Wednesday 15 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 49 and 50

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 49&50}



To read all my books click the link belowπŸ‘‡πŸ»

Maryamsbello.blogspot.com




Yau ta kama asabar suna zaune da yamma tana kwance kan cinyarshi in banda shagwaba babu abinda Zarah ke zubawa wai ita a dole sai ya samo mata awara da wainar flour kuma ita bata son home made sai dai na saidawa, irin na bakin hanya. Da yaga abin nayi ne don dole ya tashi ya fita yaje ya samo mata don yaga alama weekend dinsa bazaiyi shi in peace ba don yanzu haka kuka take masa bil hakki sheyasa ma ya tafi jiki na rawa ya bata hakuri akan xaije ya siyo mata. Saida ya fita abin ya soma bata dariya wai dama dai yadda ake fadan cikinnan ashe dai haka yake da sai ta ringa ganin kamar abin bai kai haka ba, sai yanzu ta tabbatar ma kanta da abinda ake ji. Kallon da takeyi taji gaba daya ya gundure ta a hankali ta mike taje zata kashe tv taji an kwankwasa kofa, takawa tayi har bakin kofar tace, "Wanene?" Jin anyi shiru yasa ta bude a hankali wara idanu tayi ganin Hafsat da yayanta Yasir ay batasan lokacin datayi hugging dinsu ba tana ta ihun murna gaba daya bata iya misalta farin cikin da take ciki a yanzu, hannun Hafsat ta jawo har cikin parlor tana jan traveling bags dinsu da sukazo da ita, Yasir yana binsu a baya, zazzaunawa sukayi ita kuwa tana zaune kusa da Yasir ta kasa boye farin cikinta, "Ya Yasir shine baka kirani ba kace zaka zo ba?" Yayi dariya, "Bake kin iya bawa mutane surprise ba? Tou ya kikaji dana rama?" Tayi dariya, "Afuwan angon Hassatu, bari na kawo maku abinci ko?" Yasir yace, "Sallah zanyi amma ina mutumin?" Tace, "Ya fita amma bazai jima ba zai dawo!" Yace, "Ok naga masallaci a nan layin ku bari in tafi in dawo..." a haka ya fita ita kuma taja Hafsat guest room dinsu wanda yake a gyare tas tace ta shiga tayi alwalla tayi sallah, sai bayan tayi sallah ne tayi wanka suka ci abinci lokacin har Yasir ya dawo daga mosque. Tunda suka gano dukkansu suna dauke da jariran ciki ba karamin murna sukayi ba especially Zarah ta taya dan uwan nata murna ba kadan ba. Suna kitchen da daddare suna dafa dinner don kuwa Ashraf da Yasir sun fita zaga gari. Zarah ta kalli Hafsat cikin sigar zolaya tace, "Yanzu Inlaw wai ciki gareki ko? Na kasa yarda wai ya Yasir zai haifa mana da ko diya is so hard to believe he's going to be a father soon!" Dariya Zarah ta bata yadda take maganar kamar itama ba cikin ne gareta ba. "Kajiki yadda kike magana sai kace ke ba cikin ne dake ba? Kawai Ashraf yayi mana ajiya a cikin wannan shafaffen cikin naki." Dariya tayi daga haka ta samu ta kashe ma Zarah baki kuma bata sake tankawa ba har suka gama dafa macaroni da sauce din kaza suka jera kan dining, ta kai komai harda coconut drink dinta da basu sha da rana ba ta fiddo yayi sanyi sosai bayan sun gama suka gyara kitchen din sai suka hau kallo sunayi suna yar fira cike da nishadi. Jim kadan suka shigo hannuwansu niki niki da leda, kan dining suka aje sannan suka dawo parlor suka zazzauna suna cigaba da fira cike da nishadi. Hafsat ta kalli Zarah tace, "Ohni ko kunya mijinki na dawowa zaki fara murmushi?" Dariya tayi sosai parlon aka kwashe da dariya, Ashraf yace, "Hafsat ina ganin mutuncinki fa ki kyale man mata." Aka sake sa dariya, suna kallon Ashraf sai wani ririta Zarah yakeyi ko wurin cin abincin ma kamar ya tauna mata ita kuwa gaba daya kunya ta rufe ta, hararar wasa kawai take galla mashi akan ya daina akwai baki. Ta kasan table Yasir ya kamo hannun Hafsat, "Uhm anya Hafsat zamanmu gidannan zai yuwu? Ni gaba daya sunsa ni jin kunya!" Wani murmushin mugunta Hafsat ta sakar masa "A'a muyi zamanmu ay jibi ne fa zamu koma barsu suci karansu ba babbaka." Hararar wasa Zarah ta maka ma Hafsat, "Wallahi ki kiyayeni wannan Inlaw din tam!" Dariya akasa gaba daya, mikewa Ashraf yayi ya jawo hannun Hafsat, "Tou bari mu barku haka nan dare yayi ku cigaba da soyewa lafiya." Itadai Hafsat banda dariyar mugunta babu Abinda takeyi, dafata tayi, "Inlaw afuwan bari mu wuce mu kwanta sai da safe." Mikewa tayi zata cafko ta Hafsat ta saki yar kara ta boye bayan Yasir, "Fito nan mana kigani inba ga tsoro ba." Yasir ya saki dariya, "A'a malama ki bimin mata a hankali." Dariya suka fashe da ita sannan suka masu saida safe suka tafi daki don su kwanta. Suna tafiya ya jawota ta fado masa a hankali ya rungume ta, "Ya dai yan mata? Ba mun shirya ba ko har yanzu fadan mukeyi?" Dariya ma abin ya bata wato ma har ya saba da fadansu yanxu, dukan wasa ta kai masa tana dariya, "A'a fada man tun yanzu in bada hakuri ba sai anjima ba..." dariya tayi tana kokarin zillewa, "Don Allah ka daina." Ta fada tana binshi da hararar wasa, janta yayi cikin daki rungume da ita kamar za'a kwace masa ita. Ranar dasu Yasir zasu tafi har kuka Zarah tayi dan uwa mai dadi, da xasu tafi ta dauki atamfa guda biyu da turare ta ba Hafsat, har airport suka kaisu ko wane cike da kewarsu, a hanyarsu ta dawowa ne taga kiran Hoodah ya shigo video call da sauri ta dauka cike da farin ciki, ganin fuskar Hoodah yasa ta turbune fuska, "Ya zaki nuna man wannan fuskar taki bani babies dina ni in gansu." Hararar wasa Hoodah ta watsa mata, "Aikuwa ni zaki gani basu ba..." Zarah tace, "Don Allah kiyi hakuri in gansu." Hoodah tayi dariya sannan ta seta camera din inda suke kwance suna ta bacci peaceful, Zarah ta dafe kirji, "Awwwn so adorable MashaAllah," sun kara kyau sunyi bulbul MashaAllah kamar ta sace su, Hoodah ce ta bayyana a screen din, "Happy now? Sai ki shafa man lafiya, yanzu dai ina yayan nawa yake?" Zarah tayi dariya ta saita masa wayar ya karba, kalla yayi yana murmushi, "Lil sis how far?" Itama tana murmushi tace, "Fine fine ya kuke?" Yace "Alhamdulillah ina babies dina?" Ta nuna mashi shima cike da sha'awa yace, "Blessed them." Tace "Thank you," yace "Ina sarki?" Tace "Yanzu ya fita fada." Yace "Ki gaishe min dashi," tace "InshaAllah." Ya mika ma Zarah wayar, "Tou mai ciki naga ma kamar baku gida bari na barki." Zarah tace, "Eh wallahi su ya Yasir muka kai airport." Hoodah tace, "Haba sunzo ne?" Ta gyada kai tana murmushi, Hoodah tace "Ayyah Allah ya kaisu gida lafiya." Tace "Ameen ya Rabbi, take care." Daga haka sukayi bankwana. Wani shopping mall suka tsaya suka siya groceries da abinda take bukata harda kayan lashe lashe. Wurin snacks sukaje ta kwashi frozen ones da su frozen yogurt da ice cream. Suna isa gida ta dinga taya shi kwasar kayan saida ya nuna mata da gaske fushi zaiyi sannan ta daina saida ya gama kai kayan tas sannan ita dauko robar ice cream ta bishi cikin gida. Katuwar robar a ciki ta dauka ta rufe fridge din ta juyo tana kallonshi kanta ko dankwali babu, "Wallahi kwadayi nakeji muje muna kallo zakaga mun shanye shi." Dariya yayi yana shafa cikinta, "Kai kuwa bawan Allah ka cika kwadayi ka barmu mu dan sarara haka nan mana!" Dariya tayi tana kai mashi dukan wasa gaba tayi da robar ya bita parlon yana dariya, "Tou daga fadan gaskiya sai kiyi gaba ki barni tsaye ni kadai?" Cokalin hannunta ta dauka ta jefa mashi ya kauce yana dariya.

FEW MONTHS LATER...

Zarah na zaune kan 3 sitter tana sanye da kayan bacci tana cin goruba, cikinta ya fito yayi tulele ya rinjayeta, tana gidansu inda ta tafi can haihuwa, Khadija tana bata kulawa sosai tana kula da ita ta gyara mata dakin kasa a nan zata zauna idan ta haihu. Mummy ce ta sauko daga sama ta xauna gefenta, take Zarah aka wani shige cikin jikin Mummy, "Zarah kinaso ranki ya baci ko?" Zarah ta dago tana kallon Mummy, "Mummy menayi?" Mummy tace "Kinyi wanka yau?” Zarah tace "Meye amfanin wankan Mummy? Na zama katuwa nayi muni nayi nauyi!" Mummy mikewa tayi ta jawo hannunta da kyar take jan kafarta saboda tsananin nauyi, har dakinta ta kaita ta hada mata ruwan wanka, nan ta shiga cikin kwamin da aka cika da ruwa tayi zamanta a ciki tana wasa da bubbles, Bayan ta gama wankan ta fito daure da towel. Shiryawa tayi cikin loose cotton pink gown, turare masu dadi ta shefe jikinta dasu, gashinta ya kara tsawo ya kara zama baki wulik maybe saboda cikin ne. Wayarta ta dauka ta duba time karfe 2:10pm. Sallaya ta shiimfida ta fara sallah, tayi raka’a biyu tana na ukun ne ta ji muryar Ashraf. Dama tun tana sallar takejin bayanta na ciwo da mararta haka nan dai ta daure ta karasa sallar a haka, shiru tayi a tunaninta kawai normal pains ne saboda daman tana dan jin haka kwanan nan, sai kawai ta fita batun. Duk suna parlor suna kallo Yasir ne kawai babu don shima shekaranjiya Hafsat ta haihu baby boy ansa masa Khaleel. A hankali ta tashi ta shiga daki daidai bakin kofa kawai ta fasa wata irin kara ta zube nan dafe da cikin, a rude kowa yayi kanta, Mummy ce ta kamo ta Ashraf ya taimaka mata suka sata mota, Khadija ta dauko box din haihuwanta da sauri tayi mota. A haka suka isa aka karbesu da gaggawa. Ba Zarah ba hartta Ashraf zufa yakeyi yana kallon yadda take kokarin kawo babynsu duniya. Cikuikuye Ashraf tayi cikin kuka tace, "Bazan iya ba Allah mutuwa zanyi." Kara rungume ta yayi yace "Zaki iya princess just try!" Nurse din tace, "Naga head din just push one more time okay?" Nan suka dinga bata kalaman karfafa guwiwa ay batasan lokacin data fasa ihu ba sai jin kukan jarirai sukayi har biyu. "My princess did it! Weldon! Now look we have two babies!" Zarah ta fashe da kuka, nurse din tace "Congratulations it's girls!" Bisa kafadunta aka dora mata ko wane side take ta kara fashewa da wani kukan tana shafa kansu tana kissing dinsu Ashraf yana tayata.

Congratulations princess, we did it...!” Tayi murmushi cikin kuka.

Tace "We did it!" Yace "Thank you." yace yana hugging kanta yana mata kiss a goshi.

“Thank you..." ya sake cewa yana kokarin maida hawayen da suke shirin zubowa. Bayan an kimtsa babies din aka gyare su tas itama akayi stitching dinta aka kimtsa ta. "Ya sunansu?" Ya shafa gashinta, "You can decide princess." Tace "Your mother's name and my mother's name, sai mu dinga kirnasu Alinah da Alishah." Yayi murmushi yana kara hugging dinta, "Thank you." Zuma aka lasa masu sannan ta dora kanta bisa kafadar Ashraf tana lumshe ido kamar mai bacci, tana dauke da Alishah a cinyarta, bude ido tayi ta kalleshi, "They're so cute.." tace tana kissing kanta, dan turo baki Ashraf yayi, "Am jealous the babies have been receiving kisses but none from me." Zarah tayi dariya, "You’ll get yours idan na tashi daga bacci..." tayi hamma, don ta gaji ba kadan ba, Ashraf ya gyada kai yana tashi tsaye, "Bari naje nayi wanka, kema ki kwanta ki huta yanzu su Mummy zasu shigo wurinki..." yayi kissing dinta tare da twins din sannan ya juya yayi hanyar kofa. Har ya kai kofa ya juya yana murmushi, "I like the names you choose for them." Tayi murmushi "I like it too..."

Alishah and Alinah.

Washe gari su Hoodah suka iso nan da nan murna ta barke tsakaninsu, Su Aman sun girma sun kara kyau kai kace wasu black indians. Kowa ya gansu sai yaji sha'awar daukarsu ga su da shegiyar kyuya in ba Hoodah ba basu yarda da kowa sai Zarah shima ba ko yaushe ba. Da kyar suka saba da kawun nasu wato uncle Ashraf take ya shaku da yaran suka cigaba da makale masa. Haka aka cigaba da zaman barka mai jego da babies na samun kulawa wurin Mummy. Ranar suna anyi taron suna lafiya kuma ya kayatar mai jego tayi fes da ita tana sanye cikin wani golden lace sai kyalli takeyi kamar wata amarya. A haka aka sha pictures anci ansha an watse sai fatan Rabbi ya raya su cikin aminci.

-----

Bayan Zarah ta haihu da wata daya akayi bikin Khadija da angonta Dr Hafiz duk da mahaifiyar tashi batayi na'am da ita ba amma hakan bai hanata tayi hidimar bikin dan nata ba. Bayan an gama taron biki lafiya amarya tana dakinta suna zaman amarci lafiya, ba karamin gwargwamaya aka sha ba kafin mother Inlaw din tata tayi accepting dinta amma yanzu Alhamdulillah komai yana tafiya yadda ya kamata suna zamansu lafiya itada mijinta. Kawai matsalar ta daya rashin haihuwa duk yadda zataso walwala in ta tuna sai taji komai ya fice mata kai, Dr Hafiz ma ke bata kwarin gwiwa akan ay wannan ba abin tada hankali bane ba.

-----

Haka rayuwar ta cigaba da gudana inda Khairy yanzu haka danta ya warke har ma ta samu mijin aure wani carpenter wanda ya amince ya aure ta haka aka tattara aka aurar da ita dayake shima yana dauke da irin cutarta a haka suka cigaba da xamansu tare suke zuwa karbar magani, yanxu haka Hoodah ta bata kudi taja jari ba karamin godiya tayi ba. A bangaren Karimah kuwa abin sai wanda ya gani bayan doguwar jinyar da tasha Allah yayi mata cikawa ta rasu ranar wata alhamis da tsakar dare inda a ranar ta dinga kururuwar fitar rai take ta rasu inda aka rufe ta washe gari bayan an sanar da Abba har inda take yazo ba karamin girgiza yayi ganinta ba, nan yayi mata addu'ar rahamar Allah tare da fatan Allah yasa iyakar wahalar kenan. 

-----

Haka rayuwar ta cigaba da gudana a kowane bangare ko wace sai sam barka yanzu haka twins din Hoodah shekararsu daya harda yan watanni inda ta kara samun wani cikin, suna nan twins sai dada kyau suke suna samun kulawa don a yanzu haka ana kiransu prince and princess, duk inda kaga daya zakaga dayan, Hoodah kuwa bata fasa aikata aikin alkhairi ba sai bunkasa garin suke yanzu haka da wuya kaje kaga almajiri na bara ko daya baka gani duk a sanadiyar Hoodah, kullum soyayyarsu dada bunkasa takeyi suna kara samun cigaba a rayuwarsu..... 






             ALHAMDULLAH!


MashaAllah Alhamdulillah a nan na kawo karshen novel dina mai taken YAR AGADEZ, darasin dake ciki Allah ya bamu ikon dauka, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana πŸ™πŸ»πŸ™πŸ», A Gaskiya naji dadin yadda kuke bani kwarin gwiwa da comments naku nagode sosai Allah ya bar zumunci love you all.πŸ”₯πŸ”₯πŸ’•❣️🧑❤️

Friday 10 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 48

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 48)



To read all my books click the link belowπŸ‘‡πŸ»

Maryamsbello.blogspot.com



Har ta iso dab dashi ganin yadda ya tsareta da idanu sai kawai ta sunkuyar da kanta ta juya kekenta tayi cikin gida saboda bataso ya gano yanayin da take ciki don ita gaba daya abinda takeji yafi karfinta, Dr Hafiz yabita da ido har saida ta shige, murmushi kawai yayi sannan ya cigaba da shan juice dinshi, tunani kawai yake shin wannan wace irin mutum ce? Yau zai ganta gata nan all moody wani time din kuma lafiya lau cike da nishadi. Da yamma tana fitowa daga dakinta da yake yanzu dakin kasa aka gyara mata nan ne dakinta, tana fitowa taci karo da Mummy tana waya da alama Zarah ce ke kan layi, da murmushi ta karaso kusa da Mummyn tana binta da ido har saida ta kammala wayar, Mummy ta kamo hannunta tace, "Har kin tashi? Ay tun dazu na dawo na leka dakinki naga kinata bacci abinki kina hutawa." Tayi murmushi "Mummy ina yini? Ya aiki?" Mummy tace "Alhamdulillah ya therapy din?"  Tace "Lafiya lau." Mummy tace "Tou kinyi sallah?" Ta girgiza mata kai, "Ina hutu." Mummy tace, "Ok Mama Hauwa ta kwantar dake kan gado?" Ta gyada mata kai, "Eh ay ita ke kula dani indai baki nan." Mummy tace, "MashaAllah, tou abinci fa?" Tace "Zanci anjima." Mummy tace, "Haba Khadija, kinsan akwai maganin karfe biyar kuma ana so a bada gap da abinci kafin a sha." Mummy ta mike ta nufi dining don zubo mata abinci, saida ta xubo ta dawo sannan ta fara bata abincin, sai da tayi nisa a bata sannan ta dakata tana kallon Khadija kafin tace, "Yauwa Khadija dama kuwa ina son magana dake?" Khadija tace "Ok gani Mummy." Mummy ta danyi shiru kafin tace, "Khadija ni sai inga kamar Dr Hafiz sonki yake..." da sauri ta dago tana kallon Mummy lokaci daya kuma gabanta ya fadi, da sauri ta girgiza mata kai, Mummy tayi murmushi, "Ba lallai bane ki sani duk da nasan ya kamata ki fahimta, duba da yadda yake dawainiya dake yake baki kulawa na tabbatar ba banza ba Khadija, don haka ki nutsu nidai har ga Allah Dr Hafiz ya kwanta min a rai kuma na yaba da halinsa, ki nutsu Khadija and also listen to your heart..." Khadija ta sunkuyar da kai take taji ta koshi da abincin kuma.

---

Ranar wata juma'a tana zaune parlor da safe Mama Hauwa tana tsefe mata kai Mummy ta fito da shirin fita office tana murmushi tace, "Yauwa ko kefe? Da kin zauna da kai sai kace ciyawa, anjima ki daure kije salon a wanke maki kan Khadija in kuma a gida kikeso zan dawo in wanke maki anjima." Khadija tace, "Inason inje salon din Mummy." Mummy ta ciro kudi dubu biyar ta bata, "Gashi Mama Hauwa sai ta rakaki salon din," murmushi tayi sannan ta karbi kudin, "Thank you." Mummy ta maida murmushi, "Take care." Tana fadan haka ta fita bayan ta masu bankwana. Da yamma bayan ta dawo daga salon din tana zaune garden ita kadai tana practicing zana wata gown da aka basu as assignment kamar daga sama ta hango shi yana shigowa, dagowa tayi tana kallonsa ganin irin shigar da bata taba ganinsa da ita ba wato kayan hausa kullum ciki jeans yake da riga amma yau yana sanye da dark blue shadda harta hular kansa kalar kayan jikinsa ce, a hankali ya karaso tare da turarensa wanda ya cika wurin, "Salam yan mata, zane akeyi ne?" Dan gyada mashi kai tayi a hankali tana jin kamar ta bar wurin, "Ya naganki haka kuma? Ko don nace Doctor dinki ya saki kuka rannan Khadija, fushi ake dani?" Bata san lokacin data zabga mashi harara ba, "Ohni Hafizu da harara na kisa dana dade da mutuwa, yanzu dai kiyi hakuri am sorry you hear?" Turbune fuska tayi ita sai yanzu ma ta lura bata san meya bata haushi ba, "Wai bana bada hakuri ba, yanzu dai me zanyi ki daina hararata don Allah?" Girgiza kai tayi, "Babu, ni zan tafi cikin gida."

Girgiza kai kawai yayi yace, "Nasan wani wuri a nan inda suke yin arts na fashion..." da sauri ta juyo tana kallonsa, "Really? Please mu tafi wurin mana." Yasan hakan kadai ne zaisa ta dawo daidai, da sauri ta gyara gyalenta wanda yake daure bisa kanta sannan ta turo kekenta har gaban motarsa, saida tazo shiga kuma sai ta tuna bata fada ma Mummy ba da sauri ta bude wayarta ta kirata nan ta bata izinin tafiya da kyar. Har suka isa wurin tsit kakeji a cikin motar, suna isa ta gwale idanu waje, "Wow Doctor Hafiz wurin nan ya hadu." Yayi dariya "Ashe dai ansan sunana?" Har ya karaso inda take tare da fiddo kekenta yana dariya tace, "Zaka fara ko?" Dariya yayi yana daga hannu alamun hakuri kafin ya fara janta har suka karasa ciki, baki bude take kallon wurin tun da take bata taba ganin inda ya birgeta ba irin wurin nan ba, babu abinda take sai murmushi zuciyarta fes, "Ban taba ganin murmushinki haka ba Khadija..." ya fada yana kallon yadda take snapping arts din da camerar wayarta, "Tou kawo wayar kema in maki hoton, I just love your smile today." Bata masa gardama ma ta mika masa wayar, har sai da ya dauketa kala kala kai harda ma wayarsa ya hada yana daukarta. Yana cikin daukar hoton ne wayarsa ta fara kara ganin Dr Haiydar yasa ya dauka yana fadin "Doctor yaya?" Dr Aliyu yace, "Please kuna tare da Khadija?" Yace "Eh muna tare lafiya dai?" Yace "Ah lafiya lau dan bata please minti daya." Mika mata wayar yayi yana murmushi, ta kara a kunne, "Hello ina yini Doctor?" Yace "Alhamdulillah, abinda yasa na kiraki karki zo appointment gobe sai jibi InshaAllah, abinda yasa banida number ki sheyasa na kira da wayar Dr Hafiz..." tayi murmushi "Laa bakomai Doctor Allah ya kaimu ba damuwa." Taji sautin murmushinsa "Tou godiya nake sarautar mata." Tayi dariya sannan ta mika masa wayar saida sukayi bankwana sannan ya katse kiran yace, "Yanzu Khadija sarauyinki wayata ma xai kira tsabar bai iya nemo taki number din?" Ta tintsire da dariya, "Wai saurayi! Dr Aliyu ne fa." Murmushi kawai yayi ya kyaleta daga nan wani shop taga sun nufa, tana dubawa taga shagon saida electronics ne, tsayawa tayi tana kallonsa fuskarta da alama tambaya yayi murmushi, "To make life easier for you am gonna buy you a laptop..." Girgiza kai tayi da sauri, "A'a don Allah basai ka siya ba zan cigaba da zane na a paper." Ko saurarenta baiyi ba kawai taga ya shiga shop din ya jima kadan can ya fito hannunsa dauke da tsadaddar laptop kirar apple, yana shigowa motar ya mika mata take sai yaga tana hawaye, a dan rude yake kallonta, "Khadija kuka kuma? Why are you crying please?" Share hawayenta tayi tace, "Doctor why are you doing this?" Shiru yayi ya murza key ya tada motar ya cigaba da tafiya abinsa, ta sake tambayarsa, "Please don Allah doctor ka fada man meyasa kake dawainiya dani?" Ta fada tana tsareshi da idanu, can ya numfasa, "Karki damu zan fada maki very soon Khadija..." daga haka tayi shiru har suka isa gida. ---

A hankali soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Dr Hafiz da Khadija duk da da farko tayi tunanin Dr Haiydar takeso sai daga baya ta fahimci zuciyarta tafi karkata da Dr Hafiz, duk wata kulawa daya kamata ya bata yana bata, kuma yanzu alhamdulillah ta warke tangaram ta mike kafafunta suna takawa don dai kawai dan limping din da takeyi kadan kadan amma dai ta samu lafiya. Bayan yan lokuta da basu wuce wata biyu ba aka sanya bikin Dr Hafiz da Khadija za'ayi bikin nan da wata biyar bayan Zarah ta haihu. Ranar da aka shirya akayi zataje gaida mahaifiyar Dr Hafiz Mummy ta shiryata tsaf ta taimaka ta shirya. Khadija tafi minti goma zaune a daki aka kwankwasa kofar aka shigo Mummy ce ta shigo tana murmushi Khadija ta mayar mata, "Amarya ango fa yana waje ke yace jira, ya kamata ki fito ku tafi kuje ku dawo..." gyada kai tayi tana faman sunna kai, Mummy ta mike ta jawo hannunta suka fito, tunda suka fara saukowa daga bene take murmushi, bankwana tayi wa su Mummy, Mummy ta mata sharadin kar dai suje su dade a can sannan ta kula da kanta. Tunda suka fara tafiya take jin faduwar gaba gaba daya a dare take, shima kansa baisan wace irin tarba mahaifiyar tashi zatayi mata, duba da yadda ya shawo kanta da kyar akan ta amince bayan dogon bincike da kuma ganowar ainahin wacece dan nata zai auro ba karamin gwargwarmaya akasha ba don har cewa take saidai ya zaba ko ita ko Khadija da kyar da jibin goshi ya shawo kanta ta hakura, amma koda wasa bai taba yarda ya fada ma Khadija reaction din Mamin tashi ba. Saida sisters dinshi wadanda ke aure sukayi takakkiya suka zo suka sa baki tace ba damuwa. Bayan sun isa ya sakar mata murmushi, "We are here amarya." Ta sunkuyar da kanta batace komai ba ta bude motar ta fito a tare suka jera har cikin parlon, parlon ba kowa sai karar tv sukayi sallama yace ta zauna bari yayi mata magana, a hankali ta zauna tana dan kalle kalle. Mami na zaune cikin daki tana shan fruit salad ya shiga da sallama, zama yayi kasa ya gaishe ta cike da ladabi ta amsa normal, yace, "Mami tana parlor tana jiranki." Da toh ta amsa, mikewa yayi ya fita ita kuma Mami ta sanya mayafi ta bi bayanshi. Khadija na ganinta ta fito tayi sauri ta zauna kasa Mami ta iso ta zauna kan kujera shi kuma Dr Hafiz yaje yayi ma masu aiki magana suyi arranging abinci kan dining. "Mami barka da wuni?" A wani yatsine take amsawa kamar tana tauna magani Khadija dai bata bari abin ya dameta ba ta saki murmushi, "Mun sameku lafiya?" Mami tace "Lafiya, ya mutanen gidan?" Tace "Duk suna lafiya." Tace "Tou madallah, feel at home bari na shiga ciki yanzu zan fito." Khadija ta gyada mata kai sannan Mummy ta mike ta shiga guest room ta fiddo mata hijab din sallah da carpet, sannan ta fito daga bakin kofar tace, "Zakiyi sallah?" Ta gyada mata kai Mami tace "Tou taso." A hankali ta mike sannan ta shiga ita kuma Mamin ta fito. A lokacin data gama sallar azahar ta fito babu kowa parlon amma da kamar tana dan jin maganganu na tashi sama sama daga kitchen, har tayi gaba sai kuma ta dawo fuskarta cike da shock tana sauraren maganganun da suke fadi, "Wai kana tunanin don kawai tazo na sakar mata fuska shine nayi accepting dinta as my daughter Inlaw? Tou ka bude kunnenka da kyau kajini, bazan taba accepting shegiya ba ban hanaka aurenta ba nidai babu hadina da ita, kaidai matarka ce amma ni ba surukata bace! Kawai sai kaje ka auro man saura a matsayin suruka ka kawo man ita cikin gida? Tou ban aminta ba kaidai da kaji zaka iya sai kaje kayi Allah ya taimaka..." idanunshi take suka kada sukayi ja yace, "Haba Mami da take Shegiya laifinta ne? Batada laifi ko kadan! Sannan da kike maganar saura shima ba laifinta bane, Mami idan yanzu akace yarki ce zakiso ayi mata haka?" Ta tsaida shi, "Tou nagode ma Allah ba yata bace! Don haka ka fita idona Hafizu!" Jikinta babu inda baya rawa har wani kyarmar sanyi takeyi, idanunta na neman kafewa dafa dining din tayi by mistake ta kado jug din dake kai ya fado kasa take Dr Hafiz ya zaro idanu waje yana rufe bakinsa da hannunsa, "Kinga abinda kikayi ko Mami? Nagode sosai...!" Da sauri ta juya ta fita daga parlon wanda yayi daidai da fitowar Dr Hafiz amma ina har ta fice da gudu, "Khadija please wait!" A haka yabi bayanta da sauri cike da tashin hankali! Khadija gudu kawai takeyi tana wani irin numfashi na wanda tashin hankali ya kai kololuwar tashi, "Innalillahi wa inna ilahir rajioon..." kawai take nanatawa a yayinda take kukan fitar rai, Dr Hafiz ganin bata cikin hankalinta kuma zata iya fada ma titi yasa yayi wani irin gudu yasha gabanta da gaggawa sai haki yakeyi, ita kuwa cikin kidima take wani irin kuka tana jin dama ta mutu don tasan wannan bakin cikin ta dinga haduwa dashi kenan da gori har karshen rayuwarta, karshen tashin hankali ta shiga wanda ko gabanta bata gani sai duhu take gani, "Khadija! Don Allah ki tsaya ki saurareni karki tada hankalinki a kan maganar da kika ji don't take it to heart wallahi she didn't mean it, Mami tana sonki Khadija...." ya fada yana kokarin rikota ganin nema take ta cigaba da gudun da takeyi, baisan lokacin daya fizgota ba ya rungume ta a jikinsa yana karanta "Innalillahi wa inna ilahir rajioon." A jikinshi ta saki wani irin kukan da bai taba ji ba a rayuwarshi har wanji jijjiga takeyi, ji take gaba daya komai na duniyar nan ya tsaya mata cak bata gane komai, "Don Allah ki daina kuka nan Khadija, kinsan ina sonki duk a yaya kike, I don't care what anyone else think, I love you just the way you are...." magana yake mata amma gaba daya ta rufe fuskarta da hannuwanta banda kuka babu abinda takeyi sai girgixa kanta takeyi, "Dama nasan irin ranar nan na zuwa Doctor! Wallahi dama mutuwa ce ta daukeni don nasan bakin ciki da kunci zan riska har karshen rayuwata! It will keep hunting me for the rest of my life!"  Tallabo fuskarta yayi yana share mata hawaye, "Kar ki sake wannan tunanin Khadija, am here for you no matter what, tsorona karki fasa aurena akan wannan Khadija I cannot leave without you Khadija please don't leave me..." dagowa tayi a hankali taga ya kureta da idanu yana kallonta, a hankali take share hawayenta idanun nan sun kada sunyi ja, "Tashi muje na maida ki gida." Mikewa yayi yaga sai kalle kalle takeyi shi tsoronshi daya kar ta kara ballewa sheyasa ma yaki sakin hannunta ya rike gam dan baisan ta inda zai fara tarota ba, jiki a sabule Khadija ta mike ta kalli yadda ya rike mata hannu gam, ya juyo yaga sai kallon hannun nashi daya rike takeyi sai kuma kalle kalle takeyi, "Doctor ka man alkawari bazaka taba kyamatata ba no matter what."  Kallonta yayi sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya dora dayan hannunshi saman hannunsu dake rike yana kallonta kallo na kurilla yace, "I promise you Khadija, no matter what I will never ever leave you." Sai a sannan ta dan sakar masa murmushi a haka ya cigaba da janta har mota sannan yace, "Ki tsaya a nan bari inje in dauko maki bag dinki cikin gida kinji?" Daga mashi kai kawai tayi ta bude motar ta shiga, a kan kujera ya samu Mami babu abinda takeyi sai girgiza kafa ko kallonshi batayi ba ya duka daidai kafarta ya dauki jikkar sannan ya dago yana kallonta a take ta juya fuska tana kallon wani side, jiki a sanyaye ya fito daga parlon....



Kuyi hakuri da jina shiru da kukayi kwana biyu munyi rashin wuta ne, and also kuyi hakuri da wannan ba yawa!πŸ˜‚also unedited

Friday 3 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 47

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 47}



To read all my books click the link belowπŸ‘‡πŸ»

Maryamsbello.blogspot.com





Washe gari wurin karfe goma da kusan rabi aka sallami Hoodah bayan an tabbatar da babu wani abinda yake damunta itada babies, Zarah tana nan makale da yan biyu, Abbi yayi arranging tarbar da za'ayi ma Sarauniya da ita da jariranta da irin kyauttukan da ya tanadar mata, a mota Ummi na rike da daya haka ma Zarah na rike da daya, haka suka iso gida tun kafin a bude masu gate makada suka fara buga algaita suna welcoming Hoodah da jariranta, Abbi na tsaye har suka fito daga motar inda aka karasa masa da jariransa yayi bismillah ya karbe su, wani irin farin ciki yaji ya lullube shi ya jima yana kallonsu kafin ya fara tofe su da addu'oi sannan yace, "Allah ya raya Safinah da Ahmad yayi maku albarka, Allah yasa su gaji mahaifinsu." Aka amsa da Ameen, (Ahmad sunan Abbi ne na asali) nan ya mika yaran ya kalli Hoodah yayi mata sannu ta amsa sannan Sultan ya kama ta yayi ciki da ita har dakin Ummi ya kaita, tana shiga tayi arba da Kaka xaune tsaye tayi cike da shock, batasan lokacin da fada ma kaka ba cike da murna, "Kaka yaushe kikazo?" Kaka ta kara rungume ta sosai cike da murna, "Jiya da daddare na iso, ay dama nace ni zan fara yi maki wanka bazan bari a rigani ba." Hoodah tayi dariya, nan aka miko ma Kaka yaran tace, "Kai tubarkallah ya akayi kika haife wadannan tula tulan yaya MashaAllah, lallai mamansu a koshe take." Aka sa dariya har kasa Sultan da Ashraf suka gaisheta ta amsa, sannan suka sa kai suka fita, nan Zarah ta tsugunna itama da gaida Kaka, Kaka tace "Zahara shine kika gudo kika barni ko? Ay da sai ki jirani mu taho tare ko." Zarah na murmushi tace, "Kiyi hakuri Kaka nida Ashraf muka taho, Abba ne yace mu bari zai taho dake." Tace "Nidai bawani, kawai a kawo min ruwa in gashe jikata da wadannan yan mitsa mitsan." Zarah ta mike kenan sai ga Ummi ta shigo da katuwar kula ta ruwan zafi ta dire bakin kofar bathroom tace, "Tou Kaka ga ruwan nan amma zaki iya yi mata ko inyi mata?" Kaka tace "Yi mata zanyi tas, ke sai kiyi wa jariran." Ummi ta amsa da toh sannan ta fita ba'a jima kwarai ba ta dawo da robar da za'ayi wa babies din wanka nan Zarah ta mike ta taimaka mata suka hada ruwan farko suka kai na Hoodah a guest room don sai yafi dadin wanka yafi space. Kaka ta mike taja hannun Hoodah suka fita, nan Ummi ta gyara zama Zarah ta cire ma Ahmad kaya ta mika shi nan Ummi ta sumbule shi tas Zarah ta hada masu kaya bayan ta gama aka mika Safina itama nan aka sumbule ta tas, Zarah ta shirya su sannan ta kwantar dasu, ana gamawa sai ga Sultan yasa an kawo sauran kayan babies da na Hoodah bayan an dire kayan tas sannan yace da Ummi, "Ina Hoodar?" Ummi tace "Wanka ake mata." Yace "Ok ga rago nan nasa a gasa mata sai taci sosai," Ummi tace, "Ok tou, nima gashi nan nasa ana dama mata kunu abinci ma data fito zata ci." Yace "Ok." Wurin babies din ya tafi inda Zarah ke basu kulawa ya sake dubasu sannan ya fita yana murmushi. Kafin kace me gidan ya dau harami shiga kawai ake ana fita duk da ma akwai security ba kasafai ake shiga din ba sai da umarnin sarki, yan uwa da abokan arziki ana ta zuwa ganin babies, kullum Kaka ke ma Hoodah wanka sau biyu a rana sai Ummi tayi wa babies din, ita kuwa Zarah gaba daya itace ke kula dasu ashe tanada son yara haka. Ba karamar kulawa suke samu ba daga mai jegon har jariran. Hoodah har ta fara dawowa Hoodan da muka sani yar budurwa tayi kyau ta gasu abinta, babies din kuwa tuni sun murje sun yi jajir sun fara kiba. Ana gobe suna su Yasir suka iso shida Hafsat, wani irin murna su Zarah sukayi suka basu kyakkyawa tarba nan da nan aka cika masu gabansu da kayan motsa baki da abinci da drinks. Ranar suna Abbi yayi organizing gagarumar walima, gaba daya ma harda invitation card aka buga da pass, nan masu taya murna suka fara hallara, mai jego da safe ta saka super mai kyau inda aka sha hotuna sai da yamma ta cire ta maida dankareren lace wanda yasha dinki tayi bala'in kyau tasha light makeup, gaba daya Zarah da Hafsat suna tare da mai jego suma sunsha kyau ba kadan ba. Can na hango su Hafsat da dukkan members na Yar agadez sai faman dibar abinci suke suna sawa a leda da sauri nace masu haba ku kuwa ku bari mana za'a sa maku har sai kun tureπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜πŸ˜œ. Su angon jego dasu Ashraf da Yasir suma suna tare a cikin fada tare da Abbi a can suka ci abinci kafin a fara daukar pictures, sai gab da magrib taro ya watse sai fatan Allah ya raya mana Ahmad da Safina inda Sultan ya bukaci a saya sunan saboda yace bazai iya ringa kiran sunan mahaifiyarta kai tsaye ba, shine aka sa mata Afreen inda Ahmad za'a dinga kiransa da Aman. Bayan sallar magrib su Hoodah da Zarah suna zaune palor suna cin snacks da peppered chicken inda su kaka suna dakin Ummi suna faman hutawa don ba karamin gajiya sukayi ba, su Sultan kuwa Ashraf ya hada masu wata yar get together ta maza kadai suna can sunayi, knocking kofa akayi jakadiya da wasu maids da ke ta faman gyara parlon inda ya baci ta fita wajen kofar ta bude, wani dogari ne a tsaye yace da ita, "Jakadiya, Sarauniya tayi bakuwa a waje, amma ban ce ta shigo ba tukunna sai naji idan tana da appointment?" Jakadiya tace "Tou bari a sanar mata dan jira a nan." Nan taje gefen Hoodah ta tsugunna har kasa tace, "Allah ya karawa Sarauniya lafiya kinada bakuwa a waje." Tace "Wacece?" Jakadiya tace "Nima bansani ba bari in tambaya." Tana fadan haka ta mike, nan Ummi ta bukaci Zarah ta kawo su Afreen ayi masu wanka, Zarah dama tana goye da Aman Hafsat kuma na goye da Afreen, nan Zarah ta fara mikewa ta shiga ciki. Jakadiya ce ta dawo ta tsugunna, "Allah ya kara maki lafiya wai maman Khairy ce." Nan gaban Hoodah ya dan fadi tadai dake tace, "Ba damuwa a shigo da ita, ta sameni gazebo." Daga haka ta mike ta yafa gyalenta tayi hanyar kofa, maids dinta guda biyu suka rufa mata baya. A cikin gazebo din ta zauna bisa kujerun wurin alamun na hutawa ne, tana zaman jiranta sai gata ta karaso dogari na gaba ita tana baya, saida yazo gaban Hoodah ya sunkuya, "Ranki shi dade gata nan." Godiya ta masa godiya inda ta sallame shi nan ta kalli maman Khairy tana murmushi tace, "Bismillah shigo Mama." Da sauri ta shigo zata bada gaisuwa Hoodah ta tsaida ta tace, "Don Allah karki gaishe ni Mama." Mama tayi murmushi ta zauna kujerar dake gefen ta Hoodah, Hoodah tace, "Ina yini Mama?" Tace "Lafiya lau Alhamdulillah, ashe an samu karuwa?" Hoodah tayi murmushi, Mama tace "Tou Allah ubangiji ya raya mana ya masu albarka." Hoodah tace "Ameen."

Mama ta numfasa sannan tace, "Kiyi hakuri da wannan zuwan ba zatan da nayi maki, da naso sai hidima ta lafa amma kuma sai naga ya cacanci inxo maki barka sheyasa nace bari inzo gaba daya, wata alfarma ke tafe dani idan bazaki damu ba?" Hoodah ta numfasa, "Allah sarki ay babu damuwa anytime kike son xuwa xaki iya zuwa Mama wannan ay ba wani abu bane, komai fa ya wuce tsakaninmu wallahi babu komai." Mama tace, "Hakane." Hoodah tace, "Wace alfarma ce wannan Mama?" Mama tace, Akan Khairy ne taimakonki muke nema..." Hoodah tace, "Ina jinki?" Mama tace, "A lokacin da Khairy zata haihu na farko bayan ta haihu ta kamu da matsalar yoyon fitsari wannan lalura munyi magani har mun gaji abu yaci tura, tana nan yanzu in ba mu da muka zame mata dole ba wallahi babu mai son ta matso kusa dashi duk ta zama kazamar karfi da yaji ranki shi dade, sai abu na biyu bayan ta haihu sai dan ya fito da matsala irin jariran ne da ake haifan su da katon kai wallahi akan yaronnan munyi karkaf nida mahaifinta yanzu abun ya kai har motarsa saida ya saida, kullum muna zarya hanyar asibiti yan uwanmu sunyi iya nasu wallahi basuda karfin taimaka mana, yanzu tana nan a gida ga jikinta yadda kikasan an yaba mata gawayi wasu kattan kuraje takeyi a fuska da kuma wasu wurare na jikinta, wallhi ko asibiti sun kasa karbarta fuskarta ma kanta sai ta baki tsoro, shine nazo wurinki ki taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ki, ki cece wannan yara da kudin magani ko yaya ne abinda Allah ya hore..." ta karasa tana goge hawaye, matukar tausayi ta bata, Hoodah tace, "Innalillahi wa inna ilahir rajioon, Allah ya basu lafiya yasa kaffara ne, yanzu zan fara baki wani abu ki rike, don  sarki baya gida idan ya dawo zan same shi in mashi bayani nasan bazata gagara ba InshaAllah." Mama ta sake share hawayenta da hannu tace "Mungode Allah ya saka maki da alkhairi ya kara girma da arziki, mungode sosai da sosai, sheyasa akace dan adam kowa da baiwarsa kuma babu kyau wulakanta mutum saboda shi wannan da kake wulakantawa a gaba zai iya taimaka maka..." Hoodah tayi murmushi ta mike tana kallon Mama, "Mama ina zuwa." Daga haka ta fara tafiya maids dinta na biye da ita, da tagumi Mama ke binta da kallo abun duniya duk ya ishe ta, Hoodah ta kai kusan mintina sha biyar can sai gata ta dawo fuskarta dauke da murmushi har tazo ta zauna hannunta rike da envelope, ta kalli Mama tace "Mama ga wannan ku fara amfani dasu zuwa gobe InshaAllah zamu zo sai muga abinda zamuyi a kai." Mama hannunta na rawa ta karbi envelope din tana ta jero godiya tana kuka sosai Hoodah na nuna mata ay babu damuwa ta daina kuka, "Dole ne in maki godiya ranki shi dade, kin mana abinda ko dan uwanmu bai mana ba, duk da abinda Ummalkhairy tayi maki amma gashi kece silar taimakonta, dole ne mu kara jin tsoron Allah wallahi rayuwar nan ba komai bace." Hoodah tayi murmushi, "Babu komai Mama dama ita duniya makaranta ce a cikinta muke daukar darasi, kuma a cikinta ne muke banbance fari da baki, don haka kedai kije ki kai yarki da jikanki asibiti Allah ya kara lafiya." Mama na murmushi tace, "Tou nagode kwarai da gaske ni zan koma." Hoodah tace, "Bazaki shiga kiga babies ba? Sannan zaki tafi ko ruwa baki sha ba ki shigo ciki." Bata musa ba suka mike inda suka taka har ciki ta shiga tayi barka sai yaba kyan babies din takeyi kamar ta sace daya takeji, sannan basu barta ta tafi ba saida aka kawo mata abinci dasu snacks da drinks ga kaji da salad saida taci sannan Hoodah tasa daya daga drivers dinta ya dauketa ya kaita har gida aikuwa tana zuwa ta basu labari jikin Khairy duk yayi sanyi, ji take dama za'a iya komawa baya da zata gyara rayuwarta sannan ta gyara barnar da tayi. Ganin kudin yasa suka razana Baba ya kirga yaga million daya ne harda wani abu a kai, tagumi yayi yana bin Khairy dake kwance kan tabarma da kallo  yace, "Kinga rayuwa ko Ummalkhairy? Kinga abinda na dade ina fada maki ko? Amma duk kikayi watsi da maganata kika dinga aikata abinda ranki yakeso, Khairy duk da na yafe maki amma na kasa mancewa da abinda kika aikata Khairy, kin kai kanki kin baro Khairy wallahi sheyasa annabi yayi gaskiya da yace mai hakuri yana tare da nasara yanzu da kinyi hakuri da duk abinnan bai faru da ke ba abu goma da ashirin duk ke kadai?" Khairy kuka Mama kuka, ya numfasa, "Yanzu ay bamuga ta zama ba tashi zakuyi muje mu fara biyan kudin aikin yaron nan ko ya samu saukin rayuwa, wannan ruwan dake fito masa babu dadin gani, ke kuma idan Sarki sukazo suka kara taimaka mana sai a diba ciki a fara naki treatment din..." ta gyada kai wasu hawayen masu dumi na gangaro mata daga haka Baba ya mike yana fadin, "Bari in dan fita nan waje kafin ku kimtsa ba jimawa xanyi ba." Mama ta masa a dawo lafiya sannan tace "Sai ki tashi ki shirya mu tafi, sannan inaso mu siya maki wannan robar da akesa wa masu yoyon fitsari wannan zaurin da kike yi babu dadi Khairy, sannan shima yaron nan kina daukar shi a jikinki kina sa masa zauri, yanzu ki tashi kije kiyi wanka ki chanza wadannan kayan masu zauri, shima yaron ki chanza masa." da toh ta amsa hawaye masu matukar zafi suna zubo mata, ta yunkura ta mike tana dunkuna zani yadda fitsarin bazai zubo kasa ba ta wuce bandaki, ita kuma Mama ta dauki yaron a hankali ta shiga daki dashi don ta kimtsa shi.

---------

Ranar wata laraba Ashraf ya dawo daga aiki da yamma lis misalin biyar da da rabi, a gajiye ya shigo, daga bakin kofa Zarah ta tare sa sukayi hugging juna kiss ya mata a kumatu kamar yadda ya saba duk sanda ya shigo gidan, hannunsa ta kama ta taimaka masa ya zauna kan kujera, manne masa tayi tare da kwantar da kanta bisa kafadarsa tana mai lumshe idanu tace, "Yanzu wanka zakayi ko abinci zaka fara ci?" yayi murmushi yana jin sonta na kara ruruwa a cikin ransa, yace

"Duk abinda kika ce princess shi zan fara yi?" Tayi dariya tace

"A gaskiya wanka ya kamata ka fara yi saboda zakaji saukin gajiyar da ka kwaso daga nan sai kaci abinci ko?" Yace "Yess! princess hakan za'ayi." A tare suka mike hannunsu sakale cikin na juna. Ta hada masa ruwan wanka sannan ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa, ko wane motsi nata akan idonsa ji yake kamar ya hadiye ta don so, ya sauke ajiyar zuciya yace

"Princess a gaskiya ki daina shagwaba ni da yawa, kinsan irin wannan duk ranar da bakida lafiya ko nayi tafiya zan sha wahala fa..."

Tayi dariiya bayan ta cire masa 

riga tace, "Wannan kuma ay daban ne, kuma ni ka daina cewa ranar da baka nan tou ina zaka je ma?" Yayi murmushi yana kamo hannunta duka biyun, "Kinsan tafiya na iya kamawa ko kuma mutuwa..." Da sauri ta toshe masa baki tace "Ka daina fadan haka, in ma mutuwa ce bana fatan ta riga daukar min kai na fiso ta fara daukata ta." Yayi murmushi

"Ba wanda yasan gawan fari princess, mudai yi addu'a Allah yasa mu cika da imani"

A sanyaye tace "Amin"

A haka ya shiga wanka, ita kuma ta fiddo masa kayan da zai sanya marassa nauyi saboda yanayi ne na zafi. Bayan ya fito ta taimaka masa ya shirya ta fesa masa turare sannan ta kamo hannunsa suka fito parlor. Kan dinning ta zaunar dashi bayan ta zuba masa jollof d'in taliyar data ji kifi da kayan lambu sai lemo mai sanyi. Sai da yaci yayi nat sannan suka koma parlor suna kallo suna fira har aka soma kiran sallar magriba.

----

Ranar wata litinin tafiya ta kama Ashraf zuwa Nigeria Kaduna duk da dai tafiyar daga office d'insu ne bama shi kad'ai zaije ba harda abokan aikinsa su kusan biyar, tun da yake wayar Zarah dake kwance gefensa ke masa wani irin kallo har ta kai ya tsargu, sai da ya gama wayar ne ya juyo yana kallonta yace "Yada kallo haka princess?"

Ta bata rai hade da zumburo pink lips nata masu kara mata kyau tace cikin shagwa6a "Ina zakaje?" Yayi murmushi yace "Wallahi tafiya ce ta kama mu yau d'in nan amma kar ki damu kwana biyar kawai zamuyi mu dawo." Ta juyar da kanta gefe alamun fushi, yayi murmushi tare da kamo ta ya maido bisa jikinsa yace

"Fushi kuma princess? Meyafaru?"

Idanunta suka kawo ruwa tace

"Naji kana zancen tafiya ka barni, kuma kai kanka kasan tunda mukayi aure baka taba tafiya daidai da rana daya ba, sannan kasan ban iya bacci idan baka kusa dani" Take yaji babu dadi saboda shima din ba iyawan zaiyi ba sai dai yazama dole ya tafi saboda aiki ne zai kaishi don haka sai ya rungume ta tare da fara aika mata da sakkonin kisses ta ko ina, itama ta biye masa sun d'auki tsawon lokaci a haka kafin Ashraf ya sauke ajiyar zuciya yace

"Princess wallahi inda kinsan dauriyar da zanyi muje mu dawo da bakiyi magana ba, wallahi zanyi missing dinki sosai, kiyi hakuri kar kice zakiyi kuka don bazan iya jure jin kukanki ba, i love you so much kwana biyar kawai zamuyi mu dawo insha Allah kinji my princess?" Ta kankame shi tace

"I love you more, inshaAllah zan daure har ka dawo amma kasani zanyi kewarka sosai." Yace

"Yes i know princess nima haka."

Daga nan Zarah ta tashi ta hada masa hadaden breakfast, ta shirya masa kayansa kafin ya fito wanka hade da fiddo masa kayan da zai sanya. Tana gamawa itama tayi wanka tasa wata bakar loose top marar hannu da pink dogon skin tight sai ta daura red dan kwali, ta kimtsa ta fito. Dakin Ashraf ta leka a lokacin yana shafa mai, ganinta yasa ya saki murmushi ta mayar masa, karasawa tayi ta taimaka masa ya shirya suka nufi dinning suka karya. Tunda suka fara cin abincin Zarah ke kallonsa kamar zata cinyesa, ya kalleta yace

"Princess?" Ta sadda kanta kasa tana murmushi tace "Na'am?" Yace "Na gama fa sai tafiya yanzu kuma..." Sai kuma ta 6ata rai duniya ba abinda ta tsana taji zatayi nisa da Ashraf dinta, yana ta lura da yanayinta amma sai yayi sauri yace, "Ga wannan." Ya mika mata kudi dubu hamsin yace "Ki rike wannan abinda kike 6ukata kiyi yi amfani dasu har Allah yayi mana dawowa, kuma duk sadda kikaji kadaici ki tafi wurin su Kaka kuma kinga gidan akwa maids ko ina so bakida kadaici." Tana dai ta daurewa bataso tayi kuka amma abu yaci tura sai kawai tasa kuka, take hankalin Ashraf ya tashi ya rude, hugging dinta yayi yana ta aikin lallashi tare da assuring nata cewa kwana biyar dinnan zaiyi ya dawo kuma duk abinda take bukata ya aje mata, sai da ya tabbatar ta bar kukan sannan ya tafi. Bayan tafiyar Ashraf duk gidan gaba d'aya ya mata fadi ba dadi sam, yau batasan ya zatayi bacci ba babu Ashraf a kusa da ita.

Haka ta wuni daga kallo sai chatting, idan ta gaji ta buga game a wayarta ko kuma ta kira Hoodah a nuna mata twins dinta.

Tunda ya isa ya kira ta ya sanar mata sun isa lfy...

------

Mikewa yayi yana kallonta da yar dariya yana kallon kofa, "Tou Khadija tunda nidai yanzu ba'son ganina sai Dr Haiydar sai yayi maki shi." Ko kadan baiji haushi sai ma dadi tinda da taimakon shi akan iya ceto rayuwarta, sunkuyar da kanta tayi tana murmushi irin am sorry dinnan ta kusa minti ashirin a office din Dr Hafiz amma duk maganar da zai mata bata ce masa kala kuma taki sakin jiki dashi yayi mata therapy din yadda suka saba karshe yace mata ko a kira mata Dr Haiydar sai a lokacin ta daga mashi kai alamar eh, sai kuma tayi murmushin jin kunya tana dan girgiza kanta. "Allah ba haka nake nufi ba." A hankali ta furta shi kuwa Dr Hafiz sai yayi dariya yana faman tattara wasu files ya mike ya nufi hanyar kofa, tun ranar da suka yi therapy da Dr Haiydar tou kullum sai ya kira mata shi, "Kila dai daga yanzu zan dinga maki kwatancen office dinsa ba sai kin dinga tashina daga office dina ba..." daga haka ya fita yana murmushi, can Dr Aliyu ya shigo yana kulle office din a hankali saida ya karaso kusa da ita yace, "Khadija kina lafiya?" abinda ya tambaya kenan a hankali ta dago tana kallonsa tana murmushi a hankali, "Alhamdulillah, ina kwana?" Kallonta yake sosai yana murmushi shidai baisan dalili ba amma Khadija tana burge shi kuma sosai ba kadan ba, duk da cewar duk wanda ya kalleta yasan tana tare da tarin damuwa kuma sai kaji kana son taimaka mata da dukkan wani iko da Allah zai baka. Murmushi yayi a hankali yace, "Ina kwana kuma? Ay saidai ina yini don ba dadewa xakiga har sha biyu ta buga," gyada kai tayi alamun ta tuna, "Tou ina jinki Khadija yaya dinki? Ana class din ko kuwa?" Ya tambaya yana kureta da idanu, dagowa tayi da fara'arta alamar zatayi maganar abinda takeso. "Sosai ina jin dadin class din, na manta wayata a gida dana nuna maka wasu pictures." Murmushi yayi inda ya mike yajata zuwa therapy room din daga nan ya fara aiwatar da aikinsa cikin gwaninta da kwarewa, yaji dadi yadda ake samun improvement kuma da alama bazata dade kwarai ba zata samu sauki sosai. Yana cikin aikin ne yace, "Yanzu yaya batun karatu kuma Khadija?" Tace, "Final year nake na kusa gamawa InshaAllah." Yace "Kina zuwa?" Ta gyada masa kai alamun eh, yayi murmushi, "Yanzu da ace Allah xai baki dama ki goge wani abu daga cikin rayuwarki gaba daya Khadija me xaki goge?" Gabanta ya fadi kafin tace, "Abubuwa da yawa Dr, da ina da iko da na goge wani abu da nayi wa yar uwata wanda bazan iya fada maka ba, sannan da ina da iko zan goge ta hanyar da aka bi aka sameni da kuma kaddarar data afka man kwanakin baya, zanso inga mahaifiyata in rayu da ita ta bani mother's love duk da dai ban rasa wannan ba amma dai I still wish zan ga mahaifiyata koda sau daya ne..." zuwa yanzu kuka take kamar ranta zai fita tunda akayi mata fyade takejin rayuwarta ta kare sannan takejin duk wani pain dake ranta ya darsu da abubuwan da suka faru da ita, saida ya barta ta gama kukan kafin ya mika mata hanky, "Sannu ko in baki ruwa?" Ya tambaya yana yin hanyar fridge da sauri ta daga mashi kai disposable cup ya aje mata saida tasha ruwan hankalinta ya dan kwanta kafin shima ya koma ya zauna. "Allah ya jikanta Khadija, sannan komai da kikaga ya faru mukaddari ne daga Allah nima nan da kike gani banida mahaifiya a hannun kishiyar uwa na tashi." Da sauri ta dago tana kallonshi, "Da gaske?" Yayi mata murmushi "kwarai kuwa, tun ina dan shekara biyar ta rasu ta barni hannun matan babana..." take taji ba dadi, "Allah sarki Allah yayi mata rahama." Yace "Ameen." Mikewa yayi bayan ya kammala therapy din yana yar dariya yana kallon wrist watch din hannunshi ganin har lokaci ya kure, "Ya kamata mu tashi haka nan mun bar Mummy tana jiranki a waje..." ta kalleshi, "Da driver muke ita tana wurin aiki." Kamo wheelchair din tata yayi ya fara janta zuwa wajen asibitin, a haka suke tafiya yana bata labarin rayuwarshi, babu abinda ke ciki sai tsantsan tausayi rike kukanta takeyi har sukayi bakwana yasata a mota, tana shiga mota ta saki kukan sosai kuka take kamar an aiko mata da sakon mutuwa, driver din babu abinda yake sai faman bata hakuri yana mata sannu shi ya dauka ma ko ciwo takeji a jikinta. Shiga tayi cikin gida bayan Mama Hauwa ta dora ta saman wheelchair dinta suna tafe tana goge hawaye, kamar daga sama taji ance, "Wai nikam dadin kuka kikeji ne?" A razane ta juyo taga Dr Hafiz zaune bisa daya daga kujerun garden gefensa drink ne da snacks hannunsa da waya yana latsawa, da sauri ta goge hawayenta tana mamakin ganinsa, "Ina yini?" Yayi murmushi "Ina yininki? Tou ya exercise din akwai wahala? Shi wancan likitan haka ake therapy ki dawo gida kina kuka?" Yar dariya ta subuce mata. "Ba ruwansa..." da murmushi saman fuskarshi yace, "Aww haka zakice? Wato karesa ma kikeyi ko a gabana?" Yar kunya ta kamata hakan yasa ta kama keken nata ta karasa kusa da shi fuskarta a sunkuye...