Tuesday, 14 March 2017

KHALEEL Page 49&50

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻49&50✍🏻✍🏻


Fakar idonsa yayi ya duk'a gami da d'auko bindigar ya rik'e ta gam gam, yayi ma Deen irin kallon sai na koya maka hankali sannan ya mik'e, ba zato Deen yaji wani abu a kansa, a hankali Khaleel ya tako ya tsaya a gaban Deen da bindigar daidai saitin kan Deen, a razane Deen ya fara zaro idanu yana kallon Khaleel a tsorace, wanda sanadiyar hakan har wani kyarma yakeyi, duk yabi ya tsure. Khaleel fuska d'aure yace
"Zan baka za6i biyu, cikin biyun ka za6i d'aya, na farko! Muje ka kaini inda ka 6oye Hanifah na d'auke ta salin alin ba tare da wani tashin hankali ba. Na biyu muje na kaika wurin y'an sanda su suka san hukuncin da yace suyi maka, na baka second goma ka za6a, in ba haka ba banida wani choice illa na mik'a ga hukuma"
Deen bakinsa har wani kyarma yakeyi yace
"Na yarda zan... zan kaika inda na 6oye Hanifah"
Dad'i ya ziyarci Khaleel yace
"Muje kuma kai zaka tuk'a"
Haka suka shiga mota, bindigar na hannun Khaleel yana basa tsoro da ita, har suka iso gidan. Bayan ya tsayar da motar Khaleel ya kallesa da mamaki yace
"Wannan gidan waye ka kawo min mata?"
Deen cikin tsoro yace
"Wallahi nima bansani ba"
Khaleel ya mak'e kafad'a alamun oho, a tare suka fito Khaleel ya finciko masa wuyan riga ga bindiga saitin kansa haka suka shiga ciki.
Koda isarsu d'akin ya duba ba matar nan sai ya shiga k'wala mata kira.
"Omotola! Omotola!!!"
Shiru kakeji, hakan yasa suka wuce d'akin da aka aje Hanifah kai tsaye don dama yana da key d'insa a hannu, a bakin k'ofa suka yi turus, d'akin bud'e ba Hanifah ba alamarta, nan Deen idanu suka fara raina fata, a fusace Khaleel yace
"Ohh dama raina min hankali kakeso kayi yasa ka kawo ni nan ko?"
Deen yace
"Wallahi, na rantse da Allah a nan na kawo ta na aje"
Khaleel ya k'ara danna masa bindgar a kai yace
"Ina take toh? Nace tana ina zan harba fa!"
"A'a kayi min rai kar ka kashe ni wallahi tallahi nan na kawo ta, bansani ba k'ila ko guduwa tayi wallahi iyakar gaskiya ta na fad'a maka"
Cewar Deen kamar zaiyi kuka. Khaleel ya finciko sa suka fito waje ya yasar dashi k'asa tare da gyara bindigar alamun zai harba, Deen ya runtse idanunsa yana jiran yaji shi a lahira don yadda yake ganin idanun Khaleel shi kansa ya ji tsoro.
Khaleel yace
"Last chance! Zan baka dama ta k'arshe ka fad'i min inda matata take"
Deen kamar zaiyi kuka yace
"Wallahi Allah nan na kawo ta daga nan ban san ina take ba wallahi"
A fusace Khaleel ya saita masa bindigar, Deen ya rufe idonsa gam gam yana hawaye, k'arar bindigar da suka jishi har cikin k'walwarsu, Deen yama d'auka shi aka harba har ya sadak'as, sai da yaji baijin wani ciwo sannan a hankali ya bud'e idanunsa ko wane 6angare na jikinsa rawa yakeyi, wata k'ila ma har fitsarin wando yayi waya sani!
Idanunsa suka sauka kan fuskar Khaleel da ke tsaye da bindigar a hannunsa tana hayak'i alamun anyi harbi da ita, Khaleel kuwa kamar wani soja, ko alamun d'ar babu a tattare da shi amma fuskar nan tasa a d'aure kamar bai ta6a dariya ba. Khaleel yace
"Wannan kad'an ne daga cikin harbin da na tanadar maka muddin baka fito min da Hanifah ba, akace maka nayi kama da kalar mutanen da zaka raina ma hankali ne? Na baka minti biyar ka fito da idan ba haka ba, zaka sha mamaki"
Deen yama rasa me zai ce masa ya yarda, bai ta6a tunanin Khaleel is brave enough da zai iya tsorata sa ba. K'ara fincikosa Khaleel yayi a fusace yana nuna masa bindiga, tsorata kam Deen ya gama yinta sannan jikinsa yayi mugun sanyi, baisan wace kalma zai iya amfani da ita wajen fahimtar da Khaleel cewar banda nan d'in baisan inda take ba. Khaleel yace
"Na lura taurin kai kakeson nuna min to muje na mik'a ka hannun hukuma, su zasu saka ka fad'i gaskiya ay"
Haka ya shiga jansa yana tirjewa har suka fito wajen gida, turus suka tsaya cike da mamaki kowanensu ya kasa wani k'wak'waran motsi, Khaleel ne yayi k'arfin halin cewa
"Saif... Ta yaya kuka zo nan?"
Kafin ya bashi amsa idanunsa sun sauka kan motar y'an sanda guda biyu, fitowa y'an sandar suka shiga yi d'aya bayan d'aya ko wace mota akalla tana d'auke da polisawa biyar biyar majiya k'arfi. Tsaye sukayi sun zazzagaye su Khaleel, Khaleel ya k'ara tambaya a karo na biyu
"Saif ya akayi kuka san muna nan? Please kayi min magana mana"
Saif yayi murmushi yace
"Yaya kenan, wai a tunaninka zanje nayi zaune ne ba'a ga Hanifah ba sai kace wanda baisan inda ke masa ciwo ba? Kana sa k'afa kana tahowa nima na bar gida, ban zame ko ina ba sai office d'in y'an sanda na kai report, kuma alhamdulillah sun taimaka sosai yanzu bada jumawa zaka ga d'aya daga cikin nasarar da muka samu a yau d'innan"
Saif ya kalli d'aya daga cikin y'an sandan yace masa
"Fito da shi"
Da sauri police d'in ya juya ya bud'e mota ya jawo wani mutum hannunsa ansa masa ankwa. Jawo shi sukayi har gaban su Khaleel sai a lokacin Deen ya kalle shi, a razane yace "Tboy!"
Tboy yayi murmushi
"K'wari nine maci amana kawai, kaganni nan nine na tona inda kake, wai har ni zaka yaudara, nawa nake binka tun jiya nake kiranka kak'i d'auka, k'arshe ma ka turo man message d'in cin mutunci, to nima gani nayi ga dama ta samu da zan rama abinda ka min shine na tona inda kake, har ni zaka ci amana ta duk da taimakon wa kake cimma burinka..."
"Kai ya isa haka mana!" Saif ya katse sa, Deen kuwa magana ya kasa saboda bai da abin cewa sai dai wani mugun kallo yake bin Tboy d'in da shi. Saif ne yayi umarnin a maida Tboy a mota inda kuma Fahad ya fito yana ma abokin nasa wani mugun kallo har ya k'araso inda yake, da sauri Deen yace
"Fahad..."
Fahad ya d'aga masa hannu
"Ba ruwana da kai daga yau Deen, ashe haka kake? Mugu azzalumi! Ka d'auko d'iyar mutane matar aure fa Deen, bakada hankali? Ka bani mamaki ka bani haushi, ban ta6a tunanin zaka aikata aiki makamancin wannan ba, ka cuci d'iyar mutane ka zalunci mijinta kuma kasani Allah bazai ta6a k'yaleka ba"
Deen yace
"Haba Fahad! Ko kowa ya juya min baya bai kamata kai ka juya min ba, banida amini tamkar ka, ka yafe min dan Allah"
Fahad ya d'aga masa hannu
"Ka daina had'a ni da abinda yafi k'arfina, ni nayi iyakar k'ok'ari na Allah ma yasani, don naga ka saitu amma ina bakaji Deen, to kasani na fad'a ma Hajiya (mahaifiyar Deen) kuma tayi mugun fushi da kai tace su kulle ka ta bada goyon baya har sai ka nutsu ka dawo cikin hankalinka"
Yana gama fad'ar haka ya juya ya koma mota don baya son ganin ana sa ma Deen ankwa.
Khaleel ba bakin magana jikinsa ya mutu mututus, har yanzu baiji ance anga Hanifah ba, Saif yace
"Ku kama shi"
Deen baiyi wani yunk'uri ba sai ma da kansa ya mik'a hannu aka kafe masa ankwa sannan suka tura shi motar da Tboy ke ciki.
Saif ya kalli y'an sndan yace
"Kuyi gaba gamu nan zamu biyo ku yanzu"
Ba musu suka soma shishiga motocin su daga bisani suka tada jiniya, haka suka jeru suka tafi.

Saif ya tako inda Khaleel ke tsaye ya dafa sa, yace
"Ya Khaleel kazo mu tafi yanzu kuma mu fara neman Hanifah"
Khaleel ya kalli Saif yace
"Kaje Saif idan har kaga na bar dajin nan to sai da Hanifah, don inada tabbacin duk yadda akayi tana kusa da nan inaji a jikina"
Saif yayi murmushi mai ciwo yace
"Nasan da haka amma kazo muje idan muka had'u gaba d'aya yafi"
Khaleel ya dafa sa had'e da girgiza kansa yace
"Ka dena 6ata lokacinka Saif tunda nace kaje, kaje kawai ba abinda zai sameni insha Allah, zan nemi matata na dawo da ita gida, kayi ma Ammi bayani"
Saif baya son jan zance yasa kawai yace ya amince suma can zasu cigaba da nema, musabaha sukayi Saif yace
"Good luck bro"
Khaleel yayi murmushi yace
"You too"
Yana kallon Saif ya shiga mota ya tada har ya 6ace masa. Tsaye yaya yana nazari kafin ya duba agogon wayarsa, ya salam! Uku da minti sha shidda 3:16 PM, komawa yayi cikin gidan ya samu ruwa ya d'auro alwalla, yayi sallah sannan ya fito ya shiga motarshi ya zauna, ruwan robar da yazo da ita da biscuit su ya d'auko yaci ya sha ruwa, bayan ya gama ya kalli gabas kudu da arewa, sai kawai ya yanke shawarar bin gabas, addu'a yayi sosai kafin ya tada motarsa ya fara tafiya.


*****

Hanifah kuwa tunda ta fito daga gidan take gudu sosai, sai da tayi gudun kusan rabin awa taji bazata iya cigaba ba, wata bishiya ta zuba k'asanta tana maida numfashi, ta gaji sosai banda yunwa ga k'ishirwa tana ji, sai da ta d'an huta sannan ta mik'e da k'yar tana tafiya kamar zata fad'i. Burinta da addu'arta taga koda titi ne tasan yadda zata gida. Haka tayi ta tafiya amma bataga titi ba, duk tafiyar da takeyi jinta take cikin daji ga ba mutum ko k'wara d'aya, da k'ila ta samu wani koda tambayarsa tayi tasan zai taimaka mata.
Haka ta cigaba da tafiya duk da ta gaji amma ta daure haka nan, k'afuwanta har wani zogi suke mata gashi ba takalmi k'afanta.
Tafiya kam tasha ta har ta gode Allah, ita kad'ai tasan mai takeji saboda gajiya, dama zata samu inda zata kwanta da tayi bacci, ina ace ya Khaleel d'inta na kusa da ita da taji d'uminsa, take kuma taji k'walla na neman zubo mata, tayi missing Khaleel bazata iya kwantata yadda takeson sashi a idanunta ba.



*****


Sai da Khaleel ya doshi dajin sannan yayi parking daga gefen hanya, fitowa yayi ya fara tafiya yana waige waige kozai ganta amma wayam!
Kutsawa yakeyi cikin jejin nan yana kiran sunanta, ji yake kamar ya rufe idonsa ya ganta gabansa da yafi kowa farin ciki, yana son sa Hanifah a idanunsa fiye da tunanin mai karatu,  yana tafe yana tuna lokacin da take nuna masa zallar so, murmushi kawai yakeyi shi kad'ai yana tafiya. Suna k'aunar junansu gashi yanzu sunyi nisa da juna!
Ya nitsa cikin dajin sosai yana tafe yana k'wala mata kira da dukkan k'arfin da Allah ya bashi.


MSB✍🏼

No comments: