YAR AGADEZ
{Page 37}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
-----
Zuwa yanzu Hoodah ta kara kyau tayi fresh tayi yar kiba abinta, kana hangen tudun cikinta ya bullo, musamman Sultan ya samo mai zama da ita don kula da lafiyarta wata yar dattijuwa. Don yanzu saura kiris cikinta ya shiga na wata shidda cip, kullum sai Baaba Hinde ta bata addu'oi tasha wasu a shafa cikin dasu, ga magungunan gargajjiya da ake bata duk dai wasu na kariya ne wasu kuma na lafiyarta ne dana babynta.
Kamar kullum suna daki itada Sultan sun gama sallar isha'i suna lazimi Hoodah tawani yatsina fuska tana mika ta kalleshi cikin sigar shagwaba tace, "Sultan babynka yana jin kwadayi fa." Ta fada cike da zolaya don tasan tashin hankalin Sultan bai wuce ta fada masa tana jin kwadayi ba tana son wani abu especially cikin dare koda sassafe, don bata ta6a neman abu mai sauki ba kullum sai ta bashi wahala. Kallonta yake cike da tashin hankali yana fadin na shiga uku cikin ransa kafin yace, "Kai kuwa dan Baba ya zakayi man haka? I thought mun gama yarjejeniya da kai cewar babu abu mai sauki cikin dare sai da safe ko?" Yayi wata irin muryar tausayi hannunshi yana cikin na Hoodah. Itama hannunta ta dora bisa nashi idanunsu cikin na juna wata irin kaunar juna ce ke kara ratsa zukatansu, "Tou dan Baba kaji mudai bado mukesan ci da tuwon shinkafa miyar yakuwa sai gasashen kifi mai yajin nan wanda ake ci da sauce din albasa, su Daddy ayi sauri a nemo mana kar na haihu ban shirya ba." Ta fada miyanta na tsinkewa tana ji kamar ta gansu gabanta, dariya ta soma yi ganin kallon tsoron da Sultan ke binta dashi, babban tashin hankalin da yake ciki bai wuce inda zai samo yakuwar kanta ba balle azo ga bado, da kuma kifin, tuwon shinkafar kam ba'a maganarsa. Marairaice fuska yayi "Dan baba dan Allah ka taimaka man, kuyi hakuri ku chanza abinda zai samu a gidannan, gobe idan Allah ya kaimu shine abu na farko da zan fara nemowa." Ji yake kamar yayi kuka don yasan idan ta fara haka kamar wasa to ranar babu bacci za ta fara masa kukan fitan rai in bai samo ba. "dan baba muyi ma baba hakuri a bamu oats ko custard ko pancake mu dan rage zafi." Dan tasan Sultan ya hanata shan sugar, wata ajiyar zuciya ya sauke yana fadin "Eh naji din zan hado maku kusha amma dai na yau kawai." Mikewa yayi cikin mintina yaje ya hado mata oats ya kawo mata, a hankali take sha shi kuma ya cigaba da addu'oinsa, tana gama sha a nan kan sallayar ta 6ingire ta fara bacci kallonta yayi ya saki murmushi kafin ya cigaba da abinda yakeyi. Sai da ya gama ya dauketa bayan ya cire mata hijab sannan ya kwantar da ita kan gado tare da lullubeta, saida yayi wanka sannan ya kimtsa kafin ya kwanta ya rungume ta a haka bacci yayi awon gaba dashi.
------
2WEEKS LATER
Shopping sukaje itada Sultan na siyayyar kayan baby sun kwaso abubuwa daban daban duk da Sultan yace bayaso ayi mata scanning suga sex din baby, hakan yasa yace mata amma shidai yana son yar mace ita kuma tace namiji, gardama sukeyi akan kalar kayan daya kamata su siya nan Sultan yace "Tsaya kowa ya dauki kalar da yakeso idan kin haihu nayi winning zaki bani kyauta ta musamman idan ke kikayi wining zan baki kyauta." Tace ta yarda haka suka fara jidar pink and blue har suka kammala suka fito. A gajiye suka isa gida ko kayayyakin basu ce a sauke ba suka wuce ciki, wanka sukayi a tare sannan sukayi sallar isha'i sukaci abinci dama pizza yayi masu order babba da juice mai sanyi. Kwance take kan gado daga ita sai rigar bacci fara wadda ta fiddo mata da cikinta, kafarta yake matsa mata a hankali har bacci ya fara surarta, wayarsa ce ta fara ringing gashi wayar na kusa da ita, bude ido tayi ta dauko wayar tana kallon screen din, Number din Abbi tagani kasake tayi rike da wayar gabanta na faduwa, "Dauka mana kisa a speaker." Tana sakawa a speaker din sukaji muryar Abbe tangaram, kamar daga sama kuma sukaji muryar Ummi itama tana fadin, "Sultan? Ya kuke? Baka rame ba dai ko? Kana cin abinci?" Da sauri Abbi ya karbi wayar yace "Sultan, alhamdulillah mun samu lafiya ana shirin sallamarmu daga asibiti ma, nasa an maku visa kaida matarka, gobe karfe 9 ku hau private get dina ku taho, driver zaizo ya daukeku karfe tara na safe sai ku shirya." Ihun da sukeyi kamar wasu kananan yara tsalle sukeyi sosai tsakiyar gado suna rungume juna, baccin da ba'ayi ba kenan suka hau parking kaya ko wanensu bakinsa yaki rufuwa, "Abbi da Ummi are back! Safe and sound Alhamdulillah!" Daren ranar kasa runtsawa sukayi gaba daya ji suke gari yaki wayewa tsabar yadda suka kagara.---
A gajiye suka iso asibitin saidai baka gane gajiyar saboda ko wane fuskarsa shimfide take da farin ciki da kuma annashuwa, jikinsu babu inda baya rawa burinsu bai wuce suje suga halin dasu Abbi ke ciki ba, Abbi kam saidai ace ya warke tangaram saboda in ka kalleshi kamar bai taba rashin lafiya ba, Ummi da yake tafi jin jiki don ita sai last week ma ta fara magana da saidai ido, kalmarta ta farko itace Ina su Sultan? Tou tunda ta fara magana babu abinda take fada sai ina su Sultan Abbi yayi tunanin duk zafin ciwo ne har dai ya kira mata Sultan din, lokacin har ya masu visa din ma. Tsaye yayi yana bin Abbi da kallo cike da farin ciki kafin ya rugo da gudu yayi hugging dinsa cikin tsantsan farin ciki, itama Hoodah Abbi yayi mata tarba cike da murna a lokacin basu samu ganin Ummi ba sai zuwa anjima Doctors sukace zasu iya ganinsu. "Sultan kodai na kaika masaukinku ku huta zuwa anjima sai ku dawo? Nasan tana bacci ne sheyasa aka hanaku shiga yanzu." Ba don komai yace haka ba sai don Hoodah ganin dan cikinta daya bullo yasan tana tare da gajiya, nan kuwa can kasan ransa wani irin farin ciki yakeji yana ratsa shi saidai bai bari ya nuna ba, Hoodah ce tayi saurin cewa "A'a Abbi don Allah zamu jirata har sai ta tashi." Gani take tafi Sultan kagara taga Ummin nan, Abbi yar dariya yayi kafin yayi leading dinsu hanyar dakin da Ummin ke ciki bayan magiya da roko da sukayi ma Doctors din har finally suka barsu su shiga ciki. "Hoodah ke nafi tausaya mawa naga kinyi nauyi da yawa, haba Sultan shine ko ka fada man na fara siyayyar kaka ko?" Ya fada yana mai kamo kunnensa guda daya yana murdewa cikin wasa, kunya duk ta kama Hoodah shi kuwa Sultan yar kara ya saki "Am sorry Abbi ba gashi kagani ba yanzu? Kyautar me za'a ba baby?" Dariya Abbi yayi yana fadin "Kaci gidanku, kyautar kaina zan bawa dan marar kunyar wofi!" Dan duka ya kai mashi daidai time din da suka bude kofa suka shiga dakin, da murmushi a fuskarsu duk suka tsaya turus suna bin nurse da kallo tana ba Ummi medication sannan tana mata dressing ciwonta, dagowa Ummi tayi tana binsu da kallo da sauri Hoodah ta boye bayan Sultan don wata irin kunya taji ace Ummi wai zata ganta da ciki don cikin ya bullo sosai kamar dan wata bakwai, "Sultan..." ta furta muryarta na rawa daka ganta idanunta ya cika da kwalla, kamar wani yaro haka ya fara takawa wurin gadonta hannunta take miko mashi ya riko sai hawaye shar shar, hugging dinta yayi gaba daya sai suka fara kuka daga ita har shi sai can cikin kuka ya fara magana, "Ummi na dauka tafiya zakiyi ki barni bazan sake ganinki ba, muryanki, fuskanki komai naki kullum sai nayi mafarkinki..." breaking hug din Ummi tayi, "Haba Mummy's boy meyasa zakayi irin wannan tunanin? Ka kwantar da hankalinka everything will be okay soon InshaAllah, ya kamata ka daina kukan nan kada Hoodah tayi maka dariya." Murmushi ya kakalo yana goge hawayen dake zubo masa, Ummi kam tuni ta daina kuka saidai fa daka kalleta kasan dannewa kawai takeyi, hannunta ya sake gyara ma riko ya cigaba "I really missed you Ummi, how are you feeling now? Thanks for getting better for us all because we all need you two, and don't worry you'll soon be okay and back on your feet InshaAllah," hannun Hoodah ya kamo ta dawo kusa dasu ta tsaya tana binsu da kallo, kallon mamaki take bin Hoodah dashi baki sake a hankali idanunta suka sauka kan cikin Hoodah don dole ta saki hawayen suka zubo, a hankali Hoodah ta zauna sannan tayi hugging dinta tightly, "Ummi...." ta fada da muryar kuka, wani irin farin ciki na ratsa ta tunda take bata taba jin nutsuwa da tayi hugging Ummi ba kamar yau ji take kamar mahaifiyarta ce tayi hugging haka take jinta har can kasan ranta, "Hoodah.... Ikon Allah..." sai ta fara dariya kuma tana taba cikin sannan ta dawo tana taba fuskarta cike da soyayya ji take kamar itace ta haifeta, "Hoodah how are you? How did it went?" Ta kara tambaya tana kallonsu daga ita har Sultan din, share hawayenta Hoodah tayi da sauri sannan tace "It was not good Ummi, munyi kuka kamar ranmu zai fita, amma Alhamdulillah you're both fine keda Abbi, we couldn't thank Allah enough daya baku lafiya keda Abbi," Abinda Hoodah ta furta kenan tana kara hugging Ummi cikin muryar kuka, dan dukan wasa Ummi ta kaiwa Sultan tana fadin "Wace kalar mugunta kayiwa yata da bana nan? Naso ace ina nan ay da sai na rama mata duka muguntar da kake mata." Hoodah tayi murmushi cike da shagwa6a tace "Wallahi Ummi zo kiga muguntar da ya dinga mun kamar ba Sultan dinki ba." Ware idanu yayi yace "La ila sharri zakiyi man? Ni babu wata muguntar da nayi maki." Duk da cewar Baba na tsaye ganin Ummi cike da farin ciki ba karamin dadi yaji ba shima sai suka saka shi cikin nishadi da annashuwa, yace "Indai mugunta ce akazo kan Sultan kuma an gama magana, rainon turai ne fa kema dai maman yara kinsan haka yake kika barshi da Hoodah a gida dama ay kinsan abinda zai biyo baya kenan." Ya fada yana dariya, dariya duk suka kwashe dashi don itama kanta Hoodah tasan labarin yadda Sultan baiyi zaman Niger ba yana can gidan wata aunty dinsa can yake zama. Bayan zuwansu da sati kusan uku aka sallami Ummi dama shi Abbi tun satin da suka zo aka sallame shi, aikuwa ana sallamota da kwana biyu suka tattara suka koma gida.
Tunda suka koma gida masauratar ta kacame da baki shiga kawai ake ana fita yadda kukasan ana wani biki haka gidan sarki ya koma gaba daya ya cika ba matsaka tsinke, kowa yana zuwa yi ma su Abbi barka da arziki saida akayi kwana kusan goma ana baki sai a hankali a hankali mutanen suka dinga ragewa gidan ya fara dawowa daidai, gashi dama tunda Abbi ya kara warwarewa kawai ya hau gyaran gida gaba daya wasu wuraren rushe su akayi aka maida su modern, gidan sai ka rantse wata villa ce, duk su Sultan sun zama confuse akan dalilin gyaran nan yaki fada masu har daga karshe suka hakura suka zuba masa idanu har ya kammala nan kuwa wani shiri ne yakeyi babu wanda yasani, surprise ne yake so yayi ma kowa. Sultan ne ya fiddo wani golden box daga cikin wardrobe dinsa sai shining yakeyi, a hankali ya bude shi da sukaje India ta masa mugun kyau ya siya a boye ya adana da niiyyar yaba Hoodah abin kaunarsa, fitowa yayi daga side din nasu wanda akayi ma gyara sosai ya nufi sashen su Abbi nan ya tarar da Hoodah da Ummi zaune bisa yar varendar gidan suna shakar iskar wurin da alama suna enjoying kansu, fira suke jefi Ummi na yanka ma Hoodah apple da banana tana ci suna firarsu cike da nishadi, har kasa ya durkusa ya gaida mahaifiyar tasa yana murmushi itama ta mayar masa da murmushin tana fadin, "Wai ya kake ta mana safa da marwa a nan wurin ne? Ko don na karbe maka mata sheyasa kake ta zuwan man nan ka hanani sakat." Ta fada cike da zolaya, hararar wasa ya aika ma Hoodah wacce ke masa gwalo tana dariya kasa kasa, "Laa Ummi wallahi ba haka bane wurin Abbi zanje shine dana bi ta nan nace bari na tsaya na gaishe ku." Ya fada tare juyawa zai fita da sauri Ummi ta damko masa hannu hakan yasa Ummi da Hoodah dariya sosai, don sarai tasan meya kawo shi nan, "Words bazasu isa nayi expressing farin cikina ba, wai ace na kusa ganin little Sultan suna gudu cikin gidannan." Ummi ta fada cike da farin ciki ita kuwa Hoodah kunya ce ta lullubeta haka ta dinga wani sunna kai kasa, cikin farin ciki Sultan yake kallon Hoodah yadda duk ta zama uncomfortable kuma yanzu, Ummi ta kuma cewa. "Allah yayi maku albarka ya kuma sauketa lafiya." Yace "Ameen ya Rabbi." Yana gama fadan haka ya fice da sauri zuciyarsa fes.
Shiga parlon sukayi bakunansu dauke da sallama Abbi dake zaune shida mutanensa ya amsa sallamar tasu sannan suka samu wuri kasa suka zaune kansu a kasa bayan sun gaishe da sarki ya gyara zama yana fuskantansu yace "dalilin dayasa na bukaci ganinku cikin gaggawa da kai da matarka Hoodah shine, inaso dukanku ku shirya gobe idan Allah ya kaimu akwai wani taron da za'ayi cikin gidannan bayan sallar la'sar, taron yanada matukar mahimmanci dan haka banason ayi wasa da lokaci sannan ya kasance kun halarci taron..." Sultan ya dago yana kallon Abbi yace "Allah ya baka yawon rai taron na menene dan musan irin shirin daya kamata muyi?" Murmushi Abbi yayi irin nasu na manya yace "Kawai kamar yadda na fada maku kuje ku shirya kawai kuyi hakan zan turo jakadiyya da kayan da zaku saka goben..." da tou suka amsa kafin ya basu izinin tafiya a sanyaye suka mike kowane yana faman sake sake cikin ransa.
Washe gari wani irin gagarumin shiri akeyi wanda babu wanda yasani daga Abbi sai Ummi amma ya hanata furta komai akan zancen, kamar yadda sarki ya gayyaci mutanen garin suma haka suke shiri basu san me ke faruwa ba, saidai kuma daka kalli kowa kasan cikin farin ciki yake tun safe aka fara gudanar da shiri masauratar Niamey ta dauki harami babu abinda kakeji sai karar algaita da kalangu, hayaniya kam ba'a magana kudi Abbi ya damka ma Ummi masu uban yawa na abinci da kaji da snacks sai drinks nan da nan ta fara aiwatar da nata shirin itama, komai yana faruwa da sauri lokaci nata matsowa, tun safe sarki ya aika masu da kayansu kamar yadda yayi alkwari cike da mamaki Sultan ke kallon kayan ita kuwa Hoodah harda uwar alkyabba mai shegiyar kyau sai kyalkyali takeyi, duk ya hada masu harda takalma tou wai shi Abbi me yake nufi? Kuma taron menene haka ya hada? Bari dai mugani. Suna gama sallar la'asar suka hau shiri nan maids din suka fara taimaka masu da shiri hanawa sukayi sukace ay zasuyi da kansu, shifa Sultan da har ya manta ana wata sarauta saida Abbi ya dawo gani yake normal mutum ne yanzu har komai ya chanza. Bayan sun kimtsa sunyi kyau sosai nan maids suka rakasu har fada inda tuni sarki da Sarauniya suke jiran isowarsu, taku dai dai sukeyi cike da kasaita wuri ya dauki sowa da kirari kala kala kowa na wurin su yake bi kallo ga fadar ta cika makil ba masaka tsinke, da king makers, title holders da sauransu duk suna wurin, bayan sun zauna wurin ya dan natsu Abbi ya mike tsaye yana rike da sandar sarautarsa ya fara magana. "Muna ma kowa barka da zuwa wannan gagarumin taro da na shirya wanda na barshi a boye ba tare dana fada ma kowa kuduri na ba, nayi hakan ne dan yazama surprise dana yarima da matarsa, ba tare da bata lokaci ba! Ina so na sanar da al'umma ta cewar daga yau da nake tsaye a nan na aje wannan sarauta...." kowa na wurin saida ya zama shocked banda Ummi data riga tasan meke faruwa sai murmushi takeyi, shima sarki murmushin yayi na manya sannan ya cigaba "Karku damu abin farin ciki ne zan fada, bakomai bane yasa nayi haka saboda rashin Lafiyar da nayi sannan jikina ya kawo karfi na fara tsufa, don haka inaso in sanar da al'ummata cewa inaso in nada dana Sultan ya maye gurbina wato ya zama sarki don ya gaje ni...." bama Sultan kadai ba harta Hoodah saidai abin ya girgiza ta mikewa tsaye sukayi Sultan ya isa inda Baban ke tsaye yana kallonsa da murmushi a fuskansa Sultan yace "Abbi I can't do this, please..." Abbi ya dafa kafafarsa yace "You can and will do it InshaAllah, wannan decision din nayi tunani a kai don haka inaso ka zama sarkin garinnan Sultan..." hannunshi ya kamo yace ya tsaya daga gaba gaba matarsa na gefensa, sarki ya kalli king makers yace "A nada masa." Alkybba Abbi ya cire ya mika masu suka sanya masa sannan a hankali suka fara masa daura masa rawani, daga shi har Hoodah idanunsa cike yake da kwalla, bayan an gama duk wani formalities aka masa handing staff of office sannan aka ce ya zauna bisa karaga, sai a lokacin abin ya natse shi yanzu shine sarki, Sultan sarkin Niamey sarki na goma sha daya a kasar Niamey! Duka title holders suka matso gabansa suka fara masa congratulations na zama sabon sarki harda Abbi da Ummi wani irin gagarumin kwalla yaji ya taho masa, shidai yasan royalty bata dame sa ba sai gashi Abbi ya bashi wannan girman da bai taba tunani ba, take gaisuwa ta fara daga mutane daban daban hade da kirari na ban mamaki! Bayan an gama roundin up sai ya tashi ya isa inda Abbi ke tsaye yana zuwa kawai sai ya zube bisa kafadunsa ya fara kuka....
Dafa shi Abbi yayi shima kamar zaiyi kukan yace "Kar kayi kuka Sultan kai fa yanzu sarki ne, sarakai basa kuka." Ya fada da murmushi fuskansa, "No Abbi bazan iya ba, nauyin da yawa a kaina Abbi." Yayi murmushi "Wannan kuma kai zakayi deciding Sultan wannan alkawari ne na dauka kuma dole sai na sauke, kuma waya fada maka bazaka iya ba? Kwarai zaka iya kawai kayi focusing and you'll see, sarauta a jininka take you were born to lead, wannan hakkinka ne dole kayi facing dinshi cike da kwazo." Ya fada babu alamun wasa a tattare dashi hannunsa ya kamo ya zaunar dashi sannan yace "Zauna ka saurareni da kyau Sultan." Ya fada yana murmushi na son nuna masa kwarin gwiwa, "Kakanka wato mahaifina kafin ya rasu ya bar man wasiyyar cewa indai da haifi namiji tou in tabbatar ya gajeni, sannan inyi masa alkwari basai na mutu ba za'a dauki sarautar a damka maka a'a da raina ya kamata ace muna dora sa kan hanya har ya iya gudanar da harkokin sarauta, Alhamdulillah na dade ina jiran wannan ranar dama nace sai ranar daka zama responsible mutum ka kusa zama uba sannan zan karya alkwarin dana daukar wa mahaifina. Sultan bazance sarauta abu ne mai sauki ba saidai idan har ka natsu zaka fahimci tanada sauki da mutum ya maida hankali. Zama leader zai iya kai mutum wuta ko ya kaishi aljanna ka zama mutum mai adalci da sanin ya kamata, karka yarda power ta shiga kanka ka xamana mai yawan addu'a ya baka sa'a yasa ka zama adalin sarki, kayi koyi da qurani da kuma koyawar sunnar annabi (SAW), komai kaga ya faru haka Allah ya kaddara, idan ka dauki nauyin nan with seriousness and religiously bazaka kaga komai ba sai alkhairi InshaAllah, ina maka fatan alkhairi Allah ya albarkaci rayuwanku ya baka ikon aikata aikin alkhairi ga al'ummarka gaba daya." Goge guntun kwallan da suka zubo masa yayi sannan ya kalli Hoodah da murmushi shimfide saman fuskarta tana gyada masa kai, ya ce "Nagode Abbi Allah ya saka maka da alkhairi ya kara maka lafiya da tsawancin kwana, thank you." Abinda ya furta kenan saboda bai samu kalmomin da suka dace ya fada masa a daidai wanann lokacin ba, bayan ya gama sauraren dogon bayanin Abbi sai yaji sanyi cikin ransa da relief. Daga nan aka cigaba da gudanar da shagulgulan nadi, makada suka cigaba da kidinsu, kirari suka cigaba dayi ma sarki da Sarauniya Hoodah, daga nan akaci aka sha nan kuma aka dinga gudanar da kyaututtuka, manya manyan mutanen da suka samu halarta taron sune suka dinga kawo masu gift wasu kayan jarirai ne, wasu shadda, wasu atamfa, wasu lace, wasu rawani, wasu alkyabba, wasu jewelries, kai komai aka dinga basu as a gift, nan makada suka zagaye Hoodah suna mata kirari suna kidi, "Sarauniya Hoodah yar gaban goshin mai martaba, farar mace turar mata, farar mace alkyabbar mata, Allah yaja zamanin uwar gida a gidan mai martaba ya sauke ki lafiya." Babu abinda takeyi sai murmushi sai da aka lafa Ummi tazo tasa mata alkyabbar sarauta sanann aka zaunar dasu bisa karaga itada sarki, hannunta ya kamo yana murmushi sannan yakai fuskarsa daidai kunnenta yana fadin, "You look stunning my love." Batace komai ba kanta dai na kasa tana murmushi, haka aka cigaba da gudanar da shagali har saida suka ji kiran sallah sannan aka kare daga haka taron ya fara watswa, burinshi bai wuce ya dawo daga sallar isha'i ba ya tafi wurin Sarauniyarsa yasan tana can tana jiransa.....
Karfe kusan tara ya shiga da sallama turus ya tsaya kamar yau ne ranar farko daya fara ganinta saboda kyan da tayi masa don kuwa ta chanza shiga tayi kyau MashaAllah har yanzu bata cire alkyabbar ba, har ta amsa sallamar tasa baiji ba saboda yayi nisa a kallonta, a hankali yake taku har ya shiga cikin dakin sosai ya zauna kusa da ita, a hankali ya kamo hannunta cikin nashi yace "Ya kike?" Ta sadda kanta kasa tace "Alhamdulillah my king." Murmushi ya su6uce masa yana kallon fuskarta yace "Naga bakici abinci ba a wurin taro nasan kina jin yunwa ko?" Ta girgiza kanta da sauri "A'a banaji, nasha fura." Yace "Kin tabbatar?" Ta gyada kai yace "Okay then bari na zuba maki koda yoghurt ne ki kara dashi." A cup ya zuba mata yoghurt din yasa ta shanye kafin ya gyara zama yana fuskantarta, "Welcome to the life of a queen Hoodah, na maki alkawarin cigaba da kula da ke iya karfina, zan cigaba da kokarin baki hakkinki kuma InshaAllah bazaki taba nadama ba a tare dani ba, zan cigaba da baki kulawa ta musamman har ki haihu lafiya," shiru yayi dan yayi catching numfashinsa kafin ya cigaba "I promise to be the king of my kingdom and also promise to be your king my queen, do you also promise to be the queen to my kingdom and the queen to my heart?" Ya tambaya fuskarsa dauke da murmushi ta gyada kai wani guntun kwalla na zubo mata daga idanu, hannu yasa ya share mata yana fadin "Duk kwallan da zaki zubda a gidana saidai ya zama na farin ciki InshaAllah." Hannunta ya kamo "Muje muyi wanka sai muzo mu kwanta ko?" Mikewa tayi har yanzu bata bar murmushi ba don ji take kamar wasu sababbin couples duk komai ya dawo mata sabo, bayan sun fito daga wankan suka kimtsa suka hau gado, dora mata kanta yayi bisa kirjinsa yana shafa gashinta a hankali take rufe idanu haka har bacci yayi awon gaba da ita.
Washe gari maids suka hada masu ruwan zafi bayan sunyi wanka Sultan ya fara yi nan ya zauna jiranta parlor, shiru yaji nan ya tashi ya leka sai ganinta yayi ta kimtsa da sauri ya nufi dakinsa ya bude wardrobe dinsa ya dauko box dinnan ya koma daki, yana komawa dakinta ya nufeta da murmushi yace "Close your eyes my queen." Da hesitating tayi sai kuma ta rufe, gab da ita ya matsa ya bude box din ya jawo golden necklace dinnan sai shining take, sanya mata yayi sannan yace "Open your eyes now my queen." A hankali ta bude idanunta tana bin sarkar da kallo, kallonsa tayi ya sakar mata murmushi "You deserve it my queen, naki ne is all yours." Bata san lokacin da tayi hugging dinsa ba tana fadin "Thank you my king you are the best." Murmushi yayi yace "Ke nake jira mu wuce, and don't forget to put on your alkyabba please." Ta gyada kai tana murmushi daga haka ya fita ita kuma ta karasa sannan ta fito, hannunta ya kama suka fito waje nan guards suka fara kai masu gaisuwa da kirari. Da takun kasaita suka isa sashen su Ummi guards na biye dasu, Ummi suka gaida sannan suka zauna yin breakfsat, bayan sun kare suka mike don zuwa gaida Abbi. Message din Abba ya shigo wayar Hoodah ta bude tana murmushi yace "Assalamu Alaiki ya ke diyata, kiyi hakuri bansamu halarta taron da akayi ba na nadi ayi man afuwa wani abu ne ya tsaida ni amma InshaAllah zanyi tattaki har nan zanzo in tayaku murnar wannan abun alkhairin daya sameku, ki gaida Sultan da duk sauran mutanen gidan, Bissalam." Murmushi tayi tana kokarin maida kwallan dake neman zubo mata. Bayan sun gama suka fita Sultan har sashensu ya raka Hoodah sannan ya juya guards na biye dashi zuwa haraba, yau ce ranar farko da zai fara duty dinsa a matsayinsa na sarki....
No comments:
Post a Comment