Wednesday, 28 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 38

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 38}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




----

Nada masa rawaninsa takeyi cike da gwaninta bayan ta gama tana murmushi tace "Here you go my king." Mirror ya kalla yana wani murmushi ya juyo yana kallonta cike da kauna sannan ya zagayo da hannayensa duka biyun yayi wrapping waist dinta yana kallon fuskarta, kokarin kwace kanta takeyi tana murmushi ya kara matse ta yana fadin, "Ina zakije? Stay here with me my queen." Ya fada cikin kunnenta alamun rada rada hakan yasa tayi dariya sonsa na kara ruruwa a cikin ranta. An kai kimanin sati biyu yanzu da yin nadin sarauta kuma Alhamdulillah abubuwa suna tafiya smoothly, ya fara fahimtar yadda al'amurran suke wakana da taimakon Abbi kuma yana ganewa sosai, mutane na jin dadin mulkinsa Hoodah is supportive tana kuma bashi kwarin gwiwa dari bisa dari sannan tana sashi a hanya idan taga ya kauce itama koba komai tanada experience tunda Abbanta sarki ne. Bata taba complain ba idan ya zama busy da yawa tana masa uzuri, bata complain tunda yanzu rayuwar ta chanza ba kamar da ba privacy dinsu ya rage sosai, tana girmama iyayensa da mutanensa wanda hakan ba karamin dadi yake masa ba. Kullum dada kara jin dadin zama da ita yakeyi, banda riko da addininta wanda tunda sukayi aure ya fahimci tanada sani sosai yanzu ma tare suke karatun quraninsu suna tunatar da juna, ga horse riding suna enjoying sosai a tare, sai kuma duk yamma sai ya fita da ita strolling yana rike da ita har su dawo. Jawota yayi a hankali ta zauna bisa cinyarsa yana wasa da yatsunta, shiru tayi tana so ta mike can dai tace "Zaka makara zuwa fada my king, in fact ka makara ma already bari na raka ka." Ta fada tana kokarin mikewa tsaye, a shagwabe yake kallonta yana fadin "O'o korata ma kikeyi ko Hoodah? I just want to spend some time alone with my wife." Amma ina Hoodah bata yadda ba bataso yayi late xuwa fada, "Saidai idan ba sarki bane shi kuma wannan sarkin ya makara zuwa fada oya tashi muje." Mikewa yayi kamar zaiyi kuka gaba tayi yana biye da ita a baya har bakin kofa, tsaye yayi kafin ya bude kofar hakan yasa ta juyo tana fadin, "Kayi mantuwa ne....?" Bata karasa magana ba taji ya janyo gently ta fado jikinsa, Kisses yake aika mata ta ko ina hakan yasa ta dinga dariya tana kokarin kwace kanta, saida ya gaji dan kansa sannan ya sake ta yana murmushi kafin yayi mata bankwana ya wuce fada, Hoodah tafi minti goma tsaye tana bin wurin daya bi da kallo kafin ta juya ta koma cikin gida fuskarta ta kasa daina murmushi. Tana komawa ciki da mintina kadan sabuwar jakadiya itace head of servants tadah ta shigo parlor Hoodah na zaune maids su biyu suna dan danna mata kafarta dake kumburi kadan kadan, jakadiya ta zube kasa tana bada gaisuwa "Barka da kwana ranki shi dade?" Hoodah na murmushi tace "Kina lafiya jakadiya?" Tace "Lafiya lau Sarauniya, dama abinda kikace a girka maki dazu tou an kammala Allah kara maki lafiya." Hoodah tace "Okay toh a bar man shi a dining zanci a can nagode." Jakadiya tace "Allah ya kara maki lafiya akwai wani abin da za'ayi miki yanzu?" Ta girgiza kai "A'a yanzu dai babu jakadiya kina iya tafiya." Jakadiya ta gyada kai ta sake mata kirari cike girmamawa sannan ta mike ta fita.---- 

A hankali yake taku maids dinsa na binsa a baya yasa kai cikin fada, wasu daga cikin title holders dake ciki suka gaishe shi ya amsa da murmushi saman fuskarsa bayan ya zauna ya umarce su dasu zauna suma, daya daga cikin dogarai ne ya sunkuya yana fadin "Ranka ya dade Malam Ibrahim din ya karaso, a shigo dashi ciki ne?" Ya gyada kai "Har ya karaso? Bismillah kace ya shigo." Tashi yayi ya fita ba'a jima kwarai ba suka shigo malam Ibrahim na binsa a baya ya karaso da sallama aka amsa masa, ya sunkuya yana gaishe shi "Ranka ya dade barka da kwana?" Sarki yace "Lafiya lau, Alhamdulillah malam Ibrahim yaya iyali?" Yace "Alhamdulillah nazo da yaran ranka ya dade."  Yace "Bismillah ka shigo dasu." Ya durkusa cike da girmamawa ya fita, can sai gashi ya shigo da yara maza kusan su talatin suna biye dashi zasu kai kimanin shekaru daga sha uku zuwa sha shidda. Kwanakin baya malam Ibrahim ya gayyaci Sultan saukar qurani ranar wata asabar, yaran almajiransa ne irin wadannan da ake turowa karatu daga gari gari suna zuwa bara don su samu abinda zasu ci, don wasu ma duk da sun sauke bazasu koma gida ba saboda neman na kansu da suke fafutika wasu zaka tsince su yashe a titi kwance, wasu cikin bola wasu kuma kullum suna bin gida gida suna bara, wasu sai suyi bara gida goma ma babu abinda suka samu, saidai idan wasu sun fito bada sadaka baifi su samu kosai uku uku ba ko kuma panke in kuwa masa ce da kyar suke samun biyu. Yinin ranar daya dawo gida babu abinda yake tunani sai hanyar da zaya bi don taimaka ma wadannan almajiran, wace hanya zayabi don rage yawon barace barace da suke yi? Ranar dai har Hoodah ta fahimci yana cikin damuwa ta tambayesa meke damunsa, shine ya fada mata ay taimaka ma almajirai yakeso yayi amma baisan ta wace hanya ba, "Meyasa bazaka basu jari ba su fara business don su taimakawa kansu tare da iyayensu? Dan abinda suke samu sai kaga suna dan aika ma iyayensu da wani abu, kasan dalilin da yawancinsu idan sun kammala karatu basu komawa gida? Saboda sunsan basu tara komai ba sai suga babban faduwa ce ace sun koma gida basuda ko sisi duk da sun yi ilimin, tou don hakane zakaga sun tafi wurare masu nisa suna neman hanyar da zasuyi surviving, yawancin almajiran tun suna yan kanana iyayensu ke turo su karatu, wasu iyayen suna zuwa wasu kuwa basu taba zuwa ba saidai idan sun girma su dinga zuwa ganin gida once in a while, wasu ma manta identify nasu sukeyi so kagani idan ka basu jari ba karamin taimakonsu zakayi ba su tsaya da kafuwansu, su zama responsible su san menene rayuwa. Bayan ka rage yawan almajirai da rage yawan barace barace a titi zaka iya hada committee funds na wadannan makarantu zaka iya dinga taimaka masu da abinci, ko kayan sanyi cikin sanyi, ko kuma kayan sawa ko kuma yan takalma haka slippers wallahi ina matukar tausayawa almajiran dake yawo babu takalmi haka xaka gansu kafafunsu duk a tsage abin tausayi, iyaka ka dinga zuwa duba su kana ganin abinda suke yi daga lokaci zuwa lokaci, sai ka masu alkwarin idan sun maida hankali ga karatun nasu zaka basu kudi suja jari, wannan ba karamin taimaka masu zaiyi ba kafin azo ga maganar ladarka wurin Allah," ta kare da murmushi saman fuskarta tsayawa yayi yana kallonta ba kakkautawa cikin ransa kuwa hamdala yake ga ubangiji daya bashi mata kamar Hoodah, mace ta gari mai kaifin tunani da hangen nesa da sanin ya kamata, Baisan lokacin daya rungumeta ba, tare suka zauna suna shawarwari  akan irin kasuwancin daya kamata yayi setting ma yaran, dago kanta yayi yan fadin "Allah ya saka maki da alkhairi, ya baki abinda kike nema duniya da lahira Allah yayi maki albarka ya kuma sauke ki lafiya." Yaran duk suna tsaye suna binsa da kallo abin tausayi gaishe shi sukayi, dama yayi waya da malamin nasu ya fada masa kudurinsa akan yaran bayan yayi shawara da Abbi da sauran manya suka amince masa dari bisa dari, malam Ibrahim ba karamin murna yayi ba ya dinga jera masa addu'oi ba adadi, shine sarki ya fada masa yazo mashi da yaran yasa masa rana shine ya kawo su yau. Kallonsu yakeyi fuskarsa dauke da murmushi yace "MashaAllah na tayaku murnar sauke qurani wannan shine farkon cigabanku a rayuwa InshaAllah," duk suka amsa masa da ameen cike da jin dadi, "Nasan dai malaminku ya fada maku dalilin zuwanku nan ko? Inaso mu yi wani abu kamar kasuwanci ne dani daku, zan kasance nine mai capital ku kuma entrepreneur din business din, zan baku jari ko wanenku ya fara sana'ar da tafi kwanta masa a rai, amma nidai a shawarce zaifi kuyi na siye da siyarwa amma ku tabbatar sana'arku ta halali ce karku sake ku yarda ku saida haram da kudina, na tabbatar kuna da ilimi kunsan abinda nake nufi, sannan banda riba, riba haramun ne ko a musulunci an bayyanata  a wurare daban daban a cikin alqurani da hadisin annabi (SAW), subhnallah Allah ya sa mu gane ya tsare mana imaninmu." Suka amsa a sanyaye, ya cigaba da magana "Kamar yadda na fada maku wannan sana'a tamu zamuyi fixing prices daku 50 50 duk abinda kuka samu zamu raba idan kuma kukayi asara nima zan dauki asarar tare daku hakan ba yana nufin ku zama careless ba, sannan inaso kusani zan zama responsible idan akayi asara a sana'ar da akayi ba ha'inci, duk mutanen wurin zasu zama shaida zan baku kudaden nan don haka ko wanenku ya zauna yayi tunanin kalar sana'ar da ya kamata yayi gasu nan ba iyaka, duk wacce kaji ta kwanta maka a rai sai ka fara da ita." Ya fada yana handing masu kudaden da yayi niyyar basu tare da alkwarin cewar zasu dinga reporting akai akai shima kuma zai dinga ziyartar su yasan me suke ciki, haka sukayi masa godiya sannan suka tafi cike da farin ciki marar misaltuwa. Bayan sun tafi sai ya kira malam Ibrahim don kar suji abinda zai fada masa in private yace "Maganar rabin kasona da na fada maku babu abinda zanyi da ita so nake a dinga masu saving, a hankali su dinga tarawa yadda ko aure suka tashi ba lallai bane su samu matsalar kudi, saidai banaso ko kadan su san da maganar nan a barta a yadda na fada masu cewar kudin nawa ne idan an raba da fatan ka fahimta?" Idanunsa taf da hawaye ya shiga masa godiya "Bansan da wane irin kalmomi zanyi amfani ba wurin nuna farin cikina gami da godiya da wannan taimako na alkhairi da kayi, Allah ya saka maka da alkhairi, Allah ya kara arziki Allah ubangiji ya taimakeka ya kara daukaka ya biya maka bukatunka na duniya da lahira," dukewa yayi rike da kafarsa yana kuka saboda farin ciki... "Wallahi ranki dade mungode mungode sosai Allah ya kara girma." Sultan ya dafa shi "Wannan duty dina ne so kar ka damu, kabi yaranka ka kuma kula dasu sosai kasa ido akansu amana ce a hannunka." Gyada kai yayi yana share hawaye kafin ya mike ya fita.

-----

Ki tuba kafin lokaci ya kure miki." Abinda Khairy keji a mafarki kenan kullum indai ta rufe idanunta koda idanunta biyu haka takeji ko kuma cikin bacci, haka duk ta rikice ta kasa komawa bacci tsoro duk ya rufeta, ba yadda Mama batayi da ita ba akan suje ta roki gafarar Hoodah amma abin ya gagara saboda shegen taurin kan tsiya, a yanzu Mama ke zama da ita cikin dare tana hanata yin kururuwa amma no matter what sai tayi. "Ki tuba kafin lokaci ya kure miki." Khairy tace da Mama tana mai fashewa da kuka makalkale da ita, “Kullum haka nakeji indai na kwanta sai an fada mun haka” wani kukan ta kara sawa “Ya isa Khairy ki daina wannan kukan sannan ki tabbatar kinyi addu’a kafin ki kwanta” “Mama ko nayi addu'a sai naji haka." Cikin sigar lallashi Maman tace "Nasan kinayi kuma hakan na taimaka miki sosai, kawai dai kiyi kokari ki samu bacci ko yaya ne” Ajiyar zuciya Khairy ta sauke sannu a hankali ta rufe idonta bayan ta tofa addu’oi marrasa adadi, aikuwa tana rufe idanunta take mafarkin data saba yi ya kuma dawowa har ta fara ganin wasu halittu suna nufo ta. Zaune ta mike tana share zufa don ta kuduri bazata koma bacci ba yafiye mata ta zauna idonta biyu don muddin ta rufe idonta sai ta gani, Mama ta mike jin Khairy na tabata, farkawa tayi tana binta da kallo. "Ke lafiya?" Khairy da idanunta sun kawo ruwa tace  “Mama ina son ganin Hoodah” Mama ta ware idanu "Bakida hankali? Tun tuni nake binki kije sai yanzu data zama Sarauniya wanda kinsan ganinta babban aiki ne, yanzu fa ba Gimbiya bace Sarauniya ce taya kike tunanin za'a barmu mu ganta kai tsaye?" Kuka ta fashe dashi kamar ranta zai fita tace, "Nidai don Allah ki taimaka mun Mama inganta, ganin nata shine kawai nutsuwar raina ki taimake ni” tasa kuka sosai, jinjina kai takeyi tana nazari kafin tace "Shikenan zanwa babanki magana inje gobe inga ko ganinta zai yuwu, Insha Allah." ta rungume Mama tana share hawayenta "Nagode Mama thank you." Mama tayi murmushi "Lokaci yayi da ya kamata ki sauke nauyin dake kanki ko kya huta da wadannan mugayen mafarkan da kikeyi” Khairy tace tana murmushi  “Insha Allah”  Mama tace “Kisani Allah ne yake sonki da rahama Ummalkhairy tunda har yake nuna maki a mafarki, just know that you are lucky." Khairy ta gyada kai tace “Hakane, Allah ka raba mu da son da zuciya Mama shaidan ya kaini ya baro.” Mama tace "Ameen tashi toh ki dauro alwala kiyi nafila." gyada kai tayi tana murmushi ta mike ta nufi bathroom tana jan kafa da kyar saboda cikinta da yayi mata nauyi, bayan ta gama ta idar tana kwanciya ta rufe idonta and for the first time da bataga komai ba, batayi wani mummunan mafarki ba.  Tabbas Allah mai rahama ne kuma mai jin kai ne, kuma idan har kayi wa wani laifi ko ka cuce shi ka zalunce shi idan har ka roke shi gafara ko kayi niyya zakaji kamar an wanke ka daga wani irin datti. 

Washe gari da safe wurin karfe sha biyu suka isa fada da Khairy harda iyayenta duka, saidai cikin rashin sa'a aka hanasu shiga don dogarin ma tambayarsu yayi yace "Kunada appointment da mai martaba ko ita Sarauniya?" Suka girgiza kai a sanyaye Baba yace "Kayi hakuri yaro sun sanmu ba saida appointment ba." Ina dogarin nan ya hanasu shiga sai da kyar shima wai sai dai aje a tambayo sarki in yace a shigo dasu sai a shigo dasu, shine fa ya bada izini sannan ya yarda su shiga. Sultan da Hoodah na bangaren su Abbi suka shigo da sallama don basu ma dade da gama breakfast ba lokacin. 

Ganin Ummalkhairy yasa duk suka tsorata duk ta rame ta kode in banda tsinin cikinta da haihuwa ko yau ko gobe, jikinta duk wani tabon kuraje ne sun bata mata jiki burjit, cikinta ya rinjayi sauran jikinta, tuna Khairy yar gayu mai ji da kanta da aji yau itace ta koma haka? Lallai Allah abin tsoro.  Mama ta taimaka mata ta zauna, Ummi da Abbi suka bita kallon tsoro kamar yadda Sultan da Hoodah suma suka zama shocked don sun kasa koda kwakkwaran motsi daga inda suke, “Mungode da kuka bamu izinin shigowa fada." Khairy manage to say “Sannu khairy” Mama ta fada ganin yadda take nishi kamar mai asthma, murmushin karfin hali tayi “Dama...." sai kuma numfashinta ya fara barazanar daukewa “Subhanalillah! Meyafaru haka??” Ummi ta tambaya har yanzu bata daina ma Khairy kallon tsoro ba, Mama tayi karfin halin fara magana, "Ranki shi dade abubuwa sukayita faruwa wanda nasan kin san da saninsu, tou karshe dai da aka tabbatar cutar kanjamau gareta dah kamar duka kenan tana shan magani amma yanzu bata sha ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, ta yaya take tunanin zata samu sauki?” Jira sukayi har sai da numfashinta ya daidaita sannan ta fara magana. “Nasan abinda na aikata zaiyi wuya ku yafe man especially Hoodah da Sultan, abubuwan dana yi maki inda ina da hankali ko dabba akace nayi ma haka ya kamata naji tausayinta ballantana mutum mace ma kuma yar uwata. Dafarko dai zan fara da cewa, ku yafe man saboda munanan abubuwan dana aikata yanzu banida sukuni banida kwanciyar hankali, rabona da inyi bacci koda na awa biyu ne har na manta sai mugayen mafarkai, mun dade muna soyayya da sarki amma rana daya ya auro wata ba karamin ciwo abin yayi mani ba, tun daga wannan lokacin na tsani Hoodah, na dinga shuka mata abubuwa da dama a tunani na shine hanyar da zanbi in rabasu ashe Allah yafini, na dinga bin bokaye da malamai ganin na kawar da ita....”  “Subhanalillahi Khairy abin naki har ya kai haka? Hoodah bata ta6a cutar dake ba, bata shiga harkarki, kuma ay ba laifinta bane ba don nace ina sonta, why Khairy? Meyasa zakiyi shirka kinsan girman laifin shirka kuwa?” Ya fada yana huci, tace "Nasani inama za’a iya komawa baya don na gyara 6arnar dana tafka, inama za’a sake bani wata damar na gyara laifuka na? Wallahi son danake maka shi ya jawo komai, I made sure to destroy your relationship, amma sai nayi realized your bond is strong, so strong that it will be difficult to seperate you, and so a brilliant idea come to mind, I decided to kill her, a cewata shine kadai hanyar da zanbi ganin na rabaku har abada, I was so angry dana ga tanada rai, ashe nice za'yiwa fyade, so when I learnt Khairy is pregnant I to plan to kill the baby as soon as aka haifesa, but I guess Allah has other plans for me!” “You want to do what?” Sultan ya mike a fusace zai yi kanta, Abbi ya dakatar dashi “Zauna Sultan, please”  Zama yayi yana huci, Hoodah kuwa fashewa tayi da kuka wannan wace irin kiyayya ce? “Innalillahi wa inna ilahir rajiun, Khairy yanzu duk kin akaita hakan saboda kishin banza? You decided to kill Hoodah saboda kishi are you normal? You framed her several times Allah na fiddata, kin kulla mata sharri kala kala Khairy bakiyi nasara ba, am ashamed of you, you stoop so low Khairy just because you want Sultan all to yourself!” Abbi ya fada a fusace, kuka take rerawa tace  “Nasani Abbi amma yanzu na gane kuskurena, please find it in your heart to forgive me, idan baku yafe mun ba I will never have peace” “So you think it’s easy just to forget and forgive you Khairy?” Sultan yace a fusace zuciyarsa sai tafarfasa takeyi “Don Allah don annabi kayi hakuri, Hoodah, Please ku yafe mun, Abbi da Ummi ku taya ni rokon Hoodah ta yafe mun," kowa yayi shiru, can Ummi tace, “Haba Hoodah meyasa kukaki yafe mata? A cikin alquran cikin surori daban daban Allah yayi maganar yafiya kada ku zamto cikin mutanen da basa yafiya mana, Allah kansa ma muna masa laifi mu roke sa ya yafe mana, meyasa ku bazaku iya ba? Meye ba'ayi wa annabi ba? Ku dubu darajarsa wanda akayi duniya da lahira domin sa ma ya yafe balle mu karan kada miya, Allah kansa yana yafe mana idan muka nemi yafiya don haka kuyi hakuri ku yafe mata tunda ta gano kuskurenta." Numfasawa Hoodah tayi "Tabbas hakane Ummi mu su waye da bazamu iya yafiya ba? Allah kansa yana yafe mana idan mun tambayesa, don haka na yafe mata." Sultan yace "Na yafe mata shi dan adam ajizi ne sannan ina so in baki tawa guddumuwar sai ayi maki treatment da kuma bukata idan ta taso, sannan zan baki shawara idan kin sauka lafiya ki sha magani daga nan kisamu miji kiyi aure Allah ya taimaka." Cike da jin dadi Baba da Mama suka fara godiya "Allah ya saka da alkhairi ya biya maka bukatunka na alkhairi, Allah ya kara arziki ya kara girma, Allah ya jikan magabatanmu ya haskaka kabarinsu, Allah ya kara dankon zumunci ya hada kanmu dana yayanmu baki daya, Allah kuma ya tsaremu daga sharrin dukkan sharri ya karemu daga rudun zamani dana shaidan. Mungode mungode Allah yasaka da alkhairi." Khairy ba karamin kuka tayi ba, tashi yayi ya kira Hoodah ya shawarce ta akan nawa xai basu, tace "Duk yadda Allah ya hore maka kawai ka basu." Million kusan biyu ya bata zo kuga godiya ranar sun sa masa albarka sunyi murna, nan Baban yace zai fiddata waje don inganta lafiyarta....

-----

Gaskiya ne da akace duk abinda ka shuka shi zaka girba, Karimah tana nan tana rokon mutuwa ta dauke ta amma shiru, idan ciwo ya motsa ji take kamar zata mutu, amma wani lokaci kuma kamar ba abinda ke damunta, anyi admitting nata asibiti don bata taimakon gaggawa sunce yanzu stage 3 take kullum burinta bai wuce ta mutu ba amma mutuwar taki daukarta azabar yau daban ta gobe daban duk ta rame ta jeme, ga cikinta wani irin kumburi yakeyi yana neman rinjayar jikinta su kansu likitocin tsoron ta6ata sukeji, don ya kamata ayi mata surgery amma suna gudun idan suka ta6ata zata iya rasa ranta saidai suyita ja mata rai suna sa ranar aikin, idan ranar tazo sai su daga kuma gashi babu wanda ke kula da ita dama duk ta watsa ya uwanta, wasu ma tun tana gidan Abba korar kare tayi masu, sai yanzu gashi tana bukatarsu kowa ya gujeta, kuka kam babu irin wanda batayi ba na bakin ciki da dana sani, kullum adduarta Allah ya dauki ranta ta hutu amma shiru sai tarin azabar ciwo sometimes kamar zatayi hauka idan ya motsa ta dinga kururuwa kenan tana ihu, yanzu dai sunce sai sun sa mata oxygen amma fir taki tace ita batason wani taimako mutuwarta kawai take jira har magungunanta da allurai duk bata yarda ayi mata, a cewarta ay idan tayi medication zata iya warkewa gara ta mutu gashi kuma mutuwar taki zuwa, saidai kullum ta zauna taci kukanta ta koshi...

------

No comments: