✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_
P.M.L
🌹41 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
A hankali ta bud'e idonta juyi d'aya tayi ta hango shi bakin wardrobe da alama wanka ya fito yana shirin fita, duba agogo tayi k'arfe 8:30am, zumbur ta mik'e tana mamakin abinda ya haddasa masa makara yau, zaune ta mik'e tana kallonsa yana k'ok'arin d'aura agogo a hannunsa, ta sauko daga gadon ta kamo hannunsa tana cigaba da sa masa.
"Yau ka makara my soul."
Jin yayi shiru ya sanya ta d'ago tana dubansa da mamaki, damuwa ta gani k'arara bayyane a fuskarsa wanda idanuwansa ma sun nuna hakan.
"Meyake damunka my soul?"
Yace
"Babu komai, kije kiyi wanka yau tare zamu fita, sannan ki sanar da Zarah ta tamabayi mijinta ya bata izini zamu fita tare da ita."
Tayi shiru tana tunani can kuma tace
"Lafiya?"
Yace
"Koma me kenan zaki gani nan da lokaci kad'an, kedai kawai ki kirata ki sanar da ita."
Tace "To." Sannan ta wuce tana tunanin dalilinsa nace mata haka.
Tayi wanka ta sanya bak'ar after dress, tea kawai suka sha inda a waje sukayi kaci6us da Zarah inda take shaida musu da mijinta zasu tafi yace zai kaita, haka ma Anisah tazo a daidai sadda zasu shiga mota, itama ta shaida musu mijinta zai kaita, nan kuma kowa ya fara shirin tafiya.
A mota babu wanda yayi magana ko wane da tunanin da yakeyi, ta kai dubanta ga Faruk da alama ya zurfafa cikin tunanin, ta ta6o sa tace
"My soul wai meke faruwa haka ne? Sannan duk ina zamuje da su Anisah?"
Ya karkato kad'an ya kalle ta sannan ya maida kansa ga titi yace
"Ki gafarce ni my baby."
Tace
"Akan me fa?"
Yace
"Kawai ki yafe min akan abinda zai faru yau."
Cikin rashin fahimta tace
"Me zai faru yau?"
Bai kai ga bata amsa ba wayarsa tayi ringing, ya d'auka yace
"Hello Usman."
Usman yace
"Muna hanya ka turo mana address d'in."
Yace
"Muma muna hanya, zan turo maka sai mun had'u d'in."
Ya kashe kiran ya tura masa address d'in.
Meenah da zuciyarta fal damuwa tace
"Kaji my soul, wai meke faruwa?"
Yace
"Kiyi hak'uri zaki ga koma menene."
Ganin ya d'auki hanyar unguwarsu ya sanya tace
"Daman gida zamu shine kak'i sanar dani?"
Ya d'anyi murmushin k'arfin hali a zuciyarsa yace
"Nasan yau zanyi breaking heart d'inki my baby, amma abinda zanyi ya zama dole in ba haka ba hankali na bazai ta6a kwanciya ba."
Ya kalle ta yaga ta zurfafa cikin tuanani, yayi ajiyar zuciya a lokacin da ya karya kwanar layinsu Meenah.
Ganin motoci a k'ofar gidansu ya sanya ta d'an razana kad'an gami da zaro idanu waje, ya kalleta ya kawar da fuskarsa gefe, yasan kota masa tambaya baisan abinda zai ce mata ba.
Yayi parking ya fito daga mota, yana d'an kalle kalle, ganin ba motar Usman ya sanya yasan bai iso ba, amma motoci hud'u sun iso na abokanan aikinsa, su Zarah duk sun iso inda take ta tambayar abinda ke faruwa. Amsa d'aya take samu wato,
"Nima bansani ba."
Su Najeeb ne kad'ai suka san abinda ke faruwa saboda ya sanar musu daman.
Ya d'auki waya ya kira Hajir ya sanar mata yana k'ofar gida. Tace she's ready tun d'azu. Nan suka cigaba da tsara plan d'in nasu.
Ita dai Meenah bata k'ara magana ba illa dai gabanta da ya tsananta bugu.
A 6angaren Bilki kuwa tunda ta tashi da safe k'awarta ta iso akan yau zasu walimar bikin d'iyar wani sanata da za'ayi a cikin garin Abuja, Baba kuwa yana d'akinsa yana wanka zai fita, shiryawa tayi cikin wani dank'areren leshi mai matuk'ar tsada sai k'yalli takeyi, wayoyin da ke hannunta sun kai kala uku kuma manyan wayoyi masu tsadar gaske, ta fito parlor sai zuba k'amshi take kamar shagon saida turare, kaci6us tayi da Hajir sanye cikin bak'ar after dress tayi tsaye a bakin k'ofa idanunta manne cikin bak'in glass wato no respect.
Suka ja suka tsaya Bilki ta kalle ta daga sama har k'asa tace
"Ke Atika meye haka? Ina aikin dana saki zaki zo kiyi wa mutane tsaye a ka haka! Matsalar d'an k'auye kenan ka wayar da shi sai daga baya ya nuna yafika wayewa. Mts."
Laila tace
"Gaskiya kam da alama don wannan yarinyar 'yar rainin hankali ce, ke Malama ki bamu wuri zamu wuce."
Hajir ta kalle su da chewing-gum a bakinta sai hannunta dake hard'e tace
"Wacece Atika don Allah?"
Bilki tace
"Ahh! Kiji min neman magana fa, yo wacece Atika 'yar aiki in ba ke ba? Kaji min yarinya zata nemi ta maida ni k'aramar yarinya."
Laila tace
"Gaskiya wannan ta samu wuri da yawa. Da nice ke da tuni na sallame ta don bazan iya ba, zan iya farfasa mata jiki."
Bilki tace
"Eh gaskiya ne, ke Atika! Ki wuce kije ki d'ora girkin rana kafin mu dawo."
Hajir ta kallesu a wulak'ance tace
"I'm sorry to say Hajiya, amma bazanyi ba, sai dai idan kece zaki je ki d'ora."
Suka fara salallami suna tafa hannu, Laila tace
"Wai bazaki gaura mata mari ba, ni wallahi sheyasa kikaga bani d'aukar 'yan aiki saboda bansan wadda zan kwaso ba, ya za'ayi ki zauna kina fad'a tana fad'a? Ki d'auki mummunan mataki akanta mana."
Bilki tace
"Lallai kin k'oshi da sadda aka kawo ki kamar zakiyi min sujjuda amma yanzu kin k'oshi kin mik'e k'afa ko? Lallai sannu Atika, to wallahi kizo ki kwashi kayanta ki bar min gida munafuka kawai."
Hajir tayi murmushin mugunta tace
"Daman yau zan bar miki gida Hajiya kar ki damu."
Bilki tayi tsaye ta rasa ma me zatace sai tafa hannu kawai takeyi.
Minti goma tsakani Faruk ya doka sallama, Bilki ta washe baki tace
"Ah kinga surukinmu ne yazo, sannu da zuwa Faruk."
Ya shigo yana k'are ma gidan kallo, yana d'aga kwalar rigarsa yace
"Ki gyara kalamanki Hajiya ba Faruk zakice ba, Inspector Faruk Adam Ishaq zaki ce."
Suka kalli juna itada Laila, Laila ta rad'a ma Bilki a kunne
"Adam Ishaq fa yace, me hakan ke nufi kenan?"
Hajir tayi murmushi ta cire after dress d'inta ta dawo kusa da Faruk tace
"Sunana Inspector Hajir ba Atika ba."
Bilki tace
"Ke kamar ya keba Atika bace, to wacece ke?"
Meenah da Zarah da Anisah suka shigo ganin Ikon Allah a daidai nan Baba ya sauko yana gyara hular kansa ganin mutane da hayaniya ya sanya yaja tsaya yana tambayar lafiya?
MSB💖
Tuesday, 29 August 2017
Sunday, 27 August 2017
AUREN FANSA 40
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_
P.M.L
🌹40🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Ya shigo gidan a lokacin da ya tarar da Meenah a bakin k'ofa, tana sanye da brown and cream atamfa d'inkin riga skirt, tayi kyau sosai, da sauri ta taro sa ya k'ura mata idanu yace
"My baby ya akayi ne?"
Yaushe rabon da taji sunan nan a bakinsa har ma ta manta, tayi murmushi tace
"Jidda ce tun d'azu banganta ba, ko da saninka ta fita?"
Ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, tace
"Ikon Allah kenan, amma Jidda bata yi wa kanta adalci ba, amma sai inga duk bai kai na saki ba my soul."
Ya kamo ta suka dawo parlor suka zauna yana kallonta sosai yace
"Rabuwa da Jidda shine mafi alkhairi a garemu my baby, saboda a gaskiya bazan iya cigaba da zama da ita a matsayin matata ba, besides ba'a son raina na aure ta ba."
Ta dube shi cike da mamaki tace
"Bangane ba my soul."
Yace
"Wato akwai wata rana na fito zan tafi aiki sai naji Jidda na magana da mahaifiyarta tana ce mata ita ba wanda takeso sai ni, a nan naji Mama na ta rarrashinta akan tayi hak'uri tunda ni ba sonta nakeyi ba, tun daga wannan lokacin sai na karaya nake ganin kamar ban kyauta ba, abin yana ta damuna sosai, a ganina abinda kawai zanyi na faranta ransu shine na bijiro da maganar auren Jidda, a tunanina sun mani komai a rayuwa bai kamata d'iyarsu tana sona nak'i ta ba."
Meenah ta kamo hannunsa tana murmushi tace
"A gaskiya kayi tunani mai kyau kuma ka kyauta, sai dai daman tun farko kayi min bayani da sai nafi fahimtarka my soul."
Yace
"Naso yin hakan my baby, amma a lokacin sai na rasa dalilin da yasa na kasa fad'a miki gaskiya, kuma wallahi bansan yadda akayi ba sai dai naji ance wai matata ce, abin zai baki mamaki is like bansan abinda nakeyi ba, kuma a lokacin Jidda tayi amfani da magani wajen jawo hankalina gareta, nidai kawai idan ta warke zan sallame ta, taje can ta nemi wani daidai da ita."
Tace
"Bazan iya saka yin abinda baka so ba, duk abinda kaga yafi dacewa kayi ni kuma zan baka goyon baya d'ari bisa d'ari my soul."
Ya kamota ya rungume a k'irjinsa gami da lumshe idanu yace
"Sheyasa nake sonki my baby."
Tace
"Nima haka, yanzu muje kayi wanka kaci abinci ko, na dafa maka abinda kafi so."
Cike da jin dad'i yace
"Allah my baby?"
Tace
"Wallahi kuwa."
Yace
"Shikenan muje, don yau ma kece zakiyi min wanka da kanki."
Ta tashi tana fari da ido tace
"Muje."
Ta wuce yabi bayanta.
****
Yana zaune a office d'insa aiki yasha gabansa wayarsa ta fara ringing, ganin Hajir ya sanya ya dakata ya d'auka.
"Hello Hajir."
Tace
"Hello Sir ina wuni?"
Yace
"Lafiya lau, ya dai?"
Tace
"Aikinka na kammala komai Sir, yanzu ya za'ayi?"
Cike da jin dad'i yace
"Da gaske kin had'a komai da komai?"
Tace
"Yes Sir komai ya kammala."
Yace
"Wow Weldon Hajir, a gaskiya nayi matuk'ar farin cikin jin haka, yanzu abinda za'ayi, ki shirya zuwa gobe zan shigo gidan, dana kiraki sai ki fita daga shigar Atika ki koma Inspector Hajir d'inki. Sauran bayanin zan kiraki. Yanzu wani d'an bincike nakeyi akan wad'anda suka turo domin kashe iyayena, nama kammala don har na tura a kamo yaran, don muna buk'atarsu."
Tace
"Yayi haka sir, sai Allah ya kaimu goben."
Yace
"Amin, thank you."
Daga haka sukayi sallama, Faruk yayi murmushin jin dad'i sosai.
****
Kiran farko na sallar asuba a kunnensa akayi, domin ba bacci yake ba, saboda tsabar farin cikin kalar matar da Allah ya bashi, shi kwata kwata bai k'ara tabbatarwa ba sai yau, tambayar kansa yakeyi anya kuwa akwai wanda ya kai shi sa'a?
Ya lalubi bed side lamp sannan ya dube ta tana bacci, numfashinta yana fita a natse.
Kyakkyawar fuskarta nata annuri, yayi ta kallonta baya ko kyaftawa har sai da idanunsa suka kawo ruwa sannan ya dawo hankalinsa, ya sunkuyo a hankali ya manna mata light kiss a goshinta, ya numfasa, Allah kad'ai yasan tarin son da yake mata. Da k'yar ya lalla6a ya sauka daga gadon ya shiga toilet yayi wanka ya fito da alwalarsa, ya shimfid'a sallaya yayi nafilfili har alfijir ya fito, sannan ya nufi masallaci.
Yanda ya barta haka ya dawo ya same ta, yayi tsaye a gaban gadon rungume da hannayensa yana kallonta.
"Wai lallai baby an gaji."
Ya zauna gefenta ya tallabo kanta sannan yace
"Meenah... Meenah..."
Ta bud'e ido a hankali tabi shi da kallo har idon ya washe gaba d'aya. Yace
"Ki tashi kiyi sallah, ko gajiyar ce ta hana ki tashi?"
Ta runtse ido tana k'ok'arin tashi, yayi murmushi kawai ya d'aga ta cak sai toilet, ya tarba ruwa masu d'umi ya saka ta ciki, ita kuwa idonta har yanzu a lumshe yake, yana tsaye yace
"Haba ragguwa sai kace first time dai."
Tayi murmushi kurum, daga haka ya fita ya bata wuri don ta kimtsa.
Tsawon minti 20 tafito, ya matso yana dariya.
"Ragguwa kawai ni tuni naje masallaci na dawo."
Ta wuce shi tayi shirin sallarta tana jin wani irin nishad'i marar misaltuwa. Kwanciyarsa yayi, ta gama sallarta tayi adduo'inta gami da mik'a godiyarta ga Allah da ya karkato mata da hankalin mijinta gareta tana fatan su dauwwama haka har k'arshen rayuwarsu. Sai kuma ta tuna Jidda ko a wane hali take yanzu? Ta dad'e tana mata addu'ar samu sauk'i, tana gamawa sai kawai ta maida kanta bisa sallayar tana lazumi. Ya d'ago yana dubanta yace
"Ya zaki kwanta a nan?"
Tace
"Haka nan."
Yace
"To kodai?"
Ta k'udundune fuskarta da hijabi ta k'yale shi, cicci6o kanta yayi ya d'ora bisa jikinsa yace
"Tashi mu koma kan gado."
Tayi shiru tana kallon kyakkyawar fuskarsa, yace
"Allah yayi miki albarka my baby."
Taji dad'i sosai ta amsa da
"Amin my soul."
Ya cigaba da fad'a mata dad'd'an kalamai masu rikita lissafi, ganin haka yasa na tashi na baro d'akin, sai dai fatan Allah ya kawo k'azantar d'aki.

Saturday, 26 August 2017
AUREN FANSA 39
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_
P.M.L
🌹39 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Meenah ta dube shi tace
"My soul bai isheka ba abincin ko?"
Ya gyad'a mata kai, ta mik'o masa hannu ya sa nasa cikin nata tace
"Zo muje na had'a maka wanda yafi wannan, babu mamaki k'ila tana son cin wannan ne."
Baiyi gardama ba yabi bayanta suka nufi sashenta, tana tsaye da plate a hannunta suka fice, galala take kallonsu har suka fice, babu shakka Meenah ta yi gaba a halin yanzu ta barta baya, dole ne ma ta d'auki mataki akan haka. Ta fito daga sashen cin abinci (dinning) ta nufi sashenta.
Zaune take abin duniya ya ishe ta, ta sak'a wannan ta warware, daga k'arshe ta mik'e ta fito daga d'akin tana cizon hannu. Shiru babu motsin kowa, da alama suna cikin d'akin Faruk, haushi ya turnik'e ta kamar zata fashe.
***
Dawowarsa kenan daga gidan, rashin ganin Meenah bata tarosa ba ya tabbatar tana makaranta don tace masa yau zatayi test har biyu.
Yana shigowa yaci karo da Jidda daga bakin k'ofa sai faman washe baki takeyi.
"Sannu." Tace dashi tana taunar chewing-gum, yayi tsaki yace
"Yauwa." Ya sa kai zuwa d'akinsa yana Allah wadaran da mace marar tarbiyya.
Yana zaune bakin gado yana cire safarsa ta shigo sai wani cika take tana batsewa. Zama tayi gefensa tace
"Ya Faruk magana nazo muyi."
Yace
"Yanzu Jidda daga dawowata sai ki tare ni da wata magana kuma, ay kya bari in huta dai ko."
Tace
"Nidai ka bari na fad'a maka."
Ya dakata yace
"Ina jinki."
Tace
"Ay dai kace kai baka tauye hakkin iyalanka ko?"
Yace
"Haka ne."
Tace
"Yauwa, to tunda baka tauye hakkin iyalanka so nake ka barni na tafi Dubai, na karanta Fashion and Design."
Ya karkato yana dubanta yace
"Da igiyar wa?"
Tace
"Da igayarka mana."
Yace
"Kinga Malama banson zancen banza, ta yaya kina matar aure kawai don rashin hankali sai ki tafi wata uwa duniya da sunan karatu, ke bari ma kiji ni ba irin mazan nan bane da mata ke juya su yadda suka ga dama ba, don haka wallahi sai na sa6a maki kika k'ara yi min zance makamancin wannan."
Cike da shagwa6e tace
"Haba don Allah ya Faruk, wai ni meyasa kake min haka ne? Saboda Allah ita Meenah ay ka barta tana karatu sai ni zaka hana ni."
Yace
"Ita Meenah ba kina ganin cikin garinnan take ba? Yau ga zancen banza zancen wofi, ke nafa gaji da rigimarki haba! Mutum kullum da abinda zaice daga wannan sai wannan to wallahi na gaji."
Kawai ya tashi ya bar mata d'akin.
Ita kuwa sai tasa kuka tana ta magana ita kad'ai.
****
Ranar wata Juma'a Luby tazo gidan, nan suka baje suna fira. Jidda ta dubi Luby tace
"Luby gaskiyar magana nayi dana sanin wannan aure, banida tantama alhakin Meenah ne ke bibiyata, ke tunda nazo gidannan ban ta6a tsintar farin ciki ba daidai da rana d'aya ba, nikam na gaji wallahi auren ma ya fita raina, mutumin nan sai shegen kulle baya bani abinda nakeso, ga abin takaici wai Meenah yanzu tayi min in mata batada tsoro ko kad'an, ke wallahi aurennan na gama shi sai ya sake ni."
Zumbur Luby ta mik'e tana salati tace
"Yanzu Jidda abubuwa nata faruwa shine bansani ba? Baki iya fad'a min? Sai da abubuwa suka jagule miki suka fi k'arfinki shine zaki sanar da ni yanzu ko?"
Jidda tace
"Kiyi hak'uri Luby wallahi na d'auka zan shawo kan abin ne."
Luby tace
"Aiko sai mun d'auki fansar abinda tayi miki, bata isa ba, wacece ita? Ke kin bani kunya kinfa girme ta, amma kin zauna tana juya ki."
Jidda tace
"A'a Luby ke kinsani sarai mu da magani mukayi aiki, ita fa? Ay ba d'aya bane ba ma."
Luby tace
"Shikenan, amma kar kiyi saurin karaya, aure kuma yanzu kika soma shi, yo mekenan idan kika tafi tun yanzu, ay ko baki warci wani abu ba ni kya wabto mani, kuma ke ina son da kike masa? Ko dama k'aryar banza ce?"
Jidda tace
"Luby don bakisan irin wahalar da nake sha ba, babu fa yadda muka iya saboda matarsa tayi mana zarra."
Luby tace
"Wallahi k'arya takeyi! Kedai ba kina amfani da kwallin da turaren ba?"
Jidda tace
"Wallahi ina yi, kedai Luby munzo inda aka kere mu."
Luby tace
"Yanzu akwai wani abu a wurinki?"
Jidda ta girgiza kai
"Babu komai sai tarin wahala da takaici."
Luby tace
"To zan san matakin da zan d'auka, zan dawo anjima ko gobe."
Washe gari da sassafe ta dawo, ta d'auki Jidda amma sai da suka shirga ma Faruk k'arya sannan ya barsu da k'yar, shima akan kar su dad'e.
Suna tafe a mota Luby tace
"Kar ki damu k'awata, zan kai ki inda za'a share miki hawaye."
Jidda tace
"Ina kenan?"
Luby tace
"Me kike ci na baka na zuba, kedai ki tsaya ki gani."
Luby ta koro ma Barmuje bayani, yayi 'yan tsubbace tsubbacensa zuwa can yace da Luby
"An 6ata aiki ay, saboda tun farko sai dana fad'a miki kar ya wuce daren farko baiyi tarayya da ita ba, amma ina bakuji ba, sannan kuma sai da ya fara yin tarayya da uwar gidanki akanki, don haka aikinki bazai ta6a yin tasiri ba! A yanzu komai ya wargaje saboda uwar gidanki tana da rik'o da addini sosai, a gaskiya kafin wani abu ya kamata da wuya. Ina tunanin kawar da ita ne kawai zai baki damar mallakar mijinki don haka sai kisan abinyi."
Suka kalli juna itada Luby tace
"To yanzu meye abinyi?"
Barmuje yace
"Akwai maganin da zan baki, zaki zuba mata a wani abun sha, kamar koko, fura da sauransu, wannan abin da kike gani guba ce data sha ita da duniyar nan sai dai a lahira."
Luby tace
"Akwai wata hoda da ka bani jiya, inaga kamar zata fi yi mata amfani."
Yace
"Tabbas! Zaifi sauk'i sai dai zan k'ara gargad'inki da kada ki kuskura ki shak'i hodar nan don idan kika shak'a.... hahaha to kema zaki bak'unci lahira, idan kuma baki mutu ba... haha! To zaki wahala a nan duniyar sai kin zamo abin tausayi."
Luby tace
"Zata kiyaye ma."
Da haka suka baro dajin da Barmuje yake, suka dawo gida.
Luby tace
"Yanzu dai ga maganin nan, kuma kinji gargad'in Barmuje wallahi kibi a sannu."
Jidda tace
"Haba kar ki damu komai zai tafi yadda akeso."
Luby tace
"In ta mutu ki sanar dani, zan had'a mana grand party."
Jidda tace
"Ay dole ne ma wannan."
Suka k'yalk'yale da dariya gami da tafawa.
Daga haka sukayi bankwana Luby tayi gida cike da murna.
****
Meenah na kwance a d'aki tana baccin rana inda Jidda ta lalla6o da hodar a hannunta, Jidda ta huro mata hodar tayo baya da sauri, sai dai mey? Memako Meenah taji wani abu sai ma ita Jiddar ta kurma uban ihu sakamakon jikinta dake mata rad'ad'i. Meenah ta farka tana salati sannan ta fito da sauri ganin meke faruwa.
Jidda ce a tsakar parlor tana kurma ihu tana soshe soshe, Meenah tayo kanta tana tambayar lafiya? Ture ta Jidda tayi, sannan tayi d'akinta da gudu ta fad'a toilet tayi wanka da ruwa masu sanyi sosai. Sai dai babu wani sauk'i data samu. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuka kawai takeyi, ga sam ta hana Meenah ta ta6a ta, sai surutai takeyi marassa kan gado.
Hijabinta ta saka ta fito parlor a lokacin Meenah na sallah d'akinta, aiko da sauri ta fito ta tafi gidansu.
Mama na d'aki tana sallah ta shigo tana kuka, sai tirje tirje takeyi, bayan Mama ta sallame ta juyo tace
"Ke lafiya..."
Bata k'arasa magana ba Mama taja baya cike da tsoron ganin fuskar Jidda kamar ba tata ba, Mama ta fito da gudu tana salati tana fad'in
"Wacece ke?"
Jidda na biye da ita tana dariya tana cewa
"Ni ce, nice naje wurin boka nida Luby muka anso magani zamu kashe Meenah."
Mama tasa salati tana fad'in
"Jidda. Meya kaiki? Mekika zama? Innalillahi wa inna ilahir raj'iun! Jidda."
Jidda tasa dariya, sai ta susa kai, ta susa jiki tana zum6uro baki tace
"Wai laifina ne? Kaji man Mama, nifa kawai d'ora ni akayi akan turbar nabi kuma."
Ana haka Dada ya dawo, shima cike mamaki yake tambayar lafiya. Mama ta kwashe komai ta fad'a masa abinda Jidda ke cewa.
Dada yace
"Da alama fa kamar hauka takeyi ko?"
Mama tace
"Nima shi nagani."
Suka sa salati, Dada yace
"Duniya budurwar wawa Jidda, Allah ya shiryeki, Hajiya kamo ta ki kai ta d'aki ki rufe kafin mu san abinyi."
Tace
"To."
Ta kamo Jidda, tana tirjewa da k'yar suke tafiya, Jidda taci kwalar Mama tana dariya tace
"Ina zaki kaini? Iye?"
Mama tace
"Muje d'aki ki kwanta."
Jidda tasa dariya, can kuma tasa kuka, can tasa dariya, sai kuma tasa kuka, ta jawo hancin Mama ta matse tace
"Daman haka boka yake? Laifin duk na Luby ne saboda ita ta kaini tun farko, saboda ban ta6a zuwa ba ay ko?"
Mama tana kuka tace
"Eh muje."
Mama ta sha wahala don da k'yar ta kai ta d'aki ta rufe, sai dai taji ana bubbuga k'ofar ana ihu, can taji dariya, can taji surutai, can kuma taji ana cewa
"Boka, boka, Barmuje sunansa."
Mama tayi tsaye tana kuka, tace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Jidda kinga halin da kika jefa kanki ko? Kinzo kiyi wa wata asiri ya dawo kanki, duniya ina zaki damu? Ka haifi d'a amma baka haifi halinsa ba. Allah ka shirya shine kawai abinda zan ce miki Jidda, Allah kuma ya yaye miki."
Dada ya kira Faruk ya sanar masa yazo yana nemansa yanzu yanzu.
Ba'a d'auki lokaci ba ya iso, Baba ya kwashe komai ya fad'a masa, Baba ya d'ora da cewa
"Ina so idan ta warke ka sallame ta, baka buk'atar cigaba da zama da ita, tunda har kamar Jidda tasan tayi kisa ay kaga zama da irinsu ba amfani.
Faruk yace
"Allah ya kyauta, Allah kuma ya bata lafiya."
Baba yace
"Amin."
Faruk yace
"Bari na dubo ta, daga nan sai na nemi asibitin da za'a kaita."
Baba yace
"To kabi a hankali, don jikin ba dad'i."
A hankali ya tura k'ofar d'akin tana zaune dirshen a k'asa tana kwa6a sabulu da toothpaste cikin wata roba, ya kalle ta duk ta shafa ma kanta, ya zauna a bakin gado yana kallonta cike da tausayi, wannan wace irin rayuwa ce? Wai Jidda tasan taje wurin boka? Ya kalli Dada dake tsaye a bakin k'ofa sannan ya maida dubansa ga Jidda da ke shafa sabulun a jikinta.
Ya gama kallonta yayi mata adduo'i sannan ya tashi ya fita.
Ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba ya je ya nemo asibitin da za'a kaita, daga nan aka kwasheta da da k'yar daga gidan. Faruk ya sanar ma sauran 'yan uwanta suma sunyi jimami sosai, daga k'arshe sukayi mata fatan shiriya da samun lafiya.

AUREN FANSA 38

🌹38 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Daddare bayan sallar maghrib Faruk ya kirawo su a babban parlor yana son magana dasu. Bayan sun iso ya fara magana kamar haka.
"Abinda yasa na tara ku a nan shine, na farko ina so ku sani shi aure ba abin wasa bane, sannan ban k'ara aurennan da wata manufa ba sai alkhairi, kamar yadda kuka sani ana yi wa ko mace kwana biyu ko uku, don haka na ware kwanaki biyu zan rik'a yi wa ko wacenku, ranar girkinki ya zagayo zaki kar6i girki, saboda Meenah ba baiwa bace da zata rik'ayi maki girki sai dai kici. Sannan banison raba abinci, idan girkin d'aya ne to zata dafa ma duka gidan abinci, da fatan kun fahimta?"
Meenah tace
"Mun fahimta."
Yace
"Yauwa daman shine maganar."
Jidda ta k'ule meye na ci mata mutunci a gaban Meenah?
***
Da safe Faruk na d'aki yana shirinsa zai fita aiki Jidda ta shigo sai faman zum6uren baki takeyi, ya kalle ta ya kawar da kansa tare da cigaba da abinda yakeyi, ta matso kusa dashi tace
"Ya Faruk ina son magana da kai."
Ba tare da ya kalleta ba yace
"Ina jinki."
Kai tsaye tace
"Mota nakeso ka siya min."
Ya dakata daga abinda yakeyi ya juyo yana kallonta cike da mamaki yace
"Mota fa kika ce? Anya kina da hankali kuwa?"
Tace
"Da hankalina ai itama d'ayar matar taka tana hawa mota, ni bana hawa, don haka ance kayi adalci a tsakaninmu nima sai ka bani mota."
Yayi ajiyar zuciya yana fad'in
"Jidda, Jidda, a gaskiya rigimarki ta fara isata, idan kina maganar mota dana bawa Meenah ina kikaga tana zuwa inba makaranta ba? Ke kuwa ba zuwa makaranta kike ba saboda bakici Jamb ba koba haka ba? Don haka tunda bakya zuwa makaranta ni ba motar da zan baki, da dai kina zuwa ne wannan is understandable sai na d'auki d'aya daga cikin motocina na baki kema kina zuwa makaranta, don haka kar na k'ara jin wannna maganar a bakinki ma."
Ta juyo cike da masifa tace
"Ni gaskiya baka kyauta min ba, kawai don nace ka bani mota sai ka min gori? Ni gaskiya ka bani mota tam."
Yace
"Bazan bada ba zo ki k'wata, ko ita Meenah ba rok'a na tayi ba ni naga dacewar hakan na bata, don haka kema idan naga ya dace na baki zan baki."
Ta fara jijjiga jiki tana masifa
"Kawai don nace a bani mota shine mene? Naga dai motocinnan kana da su to meye don ka bani d'aya?"
Yayi tsaki yace
"Ke kinga tashi ki fita ki bani wuri, mota kuma zo ki k'wata sai muga ta tsiya, sakaryar banza wadda batasan ciwon kanta ba, kullum ke kenan rigima daga kice wannan sai kice wannan? Haka kikaga 'yar uwarki nayi ne? Haba!"
Tashi tayi ta fita tana wannan cika tana batsewa ita a dole an 6ata mata rai, shi kuma Faruk tsaki kawai yakeyi har ya kammala shirinsa.
Haka ta koma d'akinta zuciyarta na rad'ad'i ta dubi agogo k'arfe bakwai da minti hud'u 7:04am, Faruk mamaki yake bata kafin suyi aure kamar zai maida ta cikinsa, amma sunayin aure komai ya chanza mata, gashi bata son sanar da Luby halin da take ciki gudun kar ta mata dariya sheyasa ma ta bar abin a ranta.
BAYAN KWANA BIYU
Bayan kwana biyu kuma ta samu Faruk ya lafa mata tunda har yana kwana d'akinta kuma yana kulata, don haka sai ta fara jijji da kanta a gaban Meenah, wai ita nan ta fara samo kansa.
Meenah ta kira Faruk a waya ta tambayesa zataje gida kuma ya barta, don haka ta shirya tsab direba zai aje ta, don yau ma Zarah zataje gida itama, ta fito parlor nan ta iske Jidda nata faman shan kankana duk ta 6ata wurin, Jidda badai k'azanta ba.
Jidda ta d'ago ta dube ta a shek'e ta ta6e baki sannan tace
"Fita zakiyi ne?"
Meenah tace
"Gida zanje."
Jidda ta bushe da dariya sannan ta dubi Meenah tace
"Haba Malama ke dai fad'i gaskiya, ashe duk k'aryar banza ce kikace kissa tafi magani, tunda gashi zaki fita neman maganin kema? Sai dai kin makaro don kinga yanzu Faruk ya k'ara dawowa hannuna kuma, kuma kisani na riga nayi miki nisa sannan a sannu zan tantance miki da magani da kissa wane yafi tasiri, kuma yanzu kika soma ganin chanji don nayi alk'awarin sai kin bar gidannan kika k'aryata ni, to muje dai zuwa, don haka kema kinbi sahu ay sai mu goga ni da ke."
Meenah tayi murmushin da ya k'ara bayyanar da kyawunta tace
"Ko shakka babu ni na fad'a miki kissa tafi magani tasiri kuma zaki gani, babu boka babu Malami, nayi alk'awarin nuna miki tasirin da kissa take da shi, ki fara k'irga daga yanzu na baki kwana bakwai kima fara lissafi tun daga yanzu, sannan banga ta yadda kina k'azanta zaki iya zama da miji lafiya ba ko wannan kad'ai ya isheki, ni na tafi sai na dawo."
Tasa kai ta bar gidan, Jidda ta sake bushewa da dariya tana wani huro chewing-gum d'in da ke bakinta tayi k'wai tace
"Da sannu dai zan ci ubanki sai kin gwammace kid'a da karatu."
****
Gaba d'aya Meenah ta dage da addu'a ba dare ba rana, sannan ga extra kula tana masa da kuma kaucewa duk wata hanya da zata sa su samu sa6ani, lalla6a sa takeyi kamar k'wai, shiyasa ma take ganin chanji sosai.
Yau da rana abinda yake so tayi masa wato waina da miya, ta masa zo6o mai dad'i da kunun aya tayi masa tasani sarai yafison abubuwan gargajiya akan tarkacennan. Yana cikin cin abincin ne Jidda ta shigo ta wani kashe d'ankwalin ture kaga tsiya tana taunar chewing-gum, da sauri ta janye plate d'in tana ma Jidda wani irin kallo. Tace
"Baby ban yarda da abincinnan ba, ka daina ci kazo na had'a maka wani."
Meenah ta mik'e tace
"Sai dai ki jira zuwan ranarki."
Faruk yace
"Kinga Jidda don Allah ki wuce ki bamu wuri banason tashin hankali."
Cike da mamaki ta kalle shi tana kad'e kai tace
"A gaskiya bazakaci abinnan ba, saboda sam ban aminta dashi ba."

AUREN FANSA 37

🌹37 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
A zuciye ta shige ko gabanta bata gani sosai, tana shiga suka d'ago suka dube ta sai sukayi ido hud'u da Faruk, wani tsananta ya sake dira a zuciyansa ga wani zafi yana ji a k'irjinsa, yanzu a yadda yakeji baya jin son wata 'ya mace a duniya in ba Meenah ba, ya kalli inda Jiddar ke tsaye da rik'ak'en k'ugu tana kad'a jiki kamar wata mazari. Wayancewa yayi ya jefo mata tambayar rainin hankali
"Jidda ya gida?"
Ta yamutsa fuska gami da yin fari da ido tace
"Lafiya."
Yayi murmushi kad'an yace
"Kina son wani abu ne? As you can see I am busy here."
Tambayar ta bata haushi sosai ta kuma 6ata mata rai ainun, ta dube shi tace
"Inada buk'atarka ko ka manta matsayinka gareni?"
Yace
"A'a ina sane, kije zanzo muyi maganar."
Ta cika tayi fam tace
"Babu inda zanje, wai shin ya Faruk wane irin aure mukayi? Na k'iyayya ko na soyayya?"
Yace
"Bafa haka bane, nace ki dai je zanzo, idan kuma kina da buk'atar wani abu ki fad'a min."
Tayi shiru tana tunani, ta dubi Meenah da ke tsaye kamar abin bai dame ta ba, sai tayi mamakinta sosai, ta d'auka Meenah macece mai sauk'in kai har ma tayi tunanin zatasa baki a cikin maganar ko don ta taimaka mata, to me hakan ke nufi?
Kawai sai Jidda ta fita da gudu daga d'akin tana dana sanin zuwan da tayi da kuma zubar da class d'inta da take da shi a gaban kishiya da kuma mijin da bai damu da ita ba. Sai dai ta k'udiri gana ma Meenah wuta, har sai ta gane matsayinta a gidan, a shirye take don ganin hakan ta faru kuma sai ta fi kowa farin cikin ganin hawayenta!
Washe gari da safe Meenah na kitchen tana had'a kalacin safe Jidda na la6e tana jiran ta gama don ta san abinda ta shirya mata!
Sai da Meenah ta kammala abincinta soyen dankali ne da sauce d'in k'wai, ta zuba ma Faruk nasa a plate da na kowa sai ta koma d'akinsa don sanar masa ya fito ya ci abinci.
Tana ganin ta shige sai ta fito cikin sand'a ta bud'e abincin Faruk ta zazzaga ma sauce d'in uban yaji sannan ta zazzaga ma dankalin gishiri mai yawa. Tafiya taji ya sanya ta koma d'akinta a guje tana dariyar mugunta don yau zatayi kallon fad'an da Faruk zaiyi ma Meenah. Sai murna takeyi.
Meenah ta shigo d'akinta ta kalle ta tace
"Ki fito kici abinci ko."
Tayi 'yar dariya tace
"Yanzu kuwa."
Da d'an tsalle tsalle ta fito daga d'akin sannan kuma ta nutsu tabi bayan Meenah.
Kowa ya nutsu kan dinning zasu fara cin abinci, Faruk ne zai fara cin abinci har ya fara d'ebo dankalin kawai kwatsam Meenah ta lura da d'igen d'igen yaji a gefen plate d'insa sannan ga abincin ya chanza kala ya zama jawur, take ta fara tunanin yadda akayi hakan ta faru, sai ta kai dubanta ga Jidda yanayinta kad'ai ya isa ya tabbatar ba wanda ya aikatan hakan sai ita.
Cikin dabara ta kwa6ar da lemon da ke cikin cup a gaban faruk, hakan ya dakatar da shi daga cin abincin da zaiyi wanda saura k'iris ya kai bakinsa.
"Subhanalillah garin yaya hakan ta faru?"
Meenah ta mik'e da sauri tana cewa
"Kayi hak'uri wallahi ban lura ba, bari na goge."
Cikin dabara ta janye abincin Faruk ta matsar kusa da abincin Jidda ta shiga kitchen ta d'auko tsumma ta soma gogewa, ta faki idon Jidda ta sauya abincin dana Faruk sai ta tura na Jidda a gaban Faruk da sauri.
Bayan ta gama ta dawo ta zauna tace
"Sorry please, kaci abincin mana."
Yace
"Ay da kin bari sai da aka gama kika goge."
Tace
"Hakan yayi ay kaga yanzu sai aci abincin cikin kwanciyar hankali."
Ya d'ebi abincin ya kai bakinsa, Jidda nata kallonsa tana dariyar mugunta sai dai me? Bata ga komai ba sa6anin abinda tayi tsammani, ta shiga rud'ani, ta kalli plate d'inta sai taga na Faruk ne aka chanza mata, ta kai dubanta ga Meenah taga tana mata kallon irin ya kika ga nayi k'ok'ari ko?
Meenah ta k'ura mata ido tana murmushi, Faruk ya d'ago ya dubi Jidda yace
"Ya naga bakya cin abincin ne? Kici mana yayi dad'i."
Meenah tayi murmushin mugunta tace
"Eh kici abinci Jidda, yayi dad'i sosai."
Ta fad'i haka har yanzu bata bar murmushin ba, ba yadda ta iya haka ta d'ebo ta kai spoon a bakinta, take taji wani irin yaji da gishiri ya had'an mata, ta dinga taunawa da k'yar tana hawaye tana gogewa don kar a gane.
Faruk ya kammala cin abincinsa ya mik'e yana fad'in
"Zan tafi aiki, sai na dawo."
Meenah tayi murmushi tace
"Sai ka dawo, amma bari na gyara maka zaman rigarka."
Yayi murmushi yace
"To."
Ta gyara masa sannan ta fita raka sa bakin mota, suna fita Jidda tayi toilet da gudu tana faman tari da kakarin amai, sai da ta d'auki lokaci mai tsawo tana wanke bakinta sannan ta fito tana faman goge bakinta da har yanzu bai bar mata yaji ba.
Kaci6us tayi da Meenah a bakin k'ofa ta hard'e hannayenta duka biyun tana murmushi. Ganinta yasa ta d'an dafa ta tace
"Meyafaru?"
Jidda ta kwa6e mata hannu cike da masifa tace
"Muguwa! Azzaluma kawai."
Dariya ta su6uce mata tace
"Muguntar me nayi? Sannan kuma zalunci me nayi?"
Jidda ta dalla mata harara sannan tace
"Wallahi kin bani mamaki Meenah, nayi tunanin ke macece mai sauk'in kai ashe ba haka bane? Ashe haka kike?"
Meenah ta dawo tana fuskantarta ido cikin ido da hannayenta a hard'e sannan tace
"K'warai ina da sauk'in kai idan aka bini ta sauk'in kai, sannan kuma ina da wuyar sha'ani idan aka bini bata lalama ba, Jidda kar kiyi tunanin kina ganina kamar bansan abinda nakeyi ba, to da hankalina sannan kallonki nake tar! Nasan ke wacece sannan nasan wane irin zama ya kawo ki, a dah nayi niyyar muyi zaman lafiya dake, amma tunda na gano sirrinki da kuma k'udirinki na son rabani da Faruk na sake taku.
Wallahi baki isa ba, kinyi kad'an kice zaki rabani da Faruk, nasani ta yadda kika k'waci soyayyarsa ta k'arfi da kuma ta magani, anma kisani duk abinda aka d'ora shi ba bisa tirba ta gaskiya ba to labari ne."
Jidda ta daka mata tsawa
"Ke Meenah! Yafa isheki haka, shiru shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne, kar ki nemi ki fad'a min magana yadda kikeso fa."
Meenah tace
"Ni ba fad'a zanyi da ke ba, amma kisani zan fad'a zan kuma k'ara fad'a ke baki isa ki rabani da Faruk ba, saboda yana yi min true love ne babu boka babu malami, soyayyarmu had'in Allah ce, kuma banga ta yadda zaki raba abinda Allah ya had'a ba, duk naji conversation d'inku keda k'awarki sannan a shirye nake nayi fighting back don ganin baki rabani da Faruk ba."
Jidda tace
"Haka kika ce?"
Meenah tace
"Haka nace."
Jidda tace
"Shikenan mu zuba, niko bama Faruk ba har gidannan sai na raba ki dashi, ta yadda idan kika fita har abada bazaki dawo ba."
Meenah tace
"In kin dama ki rabani da duniyar nan gaba d'aya bama gidan ba, sannan kisani babu abinda kika isa kiyi min sai abinda Allah yayi min, sannan ina so ki sani k'arya fure take bata 'ya'ya!"
Jidda tace
"Zaki gani."
Meenah tace
"Zanga alkhairi."
Daga haka ta sa kai ta fice zuwa d'akinta, inda ta bar Jidda tsaye kamar gunki in banda cizon yatsa babu abinda takeyi, gaba d'aya idanunta sun sauya daga fari zuwa ja, cikin sanyin jiki ta koma d'akinta tana mai mamakin Meenah da kuma maganganun data fad'a mata a yau.

Friday, 18 August 2017
AUREN FANSA 36
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_
P.M.L
🌹35 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Washe gari aka kai lefen Zarah akwati bakwai da kit, yayinda aka kai ma Jidda akwati takwas da kit.
An fara gudanar da shagalin biki a wadace, sai dai matsalar Jidda d'aya da ta masa maganar kud'i sai sunyi fad'a, sannan idan har suna tare yana nuna mata so da k'auna marar iyaka amma da zarar sun rabu shikenan ko kiranta baiyi sai dai ita ta kirasa. Hankalinta ya fara tashi haka kuma ta soma tunanin ko maganin ya fara dena aiki ne?
Ranar da akeyin event d'in Jidda anyi kwalliya ta gogaggun 'yan matan nan, ta had'u har ta gaji duk da ba wani kyau gareta na azo a gani ba. 'Yan matanta kansu da ka kallesu kaga gagaggun 'yan mata masu ji da kansu, Luby best friend d'in amarya ita nata ashobin ya banbanta da na sauran ya kuma fi tsada da kyau.
Suma kuwa su Zarah na can suna shan tasu hidimar, da yake bazasuyi abubuwa da yawa ba, kuma bikin nasu yafi tsari da kyau.
K'arfe biyar da rabi Faruk ya iso ya kira wayar Jidda, can sai ga ta fito itada k'awayenta su da yawa kamar wata tawaga.
Bayan sun iso aka fara gabatar da events cike da kwanciyar hankalin, Luby ita ta fara bud'e wurin da rawa yadda kasan ba kowa wurin haka take tik'ar rawa ba ko kunya.
An gayyato amarya da ango don taka rawa, shi kam ango kunya ta hana shi rawa sosai ba, ita kuwa amarya bako kunya sai wani rausaya takeyi kamar ba amarya ba. Faruk sai yanzu yake k'ara gane halin Jidda, bai ta6a tunanin haka take ba. Sai yanzu ya fara tunanin aurensu shida Meenah komai cikin tsari haka akayi shi.
K'arfe sha d'aya aka tashi taron, ya ajiye Jidda gida shima ya nufi nasa gidan.
Washe gari ya tashi yana ta hidimar d'aurin aure. K'arfe biyu daidai dubban mutane suka shaida auren Jidda da Faruk sai Zarah da Khaleel.
Dad'i Meenah takeji Zarah kusa da su za'a kawo ta, bayan an gama aka zarce 'yar walima da Faruk ya had'a masu.
****
Tana zaune kan gado taji ana maganar an d'aura aure, haba kanta ya k'ara girma ji take kamar a mafarki, mutumin da take ganin shine class d'inta yau ta malleke shi a matsayin miji, wani murmushi tayi tare da lumshe idanu, Luby ta daka mata duka a baya tace
"Banza keda wa kike murmushi ke kad'ai?"
Ta dube ta tace
"Ina tunani gami da yin mamaki wai yau nice na zama matar ya Faruk ya zama mallakina fa kenan?"
Luby tace
"Ke ni ba wannan ba, kinsan mutumin nan yana da mata, kuma kinsan yadda yake k'aunar ta kawai suddabarunki ne yake aiki, baki gudun maganin ya bar aiki mu shiga uku mu lalace? Ke nifa na fara ji miki tsoro kar ya wulak'anta ki, sannan yasan babu, baki gudun labari yasha banbam?"
Ras ras! Gabanta ya yanke ya fad'i tace
"Haka ne fa, ko da yake ay kin min tanadi mai kyau kar kiji komai."
Luby tace
"Keni sheyasa nake son auren yaro wanda baisan dawon garin ba, amma masu mata ay sun san komai."
Haka aka cigaba da shagalin biki, jikin Jidda yayi mugun sanyi saboda gudun abinda zaije ya dawo tsakaninta da angonta.
K'arfe tara da rabi motoci suka soma layi a k'ofar gidan su amarya, bayan fad'a da nasihohi daga Mama da Dada har Faruk sai da yasha fad'a sosai da nasiha.
Uwar gida kan gida Meenah tana zaune a d'akinta ta ci ado tsayawa fad'ar kwalliyarta ma 6ata baki ne. Gud'a ta matan da suka rako amarya itace ta fara yo sallama, Meenah ta danne kishinta sosai ta k'ak'alo murmushin dole, amarya tana rik'e a hannun wata mata.
Kansu tsaye d'akin amarya suka nufa, 'yan kawo amarya, k'ofa ce kawai zatayi linking d'inka zuwa d'ayan 6angaren na sashen Jidda.
Masu kawo amarya suka shiga zagaye gidan don kashe kwarkwartar ido. Suka gama kallon komai sukayi niyyar tafiya gida.
Washe gari akayi walima k'arfe biyar na yamma Hajiya Lami ta rik'o hannun Jidda ta nufi parlon Meenah, sukayi sallama Meenah ta amsa. Hajiya Lami ta ce
"To ga amarya nan don Allah ku had'a kanku ku zauna lafiya, yanzu an bar haukan kishin nan zaman lafiya shi kowa ke buk'ata.
Tayi murmushi
"To Allah ya taya mu rik'o."
Suka tashi suka maida amarya d'akinta bayan iyayen sun kama gabansu, d'akin ya rage daga amarya sai 'yan matanta wad'anda ke zaman jiran ango.
Luby tace
"Kar fa kiganta kamar mutuniyar kirki ki raga mata, idan tace miki kul ki ce mata cas cas! Kinji na fad'a miki."
Nan sukayi ta zuga ta har akayi isha'i.
K'arfe takwas, tara, goma, shiru ba ango ba alamunshi, har dai sha d'aya ta wuce
Luby tace
"Nidai zan tafi gida na gaji da jiran ango."
Haka suka tarkata suka tafi, Sai dai ta dinga binsu da ido don batada bakin magana da kuma tana son jin dalilin rashin zuwan ango duk da tanadin da tayi masa, haushi kamar zai kashe ta.
"Kar dai yana wurin waccan tsinanniyar?"
Gabanta ya fad'i, ta hau sak'e sak'e, tayi ta kiransa yana rejecting, daga k'arshe ya tura mata sak'o kamar haka:
"Kiyi hak'uri ki bar kirana yau bazan shigo wurinki ba."
Ta rud'e ta gigice gashi maganin idan aka wuce yau shikenan ya kare!
Ta hau salati tana cigaba da kiransa amma ina sai ma ta kira taji ta a kashe.
Safa da marwa takeyi daga k'ofa zuwa gado, tana tunainin mafita a gareta, don akwai had'ari muddin ango baizo gareta ba a daren yau ba!

Tuesday, 8 August 2017
AUREN FANSA 35

AUREN FANSA 34

🌹34 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Meenah kuwa duk wani abu bazata fasa yi masa ba, har girki sai tayi koda kuwa bazaici ba, ga tana k'ok'ari wajen ganin ta kai zuciyarta nesa don gudun fitina, sauk'inta ma yanzu shiryen-shiryen bikin Zarah ya fara kankama hakan yasa ta rage yawan shiga damuwa, don kuwa tana gida kuma bata cika dawowa ba sai yamma.
Karo na farko da ta fara shiga gidan Aneesha tunda sukayi aure, bayan ta shirya cikin green d'in material d'inkin doguwar riga sai ta gyala gyale marar kauri sosai. Da sallama da shiga gidan, Aneesah na kitchen tana fama da girki taji sallama ta lek'o, murmushi tayi tace
"Bismillah shigo."
Bayan ta zauna Aneesah ta shiga kawo mata lemo da kayan motsa baki, yau duk kunya ta kama Aneesah ganin itace k'arama kuma ko sau d'aya bata shiga gidan ba. Meenah tayi murmushi tace
"Baki gane ni ba ko?"
Aneesah tace
"Nagane ki mana, matar ya Faruk ce nasanki."
Meenah tace
"Allah sarki ya gida?"
Tace
"Lafiya lau."
Shiru ya biyo ba, na 'yan mintina sai suka kafa ma tv ido ana wani film. Meenah ta katse shirun ta hanyar mik'a mata kati
"Daman Iv na kawo maki na bikin sister d'ina."
Aneesah tayi murmushi tace
"Allah sarki, Allah yasa alkhairi yasa munada rabon gani."
Tace
"Amin ni zan koma."
Aneesah tace
"Haba tun yanzu? Na d'auka sai kin ci abinci tukunna."
Meenah tace
"Kai haba, bamuda nisa ta yaya zan cinye ma amarya girkin angonta?"
Aneesah tayi murmushi cike da kunya tace
"Kai a'a wallahi ba haka bane."
Meenah tayi dariya tace
"Kedai wasa nake miki, idan na dawo next time zanci insha Allah."
Aneesah tace
"To ina zuwa."
Ta mik'e ta shiga ciki, can ta dawo hannunta d'auke da leda tana murmushi tace
"To ga wannan."
Meenah tace
"La harda wahala haka?"
Aneesah tace
"Ba wata wahala wallahi."
Meenah tace
"To nagode ni zan tafi."
Aneesah tace
"Nima zan shigo, ay kina WhatsApp ko?"
Tace
"Eh inayi."
Aneesah tace
"Zamu rik'a gaisawa insha Allah, nagode sosai wallahi."
Meenah tace
"Babu komai wallahi."
Sukayi bankwana ta tafi, tunda Meenah ta tafi Aneesah ke raya kyawunta da kirkinta, sai taji haushin kanta da meyasa bata ta6a shiga sun gaisa ba, amma ta k'udiri a ranta zasu fara zumunci daga yau.
****
Meenah sun soma lectures, yanzu damuwarta ta ragu sosai, kuma tayi sa'a yana bata mota idan zata tafi.
Ranar litinin da daddare sai ga Faruk ya shigo da akwatina guda biyu, tunda Meenah ta ganshi tasan na menene, don haka bata nuna damuwarta ba ko kad'an, sai ma fatan alkhairi da tayi masa.
Hakan ba k'aramin mamaki ta basa ba, kuma sai ta bashi tausayi, nan ta bubbud'e akwatina ta gani bayan ta gama ta tashi ta shiga ciki. Ya dad'e zaune ranar farko da ya ji auren ya fita a ranshi kuma.
Mik'ewa yayi cikin sanyin jiki ya bita ciki, tana kwance a d'aki tayi ruf da ciki idanunta a lumshe, hakan ya k'ara bayyanar da zara zaran eye lashes nata. Ya dad'e tsaye yana kallonta kafin ya tako a hankali yatsaya yana k'are mata kallo. Sanye take da 'yar k'aramar vest pink color sai tasa pink dogon wando, harta ribbon d'in kanta pink ne, daga gani ba bacci take ba amma kuma tak'i bud'e idanunta.
"Meenah..."
Ta bud'e idanunta a hankali ta sauke bisa fuskarsa da yake kallonta kafin ta amsa da
"Na'am."
Sai kuma ya rasa abin cewa, ya sosa kai yace
"Dama zuwa nayi naji ko kina lafiya."
A ranta tace
"Sabon salo sai kace damuwa yayi da ni bare kuma lafiyata."
A fili kuwa cewa tayi
"Lafiya lau."
Shi yadda take sharesa d'innan yaji ba dad'i, yayi missing kula da shi da takeyi, amma yanzu ko kallonsa bata son yi, magana ma da k'yar take amsa masa. Da yanzu ta tambeyesa ko yana buk'atar wani abu, amma yanzu ta daina.
"Ko kana buk'atar wani abu ne?"
Yayi sauri yace
"A'a, sai da safe."
Tace
"Allah ya kaimu."
Ta rufe idanunta alamun bacci, ya dad'e tsaye yana kallonta kafin ya fita daga d'akin a sanyaye.
Yana shiga d'akinsa ya iske miss calls ba iyaka daga Jidda, kiranta yayi bugu d'aya ta d'auka.
"Haba my dear ina ka shiga inata kiranka?"
Yace
"Sorry na shiga wanka ne."
Yace
"Ok daman kud'in da zan siya anko ne na 'yan mata baka bada ba..."
Yace
"Kud'in anko kuma?"
Tace
"Eh da kud'in k'unshi."
Yace
"To fah har nawa?"
Tace
"Gaba d'aya dubu 500 ne!"
Yace
"What? Dubu 500? Gaskiyar magana ko banida su, bazan iya baki dubu 500 ba."
Tace
"Haba mana my dear, wai nan fa na maka sauk'i."
Yace
"Dubu 100 zan baki, idan baki so good and fine."
Tace
"Wai wannan fad'an na menene daga tambayarka kud'i?"
Yace
"Jiya jiya kika tambayeni dubu 200 na baki, shekaranjiya dubi 50, yanzu kuma dubu 500, to banida su."
"Don Allah kayi hak'uri ka bani, daga yau bazan k'ara tambayarka wasu kud'in ba."
A fusace yace
"Ke kar ki raina min hankali fa! Na riga nace bazan baki ba, don haka sai da safe."
K'it ya kashe wayar, cike da jin haushinta, gaba d'aya haushinta yakeji. Yau ko baccin kirki ya kasa, haka yasa ya mik'e ya lek'a d'akin Meenah tana kwance tana bacci peacefully, ta masa kyau sosai, sai dai dole ya koma d'akinsa ya kwanta amma ina ya kasa bacci, sai gabansa dake ta fad'uwa ya rasa dalili.
Washe gari sai ga 'yan jere, nan sukayi ta hidimarsu ita kuma Meenah ko fitowa ma batayi ba, tana d'aki tana jinsu suna ta aikin jerensu, har dare suna nan basu gama ba, har washe gari sai da suka dawo da safe suka k'arasa wanda basu idasa ba.
Itama Meenah jeren Zarah suka tafi the next day, hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba.
Biki nata matsowa yau saura kwana biyu a d'aura aure....

Monday, 7 August 2017
AUREN FANSA 33
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_
P.M.L
Kuyi sorry Fans muna fama da matsalar rashin wuta🤗
🌹33 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bayan ta kammala abincin suka ci sai ta zarce zuwa gida don kai ta, Bilki bata zargi komai ba sai ma murnar samun mai taya ta aiki dama Zarah keyi to zata fara zuwa makaranta ga bikinta da za'a sanya.
Nan aka gabatar mata da ayyukan da zata rik'a yi tun daga su shara, wanki, wanke-wanke, girki da sauransu.
Kafin ta tafi sai da shiga wurin Baba da ke zaune parlor yana kallon news, ganin Meenah ta shigo ya sanya yayi murmushi, ya bita da kallon k'urilla a lokacin da take zama kan carpet.
"Baba ina wuni?"
Ya gyara zamansa yana kallonta yace
"Lafiya lau Amina, ya gida ya kuma mai gidan naki?"
Tace
"Duk lafiya lau Baba yana wurin aiki."
Yace
"Madallah, naji zancen zai k'ara aure hakane?"
Ta had'iye miyau mai d'aci tace
"Hakane Baba."
Yace
"Kinsan komai muk'addari ne daga Allah Amina, kar ki d'aga hankalinki ki jure, ki zamo mace mai hak'uri da biyayya kinji? Allah ya za6a maku mafi alkhairi, ya bada zaman lafiya."
Tace
"Amin Baba nagode, daman zan wuce gida yanzu."
Yace
"To ki gaida mijin naki, da fatan baki buk'atar wani abu?"
Tace
"A'a Baba."
Yace
"Kuma zaku tafi jami'ah, ku kula sosai, karatu kukaje yi shi zakuyi Allah ya taimaka."
Tace
"Insha Allah Baba, amin."
Sukayi sallama ta tafi gida.
K'arfe goma saura ya shigo gidan, tana zaune tana karatun alk'ur'ani, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana sauraron muryarta tana karanta suratul Mujadala, yayi tsaye shi bai shigo ba haka ma shi bai fita ba, take kuma ya tsinci kansa cikin nutsuwa don karatun yana masa dad'i.
Sai data kai aya sannan ya shigo, ganinshi ya sanya tayi saurin mik'ewa ta isa garesa gami da amsar brief case d'insa, tayi murmushin da bai kai zuci ba tace
"Sannu da zuwa."
"Yawwa." Kawai yace ya wuce zuwa ciki, ranta ya sosu ta dai daure ta bishi ciki a lokacin data shiga taji alamun watsa ruwa. Sai kawai ta fito ta zauna parlor tana kallo abinta.
Shiru bai fito ba har kusan sha d'aya ta wuce, ga ita kuma tana kunyar binshi d'aki yanzu kada ya fassara ta, sai kawai ta mik'e ta tattara abincin tasa fridge ta wuce d'akinta.
Gaba d'aya ta kasa bacci sai uban tunani, ko a mafarki akace mata Faruk zai mata haka bazata yarda ba. Ganin hakan bashi ne mafita ba ya zama tilas ta kai kukanta ga Allah don shine zai share mata, toilet ta fad'a ta d'auro alwalla ta fara sallah tana kai kukanta ga Allah.
Tana wurin har akayi sallar asuba, hakan yasa tana gama sallah kanta ya fara yi mata barazanar ciwo, ta lalla6a ta kwanta ba'a d'au lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita.
Cikin baccin ne taji kamar ana ta 6arar da abubuwa, a gigice ta farka tana salati, duba lokaci tayi k'arfe 11:41am lallai tasha bacci.
Hijabinta ta d'auko ta sauko daga gadon, tana lek'owa taga mutane maza suna ta aiki a gidan, gabanta ya yanke ya fad'i, maganar Faruk ta dawo mata a cikin kanta.
"Gobe za'a fara gyaran gida, za'a k'ara fasa d'aki da parlor da kitchen daga can baya."
Dafe kanta tayi da ke juya mata sannan ta fara bin bango ji take kamar zuciyarta zata fad'o k'asa.
Note ta gani a bisa drawer d'inta hannunta na kyarma ta d'auko ta warware ta ta soma karantawa...
"Na tafi office, kamar jiya yau ma azumi nakeyi kar ki wahalar da kanki yin wani girki sai dare zan dawo, idan masu aikin nan sun gama da na yau ki shiga d'akina ki d'auko 5k ki basu zan kirasu na masu bayani."
Wani k'ululun bak'in ciki ne ya tokare mata mak'oshi, ta daure tayi ta maza ta maida note d'in ta ajiye a inda ta d'auka, ta rasa dalilinsa na shan ruwa a waje, at least ko bai dawo da wuri ba ay ya kamata ya ci abincin data girka masa komai dare, amma ta lura kamar baya son cin abincin ne gaba d'aya a nan.
Da k'yar ta sha ruwan tea ta koma d'aki ta kwanta, k'arar aikin gidan ne ya ishe ta shi yasanya ta kasa baccin kirki.
Allah ya taimake ta Zarah tazo zasuje makaranta registration, tayi ta murna ta kirasa don shaida masa amma bai d'aga ba sai kawai ta aika masa da sak'o.
Cikin sa'a kuwa suka kammala komai suka dawo gida, Zarah tsabar haushin gyaran inda kishiyar yayarta zata zauna yasa ko gidan bata iya shiga, daga waje sukayi bankwana ta tafi gida.
Yanda ya umarce ta hakan tayi don kuwa k'arfe shiddan yamma suka gama, ta shiga ta d'auko masu kud'in ta basu suka tafi.
Haka kullum sai sun zo da safe su gama k'arfe shidda, da yake ana sakin kud'i sai gashi ginin har ya mik'a sosai.
A zamantakewar auren Meenah kuwa babu abinda ya chanza gaba d'aya Faruk ya chanza mata kamar bashi ba, bai damu da ita ba bare cinta, shanta da kuma lafiyarta.
Abincinta ma baya ci ko tayi masa, tun yana bata excuse har ya fara fitowa 6aro 6aro yana ce mata bazai ci ba. Ga abu kad'an fad'a da masifa, nan da nan sai ya hau fad'a ba dalili.
Nan kuwa yana can ya tare wurin Jidda, wani lokacin can yake da anyi sallar isha'i har goman dare. Kuma komai ta bashi ci yakeyi, gaba d'aya ya sussuce ya rikice.
Hakan yasa aka sanya bikin sati uku masu zuwa, don ya kusa kammala aikin gidansa saura kad'an ya rage, haka aka tattara aka sanya bikin aka had'a dana su Zarah da Nabeel.
Shi kuma ya cigaba da had'a lefe da kuma akwati biyu na kayan fad'ar kishiya da zai kai ma Meenah.

Thursday, 3 August 2017
AUREN FANSA 32
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
*_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_*
P.M.L
Alhamdulillah duk wani masoyina da ya damu dani nagode sosai Allah ya saka da alkhairi! Naga sak'konnin gaisuwarku na kuma gode da kulawa Allah ya bar zumunci ameen. 😘
Haka masu kirana da turo man sak'ko don jin lafiyata kuma nagode sosai Allah ya bar zumunci.😘😍
Wannan page d'in naku ne members na AUREN FANSA FANS, thank you so much for everything!😍🌹
🌹32 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Duka duka batafi minti ashirin ba ta dawo hannunta d'auke da tray mai d'auke da lemo a cikin glass cup da aka riga aka zuba, gefe kuma kwalin lemon 5alive ne. Tafe take tana faman smiling tana kashe ido, tafiyar ta kuwa kamar tana tsoron taka k'asa, fuskarta cike da fara'a da nishad'i kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da hakan.
Da isowarta sai ta rissuna a hankali ta ajiye tire d'in, sannan ta dawo ta zauna a kusa dashi tace
"Ya Faruk ga ruwa kasha."
Kallonta yake bako kyaftawa zuciyarsa tana ayyana masa abubuwa da dama game da ita.
A hankali ta mik'o masa lemo tace
"Bismillah."
Bai iya mata musu yakeji koda kuwa yaso hakan, don haka sai ya kar6a ya fara kur6a kad'an kad'an, kuma a hakan suna ta6a fira.
"Kamar yadda na fad'a ma Dada cewar nazo mu daidaita kanmu to kema haka zan sanar da ke, don haka me zakice game da hakan? Duk da kuwa na dad'e da sanin sirrin da ke ranki shiru kawai nayi, amma duk da haka ina so naji ta bakinki, kin shirya aure na ko kuwa?"
A cikin ranta mamaki take yadda tashi d'aya ta sato zuciyarsa a tafin hannunta! Lallai indai kuwa hakane komai zaizo mata da sauk'i tunda har ya kamu da wuri haka. A fili kuwa murmushi tayi tace
"To yadda za'ayi ka samu Dada da maganar don maganar tana hannun manya, amma tambayar amsar ka itace, eh na yarda kuma na shirya aurenka ya Faruk."
Yayi murmushi
"Kina so na kenan?"
Ta gyad'a kai cike da farin ciki, yayi murmushi yace
"To ba matsala ay, kuma gaskiya bana son aja lokaci mai tsawo, in zan samu ne ma nan da sati biyu yayi min, amma da yake zanyi gyaran inda zaki zauna ana iya sashi nan da wata d'aya."
Tace
"To duk yadda kace ni yayi min."
Da zai tafi ya fiddo kud'i masu tsoka ya bata, yace
"Kya sa kati da wannan, sai munyi waya."
Ta kar6a tace
"Nagode."
Sukayi bankwana ta shige d'aki, tana zuwa ta kira Luby, ta kwashe labarin komai ta fad'a mata, ta sanar mata ya bata kud'i masu tsoka.
Luby tayi shewa
"Duniya sabuwa, kinga a nan kenan kin harbi tsuntsu d'aya da igiya biyu."
Jidda tayi dariya tace
"A gaskiya nagode Luby bansan ya zanyi ba idan baki ba, kin taimaka min sosai."
Luby ta k'yalk'yale da dariya tace
"Somin ta6i ne ay, ya Faruk sai ya raina kansa, sai ya dawo kamar zai maki sujjada"
Jidda taji dad'i tace
"Nagode 'yar uwa sai munyi magana gobe."
Sukayi sallama ta kwanta rigingine tana tunanin ranar da zata mallaki Faruk a matsayin mijinta.
Koda ya koma gida bai iske Meenah a parlor ba, kuma sai yaji bai wani damu ba, d'akinsa ya wuce kansa tsaye yayi wanka ya kimtsa cikin kayan bacci ya hau gado ya kwanta, sam ya kasa bacci sai tunanin Jidda da ya addabe shi, wayarsa ya d'auko ya kira ta amma har ta tsinke ba'a d'auka ba, ya sake kira a karo na biyu nan ma sai da ta kusa tsinkewa ta d'auka.
"Hello ya Faruk..."
Ya lumshe idanu kafin ya bud'e, sannan yaja ajiyar zuciya yace
"Kar dai har kinyi bacci na tashe ki?"
Tayi murmushi
"Eh na fara sama sama dai, da fatan ka koma gida lafiya?"
Yace
"Lafiya lau, gani nan ma har nayi shirin bacci."
Ta mik'e da sauri daga kwance da take tace
"La ya Faruk kuma shine ka kira ni? Idan amaryarka ta farka taga kana waya dani fa?"
Yayi murmushi
"Kar ki damu bazata farka ba, besides tama san da maganarmu so kar ki damu."
Tayi wani shu'umin murmushi tace
"To shikenan ya Faruk sai da safe."
Ya 6ata rai
"Kar dai har mun gama firar?"
Tace
"Eh."
Yace
"Gashi ban gaji da jin muryarki ba."
Tayi dariya
"La ya Faruk, nima haka, amma bacci nakeji yanzu.
Yace
"To shikenan sai da safe."
Tace
"Allah ya kaimu love you."
K'itt! Ta kashe bata jira ya bata amsa ba. Ya sagale wayar a kunnensa ya kasa cirewa. Haka ya kwanta da tunaninta har garin Allah ya waye.
Kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da tana cikin matsananciyar damuwa, banda idanunta da suka rikid'e suka koma ja alamar rashin bacci da kuma kukan da tayi a daren jiya.
Sanye take da wani navy-blue atamfa d'inkin riga da skirt sai wani yalolon gyale data gyala a saman kanta. Kwata kwata yau batada kumari haka take jinta wani iri tunda ta tashi batada walwala.
Tsaye take a kitchen tana faman had'a masa kalaci mai rai da lafiya. Sai da ta kammala komai ta jera saman dinning sai ta koma ta kimtsa kitchen d'in.
Tana tsakar yi ne taji alamun tafiya, hakan ya dakatar da ita gami da fitowa daga kitchen d'in. Sanye yake da uniform d'in aikinsa wato komai in black tun daga sama har k'asa, ta k'ara dubansa a karo na biyu gami da yin murmushi. Maimakon ya maida mata murtani sai ya fara k'ok'arin gyara zaman belt d'in wandonsa. Hakan ba k'aramin k'ona ranta yayi ba gami da bata mamaki tsantsa.
Ta daure tare da had'iye 6acin ranta ta k'araso inda yake tsaye tace
"Ina kwana?"
Bai motsa ba ya amsa
"Lafiya."
Ta dai daure tace
"Naga kana shirin fita baka karya ba."
Sai a sannan ya d'ago yana dubanta amma fuskarsa babu annuri ko kad'an kamar wanda aka aiko ma da sak'on mutuwa. Yace
"Azumi nakeyi."
Tace
"To... wane iri naga yau ba Monday ba kuma ba Thursday ba?"
Ya k'ule da tambayarta sai ya kalle ta kad'an yace
"Dole sai wannan ranakun Allah ya halasta azumi? Mutum yana iya yi ko yaushe don samun lada."
Ta k'ak'alo murmushi tace
"Haka ne kam, Allah ya bada lada."
Yace
"Amin, ni zan wuce sai dare zan dawo yau."
Tace
"To a ina zaka sha ruwa?"
Yace
"Zan siya abinci, don yau aikin da ke gabana da yawa da k'yar zan samu dawowa wannan lokacin yau."
Tace
"To."
Har yayi hanyar waje sai kuma ya dakata tare da karkatowa kad'an yace
"Gobe za'a fara gyaran gida, za'a k'ara fasa d'aki da parlor da kitchen daga can baya."
Bata tanka ba don ta gane inda maganar ta dosa, shi kuwa gogan daga haka kawai sai yasa kai ya fice don shi ko ganinta bai son yi yau, Jidda kawai yake tunani.
Yana fita ta fashe da kuka mai tsanani don ko maganar auren da ya tarkato bata d'aga mata hankali irin yau da taga yadda ya chanza mata.
***
Yana office yana shirin fita don an kirasa wai akwai wani kisa da akayi a wani gida, zasu je bincike. Yana tsakar tattara mahimman abubuwan da zai buk'ata aka shigo da sallama. Ya amsa tare da bada izinin shigowa, sai dai a yadda ya tsaya yana kallonta cike da mamakin sauyawar da tayi kamar ba Hajir ba, gaba d'aya ta zama bak'auya sak!
Sanye take da wani tsanwar atamfa ta k'ok'e sosai, d'inkin k'auyawa riga da skirt, sai d'ankwalin daban, fuskarta harda d'ige d'igen kwalliya. Hakan ba k'aramin dariya ta basa ba. Sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata yana kallonta yana tafa hannu.
"Bravo! Lallai kinyi k'okari Hajir, aww na manta Atika ashe. Aikinki yayi kyau, are you ready?"
Tace
"Yes sir."
Yace
"Good, d'auko kayanki inada wani aikin da zamuje muyi yanzu, amma ina iya kaiki gidana da zarar na dawo sai mu kaiki gidan da zaki zauna."
Tace
"Haka ma yayi sir."
Kayanta ta d'auko dake cikin ghana most go tabi bayansa.
Da sallama suka shiga, tana zaune a parlor tana karatun wani novel, ganin Faruk ya shigo yasa ta dakata gami da amsa sallamar tasa. Tare suka shigo da Hajir, bayan sun zauna Faruk ya soma magana.
"Meenah wannan 'yar aikin da kika ce a samo miki ce, sunanta Atika, yanzu ina sauri zan koma aiki, so zan barta nan sai na dawo sai mu kaita ko?"
Taji dad'i sosai suka gaisa da Hajir a mutunce sannan tace masa.
"Ay naji kace yau zakayi dare a wurin aiki, why not ka bari na kaita da kaina ko ya ka gani?"
Ya mak'e kafad'a alamun oho yace
"Hakane tunda kin iya mota ki d'auki d'aya daga cikin nawa sai ki kaita, ni zan koma."
Ta masa a dawo lafiya ya fice. Meenah ta kalli Hajir tace
"Don Allah ki tashi daga k'asa ki koma kan kujera."
Hajir ta koma kan kujera tana ta faman murmushi. Meenah tayi murmushi tace
"Ko kefa, bari na k'arasa abincin rana kici sai na kaiki ko?"
Hajir tace
"To nagode."
Meenah tayi murmushi ta mik'e ta shiga kitchen.

Subscribe to:
Posts (Atom)