butulci..." Abidah tace "Wai har yanzu maganar nan baki manta da ita ba ki dauki kaddara ba...?" Tace still a fusace "Kaddara kuma? Tou bari kiiji in fada maki ina nan ina jiran wacce zai auro zatazo ta sameni wallahi sai ta gwammace dama bata shigo ba, sai na dasa mata tabon da bazata taba mantawa dashi ba sannan kuma sai na addabeta yadda zai zamana ko kwadayin zama da yarima batayi zansa ya tsane ta, ya kuma kyamaceta ta yadda na rasa shi haka itama zata rasa shi bazan taba bari su zauna lafiya ba! Wallahi...! Sai illata rayuwarta! Saina muzunta mata! Sai kuma na rabata da yarima ki rubuta ki aje....!" A tsorace Abidah tace "Innalillahi wa inna ilahir rajioon, da hankalinki kuwa Ummalkhairy? Wai kishi hauka ne? Na shiga uku!" Khairy tace "Eh hauka ne kuma sai na nuna mata ni mahaukaciyar ce wacce ta fara sabon hauka a titi....!"
No comments:
Post a Comment