π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
ππππππ
π♥️π♥️π♥️π♥️π♥️
♥️π♥️π♥️π♥️π♥️π
Masha Allah Asma'u Allah ya raya mana baby boy ya baku lafiyaππππ
©PERFECT WRITERS FORUM
(P.W.F)❤️
πππππ
*KHALEEL*
πππππ
Written by Maryam S bello {MSB}✍π»
http://MaryamSBello.blogspot.com
March 2017π
PAGE
✍π»✍π»61&62✍π»✍π»
TWO WEEKS LATER
Life goes on, haka dai rayuwansu Hanifah ta cigaba da gudana cike da so da k'auna, tuni Hanifah ta cire kunya ta aje ta gefe tsantsan kulawa da soyayya zalla take nunawa mijinta, zuwa yanzu sun saba da junansu wanda basa iya jure yin nisa da juna musamman Khaleel da yanzun ne yake k'ara k'aunar matarsa, tattali da kulawa ba irin kalar da Hanifah bata gani ba.
Ko bacci zasuyi suna nan mak'ale da juna. Ranar weekends ma Khaleel bai yarda Hanifah ta shiga kitchen ita kad'ai a tare sukeyin komai, hartta gyaran gida Khaleel na taya Hanifah, shi sam baya ganin komai indai har zai faranta ma Hanifansa rai, sam baya k'aunar 6aci ranta. Itama a nata 6angaren haka ne bata san 6acin ransa ko kad'an, duk wani abu da tasan baya so takanyi k'ok'ari wajen ganin ta kauce masa, duk abinda yace mata tayi to tanayi gudun 6acin ransa, sheyasa soyayyarsu take dad'a bunk'asa ako da yaushe, saboda ko wane yana gudun 6acin ran d'an uwansa, ta yaya ma zasu samu sa6ani?
*****
Ranar wata laraba Khaleel ya dawo gida da yamma a gajiye ya shigo, daga bakin k'ofa Hanifah ta tare sa sukayi hugging juna, kiss ya mata a kumatu kamar yadda ya saba duk sanda ya shigo gidan, hannunsa ta kama ta taimaka masa ya zauna kan kujera, manne masa tayi tare da kwantar da kanta bisa kafad'arsa tana mai lumshe idanu tace
"My only wanka zakayi ko abinci zaka fara ci?yayi murmushi yana jin sonta na k'ara ruruwa a cikin ransa, yace
"Duk abinda kika ce my princess shi zan fara yi"
Tayi dariya tace
"A gaskiya wanka ya kamata ka fara yi saboda zakaji sauk'in gajiyar da ka kwaso daga nan sai kaci abinci ko?"
Yace
"Yess! My princess hakan za'ayi"
A tare suka mik'e hannunsu sak'ale cikin na juna. Ta had'a masa ruwan wanka sannan ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa, ko wane motsi nata akan idonsa ji yake kamar ya had'e ta don so, ya sauke ajiyar zuciya yace
"My princess ki daina shagwa6a ni da yawa, kinsan irin wannan duk ranar da bakida lafiya ko nayi tafiya zan sha wahala fa"
Tayi dariiya bayan ta cire masa takalmi tace
"Wannan ay daban ne, kuma ka daina cewa ranar da baka nan to ina zaka je ma?"
Yace
"Kinsan tafiya na iya kamawa ko kuma mutuwa..."
Da sauri ta toshe masa baki tace
"Shhh, daina fad'in haka my only, in ma mutuwa ce bana fatan ta riga d'aukar min kai na fiso ta fara d'auka ta"
Yayi murmushi
"Ba wanda yasan gawan fari my princess, mudai yi addu'a Allah yasa mu cika da imani"
A sanyaye tace
"Amin"
A haka ya shiga wanka, ita kuma ta fiddo masa kayan da zai sanya marassa nauyi saboda yanayi ne na zafi.
Bayan ya fito ta taimaka masa ya shirya ta fesa masa turare sannan ta kamo hannunsa suka fito palo. Kan dinning ta zaunar dashi bayan ta zuba masa jollof d'in taliyar data ji kifi da kayan lambu sai lemo mai sanyi. Sai da yaci yayi nat sanann suka koma palo suna kallo suna fira har aka soma kiran sallar magriba.
Bayan sallar isha'i sai ga Saif ya shigo gidan, Hanifah na kitchen tana dama fura ta jiyo fira na tashi had'e da dariya, murmushi tayi tace
"Su ya Saif an zo kenan"
Bayan ta gama ta samu cup guda uku da tray ta zuba fura da nonon sai ta bi da ice block a sama. Da sallama ta k'araso ta zauna bayan sun gaisa da Saif ta mik'a musu fura, kowa na sha suna fira gwanin sha'awa. Sai kuma shiru ya biyo baya, Saif ne ya katse shirun ta hanyar mik'a ma Khaleei wata farar takarda a linke cikin envelope yana murmushi. Khaleel yace
"Meye wannan kuma Saif?"
Saif yace
"Bud'e ka gani"
Ba musu Khaleel ya bud'e ya soma karantawa, sai ya fad'ad'a murmushinsa yace
"Wow! Congratulations Saif Alhamdulillah! Ashe aiki ya samu kai nayi murna Allah ya sa alkhairi"
Itama Hanifah sai ta hau murna tana taya d'an uwanta, kafin Saif yace
"Amma fa a Abuja na samu"
Take mood na kowa ya chanza Khaleel yace
"Abuja kuma? Meyasa ba'a Kaduna ba?"
Saif yace
"Wallahi nayi k'ok'arin ganin na samu a nan d'in amma hakan ya gagara, nima ba haka naso ba, na nafison kusa da y'an uwa na"
Khaleei yace
"Bakomai ay Saif, dana nan da Abujan duk d'aya ne, an mayi ta barka tunda an samu aikin shine the most important, and naga harda gida fa da motar office aka baka"
Saif yace
"Haka ne kam, ranar Monday suka kirani, so zanje in dawo idan na dawo sai muje na kaika kaga wurin"
Khaleel yayi dariya
"Ka kaimu dai"
Sukayi dariya gaba d'aya Saif yace
"Ay dama nasani, bazaka wani yarda ka bini ba tare da wannan gum d'in ba, ya kamata ta dinga barinka kana shan iska"
Aka sake saka dariya, Khaleel yace
"Kaga laifina ne wai? Kaima wata rana haka zaka yi kace baka iya tafiya ka bar Salma ko"
Yace
"Eh mana"
Khaleel yace
"To kagani, ya kamata fa azo a fara maganar sa rana ma bansan me kake jira ba"
Saif yace
"Kai ya Khaleel tun yanzu?"
Khaleel yayi dariya
"Ahh sai yaushe to? Bawani nan nasan ka k'agara zaka yi mana bogi"
Aka sake sa dariya, haka suka k'arasa firar su gwanin sha'awa sai wuraren goma saura Saif yayi sallama ya koma gida.
Kamar yadda Saif d'in yace ranar Monday tun wuraren k'arfe 8 na safe ya bar Kaduna, yana isa ya wuce direct wurin aikin inda yana zuwa yayi signing wasu papers a take kuma aka d'auksa aiki, tun kafin ya bar wurin ya kira Ammi da Khaleel ya sanar da su nasarar da ya samu sannan yanzu zai wuce ya ga gidan da aka basa, Gida ne madaidaici flat mai d'akuna uku da kitchen sai dinning. Bayan ya gama abinda zaiyi a washe gari ya bar Abuja inda aka shaida masa ya fara zuwa aiki sati mai zuwa.
*****
A gaggauce ta had'a breakfast ta rasa meya haddasa mata makara yau, d'akin Khaleel ta shiga a lokacin ya fito daga wanka yana k'ok'ari sanya kaya, tayi sallama ya amsa mata, toilet d'insa ta shiga ta kimtsa ko ina ta fito, yana tsaye gaban madubi yana taje sumar kansa ya tsaya yana kallonta ta madubi, yayi murmushi yakalli fuskarta yadda ta had'e fuska kamar hadari, yasan fushi take da shi saboda bai tashe ta da safe ba kamar yadda ya saba, kayansa da ya cire take tattarawa sai ji tayi an rungumota ta baya, ta k'ara had'e rai tana mai cigaba da abinda takeyi, juyo da iya yayi tana fukantarsa sai kawai ya rungumo ta tsam a jikinsa, ture sa ta shiga yi sakamakon zuciyarta ta taji tana wani irin tashi, duk Khaleel bai fahimta ba a tunaninsa duk cikin fushin ne.
Wani irin k'arfi yazo mata a sakamakon wani amai da ya taso mata ba shiri tayi toilet da gudu, ta shiga kwara amai kamar zata amayo y'an cikinta, da sauri Khaleel ya rufa mata baya, cike da mamaki yake tambayarta abinda ya sameta, ganin aman takeyi sosai ya sanya ya nufo ta, hannu ta d'aga masa cikin wata irin murya mai wahala tace
"Kar ka matso nan my only zaka 6ata jikinka"
Bai saurareta ba ya rik'e ta har ta gama, ya gyara wurin tare da jikinta. Gefen gado ya zaunar da ita yana shirin hugging d'inta tace
"Kar ka matso kusa dani my only bana son warin turarenka"
Da mamaki yace
"Yau kuma my princess? Kullum fa kece kike fesa min"
Tace
"Eh yau kam bana sonshi"
Yayi murmushi ya mik'e ya chanza kaya ko turare bai fesa ba ya zauna kusa da ita, a hankali ya rungumo ta yace
"Haka yayi miki?"
Ta gyad'a kai, yace
"Meyake damunki haka my princess?"
Tace
"Wallahi bansani ba my only"
Ya rungumo ta tsam a jikinsa yace
"Ko asibiti zamuje?"
Ta girgiza kanta alamun a'a, yace
"Ok muje kici abinci to"
Tace
"A'a bana jin yunwa"
Yace
"Mekika ci da zakice bakijin yunwa?"
Tayi shiru yace
"Oya tashi muje"
Dole ta tashi don ta kula har ransa ya fara 6aci.
Shi ya ciyar da ita sai dai tun kafin ta gama amai ya taso mata, da gudu tayi ciki ta shiga kwara wani aman, this time mai matuk'ar wahala saboda abinda taci wato doya da sauce, da sauri Khaleel yabi bayanta, bayan ta gama ya taimaka mata ta gyara jikinta, suka fito.
Cike da damuwa Khaleel yace
"Kodai asibiti zamuje"
Tace
"A'a don Allah my only basai munje ba, k'ila 6acin ciki ne"
Yace
"Naji amma idan aman bai tsaya ba asibiti zamuje ko kina so ko bakiso"
Tayi murmushi
"Na yarda"
Kwantar da ita yayi saman k'irjinsa yana shafa bayanta a haka har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.
MSB✍πΌ
No comments:
Post a Comment