Thursday 6 April 2017

KHALEEL Page 77&78

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥

        PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
                  (P.M.L)

               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com



              PAGE


✍🏻✍🏻77&78✍🏻✍🏻


Kafin kace mey labarin cikin Humaira ya baza makaranta, wad'anda ke zaune a hostel haka sukayi ta turarowa ganinta, tsabar gulma. Humaira ta rasa inda zatasa kanta, saboda haka washe gari asubar fari ta bar garin inda ta kama hanya zuwa garinsu. Tana isa ta tsaida adaidaita ta tafi gida gabanta in banda harbawa ba abinda yakeyi, hankali tashe ta doshi cikin gidansu, tana zuwa ta iske mahaifiyarta kitchen tana zuba ruwan tea cikin flask, ta baya ta rungumo ta tare da fashewa da kuka mai tsanani. Da mamaki Maman ta juyo tana kallon d'iyar tata cike da mamaki tace.
"Aishatu Humaira? Lafiyanki zaki shigo babu sallama, har kunyi hutu ne?."
Humaira kuka take sosai harda shassheka, da k'yar Mama ta samu Humaira tayi shiru, hannunta Maman ta kamo suka koma palo suka zauna, cike da nutsuwa Maman tace
"Ke Humaira, kalle ni nan."
Ta fad'a tana kallonta cikin ido, Humaira ta d'ago a hankali tana kallon Maman a kunyace, yanzu ita shikenan sai dai tace ma Mama tana da ciki? Wannan abun kunyar da me yayi kama?
"Wai bada ke nake magana ba? Ki fad'a min ko korarki akayi daga makarantar ne bansani ba?."
Kuka ta k'ara fashewa dashi tace
"A'a."
Maman tace
"Meye to? Ko hutu aka baku kuma?."
Nan ma "A'a."
Maman ta fusata ta mik'e, tana fad'in.
"Kaji min yarinya, kinzo gida kina ta faman yi min kuka, sannan kink'i fad'i min abinda ya same ki, ta yaya zan sani? To shikenan kar Allah yasa kiyi magana."
Tana gama fad'in haka ta juya da niyyar tafiya Humaira tayi saurin rik'o mata hannu gami da zubewa k'asa tana kuka mai tsuma rai.
"Mama na tuba, don Allah Mama idan na fad'a miki abinda zan fad'a miki kar ki kore ni amma duk hukuncin da ya dace dani kiyi min."
A d'an tsorace Maman tace
"Wai lafiyarki ke? Kiyi min magana mana haba!"
Cikin kuka tace
"Wallahi Mama ba halina bane kuma kinsan haka, wallahi tsotsai ne da sharrin shaid'an."
"La'ila ha illallah Muhammad Rasulillah! Wai wace irin magana kike haka?."
Ta k'ara sa kuka, tace
"Mama ciki ne dani, don Allah Mama kar ki k..."
Tass! Mama ta d'auke ta da mari mai zafi tace
"Ciki? Ciki fa kika ce Humaira? Wayayi miki? Ko fyad'e akayi miki?."
Kuka take hankalinta a tashe ta rungumo k'afufuwan Maman tana cewa
"A'a wallahi Mama tsotsai ne da sharrin shaid'an...."
Maman ta janye k'afarta a hankali tana kallon y'ar tata cike da tashin hankali.
"Innalillahi wa inna ilaihir raj'iun, Humaira tarbiyyar da na baki kenan? Humaira duk tsawon shekaru goma sha taran da na d'auka ina baki kyakkyawar tarbiya amma rana d'aya kiyi watsi dashi, ki watsa min k'asa ido? Humaira? Ciki kina budurwa?"
"Mama na tuba kar ki kore ni! Mama ki sassauta min don girman Allah Mama."
Maman tace
"Yau don kinga mahaifinki baya raye shine kike son nuna min gazawata wurin baki tarbiyya ko?"
Ta fad'a tana k'ok'arin yin kuka.
"Mama kar kiyi min kuka! hawayenki wani bala'i ne a tattare dani, na tuba Mama ki yafe min!"
"Wai da kike cewa in yafe miki ni kika yi wa laifi ne? Allah (S.W.A) kikayi wa laifi don haka shi zaki nemi gafarsa bani ba."
Humaira ta rasa yadda zatayi sai kuka takeyi, Maman tana kuka sosai ta yi d'akinta da sauri tana salati, rufe k'ofar da key tayi, a yayinda Humaira tabi ta da gudu tana zuwa ta shiga buga k'ofar hankali tashi.
"Mama! Ko magana kiyi min ko zanji sanyi a raina. Kinji Mama!"
"Ibrahim?." Cewar Mama tana kuka.
Hankali tashe Ibrahim yace
"Mama lafiya kike kuka?."
Mama tace
"Ibrahim kazo gida ina buk'atarka kusa dani."
Ibrahim yace
"Mama menene?."
"Kai dai kawai kazo maganar bata waya bace."
"To." Kawai ya iya cewa, aikuwa next available flight ya hau ya dawo gida.
Yana shigowa yaci karo da Humaira kwance shame shame k'asa tana gunjin kuka, da sauri yace
"Ke what's happening here wai?."
Tana ganinshi ta tashi da gudu ta rungumo shi tana kuka.
"Meya faru wai?." Cewar Ibrahim hankali tashe
"Ciki ne da ita Ibrahim."
Da sauri ya saketa yana kallon Maman cike da tashin hankali yace
"Ciki kuma? Wai Humaira keda ciki Mama?."
Maman tace
"Ita fa, Humaira dai ciki tayo."
Shima salati yasa sosai yana kallon Humaira bak'in ciki kwance a ransa yace
"Humaira! Wayayi miki ciki?."
Tasa kuka, yace
"Au bazakiyi magana ba?."
Ta tsaya kallonsa amma ta kasa magana, yace
"Ok taurin kai zakiyi? Shikenan."
Belt d'insa ya shiga zarewa da sauri da niyyar tsula mata tasa ihu, Mama ta rik'e masa hannu tana kuka tace
"Kar ka dake ta, dolenta ma zatayi magana ay bata isa ba, idan ka k'ara tambayarta batayi magana ba ka tsule ta."
Ya aje hannunsa a hankali yana kallon Humaira rai a 6ace yace
"Ina jinki."
Cikin inda inda tace
"Wani Malami ne dama....dama..."
Ibrahim yace
"Dama mey?."
Da k'yar suka sata ta fad'a abinda ya faru bata 6oye komai ba, inda ko wanensu ya cika da 6acin rai marar misaltuwa. Mama tace
"Au daman laifin naki da yawa kenan? Yanzu har akwai me biya miki buk'atarki bayan Allah har sai kin rok'i wani malamin? Ashe dama kin 6ata Humaira?."
Salati suka sa itada Ibrahim inda Humaira ke cigaba da basu hak'uri.
"Mama tace
"To yayi miki kyau, ay gashi nan kinga irinta, shashashar banza shashashar wofi wadda bazata san ciwon kanta ba, ina ma amfanin irin haka Humaira?."
Ibrahim yace
"Amma fa ba wanda zai zubar da cikinnan sai kin haife shi wallahi, kinga alhakin wata ya kama ki ko? Ta d'auke ki da zuciya d'aya ke ashe muguwa ce? Hmm to daga yau sai ki d'auki darasi."
Mama tace
"Dama ya za'ayi a zubar dashi? Ay dole ma ta haife shi, kuma sai mun nemo malamin nan dole a mik'a shi ga hukuma wallahi."
Ibrahim yace
"Dole Mama Allah ya kyauta ya tsarkake mana zuciyarmu da imani."
Mama tace
"Amin Ibrahim, ke kuma wuce muje kuma wallahi ki dage da neman yafiyar ubangiji kinji na gaya miki."
A sanyaye tace
"To nifa Mama kun yafe min?."
Mama tace
"Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu? Nidai fatana Allah ya shiryar dake Humaira amma kisani ba ruwana dake, har sai kin haihu, sannan da kin sauka aure zan miki, Allah ya kyauta."
Haka ta tasa k'eyar ta har d'aki sannan ta kalleta tace
"Daga yau idan naga kina yawo cikin gidannan sai kin sani, ki dage da istigifari har ki samu Allah ya yafe miki."
Tun daga wannan rana Humaira ta dage da addu'a da kuma neman gafarar ubangiji, hartta wayayonta ta kashe su gaba d'aya, kullum zaka ganta da qur'ani tana karatu ko cazbaha tana ja, sai dai itada Mama ba kamar dah ba, iyakancinsu gaisawa da safe daga nan kuma shikenan. Gaba d'aya gidan baya mata dad'i gatan da ake bata dah yanzu babu, tuno yadda suke mata idan ta dawo ko wane hutu kamar su cinye ta, sannan gaba d'aya suke cin abinci kan table ana fira, amma yanzu sai dai taci abinci a d'aki kamar munafuka. Tayi nadama ba kad'an ba,  sannan taga illar son zuciya abinda ya janyo mata.



*****


Cikin Hanifah ya tsufa sosai, tashi da k'yar zama da k'yar, gashi exams suke tana ta addu'a sai ta gama exams zata haihu, aiko lafiya lau ta gama har Khaleel ya shirya ya maida ita gida haihuwa inda aka cigaba da bata kyakkyawar kulawa.
Duk da haka kullum tana tare da Khaleel ko wane motsinta sai yace mata sannu. Kayan babies kuwa sai da Ammi ta taka masa burki don tarkace ya dinga kwasowa.


Yau da rana suna zaune a palo suna fira sama sama inda dama tun safe Hanifah ke jin ciwon mara da baya tana dai daurewa bataso ta nuna.
Aikuwa har dai Khaleel ya gano ta don ba shiri taji wani irin ciwo ya kama ta marar misaltuwa!
"Washh!" Tace had'e da cije le6e cike da azaba, sai gumi take had'awa.
Khaleel yayi kanta a rud'e ganin har tana neman duk'ewa k'asa.
"Hanifah! Nak'udar ce?."
Tasa ihu.
"Wayyo Allah ya Khaleel zan mutu ciwo."
Kamo ta yayi kamar zaiyi kuka yana shafa bayanta
"Sannu bari na kira Ammi."
"Ashhh! Zan mutu ya Khaleel."
"Hold on baby bazaki mutu ba insha Allah, just wait ok?"
Ta girgiza kanta da k'yar, ya tashi da gudu yayi ciki, can sai gashi sun dawo shida Ammi a rud'e, ita ta taimaka masa suka sata a mota sannan Ammi ta d'auko maternity bag nata.

 Cikin k'ank'anin lokaci suka isa asibiti, inda suna zuwa akace nak'uda takeyi.
Ba yadda ba'ayi da Khaleel ba yace sai ya shiga ciki, dole aka k'yale sa ya shigan, don yace yana so yaga matarsa yadda zata haihu. Yana shiga Ammi ta d'auko wayarta don kiran su Saif.
Ya tsorata yadda yaga Hanifah gaba d'aya ta chanza kamar ba ita ba gumi sai sauko mata yakeyi. Khaleel yaje gefenta jikinsa yayi sanyi ya kamo hannunta yana shafa kanta, kuka ta fashe dashi tace.
"Zan mutu Ya Khaleel."
Yace
"Shhh kiyi addu'a insha Allah komai zaizo mana da sauk'i kinji i love you."
Wani nishi yazo mata da k'arfi nurse d'in tace
"You are doing good, i can see the head, just 2 good pushes babynki zai fito."
Kuka take sosai cike da azaba ta k'ara wani irin nishi mai zafi inda cikin ikon Allah aka zaro mata babynta!
Nurse d'in ta d'aga babyn yana ta kuka tace
"Congrats baby boy ne!"
Khaleel ya ware idanu cike da tsantsan farin ciki yace
"Masha Allah! Allah ya raya mana."
Ya kamo Hanifah ya rungume ta sosai. Nurse d'in na murmushi tace
"Bari na gyara muku shi yanzu."
Khaleel harda hawayen farin ciki ya kalli Hanifah ya kashe mata ido yace.
"Ya alk'awari na? I'm waiting."
Ta turo baki
"Wane alk'awari bangane ba."
Yace
"Kin manta? To na kiss ni nayi winning don haka a bani kiss d'ina ina jira."
Ta ware idanu waje tace
"Ya Khaleel!"




MSB✍🏼

No comments: