π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
ππππππ
π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
©PERFECT WRITERS FORUM
(P.W.F)❤️
πππππ
*KHALEEL*
πππππ
Written by Maryam S bello {MSB}✍π»
http://MaryamSBello.blogspot.com
March 2017π
PAGE
✍π»✍π»53&54✍π»✍π»
Asubar fari Khaleel ya bud'e idonsa, a hankali ya d'ago da kansa ya sauke su kan Hanifah da alamu dai bata farka ba, tashi yayi ya shiga toilet yayi alwalla ya wuce masallaci.
Bayan ya kammala, ya dawo d'akin tunawa yayi wayarashi a kashe take tun jiya, kuma yasan hankalin su Ammi ba'a kwance yake ba, da sauri ya lalubo ta a aljihun wandonsa ya kunnata, message ba iyaka ya gani yawanci daga Saif ne sai na friends nasa, murmushi yayi tare da dialing number d'in sai data kusa katsewa sannan aka d'aga Khaleel ne ya soma magana
"Saif ya..."
"Ya Khaleel ka kyauta kenan?"
Saif ya katse sa, murmushi Khaleel yayi yace
"I know bro, kuyi hak'uri please ina Ammi?"
"Ka damu da ita ne?"
"Haba Saif! Ka dena irin maganar nan haka mana please bana jin dad'i" cewar Khaleel
"To meyasa ka kashe min waya jiya without any explanation? Meye na 6oye mana cewar kaga Hanifah kodai bada gaske kake ba?"
Khaleel yace
"Haba mana Saif ka tsaya na maka bayani kafin kayi fushi dani, naga Hanifah but bata cikin hayyacinta and duk yadda zan ma Ammi bayanin cewar bazata iya magana ba bazata gane ba..."
"Me kake nufi da ba'a cikin hayyacinta take ba?" Cewar Saif a d'an tsorace
"What I mean is that na tsince a sume shine na kawo ta asibiti, yanzu haka ma anjima kad'an zasu sallame mu da zaran ta farka"
Saif yace
"Are your she's ok?"
Khaleel yace
"Wallahi Saif lafiya lau take kawai dai suma tayi saboda rashin abinci da ruwa, but everything is going to be fine insha Allah"
Saif yace
"Alhamdulillah! Wane asibiti kuke?"
Khaleel yace
"Wata asibiti ce na gani a hanya shine na tsaya, kuma from all indication they're good ba laifi, and please kar kace zaku taho akwai d'an nisa, da an sallame mu zamu dawo straight home"
Saif yace
"If you said so, da ta farka ka kira mu muyi magana da ita please"
Khaleel yayi murmushi yace
"Kar ka damu insha Allah da ta farka zan kira, ahm ya kuka k'are da case d'in su Deen?"
Saif yace
"Suna hannun hukuma yanzu haka, anyi sorting out komai so you don't have to worry"
Khaleel yace
"Alhamdulillah Allah ya shirye su"
Saif yace
"Amin sai munyi magana anjima"
Khaleel yace
"Ok ka gaida Ammi"
Suka katse wayar.
FEW MINUTES LATER
Khaleel ne ya fito don siyan abinda zai sa ma cikinsa, bread ya siyo da Fanta ya dawo hoping Hanifah ta farka, amma unluckily bata farka ba, ya dai tarar wata nurse na zare mata drip alamun ya k'are, bayan nurse d'in ta kammala ta kalli Khaleel tace
"Drip ya k'are so idan ta farka ka sanar da doctor Ahmad don ya ganta"
Gyad'a kai yayi yayin da nurse d'in ta d'auki tray d'in maganin data shigo da shi ta fice.
Haka ya zauna ya samu yaci bread da Fanta d'in har ya ji cikinsa ya d'an cika.
Komawa yayi ya zauna kusa da Hanifah tare da jawo hannunta ya rik'e cikin nasa.
Burinshi kawai yaga ta farka amma still shiru kakeji. Kwantar da kansa yayi kamar yadda yayi da daddare har ya d'an soma bacci sama sama.
A hankali yaji ana shafa hannunsa kamar a mafarki firgit! yayi ya farka ya kalli Hanifah da idanunta ke a rufe amma hannunta na motsawa cikin nasa, da sauri ya matsa kusa da ita ya fara shafa fuskanta
"Hanifah! Ki tashi haka nan please, ki tashi ga Khaleei a kusa da ke"
Haka yayi ta mata surutai yana d'an girgiza ta kad'an kad'an, biji biji ta fara gani kafin ta bud'e idanunta ras sai akan Khaleel! Kallonsa takeyi kamar bata sanshi ba kafin a hankali tace
"Ya Khaleel?"
Cike da farin ciki marar misaltuwa Khaleel yace
"Eh nine Hanifah, Khaleel ne a kusa da ke, dad'i ya kamata take ta fara kukan farin ciki, Allah ya kub'utar da ita daga hannun Deen gata a kusa da Khaleel d'inta, neman tashi take zaune, da sauri Khaleel ya taimaka mata tare da jinginar mata da pillow a bayanta, tunawa yayi zai kira Dr Ahmad, don haka da sauri ya saki hannunta yace
"Ina zuwa Hanifah yanzu zan dawo"
Girgiza masa kai ta shiga yi
"A'a ya Khaleel kar ka sake tafiya ka barni please"
Tausayi ta basa sosai ya dawo ya zauna a kusa da ita tare da kamo hannayenta duka biyun yana kallon cikin idonta yace
"Ba inda zanje likita zan kira yanzun nan zan dawo kinji?"
Tayi narai narai da idanu kamar zatayi kuka tace
"Da gaske bazakayi nisa da ni ba?"
Yayi murmushi
"I promise you yanzu yanzu zan dawo kar ki damu kinji?"
Ta gyad'a kai tana murmushi, kiss yayi mata a goshi yace
"I'll be right back baby" daga haka ya sa kai ya fice da sauri, har ya bar k'ofar Hanifah bata bar kallon wurin ba, ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi tana murmushi, ita kanta tasan tayi missing d'insa ba kad'an ba, batak'i ya zauna tayi ta kallonsa tana jin nishad'i, sai yanzu tayi realizing ashe duk son da tace tana ma Deen duk na k'arya ne yaudarar kanta kawai takeyi? Ta yarda ta amince cewar tana k'aunar Khaleel, bazata iya kwatantawa ba.
Shigowar su ya katse mata tunani, Dr Ahmad na gaba Khaleel na biye da shi a baya, Dr Ahmad ya k'araso yana murmushi
"Madam an farka kenan?"
Hanifah tayi murmushi, Dr Ahmad yace
"Good haka akeso" ya kalli Khaleel
"Ka tabbatar taci abinci da ruwa sosai kafin ku bar nan, it's very important"
Khaleel yace
"Insha Allah doctor"
Dr Ahmad yace
"Good, zan turo nurse da takardar sallama, sannu ko Allah ya k'ara sauk'i"
Khaleel yace "Amin" daga haka Dr Ahmad ya fice.
Dama Khaleel ya siyo sabon brush da Maclean Guda biyu, yayi amfani da d'aya, fito da d'ayan yayi ya sanya mata maclean d'in akai ya kamo hannunta.
"Muje nayi miki brush, sai kiyi alwalla ki rama sallolin da ake binki"
Murmushi tayi tana kallonsa shima ya mayar mata, hannunta ya kama ya mik'ar da ita tsaye, a hankali suka soma tafiya zuwa toilet d'in, da kansa yayi mata brush d'in sannan tayi alwalla suka fito. Khaleel na zaune yana kallonta tana sallanta a natse har ta kammala, bayan ta gama addu'ointa ya taimaka mata ta zauna kan gado. Fridge ya bud'e ya fito mata da fruits d'in da ya siyo mata da robar SWAN, haka yayi ta lalla6a ta yana bata har ta sha da yawa, nan ma sai da ya tilasta mata tasha ruwan sosai kusan rabin roban tasha. Sannan ya k'yaleta. Suna gamawa bada jimawa ba nurse ta shigo da takardar sallama ta mik'a masa yayi godiya.
Bayan fitarta Khleel ya kira number d'in Ammi, bugu biyu a na ukkun ta d'auka tace
"Khaleel ya kuke? Ina Aminatun?"
Yayi murmushi
"Lafiya lau Ammi, gata nan kuyi magana"
Ya mik'a mata wayar
"Hello Ammi"
"Hanifah! Alhamdulillah, ya jikin naki hope babu abinda ke damunki?"
K'walla taji sun tarar mata da k'yar ta had'iye kukanta tace
"Alhamdulillah Ammi lafiyata lau, nayi missing d'inku"
Ammi tayi murmushi
"Muma haka yaushe zaku taho?"
Hanifah tace
"Yanzu insha Allah an sallame mu"
Addu'a Ammi ta shiga jera mata ba iyaka wanda ya karyar mata da zuciya, kuka ne ya k'wace mata so take kawai taga Amminta tayi missing d'inta sosai.
Da sauri Khaleel ya taso yana fad'in
"Haba Baby meye na kuka kuma? Stop crying komai ya wuce kinji?"
Batasan lokacin da tayi hugging nasa sosai tana kuka, hugging d'inta back yayi yana ta rarrashinta da k'yar ya samu tayi shiru.
Hannunta ya kama suka fito daga d'akin, ya tsaya ya biya kud'ad'en da ake binsa sannan suka fito.
Da kansa ya bud'e mata mota ta shiga a yayinda ya zagaya ya bud'e mazaunin driver. Cikin nutsuwa yake tuk'insa sunyi nisa sosai Hanifah bacci ya kwashe ta, gyara mata kwanciya yayi yana kallonta murmushi shimfid'e a saman fuskansa. A haka suka iso cikin garin Kaduna.
MSB✍πΌ
No comments:
Post a Comment