π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
ππππππ
π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
©PERFECT WRITERS FORUM
(P.W.F)❤️
Duk wanda ya mik'o min sak'on ta'aziyarsa nagani kuma naji dad'i sosai, nagode Allah ya bar zumunci, da duk ma wanda yayi min addu'ar fatan alkhairi ya iso gareni, Allah ya saka da alkhairi one loveπ
πππππ
*KHALEEL*
πππππ
Written by Maryam S bello {MSB}✍π»
http://MaryamSBello.blogspot.com
March 2017π
PAGE
✍π»✍π»39&40✍π»✍π»
Da asuba bayan ta gabatar da sallah, gidan ta gyare tas harda su turaren wuta da freshener aka sanya, sai tayi wanka kamar kullum ta shirya cikin wata purple and dark blue atamfa, ta tsantara kwalliya mai ban sha'awa, k'amshi kuwa kamar tayi 6arin turare.
Kitchen ta fad'a ta fera dankali ta soya, kafin ya soyu ta had'a kidney sauce d'in da taji albasa da tarugu, ta soya k'wai, sai ta had'a masa kunun gyad'a sanin Khaleel na sonshi sosai don idan Ammi tayi yana sha sosai, amma tsabar mugunta bata ta6a yi masa ba sai yau. Ta d'auko fruits ta had'a fruit salad, shima yana sonshi sosai. Nan da nan gidan ya rikice da k'amshi, ta kammala ta sanya a warmers.
Duk da abinda yayi mata jiya da daddare wai ta kasa jin haushi, a haka ma ji take kamar ta dad'e bata ganshi ba, ta zauna kan dinning tayi kalaci a natse, ta kammala ta kimtsa wurin, sannan ta zauna wuri d'aya tana zaman jiranshi ya fito.
Haka tayi ta zura ma k'ofar d'akinsa ido amma shiru kakeji, minti kusan biyar ba Khaleel ba alamar shi, sai kuma taji tsoro tace.
"Kodai ba gidan ya kwana ba?"
Motsin bud'e k'ofa ya sanya tayi saurin nutsuwa, wani sanyin dad'i taji ya ziyarci zuciyarta, fuskarsa a washe sai ya k'ara mata kwarjini da kyau sosai. Ta k'ara kallonshi sanye yake cikin jallabiya kalar toka, nan da nan taji wata kasala na saukar mata tayi wani lak'was, a lokacin kuma ya jefeta da wani shu'umi kallo, ya zauna yana kallonta yace
"Zuba min mana"
Jikinta ya d'auki rawa saboda yadda ya tsareta da ido, ko wane motsi tayi akan idonsa. Ta kammala zuba masa ta zauna jiki a sanyaye tana kallonsa jefi jefi. Haka kuma da ta kalleshi sai taga idanunsa k'yar akanta!
Kullum shi yake ce mata ya gama amma yau shiru kakeji.
Abin mamaki tama kasa k'wak'warron motsi bare ta tashi. Ta d'an saci kallonsa sai ta ga ya maida kansa ga wayarsa yana latse latse, aikuwa ta saki jiki ta dinga kallonsa tana jin nishad'i.
Hmmm So! So babbar cuta ce wallahi.
Karaf suka had'a ido yayi murmushi, ya ce
"Wurin ya miki dad'in zama ne? Ko kuwa kina jin dad'in wurin ne haka, saboda na gama tun d'azu fa"
Kunyar duniya ta kama Hanifah, ina ma k'asa ta bud'e ta shige daya fiye mata! Sum sum ta mik'e ta soma tattara wurin, yayi murmushi yace
"Kar kice fa korarki nayi y'an mata, dama tambaya..."
Da sauri tace
"Bansan ka gama bafa dama jira nakeyi na kwashe kayan" tana gama fad'ar haka tayi kitchen da sauri har tana tuntu6e da kujera. Tana jinsa yana dariya k'asa k'asa.
Tana kitchen tana goge kulolin da zata sanya abincin rana ya shigo, sanye yake cikin riga mai hannu dark blue da bak'i sai bak'in wando, sai covered takalmi shima bak'i, k'amshin turarensa kuwa duk ya mamaye mata hanci.
"Zanje office akwai important meeting da ya taso, so zan dawo bayan sallar magriba zamu je gaida Ammi"
Da k'yar ta amsa da "To" saboda jikinta ya mutu mututus. Cikin ranta kuwa cewa takeyi
"Wannan wace irin matsala ce? Shikenan da yayi min magana sai na rasa nutsuwa ta? Dama shi so d'in haka yake?"
Haka dai ta kammala ta gyara komai kan dinning, tunda ta kammala d'aki ta koma ta d'auko littafinta don karatun jamb da ya rage saura sati uku su zana. Tana gama karatun sai taje taci abinci daga nan kuma kwanciya tayi da k'yar bacci yayi awon gaba da ita, tare da mafarkin Khaleel bila adadin.
7:27 PM
Hanifah yau d'okin za'aje aga Ammi kawai akeyi, da sauri tayi wanka ta shirya cikin wani leshi maroon da ash, simple d'inki aka masa riga da skirt, aka kafe d'aurin d'ankwalin zamani, komai ash ta d'auko, gyalenta kashka shima ash color ne, sai d'ankunne simple marar nauyi, aka d'auko jaka ash daga cikin lefenta, ta feshe turare mai sanyin dad'i.
Bata jima da kammalawa Khaleel ya dawo a gajiye, wanka yayi ya had'e cikin cream yadi mai kyau, ya zauna yayi masa kyau, Hanifah na tsaye gaban madubi tana yaba kwalliyarta taga mutum kamar daga sama, take kuwa jikinta ya mutu tana k'are masa kallo cike da shauk'in so da k'auna. Ya kashe mata ido d'aya yace
"Ya da kallo haka ne y'an mata?"
Kunya ta kamata tace a ranta
"Hanifah! Ki nutsu ki daidaita kanki, sai kwaso abin kunya kike"
Murmushi yayi yace "idan kin gama muje ko?"
Jiki a sanyaye ta fito.
A mota ma ba wanda yayi wa kowa magana, Hanifah kuwa in banda satar kallonsa babu abinda takeyi har suka iso.
Da sallama suka shiga, Ammi na zaune tana kallon tashar labarai tajiyo sallamarsu, Ammi ta d'ago da sauri tana kallonsu, Khaleel ya zauna kusa da Ammi, itama Hanifah zama tayi kanta k'asa, Ammi farin ciki marar misaltuwa taji, nan aka gaisa, Ammi da kanta ta kawo musu ruwa da kayan lashe lashe da tand'e tand'e, Halisa ma tayi farin ciki sosai da ganinsu suka gaisa ta koma ciki.
Nan kuma fira ta 6arkr tsakaninsu kamar ba gobe. Ganin y'ayanta haka yasa ta farin ciki ta kuma k'ara mik'a godiyarta ga Allah, tare da fatan su d'ore haka har abada.
Basu suka tashi tafiya ba sai wurin goman dare, shima sai da Ammi ta soma korarsu akan su tashi su tafi gida dare yayi, kamar zasuyi kuka haka suka tafi.
Bayan sun koma gida ta k'ara tsantsara wankan da yafi na jiya, ta sanya rigar bacci mai sul6i brown color, ta feshe jikinta da tuarare kamar tayi 6ari. Haka ta kwanta kan gado cike da fargaba, kamar dai jiya bai shigo ba, damuwar yau tafi ta jiya saboda bata samu bacci sosai ba.
Da safe ta tashi kamar kullum ta had'a kalaci ta gyara gidan, tayi wanka ta sanya riga da wando na english wears, miskilin yau k'arfe takwas ya fito da shirinsa na zuwa office, sai wani basarwa yakeyi yana breakfast. Hakan ma ko haushi bataji ba sai ma burgeta da yayi. A ranta tace
"Namiji mai aji daban ne"
Maimakon yace ya gama kamar kullum sai kawai taga ya mik'e tsaye, ta bishi da ido, sai kawai ya kalleta yace
"Office"
Tayi murmushi, ya maida mata ya fice. Ta ta6e baki tace
"Ikon Allah kenan, yau kuma yanga akeji su ya Khaleel?"
Hakan ma bataji haushi ba ko kad'an sai ma murmushi da takeyi.
*****
"Tboy! Wai ina kaje nake nemanka tuntuni?"
Tboy yayi shu'umin murmushi yace
"Sorry Dboy wallahi nayi tafiya ne wata babe ce ta tafi da imani na a Lagos shine na tafi"
Deen yayi murmushi
"Yayi my guy, nima matsala ce tattare dani, kuma kai kad'ai nakeda a duniya da zaka bani shawara"
Tboy ya sosa gemu yace
"Ina jinka Dboy"
Deen ya soma bashi labarin had'uwarsa da Hanifah, dalla dalla har ya kawo inda a yanzu tayi aure kuma yana buk'atarta (wa'iyazubillah! Allah ka shirye mu shirin addinin musulunci)
Tboy yace
"Shi shegen mijin nata ne matsalarka kenan?"
Deen yace
"Shine mana"
Tboy yayi shiru, can kuma yayi murmushi yace
"Idan na fahimce ka, kana nufin kana buk'atarta amma sai mijinta ya sake ta right?"
Deen ya girgiza kansa yace
"Hakane"
Tboy ya k'yalk'yale da wata irin dariya yace
"Wannan mai sauk'i ne kawai mu tsorata sa da rayuwar matarsa kaga idan yana sonta dole ya sallame ta"
Dad'i ya kama Deen yace
"Tboy my guy, sheyasa nake sonka da shawarar da kake bani, yanzu ya kake ganin zamuyi"
Tboy yace
"Kawo kunnenka"
Sukayi rad'a, sai kuma suka k'yalk'yale da dariyar jin dad'i, Deen cikin d'aga murya yace
"Wannan plan d'in naka yayi my guy"
Haka suka k'arasa firarsu daga k'arshe suka shige mota suka tafi.
MSB✍πΌ
No comments:
Post a Comment