YAR AGADEZ
{Page 18}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
This page is for you Aunty Sadiya aka Sadnas😍❤️
Tsaye yayi yana kallonta tayi hanzarin tashi tsaye takamo hannunsa gam gam yayi ta kokarin fizgewa amma ina ya kasa, janshi ta dinga yi har daki tana wani irin gunjin kuka, kwantar dashi tayi kan gado ta tsugunna ta soma cire masa takalmi da socks ta kaisu mazauninsu socks din ta sanya masa a basket din wanki, zama tayi dirshen kasan gadon ta dinga rizgar kuka, irin kukan nan mai cin rai ga mai sauraro, tun yana wasu surutai da bata gane mai yake fada har bacci yayi awon gaba dashi, a nan inda take ta dora kanta bisa gadon tayita kuka, daren ranar ba irin kukan da Hoodah batayi ba a haka itama tayi bacci tana faman ajiyar zuciya.
Sai can angama sallah Sultan ya bude ido, wani irin sarawa kanshi yayi ya dafe shi ya mike da kyar yana dafe da kai, mikewa yayi yazo yi sai yaji Hoodah bisa kafarsa wani irin mummunan faduwar gaba yaji, nan ya fara mamakin ganinta a nan meya kawota nan har ta kwanta? A hankali ya daura hannunsa bisa bayanta ya ta6ata Hoodah ta bude idonta, kallonta ya tsaya yi take ta kauda fuskarta gefe sannan ta mike ta fita daga dakin, tou meya faru haka? Ya tambayi kansa, wanka yayi yayi sallah, har ya gama kimtsawa yaga Hoodah bata dawo ba, fitowa yayi ya zauna kan dining har kusan awa daya shiru babu Hoodah babu alamunta, a cikin kitchen ma baiji wani alamu ba tana ciki ba abun ya bashi mamaki ya tashi ya leka kitchen don ya tabbatar yasan bata wasa da girki ko cikin wane hali take duk da ba wani ci yake ba amma still tana yi masa. A hankali ya taka zuwa dakinta yana bude kofa ya ganta ta rakube kan gado kamar mai jin sanyi tanata kuka kamar ranta zai bar jikinta. Daga farko gabanshi yayi wani mummunan faduwa don yayi tunani kodai su Abbi sun rasu? Sai dayaga kukan nata yanada wata manufa don tana kuka tana magana ne ita kadai, "Sultan why? Meyasa zaka maido man da wasu abubuwa da suka faru a baya? Idan naga Umma na aje kwalbar nasan definitely sha takeyi don ko Abba baya gari tana sha na sha kamata ji nake kamar na dauki wuka na caka ma kaina kowa ma ya huta, tun tana yi a boye har Abba ya ya gano ta saidai kuma ba abinda ya iya yi a kai, a hankali mutane suka fara fuskantar halin da ake ciki surutu kam ba irin wanda bamu sha ba, gashi Abba bai wani damu ba sai yace ay rayuwarta ce babu ruwan kowa, sai yanzu danake tunani na wuce wannan matakin zaka maida ni ruwa tsundum? Ya zakayi man haka? Indai muna tare wata rana zamu haihu! Me kake so na fada wa yayanmu a kanka? Ince mahaifinsu bai daukar kaddara ko kuwa dai raunin imani ne akan duk abinda ya same shi? Idan bakayi tunanin feelings dina ba ay kayi tunanin na Abbi da Ummi, Abbi Ummi i have failed you ko ba ku fada ba nasan kun bar amanarsa a hannuna, your Sultan is into drugs innalillahi wa inna ilahir rajioon...." bata karasa magana ba taji an rufe mata bakinta da hannu gabanta ya bada wai ras, fargaba da nadama da tsoro ne kan fuskanshi, yanzu me zai fadawa Hoodah? Yasan bai isa ya karyata ba kuma, take ya tsaya wani tunani da karfi ya furta "Kawu!" Ta dago a hankali tana kallonsa tace "Kawu?" Ya girgiza kai wane karamin yaro, tace "Me yayi maka?" Yace "Shine yake bani drink din." Tayi shiru tana kallonsa what the hell? "Kamar yaya shi yake baka drink? Kai karamin yaro ne zai baka drink ka karba? How?" Yayi shiru "Wallahi nima bansani ba, I don't know why duk sadda ya bani ban iya masa musu, kuma na kasa fada maki har kagara nake naje ya yabani I don't know what's happening to me," shiru tayi kafin tace "Innalillah wa inna ilahir rajioon kawu Murtala fa? Your uncle? What's happening?" Shiru ta kuma yi "Definitely something is fishy, Kawu Murtala? I don't think dan Allah yazo akwai abinda yake shukawa cikin ransa, in ba haka ba how on earth zai maida kai mashayin karfi da yaji? Innalillahi." Sultan yayi shiru shi dama can bawani bonding yayi da shi ba cuz shi ba'a nan yake rabin rayuwarsa ba, so bai wani san halinsa ba "Bansan me yake nufi damu ba, but I found myself wanting to drink more idan yabani, but now I am glad da na fada maki." Tace "Ya zama dole mu gane motive dinsa, we have to keep a close eye on him, Sultan ya xama dole ka dinga lura da shi koda yaushe, he must be up to something bad, we don't know but the sooner we find out the better for us all, ina ji a jikina so yake yaga bayanmu, karka sake ka nuna masa wani abu har sai mun gano what he's up to." Gyada kai yayi wane karamin yaro mikewa tayi tana share hawaye "Bari naje nayi breakfast." Tana fadin haka ta fita daga dakin, zuciyarta na mata wani irin zafi tana kuna, what's going on here? How can his own uncle harm his own son? Wai me duniya ta zama yanzu? Ace dan uwanka na jini shine yake so yaga bayanka? Kai innalillahi wa inna ilahir rajioon, gaba daya illahirin jikinta baya mata dadi a daddafe ta gama hada masa simple breakfast tana share hawaye tana aikinta har ta kammala, bayan ta gama jera komai bisa dining ta gyara gidan tas ko ina sai kamshi ke tashi, dakinta tanufa to her surprise sai ganin Sultan tayi kwance sai baccinsa yake, murmushi tayi ta ja masa bargo tarage masa sanyin ac, daga nan ta shiga bathroom tayi wanka, har saida ta gama shiryawa tana zaune gaban mirror gaba daya ta fada duniyar tunani, kamar daga sama taji anyi hugging dinta ta baya, firgit ta dawo a hayyancinta, ta cikin mirror suke kallon juna sai can ya fara magana
"Hoodah, nasan tunda kika sa kafa kika shigo gidannan babu abunda nake kunsa maki sai tarin bakin ciki da damuwa... don Allah kiyi hakuri forgive me..." hannu tasa ta rufe masa baki "Karka ce haka..." abinda ta fada kenan sannan ta mike tsaye baki daya, juyowa tayi tana kallonsa, tana jin different feeling yana kara ratsa kirjinta, wasu hawaye ne suka gangaro mata, can sai ta goge hawayenta ta nufi bakin gado zata zauna, saurin riko mata hannu yayi "Hoodah ki bari na bada hakuri once and for all, ki bari na baki hakuri, nasan nayi hurting dinki beyond major, na kunsa maki bakin ciki kala kala da kunci nasan kin tsaneni amma ni kuma Hoodah na tsani hawayenki, your precious face is not for tears, kiyi hakuri Hoodah na maki alkawari bazan kara ba, no matter what zaiyi man bazan karba ba, kiyi hakuri ki yafe mun..." ganin jikinta yayi sanyi ya sa ya jawota kan gado ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyarsa ya juyo da fuskarta tana fuskantarsa ga hawayenta da ta kasa controlling ta fara magana "Nasan da ciwo dole yadda ka saba da iyayenka kasan dadin mahaifiyarka ka soma tagayyara, duk da bawai rasa su kayi gaba daya ba, kawu yayi using weakness dinka ya cimma wata manufa tasa, abinda kawai zan fada maka nasan is not your fault amma Sultan ka zama mai tawwakali... toh amma fa wanda ya rasa nasa daya daga cikin mahaifansa fa? Wasu ranar da aka haifesu, wasu sai sun fara girma sun fara sanin dadin mahaifansu kuma su sai su kashe kansu? Ni da kake gani ban taba sanin dadin uwa ba, lokacin da Abbana ya kara aure nayi zaton zan samu wacca zata zama tamkar uwa a gareni ashe ba haka bane, she is the most wicked step mother ever, idan naga yadda Ummi ke tarairaiyarka sai inji dama nice kai, nasan your parents are the best amma wannan ba excuse bane da zaka biye ma kawunka har ya jefa ka hanyar banza, yanzu idan yace ka shiga wuta sai ka shiga? It's not healthy, bai chanchanta ba aga yadda ka fito daga gidan girman kaifa dan sarki ne baka tunanin it will tarnished your image and reputation? You are a respectable man wallahi gara ace ma hawan jini ne ya haye maka kana zarya asibiti akan sunanka dana iyayenka dana danginka gaba daya ya lalace har abada ko ka daina yi, wannan tabon na nan bazai ta6a gushewa ba, Sultan da haka nake rokonka kayi man alkawari bazaka sake yarda ba koda wasa ka karba kasha no matter what?" Hugging dinta yayi sosai kamar za'a kwace masa ita yana jin wani sanyi yana bin sako da lungu na jikinsa, shidai yana son yadda take masa magana cikin kwanciyar hankali da fahimta, so cool and calm ba hargagi babu masifa, yace "I promise you Hoodah." Wani kiss yayi mata a kumatunta a hankali ta janye jikinta ta mike tsaye ta fita daga dakin tana murmushi, a hankali shima ya mike ya bi bayanta da murmushi shimfide saman fuskarsa.
Sun gama breakfast suna zaune kan dining yayi gyaren murya yana kallonta ta dago ido irin lafiya dinnan? "habibty dazu najii kince yaranmu zaki bani ne?" Yadda yayi kamar on a serious note, take wani irin tari ya sarketa saida tasha ruwa ta natsu kafin ta dago tana kallonsa "Ya da chanza man suna? Sultan yau kuma Hoodah dince bazaka iya kira ba? Kodai yan shagwabar ne suka hau kai?" Ita dai burinta bai wuce ya manta da maganar nan ba, "Ohh that, I find it cute to call you with it ya mugun dacewa dake, back to babies kin shirya bani su ne? Ko twins ma ko?" Idanu ta zaro waje ta mike da sauri ta fara tattara plates din da suka yi amfani dasu tana kaiwa kitchen, saida ta gama kaiwa kitchen kafin ta fara wanke wanken dole harda abunda bai kamata ta wanke ba, wata ajiyar zuciya ta sauke ganin bai dining "Ikon Allah Sultan yayi tunanin bashi amsar nan?" Kamar daga sama taji anyi hugging dinta ta baya ana sauke mata kisses bisa kanta, kyarma ta farayi "Eh mana so nake ki bani amsa, kodai don bakisona sheyasa bazaki haifa man baby ba? Kinga idan su Abbi suka warke saidai su dawo su ganki da jikansu a hannu." Da sauri ta fara kwace kanta "Sultan baka gani aiki nake? Kuma fa ya kamata ka tafi ka duba babu wani aikin daya kamata ka fara yi a can haraba? Kaje ka duba kagani." Sai neman zillewa takeyi daga jikinsa amma yaki sakinta harda nade hannunsa a kungunta. "oh my God Hoodah! Bakyasona kenan?" Yayi kamar tayi hurting dinsa cikin hanzari ta fara girgiza kanta "A'a ina sonka... ahh bana sonka, ya ilahi Sultan!" Sai kuma ta fara dukan chest nasa ganin sai dariya yake mata yadda duk ta rude ta rasa ansar da zata bashi... "Toh shikenan a barshi a kinasona, ni gaskiya babies nakeso at least 20." Ya kama hannayenta duka biyun yadda ta rufe idanunta alamun wai taji kunya, dariya yakeyi kasa kasa "20? Haba Sultan so kake in mutu?" Yayi dariya "Idan kin mutu sai na auro wata tazo ta haifa man." Tace "La la toh jeka aurota tun yanzu ni bazan haihu ba." Yar dariya yayi "Yi hakuri matata Hoodah, tou yanzu dai ya za'ayi da babies din? Sannan ashe ana kishina haka? Haha maida wukar daga ke ba kari kece amarya kuma uwar gida." Yafada yana mata kiss gefen bakinta "Nifa ka kyaleni am too young for all of this, kai you're even lucky daka sameni ka samu carbi sai ka gode ma Allah gaskiya..." ta fada tana jefa masa hararar wasan ta juya da niyyar komawa don cigaba da wanke wankenta. "iyye! You're too young ko? Yarinya xakiyi bayani wallahi, yanzu dai tunda na daina abu saboda ke what's my gift?" Tace "Aww dama ba dan Allah ka daina ba?" Ta fada tana watsa mashi wani kallo "A'a dan Allah na daina amma ay kace sila...." sai kuma ya rasa me xai ce "Tou kasa Allah a ranka..." ta na fadan haka ta juya "Habibty..." juyowa tayi ta kalleshi dawani dawani kayattacen murmushi tayi wrapping hannunta a chest dinsa "Wasa nake maka Sultan, Hoodah is yours zata haifa maka babies ko nawa kakeso...." ta fada tare da bashi wani side kiss tana gamawa ta sake shi ta ruga aguje ta bar kitchen din, dariya yayi ya bita da kallo har ta fice gaba daya zuciyarsa fes yana jin nishadin da bai ta6a ji ba, "I think am falling for you Hoodah...."
No comments:
Post a Comment