Sunday, 4 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 33

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 33}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




"Me kake tunanin kakeyi? Don kawai ina dauke da cikin his royal highness sai akace kar naci abinda raina yakeso ko? Tou wallahi cin chocolates yanzu ma na fara a gidannan, kuma duk abinda naji ina sha'awar ci sai naci kayana, kuma ciki sai an zubar din." Ta fada tana dora hannunta bisa kugu cike da masifa, hannu tasa zata dauki chocolate dinta yayi sauri ya fizgo ta, hugging dinta yayi sannan yasa hannu kan cikinta yana shafawa, wani kaunar babyn ne yakeji yana shigarshi wai shi yau Sultan ne zai zama daddy? Tab rayuwa kenan. Saurin fizge jikinta tayi cikin masifa tace "Wai kai Sultan dinnan meye haka? Ji sai wani rungume ni kakeyi kana wani shasshafa man ciki kamar wata mage, kasan Allah ka kiyayeni kar muyi tas akan babayn nan da kai toum!" Ta karasa maganar cike da bala'i don ita bataga dalilin da zai sa ya kasa fahimtarta ba. "Kinsan Allah Hoodah ki kiyayi maganar da zaki dinga fada mun, kuma daga yau na kuskura na sake jin maganar zubda ciki a gidannan sai ranki ya baci, cikin nan dai nine ubansa kuma zubarwa na hana zaki haife shi don dole koda hakan na nufi in danneki don ya karaso duniya tou xanyi da izinin ubangiji InshaAllahu." Sultan ransa a matukar bace yake ya kasa gane meye matsalar Hoodah ne. "Oho dai ciki dai a jikina yake, kuma zubarwa bazan fasa ba nima nice uwarsa don haka dole sai na zubda shi InshaAllahu..." Sultan ya bude baki zaiyi magana kenan sai jin muryar Abba sukayi kamar daga sama yana fadin "Zancen banza zancen wofi ma kenan! Kaji man shashashar yarinya kina hauka ne? Ciki dai da ubansa kuma yace sai kin haife shi, haihuwa kamar kamar kinyi ta kin gama ne ba kanki aka fara ba kuma baza'a kare a kanki ba..." cak suka tsaye cike da shock suna binsa da kallo, especially Hoodah da tayi mutuwar tsaye farin ciki, tsoro hade da haushi duk taji sun ziyarce ta, a hankali ta matso dab dashi hawaye fal cikin idanunta tana kallonshi kafin a hankali tayi hugging dinsa tare da fashewa da kuka mai tsanani, shima hugging dinta yayi back tare da lumshe idanu kafin ya saketa yana binta da kallo fuska daure, sai dai kana hango tsantsan farin cikin dake cikin zuciyarsa ya kasa boyuwa akan fuskarsa. "Hoodah kin bani kunya, meyasa zaki bude baki kice wa mijinki saikin zubar da cikinsa? Ke da aka samu naki cikin an zubar ne iyye? Haukan banza haukan wofi Hoodah meye haka? Kanki daya kuwa? Kai kuma in banda sakarci ka zauna tana fada maka magana son ranta kayi shiru ka kyaleta? Wai bazata haife shi ba yau ga shashahar yarinya....." da sauri Sultan ya saki murmushi ya yi sauri ya matso kusa da Abba yana fadin "Ehm Abba barka da zuwa? Maganar da kaji tana fada ba gaskiya bace ba wasa ne ba da gaske bane, kayi misunderstanding maganar ne ko Hoodah?" Ya fada yana kyafta ma Hoodah idanu alamun ta yarda da abinda ya fada, rausayar da kai tayi cike da shagwaba kafin ta kalalo murmushin dole "La Abba sannu da zuwa cikin wasa ne mukayi maganar ba Gaskiya bane, ahm ka zauna Abba bari naje na kawo maka koda ruwa ne kafin na daura maka abinci," tana fadan haka tayi hanyar kitchen da sauri dan tsabar tsoro ji take kamar zata fadi kasa, zama yayi yana ayyanawa a ranshi wannan yaran sun ma raina mashi hankali sun maida shi kamar wani karamin yaro, Sultan ya zauna gefensa yana fadin "Abba kasan irin abunnan na jokes ne fa mukeyi shine ma muke maganar..." kallo ya bishi dashi irin ji man yaro kai, can sai ga Hoodah ta fito da tray ta ajjiye a gabansa tana murmushin dole, juice din ta zuba masa a cup sannan ta bude masa dambun nama sannan ta tashi da sauri ta koma kitchen, shi kuwa Abba wani plan ne yazo masa a rai yadda zai ci kaniyar Hoodah don yaga sun maida shi wani sakarai ma marar wayau.

Sai da Hoodah ta kamamala abincin yaci sannan bayan yayi sallah sai yasa aka kira su, shiru yayi yana binsu da ido, kafin yace "Mamana yanzu ke da hankalinki da komai kike ikirarin zaki zubar da dan sunna? Kai kuma ya zaka zauna ka biye mata tsabar hauka? Tou bari kaji kafin in bar garinnan aure zan sa kayi sai in aura maka wacce bazata dinga maka gori ba wadda zata haifa maka yaya...," kallon kallo aka fara yi da Sultan da Hoodah ita tana tsoron abinda Abba ya furta zaiyi don ba karamin mummunan faduwa gabanta yayi ba, shi kuwa Sultan mutuwar zaune yayi, duk da dai baida tabbacin ko da gaske yake amma yanayin fuskarshi ya nuna he's serious, Hoodah ta rausayar da kai idanu duk kwalla tace "Don Allah kayi hakuri Abba, wallahi bada gaske muke ba wasa mukeyi..." Abba ne ya daga mata hannu "Nidai na gama magana, gobe zanyi magana da wani abokina akwai wata yarsa da batayi aure ba, shashashar yarinya kawai." Tuni Hoodah ta soma kuka, Abba na gama fadan haka ya mike ya nufi kofar fita, mikewa yayi Sultan shima yabi bayansa "Abba ina zaka sauka? Naga kasa an fitar maka da jakarka?" Abba Yace "Hotel zan sauka dama wata magana ta kawoni gidannan dangane da Karimah, tou nazo sai na iske wannan sakarcin da Hoodah keyi, Gaskiya yanzu raina a bace yake sai dai zuwa gobe sai muyi maganar, dan goben xan wuce InshaAllah." Sultan yace "Abba ya zaka tafi hotel muda muke dakuna bila adadin? Ka bari a gyara maka daya ka sauka a ciki don Allah kayi hakuri." Gaba yayi yana girgiza yace "A'a bakomai karka damu," nan dogarawansa sukayi gaba da akwatinsa, da sauri Sultan ya bada mota da driver yace kuma su tsaya can duk inda ya keso su kaishi. Dawowa yayi cikin gidan nan iske Hoodah bata parlor daki ya isketa ta raku6e jikin gado tana sheshekar kuka, jiki a sanyaye ya isa inda take ya zauna gefenta kafin ya kai hannu ya jawota jikinsa, tana jin haka ta saki wani sabon kuka na fitar hankali kukan da take ba karamin kona masa rai yakeyi ba, bai ce mata komai ba duk da shima zuciyar tasa tana masa zafi fiye da tunani, saida ta gaji don kanta kafin tace, "Sultan bana son kishiya, don Allah kaba Abba hakuri ya janye kudurinsa, wallahi I can't take it zan iya jure komai amma banda kishiya, I know life isn't always a bed of roses Sultan..." ta sake fashewa dawani matsanancin kukan kamar zuciyarsa zata fito, hugging dinshi tayi jikinta na kyarma haka yayi shiru ya kasa ce mata komai ko hakurin ma ya kasa bata don gaba daya shima jikinsa a mace yake. Saida kukan ya dan tsagaita kafin Sultan ya fara magana "Hoodah don Allah don annabi kiyi shiru ki daina wannan kukan da kikeyi, kiyi hakuri wannan ba laifin Abba bane ba abinda yaji ne ya tunzura shi, kawai dai mu cigaba da addu'a, sannan kema da laifinki meyasa kike son dole saikin zubar da cikinnan? Kidaina kuka don Allah ko don babyn nan Hoodah..." ya fada yana dan bubbuga bayanta don shi a tunaninsa yanzu ta hakura tana nadama ne. Da kyar ya samu taci chicken noodles kafin su kwanta, lokaci zuwa lokaci tana ajiyar zuciya can tace Ammi haka ta dinga kiran Amminta cikin daren nan, ba karamin tausayi taba Sultan ba, shidai fatansa yasa ta hakura ta janye kudirinta. 

Washe gari sama sama suka gaisa Sultan ya shirya sukayi breakfast ya wuce fada, da kyar tayi masa a dawo lafiya ta wuce daki. 

Bayan azahar tayi sallah ta dawo parlor tana kallo, dan kuwa sa ma rai damuwa babu abinda zai jawo mata sai illa, zaune take tana kallo amma zuciyarka gaba daya tana kan Sultan, don taji ance Abba yazo yana fada ta tabbatar yanzu maganar auren ma yake masa. Sallamar da taji shi ya katse mata tunani, a hankali ta mike taje ta bude kofa, Abba ta gani tsaye shida Sultan... 

bayan sunci Abinci Abba ya soma magana.... "Kamar yadda na fada maku wata muhimmiyar magana ce ta kawoni musamman, tun jiya naso muyita amma yanayin da na iske ku jiya gaba daya raina a bace na fita, anyway maganar dai data kawoni akan Karimah ce..." da sauri Hoodah da Sultan suka kalli Baba a bit shocked, Abba ya numfasa "A'a ba maganar tada hankali bace ba, wato dai da farko nayi zaman aure da Karimah tsawon shekara da shekaru bansan da wace irin mace nake zaune ba, nayi bakin ciki nayi dana sani marar adadi, saidai kuma na daukeshi a matsayin kaddara haka Allah ya tsara. Alhamdulillah Allah ne abun godiya daya tsamo ni daga cikin duhu ya maidani haske, ta aikata abubuwa daban daban wanda daga ciki akwai asiri da tayi man bana ganin laifinta, na biyu ta kashe mun matata mahaifiyar Hoodah, na uku da sa hannunta aka so kashe maka iyaye Sultan, dayan abun bai faduwa so is better dai a barshi a yadda yake, Allah ne ya kamata na gano komai, sheyasa nayi tattaki zuwa gareki yata da kiyi hakuri da duk rashin kulawar da nake baki yadda yakamata sannan ki gafarceni bansan haka kikayi rayuwa ba cikin kunci..." ya fada kamar zai zubda hawaye, tuni Hoodah ta taso ta dora kanta bisa kafafun Abba "Nasani Abba, duk nasan abubuwan da ta shuka har kisan Ammina, na zabi nayi shiru ne saboda kona fada maka ba lallai bane ka dauka karshe ma zaka iya koroni nasan baka ganin laifinta, amma Alhamdulillah da Allah yasa ka gane gaskiya Abba naji dadi sosai." Shafa kanta Abba yayi "Tou ni yanzu zan wuce Agadez dama abinda ya kawoni kenan, sannan inaso ki fada man idan kinsan inda Ashraf yake, ina bukatar shi a kusa dani..." ta girgiza kai hawaye nabin kuncinta "Bansani ba Abba, amma na tabbatar da duk inda yaje zai dawo komun dadewa wata rana zaka ga ya dawo." Ya gyada kai sannan yace "Yanzu zan tafi 3:30 ne flight dina kar inyi missing jirgi, Allah yayi maku albarka ki zauna ki rike mijinki kuma kar na sake jin maganar zubda cikin nan koda wasa a bakinki." Daga haka ya mike, Sultan da Hoodah ma duk suka mike Hoodah tace "Bari in dauko mayafina." Tana fada haka ta shige ciki da sauri, a bakin gate ta iske su tsaye Sultan da Abba suka juyo cike da mamaki ganinta da katon akwati, kallonta suke cike da shock ta kalli Sultan wanda yayi mutuwar tsaye, kauda fuskarta tayi gefe kamar mai tsoron magana ta ce "Sultan wallahi ina sonka, karka dauki abinda zan fada da wani abu dan Allah ka barni inbi Abba, and karka nemeni, babynka idan na haihu zan maido maka kamar yadda ka bukata...." kallonta suka tsaya yi har Abba kansa ya kasa furta koda kalma daya gaba daya sun zama speechless, amma daga ganin fuskarta sunsan da gaske take, da kyar ya bude baki dan wani zafi kirjinsa ke masa "Shi Abban yace kibishi ku tafi tare?" Abba ya dakatar dashi "Bance ta bini ba kuma ni bazan tafi da ita, kuma ko tazo agadez kar ta sake tazo man gida tunda taurin kai ne da ita, wai wane reason gareki na zubda ciki ashe ke sashasha ce marar hankali bansani ba? Tou nidai bada yawuna ba kuma maganar aure tana nan daram tunda kunnen qashi gareki, Sultan ni zan wuce idan kayi waya dasu Abbi ka gaishe su da jiki, kuma na yafe ba sai ka rakani airport ba kaje kaji da wannan sashashar yarinyar marar hankali!" Yana gama fadan haka ya shiga mota ko kallon Hoodah baiyi ba wacce ta juya da sauri ta saki akwatin a nan ta tafi cikin gida, bayan ya raka Abba ya juyo gaba daya he's not himself, haka yaba maids suka shigo da akwatin ciki, tsaye ya iske ta bakin kofa ta harde hannuwanta wuri daya tana kallon kasa, dan tasan idan har ta hada ido dashi zata fasa, kallonta ya tsaya yi kafin yace "Wai kin daina sona ne Hoodah har haka da baki kaunar kiga jinina? Sannan Abba yace shi baice sai kin bishi ba ya kikeso ayi yanzu?" Ta numfasa "Nifa Abba baice in bishi ba nice kawai nakeso inje, I want to be alone for some time, kuma na fada maka zan kawo maka da babynka InshaAllah." A matukar  hassale ya furta "Wai Hoodah what are you saying? Wai da gaske kike ne please? Yanzu idan kika tafi ya kike so inyi? Ina zakije? Kinsan I can't leave without you, Hoodah na roke ki kar ki tafi ki tsaya mu cigaba da rayuwarmu kamar da, mu kula da babynmu tare, please," zuwa yanzu gaba daya jikin Sultan ya gama mutuwa ya lura she became adamant ya san ba chanzawa zatayi ba baisan ya xaiyi ta hakura ba. "Nifa yanzu nace maka na yarda zan haihu, and maganar Abba duk da yace kar in je gida zan tafi sai dai ya ganni nasan bazai iya korata ba, am his daughter after all, maybe we are not meant to be." Tana gama fadan haka ko kallonshi batayi ba gudun karma ta chanza ta wuce daki. 

Can da daddare tana ji ya kwanta ya jawota amma ko kulashi batayi ba, amma bata hana shi ba saidai bata saki jikinta ba, dan ji take kamar ma ya kara auren ya gama a hankali yake magana kamar rada rada "Hoodah don Allah kiyi hakuri kinji? Yanzu idan kika barni all our dreams will be shattered, please babyna habibty na, albarkacin babynmu kinji?" Yanajin yadda ta sauke ajiyar zuciya alamun maganar ta shigeta, amma still dai he's not sure ko tayi giving up ba yet. "I will think about it just sleep kasan aljannu basa son firan dare," ta fada tare da rufe idanunta, Sultan dariya yayi kafin ya kamo hannunta yana murzawa a haka bacci ya kwashe shi....

No comments: