π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
ππππππ
π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
©PERFECT WRITERS FORUM
(P.W.F)❤️
I dedicated this page to Maman Khaleel❤️π❤️and my Aunty Xeeπmuch love dearies❤️ππ❣❤️ππ
(Happy birthday Aunty Khady Allah's noorπΌπΌπΌπΌπΌπΌπΌπΌ)
πππππ
*KHALEEL*
πππππ
Written by Maryam S bello {MSB}✍π»
http://MaryamSBello.blogspot.com
March 2017π
PAGE
✍π»✍π»63&64✍π»✍π»
Dadaddare haka Hanifah ta kwana tana amai ga zazza6i mai zafi da ya rufe ta, rud'ewa ba irin wadda Khaleel baiyi ba, duk ta galaibata saboda aman da takeyi, komai taci sai ya dawo mata. Don haka Khaleel na gama sallar asuba ya kwashe ta ya kaita asibiti, office d'in wani likita suka shiga suna zuwa ya umarce wata nurse data d'ibi jininta da fitsarinta ayi mata test. Bayan gudanar da test suna zaune office d'in likitan yana murmushi ya kalli Khaleel yace
"Congratulations sir! Your wife is pregnant almost 1 and a half getting to two months"
Khaleel can't believe he'a actually gonna be a father, ita kuwa Hanifah kunya ta rufe ta take ta sadda kanta k'asa, jawo ta yayi a gaban likitan ya rungume ta tsabar farin ciki yace
"Thank you my princess, Allah ya nuna mana babynmu lafiya"
Hanifah k'ok'arin janye jikinta takeyi cike da kunya, likitan yayi murmushi yana kallon Khaleel ya burgeshi matuk'a yadda yake nuna wa matarsa kulawa ba tare da shakkun komai ba a gaban kowa.
Likitan ya rubuta mata maganin da take buk'ata had'e da shawarwari sannan yace
"Za'ayi mata scan yanzu don tabbatar da lafiyar babyn, zaki iya biyoni" daga haka ya fice a yayinda Hanifah da Khaleel suka bi bayansa.
Wata likita doctor'n yayi ma bayani take ta yi wa Hanifah scan inda aka tabbatar da babyn lafiyansa k'alau babu wata matsala, sannan ta umurce ta da ta dawo nan da sati hud'u.
A hanya ma sai da Khaleel ya tsaya ya siya mata kayan k'walama a cewarsa zataji dad'in cinsu.
Hausawa na cewa ya lafiyar kura bare tayi hauka?! Tofa Khaleel za'a zama daddy, tunda suka dawo gida Hanifah ta soma ganin sabon sauyi tattare da mijinta, kulawar da yake bata ta linku d'ari bisa d'ari akan wadda yake bata a dah, ko tari tayi sai yace mata "Sannu" ko kuma "Kina buk'atar wani abu?" Gaba d'aya ko fita ya daina yi ya zauna don kula da babynsa da abin sonsa. Ammi kuwa tuni an kirata an sanar da ita, ba yadda Hanifah batayi ba akan kar ya fad'a mata amma yak'i k'arshe ma cewa yayi
"Ina ruwanki mamanki ko tawa?" Dole ta k'yalesa amma kunyar Ammi takeji, Saif ma ba'a barsa a baya ba shima an sanar masa, aikuwa sunsha zaulaya.
Haka ya cigaba da bata kulawa ta mussaman har ta shafe kusan sati biyu sannan ta murmure, sai dai ta rame sosai tayi d'an wuya, amma ta k'ara kyau da haske.
Bayan sati d'aya da hakan admission letter d'in Hanifah ta fito, Khaleel bai sanar da ita ba tana kitchen tana yanka karas taji an rungume ta ta baya, ta lumshe idanu tana murmushi, ya juyo da ita tare da manna mata kiss a kumatu, Hanifah tayi murmushi tace
"My only ya ka dawo da wuri haka yau?"
Yace
"Wallahi kuwa naje wani wuri ne"
Ya mik'a mata letter d'in yace
"Duba kigani"
Ba musu ta duba sai dai kafin ta k'arasa karantawa ta daka wani uban tsalle tare da k'ank'ame Khaleel, take ya d'aure fuska ya jawo ta yace
"Ke meye haka? Kin manta bake kad'ai bace yanzu? Ki dinga bi a hankali mana"
Tayi murmushi tare da shafa masa fuska tace
"Afuwan ya habibi, bazan sake ba"
Yayi dariya
"Shikenan, kinga na miki registration da komai ranar Monday idan kinje school sai ki kai department d'inku"
Tace
"Angama my only"
Yaja hancinta
"That's my princess, me ake dafa mana haka?"
Tace
"Potato casserole"
Yace
"Oya zo mu k'arasa tare"
Ta ta6e baki cikin shagwa6a tace
"A'a don Allah my only ka barshi zan k'arasa" yayi dariya tare da kwaikwaiyon maganarta yace
"A'a nidai don Allah ki barni zanyi"
Gaba d'aya suka sa dariya, a tare d'in suka k'arasa, bayan sun gama cin abincin ne Khaleel ya sake fita da tabbacin zai dawo da wuri.
******
Rayuwa tana tafiya a haka har aka zo aka sa ranar bikin Saif da Salma, ba'a d'auki wani lokaci ba gaba d'aya wata d'aya aka sa. Su Khaleel da Hanifah shirin biki suke sosai, Khaleel shi ke had'a lefe a hankali yana ajewa. Duk wani abinda ya kamata suyi sun gudanar dashi da wuri komai yana tafiya daidai.
Ana saura sati biyu bikin suka kai lefe inda dangin amarya suka buk'aci zuwa jere.
Biki yana ta gabatowa gaba d'aya Hanifah ta tattara ta koma gida har agama sha'anin biki. Gidannasu cike yake da y'an uwa da abokan arzik'i, hidima ta sha kan kowa sauk'insu ma auren namiji ne walima kawai zasuyi sai y'ar dinner da aka had'a bayan an kai amarya.
Ranar walima wani dark blue lace Hanifah ta sanya anyi mata d'inkin riga da skirt, wanda ya amshe ta ya kuma yi mata kyau, ko kwalliya batayi ba, inda Khaleel shima ya sanya light blue shadda yayi kyau sosai. A haka suka tafi walimar da za'ayi a hall. An shiga da amarya inda take sanye da pink bridal gown ya mata kyau sosai, komai pink aka sanya mata. Kowa ya halarci bikin, anyi komai daidai misali. Tunda aka fara bikin Hanifah take lura da y'an matan dake ta kallon Khaleel, tun tana daurewa har abin ya ci tura, ta cika tayi fam saura k'iris ta fashe. Tama lura wasu har zuwa suke suce ya basu number wayarsa, sai dai taji sanyi yadda ko kallo basu ishe shi. Sai dai ance mata da kishi shi ya jawo har Hanifah tayi fushi ta fice daga hall d'in, sam Khaleel bai lura da fitarta ba a cewarsa tana nan zaune tunda ya hana ta yin zirga zirga.
Sai da aka soma shirin tafiya sannan fa Khaleel ya fara duba Hanifah amma sam bata nan inda take. Kamar wasa ya duba hall d'innan kaf ba Hanifah ba alamarta, hankalinsa fa ya tashi take ya fito da sauri ya shiga dubawa daga waje.
A jikin motarsa ya hango ta tsaye ta hard'e hannayenta tana kalle kalle. Da sauri ya k'arasa inda tare da sakin ajiyar zuciya.
"Hanifah!" Ya k'wala mata kira, tana jinsa amma ko kallonsa batayi, yana isa ya kamo ta ta fizge, a d'an rud'e yace
"Wai meyasa kika fito nan bayan nace ki samu wuri ki zauna gu d'aya?"
Ta k'ara had'e rai tana kumbure kumbure.
Kallonta yakeyi yana son gano wani abu, yayi murmushi tare da kamo hannayenta cikin nashi
"Haba my princess, ta yaya ma zaki soma tunani irin wannan? Kina tunanin akwai wadda zata birgeni ne bayan ke? Wallahi Hanifah inda kinsan yadda kike a cikin zuciyata da bama zakiyi wannan tunanin ba, haba Hanifah! Kin bani mamaki"
Take kuma taji ba dad'i, itama in banda hauka da kishin tsiya ta yaya ma zata soma irin wannan tunanin?
Batasan lokacin datayi hugging d'insa sosai ba tace
"Kayi hak'uri my only! Wallahi ba zarginka nake ba, kawai naji tsoro ne yadda y'an mata ke kai maka hari"
Ya cire hannayenta daga rungumar da tayi masa yana kallon cikin idonta yace
"Ke kuma kina tsoro kar na miki kishiya ko?"
Tayi murmushi cike da kunya, dariya yayi cikin sigar zolaya yace
"Meye abin tsoro a kishiya idan ma ta shigo basai ki zaune ta ba?"
Cikin muryar shagwa6a tace
"Gaskiya ni a'a ka daina bana so"
Yayi dariya yace
"An daina"
A haka Saif ya k'araso yace
"Lalala, yanzu baku iya hak'uri da juna har a gama bikin?"
Khaleel yace
"Kajika da wani zancen, kai ina ruwanka ma?" Sukayi dariya Saif yace
"Niko keda ruwa, kunga fa kowa ya watse sai mu kad'ai kuzo mu tafi gida"
A haka suka koma gida Saif sai faman zolayarsu yake, Khaleel yace
"Rabu da shi Hanifah akwai ranar da zamu rana ne"
Washe gari juma'a ana gama sallah aka d'aura auren Saif Abdul'aziz da Salma Aliyu akan sadaki dubu hamsin. Masallacin ba matsaka tsinke saboda bainar jama'ar da suka halarci taron. Daga nan suka wuce reception inda aka ci aka sha kafin taron ya watse.
Da yamma aka kawo amarya inda ta kwana gidan Ammi akan gobe za'a wuce da ita Abuja.
washe gari asabar kuwa k'arfe tara na safe aka fara shiri, Hanifah ta shirya cikin wata golden and ash atamfa d'inki doguwar riga, sai ta d'ora bak'ar after dress mai kyau.
Amarya kuwa orange da green d'in atamfa aka sanya mata sai aka rufe mata kanta da k'aton mayafi. Aikuwa kafin akai amarya Saif yasha tsiya da tsokana wurin Khaleel. A haka aka tafi kai amarya. Dadddare aka wuce dinner inda amarya ta sanya bak'i da silver d'in lace tayi kyau.
Anyi biki lafiya amarya ana gidan Saif sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba.
*****
Hanifah ta soma zuwa lecture a cikin motarta ita ke tuk'awa ta kai kanta ta maido kanta. Ta dage tana karatu sosai ba wasa. Yawancin lectures d'inta na safe ne zuwa sha biyu, ranar da batada na safe kuwa to k'arfe biyu zuwa hud'u ne na rana. Ta saba da matar Saif sosai wadda batada k'awa sama da ita, duk wata shawara ko wani abu da ya shige musu duhu sukan tuntu6i junansu. Itama tana can ta samu admission tana karatunta.
MSB✍πΌ
No comments:
Post a Comment