YAR AGADEZ
{Page 14}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
******
"Malama Khairy lafiya kika kirani tunda sassafe haka?" Ya fada yana son jin dalilin kiran nata, ta numfasa "Naji dadin aikin da kayi man kwanaki but I have another plan, this is going to be my second success, na farko mun aiwatar dashi nayi bincike komai ya tafi yadda na zata! Am really happy about what I heard!" Yayi wata arniyar dariya "Ay ni kinsanni sarai indai da yayan banki babu abinda zai gagara!" Tace "Good! our second full proof plan is going to be a little different amma dai duk tafiyar tasu daya ce!" Yace "Ba matsala kawai ki man bayani me zan aikata maki amma fa kinsanni sarai you have to pay, in ba haka ba bazan amsa aikinki ba..." tace "Karka damu ay zan biyaka! Nidai bukatata ta biya, kagane...." nan ta zayyana masa aikin da takeso yayi mata, ya gyada kai can ya kece da dariya "Babu matsala ko kadan, zan maki amma ki tabbatar kin biya da tsoka don wannan aikin ba irin wancan bane...." tace "Babu matsala."
********
A hankali ya zare jikinshi daga nata yaje yayi sallah yana dawowa ya isketa yadda ya barta haka ya dawo ya sameta, yana kwanciya kamar tana jira ta makale shi ta kwanta bisa kirjinsa a haka ya kura mata ido ganin yadda take bacci so innocently kamar idan aka sa mata yatsa bazata ciza ba, haka ya samu kansa da cigaba da kallonta cike da sha'awa baima san yana smiling ba, gashi dan kwalinta ya zame ya cire gashi duk wani ya dawo gaban fuskarta ya dan rufe mata goshi, lips dinta ya kalla ashe haka lips dinta suke da kyau? Gasu wasu light pink sai sukaje da skin color dinta, daga gani bacci take mai nauyi, samun kansa yayi da sa hannu yana cire mata gashin fuskarta a hankali take ya kura ma lashes dinta idanu sunyi zara zara gasu masu cika wasu bakiirin dasu, gashinta yake shafawa wani irin santsi yaji da taushi marar misali, a hankali ya fara ta6a bayanta yana bubbugawa, bude idanunta tayi a hankali sai ta sauke su bisa fuskar Sultan, ta saki wani kayattacen murmushi ta danyi mika kadan "Good morning." Har yanzu bata daina murmushi ba, babu wanda ya dauka nan da minti biyar Hoodah zata iya yin fada amma dai let's wait and see no one trust her. "Morning to you too, yunwa..." sai kawai ya tsinci kansa da mata magana haka cikin kwanciyar hankali, dan tashi tayi zaune take Sultan ya fara kallonta da wata kayatacciyar night gown mai matukar kyau shi sai yanzu ma ya lura, kamar an kwance mashi noti haka yakeji, Sultan har dawani alamun shagwaba ita kuma yadda yayi haka sai kawai taga ya mata kyau, yau gaba daya sai taji yau ta tashi bata jin haushin shi, "Toh yanzu meye abinyi? Nidai kasan banida lafiya ko ya jiki ma bakace man ba..." ta fada cike da shagwa6a ba karamin burge Sultan tayi ba, "Am so sorry ya kike? Hope you slept well in my room? Ya ciwon cikin ya daina?" Idanunsu a makale cikin na juna yake mata maganar nan gaba dayansu yau mamakin kansu sukeyi, "Alhamdulillah, dasauki and yes I slept like a queen in your room thank you.. well Abincinka ko muje muyi tare?" Murmurshi Sultan yayi ya gyada kai wane karamin yaro a haka ya mike ita kuma ta tafi dakinta don yin wanka shima bathroom dinshi ya shiga don yin wanka. Haka tayi wanka har ta gama bata bar murmushi ba tana gama sa kaya taji ana knocking a hankali, kafin ma tayi magana har an shigo tana kokarin sanya sarka, galala yayi bakin kofa yana kallonta tana sanye da wata gown red color dinkin material mai taushi red and brown ne color dinta, karasowa yayi ta gaban mirror yana kallonta ta ciki, face dinta ba makeup dama ita ba makeup takeyi ba iyakarta da makeup powder da kawalli idan an kure lipstick shima bata sawa da yawa kadan kadan take shafawa, idanunta ya kalla ta mirror farare kal dasu gashi sunsha kwalli dama gasu dara dara manya dasu MashaAllah, "Should I help ma'am?" Ya tambaya yana kallon sarkar tata golden color da ganinta kasan ta gold ce marar hayaniya, fuskarshi dauke da murmushi, dukkansu sunsan cewar abinnan da suke da kyar zai kai daren yau amma kawai duk sun tsinci kansu haka yau, a hankali ya kama sarkar dake hannunta bisa neck dinta ta lumshe idanu yana kallon fuskarta yasa mata a hankali yana jin wani bakon al'amari cikin zuciyarsa, "You look stunning." Ya furta a lokacin ne ita kuma ta bude idanunta ta taji wani yanayi na daban, wani tari ne ya dan sarke ta tayi saurin fita daga dakin "Muje rana tanayi..." yana shiga cikin Kitchen to make it less boring sai Hoodah tace "Ka taba girki kuwa? Sultan karfa muzo ka kona mana abinci.." dariya tayi ya tayata. "Wai ke bakyajin dan kunyar fadin sunana? Ko Yaushe Sultan wannan Sultan wancan..." dariya ta kyalkyale dashi "Toh idan ban kira sunanka ba Sultan sunan wa zan kira? Wa nake gani a cikin gidannan kullum in ba kai ba? Ni sunan ne ma yake burgeni gashi sunan yayi kama da sunan sarauta ne wai sultan, gashi na yan gayu, sunan ajebo kuma dan mamanshi, sunan fa ya dace da kai..." tahowa yayi gadan gadan zai damkota ta fita da gudu dan tasan babu abinda ya tsana ace mashi ajebo.. ta bayan kitchen ta nufa ashe suna da wani babban lambu bata taba sani ba nan ta tsaya galala tana kallon wurin cike da sha'awa, fruits dai ba irin wanda babu ga wurin gwanin kyau MashaAllah..." tana jin tafiyarshi ya karaso tace "Sultan dama kunada lambu a nan bansani ba? Gaskiya wurin yayi bala'in kyau kasan me za'ayi mu manta da wani breakfast kaga mango din can da basu nuna ba zamu sha... katso mana guda biyu ya isa kaga manya ne sosai." Baki bude yake kallonta "Hoodah ta ina kika ta6a ganin anyi breakfast da danyan mango? Ga wadanda suka nuna nan birjit sai ki rasa wanda zamu sha sai danye?" Ta kyalkyale da dariya "A'a da dadi fa bakasani ba? Kaidai katso mana kagani." Har wani dukawa tayi wai ita nan tana rokonshi. "Wallahi baki isa ba don bazan hau iccen nan ba, saidai na kira maki gardener yazo ya katso miki..." Wani shiru tayi tana kallonshi can yace "Umar wai mangwaro take so guda biyu danyu ka katso mana idan ka katsa ka sameni backyard kitchen," yana gama fadan haka yaja hannunta suka koma ciki, a hankali ya saki hannunta babu wanda yace komai acikinsu har Umar ya kawo masu mangoes luka luka guda biyu "Yanzu kazo ka tayani mu yanka su duk abinda kaga nayi haka zakayi, kabi a hankali fa kar kaje ka yanke hannu kaja na amsa query wurin Ummi." Dan harararta yayi kafin ya wanke mangoes din sannan suka yanka shi kanana. "Bari nazo." Tafada tana nufar cabinet, wani bowl taje ta dauko mai kyau fari kal, tana kawowa ta koma fridge ta dauko kwalin milk tasan idan Sultan yaci abinnan sai yayi karamin hauka, shi dai kallonta yakeyi ta gama kwad'on mangoes dinnan ta tuttula masu madara cikin glass cup, ta dauko ma kowa spoon daya daya sannan ta debo tayi loma daya nan da nan ta lumshe idanu tana hmmm hmmm kamar wacca take cin shawarma ko kuma pizza "Kasan Allah Sultan ka dandana kaji dadi kuwa? Just give it a try....Wallahi dadi sosai." Yayi kuri yana kallonta baki bude ganin yadda take ci kamar ta samu nama, da kyar ya dauko spoon ya debo shima ya kai baki, ji yayi tsami, maggi, albasa, yaji kai komai ma, runtse ido yayi yana taunawa da kyar har ya samu ya hade, aje spoon din yayi yana girgiza kai, danne dariyarta tayi ta kara dauko spoon ta tura mashi a baki haka nan ya daure ya dinga ci gudun kar ya bata mata rai suyi fada. Idan yaji azabar yajin yayi masa yawa sai yasha madara, ruwa taje ta dauko masu tana dawowa ta lura da yanayinshi "Ya salam Sultan yaji kakeji?" Ta tambaya innocently tare da dora hannu bisa kafadarshi cike da damuwa, daga kai yayi yama kasa magana, zuba mashi madara tayi a cup ta mika masa yasha amma a banza "Ko na dauko maka yoghurt? Maybe zai daina..." Girgiza mata kai yayi, ta kara cewa "Toh me kakeso?" Ya dinga nuna ta da hannu "Nikuma? Me zan maka ko wani abin zan dauko maka?" Kafin ta kare maganar ya hade lips dinsu wuri daya take ya fara kissing dinta itama kamar tana tsoronshi ta fara responding, sai can ta farga take jikinta ya fara rawa ta fara kacaniyar kwace kanta ina ya mata wata irin damka ta kasa ture shi, take ta tuna da irin zaman da sukeyi tasan Sultan tsab xai iya juyewa ya rikice ya koma mugu ba karamin aikinsa bane, da kyar ta kwace kanta sai ta tsinci kanta da sa kanta bisa kafadarsa ta fashe da wani irin kuka, bai hanata kukan ba sai ma hugging dinta da yayi yana rarrashinta, sai can tayi shiru dan kanta kafin ya zare jikinshi ya fita daga gidan.
********
2 days later
A kwana biyun da suka gabata ya kasance Hoodah na yawan fita yawan shakatawa da yamma, a hankali sai ta fara enjoying kanta takanje park ta zauna a gurin tana ta kallon yara suna wasansu, a hankali sai ta dinga lura da wata mata sai ta rakube gefe tayi shiru, an kwana biyu ana haka ita dai Hoodah tace bari taje ta sameta taji ko lafiya? dan ta6ata Hoodah tayi hawayen da take rikewa suka gangaro mata tayi sauri ta goge, Hoodah tace "Can I sit please?" Matar ta gyada mata kai tana cigaba da share hawayenta a hankali, Hoodah ta zauna "Thank you, karki ce na maki shishigi amma na lura a yan kwanakin nan kullum nazo sai na ganki a same position, same spot, always crying, nasan ba hurumina bane but please can you tell me what's bothering you?" Matar tayi shiru na yan dakikai can tace "Ni matar aure ce na kasance ina da yaro dan shekara biyar, and that boy yanada matsalan zuciya my husband doesn't have my time he's always busy, gashi Affan ya saba da baban nan nasa toh yanzu sai ya zama baya bashi enough time, ko dawowa yayi gida baya kula shi baya ko kalllonsa...." ta karasa muryarta na rawa "Nayi iya kokarina na ganin na jawo hankalinsa especially for my sick baby, amma abu yaci tura shine boss kuma shi ya ke kula da gida gashi sisinsa bana ci baya bani, so ba lallai bane ko nayi complain ya saurareni...." Hoodah ta numfasa "Baki taba samun aiki ba? Ko bakida ra'ayi?" Ta share hawaye "Na samu aiki mai kyau amma ba'a dade ba kwarai aka koreni daga aiki..." Hoodah ta numfasa tana matukar jin tausayin matar yana ratsa ruhinta "Yanzu haka sai an masa aiki wanda muna bukatar kudi masu yawa banida halin da zan biya amma wallahi kinji rantsuwar musulmi ko? Toh Aliyu yana da kudin aikin nan, kawai dai bazai bayar ba." Hoodah cikin jin tausayin matar tace "Wannan wane irin uba ne haka? Nawa ne kudin aikin yanzu?" Matar tace "Ki yarda danii bazaki so jin kudin ba don gaskiya sunada yawa." Hoodah tace "No karki damu, zan iya taimaka maki inada halin da zan taimaka..." matar tace "Nasani ke matar dan sarkin garinnan ce, amma wannan ba huruminki bane it's not your place to help me..." Hoodah tace "Nace karki damu meye amfanina toh in bazan iya taimaka maki ba? Trust me zan taimaka maki just tell me the amount." Matar tace "Naji amma ki man alfarma daya kafin nan." Hoodah tace "Ok Menene?" Matar tace "Inaso ki taimaka man ki magana da mijina?" Dan zabura tayi tace "Na'am? Me kikace? Meyasa?" Matar tace "Bai cika zama gari ba, hotel ya cika zama meyakon gidanmu..." wani irin kuka matar ta fashe dashi "Don Allah ki cece baby na, indai kinyi niyyar taimaka man wannan nakeso kiyi man, don Allah ki taimakeni zan iya rasa dana..." Shiru Hoodah tayi tana kallonta na rashin sanin abin cewa....
Daga can nesa bakin wata bishiya wata mata ce cikin niqab kawai daga niqab din tayi tana murmushi tana juya wayarta, "Kawai kiyi accepting wannan kudirin namu, and surely you will meet your doom, just say yess Hoodah.!"
No comments:
Post a Comment