YAR AGADEZ
{Page 20}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Dedicated to members na YAR AGADEZ your comments are so mua 😘🥰I heart you all❤️❤️
********
Gaba daya ya rasa abinda ke masa dadi, sadness, helpless, confusion, lost sune abinda yakeji a cikin ransa, bai ma san abinda zaiyi da rayuwarsa ba yanzu, Allah ba yadda baya Ikonsa ko a mafaraki bai taba tunanin za'a zo masa maganar aurenshi da Zarah ba, jifa yadda kamar jiya ne yake tsara yadda rayuwarsu zata kasance shida Hoodah, bai taba tunanin al'amarin zai juya haka ba, juyi ya kuma yi a karo na bakwai, haka ya raba dare yana ta faman tunanin gashi yanzu babu abinda kansa keyi sai sarawa, tunda Yasir ya fada masa wannan news din sam bai musa ba especially da yace masa ay Hajiya ce take suggesting ta yaya ma zai soma cewa baya son yarta? Mutanen nan da suka karbe sa a lokacin da ya rasa mafita a lokacin da duiniya ta juya masa baya, saidai shi bai mata wani kallo ba daya na wuce na kanwarsa ta jini wanda ya tabbatar itama haka babu soyayya a tsakaninu. Farko da ya kawo masa shawarar har ji yayi kamar an caka masa mashi a cikin zuciya wai yana nufin ya auri Zarah? Ya salam rasa abinda zai ce yayi da farko sai daga baya ya amince ba tare da ya tsaya wani kwakkwaran tunani ba, Yasir yace masa "Kayi hakuri in har mun maka katsalandan cikin rayuwar ka Ashraf, wallahi we were just trying to help you out of this misery, ina maka addu'ar yasa wannan shine ya zamo sanadiyar samuwar farin cikinka, natsuwa da kuma kwanciyar hankali, na maka alkawari bazaka taba yin dana sanin wannan zabi da mukayi maka ba, amma fa kar ka kwari kanka in har kana da ja akan haka ina so kar kaji nauyin komai ka fito fili ka sanar dani,..." saurin girgiza kai Ashraf yayi "ko kusa banida haufi akan zabin naku, I know Zarah is a good and decent girl, she's well mannered and respectful, tanada nutsuwa da hankali nagode da wannan karamci da kauna da kuka nuna min saboda sai ana sonka za'ayi maka wannan, nagode nagode inaso ku bani dama naje gida na sanar ma da Abba..." Yasir cikin matukar farin ciki yace "Alhamdulillah nine da godiya tunda har ka amince da wannan kudurin namu kaga ko ba komai zumuncinu zai kara karfi, sannan kuma Hajiya zatayi farin ciki sosai da amincewa da kayi, mun gode abokina, amma ya kamata ku kara fahimtar junanku sosai, duk da dai naga Zarah na yawan zarya zuwa kawo maka abinci a nan..." ya fada cikin zolaya Ashraf yayi dariya "Hakane kawai tana tausaya man ne..." yace "Ay kai din abin a tausaya maka ne saidai banaso ina yawan tuna maka da batun don nidai burina bai wuce ka dawo normal ba and move on..."
Sultan yayi murmushi kurum, Yasir yace "So do you like my sister Zarah?" Ya fada yana taba masa kafada da tasa kafadar yana kashe masa ido, tashi yayi ya fita daga dakin "Yasir ni na fita na lura so kake kasa ni a gaba da safen nan!" Yasir ya bishi yana dariya "Sai ma ranar tukunna."
******
"Dama tsanar da Umma tayi man ta kai har haka? Har zata iya nema ta kashe mutum? Ko ta nemi ta tarwatsa ni because of a so called kishi! Kishin ma tanayi ne da wacce batada rai! Tayi enough I will not spare her!" Ta fada tana nufar Kawu a fusace "Kawu! Meyasa ka biye ma Umma? Bakasan ko wace irin mace bace? Zata kai ta baro ka a banza! Baka kyauta ba! Uncle your own flesh and blood? Kawu why?" Nan take ya fara dana sani jikinshi ya fara bari kafin kace me Sultan ya kira masa yan sanda, nan da nan suka iso suka ja shi yana ta faman bashi hakuri, amma ina Sultan ya zuciya yace "Mu hadu a kotu Kawu! Sai na dauku fansar abinda kayi wa iyayena! Macucu mugu azzalumi!" Da kyar Hoodah ta dinga dragging Sultan suka tafi sashensu suna zuwa ya jawo ta yayi hugging sai ya sakar mata kuka, itama take ta fashe da kukan sun dauki tsawon lokaci a haka, shi ya fara janyewa yayi scooping fuskarta "You dont have to worry, zan hukunta Umma duk abinda tayi kinji?"
**********
2 DAYS LATER
Wasa wasa daga magana Sultan ya fara kissing din Hoodah "Hoodah every girl you see pass this stage kafin ta zama cikakiyar mace, you're going to be okay kinji?" Hijab din ya yaye mata, ita kuwa gaba daya hankalinta ya fara tashi, zuciyarta kuwa kamar ta bar kirjinta, a hankali Sultan ya daina ganin fusakar Hoodah, ya fara ganin fuskarta duk gashi kamar dai ba mutum ba, ba zato taji ya turata da karfin bala'i yana nunata jikinshi har wani rawa yakeyi, "Who are you?! Karki matso inda nake kar ki kasheni!" Turus ta tsaya tana kallonsa tace "Ni? Sultan Hoodarka ce fa what's wrong with you?" Ta fada tana matsawa kusa dashi wata irin kara ya fasa wane zai fasa mata dodon kunne, take ya runtse ido ya takure wuri daya yana makyarkyatar sanyi, anan ne ta fahimci kamar hankali baya jikinshi, tashi tayi a sanyaye ta fada bathroom tayi wanka ta kimtsa jikinta, ta fito, haka daren nan bata rintsa ba dan a takaice ce Sultan kamar mai ta6in hankali ya koma ya dinga wasu misbehaving dai haka kamar bashi ba... Idan ta kalleshi saita ga ya takure jikinshi wuri daya ya kura mata ido, matsawa tayi kusa dashi a hankali ta ta6a shi sai ta ga baiyi wani yunkurin hanata ba amma dai da ka kalleshi kasan babu lafiya, a hankali ta dora kansa bisa cinyarta ta dinga dan shaffawa, idan bacci ya kwashe shi na kamar minti biyar sai ya farka a firgice yana neman guduwa, sai ta damko shi da kyar take samu ta tofa masa addu'oi sannan sai ya natsu, babu abinda takeyi sai innalillahi wa inna ilahir rajioon, wai meke shirin faruwa dasu haka? Sai bayan sallar asuba bacci yayi gaba da ita.
Bata ma san yadda akayi tayi baccin ba saidai ta farka ta dakin babu kowa, a rude ta mike ta leka bathroom taga wayam, can ta ganshi a kitchen kasa dirshen yayi kuri da ido kamar mai tunani, yana ganinta sai ya fara kacaniyar mikewa a rude, nuna ta yakeyi da hannu "Kar ki matso inda nake tsoron ganinki nakeyi." Yana fadan haka ya fice da gudu daga dakin yana zuwa dakinta ya danna lock, da gudu ta bishi babu abinda takeji sai watsi da abubuwa nan ta rude ta dinga kwala mashi kira tana bubbuga kofar da karfin bala'i, da gudu ta fita waje neman taimako sai ga dogarawa sun biyota a guje nan suka bude kofar da kyar a razane suka ganshi yadda yake fasa kwalaben turare duk yaji ciwo dashi, dogarawan nan sukayi kansa suka fara kacaniyar rike shi kafin kace me sun damke shi nan ta sa aka nemo mata family doctor dinsu, kafin ya iso an kimtsa dakin ko ina sannan sun kwantar dashi kan gado suna rike da shi don kar ya gudu, hijab dinta ta sanya jin sallamar Doctor din nan taje ta shigo dashi ya soma duba shi, shidai a iya bincikensa yace mata babu abinda yagani yana damunshi don haka baya tunanin maganin nan na asibiti ne su nemi malami ya duba shi, iyaka dai allurar bacci yayi masa ya fita.
Bayan yayi bacci ta sulale kasa kawai sai ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, tana nan a haka har akayi azahar da kyar ta samu ta lallaba ta shiga ta dauro alwalla, wai meke faruwa dasu? Duk sadda suka samu farin ciki da kwanciyar hankali sai wata fitinar ta bullo? Tana sallah tana kuka tana fada ma Allah. Addu'a ta dukufa yi tana kai ma Allah kukanta.
*****
Banko kofar tayi tana shiga ta iske Hajara da huci ta shiga, "Kin cuce ni Hajara sam ba abinda nakeso ba kenan! Ya zaku maida sh kamar wani mai tabin hankali?" Hajara ta sheke da dariya "Toh kila dai bakiyi yadda aka saki ba kin kuskure!" Tace "Ni ban wani kuskure ba, nayi duk abinda aka sani nayi, kawai dai cutata akayi! Kuma wallahi sai an biyani duk abinda na kashe!" Tsaki Hajara tayi ta ta6e baki haka Khairy ta fita fuuu a fusace.
Misalin karfe goma na dare Khairy ta dawo daga yawon gantalinta daidai wata kwana wata makekiyar mota tayi parking, sauke glass din motar akayi wanda ke mazaunin gaba ya washe baki "Su Khairy yan mata." Nan ta ganeshi wani guy ne da ta taba haduwa dashi har ya bata dubu 10 ranar yace mata ay service ya kawo shi garin, ta washe baki "Yan samari tunda har yanzu kaki bari nasan sunanka ba." Yayi dariya "Wannan ay ba matsala bane, gashi kuwa yau nazo daukarki muje shan ice cream kamar yadda nayi maki alkawari rannan. Ya zakije din ko kuwa?" Matsowa tayi daf da motar tana gyara daurin dankwalinta "Babu matsala amma dai ba zamu dade ba ko?" Yace "Ah no bazamu dade ba sharp sharp mun dawo." Ta bude motar tana shiga kenan sai ta ga ashe kusan su hudu ne cikin motar yace mata ay abokansa ne, sunyi nisa a tafiyar kenan taga sun sata a tsakiya sun mata wani irin mugun dauri, nan suka ma motar lock, a razane ta dago "Lafiya? Me zakuyi man?" Ay tuni jikinta ya fara karkarwa a take ta kara rudewa yadda ya kara gudun motar, wani irin kuka ta fashe dashi a motar, shure shure Khairy ta fara yi tunda daya ya zabga mata wani irin marin da tunda aka haifeta ba'a taba mata irinsa ba, take wuta ta dauke mata, bata kara sanin inda take ba saidai ta farka ta ganta bayan gari cikin dokar daji, sun kulle mata kafafu da hannuwa sun zagayeta suna kallonta cike da sha'awa, wata irin razananniyar kara ta saki mai rikitarwa ta fashe da kuka, kallonsu takeyi tana girgiza kai hawaye kuwa kamar an wanke mata su a fuska, kyarma ta farayi inda ta kasa koda kwakwaran motsi, wayyo Allahnta yanzu wadannan fyade suke shirin yi mata? Daya ne ya nufota gashi yana faman daga riga wani gunjin kuka ta saki zuciyarta ta harba kamar ranta zai fita, dama haka bakin ciki yake? Haka kunci da rashin sanin madafa yake? Duka rayuwarta ta taso tana abinda taga dama sai gashi ta zama hopeless a yau ba tada wani kata6us, "Ku taimaka man! Don Allah ku kyaleni kar ku cutar dani ba haka mukayi daku ba!" Kuka take har kasan ranta kyalle suka cire suka kulle mata baki dashi, sanann suka damke ta suka daga mata riga har zuwa cibiyarta haka samarin nan kusan su hudu sukayi nasaran raping din Khairy....
No comments:
Post a Comment