Sunday 9 April 2017

KHALEEL Page 81&82

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥

        PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
                  (P.M.L)

               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com



              PAGE


✍🏻✍🏻81&82✍🏻✍🏻


Last ChapterπŸ™ŒπŸ» In dedication to each and every readerπŸ‘„πŸ’…πŸ»


Two years later!


Hanifah ta kammala karatunta lafiya ta fito da first class upper! Hakan yasa Khaleel ya bata surprise na zuwa L'A (Los Angeles) murna a wurin Hanifah ba'a magana.
Gaba d'aya suka shirya harda Adnan suka tafi, sunyi enjoying rayuwansu sosai sai da sukayi sati biyu suka dawo gida.
Bayan sati ukku kuma Khaleel ya shirya musu zuwa Saudia gaba d'aya harda Ammi dasu Saif. Haka kuma suka d'unguma suka tafi Makka.


Bayan sun dawo life moved on yanzu Adnan har ya shekara biyu yana gudunsa ba inda baya zuwa, ga rashin ji sai dai Hanifah bata wasa da tarbiyansa ko kad'an, zuwa yanzu har karatun qur'ani take koya masa kuma yana yi sosai, don ko hakanan zasuji yana karantowa idan yana hidimansa cikin gida ko yana wasa, hakan ba k'aramin dad'i yake musu ba.
Yana shekara uku aka sanya sa school kuma ba laifi yana k'okari.


*****

Hanifah na kwance bata da lafiya sosai Khaleel ya matsa mata suka je asibiti harda Adnan, bayan sun ga doctor aka tabbatar mata tana daga ciki na wata biyu. Murna a wajen Khaleel ba'a magana, d'aukarta yayi yana juyi da ita cikin asibitin tana ta dariya. Haka suka fito suna ta murna a bakin k'ofa suka kusa cin karo da mutum, Hanifah ta d'ago da mamaki tana kallonta, idanu ta ware tana son gano inda ta santa, matar ta fara magana tace
"Hanifah ce?"
Hanifah ta kalle ta tana d'auke da wata yarinya y'ar wata bakwai, Hanifah tace
"Eh."
Matar tace
"Humaira ce."
Da mamaki Hanifah tace
"Humaira kece?"
Humaira tayi murmushin yak'e tace
"Nice Hanifah! Na zo kwanaki gidanki bakya nan dama gafaranki nazo nema naga rayuwa, kuma dama ance duk wanda baibi duniya a sannu ba zata koya masa hankali, nidai na tuba, ki yafe min abinda nayi miki, nayi nadama ki yafe min."
Hanifah ta dafa ta.
"Kar ki damu Humaira ni dama na dad'e da yafe miki Allah ya yafe mana gaba d'aya."
Humaira ta rungumo ta tana kukan farin ciki. Tace
"Allah ya kaddara min aure bayan abinda ya faru ga mijina nan ku gaisa."
Cike razana Hanifah tayi baya baki bud'e tace
"Wannan ne mijinki? Kinsan ko waye kuwa? Deen ne fa! Khaleel kalli Deen!"
Khaleel ya rik'o ta yana fad'in
"Calm down my princess, kibi a sannu kinga bake kad'ai bace."
Ta samu ta nutsu inda Deen ya fara k'ok'arin durk'usawa k'asa yace
"Nasan ban kyauta maku ba, bani da bakin da zan rok'e ku gafara, just find it somewhere in your heart to forgive me, na rok'e ku."
Khaleel ya d'ago sa a hankali had'e da dafa sa yace
"Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu mutane? Ay indai mutum yayi kuskure kuma ya gane kuskurensa meyasa baza'ayi masa uzuri ba? Wallahi kar ka damu na dad'e da yafe maka Allah ya yafe mana gaba d'aya."
Harda d'an guntun k'wallansa yace
"Nagode muku! Allah ya saka da khairan."
Ya fad'a yana kallon Adnan yace
"Little man meye sunanka?."
Adnan yace
"Ma ismuka ake cewa."
Deen yayi murmushi yace
"Sorry ma ismuka?"
Adnan yace
"Ismi Abdul'aziz."
Deen yace
"Nice name Allah ya maka albarka."
Yace
"Amin."
Nan sukayi musabaha da exchanging numbers Khaleel yace
"Mu zamu wuce sai anjimanku, sai munyi magana."
Deen yace
"Mun gode k'warai Allah ya saka da khairan."
Adnan ya kwasa a guje yace
"Daddy kamo ni."
Khaleel ya k'yalk'yale da dariya yace
"Ok."
Take ya bishi a guje a yayinda Adnan ya ruga yana dariya, Hanifah tasa dariya sosai inda ta bisu da sauri tana dariyar itama.
Can ta hango Khaleel ya d'aga Adnan sama suna k'yalk'yatar dariya, Hanifah na zuwa ta rungumo su ta baya Khaleel ya kamo ta yace
"Come here Maman biyu."
Ta zum6uro baki.
"Ni ba Maman Biyu bace d'aya dai."
Khaleel yace
"Kin ma isa? Ay biyun nan zaki haifa insha Allah."
Tace
"Ni a'a."
Ya jawo karan hancinta yace
"Zamu gani ay."
Adnan ya shige mota da gudu inda Khaleel ya kamo Hanifah tana bisa kafad'arsa, haka suka tako har bakin k'ofa kafin Khaleel yaja ya tsaya yana kallonta cike da so! Yace
"Allah ya barmu tare har aljanna my princess."
Tayi murmushin jin dad'i tare da hugging d'insa sosai tace.
"Amin my only I love you."
Yace
"Love you more and more."
Tace
"More and more and more."
Dariyar Adnan suka ji suna juyawa suka ga yana lek'ensu ta window yana ganin sun kalleshi ya rufe fuskanshi yana dariya, yace da k'arfi
"I love you Mummy and Daddy!"
Da k'arfi suka ce
"We love you too Adnan.!"
Suka sa dariya gaba d'aya cike da farin ciki....



           

               Alhamdulillah!


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (S.W.A) da ya bani ikon kammala littafina mai suna Khaleel lafiya!
Alhamdulillah....

Toh nidai a nan na kawo k'arshen book d'ina mai suna KHALEEL! Kuskuren da  ke ciki Allah ya yafe min, darasin da ke ciki Allah ya bamu ikon d'auka.
Ina mik'a sak'on godiya ta ga dukkan masoyana Nagode da k'aunarku a gareni.😊

Ina mik'a sak'on ta'azziyata ga friend d'ina Asma'u data rasa d'anta jariri Allah ya jik'ansa yasa mai ceto ne Amin!πŸ˜’

Godiya ta mussaman ga....

*Pure moment of life writers
*Hausa Novels na (Fatima Mansur), (Raff) and my (Chuchu)
*Lovely fans
*Rash kardam novels
*Dandalin Meesha lurv
*Talented writers group
*Khaleesat Haiydar novels
*Mu Sha Karatu

Kuna raina dukkan masoyana da wanda na sani da wanda bansani ba kuna raina! ❤️

Litattafan marubuciyar~~

1) Komin nisan dare
2)HAIFAH
3) TAGWAYE NE?
4)KHALEEL

Don Allah ina cigiyar book d'ina KOMIN NISAN DARE daga farko har k'arshe mai shi ta taimaka ta turo min shi. 😘

ALLAH ya sadamu da alkhairi! Taku har kullum mai kaunarku

MARYAM S BELLO (MSB)πŸ‘„πŸ’…πŸ»❤️

KHALEEL Page 79&80

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥

        PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
                  (P.M.L)

               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com



              PAGE


✍🏻✍🏻79&80✍🏻✍🏻


Ammi dake waje tana jiyo kukan jariri sai ta fara murna tana hamdalla, wai yau Hanifanta har ta girma haka? Ikon Allah kenan.
Khaleel kuwa manne ma Hanifah yayi yana tsokananta akan bashin kiss d'insa.
Minti biyu tsakani nurse d'in tazo da babyn nannad'e cikin showel dark blue. Mik'o shi tayi da sauri Khaleel ya amshe shi yana masa kallo cike da sha'awa! Tare suke kallon babyn dukkansu sun kasa d'auke ido daga garesa.
"Masha Allah!" Shine kad'ai abinda Khaleel ke iya fad'i. Hanifah ta kalli babyn sanye cikin overall mai layi layi dark blue da light blue wanda yayi matuk'ar kyau cikinsu, y'ar hular da aka sa masa ma kalar kayan sai motsi yake yi da hannuwansa yana motsa baki. Khaleel ya kalli Hanifah yace.
"Bari na kai ma Ammi shi ta gani tana nan waje kinga kafin na dawo an gyara miki jikinki ko?"
Ta gyad'a kai tana kallon mijinta cike so da k'auna marar misali, shima haka sannan yace cikin kalmar rad'a rad'a.
"I love you."
Tayi murmushi tace.
"Love you more."
Daga haka ya fice inda nurse d'in ta soma gyara Hanifah.

Khaleel na fita Ammi ta taso da sauri ta kar6e first jikanta daga y'ay'anta guda biyu abar k'auanarta. Kallonshi takeyi take k'walla ta cika mata ido kafin kuma ta shiga tofe shi da addu'o'i. Bayan ta kammala ta kalli Khaleel tana murmushin jin dad'i tace
"Allah ya raya mana shi! Allah ya albarka ce shi ya sa masa albarka! Allah ubangiji yasa mahaddacin alk'ur'ani ne."
Khaleel nata amsawa da "Amin." Har Ammi ta mik'o masa shi tace
"Wane suna zaka sa masa?"
Yayi murmushi yace.
"Sunan Baba za'a sa masa Abdul'aziz sai ana kiransa da Adnan."
Ammi ta ware baki cike da mamaki tace.
"Allahu akhbar Allah ya raya Abdul'aziz kasa musulmin k'warai ne, Allah ya jik'an kakkaninsa." Sai kuma tace
"Ashe ma mai gida ne? To Allah yasa dai ba raggon namiji bane don dole a kawo min kud'in cefane kullum."
Khaleel na dariya yace.
"Ay Adnan ba raggo bane Ammi don zakisha mamaki idan ya zama soja nan gaba."
Tace
"Soja? To Allah yasa haka..."
Bata rufe baki ba Adnan ya fara mitsilniya, can kuma sai yasa kuka kamar an aiko sa. Ammi tace
"Ahaf! Ay daman nasani wannan raggon namiji ne, kawo shi nan."
Khaleel ya mik'a mata yana ta dariya, tana rirriga sa tace
"Kai arr! Ashe raggo ne ma? Khaleel kar6i kayanka akai ma Mamansa yasha."
Ya kar6e sa yayi masa hud'uba sannan ya wuce d'akin da Hanifah ke ciki.

Yana shiga ya tarar har an gama kimtsa Hanifah har ta chanza kaya ma. Yana zuwa ya mik'a mata shi sannan ya zaro wayarshi daga aljihu ya shiga d'aukansu hoto Adnan da Hanifah, sunyi kyau so cute! Take ya fara sending pictures d'in Adnan a family group d'insu, bada jimawa ba aka fara turo reply.
Nurse ce ta shigo tace.
"Za'a kaita d'akin hutu k'ila zuwa safe a sallame ta ko can daddare."
Yace
"Ok."
Ya kalli Hanifah yana son zolayarta yace
"Kalle ki da Allah kin wani rik'e sa sai kace da ke yake kama."
Tace
"Dama wayace yana kama dani? Da dai mace ce."
Yace
"Ay dole kice haka, don kingansa kyakkyawa yana kama da babansa kina kishi ne hala?"
Tace
"Wane kyau? Ji hancinsa fa a baje."
Ya k'yalk'yale da dariya yace
"Lallai yarinyar nan bakisan kyau ba, kowa yagansa yasan yakai inda namiji ya kai."
Tayi tsaki cikin wasa tace
"Oho dai, ya sunansa? Usman ko?"
Yace
"Usman kuma? Abdul'aziz dai, sai ana kiransa da Adnan."
Take ta d'an 6ata rai tace
"Amma fa ce maka nayi a saka Usman idan namiji ne ko?"
Yace
"Kiyi hak'uri duk d'aya ne idan kika k'ara haifan wani sai asa masa Usman d'in. Yanzu ki barsa a mijin Ammita."
Tayi murmushi
"Allah ya raya mana ya jik'an su Baba."
Yace
"Amin ya Rabbi, zo muje a kaiki ki huta ko?"
Tana murmushi tace
"To."


Ba'a sallami su Hanifah ba sai washe gari k'arfe takwas na safe.
Suna zuwa gida daman Halisa ta sanya ruwan zafin wanka ta d'ora ruwan kunu, suna zuwa ruwa yayi kawai sai aka zuba Halisa tayi wa mai jego wanka ta gashe mata jikinta tas, sannan Ammi tayi wa jariri wanka ta sum6ule shi da mai da hoda sannan ta sa masa overall plane light blue sai zanen teddy na bacci, ta nannad'e sa cikin shawul mai taushi sosai.
Khaleel yasa aka gasa mata rago aka kawo mata tana ci.
Kafin k'arfe d'aya na rana Saif sun iso, gidan ya kacame da murna Saif kamar ya cinye babyn dan so.


A hankali gida ya fara cika da y'an ganin baby, Rufaida ma tazo ganin baby kuma tayi murna. Y'an uwa ma sun fara hallara ganin baby, duk wanda yaga babyn sai yace Khaleel ne sak.
Kullum Khaleel na manne da Hanifah sai Ammi tayi da gaske yake fita saboda mutane na shigowa.
Da yafita can bayan minti kad'an zai fara lek'e sai da Ammi ta fito tayi mai tatas sannan ya bar zuwa. Haka aka sha zaman barka.
Ranar suna ba'ayi wata bid'a ba, an dai ci ansha. Amarya tayi kyau tayi fari da fresh sosai. An sha hotuna dai kamar ba gobe. Ana gama suna Khaleel ya cigaba da mak'ale ma Hanifah Ammi har ta fara gajiya tace suzo su koma gidansu. Khaleel murna ita kuma Hanifah tace bata komawa sai tayi 40, Ammi na jinsu suna gardama sai dai tayi dariya kurum.

Saboda yadda Hanifah ke samun kula sai gashi kafin suyi arba'in ta girgije itada babyn, duk wannan kumburin haihuwar ya tafi ta zama y'ar cas da ita. Adnan wani irin girma yakeyi sosai idan ka ganshi sai kayi zaton d'an wata biyu ne ya wani zama k'aton gaske, gashi kullum sai dad'a kyau yakeyi ya zama Khaleel sak.
Suna yin arba'in Hanifah ta tarkata ta koma gidanta saboda Khaleel ya matsa.
Tana komawa kuma suka soma lectures yanzu ta shiga level 2, gashi kuma sun bud'e sabon babi na soyayya ita da Khaleel d'inta.


Bayan wata Biyu.

Bayan wata biyu kuma Salma ta haifi kyakkyawar d'iyarta mai kama da Saif. Daga nan kuma aka fara gudanar da shagalin suna. Yarinya taci sunan Ammi ana kiranta da Amal.



MSB✍🏼

Thursday 6 April 2017

KHALEEL Page 77&78

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥

        PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
                  (P.M.L)

               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com



              PAGE


✍🏻✍🏻77&78✍🏻✍🏻


Kafin kace mey labarin cikin Humaira ya baza makaranta, wad'anda ke zaune a hostel haka sukayi ta turarowa ganinta, tsabar gulma. Humaira ta rasa inda zatasa kanta, saboda haka washe gari asubar fari ta bar garin inda ta kama hanya zuwa garinsu. Tana isa ta tsaida adaidaita ta tafi gida gabanta in banda harbawa ba abinda yakeyi, hankali tashe ta doshi cikin gidansu, tana zuwa ta iske mahaifiyarta kitchen tana zuba ruwan tea cikin flask, ta baya ta rungumo ta tare da fashewa da kuka mai tsanani. Da mamaki Maman ta juyo tana kallon d'iyar tata cike da mamaki tace.
"Aishatu Humaira? Lafiyanki zaki shigo babu sallama, har kunyi hutu ne?."
Humaira kuka take sosai harda shassheka, da k'yar Mama ta samu Humaira tayi shiru, hannunta Maman ta kamo suka koma palo suka zauna, cike da nutsuwa Maman tace
"Ke Humaira, kalle ni nan."
Ta fad'a tana kallonta cikin ido, Humaira ta d'ago a hankali tana kallon Maman a kunyace, yanzu ita shikenan sai dai tace ma Mama tana da ciki? Wannan abun kunyar da me yayi kama?
"Wai bada ke nake magana ba? Ki fad'a min ko korarki akayi daga makarantar ne bansani ba?."
Kuka ta k'ara fashewa dashi tace
"A'a."
Maman tace
"Meye to? Ko hutu aka baku kuma?."
Nan ma "A'a."
Maman ta fusata ta mik'e, tana fad'in.
"Kaji min yarinya, kinzo gida kina ta faman yi min kuka, sannan kink'i fad'i min abinda ya same ki, ta yaya zan sani? To shikenan kar Allah yasa kiyi magana."
Tana gama fad'in haka ta juya da niyyar tafiya Humaira tayi saurin rik'o mata hannu gami da zubewa k'asa tana kuka mai tsuma rai.
"Mama na tuba, don Allah Mama idan na fad'a miki abinda zan fad'a miki kar ki kore ni amma duk hukuncin da ya dace dani kiyi min."
A d'an tsorace Maman tace
"Wai lafiyarki ke? Kiyi min magana mana haba!"
Cikin kuka tace
"Wallahi Mama ba halina bane kuma kinsan haka, wallahi tsotsai ne da sharrin shaid'an."
"La'ila ha illallah Muhammad Rasulillah! Wai wace irin magana kike haka?."
Ta k'ara sa kuka, tace
"Mama ciki ne dani, don Allah Mama kar ki k..."
Tass! Mama ta d'auke ta da mari mai zafi tace
"Ciki? Ciki fa kika ce Humaira? Wayayi miki? Ko fyad'e akayi miki?."
Kuka take hankalinta a tashe ta rungumo k'afufuwan Maman tana cewa
"A'a wallahi Mama tsotsai ne da sharrin shaid'an...."
Maman ta janye k'afarta a hankali tana kallon y'ar tata cike da tashin hankali.
"Innalillahi wa inna ilaihir raj'iun, Humaira tarbiyyar da na baki kenan? Humaira duk tsawon shekaru goma sha taran da na d'auka ina baki kyakkyawar tarbiya amma rana d'aya kiyi watsi dashi, ki watsa min k'asa ido? Humaira? Ciki kina budurwa?"
"Mama na tuba kar ki kore ni! Mama ki sassauta min don girman Allah Mama."
Maman tace
"Yau don kinga mahaifinki baya raye shine kike son nuna min gazawata wurin baki tarbiyya ko?"
Ta fad'a tana k'ok'arin yin kuka.
"Mama kar kiyi min kuka! hawayenki wani bala'i ne a tattare dani, na tuba Mama ki yafe min!"
"Wai da kike cewa in yafe miki ni kika yi wa laifi ne? Allah (S.W.A) kikayi wa laifi don haka shi zaki nemi gafarsa bani ba."
Humaira ta rasa yadda zatayi sai kuka takeyi, Maman tana kuka sosai ta yi d'akinta da sauri tana salati, rufe k'ofar da key tayi, a yayinda Humaira tabi ta da gudu tana zuwa ta shiga buga k'ofar hankali tashi.
"Mama! Ko magana kiyi min ko zanji sanyi a raina. Kinji Mama!"
"Ibrahim?." Cewar Mama tana kuka.
Hankali tashe Ibrahim yace
"Mama lafiya kike kuka?."
Mama tace
"Ibrahim kazo gida ina buk'atarka kusa dani."
Ibrahim yace
"Mama menene?."
"Kai dai kawai kazo maganar bata waya bace."
"To." Kawai ya iya cewa, aikuwa next available flight ya hau ya dawo gida.
Yana shigowa yaci karo da Humaira kwance shame shame k'asa tana gunjin kuka, da sauri yace
"Ke what's happening here wai?."
Tana ganinshi ta tashi da gudu ta rungumo shi tana kuka.
"Meya faru wai?." Cewar Ibrahim hankali tashe
"Ciki ne da ita Ibrahim."
Da sauri ya saketa yana kallon Maman cike da tashin hankali yace
"Ciki kuma? Wai Humaira keda ciki Mama?."
Maman tace
"Ita fa, Humaira dai ciki tayo."
Shima salati yasa sosai yana kallon Humaira bak'in ciki kwance a ransa yace
"Humaira! Wayayi miki ciki?."
Tasa kuka, yace
"Au bazakiyi magana ba?."
Ta tsaya kallonsa amma ta kasa magana, yace
"Ok taurin kai zakiyi? Shikenan."
Belt d'insa ya shiga zarewa da sauri da niyyar tsula mata tasa ihu, Mama ta rik'e masa hannu tana kuka tace
"Kar ka dake ta, dolenta ma zatayi magana ay bata isa ba, idan ka k'ara tambayarta batayi magana ba ka tsule ta."
Ya aje hannunsa a hankali yana kallon Humaira rai a 6ace yace
"Ina jinki."
Cikin inda inda tace
"Wani Malami ne dama....dama..."
Ibrahim yace
"Dama mey?."
Da k'yar suka sata ta fad'a abinda ya faru bata 6oye komai ba, inda ko wanensu ya cika da 6acin rai marar misaltuwa. Mama tace
"Au daman laifin naki da yawa kenan? Yanzu har akwai me biya miki buk'atarki bayan Allah har sai kin rok'i wani malamin? Ashe dama kin 6ata Humaira?."
Salati suka sa itada Ibrahim inda Humaira ke cigaba da basu hak'uri.
"Mama tace
"To yayi miki kyau, ay gashi nan kinga irinta, shashashar banza shashashar wofi wadda bazata san ciwon kanta ba, ina ma amfanin irin haka Humaira?."
Ibrahim yace
"Amma fa ba wanda zai zubar da cikinnan sai kin haife shi wallahi, kinga alhakin wata ya kama ki ko? Ta d'auke ki da zuciya d'aya ke ashe muguwa ce? Hmm to daga yau sai ki d'auki darasi."
Mama tace
"Dama ya za'ayi a zubar dashi? Ay dole ma ta haife shi, kuma sai mun nemo malamin nan dole a mik'a shi ga hukuma wallahi."
Ibrahim yace
"Dole Mama Allah ya kyauta ya tsarkake mana zuciyarmu da imani."
Mama tace
"Amin Ibrahim, ke kuma wuce muje kuma wallahi ki dage da neman yafiyar ubangiji kinji na gaya miki."
A sanyaye tace
"To nifa Mama kun yafe min?."
Mama tace
"Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu? Nidai fatana Allah ya shiryar dake Humaira amma kisani ba ruwana dake, har sai kin haihu, sannan da kin sauka aure zan miki, Allah ya kyauta."
Haka ta tasa k'eyar ta har d'aki sannan ta kalleta tace
"Daga yau idan naga kina yawo cikin gidannan sai kin sani, ki dage da istigifari har ki samu Allah ya yafe miki."
Tun daga wannan rana Humaira ta dage da addu'a da kuma neman gafarar ubangiji, hartta wayayonta ta kashe su gaba d'aya, kullum zaka ganta da qur'ani tana karatu ko cazbaha tana ja, sai dai itada Mama ba kamar dah ba, iyakancinsu gaisawa da safe daga nan kuma shikenan. Gaba d'aya gidan baya mata dad'i gatan da ake bata dah yanzu babu, tuno yadda suke mata idan ta dawo ko wane hutu kamar su cinye ta, sannan gaba d'aya suke cin abinci kan table ana fira, amma yanzu sai dai taci abinci a d'aki kamar munafuka. Tayi nadama ba kad'an ba,  sannan taga illar son zuciya abinda ya janyo mata.



*****


Cikin Hanifah ya tsufa sosai, tashi da k'yar zama da k'yar, gashi exams suke tana ta addu'a sai ta gama exams zata haihu, aiko lafiya lau ta gama har Khaleel ya shirya ya maida ita gida haihuwa inda aka cigaba da bata kyakkyawar kulawa.
Duk da haka kullum tana tare da Khaleel ko wane motsinta sai yace mata sannu. Kayan babies kuwa sai da Ammi ta taka masa burki don tarkace ya dinga kwasowa.


Yau da rana suna zaune a palo suna fira sama sama inda dama tun safe Hanifah ke jin ciwon mara da baya tana dai daurewa bataso ta nuna.
Aikuwa har dai Khaleel ya gano ta don ba shiri taji wani irin ciwo ya kama ta marar misaltuwa!
"Washh!" Tace had'e da cije le6e cike da azaba, sai gumi take had'awa.
Khaleel yayi kanta a rud'e ganin har tana neman duk'ewa k'asa.
"Hanifah! Nak'udar ce?."
Tasa ihu.
"Wayyo Allah ya Khaleel zan mutu ciwo."
Kamo ta yayi kamar zaiyi kuka yana shafa bayanta
"Sannu bari na kira Ammi."
"Ashhh! Zan mutu ya Khaleel."
"Hold on baby bazaki mutu ba insha Allah, just wait ok?"
Ta girgiza kanta da k'yar, ya tashi da gudu yayi ciki, can sai gashi sun dawo shida Ammi a rud'e, ita ta taimaka masa suka sata a mota sannan Ammi ta d'auko maternity bag nata.

 Cikin k'ank'anin lokaci suka isa asibiti, inda suna zuwa akace nak'uda takeyi.
Ba yadda ba'ayi da Khaleel ba yace sai ya shiga ciki, dole aka k'yale sa ya shigan, don yace yana so yaga matarsa yadda zata haihu. Yana shiga Ammi ta d'auko wayarta don kiran su Saif.
Ya tsorata yadda yaga Hanifah gaba d'aya ta chanza kamar ba ita ba gumi sai sauko mata yakeyi. Khaleel yaje gefenta jikinsa yayi sanyi ya kamo hannunta yana shafa kanta, kuka ta fashe dashi tace.
"Zan mutu Ya Khaleel."
Yace
"Shhh kiyi addu'a insha Allah komai zaizo mana da sauk'i kinji i love you."
Wani nishi yazo mata da k'arfi nurse d'in tace
"You are doing good, i can see the head, just 2 good pushes babynki zai fito."
Kuka take sosai cike da azaba ta k'ara wani irin nishi mai zafi inda cikin ikon Allah aka zaro mata babynta!
Nurse d'in ta d'aga babyn yana ta kuka tace
"Congrats baby boy ne!"
Khaleel ya ware idanu cike da tsantsan farin ciki yace
"Masha Allah! Allah ya raya mana."
Ya kamo Hanifah ya rungume ta sosai. Nurse d'in na murmushi tace
"Bari na gyara muku shi yanzu."
Khaleel harda hawayen farin ciki ya kalli Hanifah ya kashe mata ido yace.
"Ya alk'awari na? I'm waiting."
Ta turo baki
"Wane alk'awari bangane ba."
Yace
"Kin manta? To na kiss ni nayi winning don haka a bani kiss d'ina ina jira."
Ta ware idanu waje tace
"Ya Khaleel!"




MSB✍🏼

Wednesday 5 April 2017

KHALEEL Page 75&76

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥

        PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
                  (P.M.L)

               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com



              PAGE


✍🏻✍🏻75&76✍🏻✍🏻


Life moved on, Hanifah da Khaleel na zaune suna kallon indian series a ZeeWorld a yayinda Hanifah ta kwanta bisa k'irjinsa, Khaleel kuma na shafa mata gashinta. Juyo da fuskarta tayi tana kallonsa tana jin wani nishad'i a yayinda Khaleel yayi kamar bai ganta ba, don kuwa yadda take kallonsa idan yace su had'a ido baisan a wani hali zuciyarsa zata shiga ba, hannunshi ta kamo tana shafawa a hankali kafin ya kalleta finally yana d'aga mata gira sama yace.
"Yane? Ko inzo ne?."
Tayi dariya tace.
"Wai kai my only banida damar kallonka sai ka wani ce kazo?."
Dariya ta su6uce masa ba shiri yace.
"Ay indai kinga mata na ma mijinta irin wannan kallon to da magana a k'asa, nidai i won't reject you don kinsan bana gajiya dake my princess."
Tayi dariya cike da farin cikin jin kalamun shi tace.
"Nima bana gajiya da kai my only, i love you."
Yace.
"I love you more."
Hanifah ta ga yana k'ok'arin mik'ewa ta had'e rai ta kalle shi.
"Ina zakaje yanzu?."
Yayi dariya.
"Wurin budurwata mana, bana ce miki kishiya zan miki ba?."
Tayi dariya.
"Aiko bana tsoron ko wacece ta shigo ta gani idan ban kakkarya ta ba."
Yayi dariya harda duk'ewa yace.
"Hoo Hanifah! Wannan cika bakin naki fa? Yanzu da kinga da gaske nake na tabbata sai inda k'arfinki ya k'are sannan ki samu nutsuwa."
Ta harare shi da wasa tace.
"Dah kenan, banda yanzu."
Yace
"Haka kika ce?"
Tace
"Sosai ma."
Yana dariya yace
"Shikenan kar kiga laifina idan kikaga ana gyaran d'aki to ba ruwana!"
Ta tafa hannu tana dariya
"Ni zan ma taya ka gyaran d'akin."
Cikin ransa yace bari ya gwada ta ya gani. Sai ya d'auko wayarsa daga aljihu ya soma kiran k'arya. Da sauri ya bar palon ya shiga amsa waya kamar da gaske.
"Hello baby? Ya kike? Wallahi lafiya, kinsan nayi missing d'inki da yawa, yanzu ma zan shigo gidan naku ki aje min irin kazar nan da kika gasa min rannan."
Ya k'yalk'yale da dariya yana kashe murya kamar gaske yace
"Haba! Ashe kina sona kema? Insha Allah yanzu zaki ganni..."
Fizge wayar tayi da k'arfi tana huci, kallonta yakeyi yana murmushi, a yayinda ta kara wayar kunnenta da niyyar zagi, jin shiru ya sa ta duba wayar da sauri ganinta a kashe yasa ta kalli Khaleel tace.
"Au dama zolayata kake?"
Yace
"Gwada ki nayi gashi nan tun bance zanyi auren ba kin soma nuna kishinki."
Bata san lokacin da ta d'auko pilon kujera ta soma jefa masa ba, yana dariya yana kaucewa yana mata gwalo, daga k'arshe ya fice daga palon yana dariya, d'aga murya tayi tace.
"Wallahi ka kyauta my only."
Bisa kujera ta zube tana maida numfashi sannan tana dariya lokaci d'aya.


*****

Haka dai rayuwar ke gudana cikin hukuncin ubangiji wanda yanzu su Hanifah semester ta mik'a sosai, sannan kuma cikinta ya dad'a tsufa ya fito ras dashi, hakan kuma fatar jikinta kamar tayi dilka tayi haske ta kuma yin k'iba kad'an hakan ya sa tayi kyau abinta. Kwata kwata ta fita daga harkan Humaira ko magana batayi mata koda kuwa sun had'u ko kallo bata ishe ta ba. Da Rufaida suke d'an ta6a k'awance shima daga school ne kuma su rabu a nan, don ma dai suna shiri da Rufaidar amma Hanifah ta rufe k'awance don ta tsorata.

Yau lecture d'in yamma sukayi suna fitowa ta hango motar Khaleel don kuwa yanzu ya hana ta driving, da sauri ta k'arasa tana murmushi, yana hango ta ta madubin gaban motar ya saki murmushin shima, har ta k'araso yana kallonta itama shi d'in take kallo, tana shiga ya ja motar suna tafe suna fira gwanin sha'awa, kafin su isa gida sai da ya tsaya yayi mata shopping ya kuma siya mata kayan lashe lashe da yasan zataji dad'in cinsu.


*****

Tana shiga hostel d'in ta yar da jakarta kan katifa sannan ta fad'a bisa tana maida numfashi, Rufaida da itama yanzu ta shigo d'akin tana sauya kayan jikinta ta tsaya tana kallonta, can kuma taja tsaki ta cigaba da abinda takeyi.
Tana gama chanza kayan ta ga Humaira ta tashi tayi toilet da gudu sai dai Rufaida ta jiyo kakarin amai, da sauri ta k'arasa ciki tana tambayar abinda ya same ta.
Tana cikin aman sauran room mates d'insu suka soma shigowa su kusan hud'u, jin amai yasa suka shiga suna tambayar abinda ya same Humaira, Rufaida ce tabasu amsa.
"Wa ma yasani? Nima yanzu naga tana ta aman."
D'aya daga ciki tace.
"To! Allah ya sauwak'e."
Haka ta gama aman ta dawo d'akin ta zauna rigib kan katifa, gaba d'aya zuciyarta tashi takeyi ta rasa dalili.
Haka dai ta wuni tana aman a wahalce dole su Rufaida suka taimaka mata suka kaita asibiti, an gudanar da gwaji inda aka tabbatar mata da tana d'auke da d'an jaririn ciki na wata kusan d'aya. Ana fad'a mata ta zube k'asa sai ta dinga rusa ihu, sai sambatu takeyi tana kiran ta tuba wai son zuciya ya ja mata. Haka kuma aka dawo da ita still tana surutan sai cewa take ta shiga uku tana kuka wiwi, y'an d'akin nasu sun taya ta jimami sosai sannan kuma sun mata fad'a da tambayoyi barkatai akan ta fad'a musu yadda akayi ta kwaso ciki tana budurwa, wannan abin kunya ina zasu kaishi? Ita dai Humaira ba bakin magana gaba d'aya jikinta yayi sanyi, banda tunanin iyayenta da yayanta ba abinda takeyi, yanzu da wane ido zata kallesu? Tunani barkatai takeyi a yayinda take kuka sosai tana dana sani. Cikin kuka tace
"Na shiga uku ni Humaira! Yanzu ya zanyi? Na cuci kaina na cuci rayuwata, Sadiya kin cuce ni yanzu ina zan sa kaina?"
Tana magana tana d'ora hannunta saman kai, duk tafi jin Mamanta tasan ma kashe ta kawai zatayi. Duk yadda su Rufaida suka so rarrashinta abin yaci tura, ta kalli Rufaida da jajjayen idanunta tace
"Nasan kinsan abinda muka aikata, wallahi sharrin shaid'an ne ki taimake ni ki fad'a min yadda zanyi don Allah?."
Rufaida tace.
"Tabbas sheyasa akace kabi duniya a sannu sannan duk yadda kika d'auke ta haka zata zo miki, idan kika d'auke da sauk'i to fa haka zata zo miki, sannan akasin haka ma, wallahi ki nutsu kindai ga sakamakon ki tun a duniya kafin ki riske na lahira. Duk abinda kika aikata na sani kawai kallonki nake, wai Humaira har kibada kanki ga wani k'ato wanda ba muharraminki ba yayi amfani dake saboda wata buk'ata taki can ta banza? Sannan shawarata ta k'arshe a gareki shine kar kiyi gigin zubar da cikinnan koda wasa."
Humaira ta kalle ta da mamaki tace.
"Kina nufin na haifi d'an shege ina zan kai kunyar duniya?."
Rufaida tayi murmushin takaici tace.
"Kina so ki aikata laifi akan laifi kenan? Ga laifin zina gana kisan kai? Sanda kika bada kanki ga wani can bakiji kunya ba sai da kika d'auko cikin zakiji kunya? Lallai ma!"
D'ayar mai suna Hafsat tace.
"Gaya mata dai y'ar uwa, idan kunne yaji to jiki ya tsira."
Haka dai Humaira take binsu da kallo d'aya bayan d'aya tana hawaye, shikenan ita yanzu d'an shege zata haifa? Ta d'ora hannu a kai tare da fashewa da wani irin kuka.
"Wayyo ni Allah na, yazanyi da mahaifiyata? Me zance mata? Na cuci kaina gaskiya."
Hafsat tace
"Hak'uri zakiyi ki kar6i duk hukuncin daza tayi miki, saboda kin cancanta."  Humaira cikin mik'a wuya ta mik'e tsaye tana hawaye tace.
"Tabbas ya zama tilas na sanar da ita, sannan a shirye nake na kar6i ko wane hukuncin da zatayi min, fatana kar ta yafe ni, Allah yasa ta yafe min."
Rufaida tace
"Insha Allah komai zaizo da sauk'i, kidai yi addu'a sannan ki dage da isgifari don neman gafarar ubangiji."
Humaira tace
"Na tuba Allah! Allah na tuba ka yafe min..."



MSB✍🏼

KHALEEL Page 73&74

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥

        PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
                  (P.M.L)

               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com



              PAGE


✍🏻✍🏻73&74✍🏻✍🏻

Bayan Sati Ukku!

Bayan sati ukku Su Hanifah suka soma komawa makaranta.
A yau ne Humaira ta tashi tana ta baza sauri wanda duk abinda takeyi akan idon Rufaida, shirinta ta gama tsab tare da d'auko wayarta ta latsa wasu numbers, can tace
"Hello? Kina ina?."
Humaira tace
"Yauwa mu had'u wurin round yanzu don gani nan zan bar hostel. Yauwa sai nazo."
Ta juyo tana kallon Rufaida wanda take ma tunanin tana bacci, Rufaida kuwa da sauri ta maida idonta ta rufe don kar ta gane. Ganin haka yasa Humaira tayi murmushi ta fice daga hostel d'in,  hakan ya sanya Rufaida tayi wuf! Ta mik'e gami da dauk'o hijabinta da nik'af tabi bayanta.
Da dubara ta samu tayi ta bin Humaira har suka fito wajen gate daga wani lungu take hango komai inda take tsaye. Ganin sun tsaida adaidaita ya sanya ta tsaida wata da sauri ta cigaba da bin bayansu har taga sunyi tafiya mai nisa.
Daga wajen gari taga suka tsaya tare da fitowa, sai da ta bari sunyi  nisa tukunna ta fito itama sanye da nik'af tabi bayansu, wata y'ar bukka ta tsaya inda ta samu bayan ginin ta la6e tana hangen komai kuma tanaji. Ga mamakinta wani mutumi taga ya fito da carbi a hannunsa inda suka baje nan k'asa. Malamin ne ya soma tambayarsu.
"Meke tafe daku?."
Wadda suka je tare ce ta fara magana
"Allah gafarta Malam, kamar dai yadda na maka bayani a waya jiya shine ya kawo mu, yau d'in."
Ya gyara zamansa yana kallon k'awarta wadda taji Malamin na kira da Sadiya, yace.
"Naji dai, amma dai Sadiya kin mata bayanin yadda nake aikina?."
Tace
"Tabbas na mata bayani Malam, kuma ta yarda."
Yace
"Madallah, yanzu ke a naki jawabin kince wani saurayi kike so ki mallaka sai yadda kikayi dashi? Sannan yanada mata hakane?."
Humaira ta girgiza kanta alamun eh tace
"Haka ne Malam, a taimaka min Malam, ni buk'atata dukiyarsa nakeso da nace ya bani zai bani ko nawa ne."
Malamin yace
"Ba damuwa, taso ki shigo daga ciki."
Ba musu ta tashi ta shiga, nan taba Sadiya ajiyar jakarata.
Duk Rufaida na tsaye ta cika da mamaki marar misaltuwa!
Can sai gasu sun fito Malamin ya mik'a mata wasu magunguna Rufaida ta kasa kunne tana jin bayanin sosai, sannan tayi sand'a ta fita da gudu.


Da daddare suna bacci Rufaida ta tashi ta chanza magungunan da aka ba Humaira, wasu ma cikin k'aramar jarka suke masu kama da rubutu, tayi dabaru ta zubar ta chanza wasu, haka ta kwanta zuciyarta fal farin ciki, kuma haka ta k'udiri aniyar wargaza duk wani shiri da zatayi don samauwar farin cikin rayuwar auren Hanifah.


******

Karatu ya fara kankama na second semester, karatu suke ba kama hannun yaro.
Rayuwar Hanifah sai wanda ya gani, don Khaleel yanzu ba abinda yake bata sai kulawa, soyayya da kuma farin ciki, ko aikin gidan baya bari tana yi, tattalinta yake kamar k'wai, ga cikinta yanzu ya turo ya fito ana ganinshi.
Kullum Hanifah cikin gode ma Rufaida takeyi akan hallacin da tayi mata, don ta taimake ta ba kad'an ba, yanzu gashi suna gudanar da rayuwarsu cikin farin ciki da walwala tare da kulawa da junansu.

Ranar wata Juma'a Saif ya kira Khaleel bayan sun gaisa ne Saif yace.
"Ya Khaleel gamu nan zamu kama hanya zamu zo Kaduna."
Cike da farin ciki Khaleel yace
"Seriously? Can't wait sai kun iso."
Bayan sunyi sallama ya sanar da Hanifah aikuwa tayi ta jin dad'i.

Washe gari asabar sanin Khaleel ya hana ta ko wane aiki ya sa Hanifah bashi surprise, a hankali tayi kitchen ta had'a masa had'dad'en breakfast mai rai da lafiya tabi da kunun gyad'a a sama sai k'amshi ke tashi. Toilet ta wuce ta tsantsara wanka ta sanya wasu kaya masu bayyanar da surar jiki da wani fitanannen turare mai dad'i. Kitchen ta koma ta jera komai kan tray ta nufi d'akinsa. Yana kwance yana bacci peacefully a hankali ta d'ora tray d'in saman side drawer sannan taje gefensa ta zauna tana kallonsa cike da sha'awa da k'auna marar misaltuwa!
Gefen fuskarsa take shafawa a hankali tana kallon yadda yake motsi sai ya k'ara mata kyau da kwarjini. Jin ana masa yawo a fuska yasa ya bud'e idanunsa tar akan Hanifansa!
Wani kallo yabi ta dashi yana smiling, light kiss ta masa a kumatu sannan taje daidai kunnensa ta rad'a masa, gaba d'aya ta kashe masa jiki da k'amshin turarenta. Dama Hanifah tasan a rina don duk cikin turarukanta ya fison wannan sheyasa ma ta feso shi.
"Good morning handsome! I made you breakfast in bed."
Ya kalleta sai kuma ya had'e rai yace.
"But why my princess? Bana hana ki ba?."
Hannu tasa a bakinsa tace.
"Shhh! I'm sorry my only, don't reject my offer, i just want to show you how much i love you, that's all, pleasee."
Ta k'arasa cike da shagwa6a wanda tasan idan har tanayi to fa tana kashe ma Khaleel jiki, gaba d'aya ya narke da shagwa6ar Hanifah.
A hankali ta mik'ar dashi tace.
"Muje kayi brush."
Ba musu ya mik'e har toilet ta sa masa Maclean ta mik'a masa yana yi tana basa  ruwa, har ya gama suka fito daga toilet d'in.  Kamo ta yayi ta fad'o jikinsa ya shiga aika mata da best kiss of her life, take itama ta shiga maida masa, sun d'auki tsawon lokaci kafin ya sake ta ya kamo ta yana jan karan hancinta, cike da zolaya yace.
"Tunda kika dafa abincin nan to fa tare zamu cinye shi."
Dariya tayi wanda ke k'ara mata kyau tace.
"Allah ko? To mugani dan ni bana jin yunwa."
Yana dariya yace.
"Ay baki isa ba, don d'ure zan miki."
Ta k'yal'kyale da dariya tace.
"D'ure ya Khaleel? Sai kace dai yarinya?"
Yace.
"Duka duka yaushe ma kika girman? Da wake baki abinci?"
Ta turo baki tace.
"Oho."
Yace
"Kingani ko? Kema kinsan gaskiya don haka yi miki d'ure bazai min wahala ba."
Ita dai sai dariya takeyi.
A haka suka k'arasa kan gado Khaleel na zolayarta tana dariya, suka karya cike da farin ciki a zukatansu.

Da yamma suka shirya sukaje gida, a nan suka tarar da su Saif. Nan da nan gidan ya rikice da fira, itama Salma cikinta har ya fara fitowa.
Da daddare suna zaune suna cin abinci Khaleel ya kalli Ammi yace.
"Gaskiya Ammi kiyi wa Hanifah magana wai ita dole sai ta dawo gida wankan jego."
Kowa ya bud'e baki cike da mamaki, Saif yace.
"Kai Ya Khaleel! Ko kunya bakaji kana maganar nan a gaba Ammi."
Khaleel yace
"Kunya? Mamata ce fa wace kunya?."
Ammi tace.
"Wai kai ina ruwanka ne Saifullahi? Meye naka a ciki?."
Saif ya ta6e baki.
"Dama nasan hakan zata faru, Ammi akwai kushe mutum akan Khaleel."
Khaleel yayi dariya.
"Kana kishi ne? Ammi tafi sona."
Saif yace.
"Naji d'in."
Hanifah da Salma na gefe suna dariya, Hanifah cikin dariya tace.
"Nifa da gaske nake gida zan dawo haihuwa."
Ammi tace
"Gidanku, kya bari dai mijinki ya baki izini ay ko?."
Hanifah ta turo baki cike da shagwa6a tace
"Ni gaskiya a'a Ammi."
Khaleel na kallonta yana dariya yace
"Dama wayace bazaki haihu nan ba? Amma dai ay duk d'aya ne da nan da can d'in ko?"
Hanifah tace
"Naji nidai dan Allah nan."
Ammi ta mik'e tana hamma
"Kunga tafiyata sai da safe."
Khaleel yace
"To muma ku tashi mu tafi gida."
Hanifah tace.
"To ay bamu gama magana ba."
Khaleel yace
"Idan mukaje gida ma k'arasa."
A haka sukayi bankwana suka tafi. A mota ne Hanifah tace
"Ina jinka my only."
Yayi dariya ya kwaikwaiye ta.
"Ina jinki my princess."
Ta soma bubbuga kafad'a tana kukan shagwa6a. Yana ta mata dariya yace
"Kar ki damu my princess zaki dawo gida kinji? Don't worry."
Cike da jin dad'i tace
"Da gske my only?"
Yace
"Sosai ma! Anything for my princess." Bisa fad'ad'an Kafad'unsa ta kwantar da kanta had'e da lumshe idanu, a hankali tace.
"Thank you my only. I love you so much."
Da hannu d'aya ya shafi gefen fuskanta yana murmushi yace.
"Love you more."
A haka suka isa gida tana kwance bisa kafad'arsa.



MSB✍🏼