Monday, 27 March 2017

KHALEEL Page 67&68

♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 March 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻67&68✍🏻✍🏻


Bayan dawowar Khaleel da kwana biyu Humaira ta ce zata kawo ma Hanifah ziyara, dama dai ta sanar da ita tun jiya zatazo, da har Hanifah zata sanar da ita yau  mijinta na gida amma kuma sai ta kasa, kawai tace mata "To"
Ta sanar dashi zuwan sabuwar k'awarta da suka soma k'awance a kwanakin baya yace mata ta tashi ta girka mata wani abu da kayan motsa baki, sam cikin ranta bata son zuwan Humaira amma ba yadda ta iya saboda tace zatazo d'in. Tana cikin wanke shinkafa Khaleel ya shigo kitchen d'in daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana kallonta yadda tayi kicin kicin da fuska, a hankali ya k'arasa ya kamota ta baya tare da kissing lallausan gashinta dake k'amshi. Yace
"Yau waya ta6a min my princess haka?"
Ta k'ara had'e rai ta cigaba da abinda takeyi, yayi murmushi yace
"Tunda baza'a kulani ba bari nayi wanka na bar gidan sai anjima zan dawo"
Har cikin ranta taji sanyi wannan kishi nata ina zata kaishi wai? Sai kawai tayi murmushi ta zuba shinkafar cikin ruwan dake tafasa a tukunya, salad ta soma yankawa har ta kusa gamawa ta jiyo hayaniya daga palo, aje wuk'ar tayi da sauri tare da lek'awa, Khaleel ta gani da Humaira da alama sun san juna tana ganin duk maganar da sukeyi kuma tana ji.
Khaleel yace
"Allah sarki ina Ibrahim d'in yanzu?"
Tace
"Yana nan lafiya lau yana lagos can yake aiki yanzu"
Khaleel yace
"Haba nidai ina ganinki naga kamar da kukeyi da shi ta nan nayi saurin gano ki ay, gaskiya kin girma sosai yasu Mama?"
Tace
"Lafiyansu k'alau"
Daidai nan Hanifah ta fito tana k'ak'alo dariyar yak'e tace
"Laa ashe ma kunsan juna?"
Khaleel cikin dariya yace
"Wallahi kuwa, k'anwar Ibrahim ce wanda mukayi karatu a turai da shi, a lokacin can suke zaune ay ina yawan zuwa gidan, sai dai yanzu naga ita Humairar ta girma barakallah"
Hanifah tayi yak'e
"Yayi kyau kam, to itace ay y'ar ajinmu wadda nake baka labari"
Yace
"Allah sarki, feel at home Humaira ni zan fita sai na dawo"
Hanifah tace
"A dawo lafiya"
Zama sukayi kan kujera a tare inda Hanifah tace
"Ashe da gaske dai kina tafe?"
Humaira tayi dariya
"Eh wallahi zaman hostel d'in ya isheni na rasa abinyi sheyasa nace bari nazo, ashe ma oga na gida ay da kin sanar dani da banzo ba"
Hanifah tace
"Kai bakomai, yama fita bari na kawo miki ruwa"
Hanifah ta mik'e ta shige kitchen, can sai gata ta dawo hannunta d'auke da tray, ajewa tayi inda ta soma tsiyaya mata 5alive a cikin glass cup, Humairar tana sha Hanifah ta jefa mata tambaya
"Ashe ba nan garin kike ba?" Humaira tayi murmushi
"Eh wallahi daga Bauchi nake, karatu dai ya kawo ni nan"
Hanifah tace
"Allah sarki"
Sun d'an ta6a fira kad'an Hanifah na dubo girki har dai ta kammala ta jera dinning, dawowa tayi tana kallon Humaira tace
"Muje kici abinci"
Humaira tace
"Laa wallahi na k'oshi bana jin yunwa"
Hanifah tace
"Aikuwa baki isa ba, saboda ke fa na girka amma kice bazaki ci ba?"
Humaira tayi dariya tare da mik'ewa tsaye
"Ok ba damuwa muje muci tare"
Nan suka jera har dinning suka soma cin abincin inda suna ci suna fira kad'an, ba laifi Hanifah ta saki jikinta sun d'an ta6a fira. Suna nan har aka fara kiran sallar azahar Hanifah ta soma mik'ewa tsaye ta kalli Humaira
"Lokacin sallah yayi muje muyi ko?"
Humaira ta sadda kanta k'asa tana murmushi tace
"Wallahi hutu nake kije kiyi ki dawo"
Hanifah tayi murmushi tace
"Ok"

Bayan Hanifah ta gama sallar ne ta dawo palo inda ta tarar Humaira na kallo a natse. Humaira ta kalli Hanifah tace
"Kin gama?"
Hanifah tace
"Eh nagama"
Ko minti biyu Hanifah batayi da zama ba taga Hanifah ta soma shirin tafiya, da mamaki Hanifah tace
"Keda kika ce sai la'asar, ya naga kina shiri?"
Humaira tayi murmushi tace
"Wallahi kasuwa nake so in biya amma sai naje hostel nayi wasu aikace aikace"
Hanifah tace
"Allah sarki ba damuwa, sai mun had'u a school ko?"
Humaira tace
"Eh kinji wai an lik'a time table?"
Hanifah tace
"Wallahi naji, idan na shigo sai muje mu duba"
Humaira tace
"Ok sai kin shigo d'in"
Hanifah ta raka ta har bakin gate sannan ta dawo.


******

Tun daga wannan rana kusan kullum sai Humaira tazo, ko kad'an Hanifah bata kawo komai a ranta ba, har takance lallai Humaira akwai son zumunci.
Abu d'aya ke bata mamaki yadda Khaleel gaba d'aya ya tattara rayuwarsa ya mik'a ta ga waya, bayada aiki sai chatting kuma sam ba halinsa bane, a dah idan kaga Khaleel na kan waya to browsing abu yake mai mahimmanci, ko zaiyi chatting ba koda yaushe, sheyasa ma mutane sukance ya cika wulak'anci don baya ma mutane reply a whatsapp, amma yanzu taga abin nasa ya soma yin yawa kullum yana kan waya yana latse latse.
Ko y'ar firar da sukeyi yanzu an dena, ko ta masa magana sai dai yace mata "Uhm" abin nan ba k'aramin damunta yake ba. Don haka sai tace zata masa magana.
Wata rana suna zaune da daddare ta kalle shi yadda yake latsa wayar yana wani murmushi tace
"My only"
Yace
"Na'am"
Yau ko my princess babu, sai ta daure tace
"Wai kwana biyu meke damunka haka?"
Yace
"Mekika gani?" Still hannunsa na kan waya.
Tace
"Ka chanza gaba d'aya my only, dah ba haka kake ba, meyasa?"
Yace
"Wani abu nakeyi mai mahimmanci sheyasa"
Wani k'ululun bak'in ciki ya tokare mata wuya cikin sark'ewar murya tace
"Yanzu har akwai abinda yafini mahimmanci ne idan muna tare?"
Yayi murmushi
"Hanifah kenan bazaki gane ba"
Haushi ya turnik'e ta, ta rasa meya chanza mata Khaleel d'inta, amma ta d'auki alk'awarin a sannu zata gano koma menene zata magance shi da izinin Allah.


*****


Kwana biyu tsakani abu sai dad'a gaba yakeyi, ranar wata alhamis ya dawo a gajiye kamar yadda suka saba ta taro sa bayan yayi wanka ta taimaka masa ya shirya, ta lafe bisa kafad'unsa tace
"My only muje kaci abinci"
Abin mamaki sai taga ya haye gado tare da bajewa yace
"Wallahi bana jin yunwa yau snacks naci a office, k'ila zuwa anjima dai"
Duk da ranta ya sosu amma sai ta adure tace
"Yau kuma my only? Abinda baka ta6a yi ba shine yau ka fara yi kuma?"
Yace
"Sorry dear, naji yunwa ne d'azu sheyasa naci ki bari zuwa anjima sai naci, yanzu bacci nakeji"
Ranta ya dagule wai meke shirin faruwa dasu ne? Meyasa Khaleel ya chanza mata haka? Meye dalilinsa? Tambayoyi barkatai amma babu amsoshinsu.

Bayan sallar la'asar ya tashi yayi wanka yayi kwalliya sosai sai k'amshin turare ke tashi, Hanifah ta shigo da cup d'in lemo a hannunta ta tsaya tana kallonsa. Sai gyara kwalar rigarsa yakeyi yana wani kakka6e jikinsa yana kallon kansa ta madubi. Da mamaki Hanifah tace
"My only ina zaka je da yamman nan?"
Yayi murmushi yace
"Office zanje mana"
Ta saki baki galala tana kallonsa
"Office yanzu?"
Yace
"Eh mana ba dad'ewa zanyi ba oganmu ya kiramu ne"
Sai a sannan tayi murmushi tace
"Gaskiya ka tabbatar ka dawo da wuri my only"
Yace
"Insha Allah my princess"
Mik'a masa cup d'in tayi ya kafa kai ya shanye ya mik'a mata yace,
"Sai na dawo"
Tace
"A dawo lafiya"
Daga haka yasa kai ya fice.


K'arfe goma shiru, motsi kad'an sai ta lek'a taji ko ya dawo amma shiru. Hanifah abin ya fara bata tsoro ganin har sha d'aya tayi ba Khaleel ba alamarsa, ta kira wayarsa yafi a k'irga bai d'aga ba. Can wani tunani ya zo mata ta dage k'irji tare da zaro ido waje!
"Kar dai Ya Khaleel wurin budurwarshi yake zuwa? Kai anya Ya Khaleel zai iya cin amana ta? Never i don't think so! To meye dalili meke faruwa?"
Sai dai zuwa yanzu ta soma kokwanto akan Khaleel, gabanta na harbawa ta sa kuka tana kiran "Innalillahi wa inna ilahir raji'un" bataso ta amince Khaleel nada budurwa don bata zaton haka d'inne.
Taci kuka sosai wurin k'arfe sha d'aya da rabi taji k'arar shigowar mota, da hanzari ta mik'e jikinta har rawa yake ta nufi k'ofa, shigowa yayi tare da kunna fitila, idonsa tar akanta tana tsaye kamar zakanya tana huci idonta jawur! Ya ware idanu waje yace
"Mekike yi har yanzu bakiyi bacci ba?"
Fuska d'aure tace
"Ya Khaleel daga ina kake da daddaren nan?"
Yayi murmushi
"Haba my princess wannan wace irin tamabaya ce?"
Tace
"Ya Khaleel bansanka da k'arya ba, ka fad'a min daga inda kake da tsohon daren nan!"
Ya kalli fuskarta idanunta sun rik'id'e zuwa ja, ya d'an tsorata yadda yaga yanayinta, to ya zaiyi me zai mata ne?


MSB✍🏼

No comments: