Monday, 6 March 2017

KHALEEL Page 43&44

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️



Wannan page d'in naku members d'in Hausa novels na Chuchu ❤️❤️❤️


           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻43&44✍🏻✍🏻



Kallonta yakeyi na y'an dak'ik'ai sai kuma can komai ya tuna ya sa kai ya shige d'aki.
Hanifah haushi kamar ya kashe ta, sum sum ta koma d'aki tana sak'e sak'e a ranta, wannan wace irin masifa ce!
Daren ranar da k'yar bacci yayi awon gaba da ita.

*****


Ranar da Hanifah zata zana Jamb d'inta, ta tashi ta shirya, Khaleel ya sauke ta da misalin takwas na safe da tabbacin idan ta gama ta kirashi, don motarta na wurin gyara.
Cikin ikon Allah kuwa ta gama, sai ta d'an fito waje tare da dialing d'in number d'insa. Bugu biyu ya d'auka ta sanar dashi ta gama, yace gaya nan zuwa.
Wata irin rana akeyi mai zafin gaske, ga k'ishi tana ji sosai, wani shago ta hango ana saida ruwa gaba kad'an, da sauri ta doshi shagon.
Da k'yar ma ta samu kasancewar ba masu sanyi sosai haka nan dai ta siya don kora k'ishirwa, tana cikin tafiya ba zato sai ji tayi an fesa mata wani abu a fuska, tayi taga taga ta fad'i tim k'asa! Matan da ke sanye cikin bak'aken kaya da nik'abi su biyu suka kinkime ta ganin ba mai ganinsu yasa suka tura ta motar da suka zo da ita. Take suka kira ogan nasu suka ce sun kama yarinyar.
Daga can 6angaren ya fad'a musu wata magana suka ce.
"Yes mungane angama"


Tafiya suke mai d'an nisa, kamar ma sun d'an bar gari, gidan shi kad'ai ne wurin sai dokar daji dake zagaye da gidan, suna zuwa mai gadi ya wangale musu gate, gidan kamar incomplete gida ne, haka suka shiga da ita, suna tsayawa suka kinkimo ta kasancewar batasan inda kanta yake ba, suka shiga da ita ciki,  wani d'aki ne bakomai ciki sai tabarma ko fitila baida shi bare ma wani abin more rayuwa. Wayarta suka d'auke dake yashe k'asa
Kwantar da ita sukayi sannan suka fito suka datse d'akin da kwad'o kamar yadda yayi musu umarni.


Bayan awa kusan d'aya Deen ya k'araso shida mutanenshi mugaye irinshi, matan da suka d'auko Hanifah suka iske suna gadin ta daga waje, hannu ya mik'o musu da sauri suka mik'a masa wayarta, sannan yayi musu umarni  su bud'e masa k'ofa, ba musu suka bud'e, sannan yace kowa ya jirashi waje.
Kwance take yadda aka aje ta, ruwan sanyi aka d'auko masa ya shiga kwarara mata shi a fuska, a gigice ta farka tana salati, tana murza ido tana k'are ma wurin kallo cike da fargaba, a hankali ta tashi zaune tana ware idanu, ganin mutum zaune a gabanta yasa ta fara kyarma tana cewa.
"Ina ne nan? Waya kawo ni? Ina Khaleel?"
Deen ya daka mata tsawa
"Ke!!! Ki nutsu nan ki saurare ni kina jina?"
Ta ware idanu sosai tace
"Deen!"
Ya k'yalk'yale da dariya yace
"Yess nine nan my love..."
Cike da jin haushi tace
"Kar k'ara kirana da your love, tukunna ma me nakeyi a nan?"
Yana tafa hannyensa yace
"Wow princess, har kin manta son da kike min...?"
Ta fasa wata itin giggitaciyar k'ara tana fad'in
"Ya Khaleel kana ina? Kazo ka cece ni daga   wannan mugun marar iman..."
Tass!! Taji an wanke ta da mari, tuni idanunta sun kawo ruwa, ta soma kuka tana cigaba da surfa masa zagi.
Yayi murmushi yace
"Duk ki gama haukanki, dole ne ki rabu da mijinki nine nan zan aure ki my love..."
Duk da tana jin tsoro amma hakan bai hanata magana ba
"Tirr Allah ya tsare ni da auren mugu kamar ka, nayi dana sanin saninka a rayuwata! Ashe dama haka kake?"
Yayi wata arniyar dariya yace
"It's too late baby"
Sai kuma ya mik'e tsaye yace
"Ga wayarki nan, anjima zan dawo ki kira min mijinki akwai abinda zan fad'a masa, feel at home"
Yasa kai ya fice ganin haka yasa ta taso da gudu amma kafin ta iso har sun rufe, haka ta dinga buga k'ofar tana ihu iya k'arfinta, sai data gaji don kanta ta zube nan tana kuka mai tsuma zuciya, ba wanda take kira sai Khaleel d'inta.


*****

Khaleel kuwa wuri ya samu yayi parking a bakin gate d'in makarantar, minti d'aya shiru, minti biyu shiru, har dai kusan minti goma shiru baiga Hanifah ba, hakan yasa yayi tunanin ko tana ciki, sai kawai ya fito daga motar ya lek'a cikin makarantar, amma abin mamaki baiga alamun Hanifah ba, ya zagaye makarantar kaf amma bata nan, hankalinsa ya fara tashi, ya fito daga makarantar ya fara tafiya a k'afa yana waige waige yana kiran sunanta, amma ko mai kama da ita babu, bai gaji ba yayi ta tafiya yana tambaya amma kowa sai yace masa bai gane ta ba, wasa wasa sai da Khaleel ya zagaye unguwar kaf amma ba alamun Hanifah.
Wayarsa ya lalubo amma baiganta ba, ya tuna ashe tana mota, gudu gudu haka ya isa inda motarsa take, ya d'auko wayar yayi dialing amma har ta tsinke ba'a d'aga ba, ya sake kira a karo na biyu ba'a d'auka ba, haka yayi ta kira amma ba'a d'auki wayar ba, nan fa hankalin Khaleel ya tashi sosai, ya k'ara shiga cikin makarantar ya k'ara dubawa amma still bata nan.
Fitowa yayi hankali tashe yana kalle kalle ko zai ganta amma shiru, hakan yasa ya yanke shawarar kiran Ammi ko taje gidan. Nan Ammi ta d'auka har take tambayar ya Hanifah, nan ya tabbatar da lallai bata je can ba.
"To ina zataje?" Sanin Hanifah bata zuwa ko ina. Cikin zubar k'walla yace
"Kina ina Hanifah? Gida? No! Bata gida ay ta kirani tace min ta gama to ina kike?"
Da sauri ya shiga mota ya tafi gidan, tun daga bakin gate ya tambayi mai gadi ko tazo nan, maigadi yace sam tun d'azu yake nan ko kare bai wuce ba. Hankali tashe ya shiga mota, a guje ya bar unguwar, ya shiga nemanta, duk inda yake tunanin taje sai da ya duba, amma ba labarinta. Baya so yaje masu Ammi da zancen nan don baiso hankalinsu ya tashi, sai dai ya zama dole yaje d'in k'ila akwai shawarar da zasu bada.


A sanyaye ya kama hanyar unguwa, yana yin parking ya fito, idanunsa kad'ai sun isa bada amsar Khaleel na cikin wani hali, don idanunsa sun rikid'e zuwa ja! Ya tsaya bakin gate d'in yana wani jin zafi a k'irjinsa, he can't believe Hanifah ta 6ata, abin da mamaki, to ko sace ta akayi? Ya kamo sumar gashin kansa yayi squeezing yana matsar k'walla. Da k'yar yayi gathering courage nasa ya sa kai ya shiga ciki.
Zaune ya iske ta tana karatun littafin Qur'ani, da sallama ya shiga, sai da ta kai aya sannan ta d'ago tana kallonshi, aje littafin tayi tana k'are masa kallo, lokaci d'aya ta gano da akwai matsala, tashi tayi tsaye tana fad'in
"Kai lafiya ka shigo kana kuka?"
Bai iya magana ba sai ma wuri da ya samu ya zauna, nan hankalin Ammi ya tashi ta soma tambayarshi lafiya, da k'yar ya bata labarin halin da ake ciki.
Itama Ammi salati ta soma yi a lokacin kuma Saif ya fito daga d'aki shima, nan suka fara jimani kafin su san abinyi.
Saif tashi yayi yace
"Bari na bi unguwar nan gaba d'aya nagani ko za'a ganta"
Da gudu Halisa ta bisa
"Muje na taya ka nema"
Haka suka k'arasa wahalarsu har magrba ta gabato amma basu ganta ba.
Haka suka dawo jiki a sanyaye idanun Saif sun kad'a sunyi ja, sun rasa abinyi!


*****

Kwance take tana kuka mai tsuma rai, taji alamun bud'e k'ofa, Deen ne ya shigo hannunsa d'auke da abincin take away, zama yayi ya bud'e mata yace
"Tashi kici abinci"
Tayi banza da shi, ya daka mata tsawa
"Ki tashi nace!"
Batasan sadda ta tashi ba jikinta na rawa, hawaye kuwa kamar an bud'e pampo haka yayi ta kwarara. Ta kalleshi da rinnanun idanunta tace
"Na k'oshi"
Yayi dariya
"Ke kika sani, tashi kugani inyi aikin dake gabana" wayarsa ya mik'a mata yace
"Bani number mijinki"
Tayi shiru tana sheshekar kuka. Bindiga ya d'auko daidai saitin kanta ya sa mata yace
"Bani ko na tarwatsa miki k'walwa"
Jiki na rawa ta shiga sanya masa number d'in, bugu d'aya ya d'auka...."


MSB✍🏼

No comments: