Thursday, 30 March 2017

KHALEEL Page 71&72

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻71&72✍🏻✍🏻


Washe gari Hanifah batada paper tana zaune palo ta baje guava tana ci ta jiyo sallama, da sauri ta tattara wurin ta mik'e ta nufi bakin k'ofa gami da bud'ewa, da mamaki tace
"Rufaida? Yau kece a gidannamu?".
Rufaida tana murmushi tace
"Wallahi kuwa".
Hanifah tace
"Bismillah shigo mana" ta shigo Hanifah ta bata izinin zama sannan ta wuce kitchen don nemo mata abin motsa baki, bayan Hanifah ta dawo ne suka soma gaisawa, Hanifah tace
"Ya exams?".
Rufaida tace
"Alhamdulillah, ya gida?".
Hanifah tace
"Lafiya k'alau, ashe zaki gane nan gidan?"
Rufaida tace
"Kin manta mun ta6a zuwa nida Humaira?"
Hanifah tace
"Haka ne fa na tuna".
Shiru ya biyo baya tsakani, Rufaida tunanin hanyar da zata fad'a mata wannan matsala takeyi, can tace
"Hanifah wata magana nazo muyi mai mahimmanci, amma kafin nan ina so ki kwantar da hankalinki ki saurare ni kuma ki fahimce ni, sannan kar kiyi saurin tada hankali".
Hanifah tayi shiru amma sai data samu kanta da fad'uwar gaba, ta dai daure tace
"Insha Allah komai zaki fad'a zan fahimce ki"
Rufaida tayi murmushi tace
"Yauwa, akwai wani al'amari mai rikitarwa dasa mutum shiga rud'ani, sannan mai matuk'ar mamaki. Abinda yasa kika ga zan fad'a miki wannan magana saboda nima mace ce y'ar uwarki, bazanso abinda yake faruwa dake nima ya faru dani ba"
Cikin rashin fahimta Hanifah tace
"Bangane abinda kike nufi ba, ki warware min yadda zan fahimta".
Rufaida ta dafa ta tana murmushi
"Kar ki damu yanzu zakiji komai insha Allah, wato akan maganar k'awarki ce Humaira"
Hanifah tace
"Humaira kuma? Meyafaru da ita?"
Rufaida tace
"Yadda kika d'auke ta ita ba haka ta d'auke ki ba, wato duk wata matsala ta gidanki tsakaninki da mijinki Humaira ce ke haddasawa, don da k'arfin tuwo so take ta k'wace miki miji...".
Hanifah gabanta yayi mummunan fad'uwa ta dafe k'irji tace
"Humairar?".
Rufaida tace
"Ita fa, kuma kinsan Allah dai ko? Wannan magananar da na fad'a idan har na mata sharri ko k'azafi Allah ya saka mata duniya  da lahira, amma dole ne fa sai kinyi takatsantsan da ita,  idan ba haka ba wata rana kina ji kina gani zata fi k'arfinki, sannan dole ki tashi tsaye da addu'a shine kad'ai mafita".
Hanifah hankali tashe tace
"Indai har maganganun da kika fad'a min gaskiya ne Rufaida, nagode miki kuma insha Allah zanyi a hankali, addu'a kam inayi zan dai k'ara. Sannan da sannu zanyi maganinta insha Allah, sai dai ga tambaya meyasa Humaira ke bibiyar mijina? Meye had'inta dashi?"
"A zahirin gaskiya ni tuntuni na fahimci Humaira muguwa ce, sannan wai ita nan sonsa take, amma kar ki damu zan binciko miki, komai kenan zan neme ki".
Hanifah tace
"Kai nagode sosai wallahi Allah ya bar zumunci"
Rufaida taji dad'in yadda Hanifah tayi reacting don haka sai tace
"Amin Hanifah, kuma Allah ubangiji ya shige mana gaba, duk lokacin da kike buk'atar k'arin bayani ko kuma wani abu ya shige miki duhu, don't hesitate to call me anytime".
Hanifah tace
"Insha Allah i will, nagode sosai"
Rufaida tace
"Bakomai ni zan wuce".
Hanifah tace
"Haba dai tun yanzu? Ki tsaya kici abinci mana"
Rufaida tace
"Wallahi na k'oshi next time dai"
Ba haka Hanifah taso ba, sai kawai tace
"Shikenan tunda kin k'oshi"
A tare suka mik'e inda Hanifah ta raka ta har bakin k'ofa ta juyo ciki zuciyarta na cigaba da sak'e sak'e.
Ko minti 15 batayi da shigowa ba wayarta ta fara ruri, ganin Humaira ce mai kiran taji wani bak'in ciki da haushinta sun mamaye ta, sai dai dole tabi komai a sannu bata so tayi saurin ganowa, sai kawai ta daure sosai tana murmushi tace
"Humaira yane?".
Humaira tace
"Lafiya lau kina gida ne?".
Hanifah tace
"A'a na d'an fita tun d'azu".
Humaira tace
"Da zan shigo, yaushe zaki dawo?"
Hanifah tace
"Sai dare gaskiya".
Humaira tace
"Ayya ba damuwa to".
Sukayi sallama inda Hanifah ta buga tsaki tace
"Munafuka no wonder kad'an kad'an zata ce zatazo ashe da abinda ta taka, ta Allah ba taki ba. Kuma insha Allah sai kin bar min mijina don yafi k'arfinki".


*****

Su Hanifah sun k'are exams d'insu lafiya na first semester inda yanzu sam ta daina bama Humaira fuska tana zuwa gidanta, da tace mata zatazo zata samu reason ta fad'a mata.  A school ko tare suke Hanifah bata cika zuba ba a gabanta, sama sama suke magana.
Sun samu hutu inda Hanifah suke zaune lafiya da Khaleel d'inta yanzu basuda matsala, zamansu har yafi nada dad'i.
Sam Khaleel bai san 6acin ran Hanifansa, musamman yanzu da cikinta ke dad'a girma, basu wasa da appointment d'insu.

Sun gama exams da kwana biyu Khaleel ya d'auke Hanifah suka tafi Abuja, a can d'inma sun sha dad'i da yawo, ga siyayya ba irin wacce ba'ayi ma babynsu ba, Khaleel ya kwaso kayan babies ba iyaka.
A hotel suka sauka inda da yamma bayan sun dawo daga shopping suka tafi gidan Saif. Sanda sukaje Saif na wurin aiki sai Salma suka tarar a gidan. Bayan sun gaisa Khaleel ya mik'e ya kalli Hanifah yace
"Bari na same shi office d'in".
Daga haka ya fice, nan su Hanifah suka baje suka dasa fira kamar ba gobe, cikin firarsu ne Hanifah ke bata labarin Humaira, da mamaki Salma tace
"Meyasa kike saurin yarda da mutum ba tare da kinsan ko waye ba?".
Hanifah tace
"Bari kedai tautsayi mana, ay yanzu na ja baya da friendship d'in babu dole, kuma a hankali zan fitar da ita daga rayuwarmu gaba d'aya, idan ma tak'i to zan buga mata warning ta tafi can ta nemi daidai da ita".
Salma tayi dariya
"Hakan dai ya kamata, kinga kinyi learning lesson sai kiyi a hankali saboda gaba"
Hanifah tace
"Ay dole".
Suna zaune Hanifah ta lura Salma sai faman tashi take tana zubar da yawu ta dawo, ta zubar a karo na uku ta dawo Hanifah ta kalleta tace
"Kodai mun samu k'aruwa ne?".
Salma tace
"K'aruwar me?".
Hanifah tace
"Kin fa sani zaki wani nuna baki sani ba"
Salma tayi murmushi kurum, Hanifah ta yi dariya tace
"Ah! Ni nasan da zance a k'asa kuma shine ko ki sanar dani, ni kuwa ranar dana gano nawa na fad'a miki".
Salma ta kamo hannun Hanifah
"I'm sorry kinji? Wallahi kunya naji na kasa fad'a miki".
Hanifah ta janye hannunta
"Ashema kunya, da yanzu sai dai mu ganki da ciki ko? Ke haka kikayi planning ba?"
Salma ta shiga ba Hanifah hak'uri inda ta k'yar ta hak'ura tace
"Naji yanzu wata nawa?".
Salma tace
"Wata d'aya kawai".
Hanifah tace
"Iyye! Ah lallai su Ya Saif za'a zama daddy"
Sukayi dariya gaba d'aya.
Salma ta kuma cewa
"La ni na manta fushi nake dake"
Hanifah ta zaro idanu waje tace
"Menayi miki?".
Salma tace
"Wai kuzo gari ku wani sauka a hotel"
Hanifah tayi dariya
"Kai ya za'ayi mu takurawa amare? Kedai barmu a hotel d'inmu".
Salma tayi murmushi kurum.
 Sai da suka gama firansu sannan suka tashi Hanifah ta taimaka mata suka d'ora girkin dare, jollof d'in shinkafa da soyayen kifi.
Bayan sun gama suka gyara kitchen d'in, sannan suka dawo palo suna kallon wani movie mai suna Raising Helen, su Saif sukayi sallama, bayan sun zauna ne kuma suka fara fira, da k'yar suka tashi lokacin an fara kiraye kirayen sallar magriba.
Bayan sun gama sallah ne suka d'unguma dinning suka ci abinci, suna ci suna fira. Hanifah ta mik'e taje daidai saitin kunnen Khaleel ta rad'a mishi wani abu, duk akan idon su Saif, suna kallo Khaleel ya ware idanu waje yace mata
"Ah haba don Allah".
Tana murmushi tace
"Wallahi kuwa da gaske".
Saif yace
"Kai mekuke cewa haka?".
Khaleel ya k'yalk'yale da dariya yace
"Abin arzik'i muke cewa, lallai Saif shine kuka 6oye mana wannan abin alkhairin?"
Cikin rashin fahimta Saif yace
"Wai mene?".
Khaleel yace
"Shikenan tunda baka sani ba, uhm mu bari mu tashi mu wuce hotel mu kwanta dare nayi"
Saif da sauri ya taresa yana fad'in
"Haba dai ya Khaleel, ya gs gidana zaku tafi hotel? Gaskiya banji dad'i ba".
Khaleel yace
"Wallahi bawai don bama son zuwa nan d'in bane, a'a bama son mu takura muku ne"
Saif yace
"Haba ya Khaleel! Wane irin takura kuma? You are my brother fa remember?".
Khaleel ya dafa sa
"Haba nasani Saif, but don't worry na maka alk'awarin gobe zamu dawo nan. Amma dai ka barmu muje hotel d'in yanzu mu kimtsa mu kwashe kayanmu sai mu dawo"
Saif yaji dad'i yace
"Yauwa ko kai fa, har naji dad'i yanzu".
Akayi dariya, har bakin mota suka rasa su. sannan suka koma ciki.


Haka kuwa akayi washe gari sai gasu sunzo, aikuwa Saif akayi ta murna, kullum da yamma sai sun fita yawo su dawo da daddare. A haka har sukayi sati d'aya sannan kuma suka soma shirin dawowa gida.


*****

Sun koma Kaduna da daddare inda Hanifah ke tattara kayan baby da suka siyo tana adanawa, Khaleel na gefenta yana taya ta. Wasu set na overall pink color Hanifah ta d'aga tana kallo cike da adoration Khaleel yace mata
"Wai meyasa kika kwaso na mata?".
Ta kalleshi tana murmushi tace
"Kai meyasa ka kwaso na maza?".
Yace
"Saboda nasan baby boy zaki haifa min insha Allah".
Hanifah tace
"Ni a'a mace ce ma insha Allah".
Yace
"Kece macen ay, Allah ya kawo namiji"
Tace
"Mace Allah ya kawo ta".
Kamar wasa gardama ta 6arke tsakaninsu, da k'yar Khaleel yace
"Shikenan idan macece nayi miki alk'awarin kiss hot one immediately bayan kin haihu, kuma ko gaban waye, and idan namiji ne zaki bani hot kiss koma a gaban waye"
Tace
"Na yarda Allah ya kaimu".
Cike da confidence
Jawo ta yayi ta fad'o bisa k'irjinsa yana zolayarta wai cikinta ya fara fitowa sosai, ita kuma sai shagwa6a take zuba masa, kafin ta ankara taji bakinsa cikin nata, inda kuma wasa ya chanza salo, da sauri na fito kar ka naga abinda yafi k'arfina.




MSB✍🏼

Wednesday, 29 March 2017

KHALEEL Page 69&70

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻69&70✍🏻✍🏻


A hankali yake taku har ya tako inda take, ganin yadda ta cika tayi fam ya sanya ya kamo ta tsam a jikinsa.
"Dan Allah calm down my princess, kinsan yanzu bake kad'ai bace ki daina tada hankalinki a banza, bana son wani abu ya ta6a mana babynmu"
Ta ture sa iya k'arfinta cikin tsawa tace
"Hankalina bazai kwanta ba har sai ka sanar dani daga ina kake?"
Cikin kwantar da murya ya soma magana
"Kinsan nace miki oga ya kiramu ay ko?"
Ta girgiza kanta alamun eh ya cigaba
"Bayan mun gama sai abokin aikinmu ya kad'e wani yaro a sanadiyar haka muka taimaka masa aka wuce dashi asibiti mun d'an juma a can, sh....sheyasa kika ga nayi dare haka, amma ki cire duk wani mugun tunani a ranki my dear bazan ta6a cin amanar ki ba, you know i love you from the bottom of my heart right?" Ya k'arasa yana shafa mata gefen fuska yana murmushi, kallonsa take kamar bata sanshi ba, irin kallon nan na tuhuma, yace
"Baki yarda dani ba ko?"
Tace
"Bawai ban yarda da kai ba ya Khaleel, yadda ka chanza ne dole idan kayi wannan daren hankalina ya tashi, nafiso idan har wurin wata kake zuwa ka daina 6oye min, ka fito fili ka sanar dani zai fi min sauk'i"
Yace
"Haba Hanifah! KI YARDA DANI mana, maganar dana fad'a miki haka d'inne ya faru"
Ta share hawayenta
"Shikenan na yarda Allah yasa haka d'inne" yace
"Haka ma ne my princess kinji?"
Daga k'arshe dole ta yarda ganin yadda yake kwantar da murya yayi kalar tausayi, tsakanin mata da miji kuma sai Allah take ta mance komai.
A daren ranar sunyi kwanan farin ciki inda Khaleel ya nuna mata tsantsan kulawa marar misaltuwa!


******

Abubuwa sun d'an daidaita tsakaninsu sai dai Khaleel na yawan behaving somehow kamar marar gaskiya misali idan yana waya ta shigo zaiyi saurin katsewa, dah da farko takan tuhume shi sai yace mata Wallahi ba wani abu bane, kawai k'ila sanda take shigowa ya gama wayar ne.  Kallonshi kawai take tana k'yaleshi don bata son tashin hankali ya kuma had'a su, amma deep inside her tana zargin wani abu, dan dai ance zato zunubi koda ya kasance gaskiya sheyasa sai ta daina kawo tunanin komai a ranta yanzu, sai dai damuwar data shiga ba y'ar kad'an bace, amma kuma damuwarta ta ragu don yanzu rayuwarsu ta dawo kamar dah yana bata kulawa fiye da dah ma, itama yanzu ta k'ara himma wajen ganin ta dawo da mijinta na dah.

*****

Wata rana da safe bayan sun tashi daga bacci Hanifah duk aikin da ya kamata tayi ta gama, ta taimaka ma Khaleel ya shirya kamar kullum sukayi breakfast, nan ma kafin ya tafi office sai da ya nuna mata yadda zaiyi missing d'inta itama haka, hakan da yake ba k'aramin dad'i takeji ba zuciyarta fes haka takeji yanzu.
Yana isa office ko minti biyu baiyi da fara aikinsa ba aka shiga knocking, ya d'an dakatar da abinda yakeyi yace
"Come in"
Masingansa ne ya shigo mai suna Garba, rissanawa yayi alamun girmamawa yace
"Ina kwana y'alla6ai?"
Da murmushi a fuskansa yace
"Ah Malam Garba an tashi lafiya?"
Yace
"Lafiya lau"
Khaleel yace
"Yadai?"
Yace
"Kanada bak'uwa a waje, amma ban riga nace mata kana nan ba, nadai ce mata ta jira na dubo"
Khaleel yana ma Garba wani kallo yace
"Wacece?"
Garba yace
"Wallahi bansanta ba, amma daga gani dai budurwa ce tadai ce tana son ganinka da gaggawa"
Khaleel yace
"Ok ka shigo da ita"
Da girmamawa yace
"To" sannan ya fice. Can sai gashi ya dawo tare da ita bayan fitar Garban ne da mamaki Khaleel yace
"Humaira! Mekike yi a office d'ina yau kuma?"
Tana tsaye tace
"Haba yayah! Bazaka bani izinin zama ba tukunna ba?"
Ya dafe kai yace
"Ohh i'm sorry please, zauna bismillah"
Ta zauna sannan tace
"Ina kwana?"
Yace
"Lafiya lau ya karatu?"
Tace
"Alhamdulillah"
Yace
"Meke tafe da ke?"
Tayi murmushi tace
"Dan Allah dama so nake ka ranta min kud'i zanyi wasu hidima ne hannuna ba kud'i, gashi ba'a aiko min saboda account d'ina ya samu matsala sai anjima zanje bank d'in na gyara" tana magana tana wani sunna kai alamun kunya tana kashe murya.
Ya sauke ajiyar zuciya
"Har nawa kike buk'ata ne?"
Tace
"Ko dubu 30 ma ya isa"
Da mamaki yace
"Mezakiyi da dubu 30?"
Ta sunna kai k'asa tace
"Gaba d'aya kayan abinci na sun k'are shine zan siya"
Yace
"Ok kizo gida idan na koma anjima, ko kuma ki bari zan ba Hanifah ta baki ay kuna had'uwa kullum"
Sam ba haka taso ba amma dole tabi a hankali kar yayi saurin gano ta, dan haka sai tace
"Ba damuwa nagode sosai Allah ya saka da alkhairi"
Yace
"Bakomai Amin"
Ta mik'e tana wani yanga tace
"Zan koma sai anjima"
Yace
"Sai anjima"
Sai da fito waje ta soma fitar da hucin bak'in ciki, lallai ma Khaleel ya raina mata wayau yanzu har sai yaba wannan shegiyar matar tasa kud'i ta bata kenan? Lallai da sake dole ta zage damtse idan ba haka ba bazata cimma burinta ba. Da wannan tunanin ta tari Napep ta koma hostel.

Da yamma bayan ya koma gida Hanifah ta taro sa kamar kullum, yayi wanka ta taimaka masa ya shirya suka nufi dinning, suna cikin cin abincin ne yace
"Yau k'awarki tazo office d'ina"
Da mamaki tace
"Wace k'awar tawa?"
Yace
"Kina da k'awa sama da Humaira ne?"
Ta d'aure fuska tace
"Oh hakane, me taje yi maka?"
Yace
"Wai kud'i zan ranta mata...."
Ya bata labarin abinda zatayi dashi, "So nace zan baki ki kai mata idan kun had'u school"
Sai a nan taji sanyi tace
"Ok ba damuwa"

Haka kuwa akayi ranar da Hanifah ta shirya zata school, ya bata kud'in ta kai mata. Tana isa school d'in ta kira Humairar bugu biyu ta d'auka Humaira ta soma magana
"Hanifah ya kike?"
Tace
"Lafiya lau kina ina ne?"
Tace
"Gani nan yanzu na fito daga hostel, kina ina?"
Tace
"Gani nan inda nake parking cikin motata, ki k'araso ina jiranki"
Tace
"Ok gani nan zuwa yanzu insha Allah"
Hanifah tace
"Ok toh"
Suka katse wayar. Bayan minti goma sai ga Humaira ta iso tana zuwa ta bud'e motar ta shiga tana murmushi tace
"Maman d'an baba ya baki fito daga motar ba?"
Hanifah tace
"Wallahi wai dama ke nake jira sai muje tare"
Humaira tace
"Allah sarki ya kike ya babynmu?"
Hanifah tace
"Lafiya lau, ga wannan ma" ta k'arasa tana zage zip d'in jakar ta sannan finally ta fito da wata brown envelope ta mik'a mata
"Ga sak'on ki"
Humaira fa fad'ad'a murmushinta
"Kai nagode sosai, please ki taya ni godiya"
Hanifah tace
"Haba ba komai"
Daga nan suka fito daga motar suka je suka had'o duka handouts d'in da basu dashi, suka kar6i exam card har signing an musu, don next week zasu fara exam.



*******

Tafi kwana biyu tana had'a plan yadda zata jawo ra'ayin Khaleel gareta inda finally tayi coming up with a great idea, bayan dogon bincike ta gano lokacin da yake fita.
Ranar da ta shirya ta fito bakin titin da yake bi idan zaije office, inda ta dad'e tsaye tafi minti talatin kafin finally ta hango motanshi, sai data daidaici ya iso inda take sannan tazo yin crossing road d'in wani burki ya taka ji kake k'uuuuiii! Amma still ba zato sai da ya bige ta, ta fad'i rigib k'asa. Da sauri ya fito daga motar inda ya k'araso a rud'e, tana kwance k'asa rigib tana ihun k'arya, kamar ance d'ago kanki kawai suka had'a ido, muninsa kad'ai ya isa ya bada tsoro take ta kurma ihu, tana k'ok'arin tashi tsaye, tace
"Waye kai?"
Yace
"Kiyi hak'uri na kad'e ki ba da sanina ba kuma ma ay laifinki ne meyasa kika taho kina ganina?"
Yadda takejin haushi ya sanya ta fara masifa
"Da Allah Malam ni bansanka ba kuma ka daina yi min wasu maganganu wanda bana gane makake cewa, ka tafi kawai"
Yace
"Amma ba inda kika ji ciwo ko?"
Ta k'ara kurma uban ihu
"Nace ka tafi haba!"
Tana gama fad'in haka ta ruga a guje tayi hostel tana zuwa ta fad'a bisa katifarta tana hak'i. Room mate d'inta mai suna Rufaida da ke sauke indomie daga wuta ta juyo tana kallonta tace
"Ke Humaira lafiyan ki zaki shigo babu sallama? Sannan zaki shigo a guje kamar an biyo ki?"
Humaira ta galla mata harara tace
"Sa idawa ko ina ruwanki dani kuma?"
Rufaida ta ta6e baki tace
"Meyayi zafi haka? Allah ya baki hak'uri" daga nan bata k'ara magana ba ta cigaba da abinda takeyi. Humaira ta tashi zaune ranta a jagule, abin haushi abin takaici wai duk wannan fad'uwar da tayi ta tashi a banza kenan? Ga rashin nasara ga fad'uwa k'asa, k'asan ma akan titi. Sai kawai taja wani dogon tsaki
"Mtssss" Rufaida ta juyo ta kalleta amma bata tanka ba. Tana kallonta ta tashi a fusace kuma ta fice daga d'akin.
Rufaida tace a fili
"Y'ar wahala ta maida ni banza kamar bansan me take shukawa ba, Allah sarki baiwar Allah Hanifah ta d'auketa mutuniyar arzik'i ashe ashe, sheyasa ma yin k'awa a wannan zamanin sai a hankali, nikam inaga gaskiya wata rana sai na same ta na fad'a mata abinda Humaira ke mata, don bazan zuba ido ina ganin ana cusa wa y'ar mutane bak'in ciki jna gani ba, Hanifah muna mutunci sosai don haka zan same ta kawai na fad'a mata gaskiya dama tun farko kafin abin yafi k'arfinta ta d'auki mataki"
Da wannan tunanin a ranta ta k'arasa cin indomie d'inta.


*******

Ranar da sukayi first paper d'insu bayan sun fito ne Humaira tace ma Hanifah
"Yau gidanki zanje kuwa"
Hanifah tace
"Kinsan kuwa nima daga nan ba gida nayi ba, zan biya gidanmu ne sannan na wuce gida"
Humaira ta ta6e baki tace
"Ok sai yaushe kike gida?"
Hanifah tace
"Ranar da bamuda paper mana"
Humaira tace
"Shikenan dan Allah kinga ke kinfi iya wannan course d'in don in samu ki koya min ne"
Hanifah tace
"Ok ba damuwa zuwa jibi sai kizo"
Humaira tayi murmushin da ita kad'ai tasan ma'anarshi sannan sukayi bankwana, Hanifah ta shige motarta Humaira kuwa ta wuce hostel.

A gida ta iske Ammi tana garden da alama yau iska take sha. Hanifah ta k'arasa da sauri ta rungumota ta baya tace
"Ammi!"
Da sauri Ammi ta juyo baki bud'e tace
"Lallai Amina bakida hankali, wai har yanzu baki hankali ba ko?"
Hanifah ta zagayo ta zauna gefenta tana murmushi tace
"A gabanki ay bana girma Ammi"
Ammi tace
"Zaki girma ne wata rana"
Hanifah tayi dariya
"Ammi ina kwana?"
Ammi tace
"Lafiya lau daga ina kike?"
Hanifah tace
"Makaranta exam mukayi"
Ammi tace
"Au har kun fara kenan?"
Hanifah tace
"Yau muka fara"
Ammi tace
"To ubangiji Allah ya bada sa'a"
Tayi murmushin jin dad'i tace
"Amin Ammi, akwai abinci don yunwa nakeji"
Ammi tayi dariya
"Hala bakiyi kalaci ba kika kama hanyar makaranta?"
Hanifah tace
"Eh banyi ba yau tun 7 da rabi na bar gida saboda k'arfe 8 muke da paper d'in"
Ammi tace
"Lallai ina d'ana?"
Hanifah ta turo baki
"D'anki kuma nifa?"
Ammi tace
"Ohon maki ni Khaleel kawai na sani, da ki tsaya kina surutu kije ki nemi abinda zaki ci, bai kamata kina zama da yunwa ba a wannan yanayin"
Hanifah tace "To"
Ta tashi da sauri tayi ciki, Ammi ta bud'e baki galala tana kallonta fad'i take
"Ki dai bi a hankali kar kije ki 6arar da cikin, ina amfanin rashin nutsuwa?"
Tana juyo dariyarta daga bakin k'ofa tana fad'in
"Kai Ammi"



MSB✍🏼

Monday, 27 March 2017

KHALEEL Page 67&68

♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻67&68✍🏻✍🏻


Bayan dawowar Khaleel da kwana biyu Humaira ta ce zata kawo ma Hanifah ziyara, dama dai ta sanar da ita tun jiya zatazo, da har Hanifah zata sanar da ita yau  mijinta na gida amma kuma sai ta kasa, kawai tace mata "To"
Ta sanar dashi zuwan sabuwar k'awarta da suka soma k'awance a kwanakin baya yace mata ta tashi ta girka mata wani abu da kayan motsa baki, sam cikin ranta bata son zuwan Humaira amma ba yadda ta iya saboda tace zatazo d'in. Tana cikin wanke shinkafa Khaleel ya shigo kitchen d'in daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana kallonta yadda tayi kicin kicin da fuska, a hankali ya k'arasa ya kamota ta baya tare da kissing lallausan gashinta dake k'amshi. Yace
"Yau waya ta6a min my princess haka?"
Ta k'ara had'e rai ta cigaba da abinda takeyi, yayi murmushi yace
"Tunda baza'a kulani ba bari nayi wanka na bar gidan sai anjima zan dawo"
Har cikin ranta taji sanyi wannan kishi nata ina zata kaishi wai? Sai kawai tayi murmushi ta zuba shinkafar cikin ruwan dake tafasa a tukunya, salad ta soma yankawa har ta kusa gamawa ta jiyo hayaniya daga palo, aje wuk'ar tayi da sauri tare da lek'awa, Khaleel ta gani da Humaira da alama sun san juna tana ganin duk maganar da sukeyi kuma tana ji.
Khaleel yace
"Allah sarki ina Ibrahim d'in yanzu?"
Tace
"Yana nan lafiya lau yana lagos can yake aiki yanzu"
Khaleel yace
"Haba nidai ina ganinki naga kamar da kukeyi da shi ta nan nayi saurin gano ki ay, gaskiya kin girma sosai yasu Mama?"
Tace
"Lafiyansu k'alau"
Daidai nan Hanifah ta fito tana k'ak'alo dariyar yak'e tace
"Laa ashe ma kunsan juna?"
Khaleel cikin dariya yace
"Wallahi kuwa, k'anwar Ibrahim ce wanda mukayi karatu a turai da shi, a lokacin can suke zaune ay ina yawan zuwa gidan, sai dai yanzu naga ita Humairar ta girma barakallah"
Hanifah tayi yak'e
"Yayi kyau kam, to itace ay y'ar ajinmu wadda nake baka labari"
Yace
"Allah sarki, feel at home Humaira ni zan fita sai na dawo"
Hanifah tace
"A dawo lafiya"
Zama sukayi kan kujera a tare inda Hanifah tace
"Ashe da gaske dai kina tafe?"
Humaira tayi dariya
"Eh wallahi zaman hostel d'in ya isheni na rasa abinyi sheyasa nace bari nazo, ashe ma oga na gida ay da kin sanar dani da banzo ba"
Hanifah tace
"Kai bakomai, yama fita bari na kawo miki ruwa"
Hanifah ta mik'e ta shige kitchen, can sai gata ta dawo hannunta d'auke da tray, ajewa tayi inda ta soma tsiyaya mata 5alive a cikin glass cup, Humairar tana sha Hanifah ta jefa mata tambaya
"Ashe ba nan garin kike ba?" Humaira tayi murmushi
"Eh wallahi daga Bauchi nake, karatu dai ya kawo ni nan"
Hanifah tace
"Allah sarki"
Sun d'an ta6a fira kad'an Hanifah na dubo girki har dai ta kammala ta jera dinning, dawowa tayi tana kallon Humaira tace
"Muje kici abinci"
Humaira tace
"Laa wallahi na k'oshi bana jin yunwa"
Hanifah tace
"Aikuwa baki isa ba, saboda ke fa na girka amma kice bazaki ci ba?"
Humaira tayi dariya tare da mik'ewa tsaye
"Ok ba damuwa muje muci tare"
Nan suka jera har dinning suka soma cin abincin inda suna ci suna fira kad'an, ba laifi Hanifah ta saki jikinta sun d'an ta6a fira. Suna nan har aka fara kiran sallar azahar Hanifah ta soma mik'ewa tsaye ta kalli Humaira
"Lokacin sallah yayi muje muyi ko?"
Humaira ta sadda kanta k'asa tana murmushi tace
"Wallahi hutu nake kije kiyi ki dawo"
Hanifah tayi murmushi tace
"Ok"

Bayan Hanifah ta gama sallar ne ta dawo palo inda ta tarar Humaira na kallo a natse. Humaira ta kalli Hanifah tace
"Kin gama?"
Hanifah tace
"Eh nagama"
Ko minti biyu Hanifah batayi da zama ba taga Hanifah ta soma shirin tafiya, da mamaki Hanifah tace
"Keda kika ce sai la'asar, ya naga kina shiri?"
Humaira tayi murmushi tace
"Wallahi kasuwa nake so in biya amma sai naje hostel nayi wasu aikace aikace"
Hanifah tace
"Allah sarki ba damuwa, sai mun had'u a school ko?"
Humaira tace
"Eh kinji wai an lik'a time table?"
Hanifah tace
"Wallahi naji, idan na shigo sai muje mu duba"
Humaira tace
"Ok sai kin shigo d'in"
Hanifah ta raka ta har bakin gate sannan ta dawo.


******

Tun daga wannan rana kusan kullum sai Humaira tazo, ko kad'an Hanifah bata kawo komai a ranta ba, har takance lallai Humaira akwai son zumunci.
Abu d'aya ke bata mamaki yadda Khaleel gaba d'aya ya tattara rayuwarsa ya mik'a ta ga waya, bayada aiki sai chatting kuma sam ba halinsa bane, a dah idan kaga Khaleel na kan waya to browsing abu yake mai mahimmanci, ko zaiyi chatting ba koda yaushe, sheyasa ma mutane sukance ya cika wulak'anci don baya ma mutane reply a whatsapp, amma yanzu taga abin nasa ya soma yin yawa kullum yana kan waya yana latse latse.
Ko y'ar firar da sukeyi yanzu an dena, ko ta masa magana sai dai yace mata "Uhm" abin nan ba k'aramin damunta yake ba. Don haka sai tace zata masa magana.
Wata rana suna zaune da daddare ta kalle shi yadda yake latsa wayar yana wani murmushi tace
"My only"
Yace
"Na'am"
Yau ko my princess babu, sai ta daure tace
"Wai kwana biyu meke damunka haka?"
Yace
"Mekika gani?" Still hannunsa na kan waya.
Tace
"Ka chanza gaba d'aya my only, dah ba haka kake ba, meyasa?"
Yace
"Wani abu nakeyi mai mahimmanci sheyasa"
Wani k'ululun bak'in ciki ya tokare mata wuya cikin sark'ewar murya tace
"Yanzu har akwai abinda yafini mahimmanci ne idan muna tare?"
Yayi murmushi
"Hanifah kenan bazaki gane ba"
Haushi ya turnik'e ta, ta rasa meya chanza mata Khaleel d'inta, amma ta d'auki alk'awarin a sannu zata gano koma menene zata magance shi da izinin Allah.


*****


Kwana biyu tsakani abu sai dad'a gaba yakeyi, ranar wata alhamis ya dawo a gajiye kamar yadda suka saba ta taro sa bayan yayi wanka ta taimaka masa ya shirya, ta lafe bisa kafad'unsa tace
"My only muje kaci abinci"
Abin mamaki sai taga ya haye gado tare da bajewa yace
"Wallahi bana jin yunwa yau snacks naci a office, k'ila zuwa anjima dai"
Duk da ranta ya sosu amma sai ta adure tace
"Yau kuma my only? Abinda baka ta6a yi ba shine yau ka fara yi kuma?"
Yace
"Sorry dear, naji yunwa ne d'azu sheyasa naci ki bari zuwa anjima sai naci, yanzu bacci nakeji"
Ranta ya dagule wai meke shirin faruwa dasu ne? Meyasa Khaleel ya chanza mata haka? Meye dalilinsa? Tambayoyi barkatai amma babu amsoshinsu.

Bayan sallar la'asar ya tashi yayi wanka yayi kwalliya sosai sai k'amshin turare ke tashi, Hanifah ta shigo da cup d'in lemo a hannunta ta tsaya tana kallonsa. Sai gyara kwalar rigarsa yakeyi yana wani kakka6e jikinsa yana kallon kansa ta madubi. Da mamaki Hanifah tace
"My only ina zaka je da yamman nan?"
Yayi murmushi yace
"Office zanje mana"
Ta saki baki galala tana kallonsa
"Office yanzu?"
Yace
"Eh mana ba dad'ewa zanyi ba oganmu ya kiramu ne"
Sai a sannan tayi murmushi tace
"Gaskiya ka tabbatar ka dawo da wuri my only"
Yace
"Insha Allah my princess"
Mik'a masa cup d'in tayi ya kafa kai ya shanye ya mik'a mata yace,
"Sai na dawo"
Tace
"A dawo lafiya"
Daga haka yasa kai ya fice.


K'arfe goma shiru, motsi kad'an sai ta lek'a taji ko ya dawo amma shiru. Hanifah abin ya fara bata tsoro ganin har sha d'aya tayi ba Khaleel ba alamarsa, ta kira wayarsa yafi a k'irga bai d'aga ba. Can wani tunani ya zo mata ta dage k'irji tare da zaro ido waje!
"Kar dai Ya Khaleel wurin budurwarshi yake zuwa? Kai anya Ya Khaleel zai iya cin amana ta? Never i don't think so! To meye dalili meke faruwa?"
Sai dai zuwa yanzu ta soma kokwanto akan Khaleel, gabanta na harbawa ta sa kuka tana kiran "Innalillahi wa inna ilahir raji'un" bataso ta amince Khaleel nada budurwa don bata zaton haka d'inne.
Taci kuka sosai wurin k'arfe sha d'aya da rabi taji k'arar shigowar mota, da hanzari ta mik'e jikinta har rawa yake ta nufi k'ofa, shigowa yayi tare da kunna fitila, idonsa tar akanta tana tsaye kamar zakanya tana huci idonta jawur! Ya ware idanu waje yace
"Mekike yi har yanzu bakiyi bacci ba?"
Fuska d'aure tace
"Ya Khaleel daga ina kake da daddaren nan?"
Yayi murmushi
"Haba my princess wannan wace irin tamabaya ce?"
Tace
"Ya Khaleel bansanka da k'arya ba, ka fad'a min daga inda kake da tsohon daren nan!"
Ya kalli fuskarta idanunta sun rik'id'e zuwa ja, ya d'an tsorata yadda yaga yanayinta, to ya zaiyi me zai mata ne?


MSB✍🏼

KHALEEL Page 65&66

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻65&66✍🏻✍🏻

Yau da gobe sai Allah duk da Hanifah batada niyyar yin k'awa ko d'aya amma a department d'insu ta had'u da wata Humaira, budurwa ce y'ar kimanin shekara sha tara, dalilin da yasa Hanifah ta bata fuska taga kamar yarinyan nada mutunci ko ta yanayin shigarta saboda kullum cikin k'atuwar hijabi take, gashi ba ruwanta da kowa ita kad'ai take rayuwa, ganin haka ya sanya Hanifah ta amince da ita har suka k'ulla k'awance.
Haka rayuwar ke gudana, a kwana a tashi ba wuya wurin Ubangiji yau cikin Hanifah har ya tasan ma wata hud'u, Idan har kayi mata kallon sosai zaka fuskanci cewar cikinta ya d'an 6ullo kad'an.


Ranar wata juma'a tafiya ta kama Khaleel zuwa kano duk dai tafiyar daga office d'insu ne bama shi kad'ai zaije ba harda abokan aikinsa su biyu, tun da yake wayar Hanifah dake kwance gefensa ke masa wani irin kallo har ta kai ya tsargu, sai da ya gama wayar ne ya juyo yana kallonta yace
"Yada kallo haka my princess?"
Ta 6ata rai had'e da zum6uro pink lips nata masu k'ara mata kyau tace cikin shagwa6a
"Ina zakaje?"
Yayi murmushi yace
"Wallahi tafiya ce ta kama mu yau d'in nan amma kar ki damu kwana biyu kawai zamuyi mu dawo"
Ta juyar da kanta gefe alamun fushi, yayi murmushi tare da kamo ta ya maido bisa jikinsa yace
"Fushi kuma princess? Meyafaru?"
Idanunta suka kawo ruwa tace
"Naji kana zancen tafiya ka barni, kuma kai kanka kasan tun da muka daidaita baka ta6a tafiya daidai da rana d'aya ba, sannan kasan ban iya bacci idan baka kusa dani"
Yaji ba dad'i saboda shima d'in ba iyawan zaiyi ba sai dai yazama dole ya tafi saboda aiki ne zai kaishi don haka sai ya rungume ta tare da fara aika mata da sak'konin kisses ta ko ina, itama ta biye masa sun d'auki lokaci a haka kafin Khaleel ya sauke ajiyar zuciya yace
"My princess wallahi inda kinsan dauriyar da zanyi muje mu dawo da bakiyi ma  magana ba, wallahi zanyi missing d'inki sosai, kiyi hak'uri kar kice zakiyi kuka don bazan iya jure jin kukanki ba, i love you so much kwana biyu kawai zamuyi mu dawo insha Allah kinji my baby?"
Ta k'ank'ame shi tace
"I love you more my only, insha Allah zanyi manage har ka dawo amma kasani zanyi kewarka sosai"
Yace
"Yes i know my princess nima haka"


Daga nan Hanifah ta tashi ta had'a masa had'ad'en breakfast, ta shirya masa kayansa kafin ya fito wanka had'e da fiddo masa kayan da zai sanya. Tana gamawa itama tayi wanka tasa wata farar loose top marar hannu da red dogon skin tight sai ta d'aura red d'an kwali, ta kimtsa ta fito.
D'akin Khaleel ta lek'a a lokacin yana shafa mai, ganinta yasa ya saki murmushi ta mayar masa, k'arasawa tayi ta taimaka masa ya shirya suka nufi dinning suka karya. Tunda suka fara ci Hanifah ke kallonsa kamar zata cinyesa, ya kalleta yace
"My princess"
Ta sadda kanta k'asa tana murmushi tace
"Na'am my only"
Yace
"Na gama sai tafiya yanzu kuma"
Sai kuma ta 6ata rai duniya ba abinda ta tsana taji zatayi nisa da Khaleel d'inta, yana lura da yanayinta amma sai yayi sauri yace
"Da yaushe da yaushe kike lectures ne?"
Tace
"Sai monday amma gobe inada test k'arfe tara"
Yace
"Ok ga wannan"
Ya mik'a mata kud'i duba goma y'an d'ari biyar biyar yace
"Ki rik'e wannan abinda kike 6ukata kiyi yi amfani dasu har Allah yayi mana dawowa"
Tana dai ta daurewa bataso tayi kuka amma abu yaci tura sai kawai tasa kuka, take hankalin Khaleel ya tashi ya rud'e, hugging nata yayi yana ta aikin lallashi tare da assuring nata cewa kwana biyun zaiyi ya dawo and duk abinda take buk'ata ya aje mata, sai da ya tabbatar ta bar kukan sannan ya tafi.
Bayan tafiyan Khaleel gidan gaba d'aya ya mata fad'i ba dad'i sam, yau batasan ya zatayi bacci ba babu Khaleel a kusa da ita.
Haka ta wuni daga kallo sai karatun test, idan ta gaji ta buga candy crush a wayanta.
Tunda ya isa ya kira ta ya sanar sun isa lfy,


Da daddare Khaleel ya kirata da murmushi
shimfid'e saman fiskokinsu. Hanifah tace
"My only!"
Yace
"My princess! Ya kike?"
Tace
"Lafiya lau ya gajiya?"
Yace
"Akwai ta kam, kinga da ina nan da yanzu kin min tausa, gaskiya Hanifah i missed you so much, yanzu baki kusa da ni, komai ni ke wa kaina, kin riga kin shagwa6a ni"
Yanajin saukar ajiyar zuciyarta, tace
"Nima haka my only gani nan sai tunaninka nake"
Dad'i ya kama shi sosai
Yace
"I love you so much dear, nima ay tunaninki nakeyi"
Suka cigaba da firar soyayya tare da bayyana wa junansu yadda sukayi missing juna. A daren ranar haka suka dad'e suna waya kafin daga k'arshe suyi sallama. Haka ta kwanta lamo tana tunane tunane da k'yar ta samu bacci 6arawo ya sace ta


Washe gari bayan ta gama abinda take tayi wanka ta tafi school, a bakin class ta had'u da Humaira tana karatu, suka gaisa sannan suka d'an ta6a fira kafin su shiga test d'in.
Bayan sun fito cafeteria suka wuce suka ci abinci sannan suka soma yin bankwana inda Humaira ta buk'aci taje gidan Hanifah don Hanifah ta sanar mata yau mijinta baya nan she's lonely. A haka suka wuce gidan Hanifah.
Suna shiga Humaira ta soma yaba gidan first abinda tace shine
"Wow Hanifah gidanki yayi kyau"
Hanifah tayi murmushi kurum batace komai ba, kujera ta bata izinin zama inda Hanifah ta wuce kitchen ta d'auko mata lemo da ruwa.
Bayan sallar la'asar ta soma shirin tafiya.
Hanifah ta mata godiya kuma taji dad'i sosai.
Haka Hanifah ta idasa kwananta d'aya ba Khaleel amma kullum suna nan mak'ale da juna a waya sam basa gajiya da junansu.


*******


Ranar da Khaleel zai dawo murna a wurin Hanifah ba'a magana kwana biyu kacal ji take kamar ta shekara biyu bata gansa ba, shima Khaleel a nasa 6angaren yayi kewarta fiye da tunaninta.
Tun safe Hanifah ta tashi ta soma gyara gidan tas ta kimtsa ko ina. Ta girka masa Farar taliyar da ta sa  karas sai ta yi ta minced meat, tayi masa kunun gyad'a da zo6o, ta kimtsa komai kan dinning. Tayi wanka ta shirya cikin wani matsiyacin material d'inkin fitted gown wanda ya mugun fito mata da surar jikinta, ta feshe jikinta da turare, tana gamawa wayarta ta fara ruri da sauri ta d'auka
"Hello my only"
Yayi murmushi
"My princess ya kike?"
Tace
"Lafiya lau ya hanya har kun iso ne?"
Yace
"My princess bansan ta ina zan fara ba, bamu samu tahowa ba sai jibi wai"
Tayi kasak'e tana sauraronsa, zuciyarta na harbawa ya zaiyi mata haka? Ta gama sa rai sannan yace wai sai jibi? Take ta kashe wayar ta wurgar da ita kan gado tana huci, a yayinda hawaye suka fara kwarara daga idanunta. Ta dad'e zaune k'asa tana kuka yau Khaleel ya 6ata mata rai sosai.
K'wank'wasa k'ofa aka soma yi, da k'yar ta tashi tana share hawaye ta fice wurin k'ofa, tana bud'ewa to her biggest surprise ever Khaleel ne tsaye bakin k'ofa yana dariya, ta had'e rai
"Dama wasa kake min shine kace bazaka dawo ba?"
Yace
"Yes my princess i want to surprise you ne, baza'a bani hug ba?"
Dad'i ya mantar da ita fushinta take tayi saurin basa a big hug tana dariya, a haka yayi ta tsokanarta tana dariya. Ciki suka shiga inda ta had'a masa ruwan wanka ta fiddo masa kayan da zaisa. Bayan ta taimaka masa ya gama shirinsa sai taja hannunsa kan dinning ta zuba masa abinci. Bayan sun gama yace
"I miss you my baby"
Kafin tayi magana ya d'aga ta cak kamar baby yayi d'aki da ita tare da direta kan gado tana ta faman k'yalk'yaltar dariya, a haka ni kuma na basu privacy.



MSB✍🏼

Friday, 24 March 2017

KHALEEL Page 63&64

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀




©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️


I dedicated this page to Maman Khaleel❤️😘❤️and my Aunty Xee💞much love dearies❤️💙💛❣❤️💙💛

(Happy birthday Aunty Khady Allah's noor👼🏼👼🏼👼🏼👼🏼)
           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻63&64✍🏻✍🏻


Dadaddare haka Hanifah ta kwana tana amai ga zazza6i mai zafi da ya rufe ta, rud'ewa ba irin wadda Khaleel baiyi ba, duk ta galaibata saboda aman da takeyi, komai taci sai ya dawo mata. Don haka Khaleel na gama sallar asuba ya kwashe ta ya kaita asibiti, office d'in wani likita suka shiga suna zuwa ya umarce wata nurse data d'ibi jininta da fitsarinta ayi mata test. Bayan gudanar da test suna zaune office d'in likitan yana murmushi ya kalli Khaleel yace
"Congratulations sir! Your wife is pregnant almost 1 and a half getting to two months"
Khaleel can't believe he'a actually gonna be a father, ita kuwa Hanifah kunya ta rufe ta take ta sadda kanta k'asa, jawo ta yayi a gaban likitan ya rungume ta tsabar farin ciki yace
"Thank you my princess, Allah ya nuna mana babynmu lafiya"
Hanifah k'ok'arin janye jikinta takeyi cike da kunya, likitan yayi murmushi yana kallon Khaleel ya burgeshi matuk'a yadda yake nuna wa matarsa kulawa ba tare da shakkun komai ba a gaban kowa.
Likitan ya rubuta mata maganin da take buk'ata had'e da shawarwari sannan yace
"Za'ayi mata scan yanzu don tabbatar da lafiyar babyn, zaki iya biyoni" daga haka ya fice a yayinda Hanifah da Khaleel suka bi bayansa.
Wata likita doctor'n yayi ma bayani take ta yi wa Hanifah scan inda aka tabbatar da babyn lafiyansa k'alau babu wata matsala, sannan ta umurce ta da ta dawo nan da sati hud'u.
A hanya ma sai da Khaleel ya tsaya ya siya mata kayan k'walama a cewarsa zataji dad'in cinsu.

Hausawa na cewa ya lafiyar kura bare tayi hauka?! Tofa Khaleel za'a zama daddy, tunda suka dawo gida Hanifah ta soma ganin sabon sauyi tattare da mijinta, kulawar da yake bata ta linku d'ari bisa d'ari akan wadda yake bata a dah, ko tari tayi sai yace mata "Sannu" ko kuma "Kina buk'atar wani abu?" Gaba d'aya ko fita ya daina yi ya zauna don kula da babynsa da abin sonsa. Ammi kuwa tuni an kirata an sanar da ita, ba yadda Hanifah batayi ba akan kar ya fad'a mata amma yak'i k'arshe ma cewa yayi
"Ina ruwanki mamanki ko tawa?" Dole ta k'yalesa amma kunyar Ammi takeji, Saif ma ba'a barsa a baya ba shima an sanar masa, aikuwa sunsha zaulaya.
Haka ya cigaba da bata kulawa ta mussaman har ta shafe kusan sati biyu sannan ta murmure, sai dai ta rame sosai tayi d'an wuya, amma ta k'ara kyau da haske.


Bayan sati d'aya da hakan admission letter d'in Hanifah ta fito, Khaleel bai sanar da ita ba tana kitchen tana yanka karas taji an rungume ta ta baya, ta lumshe idanu tana murmushi, ya juyo da ita tare da manna mata kiss a kumatu, Hanifah tayi murmushi tace
"My only ya ka dawo da wuri haka yau?"
Yace
"Wallahi kuwa naje wani wuri ne"
Ya mik'a mata letter d'in yace
"Duba kigani"
Ba musu ta duba sai dai kafin ta k'arasa karantawa ta daka wani uban tsalle tare da k'ank'ame Khaleel, take ya d'aure fuska ya jawo ta yace
"Ke meye haka? Kin manta bake kad'ai bace yanzu? Ki dinga bi a hankali mana"
Tayi murmushi tare da shafa masa fuska tace
"Afuwan ya habibi, bazan sake ba"
Yayi dariya
"Shikenan, kinga na miki registration da komai ranar Monday idan kinje school sai ki kai department d'inku"
Tace
"Angama my only"
Yaja hancinta
"That's my princess, me ake dafa mana haka?"
Tace
"Potato casserole"
Yace
"Oya zo mu k'arasa tare"
Ta ta6e baki cikin shagwa6a tace
"A'a don Allah my only ka barshi zan k'arasa" yayi dariya tare da kwaikwaiyon maganarta yace
"A'a nidai don Allah ki barni zanyi"
Gaba d'aya suka sa dariya, a tare d'in suka k'arasa, bayan sun gama cin abincin ne Khaleel ya sake fita da tabbacin zai dawo da wuri.


******

Rayuwa tana tafiya a haka har aka zo aka sa ranar bikin Saif da Salma, ba'a d'auki wani lokaci ba gaba d'aya wata d'aya aka sa. Su Khaleel da Hanifah shirin biki suke sosai, Khaleel shi ke had'a lefe a hankali yana ajewa. Duk wani abinda ya kamata suyi sun gudanar dashi da wuri komai yana tafiya daidai.
Ana saura sati biyu bikin suka kai lefe inda dangin amarya suka buk'aci zuwa jere.

Biki yana ta gabatowa gaba d'aya Hanifah ta tattara ta koma gida har agama sha'anin biki. Gidannasu cike yake da y'an uwa da abokan arzik'i, hidima ta sha kan kowa sauk'insu ma auren namiji ne walima kawai zasuyi sai y'ar dinner da aka had'a bayan an kai amarya.

Ranar walima wani dark blue lace Hanifah ta sanya anyi mata d'inkin riga da skirt, wanda ya amshe ta ya kuma yi mata kyau, ko kwalliya batayi ba, inda Khaleel shima ya sanya light blue shadda yayi kyau sosai. A haka suka tafi walimar da za'ayi a hall. An shiga da amarya inda take sanye da pink bridal gown ya mata kyau sosai, komai pink aka sanya mata. Kowa ya halarci bikin, anyi komai daidai misali. Tunda aka fara bikin Hanifah take lura da y'an matan dake ta kallon Khaleel, tun tana daurewa har abin ya ci tura, ta cika tayi fam saura k'iris ta fashe. Tama lura wasu har zuwa suke suce ya basu number wayarsa, sai dai taji sanyi yadda ko kallo basu ishe shi. Sai dai ance mata da kishi shi ya jawo har Hanifah tayi fushi ta fice daga hall d'in, sam Khaleel bai lura da fitarta ba a cewarsa tana nan zaune tunda ya hana ta yin zirga zirga.
Sai da aka soma shirin tafiya sannan fa Khaleel ya fara duba Hanifah amma sam bata nan inda take. Kamar wasa ya duba hall d'innan kaf ba Hanifah ba alamarta, hankalinsa fa ya tashi take ya fito da sauri ya shiga dubawa daga waje.


A jikin motarsa ya hango ta tsaye ta hard'e hannayenta tana kalle kalle. Da sauri ya k'arasa inda tare da sakin ajiyar zuciya.
"Hanifah!" Ya k'wala mata kira, tana jinsa amma ko kallonsa batayi, yana isa ya kamo ta ta fizge, a d'an rud'e yace
"Wai meyasa kika fito nan bayan nace ki samu wuri ki zauna gu d'aya?"
Ta k'ara had'e rai tana kumbure kumbure.
Kallonta yakeyi yana son gano wani abu, yayi murmushi tare da kamo hannayenta cikin nashi
"Haba my princess, ta yaya ma zaki soma tunani irin wannan? Kina tunanin akwai wadda zata birgeni ne bayan ke? Wallahi Hanifah inda kinsan yadda kike a cikin zuciyata da bama zakiyi wannan tunanin ba, haba Hanifah! Kin bani mamaki"
Take kuma taji ba dad'i, itama in banda hauka da kishin tsiya ta yaya ma zata soma irin wannan tunanin?
Batasan lokacin datayi hugging d'insa sosai ba tace
"Kayi hak'uri my only! Wallahi ba zarginka nake ba, kawai naji tsoro ne yadda y'an mata ke kai maka hari"
Ya cire hannayenta daga rungumar da tayi masa yana kallon cikin idonta yace
"Ke kuma kina tsoro kar na miki kishiya ko?"
Tayi murmushi cike da kunya, dariya yayi cikin sigar zolaya yace
"Meye abin tsoro a kishiya idan ma ta shigo basai ki zaune ta ba?"
Cikin muryar shagwa6a tace
"Gaskiya ni a'a ka daina bana so"
Yayi dariya yace
"An daina"
A haka Saif ya k'araso yace
"Lalala, yanzu baku iya hak'uri da juna har a gama bikin?"
Khaleel yace
"Kajika da wani zancen, kai ina ruwanka ma?" Sukayi dariya Saif yace
"Niko keda ruwa, kunga fa kowa ya watse sai mu kad'ai kuzo mu tafi gida"
A haka suka koma gida Saif sai faman zolayarsu yake, Khaleel yace
"Rabu da shi Hanifah akwai ranar da zamu rana ne"


Washe gari juma'a ana gama sallah aka d'aura auren Saif Abdul'aziz da Salma Aliyu akan sadaki dubu hamsin. Masallacin ba matsaka tsinke saboda bainar jama'ar da suka halarci taron. Daga nan suka wuce reception inda aka ci aka sha kafin taron ya watse.
Da yamma aka kawo amarya inda ta kwana gidan Ammi akan gobe za'a wuce da ita Abuja.

washe gari asabar kuwa k'arfe tara na safe aka fara shiri, Hanifah ta shirya cikin wata golden and ash atamfa d'inki doguwar riga, sai ta d'ora bak'ar after dress mai kyau.
Amarya kuwa orange da green d'in atamfa aka sanya mata sai aka rufe mata kanta da k'aton mayafi. Aikuwa kafin akai amarya Saif yasha tsiya da tsokana wurin Khaleel. A haka aka tafi kai amarya. Dadddare aka wuce dinner inda amarya ta sanya bak'i da silver d'in lace tayi kyau.
Anyi biki lafiya amarya ana gidan Saif sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba.


*****

Hanifah ta soma zuwa lecture a cikin motarta ita ke tuk'awa ta kai kanta ta maido kanta. Ta dage tana karatu sosai ba wasa. Yawancin lectures d'inta na safe ne zuwa sha biyu, ranar da batada na safe kuwa to k'arfe biyu zuwa hud'u ne na rana. Ta saba da matar Saif sosai wadda batada k'awa sama da ita, duk wata shawara ko wani abu da ya shige musu duhu sukan tuntu6i junansu. Itama tana can ta samu admission tana karatunta.



MSB✍🏼

Thursday, 23 March 2017

KHALEEL Page 61&62

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀


Masha Allah Asma'u Allah ya raya mana baby boy ya baku lafiya😘😘😘😘


©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻61&62✍🏻✍🏻



      TWO WEEKS LATER


Life goes on, haka dai rayuwansu Hanifah ta cigaba da gudana cike da so da k'auna, tuni Hanifah ta cire kunya ta aje ta gefe tsantsan kulawa da soyayya zalla take nunawa mijinta, zuwa yanzu sun saba da junansu wanda basa iya jure yin nisa da juna musamman Khaleel da yanzun ne yake k'ara k'aunar matarsa, tattali da kulawa ba irin kalar da Hanifah bata gani ba.
Ko bacci zasuyi suna nan mak'ale da juna. Ranar weekends ma Khaleel bai yarda Hanifah ta shiga kitchen ita kad'ai a tare sukeyin komai, hartta gyaran gida Khaleel na taya Hanifah, shi sam baya ganin komai indai har zai faranta ma Hanifansa rai, sam baya k'aunar 6aci ranta. Itama a nata 6angaren haka ne bata san 6acin ransa ko kad'an, duk wani abu da tasan baya so takanyi k'ok'ari wajen ganin ta kauce masa, duk abinda yace mata tayi to tanayi gudun 6acin ransa, sheyasa soyayyarsu take dad'a bunk'asa ako da yaushe, saboda ko wane yana gudun 6acin ran d'an uwansa, ta yaya ma zasu samu sa6ani?


*****

Ranar wata laraba Khaleel ya dawo gida da yamma a gajiye ya shigo, daga bakin k'ofa Hanifah ta tare sa sukayi hugging juna, kiss ya mata a kumatu kamar yadda ya saba duk sanda ya shigo gidan, hannunsa ta kama ta taimaka masa ya zauna kan kujera, manne masa tayi tare da kwantar da kanta bisa kafad'arsa tana mai lumshe idanu tace
"My only wanka zakayi ko abinci zaka fara ci?yayi murmushi yana jin sonta na k'ara ruruwa a cikin ransa, yace
"Duk abinda kika ce my princess shi zan fara yi"
Tayi dariya tace
"A gaskiya wanka ya kamata ka fara yi saboda zakaji sauk'in gajiyar da ka kwaso daga nan sai kaci abinci ko?"
Yace
"Yess! My princess hakan za'ayi"
A tare suka mik'e hannunsu sak'ale cikin na juna. Ta had'a masa ruwan wanka sannan ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa, ko wane motsi nata akan idonsa ji yake kamar ya had'e ta don so, ya sauke ajiyar zuciya yace
"My princess ki daina shagwa6a ni da yawa, kinsan irin wannan duk ranar da bakida lafiya ko nayi tafiya zan sha wahala fa"
Tayi dariiya bayan ta cire masa takalmi tace
"Wannan ay daban ne, kuma ka daina cewa ranar da baka nan to ina zaka je ma?"
Yace
"Kinsan tafiya na iya kamawa ko kuma mutuwa..."
Da sauri ta toshe masa baki tace
"Shhh, daina fad'in haka my only, in ma mutuwa ce bana fatan ta riga d'aukar min kai na fiso ta fara d'auka ta"
Yayi murmushi
"Ba wanda yasan gawan fari my princess, mudai yi addu'a Allah yasa mu cika da imani"
A sanyaye tace
"Amin"
A haka ya shiga wanka, ita kuma ta fiddo masa kayan da zai sanya marassa nauyi saboda yanayi ne na zafi.
Bayan ya fito ta taimaka masa ya shirya ta fesa masa turare sannan ta kamo hannunsa suka fito palo. Kan dinning ta zaunar dashi bayan ta zuba masa jollof d'in taliyar data ji kifi da kayan lambu sai lemo mai sanyi. Sai da yaci yayi nat sanann suka koma palo suna kallo suna fira har aka soma kiran sallar magriba.


Bayan sallar isha'i sai ga Saif ya shigo gidan, Hanifah na kitchen tana dama fura ta jiyo fira na tashi had'e da dariya, murmushi tayi tace
"Su ya Saif an zo kenan"
Bayan ta gama ta samu cup guda uku da tray ta zuba fura da nonon sai ta bi da ice block a sama. Da sallama ta k'araso ta zauna bayan sun gaisa da Saif ta mik'a musu fura, kowa na sha suna fira gwanin sha'awa. Sai kuma shiru ya biyo baya, Saif ne ya katse shirun ta hanyar mik'a ma Khaleei wata farar takarda a linke cikin envelope yana murmushi. Khaleel yace
"Meye wannan kuma Saif?"
Saif yace
"Bud'e ka gani"
Ba musu Khaleel ya bud'e ya soma karantawa, sai ya fad'ad'a murmushinsa yace
"Wow! Congratulations Saif Alhamdulillah! Ashe aiki ya samu kai nayi murna Allah ya sa alkhairi"
Itama Hanifah sai ta hau murna tana taya d'an uwanta, kafin Saif yace
"Amma fa a Abuja na samu"
Take mood na kowa ya chanza Khaleel yace
"Abuja kuma? Meyasa ba'a Kaduna ba?"
Saif yace
"Wallahi nayi k'ok'arin ganin na samu a nan d'in amma hakan ya gagara, nima ba haka naso ba, na nafison kusa da y'an uwa na"
Khaleei yace
"Bakomai ay Saif, dana nan da Abujan duk d'aya ne, an mayi ta barka tunda an samu aikin shine the most important, and naga harda gida fa da motar office aka baka"
Saif yace
"Haka ne kam, ranar Monday suka kirani, so zanje in dawo idan na dawo sai muje na kaika kaga wurin"
Khaleel yayi dariya
"Ka kaimu dai"
Sukayi dariya gaba d'aya Saif yace
"Ay dama nasani, bazaka wani yarda ka bini ba tare da wannan gum d'in ba, ya kamata ta dinga barinka kana shan iska"
Aka sake saka dariya, Khaleel yace
"Kaga laifina ne wai? Kaima wata rana haka zaka yi kace baka iya tafiya ka bar Salma ko"
Yace
"Eh mana"
Khaleel yace
"To kagani, ya kamata fa azo a fara maganar sa rana ma bansan me kake jira ba"
Saif yace
"Kai ya Khaleel tun yanzu?"
Khaleel yayi dariya
"Ahh sai yaushe to? Bawani nan nasan ka k'agara zaka yi mana bogi"
Aka sake sa dariya, haka suka k'arasa firar su gwanin sha'awa sai wuraren goma saura Saif yayi sallama ya koma gida.


Kamar yadda Saif d'in yace ranar Monday tun wuraren k'arfe 8 na safe ya bar Kaduna, yana isa ya wuce direct wurin aikin inda yana zuwa yayi signing wasu papers a take kuma aka d'auksa aiki, tun kafin ya bar wurin ya kira Ammi da Khaleel ya sanar da su nasarar da ya samu sannan yanzu zai wuce ya ga gidan da aka basa, Gida ne madaidaici flat mai d'akuna uku da kitchen sai dinning. Bayan ya gama abinda zaiyi a washe gari ya bar Abuja inda aka shaida  masa ya fara zuwa aiki sati mai zuwa.


*****

A gaggauce ta had'a breakfast ta rasa meya haddasa mata makara yau, d'akin Khaleel ta shiga a lokacin ya fito daga wanka yana k'ok'ari sanya kaya, tayi sallama ya amsa mata, toilet d'insa ta shiga ta kimtsa ko ina ta fito, yana tsaye gaban madubi yana taje sumar kansa ya tsaya yana kallonta ta madubi, yayi murmushi yakalli fuskarta yadda ta had'e fuska kamar hadari, yasan fushi take da shi saboda bai tashe ta da safe ba kamar yadda ya saba, kayansa da ya cire take tattarawa sai ji tayi an rungumota ta baya, ta k'ara had'e rai tana mai cigaba da abinda takeyi, juyo da iya yayi tana fukantarsa sai kawai ya rungumo ta tsam a jikinsa, ture sa ta shiga yi sakamakon zuciyarta ta taji tana wani irin tashi, duk Khaleel bai fahimta ba a tunaninsa duk cikin fushin ne.
Wani irin k'arfi yazo mata a sakamakon wani amai da ya taso mata ba shiri tayi toilet da gudu, ta shiga kwara amai kamar zata amayo y'an cikinta, da sauri Khaleel ya rufa mata baya, cike da mamaki yake tambayarta abinda ya sameta, ganin aman takeyi sosai ya sanya ya nufo ta, hannu ta d'aga masa cikin wata irin murya mai wahala tace
"Kar ka matso nan my only zaka 6ata jikinka"
Bai saurareta ba ya rik'e ta har ta gama, ya gyara wurin tare da jikinta. Gefen gado ya zaunar da ita yana shirin hugging d'inta tace
"Kar ka matso kusa dani my only bana son warin turarenka"
Da mamaki yace
"Yau kuma my princess? Kullum fa kece kike fesa min"
Tace
"Eh yau kam bana sonshi"
Yayi murmushi ya mik'e ya chanza kaya ko turare bai fesa ba ya zauna kusa da ita, a hankali ya rungumo ta yace
"Haka yayi miki?"
Ta gyad'a kai, yace
"Meyake damunki haka my princess?"
Tace
"Wallahi bansani ba my only"
Ya rungumo ta tsam  a jikinsa yace
"Ko asibiti zamuje?"
Ta girgiza kanta alamun a'a, yace
"Ok muje kici abinci to"
Tace
"A'a bana jin yunwa"
Yace
"Mekika ci da zakice bakijin yunwa?"
Tayi shiru yace
"Oya tashi muje"
Dole ta tashi don ta kula har ransa ya fara 6aci.

Shi ya ciyar da ita sai dai tun kafin ta gama amai ya taso mata, da gudu tayi ciki ta shiga kwara wani aman, this time mai matuk'ar wahala saboda abinda taci wato doya da sauce, da sauri Khaleel yabi bayanta, bayan ta gama ya taimaka mata ta gyara jikinta, suka fito.
Cike da damuwa Khaleel yace
"Kodai asibiti zamuje"
Tace
"A'a don Allah my only basai munje ba, k'ila 6acin ciki ne"
Yace
"Naji amma idan aman bai tsaya ba asibiti zamuje ko kina so ko bakiso"
Tayi murmushi
"Na yarda"
Kwantar da ita yayi saman k'irjinsa yana shafa  bayanta a haka har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.



MSB✍🏼

Monday, 20 March 2017

KHALEEL Page 59&60

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀


Ya Allah! I am so blessed to have sisters/friends like you, thank you all Ameemah is feeling so much better and it's because of your du'a! Alhamdulillah ala kulli halin jazakallah khairan❤️❤️❤️❤️


©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻59&60✍🏻✍🏻


Bayan sallar magriba Khaleel da Hanifah na zaune suna kallon wani movie suna fira jefi jefi, Khaleel ya kalleta yace
"Wai nikam Hanifah dama kina so kuwa?"
Da mamaki take kallonsa tace
"Wannan wace irin tambaya ce haka?"
Yayi murmushi yace
"Kawai, da nasan kin tsane ni ta yaya kika fara sona?"
Ta nok'e kai cike kunya, ya gimtse dariyarsa yace cike da zolaya
"Ay duk wannan mayen kallon da kike min ina sane da shi, k'yale ki kawai nayi"
Rufe fuskarta tayi cike da kunya tace
"Uhm"
Yace
"Allah kina son y'an mata?"
Tayi murmushi, yace
"Baki bani amsa ta ba" nan ma shiru tayi yace
"Shikenan idan har baki ce da bakinki ba nasan ba sona kike ba"
Tayi murmushi, yace
"Wai sai murmushi kike malama kiyi magana"
Ta nok'e kai tace
"Allah ina..."
Yace
"Kina mene?"
Tace
"Ina sonka mana"
Dad'i yaji marar misaltuwa ya jawo ta ta fad'o bisa k'irjinsa yace
"Thank you my baby, I love you even more"
Tayi murmushi tace
"Na tambayeka wani abu?"
Yace
"Ina jinki"
Sai kuma tayi shiru, ya jawo hancinta yace
"Fad'i abinda ke ranki ni mijinki ne, you are free to say what ever is in your mind, don't hesitate"
Tace
"Dama... Dama so nake na tambayeka dalilin da yasa kake min wulak'anci kwanakin baya"
Yayi murmushi yana shafa gashinta dake baje bisa bayanta sai k'amshi ke tashi.
"Tabbas ranar dana fara gane kin kamu da sona ranar dana kama ki kina satar kallona, da ban gasgata ba sai da na bi a hankali ina karantar ki, a lokacin dana tabbatar da zargina naji dad'i. Dalilin da yasa nayi miki haka shine ina so na gina garkuwa mai amfani a cikin zuciyarta, i want you to realize just how much you love me, and luckily you did"
Ya k'arasa yana kashe mata ido, kunya ta kamata tayi murmushi kurum. Yace
"Sorry baby nasan kin wahala lokacin amma komai ya wuce ko?"
Ta girgiza kanta tare da k'ara shigewa cikin k'irjinsa tana shak'ar dad'ad'an k'amshin da ke ratsa ta. A haka har bacci yayi awon gaba da ita, ya gyara mata kwanciya har ya k'arasa kallon da yake, sannan ya tashe ta suka je suka kwanta.


*****

Juyi d'aya tayi kan gado wanda yayi sanadiyyar bud'ewar idonta, gefenta ta kalla taga babu Khaleel a kusa da ita, tayi hamma tare da lalubo wayarta ta duba lokaci k'arfe takwas da minti arba'in da takwas 8:48 AM, da hanzari ta mik'e tana salati tayi toilet da sauri tayi brush ta wanke fuskanta ta fito. Bakin k'ofar fita taci karo da wani k'aramin card mai shape d'in heart pink color, an rataya shi a handle d'in k'ofa, anyi  mai design mai matuk'ar kyau, a bangon card d'in an rubuta "OPEN, IT'S A SURPRISE JUST FOR"
Mamaki bayyane a saman fuskanta ta bud'e card d'in taga an rubuta
"Good times become better and bad times become tolerable when shared with a life partner like you" murmushi ya su6uce mata ba shiri, lallai Khaleel sai dai a barshi, wato haka nan ya rubuto mata card lallai tayi sa'a. Ba tare da tunanin komai ba ta fito palo k'amshin turaren wuta ne kawai ke tashi a gidan, tayi tsaye tana k'are ma wurin kallo yayi fes ko ina gwanin kyau. "To waya gyara gidan haka?" Ta fad'a a hankali still tana bin ko ina da kallo, motsin da taji a kitchen ya sanya ta nufo wurin da sauri, turus tayi bakin k'ofa tana k'are masa kallo, sanye yake cikin gajeren wando mai ratsin brown da blue da blue top marar hannu, sai ya d'ora apron saman kayan, kitchen d'in yayi kaca kaca da alama aiki ya ci masa karo, kitchen d'in take bi da kallo cike da mamaki, can gefen cikin tray samosa ce  da spring-rolls sai meat-pie wanda ba'a soya ba, sai can  kaji ne an yayyanka, ta k'ara kallonsa yana yanka albasa yana hawaye, gyaran murya tayi ya kalleta da sauri yayi murmushi
"My princess har kin tashi?"
Sunan ya mata dad'i har wani narkewa tayi, ta daure tace
"Ina kwana ya Khaleel?"
Yace
"Lafiya lau my princess" ta yi murmushi tace
"Me kake yi haka?"
Ya aje wuk'ar dake hannunsa ya kalleta yace
"Mekika ga inayi?"
Tayi murmushi tace
"Aiki mana amma abinda ya bani mamaki ya d'aure min kai shine meya kawo ka nan alhalin ba aikinka bane, aiki nane"
Ya karkace kai yana kallonta yace
"To don aikinki ne sai akayi yaya? Ni nasa kaina don haka kije ki kwanta idan na gama zan kiraki"
Tace
"Wallahi bazan iya ba sai dai nazo muyi tare ko kuma kai ka fita ni zanyi"
Yayi murmushi
"Wane kikeso kiyi?"
Tace
"Nafiso ka fita zanyi"
Yace
"Ay baki isa ba kuma yarinya, amma da kinyi hak'uri na k'arasa na kusa gamawa"
Bata bashi amsa ba kawai sai gani yayi ta  shigo kitchen d'in ta kama masa suka cigaba da yi tare, ba yadda baiyi da ita ba tak'i gashi ba yaso tasan yau ne birthday d'inta, amma yayi alk'warin duk yadda za'ayi surprising nata zaiyi. A tare suka kammala komai suka jera kan dinning, Hanifah tana k'ok'arin gyara wurin tayi tsai tana kallonsa can kuma tace a hankali.
"Ya Khaleel"
Ya d'ago yana dubanta da murmushi a saman fuskansa yace
"Na'am my princess"
Tayi murmushi tace
"Bak'i zamuyi ne?"
Yace
"Eh"
Tace
"Suwaye zasu zo?"
Yace
"Wasu ne?"
Tace
"Su wa..."
"Kinga da ki tsaya kina cika ni da tambayoyi gwara kawai kije kiyi wanka ki shirya kafin su k'araso"
"To" tace bayan ta k'arasa gyara wurin ta shige ciki. Ajiyar zuciya ya sauke tare da shigewa ciki shima yayi wanka, ya shirya cikin farar shirt da ash wando, sai k'amshi yake zubawa. Cards d'in da ya siyo na birthday wishes but also romantically ya aje a saman dinning, sai gift d'in da ya siyo mata na musamman shima ya 6oye. D'akinta ya lek'a tana zaune kan stool din dressing mirror tana sanya y'an kunne, a hankali ya k'arasa tare da rufe mata fuska, k'amshinsa taji wanda ya tabbatar mata da shi d'inne. Murmushi tayi ta d'ora hannayenta bisa nashi tare da zame hannunsa a hankali daga rufe mata idon da yayi, a madubi suka kalli junansu tare da sakar ma juna da wani irin murmushi mai k'ayatarwa. Sun juma a haka, a hankali kafin Khaleel ya k'ar6e d'an kunnen daga hannunta yace
"Kawo na taya ki sawa"
Tayi murmushi bata san lokacin da tace
"Thanks my love" yace
"Me kika ce?"
Ta k'walalo idanu waje tare da rufe fuskarta tace
"Bance komai ba"
Yace
"Bawani nan ay naji ki, ki d'an k'ara maimaitawa sunan yayi dad'i"
Tayi murmushi tace
"Nace thanks my love"
Murmushi yayi ya sanya mata d'an kunnen sannan ya mik'ar da ita tsaye tare da sak'alo hannayensa ya zagaye wuyanta yana kallon cikin idonta. Yace
"I have a surprise just for you"
Tace
"What is it?"
Yace
"It's a surprise just follow my lead"
Tayi murmushi tace
"Ok"

Hannunta ya kamo suka fito daga d'akin, dinning taga ya nufa tare da ja mata kujera ya zaunar da ita, ita dai sai binsa take da kallo, shima zama yayi kan kujera suna fuskantar juna, idanunta ne suka sauka kan card d'in da ya aje mata gabanta, ta kalleshi yayi mata murmushi
"you are free to see"
Murmushi tayi ta d'auka tana karantawa, tsantsan mamaki wai yau birthday d'inta har ta manta sai Khaleel ne zai tuna mata? Ko da yake ba abin mamaki bane dama ya saba mata haka tun kafin suyi aure. Amma dai na yau special yayi mata, ta sauke ajiyar zuciya ta kalleshi yayi murmushi yace
"Happy birthday, Allah ya raya ki da imani, ya baki y'ay'a na gari, Allah ubangiji ya k'aro shekaru masu albarka ya nuna mana y'ay'an mu mahaddatan alk'ur'ani"
Tabbas addu'an nan ta mata dad'i ba kad'an ba, tace
"Amin, Amin ya Allah, thank you so much Ya Khaleel Allah ya saka da alkhairi"
Yace
"Bakomai bana son wannan godiyar, taso kizo nan ki zauna"
Ya nuna mata kan cinyarsa, ba musu ta mik'e tana zuwa ya jawota ta fad'o bisa shi, ya ja hancinta yana dariya, itama dariyar tayi. A haka ya zuba musu abinci ya shiga bata itama ba 6ata lokaci ta soma bashi, a haka suka kammala suna fira da labarai masu dad'i.
Bayan sun gama ya ciro d'an box d'an k'arami tare da bud'ewa, zobe ne silver mai kyau sai shinning yake, tana kallonsa ya zura mata a yatsanta na tsakiya, ya mata daidai kamar don ita akayi shi, ya kalleta yace
"I love you so much Hanifah, wannan zoben tukuicin k'aunar ki a gareni ne, na gode da kika soni kika k'aunace ni, banida abinda ya fiye min wannan jin dad'i a rayuwarta"
Murmushi tayi tace
"Nima haka"
Yayi dariya
"Kema me?"
Ta rufe fuskarta tana dariya tace
"Nima ina sonka"
Hugging nata yayi tsam a jikinsa yana shak'an dad'ad'an k'amshi dake tashi daga ko wane sak'o na jikinta.
She's so lucky to have a husband like KHALEEL, sai a yanzu ta soma ganin wautarta tun farko, meyasa ta k'i KHALEEL? meyasa ta k'i masoyinta na hak'ik'a har tana wulak'antasa, tabbas batada masoyi na gaskiya sama da KHALEEL, kuma ta gode ma Allah da ya nuna mata gaskiya tun kafin akai ko ina.
A haka dai masoyan suka wuni suna nuna ma junansu kulawa ta musamman had'e da soyayya mai ban mamaki.....!



MSB✍🏼

Friday, 17 March 2017

KHALEEL Page 57&58

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀


I dedicated this whole page to you Zainab Bapullo (Zee Bee) you are the best! Thanks alot much luv💖😘



©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻57&58✍🏻✍🏻


Sai da sukayi sallar isha'i sannan suka soma shirin tafiya, a d'aki Ammi tayi ma Hanifah nasiha sosai game da zaman aure duk da ta fuskanci inda d'iyartata ta dosa, kuma dama abinda ta dad'e tana fata kenan. Ammi ta mik'e ta bud'e drawer ta d'auko wata bak'ar leda ta dawo ta zauna tana kallon Hanifah. Wata kwalba ta fiddo mai farin turare a ciki tace
"Kinga wad'annan turaren Humra ne, kullum da safe idan kinyi wanka kafin ki bushe ki tabbatar kin shafe jikinki da shi, haka ma da daddare kar ki bari sai jikinki ye bushe tukunna, idan kika shafa ko wane lungu na jikinki sai ki bari ya bushe, zakiga a hankali zai kama miki jikinki koda yaushe kina k'amshi, sai ki shafa wannan man"
Ta fiddo y'ar kwalba mai fad'i, tana bud'ewa k'amshi mai dad'i ke tashi tace
"Mai ne na shafawa da akayi masa had'i na musamman da turaruka masu dad'i ya kasance shine man shafawanki, ga wannan kuma"
Ta fiddo doguwar kwalba tace
"Wannan a cikin ruwan wankanki zaki dinga d'igawa sai kiyi wanka dashi, idan sun k'are kiyi magana zansa a had'o miki da yawa"
Hanifah tunda Ammi ta fara kanta ke k'asa ta kasa d'agowa. Ammi tayi murmushi tace
"Magana ta k'arshe da zan fad'a miki shine ki rik'e mijinki Amina, ki kama shi duk wata kunya ki cire ta ki aje a gefe, ba'a ce kar ki nuna kunya ba a'a amma dai don ki faranta masa sai kin cire ta, wallahi Hanifah kafin ki samu mai sonki tsakani da Allah kamar Khaleel sai an tona, sheyasa tun tuni naso ki fahimta kika kasa, amma yanzu tunda kin gane to alhamdulillah, idan akwai wata matsala kiyi k'ok'ari ki sanar dani kinji ko? Ki tashi kuyi harama dare nayi Allah ya k'ara tsare ku ya baku zaman lafiya kinji ko?"
Hanifah ta gyad'a kai k'walla taf idonta, da k'yar ta maida su tace
"Nagode Ammi insha Allah zanyi amfani da shawarar da kika bani"
Ammi tace
"Bakomai Amina tashi ku tafi Allah yayi muku albarka kinji?"
Da k'yar tace "Amin" ta kwashi kayan da Ammi ta had'o mata tare da gyalenta ta fito.

A palo ta iske Khaleel da Saif na fira, suna ganin ta fito a shirye suka mik'e, Khaleel ya kalli Saif yace
"Ina zuwa bari nayi sallama da Ammi"
Suka ce "To"
Ba'a jima ba ya fito suka d'unguma waje, a bakin mota ma sun dad'e tsaye shida Saif suna fira sannan sukayi sallama.
Saif na tsaye Khaleel yaja motar ya bar gidan yana d'aga musu hannu.
Kafin suje gida sai da ya tsaya ya siya musu classy burger da ice cream, sai gassassar kaza.

A bakin gate Baba mai gadi ya tsaya yi musu murnar dawowa lafiya, sun jima suna fira saboda dama Baba mutuminsa ne, yakan fita haka nan ma suyi ta fira sannan ya shigo gida.
Bayan yayi parking ya fito da kanshi ya zagaya ya bud'e ma Hanifah ya jawo hannunta suka shiga cikin gida. Suna shiga parlor Khaleel yace
"Welcome home Hanifah.... Home sweet home"
Tayi murmushi tace
"Thanks dear"
Hannunta ya kama suka shige d'aki, sai da suka fara cika cikinsu sannan Hanifah ta tattara wurin ta kai kitchen, sanda ta dawo taji Khaleel na toilet alamun wanka yakeyi, itama d'akinta ta zarce, ta cire kayan jikinta ta d'aura towel, turaren wankan da Ammi ta bata ta fiddo tayi yanda tace sannan ta shiga wankanta, nan ma ta jima kafin ta kammala, duk turarukan da Ammi ta bata tayi amfani dasu, ta gyara gashinta ta tufke shi daga can tsakiyar kanta, sai k'amshi yake zubawa.
Wata rigar bacci ta d'auko ash color, y'ar ciki ce marar hannu iya gwiwa, mai sul6i sai ta saman wadda ita tanada mad'auri, bayan ta gama ta bi jikinta ta turaruka masu matuk'ar dad'i, kallon kanta take ta cikin madubi tana ajiyar zuciya.
Wayarta ce ta fara ruri, tun kafin ta d'auka ta san mai kiran saboda ringtone d'in da aka sa masa na daban ne, murmushi tayi ta d'auka.
"Hello.." Tace a sanyaye
Khaleel ya sauke ajiyar zuciya
"Har kin gama kimtsawa?"
Tace
"Eh"
Yace
"Ok ki zo ina son ganinki"
Tace
"Toh"
Bayan sun gama wayar tayi tsai kamar mai tunani, karo na farko da taji tana jin kunyar Khaleel, can kuma ta tuna maganganun Ammi suna mata yawo akai, batasan lokacin da ta fito daga d'akinta ba ta doshi d'akinsa. Tura k'ofar tayi a hankali had'e da sallama, jin shiru ya sanya ta shigewa ciki ta fara dube dube, ba zato taji an chafko ta daga baya, a tsorace ta juyo ganisa ya sanya ta ajiyar zuciya, kallonta yakeyi cikin ido itama haka, basu san adadin lokacin da suka d'auka a haka ba kafin Hanifah ta sauke idonta k'asa tare da juya masa baya dafe da k'irji, lumshe idanunta tayi tana jin wani abu yana ratsa dukkanin illahirin jikinta da jijiyoyinta, shima kansa Khaleel d'in yanayin da yake ciki baya misaltuwa, da k'yar yace
"Muje muyi sallah"
Tace
"Ay nayi isha'i"
Ya kamo hannunta ta baya ya juyo da ita tana kallonsa, yace
"Nasan kinyi amma zamu k'ara wata"
Ta sunkuyar da kanta sarai ta gane abinda yake nufi yanzu.
Ba 6ata lokaci sukayi alwalla sukayi sallah raka'a biyu bisa koyawar manzo (S.A.W) dafe goshinta yayi yayi ta jero mata addu'a ba iyaka sannan kuma yayi mata tambayoyi kan addini, nan ma ta amsa daidai kuma yaji dad'in hakan.
Kan gado ya baje yana kallonta da har yanzu tana zaune kan abin sallah yace
"Zo kiyi min tausa"
Tayi murmushi, ya d'aga mata gira d'aya yana murmushi, hannuwanta duka biyun tasa ta rufe fuskarta tana murmushi sannan ta taso jiki ba k'wai ta haye gadon. Ya kalleta da mamaki yace
"Malama wannan hijabin fa?"
Tace
"Da ita zan kwana"
Yace
"Kinyi kad'an yarinya dama ki cire ta"
Ta mak'e kafad'a a shagwa6e tace
"Ni a'a da ita zan kwana"
Hannu yasa zai cire mata hijibin ta rik'e ta gam tana dariya, aikuwa suka fara kokowa shi yana k'ok'arin cire mata ita kuma tana hanawa. Cikin kokowar ya janyota ta fad'o masa fuskarsu gab da juna har suna jin bugun numfashin junansu. Da wayau da dabara ya cire mata hijabin sannan ya jawo bargo ya rufe musu har kai tare da kashe fitila.


Asuba ta gari amarsu ta ango.... ****


Asubar fari Khaleel ya fara tashi ya kalli Hanifah dake kwance bisa fad'ad'an k'irjinsa tana bacci, shafar fuskarta yayi tare da janyeta a hankali don kar ya tashe ta, toilet ya fad'a yayi wanka had'e da alwalla, sannan ya cika kwami da ruwa masu zafi, cak ya d'aga ta tana bacci kamar jaririya ya dire ta cikin ruwan zafin nan, zogi da azaba ya sata wani irin ihu, lalla6a ta yayi kamar k'wai har ta gama gasa jikinta, tayi wanka tayi alwalla ta fito. Masallaci ya wuce a yayinda Hanifah ta fara sallarta, har gari ya d'anyi haske sannan ta linke abin sallar ta hau gado, ba'a jima ba bacci yayi awon gaba da ita.


Ba ita ta farka ba sai k'arfe kusan sha d'aya, kwance ta ganta bisa k'irjin Khaleel ya zagaye hannunsa ya rik'e ta gam, janye jikinta ta fara k'ok'arin yi amma ta kasa, fuskarsa take kallo ta ga da gaske bacci yake hankali kwance, sai kuma taji ta kasa daina kallonsa, wani sabon sonsa ke k'ara ratsa ta, ta jima tana kallonsa wanda batasan adadin lokacin data d'auka ba, firgit ta dawo daga duniyar tunani ta fara k'ok'ari d'auke hannunsa daya rik'e ta dashi.
"Idan ma tunanin tashi kike to ki daina"
A shagwa6e tace
"Don Allah ya Khaleei ka sake ni girki fa zan d'ora har rana ta fara fitowa"
Yayi murmushi still idanunsa a rufe
"Bafa inda zakije, ki koma ki kwanta kiyi bacci ki huta"
Zata k'ara magana taji ya k'ara matse ta dole tayi shiru ta rufe idonta.
Haka masoyan sukayi kwance har kusan azahar, sai da Khaleel yaji an fara kiraye kiraye sannan ya mik'e da sauri, wanka ya fara yi tukunna yayi alwalla, kafin ya wuce sai da ya tashi Hanifah itama don tayi tata sallar.


Wanka tayi, tayi sallah, ta gyara gidan tas kamar yadda ta saba. Bayan ta gama ta shirya cikin riga da skirt na english wears black skirt sai light pink top, turare kuwa kamar tayi 6arinsu, pink k'armin veil ta d'aura d'aurin ya mata kyau sosai, wasu y'an kunne masu tsawo kad'an suma pink tasa, lipstick ma pink aka sa, tadai yi kyau ba kad'an ba.
A bakin k'ofar kitchen taji an rungumo ta ta baya.
"Mey kike tunanin zakiyi?"
Tace
"Girki zan d'ora"
Ya juyo da ita suna kallon juna yace
"Ki aje maganar girki tukunna sai kin warke tas"
Tayi murmushi
"Ni na warke fa"
Yaja karan hancinta yace tare da kwaikwayon maganarta
"Ni ban yarda bafa"
Sukayi dariya gaba d'aya. Hannunta ya kamo yace
"Muje na siyo mana abinci muci"
A tare suka jera har kan dinning d'in, yau shi yayi serving d'insu, nan ma feeding juna sukeyi har suka kammala.



MSB✍🏼

Thursday, 16 March 2017

KHALEEL Page 55&56

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀


Wannna page d'in naku ne my dearies.
Hafsat Basheer, Maryam Sayaya, Fatima Bindawa, Asma'u Ammani, Hauwee Bash, Asmeen, Fatima Raiyana, Tafisuu, my dear CHUCHU, Miemiee bee,  Fakabir, Faty Ladan, Aisha Yakubu, Susu, Cutie, kawata Zee bee, 'Yar ficika, My besty Fatima Muhd Mansur.... And all members na PWF Hmmm banida bakin godiya akan yadda kuke nuna k'aunarku gareni da book dinnan nawa, nagode maku Allah ya bar zumunci❤️❤️❤️❤️❤️❤️ INA TARE DAKU💞



©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻55&56✍🏻✍🏻


K'ofar gidansu yayi parking a tare suka fito suka jera, Hanifah ta kalli gidansu wani irin dad'i na ratsa ta, hannunta Khaleel ya kamo suka kalli juna fuskokinsu d'auke da murmushi, Khaleel yace
"Shall we?"
Tace
"Yes" a haka suka soma tafiya zuwa ciki. Daga bakin k'ofar gidan suka soma knocking, ba'a juma ba aka bud'e, Halisa ce tsaye cike da mamaki da jin dad'i, da k'arfi tace
"Hanifah...!"
Mak'alk'ale ta tayi tana hawayen farin ciki, Halisa ta share hawayenta tace
"Alhamdulillah Amina! Allah shine abin godiya gaki kin dawo gida cikin k'oshin lafiya, Allah ubangiji ya k'ara tsare mu daga sharrin masu sharri ya tsarkake mana zuciyarmu"
Hanifah tace
"Amin Halisa, ina Ammi?"
"Tana ciki tana wanka tun d'azu dai ta shiga nasan yanzu ta..."
Kafin Halisa ta k'arasa magana har Hanifah tayi ciki da gudu tana kiran sunanta.
"Ammi! Ammi!! Ammi!!!"
Khaleel yayi murmushi suka soma gaisawa da Halisa tana masa barka.

Ammi tayi tsai tana jiyo muryar Hanifah na k'wala mata kira, da sauri ta doshi k'ofar fita daga d'akin, aikuwa a bakin k'ofa suka yi kaci6us Hanifah tayi tsaye tana kallon Ammi, itama Ammi tsayen tayi tana kallonta, da sauri Hanifah ta mak'alk'ale ta tana kukan farin ciki, sun jima a haka kafin Ammi ta fara janye jikinta da k'yar don Hanifah batada niyyan sakinta, Ammi tace
"Sannu Hanifah, ya jikin naki? Badai abinda ke miki ciwo ko?"
Hanifah tayi murmushi tana kallon Ammi tana share hawaye tace
"Babu Ammi, nayi kewarki da yawa"
Ammi tayi murmushi
"Dena kukan komai ya wuce, Allah ya kyauta gaba"
Hanifah tace "Amin"
Nan ta soma bata labarin abubuwan da suka faru sanda aka sace ta, bata k'arasa ba Saif ya shigo da sallama, da gudu Hanifah taje da mak'alak'ale shi wane za'a k'wace shi. Da k'yar ya 6an6are ta yace
"Y'ar autar Ammi ya jikin?"
Tayi murmushi
"Da sauk'i ya Saif, nayi kewarku"
Yayi murmushi
"Muma haka, Allah ya k'ara karewa ya tsare mu gaba d'aya"
Suka amsa da "Amin" a haka suka d'an ta6a fira ta yaushe gamo, Khaleel ya shigo Ammi tayi murnar ganinshi ba kad'an ba haka ma Saif, a d'akin suka baje suka soma fira, kowa yayi kewar kowa, Hanifah ce tace
"Ammi wanka nakeson yi"
Ammi tace
"Ay ya kamata kiyi wanka ko kya ji dad'in jikinki"
Ta kalli Khaleei tace
"Kai ma kaje kayi wanka sai kuzo muci abinci"
Duk suka mik'e, Hanifah d'akinta nada ta wuce ta shige toilet, ta d'auki lokaci mai tsawo tana tsaftace ko ina na jikinta sannan ta fito, a cikin d'akin ta iske Halisa tana aje wasu kaya set biyu ta kalli Hanifah.
"Wad'annan wasu kayanki ne da kika manta shine Hajiya ta aje miki su, nayi tunanin mancewa tayi dasu sai yanzu tace a kawo miki ki za6i d'aya kisa kizo ki ci abinci"
Hanifah tayi murmushi
"Nagode"
Halisa ta fice, su man shafawa da turare duk na Ammi tayi amfani da su, dark pink doguwar riga ta d'auko ta material bai matse ta ba sosai amma ya mata kyau, turare ta fesa kad'an sannan ta yafa d'an k'aramin pink veil.


Akan dinning ta iske kowa banda Khaleel, da alama bai gama kimtsawa ba, zama tayi ta zuba soyayyen dankali da k'wai da miyar hanta, ta soma ci, Khaleel ya fito, yayi k'al yayi fes da shi gwanin kyau, idonta akansa har ya k'araso ya zauna yana fuskantarta, shima ita d'in yake kallo a take kuma suka sakar ma juna da wani k'ayataccen murmushi mai tafiya da imanin masoya.
A natse suke cin abincin ko wane motsi nasu akan idon Saif, dad'i ne ya cika sa lallai k'anwarsa tayi hankali, addu'a yake Allah yasa su d'ore a haka ya karesu daga sharrin mak'iya. Ganin yadda suke kallon juna kamar zasu cinye junansu ya sanya Saif yayi gyaran murya, ita dama Ammi tuni ta gama ta koma d'aki don yin karatu. Shima Saif mik'ewa yayi yana dariya yace
"Bari na baku wuri naga kamar kun manta dani a nan"
Hanifah tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa a yayinda Saif ke ta murmushi yace
"Dama ya za'ayi mu tuna da kai mun sanka ne?"
Saif yace
"Yayi lover birds banga laifinku ba, amma dama ku lalla6a ku koma gida sai ku soye son ranku"
Khaleel yayi dariya
"Saif yaushe ka zama marar kunya ne bansani ba?" Saif yayi murmushi
"Ahh dama ni ina da kunyata ay"
Khaleel yace
"Kar ka damu bari Salma ta shigo zamu rama ne"
Sai a sannan Saif yayi murmushi bai k'ara magana ba.
Khaleel yace
"Tun yanzu har kayi sanyi kafin ma ta shigo?"
Da sauri Saif ya bar wurin yana fad'in
"Nidai fita zanyi idan kun gama ku tattara ku koma gidanku"
Khaleel ya d'aga murya
"Hala wurin Salma za'aje?"
Yana jiyo dariyarsa har ya fice daga gidan.


Bayan sun kammala k'wabta aka fara turarowa zuwa yin barka Hanifah ta dawo, gidan kamar ana biki ko suna, shiga kawai akeyi ana fita, dole Ammi tasa aka girka abincin rana da yawa saboda dole sai ka bada abinci, don wasu zaune sukeyi, kuma kar suce ba'a basu abinci ba, haka dai gidan ya koma kamar gidan biki. Y'an uwan su Hanifah ma sun kira sukayi mata barka sunce idan sun samu dama zasu zo.
Bayan sallar azahar Ammi ta tura Halisa ta gyare gidan ta share ta goge had'e da turaren wuta, don tace ana yin isha'i zasu tattara su koma gidansu.



MSB✍🏼

Wednesday, 15 March 2017

KHALEEL Page 53&54

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻53&54✍🏻✍🏻


Asubar fari Khaleel ya bud'e idonsa, a hankali ya d'ago da kansa ya sauke su kan Hanifah da alamu dai bata farka ba, tashi yayi ya shiga toilet yayi alwalla ya wuce masallaci.
Bayan ya kammala, ya dawo d'akin tunawa yayi wayarashi a kashe take tun jiya, kuma yasan hankalin su Ammi ba'a kwance yake ba, da sauri ya lalubo ta a aljihun wandonsa ya kunnata, message ba iyaka ya gani yawanci daga Saif ne sai na friends nasa, murmushi yayi tare da dialing number d'in sai data kusa katsewa sannan aka d'aga Khaleel ne ya soma magana
"Saif ya..."
"Ya Khaleel ka kyauta kenan?"
Saif ya katse sa, murmushi Khaleel yayi yace
"I know bro, kuyi hak'uri please ina Ammi?"
"Ka damu da ita ne?"
"Haba Saif! Ka dena irin maganar nan haka mana please bana jin dad'i" cewar Khaleel
"To meyasa ka kashe min waya jiya without any explanation? Meye na 6oye mana cewar kaga Hanifah kodai bada gaske kake ba?"
Khaleel yace
"Haba mana Saif ka tsaya na maka bayani kafin kayi fushi dani, naga Hanifah but bata cikin hayyacinta and duk yadda zan ma Ammi bayanin cewar bazata iya magana ba bazata gane ba..."
"Me kake  nufi da  ba'a cikin hayyacinta take ba?" Cewar Saif a d'an tsorace
"What I mean is that na tsince a sume shine na kawo ta asibiti, yanzu haka ma anjima kad'an zasu sallame mu da zaran ta farka"
Saif yace
"Are your she's ok?"
Khaleel yace
"Wallahi Saif lafiya lau take kawai dai suma tayi saboda rashin abinci da ruwa, but everything is going to be fine insha Allah"
Saif yace
"Alhamdulillah! Wane asibiti kuke?"
Khaleel yace
"Wata asibiti ce na gani a hanya shine na tsaya, kuma from all indication they're good ba laifi, and please kar kace zaku taho akwai d'an nisa, da an sallame mu zamu dawo straight home"
Saif yace
"If you said so, da ta farka ka kira mu muyi magana da ita please"
Khaleel yayi murmushi yace
"Kar ka damu insha Allah da ta farka zan kira, ahm ya kuka k'are da case d'in su Deen?"
Saif yace
"Suna hannun hukuma yanzu haka, anyi sorting out komai so you don't have to worry"
Khaleel yace
"Alhamdulillah Allah ya shirye su"
Saif yace
"Amin sai munyi magana anjima"
Khaleel yace
"Ok ka gaida Ammi"
Suka katse wayar.


FEW MINUTES LATER

Khaleel ne ya fito don siyan abinda zai sa ma cikinsa, bread ya siyo da Fanta ya dawo hoping Hanifah ta farka, amma unluckily bata farka ba, ya dai tarar wata nurse na zare mata drip alamun ya k'are, bayan nurse d'in ta kammala ta kalli Khaleel tace
"Drip ya k'are so idan ta farka ka sanar da doctor Ahmad don ya ganta"
Gyad'a kai yayi yayin da nurse d'in ta d'auki tray d'in maganin data shigo da shi ta fice.
Haka ya zauna ya samu yaci bread da Fanta d'in har ya ji cikinsa ya d'an cika.
Komawa yayi ya zauna kusa da Hanifah tare da jawo hannunta ya rik'e cikin nasa.
Burinshi kawai yaga ta farka amma still shiru kakeji. Kwantar da kansa yayi kamar yadda yayi da daddare har ya d'an soma bacci sama sama.

A hankali yaji ana shafa hannunsa kamar a mafarki firgit! yayi ya farka ya kalli Hanifah da idanunta ke a rufe amma hannunta na motsawa cikin nasa, da sauri ya matsa kusa da ita ya fara shafa fuskanta
"Hanifah! Ki tashi haka nan please, ki tashi ga Khaleei a kusa da ke"
Haka yayi ta mata surutai yana d'an girgiza ta kad'an kad'an, biji biji ta fara gani kafin ta bud'e idanunta ras sai akan Khaleel! Kallonsa takeyi kamar bata sanshi ba kafin a hankali tace
"Ya Khaleel?"
Cike da farin ciki marar misaltuwa Khaleel yace
"Eh nine Hanifah, Khaleel ne a kusa da ke, dad'i ya kamata take ta fara kukan farin ciki, Allah ya kub'utar da ita daga hannun Deen gata a kusa da Khaleel d'inta, neman tashi take zaune, da sauri Khaleel ya taimaka mata tare da jinginar mata da pillow a bayanta, tunawa yayi zai kira Dr Ahmad, don haka da sauri ya saki hannunta yace
"Ina zuwa Hanifah yanzu zan dawo"
Girgiza masa kai ta shiga yi
"A'a ya Khaleel kar ka sake tafiya ka barni please"
Tausayi ta basa sosai ya dawo ya zauna a kusa da ita tare da kamo hannayenta duka biyun yana kallon cikin idonta yace
"Ba inda zanje likita zan kira yanzun nan zan dawo kinji?"
Tayi narai narai da idanu kamar zatayi kuka tace
"Da gaske bazakayi nisa da ni ba?"
Yayi murmushi
"I promise you yanzu yanzu zan dawo kar ki damu kinji?"
Ta gyad'a kai tana murmushi, kiss yayi mata a goshi yace
"I'll be right back baby" daga haka ya sa kai ya fice da sauri, har ya bar k'ofar Hanifah bata bar kallon wurin ba, ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi tana murmushi, ita kanta tasan tayi missing d'insa ba kad'an ba, batak'i ya zauna tayi ta kallonsa tana jin nishad'i, sai yanzu tayi realizing ashe duk son da tace tana ma Deen  duk na k'arya ne yaudarar kanta kawai takeyi? Ta yarda ta amince cewar tana k'aunar Khaleel, bazata iya kwatantawa ba.

Shigowar su ya katse mata tunani, Dr Ahmad na gaba Khaleel na biye da shi a baya, Dr Ahmad ya k'araso yana murmushi
"Madam an farka kenan?"
Hanifah tayi murmushi, Dr Ahmad yace
"Good haka akeso" ya kalli Khaleel
"Ka tabbatar taci abinci da ruwa sosai kafin ku bar nan, it's very important"
Khaleel yace
"Insha Allah doctor"
Dr Ahmad yace
"Good, zan turo nurse da takardar sallama, sannu ko Allah ya k'ara sauk'i"
Khaleel yace "Amin" daga haka Dr Ahmad ya fice.

Dama Khaleel ya siyo sabon  brush da Maclean Guda biyu, yayi amfani da d'aya, fito da d'ayan yayi ya sanya mata maclean d'in akai ya kamo hannunta.
"Muje nayi miki brush, sai kiyi alwalla ki rama sallolin da ake binki"
Murmushi tayi tana kallonsa shima ya mayar mata, hannunta ya kama ya mik'ar da ita tsaye, a hankali suka soma tafiya zuwa toilet d'in, da kansa yayi mata brush d'in sannan tayi alwalla suka fito. Khaleel na zaune yana kallonta tana sallanta a natse har ta kammala, bayan ta gama addu'ointa ya taimaka mata ta zauna kan gado. Fridge ya bud'e ya fito mata da fruits d'in da ya siyo mata da robar SWAN, haka yayi ta lalla6a ta yana bata har ta sha da yawa, nan ma sai da ya tilasta mata tasha ruwan sosai kusan rabin roban tasha. Sannan ya k'yaleta. Suna gamawa bada jimawa ba nurse ta shigo da takardar sallama ta mik'a masa yayi godiya.
Bayan fitarta Khleel ya kira number d'in Ammi, bugu biyu a na ukkun ta d'auka tace
"Khaleel ya kuke? Ina Aminatun?"
Yayi murmushi
"Lafiya lau Ammi, gata nan kuyi magana"
Ya mik'a mata wayar
"Hello Ammi"
"Hanifah! Alhamdulillah, ya jikin naki hope babu abinda ke damunki?"
K'walla taji sun tarar mata da k'yar ta had'iye kukanta tace
"Alhamdulillah Ammi lafiyata lau, nayi missing d'inku"
Ammi tayi murmushi
"Muma haka yaushe zaku taho?"
Hanifah tace
"Yanzu insha Allah an sallame mu"
Addu'a Ammi ta shiga jera mata ba iyaka wanda ya karyar mata da zuciya, kuka ne ya k'wace mata so take kawai taga Amminta tayi missing d'inta sosai.
Da sauri Khaleel ya taso yana fad'in
"Haba Baby meye na kuka kuma? Stop crying komai ya wuce kinji?"
Batasan lokacin da tayi hugging nasa sosai tana kuka, hugging d'inta back yayi yana ta rarrashinta da k'yar ya samu tayi shiru.
Hannunta ya kama suka fito daga d'akin, ya tsaya ya biya kud'ad'en da ake binsa sannan suka fito.
Da kansa ya bud'e mata mota ta shiga a yayinda ya zagaya ya bud'e mazaunin driver. Cikin nutsuwa yake tuk'insa sunyi nisa sosai Hanifah bacci ya kwashe ta, gyara mata kwanciya yayi yana kallonta murmushi shimfid'e a saman fuskansa. A haka suka iso cikin garin Kaduna.




MSB✍🏼

Tuesday, 14 March 2017

KHALEEL Page 51&52

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀


Wannan page d'in naku ne members na HAUSA NOVELS na CHUCHU, RAFF and FATIMA MANSUR thanks for the love... Masu k'orafi bana typing da wuri suma suyi hak'uri kunsan Dan Adam ajizi ne bayan haka akwai hidimar da ta sha mana kai bako da yaushe muke samun time ba, a dinga yi mana uzuri please❣❣❣



©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017💎


              PAGE


✍🏻✍🏻51&52✍🏻✍🏻


Haka ya cigaba da tafiya yana k'wala mata kira amma shiru kakeji, k'ark'ashin wata bishiya ya zauna don ya huta, idanunsa suka sauka kan wani zobe na Diamond mai kyau sai shinning yake, d'auke zoben yayi yana jujjaya shi yana tuno ranar tun kafin suyi aure ya siyo ma Hanifah shi ranar ya gama karatunshi da zai dawo ya tsaya ya siyo mata, amma da k'yar ya samu ta sashi a hannunta cewa tayi bataso ashe har yanzu yana hannunta bata cire ba? Hakan ya tabbatar masa da cewar Hanifah na kusa da shi.
Murmushi yayi ya damk'e zoben gami da turawa cikin aljhun gaban rigarsa. Sai da ya d'an huta na kamar minti d'aya sannan ya mik'e ya soma tafiya yana kiran sunanta da k'arfi.
Haka yayi ta tafiya yana kiranta har rana ta kusa fad'uwa, wata irin yunwa yakeji marar misali, haka nan dai yake daurewa, da yayi nisa sai ya huta haka yakeyi.

Hanifah kuwa tafiya tayi tafiya, tun tana ganin biyu biyu har tazo ta fara ganin duhu, duniyar gaba d'aya juya mata takeyi, daga k'arshe ta zube nan ji kake tim!

*****

Gari har ya d'an fara yin duhu alamun magriba ta gabato, Khaleel ba inda bai bi ba, ko wace hanya ya hango sai ya bi kozai dace amma bai ganta ba, Khaleel ya rasa inda zai sa ransa yaji dad'i, ya kira Saif ba iyaka ko an dace amma amsa d'aya ce BA'A GANTA BA.
A gajiye ya soma tafiya inda ya ajiye motarsa don zai gwada wani wurin kuma tunda nan d'in bai ganta ba, sam yama fidda ransa da ganinsa a nan kusa shidai fatanshi Allah yasa tana raye kuma lafiya lau.

Daga nesa nesa ya dinga hango mutum kwance k'asa, da kamar ba zaije ba amma wata zuciyar tace masa yaje yaga ko menene, addu'a yayi ya doshi wurin gab da ita ya tsaya tare da lek'awa a razane yayi baya not believing what he saw, yama kasa k'wak'waran motsi, sai dai yayi gathering courage nasa tukunna ya matsa gabanta ya k'ara tabbatar da abinda idanunsa suka gane masa, tabbas ita d'in ce Hanifansa ce kwance! Farin ciki marar misaltuwa yaji, zubewa yayi bisa gwiwowinsa tare da jawota bisa cinyarsa, yana fad'in
"Hanifah! Tashi nine Khaleel, bud'e idonki ki ganni nine a kusa da ke"
Still ko motsi batayi ba, kallonta yakeyi a d'an tsorace yana fad'in
"Kar dai kin mutu Hanifah! No! Insha Allah baki mutu ba"
Yana fad'in haka yana shafa fuskanta cike da So da K'auna! Rungumeta yayi k'yam a jikinsa kamar za'a k'wace masa ita yana ta wasu surutai wanda bana gane meyake fad'i.
Daga k'arshe ya mik'e tsaye, cak! Ya d'auke ta kamar jaririya ya soma tafiya, tafiya yayi mai d'an nisa sannan ya iso inda motarsa take, bud'ewa yayi gami da bud'e bayan motar ya shimfid'e ta ya rufe, mazaunin driver ya zauna ya d'auko wayarsa ya kira Saif, bugu d'aya ya d'auka
"Ya Khaleel har yanzu baka dace ba? Ka hak'ura ka dawo gida in yaso na maka alk'awari gobe zan raka ka mu duba..."
"Saif na ganta!" Khaleel ya katse sa
Saif yace
"Me kace?"
Yace
"Na ganta Saif naga Hanifah yanzu"
Ya fad'a cike da farin ciki, Shima Saif cike da farin ciki yace
"Da gaske Ya Khaleel? A ina ka ganta? Bani ita muyi ma..."
"Hello Khaleel anga Aminatu wai?"
Cewar Ammi wadda ta k'wace wayar daga hannun Saif, k'walla yaji yana neman zubo masa yadda yaji muryar Ammi har rawa takeyi, daurewa yayi yace
"Na ganta Ammi, amma don Allah ki kwantar da hankali zan kawo miki ita gida kar ki tada hankalinki..."
"Bani ita Khaleel, bani inyi magana da ita shine kad'ai zan samu kwanciyar hankali"
Cewar Ammi
Khaleel yace
"Ammi ki kwantar da hankalinki tunda nace an ganta an ganta d'in, sai na kawo ta"
Daga haka ya kashe wayar gaba d'aya saboda yasan muddin bai kashe ba to zasu sake kiransa, tunda yanzu yasan babu ta yadda za'ayi suyi magana da Hanifah.
Tada motar yayi a hankali ya soma tafiya, yana tafe motsi kad'an zai lek'a yaga da gaske dai tana nan kuma bata tashi ba, a haka ya d'anyi tafiya mai nisa, wata asibiti ya hango daga bakin hanya ba 6ata lokaci yayi parking ya fito, bud'e baya yayi ya fito da Hanifah sannan yayi ciki da ita da sauri, k'aramar asibiti ce, wata nurse ya gani inda ya sanar da ita yana neman taimako, itama ba 6ata lokaci suka anshi Hanifah sukayi ciki da ita da sauri, Khaleel yaso shiga suka hana dole yaja ya tsaya.
Yana tsaye ya had'a tagumi wani doctor yazo ya wuce da nurse biye dashi a baya, duk yadda Khaleel yaso yayi magana dasu ya kasa, dole ya hak'ura ya zauna.

Bayan minti goma likitan ya fito inda Khaleel ke zaune, da sauri Khaleel ya mik'e ya fara tambayarsa ya Hanifah, doctor d'in yayi murmushi tare da ba Khaleel hannu suka gaisa, sannan yace masa
"Sunana Doctor Ahmad, na duba patient d'inka yanzu, well kar ka tada hankalinka she will be fine, kawai dai is like she is dehydrated ma'ana tana buk'atar alot of fluid a jikinta, banda wannan ma tana buk'atar abinci gaskiya is like tayi days ba abinci, so zan aje ta a nan for observation just drip d'aya ya isheta sai kayi k'ok'ari ka bata alot of fluid kamar su fruits da ruwa sosai, amma bayan nan babu wata matsala. So tana nan mun bata d'aki ga wannan"
Ya mik'a masa wata paper
"Magungunan da take buk'ata ne da drip d'in da za'a sa mata ka hanzarta ka kawo don a fara sa mata"
Khaleel ya maida numfashi
"Mun gode doctor amma yaushe kake ganin zata farka?"
Doctor Ahmad yayi murmushi
"I can't say gaskiya koda yaushe ma zata iya tashi ay she's alright, kai dai kawai ka tabbatar kana bata ruwa yadda ya kamata, and idan ta farka ta samu ta ci wani abu ko yaya ne"
Khaleel yace
"Insha Allah mun gode doctor"
Sukayi musabaha Khaleel ya wuce pharmacy ya siyo magungunan da ake buk'ata, sannan ya biya kud'in d'akin da aka kwantar da ita, luckily ma akwai y'an kud'ad'e a tare da shi da baisan yadda zaiyi ba.
Bayan nurse d'in ta jona mata drip d'in Khaleel ya tambaya ina ne masallaci, aka nuna masa kai tsaye can ya wuce yayi alwalla yayi sallolin da ake binsa ya dad'e yana addu'a.
Bayan ya fito zarcewa yayi ya nemo inda ake siyar da fruits, kankana ya siyo mata da lemo (orange) sai ayaba. A lokacin da ya koma k'arfe tara da kwata 9:15 PM.

Tura k'ofar d'akin yayi a hankali ya shiga, tana nan kwance yadda take bata motsa ba, ajiye kayan yayi cikin d'an k'aramin fridge d'in da ke d'akin sannan ya jawo wata kujerar roba da aka ajiye musamman saboda mai jinya, k'ura mata ido yayi kamar bai ta6a ganinta ba, kafin ya jawo hannunta ya rik'e cikin nasa gam, kayan jikinta tun wanda ta saka ranar da abin ya faru ne wata doguwar riga ta material sai hijabi kalar kayan.
Ya sauke ajiyar zuciya yana cigaba da kallonta, gashi ga Hanifanshi a kusa dashi, a hankali ya furta
"I missed you so much my baby"
Kwantar da kansa yayi gefen gadon still hannunsa cikin nata, ya jima a haka kafin bacci ya sace sa...




MSB✍🏼