π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
ππππππ
π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
©PERFECT WRITERS FORUM
(P.W.F)❤️
Assalamu Alaikum fans, first of all i want to start by apologizing for the delay, i know ban kyauta ba, but kuma ku yi min uzuri akwai dalilin da yasa haka, da fatan kun fahimce ni, i love you all so much, thanks for the love and support me love all very much❤️
πππππ
*KHALEEL*
πππππ
Written by Maryam S bello {MSB}✍π»
http://MaryamSBello.blogspot.com
March 2017π
PAGE
✍π»✍π»45&46✍π»✍π»
Khaleel na d'auka kafin ma yayi magana yaji an k'yalk'yala da dariya, da mamaki Khaleel yace
"Wa...ye?"
Deen yace
"Wani bawan Allah ne"
Khaleel yace
"To! Daga ina haka don bangane mai magana ba"
Deen yace
"Dama ya za'ayi ka gane? Ni ba wannan yasa na kiraka ba, akwai wata mahimmiyar maganar da nakeson yi da kai"
Khaleel yace
"Wace magana kenan?"
Deen yace
"A sannu zaka gane me nake nufi, amma idan har mun had'u a wani wuri don maganar bata waya bace"
Khaleel yace
"Kaga malam bansan ko waye kai ba, don haka babu inda zanje sai ka fad'i man kai ko waye"
"Hahaha! Allah sarki, hakane fa kana da gaskiya d'an uwa, kasan yanzu duniyar ta zama abinda ta zama"
Cewar Deen cikin dariya. Shiru kuma ya biyo baya kafin Deen ya k'ara magana.
"Kasani idan har baka yarda mun had'u ba to ina tabbatar maka da cewar kana cikin matsala da kai da iyalinka baki d'aya, kuma maybe ma inada useful information dazan baka"
Da mamaki Khaleel yace
"Kamar ya fa?"
Deen yace
"Kamar yadda ka fahimta, zan rubuto maka da address d'in inda zamu had'u, kuma ka tabbatar da kai kad'ai ka taho idan ba haka ba..." Yayi dariya yace
"Zakayi nadama ne, na barka lafiya"
Pat! Ya kashe wayar ya bar Khaleel da wayar a kunnensa sagale har yanzu, mamaki fal ransa. Ammi ce ta ta6o sa.
"Khaleel menene? Anga Aminar?"
Ya girgiza kansa a sanyaye yace
"A'a"
"To meyafaru? Kayi shiru?" Cewar Ammi
Saif yace
"Don Allah kayi mana magana ya Khaleel"
Sai a sannan ya fad'a musu yadda sukayi da mutumin da baisan ko waye ba, Ammi ta numfasa
"Inaji a jikina wannan mutumin yanada nasaba da sace Hanifah da akayi, da zance muje ayi sanarwa amma yanzu a d'an dakata muji me wannan zaice maka"
Saif yace
"Haba Ammi, ta yaya zamu barshi yaje? Mukasan ko waye? Mugu ne? D'an fashi? Duka bamu sani ba, bai kamata mu barshi ya tafi ba"
Khaleel ya d'ago yana kallon Saif yace
"Kar ka damu Saif zanje, indai har yana da alak'a da satan Hanifah to wallahi sai inda k'arfi na ya k'are kudai ku taya ni da addu'a"
Saif kamar zaiyi kuka yace
"Ya Khaleel baka gane..."
"No Saif, kar muyi gardama da kai, kayi shiru kawai zanje"
Ammi tace
"Addu'a zamuyi masa, kasani ko ya dawo mana da Hanifah har gida, bakasan inda za'ayi dace ba"
Saif yace
"Shikenan amma don Allah kabi a hankali"
Khaleel idanunsa suka cicciko da k'walla ya dafa Saif yace
"Insha Allah zan kula sosai d'an uwa ka taya ni da addu'a"
Saif bai amsa ba sai ya kamo Khaleel ya rungumo yana matsar k'walla, Khaleel d'in ma kukan yake, ita dama Ammi hawaye wani na korar wani. Khaleel ya yunk'ura zai tashi, yaji shigowar sak'o, da sauri ya duba, address d'inne aka turo masa, can wajen gari ne sai ma an d'anyi tafiya mai nisa, amma sam bai damu ba shidai fatanshi Allah yasa ya samo haske game da Hanifah. Ya kalli Ammi yace
"Bari naje gida nayi wanka, sai na kama hanya"
Ammi tace
"A'a ban yarda ka tafi da daddaren ba, kayi hak'uri sai gobe"
Zaiyi magana Ammi ta d'aga masa hannu
"Banason gardama Khaleel, yau da gobe duk d'aya ne ay, kaje gida sai da safe"
Ba yadda ya iya illa yabi umarninta, ko magana bai iya yi haka ya fice jiki a sanyaye. Masallaci ya tsaya yayi isha'i.
Tuk'i yake amma rabin hankalinsa naga Hanifah, Allah ne kad'ai ya kaishi gida lafiya.
Yana isa gida bai zame ko ina ba sai toilet, yayi wanka ya fito, kaya marasa nauyi ya sa ya haye gado ya kwanta, shima kansa yasan bawani baccin da zaiyi yaudarar kansa kawai yakeyi, kwanciyar ta ishe shi ya mik'e zaune ya jingina da gado, pillow ya d'auko ya mak'alk'ale. Tabbas yayi missing Hanifah, sai yanzu ya k'ara tabbatar da hakan, ji yake kamar ya ganta zaune kusa dashi da ya rungume abarsa. Muryata yaji ta daki dodon kunnensa,
"Ya Khaleel...!"
Ya fara waige waige, sai kuma yaji dariyarta. Ya sauko daga kan gadon ya shiga dubawa yana kiran sunanta
"Hanifah!"
Dariyarta ya k'ara ji tace
"Ya Khaleel gani nan fa a bayanka"
Ya juyo da sauri yaga wayam, k'wank'wasa k'ofa akayi. Yayi shiru kamar bazaije ba, daga k'arshe dai yayi gathering courage nasa ya doshi k'ofar tare da bud'ewa. Tsaye yayi cike mamaki, Hanifah ce tsaye yake gani tana ta masa murmushi, baisan lokacin da ya saki murmushi ba yace.
"Hanifah na, yaushe kika dawo? Meyasa kika tafi kika barni?"
"Oga!!!"
Firgit ya dawo hayyacinsa, cike da mamaki yace
"Baba maigadi, dama kaine?"
Baba yayi murmushi
"Nine, dama zuwa nayi in maka jaje, lokacin da ka dawo ina masallaci banga dawowarka ba, ashe abinda ya faru kenan? Allah ubangiji ya bayyana mana ita ya tona asirin azzalumai"
"Amin Baba na gode"
Haka Baba ya koma yana mai tausayawa Khaleel halin da ya tsinci kansa, aiko sai bai kwanta ba sai kawai ya d'auro alwala ya fara gabatar da nafila yana rok'on Allah Hanifah ta dawo.
Shi ma Khaleel baiyi bacci ba addu'a ya duk'ufa yi Allah yasa tafiyar da zaiyi akwai alkhairi a ciki, yasa aga Hanifah. Wannan dare gani yake ya masa tsawo, da asussuba kuwa bayan ya gama sallah, wanka yayi ya shirya cikin cream yadi marar nauyi. Ko kalaci baijin zai iya yi.
Ya fito suka gaisa da Baba yace masa zai fita.
Gida ya fara zuwa sukayi sallama da su Ammi, ya sha addu'a da fatan dacewa, jiki a sanyaye ya fito ya tura text yace
"Gani nan na kama hanya yanzu"
Deen yayi murmushi yana jujjuya wayar a hannunsa yace
"Good job Deen, i am waiting for you"
Khaleel a sanyaye ya shiga mota, yayi addu'a ba iyaka sannan ya tada kan motar, ya harba titi.
Nasan zakuce na yau ba yawa, afuwan pls ππ
MSB✍πΌ
No comments:
Post a Comment