YAR AGADEZ
{Page 19}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Murda kofar tayi ta shiga tana wani cika tana batsewa, kallon gidan ta fara yi da wani expression na rainin wayau, nan tayi tsaye ita batayi sallama ba ita bata ida shiga ba, tafi minti biyar a nan tana kare ma gidan kallo tana wani tauna chewing gum, bayan minti kusan uku sai ga Hoodah ta fito daga daki da alama sallah ta gama dan ga carbi nan a hannunta tana azkhar, da mamaki ta tsaya tana kallonta tace "Ah bakuwa mukayi? Ya kika tsaya a nan ki shigo ki zauna mana, sorry banji sallamanki ba ina ciki ina sallah." Khairy ta wani yi mata kallon uku saura kwata ta shigo tana wani yauki ta samu wuri ta zauna ta dora kafa daya kan daya tace "Tooo bakiji ba? Alright ba matsala mai gidan na ciki?" Da mamaki Hoodah ke kallonta "A'a baya nan, lafiya kike nemansa? Sorry ban gane ki ba?" Khairy tayi wani murmushi "Of course bazaki ganeni ba! Tunda kin shigo inda baki chanchanta ki shigo ba..." Hoodah da lokacin ta fara gane wannan bada arziki ta zo mata ba tace "Excuse me? Anya kinsan da wa kike magana? Who are you da xakizo gidan mutane kina masu isa?" Khairy ta tabe baki "Gidan mutane? It's supposed to be my house not yours! But you snatched it away from me! Kin kwace mun masoyina and now you are calling this your house?" Hoodah tace "Ohh na fahimce ki if am not mistaken kina nufin kece wadda Sultan ya kamata ya aura bai aureta ba ya aure ni?" Khairy tace "Of course am the one! You are the reason am in pain now, I have done everything possible to separate you but to no avail! Wai wane irin asiri kika yi masa? Nace wane barbaden kikayi masa har ya kasa rabuwa dake? I was his first love! Mun tsara duk yadda rayuwarmu zata tafi amma rana daya kika rusa mana farin ciki! Why Hoodah!?" Hoodah tace "Na rusa maku farin ciki? You must be joking ni na auri kaina? Shida ya auro ni shi zakije kiyi ma haushin nan da kikeyi kamar wata karya amma ba ni ba! Bakida labarin shine yaje har garinmu ya auro ni? So please banida lokacinki I have things that are more important to do zaki iya tashi ki fitan man daga gida," Khairy ta kule ta mike tsaye "Toh bari kiji in gaya maki! I will not rest sai na fitar da ke daga gidannan, baki isa ba, duk wanda nayi a baya baiyi working out ba though dai na fara cin nasara, amma zaki sha mamaki yadda zanyi dake sai kin raina kanki!"
Hoodah ta mike tsaye har wani 6ari jikinta yakeyi, so itace ta dinga plotting against against her kenan? Itace ta nema tayi tarnishing image dinta a banza duk da sunan kishi? Toh wai kishi hauka ne? "And sai da kika gama bata ma kanki lokaci kikaga plan din naki yayi backfiring? Ke bakisan zuwa da kikayi nan ba kinyi downgrading kanki? Kin kaskantar da kanki! And let me tell you something I am glad naji dadin makirci da kika kulla you know why?" Tafada tana nufar inda take tana kallon cikin idonta "Because duk Abinda kika shuka every single plan of yours has drawn us closer to each other, relationship dinmu ya gyaru, so ina fatan zakije ki sake shuka wani makircin? Kuma ko me xakiyi bazai tasiri ba cuz Sultan yayi trusting dina more than he had ever trusted anyone! And also da yake banida hakki a kanki sai gashi kin kawo kanki da kanki kin tonawa kanki asiri, dama I have been looking for you, cuz na fara ganowa is all a plot! Abbi ma yana ta fafutar bincike a kanki sai gashi yau kin kawo kanki wow Alhamdulillah! So wama kike da suna? Do you think I will let you go so easily? Kin yi karya sai na dauki fansar abinda kikayi man!" Wani damka Hoodah ta kai mata a fusace sai yanzu ma anger din tate ke sake haye mata, tana tuna what she went through all because of this witch! Wani irin duka Hoodah ta kai mata, take Hoodah karfi ya kara yazo mata ta dinga dukanta ta ko ina ta fuska ta ciki, ba abinda Khairy keyi sai ihu tana dana sanin kawo kanta da tayi, "You witch! Har kin isa? Baki san ko ni wacece ba da har xaki neme ki shigo man gida! How could you do this to me?" Take bayi suka fara shigowa ba abinda suke sai rokon Hoodah akan ta kyaleta! "Gimbiya don Allah ki kyaleta have mercy on her!" Hoodah ta dago a fusace "Jeki kira wanda ke tsare da dungeon!" Da sauri ta fita nan Khairy ta tsorata ta fara bada hakuri "You have the audacity to ask for my forgiveness, kina tunanin da boka na dogara? Ke har kinyi tunanin kafin nayi wining Sultan har sai na hada da boka? Never! Sai dai idan kece zakibi bokaye da malamai don a karkato maki da hankalinsa, you are very stupid! Wallahi duk garinnan babu wanda zai tsaya maki idan na kulle ki! Ni dai kika nemi bata ma suna ko? Toh naki sai ya linka nawa sau dari! Ke har wani abu ma ya gani a jikinki da har zai ce yana sonki? Kalleki fa wata kucaka da ke! Kazama! Har kina tunanin zaki goga dani? Kinyi karya!" Hawaye ya fara shatata da idanun Khairy a matukar tsorace tace "Don Allah don annabi kiyi hakuri wallahi sharrin shaidan ne just spare me wallahi bazan sake koda kallon Sultan ba bare har in masa wani kallo da idon soyayya! Please believe me princess na tuba." Ta fada tana tsugunnawa bisa gwaiwarta alamun roko ta hade hannayenta wuri daya. Hoodah na rike da kwalar rigarta tayi murmushi "I will not fall for your trap you witch! Ke kika kawo kanki ina nemanki ma bare kuma yanzu da kika kawo kanki har taya kike tunanin zan barki ki tafi? Never! Allah ba azzalumin bawansa bane!" Khairy ta dinga gunjin kuka.... Sultan ne ya shigo turus ya tsaya yana kallon abinda yake faruwa "Hoodah! Lafiya?" Tana ganinshi ta saki Khairy wurinsa ta nufa idanunta cike da hawaye tace "Itace take neman tarwatsa farin cikinmu she's the one sultan, she has been plotting against me don ka tsaneni!" Ya juya yana kallonta take yabude idanunsa a waje yace "Khairy? You? Dama duk kece kike hadani da matata Hoodah!" Da sauri ta mike tana tangadi "Sultan ni ya kamata na zama matarka! Remember we used to love each other...? Kar ka gujeni kasan ina sonka kuma kaima nasan kana sona, kar ka bari wannan ta rabamu nice kakeso please Sultan..." hannu ya daga mata "Shut up! Haka ake so? Dama shi so zaka iya hurting wanda kakeso? You hurt me several times Khairy and now you're claiming you love me? You must be joking!" Ta nuna kanka "Ina sonka Sultan! Duk abinda nayi saboda kai nayi shi, don ka rabu da ita ka dawo muyi aure nasan nice wacce kakeso remember wannan kawai hada ku akayi?" Ya mata wannan irin mugun kallo "Let me tell you something no matter yadda kike kishi bazaki aikata abinda kika aikata ba, Khairy ba sona kike ba obsession ke damunki! And kinga matata Hoodah I trust her more than anything else in this world! Ina so kisa wannan aranki, your plots and tricks will not work on us again! And bari na fada maki magana ta karshe ki fita harkata nagane bakida hankali bakida wayau! Ni kuma bazan iya zama da mace irinki ba! I hate you Khairy I hate you! And now leave my house kuma ki fita harkata don idan nasake jin kinyi wani abun kuma you will regret ever being born! Guards! Zo ku fitar da mahaukaciyar nan daga gidana ko shadow dinta kar na kara gani a kofar gidannan! Kuyi mata bulala hamsin sannan ku bata kashi yadda ko tafiya bata iya yi, kafin ku barta ta tafi...." Wani irin ihu ta kurma "No Sultan kar kayi man haka! Kasan ina sonka!" Haka aka fiddata daga sashen kamar mahaukaciya!**
Da kyar take jan kafa tana tafiya hawaye na wanke mata fuska, a duniya zata iya daukar komai amma banda wulakanci, wulakancin ma daga masoyinta a gaban matarsa matar da tafi tsana duk fadin duniya itama meya kaita? Ay saida kawarta tace mata kar taje amma ta kafe ay ga irinta nan yanzu da wane ido zata kalli kawar tata ji yadda aka farfasa mata fuska da baki duk ya kumbure, ido duk yayi baki, she was heartbroken and miserable, meyasa zai mata haka she thought he loved her ashe ba haka bane? Is he dumb or something? Ta ya zai ma fara rejecting dinta yama san kuwa yadda take? me waccan tsinanniyar zata gwada mata in banda sarauta? She cannot tolerate this bullshit, kwankwasa kofar gidansu Hajara kawarta tayi, tana budewa sai tayi tsaye sakaka tana kallonta "Ke lafiya? Meyafaru dake?" Ta gefenta tabi ta wuce ta tafi parlor ta zauna tana huci, bin bayanta tayi da hanzari tana zuwa sai Khairy ta fashe da kuka "Yau bakiga dizgin da akayi man ba Hajara! Yau ni Sultan zaici mutuncina?" Hajara ta kyalkyale da dariya "Maganinki kenan! Ay saida nace kar kije kika kafe ay ga irinta nan!" Tana fadan haka ta nufi kitchen ta dora ruwan zafi ta dauko karamin towel, tana fara danna mata towel din data zunduma wani irin ihu kamar ana cire mata rai ita kuwa Hajara babu abunda takeyi sai dariya, "Gobe ma ay kya kara sannu mai masoyi, da kinbi shawarata ay da ba'a kai haka ba nace maki shi irin wannan bakayin haka ay, yanzu gashi nan banda ma haka kinje sun gane abinda kika shuka kuma ke a tunaninki a iya dukan nan abin xai tsaya? You are wrong ay kin kai kanki yarinya!" Tsawa ta daka ma Hajara "Da Allah ya isa haka! Wallahi bawai na daina bane ni wannan karon ma abinda xan mata sai yafi wanda nakeyi a da! Sai na dauki fansa sai ta raina kanta wallahi!" Hajara tace "Nadai fada maki you should be careful in kunne yaji?" Da haka ta cigaba gasa mata jikinta in banda ihu babu abinda takeyi.... ita kuwa ta kuduri sai tayi destroying life din Hoodah ko ta wane hali ne.
********
Bayan sallar isha'i Sultan ya shigo gidan fuskarsa cike da annuri da murmushi, direct dakin Hoodah ya shiga yaga ta zauna jugum alamun tana cikin damuwa, saboda a fuskarta ma ya nuna hakan, a hankali ya zauna kusa da ita saida ya rike hannunta ma tasan ya shigo dakin. Share hawayenta tayi ta juyo tana kallonsa "Habibty meya faru? Ko abinda ya faru dazu ne kike ma kuka?" Tambayar da yayi mata kenan hade da rungumota ta gefe fuskarta cike da damuwa, duk sadda yaga Hoodah cikin damuwa sai yaji zuciyarsa bata masa dadi ko kadan, balle ma yanzu daya fara fuskantar feelings dinsa akanta duk da yasha karyatawa ya kasa yarda, ba karamin tausayinta yakeji ba, "Sultan am scared..." sai kuma ta fashe da kuka, hugging dinta yayi "Haba Hoodah, why would you be scared when I am always here with you? You have me in your life kuma I will be there for you, you have Abbi and Ummi, you have your Abba, kuma kisani babu wanda ya isa yayi maki komai sai abinda Allah yayi maki, as I told you before I trust you Hoodah no matter what babu wanda zai sake shiga tsakaninmu again, then meyasa zaki ji tsoro? Dont be scared you have me to protect you always." Da kyar tayi shiru jawo hannunta yayi suka parlor nan taga ya siyo masu kaza da yoghurt sai ice cream, bayan sun kammala ya ja hannunta suka nufi daki yana ta faman tarairayarta lallabata.
*********
Buga kasa yayi yana shekewa da dariya "Meke tafe dake?" Ta gyara zama "Wannan da kake gani kawata ce malam, akayi mata kwacen saurayi toh duk tayi iya abinda xata iya na ganin ya dawo hannunta abun ya ci tura, shine nake bata labarinka aikinka kamar yanka wuka yake, nace da kayi anyi angama shine mukeso ka taimaka malam a dawo mata da saurayinta hannunta...." malamin wanda baya da maraba da boka ya sheke da dariya "Za'a iya haka, saidai ina fatan kin mata bayanin yadda nake aikina?" Tace "Na mata bayani tace zata iya..." yace "Toh yanzu me kukeso ayi mata? A kasheta? A haukatar da ita? Ku fada da kanku!" Khairy tace "Nidai malam so nake asan yadda akayi ta rabu da shi, kawai nidai burina su rabu ko ta wace hanya ce" mikewa yayi ya juma can sai gashi ya fito da wasu kwalabe da kullin magani "Wannan kwalbar zaki amfani da ita ki sha kafin ki sha zaki ambata sunan shi saurayin naki sau uku..." zaki ga result mai kyau, Wanann kuma zakiyi wanka dashi kwana uku, dayan kuma sha ne da madara kwana 7..." tace "Malam mungode..." nan ya umarce ta data tashi ta bishi cikin dakin haka ta bada ajiyar jakanta ta mike ta bi bayansa, wa'iyazubillah Allah kasa mufi karfin zuciyarmu.... sun dauki lokaci sai gasu sun fito nan suka bashi kudinsa sannan suka tashi suka tafi....
*******
Sultan ne ya fito daga sashensu, a hankali ya tsaya ta window jin kawu yana wasu yan maganganu
"Wallahi Hajiya Karimah bana tunanin duk abinda muka tsara fa yana aiki, ni gani nake ma kamar kara tsunduma wa suke kogin son juna, the more muke son tarwatsa su the more suke son kara kusantar juna...." yayi kwafa "Tou bazamu ce da sauki ba amma gaskiya suna can jikin dai gashi nan sai a hankali...... wallahi nayi duk abinda kika sani kawai dai akasi aka samu..... yanzu meye mataki na gaba da xamu dauka?...... ina jinki..... Toh shikenan zan kiraki zuwa gobe...... ok.... sai anjima...." wani irin tafasa zuciyasa keyi baisan lokacin da ya kutsa kai cikin harabar ba idanun nan jajir Kawu na ganinshi kawai sai ya saki wayar ta silale kasa ya mike, Sultan tsaye yayi yana kallonshi da hawaye a idanu "Kawu? So is all you all along? You of all people? Dama haka kake?" Ya fada yana nufarsa tare da damko masa wuyan riga ya hada shi da bango sai da kansa ya kume yabada wani kummm! Girgiza shi ya shiga "Dama kaine kaso kashe Abbi da Ummi! Kawu kai? Your very own blood? Kai da waye kuka hada baki kuke aiwatar da aikinku?" Ya sake kai masa kai a bango shi kuwa Kawu harda wata yar kara, "Step mother din Gimbiya ce, Umma...." karar wani abu sukaji suna juyawa sukaga Hoodah ce rike da tray da cup na glass ta sake su baki bude tana kallon Kawu, tace "Umma?"
No comments:
Post a Comment