Thursday, 2 March 2017

KHALEEL Page 37&38

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


Thank you all for the du'a Allah ya saka muku da alkhairi l love you all so much😍



 March 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻37&38✍🏻✍🏻


Kwance take kan gado rigingine ta k'ura ma bango ido ga ruwan hawaye dake ta faman sintiri bisa kumatunta, ita kad'ai tasan yadda takeji a zuciyarta, Khaleel kuwa wanka yayi, yayi shirin office ya fito a tunaninsa ma Hanifah bata tashi ba don ya fita ya barta tana bacci, tura k'ofar d'akin yayi gami da yin sallama, kusa da ita ya zauna tare dafa ta.
"Hanifah..."
Firgit ta juya suka had'a ido tayi saurin sunkuyar da kanta tana share hawaye.
Hankalinsa yayi matuk'ar tashi yace
"Meyafaru Hanifah? Ko bakida lafiya kuma?"
Tayi shiru
Yace
"Hanifah...! Nasan damuwarki, nine matsalarki ko? Nine kika tsana har yasa kike kuka saboda na takura miki zama dani ko?"
Ta dago da sauri a yayinda da wasu hawayen sukayi nasarar saukowa, yasa hannu ya goge mata yace
"Sorry don't cry kinji?"
Wani abu ya taso mata cikin k'walwarta ya dinga ratsa jijiyoyinta har tafin k'afarta. Take kuma tsigar jikinta ta tashi tayi yarr. Magana yake mata mai hargitsa k'walwa, ta shiga rud'ani a inda jikinta ke cikin wani irin yanayi.
Ya k'ara jefa mata tambaya a karo na biyu
"Bazaki fad'a min meke damunki ba? Baki magana ne?"
Yayi shiru yana kallonta, sannan yace
"Allah ya kawo min ranar da zakice I love you..."
Ya kwanto kusa da ita yace
"Idan kuma lokacin bana raye shikenan kinga kin huta, sai ki fad'a ma wanda kike so amma don Allah Hanifah ki daure ko gawata ki fad'a mata kinji?"
Gabanta yayi mummunan fad'uwa a karo na farko wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba. Ranta ya 6aci "meyasa zai dinga ce min zai mutu ana zaune k'alau, ko da yake mutuwa na kan kowa"
Ya tallabo sai taga yana hawaye, cikin wata irin murya yace
"Bakisona ko? Baki tausaya min ko Hanifah?"
Ta runtse idonta gam sai ta samu kanta dayin kukan itama. "Kukan menene?" Ta tambayi kanta. A lokacin kuma taga ya mik'e tsaye yace
"Kina buk'atar wani abu?"
Ta girgiza kanta alamun a'a
Yace
"In ma dai kina buk'ata ki kirani a waya, ni zan fita sai na dawo"
Dama bai cika jiran amsarta ba idan yayi magana saboda yasan ba amsawan zatayi ba, sai kawai yasa kai ya fice. Tabi shi da kallo har ya 6ace, ranar farko da taji tausayinsa ya mamaye mata zuciya. Tace
"Allah sarki bawan Allah duk abubuwan nan da nake masa bai damu ba shidai burinsa ya faranta min rai? Kwata kwata bayason 6acin raina.
Ta koma ta kwanta don tayi bacci kafin goman dare ta tashi tunda yanzu ba abinda zatayi.
Ta kwanta lamo sai dai gaba d'aya ta kasa bacci, tunanin fal ranta! Sannan kuma ta ringa jin wani irin nishad'i yana ratsa dukkanin illahirin jikinta. Murmushi ne ya su6uce mata ba shiri tuno yadda yake zolayarta da ranar da yace mata hancinta kamar tumatiri, batasan lokacin da ta k'yalk'yale da dariya ba, sai kuma zumbur ta mik'e zaune "innalillahi wa inna ilaihir raji'un, wai meke faruwa dani ne?"
Kuka take wiwi hankalinta duk ya tashi, ta rikice lokaci d'aya.
Sai da ta gaji tayi shiru don kanta, gajiya tayi ta mik'e ta fad'a toilet tayi wanka, ta shirya cikin wani cream d'in atamfa mai jar flowers, ta kammala ta fito palo don a ganinta zata samu sauk'i a cikin zuciyarta, nan d'inma bata tsira ba don tunani ya hana ta sak'at.
Remote ta d'auko ta gano Zee World, series d'in da akeyi bata gajiya da kallonshi, ya mata kyau, (Twist of fate) na Abhi da pragya, sai purabh da bulbul, a da purab na mata kama da Deen amma yau ya koma Khaleel sak! Dama Surayya ta sha fad'a mata
"Hanifah ya Khaleel na kama da Purabh" amma saboda son zuciya irin tata take k'aryatawa.
Yau kam Hanifah ta ga ta kanta tunanin Khaleel zai haukatata.
Tashi tayi ta koma kitchen ta soma had'a kalaci don yunwa takeji, haka taci amma fa hankalinta gaba d'aya yana ga Khaleel.


Wajen k'arfe sha d'aya na safe ta shiga kitchen, abin mamaki yau shinkafa da miya harda coleslaw aka had'a masa, ta kammala ta jera kan dinning sannan ta feso wanka, sai da ta 6ata awa kusan d'aya ta tsaftace jikinta sannan ta fito. Shirin kanshi yau na daban ne,  wani lace ta sanya marar nauyi d'inkin riga da skirt sky blue da pink ya kar6eta sosai, duka duka sau biyu ta ta6a sanya su, ya zauna das a jikinta don ma ta d'an rame, kamshin da ke tashi daga jikinta ma na daban ne saboda had'in turarukan da tayi masa, light pink lipstick tasa wanda yayi mata kyau sosai, tayi murmushin mugunta tace.
"Yau dai duk miskilancinsa sai..."
Gabanta yayi mummunan fad'uwa ganinshi tsaye bakin k'ofa, kallonsa takeyi saboda bai ta6a yi mata kyau ba irin yau ba. K'anan kaya ne jikinsa ash jeans sai dark blue riga marar hannu an rubuta a gaban rigar "come to me baby"
"To yaushe ya dawo da har ya chanza kaya?" ta kalli idonsa tace a ranta shin da gaske yake abinda aka rubuta a rigarsa ko kawai....
"Kin tsareni da ido baki amsa sallamata ba, sannan baki bani izinin shigowa ba, kin barni tsaye kamar wani soja"
Kunyar duniya ta kamata, wannan wane irin dizgi ne? Amma tsabar raini ya...
"Dama daga office Ammi ta kirani tace zamuyi bak'i shine na dawo, so sanda na shigo kina wanka..."
"Wai a ina yayi wanka ne?"
Yayi murmushi
"Wannan wace irin tambaya ce Hanifah?"
Ta k'walalo idanu badai maganar zuci ta fito fili ba?
"Yau na bani! Wai meke damuna ne haka ni Aminatu? Wai so hauka ne?"
Ta fad'a a ranta
Dariyarsa ce ta katse ta sannan yace
"Kidai kimtsa kafin su k'araso"

Kitchen ta koma ta bud'e fridge akwai samosa da meatpie ta fiddo ta soya tasa a warmers, ta had'a zo6o. Ta kammala ta kimtsa kitchen d'in ko zama batayi ba aka shiga doka sallama. Ta dafe kanta tare da jan guntun tsaki tace a ranta "yanzu zasu hanani kallonsa son raina" ta runtse idanunta a tunaninta ya fita bud'e musu k'ofa, ta saki ajiyar zuciya, kawai tana bud'e idonta ta ganshi tsaye hannayensa sark'e a aljihu yana kad'a k'afa, nan da nan jikinta ya fara rawa, ta mik'e sum sum zata wuce yace
"Ki nutsu Hanifah"
Da sauri ta fice gabanta na dukan tara tara. Ta rasa dalilin da yasanya hakan amma tabbas ta tuna tana yarinya ko magana yayi mata gabanta sai ya yanke ya fad'i.

Zaune suka kan kujerun palon bak'in, Anty Aisha da tawagarta (y'an yayy'en ne ga Ammi), sai maza biyu wad'anda suma suke yayy'en  Ammi, Hanifah tayi murmushi tana fad'in
"Salamu Alaikum"
Duk suka amsa sallamar suka ce
"Amarsu ta ango mai dad'in tuwo"
Bayan an gaggaisa, Fiddausi da suke abokanan wasa ta kalli Hanifah tace
"Lallai Amina har kin kwaso daga shigowa?"
Duk akayi dariya, Mustapha yace
"Baki amai ko?"
Ya fad'a cike da zolaya, ta d'aure fuska, Ta kalli Fiddausi
"Wai waya ce miki ciki gareni?"
Khaleel cikin dariya yace
"K'yaleta Hanifah cikin ne dake sai me, kafin ki fara ita ta fara ay"
Jikinta ya bada ras! Kunya ta kamata su kuwa abin takaici dariya suke tayi"
Bayan an gama gaisawa da fira, mik'ewa tayi taje ta kwaso abinci, don dinning d'in bazai d'auke su ba su duka.
Tana ajiyewa ta shiga serving d'insu, tanayi tana satar kallonsa, mamaki kawai take ba Khaleel.
Kowa yaci yayi nat, ita kanta nan taci nata. Basu tafi ba sai bayan sallar isha'i, har mota suka raka su, suna dawowa ta shige d'aki ta tsala wanka, ranar farko data bud'e akwatin lefenta ta zaro wata pink riga iyakar gwiwa, k'amshi ta ko ina yake fita daga jikinta. Ta kud'iri a ranta na bashi mamaki, gado ta haye tana jiran shigowarsa cike da fargaba.
K'arfe goma siru, sha d'aya shiru! Har dai wurin k'arfe sha biyu bai shigo ba. Ranta ya sosu sosai, a hankali ta tashi ta bud'e k'ofar palo, ta kunna fitila amma abin mamaki wayam ba kowa, tayi turus wato d'akinsa ya tafi?
Tace
"Na bishi can?"
Sai kuma tayi tsaki
"Never! Allah ya tsareni da binshi"
Cike da takaici ta koma ta kwanta duk wannan gayun ya tashi a banza yake nufi?
"Lallai Khaleel ya cika wulak'anci" ta fad'i
Kamar zatayi kuka.



MSB✍🏼

No comments: