YAR AGADEZ
{Page 12
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
A bangaren Sultan kuwa sashen Ummi ya nufa, tana kwace daki ta mike kafa bayinta na mata tausa, gefenta bowl din guava ce tana yanka tana ci a hankali tana kallon series a Zee world, "Ummi baku gajiya ko? Salamu Alaikum..." ya furta yana nufar inda take zaune..." amsa sallamar tayi ta juyo ta amsa masa sannan ta juya ta cigaba da kallonta, wannan yana daya daga cikin abinda yasa ya tsani Zee world, shidai Umminsa tana son kallon channel din zata iya bata minti 20 ta kalla abinta batako kula shi ba. Dama episode din ya kusa karewa sadda ya shigo sai da aka kare ta juyo tana kallonshi da murmushi a fuskarta tace "Afuwan Sultan I was carried away that's why.... kasan Jodha ta..." katse ta yayi da sauri jin zata fara bashi labari yace "Su Akhbar da Jodha ko? Ummi naji labarinsu har nagaji tun anayi a zee tv na kalla ta bakinki yanzu dai ina kwana?" Yayi tambayar yana kwantar da kansa kan cinyarta don dama ta sauko da kafafunta kasa daya shigo. Tayi murmushi "Lafiya lau an tashi lafiya? Dazu ay mun shiga sashen naku hala baka tashi daga bacci ba?......" Suna cikin firar ne sai ga mai martaba ya shigo a natse yana ganin Sultan ya ware idanu waje "Wai kai bazaka girma bane? Ke kuma kina kallonshi kika barshi ya wane haye kan cinyarki god'e god'e dashi wanda ya isa ya aje yara amma jishi dan Allah, kai da Allah tashi ni kar na sake ganin ka a haka, ita diyar mutane da ka aje gidanka batada uwar zata hau kan cinyarta sai kai katoto dakai ka wani dale bisa cinya, kasan Allah Sultan ka fita daga idona...." nan Abbi ya rufe ido ya dinga bala'i ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba Ummi tace "Komai girmansa ay nice uwarsa yaro baya girma da mamansa ay..." yace "Nadai gaya maku yaron nan lalaci gareshi ni banga ta inda zai iya rike masauratar nan ba duk sadda akace babu ni, tunda ya dawo ban taba ganin ya kama man komai ba sai shiririta, kai daga yau ka dinga zuwa ina dora ka bisa hanya ka dinga ganin me akeyi ina ma amfani? Kuma yawon zuwa da kake nan bangaren yayi yawa kar na sake ganinka nan sai weekend har sai aurenku yayi wata biyu ka zauna can wurin matarka kana ji na?" Shi yanzu ina zai rika zuwa? Dama ba fita yake idan anga ya fita toh ya tafi farauta shida dogarawansa sai kuwa yawon shakatawa da yake zuwa da yamma, gashi an hana shi zuwa gida wai sai weekend, lallai Hoodah zata dandana gudarta badai ance sai ya xauna da ita ba 24/7 toh wallahi sai ta kirasu tana kuka akan su barshi ya dinga zuwa wajen Ummi tsabar azabar da zai mata sai ya gasa mata aya a hannu. Haka ya mike ya bar Abbi yana ta faman mita yau Ummi ta bani dama ya sabayi mata.
Sashensu ya koma yana isa ya jiyo sautin muryarta saman dining tana gurza carrots ko lura dashi batayi ba, cikin muryarta mai sanyi da dadin sauraro da alamar cikin damuwa take karanta Qurani mai girma cikin suratul Maryam, kan doguwar kujera ya kwanta tun Sultan na jiyo sautin muryarta har bacci yayi awon gaba dashi dama bacci sama sama yayi jiya. Saida Hoodah ta gama hada lunch dinta tsab baiji abinda takeyi ba, kawai tazo wucewa daki zatayi wanka da alwala kawai sai ta hango shi kwance da farko tsoro ya bata saida ta leka sai ta ganshi yana ta sharar baccinsa hankali kwance, cike da fargaba ta taka inda yake saboda ita har ga Allah tana jin tsoro ta shiga wanka ta barshi parlor yana iya shigo mata, da wannan tunanin yasa tayi hanzarin karasawa inda yake din tana dan bubbuga kafadarsa a hankali, ashe shikuma wani mummunan mafarki yakeyi Hoodah bata sani ba, aiko tana dafa shi yayi wani irin kukan kura ya finciko ta tilas ta fado bisa shi take yawani makalkaleta ya saki ajiyar zuciya ya koma baccinsa, toh shi dama koda yana yaro idan yayi mafarki mai ban tsoro haka zai kankame Ummi a haka zasuyi bacci har asuba, take jikin Hoodah ya fara 6ari ta fara kacaniyar kwace kanta sai ga hawaye shar shar zuciyarta na harbawa, aikuwa ashe hawayenta bisa kirjin Sultan suke sauka, cikin sheshekar kuka tace "Don Allah Sultan kayi hakuri, wallahi tunda ka fita ban kunna tv ba dan girman Allah ka rabu dani Wallahi sallah zanyi..." tama rasa dame zata rokeshi ya kyaleta ita dai burinta ya rabu da ita. Cikin bacci ya bude idanunsa wanda yayi sanadiyyar saukarsu cikin idanun Hoodah wanda har yanzu hannunshi na nade a kugunta, wani sabon tsoro ya shigeta da sauri ta kulle idanunta gam gam "Babu abinda xan maki kinji? Ummi haka take min idan nayi mafarki marar kyau hold on for a moment please." Ya fada bakinshi na rawa dan har yanzu jinshi yake tsundum cikin mafarkin.. "A'a Amma...." ta fara rokonsa yayi sauri yace "Please Hoodah, koda minti biyar ne, kawai calming zanyi in ba haka ba zan iya suma..." ya fadi maganar a hankali tare da rufe idanunshi, ba yadda Hoodah ta iya illa tayi hakuri ta dora kanta bisa kirjinsa comfortably itama ta rufe idanunta itama kanta so take ta samu nutsuwa don har yanzu jikinta bai bar kyarma ba.
********
Zaune suke a garden Sarauniya Karimah na hakimce kan kujera an cika mata gabanta da kayan makulashe bayinta na ta aikin fita, da alama dai wani take jira tana nan har kusan minti goma sha uku sai gashi ya iso cikin shiga ta alfarma, da sauri tasa akayi masa iso ya shigo nan ta sallami bayinta suka fita da sauri, zama sukayi kan kukera a take nan Karimah tace "Barka da isowa? Da fatan dai ban takura ka ba?" Yace "Ko kusa it's a pleasure to be here..." tayi murmushi "MashaAllah, Da fatan dai kasan dalilin da yasa na kiraka a nan?" Yace "Nasani ay zuwan nawa nan din nasan zai amfane ni sheyasa kikaga na zo..." tace "Alhamdulillah, ay dai kana da alaka da sarkin Niamey ko?" Ya gyada kai "Kwarai ma kuwa, cousin dina ne na jini da mahaifinsa da mahafiyata uwarsu daya ubansu daya..." tace "MashaAllah, dama musabbabin kiran kenan, don mu cigaba da tattaunawa kan maganar mu ta rannan? Are you still interested ko kuwa?" Yace "Inaso sosai indai har zan samu mai zai hana?" Ta numfasa "A rayuwata banaso inga Hoodah cikin farin ciki ko kadan! Nafiso ta kasance cikin kunci da bakin ciki sheyasa tun farko na tsiro da wannan aure saboda cimma wata manufata, inata tunanin hanyar da Zan bullo nan na fara aiwatar da bincike akan Sarkin Niamey aka gano man cewar ay baida kowa sai kai, iyayensa shi kadai suka haifa..." yace "hakane..." tace "Kaga kenan idan ya mutu dansa ne zai gaji sarautar ko ba haka bane?" Yace "Hakane..." tace "Toh nikuma bazan zira ido inga Hoodah na samun cigaba ba, inaso mu hada karfe da karfe mu tarwatsa farin cikinta..." ya gyara zama "meyasa? Kuma ta yaya zamuyi hakan?" Tace "Inada shawara! Idan har plan din namu yayi working successfully tou ina tabbatar maka da kaine zaka gaji sarautar sannan idan ka hau kan mulkin sai yadda kakeso zakayi, amma kafin nan sai nasa an kawar da sarki shida matarsa, sannan mu samu yadda mukeso ta karfi zakayi a matsayinka na kawun Sultan, zaka rikide ka zama mugu, nikuma daga nan zan rika baka order abunda xakayi, kasani riba gareka ga ta hayewa kan karagar mulki by force, nima daga gareni kana da kasonka mai tsoka nidai burina shina ka yarda ka kuma bani hadin kai..." ya numfasa gamida gyara zama "Na dade ina kwadayin kujerar nan saidai nasawa kaina dangana nasan bazan samu ba, amma naji dadin maganar nan da kika kawo man saidai wani hanzari ba gudu ba, kina ganin asirinmu bazai tonu ayi saurin gano ba?" Ta kyalkale da dariya "Ba ubanda ya isa ya gano mu na dade ina shirya wannan plan din nawa, kai kana ganin a banza na hada auren Yarima da Hoodah ne? Ay ina sane da abunda nakeyi, don haka kar ka samu damuwa yanzu haka ma sarki baya nan sheyasa kaga na kiraka ban bar wata kofar da za'a zarge mu ba, yanzu zan fada maka yadda zamu fara aiwatar da wannan shiri namu...." yace "Toh Alhamdulillah, nagode kwarai da gaske kuma naji dadin wannan daukaka da kika zo man da ita na maki alkawari ko mey kika sani zan maki shi without any hesitation..." ta saki dariya "Good, zan neme ka ta waya yanzu ka tashi ka tafi kafin sarki ya dawo bana so plan dinmu ya ruguje, zan maka bayanin komai ta cikin waya..." wani briefcase ta dora masa bisa cinyarsa, bude masa tayi sai ga kudi dollars makil ciki ya saki salati yana ta6a kudin not believing his eyes ya dago yana kallon Karimah "Duk naka ne wannan, wannan ay somun ta6i ne muddin xaka bani hadin kai..." yana kyarmar jiki yace "Kisa a ranki anyi an gama kawai..." ta saki dariya "Very good, ka tashi ka tafi din zan neme ka..." mikewa yayi da sauri yana faman washe baki "anytime kike da bukatar magana dani just call me babu wata matsala!" Tace "Tou shikenan malam Murtala nagode." Daga haka sukayi sallama yayi gaba cike da farin ciki.
***********
Kamar yadda Sultan yayi alkawarin minti biyar din nayi yayi kokarin mikewa tana ganin haka tayi zumbur ta mike cikin rudu ko kallonshi batayi ba ta wuce dakinta direct ta rufe kofar da key tayi hanzarin fadawa bathroom don yin wanka, koda ta fito saida ta bata lokaci sosai sannan ta shafa mai tasa kaya, gabatar da sallah tayi tana idarwa tayi azkhar dinta da kartun quran dinta ta dade tana adduar Allah ya kareta daga sharrin masu sharri sannan ta tattara kayan ta adanasu inda suke, zama tayi gefen gado yunwa na cinta amma tsoron fita takeyi, can dai taga zaman bayi mata zaiyi ba ta mike ta fita daga dakin aikuwa sai gashi ya shigo da alama daga masallaci yake, komawa tayi da gudu dama bai lura da ita ba zama yayi gamida kunna tv ya fara kallon sports, ta kara akalla minti 30 can dai tayi shahada ta fito daga dakin yanajin motsinta yayi sauri ya kashe tvn, nan ta saki baki tana mamaki toh shi meyake nufi kenan ita bazata yi kallo ba sai shi? Wata irin uwar tsawa ya daka mata bakasan lokacin data zabura ba gabanta yayi wani mumunan faduwa. "da kikayi tsaye a nan kina kallona cikin cikinki xaki maidani ki sake haifeta? Malama zaki daina kallona ko kuwa?" Kasa daga idanunta tayi tana jin tsoro ita dai abubuwanshi sun fara bata tsoro, yanzu he's kind and caring anjima yafi wuta zafi... Mikewa yayi ya nufi dining fuskarshi kamar saukar mutuwa, shi ba komai ke bashi haushi ba sai yadda ya dinga rokonta tayi huggin dinsa ashe dai shi sakari ne baisani ba? Har Yaushe zai tsaya rokon wannan hug? Yayi mey da banzan jikinta? Shi ma idan ma ba wawanci ba da ban haushi irin nashi wannan har nawa take fisabillahi da zata dauke mashi hankali? Wani mugun tsaki yaja cikin jin haushin kanshi ya daga kai ya hango ta tsaye inda ya barta hawaye sun taru a cikin idanunta amma basu sauko ba, "Zakizo ki zuba man abinci ko kuwa? Ko so kike ni in zuba da kaina ne?" Wata tsawar ya daka mata wanda batasan lokacin data karaso kan dining din ba dan har tuntu6e ta kusan yi da kasan rigarta, idanunta na kan warmers ta tambayeshi mai zai ci? Don tana gudun kar ta kalleshi kuma cibi ya zama kari, bai amsata ba sai kawai ya bude laptop dinsa ya fara danne danne, jollof rice da coleslaw sai peppered chicken ta zuba masa hade da zobo mai sanyi, plate ta kara daukowa zata zuba ma kanta yayi wani irin uban tsaki, hakan ya dakatar da ita daga zuba abincin, "Ke daga yau duk inda kika ganni kar ki kara wuce minti biyar a gurin, karki kara cin abinci tare dani ni ba sa'anki bane ba don Wallahi 6alla ki zanyi kika take dokata a gidannan kinji ni?" Ta gyada kai a hankali don ita bazata ma iya amsa masa ta rasa meyake takama dashi duka abinda yake takama dashi itama tana takama dashi, koko don ya ganta yar yarinya yake mata wannan abubuwa yana ganinshi wani babba, wata tsawa ya daka mata mai gigitarwa batasan sadda tace toh ba har razana tayi jikinta na rawa ta juya da sauri ta shiga daki. Tana shiga ta aje plate din bisa dress mirror ta fashe da wani irin kuka. Kuka takeyi har cikin ranta bamai rarrashinta, itafa batace dole sai sunyi rayuwar aure da Sultan ba, ya kamata dai yayi treating dinta kamar mutum, wulakanci da yake mata ya fara isarta, gashi batajin zata iya fighting dinsa back tsoronshi take har cikin ranta.
Sai can lokacin la'asar taji karar fitarshi daga gidan da sauri ta fito ta kwashe kayan ta tattara komai ta gyara wurin tas, da gudu ta ruga dakinta tayi sallah, tana gama azkhar sai ta fara tunanin tayi masa dinner tun yanzu kafin ya dawo, haka kuwa akayi, tana hada miyar egusi ta jiyo sautin tafiyarshi, da sauri ta maida kofar Kitchen din ta rufe don bataso ya ganta abin ya zama wani bala'in.. zafi ne ya isheta amma tasan ko zata mutu bazata bude ba sai ta jira ya bar parlorn. Hawayenta ta goge tana cigaba da aikinta, har ta gama tsab amma tilas ta zauna a kitchen saida ya tafi sallar magrib sannan ta fito ta jera saman dining sannan ta tafi dakinta.
Can wajen karfe tara tana kwance kan gado tana waya da kaka kamar daga sama taga mutum a kanta wata irin zabura tayi har sai da kashin bayanta ya bada wata yar kara, hannunsa yake miko mata alamun tasa masa wayar tata, mika masa tayi jikinta na rawa ya amsa fuskar daure kamar tashin duniya ya kara a kunne yaji ance "toh amma kin tabbatar da babu abinda kikayi masa?" Bude baki yayi yana kallonta, Hoodah a rikice ta mike da gudu tayi hanyar bathroom, har ta kai kofa taji an finciko ta da karfin bala'i a rikice ta fasa wani uban ihu, bayanta ya hada da bango ya damki kumatunta da hannunsa biyu "Ashe ke munafuka ce? Uban ne kikaje kikace nayi maki? Ke baki fada masu abinda kika aikata bane? Why are you after my life?! Ko so kike ace wani abu nayi maki ki kira man mazinata yan uwanki su kasheni?" Yayi maganar cikin tsantsar tsanar da yakeyi mata, har shaking kafadunta yakeyi idanunsa sunyi jawur yana mata wani irin mugun kallo kamar zai kasheta! Jijiyoyin wuyanta babu wacca bata fito waje ba hawaye kuwa kamar an koro su, wani irin karfi yazo mata ta shako masa wuyan riga "Ni ba mazinaciya ba! Daga yau karka sake kira na da mazinaciya na gaji na gaji!" Ta fada cikin sheshekar kuka. Wani irin mari taji a kumatunta mai rikitarwa ta fasa wani irin ihu bata san lokacin da tace "Kayi hakuri Dan Allah dan annabi ka kyaleni!" Ta fada kamar ana kara yawan hawayen idanunta, wani irin kallo yake binta dashi idanunshi kadai abin tsoro ne can yace "Hakuri my foot!"
No comments:
Post a Comment