Thursday, 17 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 17

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 17}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



"Kayi hakuri Sultan attackers ne da alama dai makiya ne suka diro, kafin muyi wani yunkurin kama su har sun gudu, kayi hakuri amma duk sunada rai babu wanda ya rasa ransa a cikinsu, munyi making duk wani arrangement a fita dasu waje yanzu nan da awa uku za'a tafi, sannan likitoci sun tabbatar mana cewar indai aka barsu a nan zasu iya rasa ransu..." A hankali ya dago kansa yace "Kawu? Yaushe kazo?" Kawu Murtala yace cikin damuwa "Saukar dare nayi jiya sanda na iso kayi bacci, da niyyar in kawo ziyara na taho ashe abinda zan tarar kenan?" Ya fada yana fashewa da kuka. Wata ajiyar zuciya suka sauke shida Hoodah jin ance ay basu rasu ba, kafin Hoodah ta rike Sultan tana sheshekar kuka, tabbas tayi bonding dasu sun zama tamkar iyayenta. Kafin nan da minti 30 sai ga ambulance din asibiti ta iso nan da nan aka fara basu taimakon gaggawa, Sai da aka jojjonasu da machines sannan sukayi masu bankwana nan aka samu kannen Ummi su biyu mace da namiji zasu tafi dasu, kamar ransu xai fita haka suka dinga yi masu Abbi sallama kamar suna jinsu, bayan sun tafi nan Sultan yayi tsaye yana bin motar da kallo har ta bace bat bai daina kallon wurin ba, ji yayi an riko hannunsa ya juyo da kyar yaga Hoodah ce tsaye idanu sun kumbure, janshi ta shiga yi da kyar yake daga kafarsa kafin ya iya takowa zuwa babban parlor, memories suka dinga dawo masa kala kala idan ya yakalli parlorn, zama yayi dirshen a kasa hannunsa cikin na Hoodah itama a hankali ta silale a gun ji yake kamar wanda aka zare ma lakka, kuka yake so yayi amma jin yadda Hoodah tayi squeezing hannunsa ya sanya ya fasa kukan, yafi minti sha biyar a haka kafin a hankali ya fara magana "Ummi da Abbi nasan ko bakuji abinda kowa yake fada ba nasan zakuji nawa, ko ban fada ba nasan kunji Sultan, your one and only son, sai cewa sukeyi ba lallai bane ku dawo da rai daga can zaku iya tafiya ku barni shikenan bazan sake ganinku ba? Sai dai nasan ba gaskiya bane, how can they leave their life and go elsewhere? Am their life bazaku iya tafiya ku barni ba ko Abbi? Ko Ummi? Kuma ko su waye suke da sa hannu a wannan muguntar na gano su wallahi sai na dau fansa!" Sai ya fashe da kuka dama Sultan ya lafiyar kura bare kuma tayi hauka? Ay indai kuka na baya masa wahala. Hugging dinshi Hoodah tayi tana share hawaye, breaking hug din yayi "Mamata tafi ta kowa she can sacrifice the world for you just to be happy, nasha fada mata  I love her so much, kar tayi losing hope and keep fighting, fight for me and for us, Ummi batada makiyi ko daya toh waye yake son ganin bayanta? Also Abbi, you are everything a son would have ask for, you will make it inshaAllahu I know you will I have faith in Allah, InshaAllah zai dawo daku lafiya..." Hoodah ta share hawayenta ta fara magana "Tunda nazoo nan sun nuna man kauna, sun yarda dani they also trust me, i look up to them as my biological parents, banida mahaifiya bansan dadinta ba, amma danazo ta fara maye man gurbin Ammina, dan Allah Ummi be strong for us, I need you more than i have ever needed anyone in my life, idan babu ke our lives will have no meaning, dan Allah for our sake be well again." Ta girgiza hawaye na cigaba da shatata "Abbi, he was like a father to me, ya kaunace ni, dan Allah ka warke ka samu lafiya..." ta karasa muryarta na rawa, kan cinyarta Sultan ya kwanta "Nayi missing su Abbi kina ganin zasu dawo?" Sai yanzu hawayen nashi suka samu damar zuwa yadda ya kamata fiye da da, wani irin tausayinsa ke ratsa ko wane lungu da sako na jikinta, tasan zafin rashin mahaifi ko mahaifiya ta rasa daya bataji da dadi ba inaga Sultan da yake neman rasa duka nashi a take? Wa yasani ko zasu dawo ko bazasu dawo ba? Hannu tasa cikin sumar kanshi a hankali tana murzawa "I can't say zasu dawo ko bazasu dawo ba Allah kadai yasan gaibu, Sultan abinda zamu sa ma ranmu shine Abbi da Ummi suna sonmu bazasu yarda su tafi su barmu ba zasu dawo InshaAllah, nasan kana sansu more than anything else amma ka yarda dani they're part of me too, I lost my mother at a very tender age, Ummi is now the only mother figure I have in my life..." sai kuma tayi shiru ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, a hankali Sultan ya dago yadda take kukan tamkar za'a zare mata rai, take tausayinta ya kama shi, a hankali ya mike zaune ya matso daf da ita ya rungume ta a kirjinsa yana shafa kanta, "Duk yadda rayuwa ta kasance maki zaki iya zuwa ki sameni Hoodah, don naga alamar banda abinda ya faru akwai wani abu dake damunki, ban dade da saninki ba amma ki yarda dani nasan kina cikin damuwa, bansan meke damunki ba amma zan iya baki hakuri idan zaki iya hakura, kiyi murmushi kinada wadanda suke sonki a rayuwa wadanda ko duniya zata juya maki baya suna tare da ke Hoodah, nasan Abbi da Ummi suna ciki sannan nima ina so ki sani cikin jerin mutanen nan a cikin rayuwarki." Shidai yasan bazai iya cewa yana sonta ba dan yasan babu digon sonta a cikin ransa, amma kuma he respect her, cares for her and also adores her, yana jin dadin zama da ita yasan shi dai ba soyayya bace tou menene? Shiru Hoodah tayi kafin a hankali ta dago da idonta tana kallonsa, ido cikin ido suke kallon juna "Are you sure duk sadda nake cikin damuwa zan iya fada maka? I am safe with you right?" Gyada mata kai yayi ba tare da yace uffan ba, ajiyar zuciya ta sauke, a nan suka cigaba da zama kowane na addua'ar samun lafiyar su Abbi. Murtala ne ya shigo da tun dazu yake tsaye bakin kofa ya karaso ciki zama yayi kan kujera ya dafa shi "Ka dangana addua'ar ka ita kadai suke bukata ba kuka ba, bacin haka ma kai ne zaka jagoranci mahaifinka har Allah ya basu lafiya, kai zaka karbi mulkinsa kai zaka cigaba da yi har ya dawo cikin koshin lafiya." Girgiza kai yayi "Bazan iya ba kawu, mulki dawani sarauta ni ba damuna sukayi ba sheyasa ma kaga ban fiya xama nan ba saboda bana son wani abu daya shafi hakkin mutane a kaina, dan haka wallahi bazan iya ba kawu." Murtala yace "Hakuri zakayi wa yake dashi da zai iya karba in ba kai ba? Dolenka zakayi ay ba wai don kana so ba..." yace "Kaifa? Ba dole sai ni ba, badai rikon kwarya bane don Allah ka karbar masa kafin Allah ya basu lafiya..." yar razana yayi "A'a Sultan kabar ma wannan maganar ma hakan bazai taba yuwuwa ba, kaine ya cancanta ka karba bani ba kaima kasani..." Sultan yace "Bakomai kawu, ni da bakina nace na bar maka tou meye a ciki? Kaima fa yayan Abbi ne uwa daya kuma uba daya Menene don ka karbar masa mulki?" Kawu Murtala yace "Jayayya bashida wani amfani Sultan, amma tunda ka kafe ka nace zan karba din nagode." Sultan yayi murmushi "Bakomai." D'aga Hoodah yayi data fara bacci bisa kafafarsa yace "Tashi mu tafi bangarenmu, an kusa kiran asuba..." mikewa tayi ya kama hannunta suka tafi sashensu. Saida da suka yi nisa kawu ya saki murmushi da shi kadai yasan ma'anarsa sannan ya dauki wayarsa ya kara a kunne....

****

Da daddare Sadiya d'aya daya cikin bayi ce ta kawo masu dinner wurin karfe taran dare, gaishe su tayi ta aje masu kan dining kawai ta juya ta fita, tuwon shinkafa ne da miyar gyada, shi kuma Sultan ko miyar miye bazai ci ba yadda ya tsani tuwo, indai kaga yana cin tuwo toh Ummi ca ta girka duk bala'in mutum bazai ci indai ba ita tayi ba.

Hoodah ta mike ta zuba masu a plate daya dan tasan baci zaiyi ba sosai, hannunsa ta kamo har sai ya zauna k'asa kusa da ita, "Kaci abinci please." Abinda tace kenan da disashiyar muryarta, girgiza kai yayi a shagwa6e ya tabe baki, nan taga zallar shagwa6a a fuskarshi tayi murmushi, koda Ummi ce tasan bazai ci tuwon nan ba yau saidai in ma zaici saidai ta bashi a baki. "Ko na baka a baki nima?" Ya girgiza kai alamun a'a "Dan Allah haba Sultan ka daure kaci please." Tayi rai rai da idanu kamar zatayi kuka, duk yinin yau ba wanda yaci wani abun arziki, "Kici kema toh." Ya fada wane karamin yaron daya yi kuka, "A'a sai kaci sannan zanci nima." Abinda tace kenan tare da kai hannunta wurin bakinsa amma ya juyar fa fuska "A'a kinga Hoodah kici abincin nan yanzu idan su Abbi suka dawo sukaga kin rame zasu ce mugunta nake maki, bana baki abinci ko bazasu ce haka ba?"  Ya fada idanunsa na ciccikowa da kwalla, dan murmushi yayi yace "Abbi will be like "Sultan bana son muguntarka fa yanzu dan kaga bana nan shine ko abinci baka bata? So kinga please kici." Girgiza kai tayi tana sharbar hawaye "Zasu dawo, kuma Abbi bazai ce maka haka ba, zanci abincin amma kaima sai kaci." Ta fada tana tallabo fuskarshi kafin a hankali ta dinga feeding dinsu tare. 

Washe gari Sultan yayi shawara take kuma waziri da sauran manyan manyan mutane bayan jayayya na wani lokaci daga karshe aka yanke baza'a nada shi ba amma zai zamana shine zai dinga tafiyar da harkokin garin, da kuma duk wasu ayyuka da ya kamata yayi. 

Wayarsa ce ta fara ringing sai da ya ke6e ya dauka "Da fatan kayi completing abinda na saka?" Yayi kasa kasa da murya "Nayi saidai duk basu mutu ba kamar yadda muka tsara amma dai rai a hannun Allah, saidai fa ina jin tsoro don garin gaba daya an baza yan sanda ana gudnar da bincike..." ta sheke da dariya "Kai da Allah! Nace maka babu ubanda ya isa ya gane mu dan haka kar ka damu kaidai ka cigaba da yin duk abinda na saka..." yace "Toh shikenan ranki ya dade angama," tace "Bissalam." Kit ta kashe wayarta tana wani dariya.

*****

Satika sun tafi tun su Hoodah nasa ran dawowar su Abbi har suka hakura, ya zama busy tare suke gudanar da harkokin gari shida kawu Murtala, kawu murtalan shine yake jawo shi a jiki yana nuna masa aiyyukan tun baya yarda har ya hakura yana binsa..... 

2 days duk Sultan ya zama wani iri dashi kullum cikin damuwa zaka ganshi gaba daya ya chanza, gashi baya bacci sosai cikin dare wani lokaci sai Hoodah ta farka taga hawaye na sauka bisa kuncinsa, haka zatayi ta lallashinsa wani lokacin sai ta fara kuka sannan yake shiru gaba daya Sultan yazama wani sabon Sultan ba wanda tasani ba a da. Wannan Sultan din baya son magana, ya wani da  rashin son mutane Sultan din yanzu sai tayi magana yafi sau biyar bai bata amsa ba. Gashi kullum yayi video call da yan asibiti basu yarda su bashi yayita roko a nuna masa fuskokinsa, kullum idan yace zaije India sai a hana shi ace ya zauna ya kula da harkokin Abbi. Kwana biyu da suka wuce Hoodah ta fara lura da yanayinsa ya fara canzawa, ga wani irin mugun bacci daya koya Idan ya shigo gida sometimes a parlor zai zube. Toh yau kam abin yafi na kullum har sha biyun dare bai dawo ba ta kalli window yafi a kirga shiru kakeji, bataso tasa ma ranta tunanin da takeyi a kansa ya zama Gaskiya, tasan alamu tasan signs tasan how they act, babu abinda bata gani ba tana yarinya Umma babu abinda batayi, salo salo na iskanci kala kala, don har mamaki takeyi wai mace da wannan dabi'un? "Ya Allah ya Allah kasa ba haka bane!" Abinda ta fada kenan tana faman zagaye parlornsu, ta zauna ta tashi, ta shiga daki ta fito har daya ta gota bai dawo ba, zama tayi kan kujera ta dafe kai kamar daga sama taji an banko kofa, tangadi yakeyi kamar zai fadi ga robar coke yana rike da ita a hannu daya, a razane ta mike ta karasa inda yake tsaye kafin ma yayi wani yunkure har ta fizge robar ta bude ta da sauri takai hanci kawai saita saki robar duk abin ya malale a kasa, tana furta "Innalillah wa inna ilahir rajioon! No not you Sultan not you!" Kafin kace me hawaye ya wanke mata idanu, wani irin kuka ta saki tana girgiza kai, baya baya takeyi tana faman girgiza kai, tasan kamshin abin don tun batada wayau take ganin kwalbar a dakin Umma tasha boyewa, har dauka take tana sinsina don haka tasan wannan ko menene har ta mutu bazata taba manta warinsa ba. "Sultan me ka jefa kanki a ciki? What have you gotten yourself into? Meka rasa Sultan? Dama baka dauki kaddara ba? Wannan wace irin rayuwa ce ka jefa kanka a ciki?"  Kuka takeyi bil hakki kamar ta fiddo Zuciyarta ko zataji sanyi, yanzu Sultan mijinta shine ya koma dan shaye shaye? Tangal tangal yazo inda take sai tayi sauri taja baya "Waya jefa ka wannan harkar Sultan? Innalillahi wa inna ilahir rajioon! Nasan dai ko kayi magana yanzu duk karya ce." Ta ma rasa abinda ya kamata tayi, tasan dai da kyar idan ba wani bane ya jefa shi wannan hanyan.... toh who? Umma? But how? Umma dake can Agadez ina taga Sultan? Haka ta jera ma kanta tambaya amma ba amsa. Zai fada kan kujera tayi saurin damko masa riga "Let's go to bed...." kallonta yakeyi kamar wani sakarai, toh wai kukan me takeyi? Shi ya ya kamata yayi kuka ta zubda mashi drink, drink din da kawunsa ya basa yace idan yasha zai rage damuwa, yasha kwalba tafi uku a yau, sanda ya fara bashi da da farko ya nuna bazai sha ba sai yace masa ay coke ne kuma mai sanyi, nan ya kafa kai ya shanye, toh tun daga wannan ranar kullum sai yaje ta bashi yasha, Hannunshi ta kamo ga hawaye gawani tukar bakin ciki dake cizon ranta, fizge hannunsa yayi yawani tunkudeta ta fadi tim bisa kujera!

No comments: