Sunday 26 February 2017

KHALEEL Page 33&34

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻33&44✍🏻✍🏻


Ta juyo da sauri har ta kusa cin karo da shi, da hanzari tayi baya. Ta d'aga ido tana k'are masa kallo sanye yake cikin farar singileti da bak'in gajeren wando, sai takalmin Adidas, yayi murmushi yace
"Yanzu kin kyauta kenan? Har kika tashi sallah bazaki tashe ni ba ko, shikenan alhaki ya hau kanki"
Juya tayi da sauri tayi kamar bata jishi ba, sannan ta juya tayi cikin gida.
Biyo ta yayi harda d'an gudunsa yace
"Hanifah! Muje ki bani abinci yunwa nakeji"
Kamar ta bigeshi ya fad'i k'asa haka take ji don takaici da haushi. Tace
"Ko kunya wai ni zaiyi wa shagwab'a da wata shegiyar shigarsa sai kace wani yaro"
Da sauri ya cimmata tare da chafko hannunta yace
"Kinma isa yarinya ki barni biya, mu shiga tare"
Haushi ya turnik'e ta, ta fara kicinyar k'wace hannunta amma ina! Ta kasa dole ta hak'ura suka k'arasa ciki tare.
Ya zauna kan kujera Hanifah ta zuba masa tsurar doyar da ko soyawa batayi ba, ta had'o masa ruwan tea ta tura masa gabansa, sannan tasamu wuri ta zauna tana fuskantarsa tana jiran ya gama ta kwashe kayan kamar yadda yayi mata umarni!
Yana ci yana karkad'a kai da k'afa yana d'an girgiza kansa, har ya kammala babu wani complain kamar yadda Hanifah ta buk'ata, sanin cewar Khaleel mutum ne shi mai son varieties na abinci, yana son ya ga an cika masa abinci kala kala kamar yadda Ammi ke masa, bama kamar da safe koda rana. Haushi ya kama Hanifah taso ace yaci abincin yayi complain ko ta ji dad'i.
"Tattara kayan ki same ni d'aki na"
Ya fad'a tare da mik'ewa tsaye. Tace to tare da watsa masa wata uwar harara wane zata zazzago da idonta waje.

Zaune yake kan carpet ya baja takardu a gabansa yana duddubawa, nuna mata kusa dashi yayi alamun ta zauna, ta zauna fuskar nan tamau kamar hadari, ya kalleta sai yaji dariya ta ku6uce masa, ya sunkuyar da kansa k'asa yayi dariyarsa sannan ya d'ago yana kallonta yace.
"Hanifah kenan, kina fa burgeni ba kad'an ba, wannan fuska taki kamar tsohuwa taga zaki"
Ta k'ara tsuke fuska. Khaleel ya girgiza kansa ya soma magana
"Wannan takardun na rabon gadonmu ne wanda aka bani saboda haka na d'auki kaso na dama harda wannan gidan wanda Abbanki ya fara ginawa shine ya mallaka min shi halak malak, ku kuma ga naku keda Saif, idan ma kinason zuwa sai na kaiki, idan kuma sai Saif ya dawo nan da wata biyu a lokacin ya kammala masters d'insa to ba matsala, zaki iya ajewa har sai ya dawo, kud'ad'en kuwa, kowa na tura   masa a account d'insa"
Ta kwashi takardun zata mik'e ya ce
"Sorry ban gama magana ba y'alla6ai"
Ta gyara zamanta amma ko uffan bata ceba, ya cigaba.
"Ina so ki sanar dani irin motar da kikeso zan bada ayi miki order, don ki samu ki fara koya"
Da sauri ta d'ago tana dubansa, annurin fuskarta ya bayyana, batason lokacin da dariya ta ku6uce mata ba, komai ta tuna kuma sai ta d'aure fuska tace
"Bana son motarka ka rik'e kayanka, bana buk'ata"
Yayi dariya yace
"Dama ay bance kinaso ba dole, idan har baki sanar dani ba toh zan siyo miki duk wacce ta kwanta min a rai"
Tace
"Wannan kuma za6inka ne kai kaji zaka iya"
Ita kanta tayi mamakin yadda akayi ta iya fad'a masa magana haka.
Daga haka bai k'ara magana haka itama ta mik'e tayi dak'inta da sauri.


*******

Zaune Hanifah take a d'akinta, tunani ya isheta tare da mamakin chanzawan Khaleel lokaci d'aya.
Yau sati biyu da bikinsu, amma abin mamaki tun ranar da abinnan ya faru ta fad'a masa magana bai k'ara mata magana ba, gashi dai wulak'ancin yau daban na gobe daban take masa, amma ko uhm bai ce mata, kamar idan ta kai masa abinci ta zauna zaman jira ya gama, tana lura zai ci abincin kad'an sannan ya k'ura mata ido, sai ta zo mik'ewa da sauri zai riga ta tashi.
Ga bata yi masa wani abin da'di daga doya sai dankali babu ko k'wai da safe kenan, da rana kuwa dama farar taliya takeyi idan yaso yaci da manja wannan ruwansa, ita babu abinda ya dame ta.
Haka to abubuwan ke gudana, zaman kurame sukeyi a gidan, idan kuwa ita Hanifah ta ga dama sai ta ya6a masa magana son ranta, amma ko uhm bai ce mata, irin abin yafi ciwo kayi ta magana a maida ka kamar wani banza.
Kullum Hanifah ke riga Khaleel tashi, da ta tashi zatayi kitchen don had'a kalaci, idan Khaleel ya tashi zai gyara gadon ya share d'akin ya goge, da kansa yake jona abin turaren wuta.
Gaba d'aya ya zama wani shiru shiru, duk wani fad'ansa, da nuna isa da gadara duk  ya sauke su, ya maida kansa kamar wani yaro, a lokacin ita kuma Hanifah ta baje kolin iskancinta kala kala.

A haka motar Hanifah ta iso, sabuwa dal agogo a leda, KIA bak'a wulik! Kuma ya bada umarnin koya mata da kansa, sai a nan taga Khaleel d'in da, cikin ikon Allah kuwa cikin sati d'aya ta k'ware ba inda bata shiga.


*******


Ranar wata saturday Hanifah bata tashi da wuri ba, ta duba agogo k'arfe takwas da rabi ta kalla ba Khaleel kusa da ita, wato ramawa yayi kenan.
Ko wanka batayi ba ta fad'a kitchen, tana cikin  soya dankali Haruna d'an aiken su ne yayi sallama, hannunsa d'auke da da katon d'in su swan, da lemuna, ya dire yana gaishe da Hanifah. Ta amsa ba tare data kalle shi ba.
Bayan ta kammala ta nufi d'akinta don yin wanka, abin mamaki Khaleel ne tsaye yana jera gugar Haninfah da aka kawo jiya da yamma, tsaye tayi turus ta cika da mamaki! Yanzu sauk'in kansa har ya kai haka? Kai ina yaudara ce ko kin manta halinsa? Mugu fa ne wanda baya son farin cikinki, haka tayi tsaye tayi ta sak'e sak'e a ranta.
D'agowa yayi suka had'a ido ya sakar mata murmushi.
"Kinga yau ban tashe ki ba ko? Naga bakya sallah sannan kin sha fama da ciwon ciki ga bakiyi bacci da wuri ba, sheyasa na k'yale ki don na kula baccin yana miki dad'i bana son na katse miki shi"
Bata tanka ba har ya gama zubarsa dama shi take jira ya gama, da ya lura bata tanka ba sai yayi shiru har ya gama gyara kayan.
Haka suka zauna kan dinning kamar kullum har ya gama, ta mik'e ta tattara kayan ta kai kitchen ta dawo a lokacin baya wurin, ta gyara wurin ta kimtsa sannan ta nufi d'aki.
Tana shiga d'aki nan ma taga baya nan, taji dad'i sosai, shirin wanka tayi ta fad'a toilet.

K'arfe sha biyu saura ta kammala ta fito, kitchen ta nufa ta d'ora farar macaroni dama akwai miya a fridge ta d'umama, abincin kenan kullum daga taliya sai macaroni amma ko a jikinsa.
Ta jera kan dinning, ta hau karanta wani online novel a wattpad mai suna Bond.
Sai dai 6angate d'aya na zuciyarta na tunanin dalilin da yasa ya Khaleel ya chanza mata, gashi kullum addu'arta d'aya Allah yasa masa tausayinta ya sallame ta daga wannan auren wanda take ji tamkar tana kurkuku ne.
K'ara shigowar message taji, ta mik'e zaune tana dubawa, ga abinda aka ce.
"Gaisuwa a gareta Hanifah tare da fatan alkhairi, bazan iya bayyana miki da ko ni wanene ba,amma abu d'aya zuwa biyu  nakeso na sanar da ki. Na farko!
"Kin yaudare ni, kinyi aurenki ashe dama haka kike mayaudariya, to ki sani baki ci bulus ba sai na d'auki mataki akan haka, sannan abu na biyu!! Na baki nan da wata d'aya kiyi getting rid of that your stupid husband and come back to me, or else you left me with no other choice than to....
Kinsan dai sauran, zan iya yin komai don na cimma ma burina. Bisslama na barki lafiya"
Tashi tayi zaune tana zaro idanu waje, gumi take had'awa duk kuwa da sanyin ac d'in da ke d'akin. To wannan waye? Kuma a ina ya samu number ta?" Shine tambayar da take ta jera kanta kenan, can kuma ta zabura ta mik'e zaune tare da fad'in Deen....!




MSB✍🏼

Friday 24 February 2017

KHALEEL Page 31&32

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻31&32✍🏻✍🏻


I dedicate this page to all members na Lovely fans❤️❤️❤️


Anty Hassana ce rik'e da ita har suka shigo d'aki, bayan y'an rakiyar amarya sun gama ganin gidan suka sanya alheri kowa ya kama gabansa. D'aki ya rage daga Anty Ikilima sai Anty Hassana suna ta faman lallashin Hanifah suna bata hak'uri, Anty Ikilima ce ta dafa kafad'arta tace.
"Hanifah kiyi hak'uri kada kanki yayi ciwo, kinsan kuwa rayuwar nan ba mattabata bace? Daga lokacin da aka d'aura miki aure aka bud'e miki shafin rubuta lada,  aljannarki na k'akashin tafin k'afar mijinki, yi nayi bari na bari shine zaman aure, kar ki zamo mai tsiwa, rashin biyayya da kuma gadara, manzon Allah (S.W.A) a cikin hadisinsa yace Ku fad'i alkhairi ko kuwa shiru, idan har kinsan bazaki fad'a masa maganar da zata faranta masa rai ba  to fa kiyi shiru" Gaba d'aya maganar Anty Ikilima sun soma gundurar Hanifah don haka da sauri ta d'ago tana dubanta tace
"Insha Allah Anty, nagode da shawarar da kika bani Allah ya saka da khairan"
Tayi murmushi tace
"Yauwa d'iyata, Allah ya baku zaman lafiya"
Anty Hassana ce ta mik'e tsaye tana fad'in
"Bari na d'auko mana abinci kinga har sha biyu ta wuce don ni ko karyawa ma banyi ba"
Haka suka zauna da Hanifah suna ta janta da fira sai da sukayi isha'i sannan sukayi sallama suka tafi.
Tana jinsa da abokanansa a palo suna ta fira harda k'yalk'yata dariya, ganin basuda niyyar kiranta tayi ta jin dad'i, dama itama baso take taje ba.

K'arfe sha daya saura har Hanifah tayi wankanta ta sa kayan bacci tabi lafiyar gado amma sam ta kasa bacci, can wurin k'arfe sha daya taji shigowarsa, gabanta yayi mummunan fad'uwa, tayi kwance lamo kamar mai bacci, ya kalle ta, fuskarsa babu alamun fushi haka ma babu alamun dariya yace
"Hanifah tashi ki dawo nan zanyi magana da ke" ya nuna mata kusa da inda yake zaune ma'ana bakin gado.
Ta taso ba musu sai dai fa fuskarta ba yabo ba fallasa ta zauna d'an nesa da shi, shi da yace zaiyi magana da ita maimakon ta kalle shi a'a, sai ta juya masa k'eya.
Wata tsawa ya daka mata, bata san yadda akayi ba sai dai ta ganta kusa da shi sai kyarma takeyi, kamar wata mai jin sanyi, duk jikinta gaba d'aya kyarma yakeyi, sai kuwa tasa kuka mai sauti, ba wai tsawar da yayi mata kad'ai yasa ta kuka ba illa dai ta tuna wai yau Khaleel ne mijinta, mutumin da ta dad'e tana ma kallon yayanta ciki d'aya, sannan bata sonsa ko kad'an, yau shine mijinta.
Haka ta d'auki tsawon lokaci tana kuka, ko uffan bai ce mata ba har sai da ta gaji  tayi shiru don kanta, jin tayi shiru ya sa yace.
"Har kin gama kukan?"
Ta d'ago tana kallonsa a ranta tace
"Wanann tambayar ta rainin wayau ce ko me?"
Tambayar ta matuk'ar 6ata mata rai.
"Ya kamata dai ki rage kukan da kike kar ki je ki ja ma kanki wani ciwo"
"Jikinka ko nawa?" Ta fad'a hankali, ta d'an ji tsoro don a tunaninta yaji amma abin mamaki sai taga yayi murmushi yace.
"Wallahi idan kina kukan nan jinsa nake har cikin raina, hankalina tashi yake gashi ni bana so kina yawan d'aga hankalinki nafiso ki samu nutsuwa da kwanciyar hankali"
"Ina naga samun nutsuwa da kwanciyar hankali zanyi tarayya da mugu"
Ta fad'a cikin ranta.
Ya dan runtse idanunsa yace
"Da ina iya hak'ura da ke Hanifah na rantse da Allah da tuni na hak'ura don ki samu farin ciki, amma duk da haka ina so ki sani bakiyi kuskuren aurena ba, don na miki alk'awarin nine zan saki farin ciki Hanifah, zan koyar da ke sona, zan baki jin dad'i da farin ciki, fatana Allah ya bani ikon cika alk'awarin dana d'auka"
Ya d'an yi shiru na y'an dak'ikai kafin ya cigaba.
"Hanifah naso ace kinsan irin d'imbin k'aunar da nake miki, tabbas son ki ya wahalar da ni a rayuwa ku duba fa kigani Hanifah tun kina jaririyarki cikin tsumma, sanda nafara ganinki a lokacin Allah ya d'ora min sonki, duk da lokacin ma bansan meye SO d'in ba, don haka ki kwantar fa hankalinki, ni nasan wacece ke, nasan me kike so da wanda bakya so.
Sai magana ta gaba, ina so ki sani ke k'anwata ce ta jini, sannan kiyi la'akkari da ni ba tsaranki bane na girmeki, na aure ki ne don ina sonki ba sadakarki aka bani ba"
Sannan yayi shiru na second biyar zuwa shidda, sannan ya d'ora.
"Bazan d'auki raini ba, sannan bazan yarda ki cigaba da azabtar min da zuciya ba kamar yadda kika saba ba". Sai kuma ya nuna kansa da yatsa
"Yanzu a gidana kike a matsayin matata dole ayi min biyayya, a kuma kyautata min saboda ina da iko kuma a k'arkashina kike.
Sannan ki sani doka ce nasa ba zancen kwana d'aki daban daban ko kiso ko kar kiso a d'akina ko dakinki zamu dinga kwana no matter what. Hanifah! And most importantly maganar girki, bana son mai aiki, ke da kanki zaki shiga ki dinga girka min, bana son k'azanta dole ki tashi ki tsaftace muhallinki. Sannan maganar hakk'inki na aure har abada bazan tilasta miki ba, har sai kin shirya...."
Nan da nan ta saki ajiyar zuciya tare da maida kanta k'asa, dama abinda take fatan ji daga gareshi kenan, wanda tasani cewa har abada kuwa bazata ta6a kai kanta gareshi ba, yama za'ayi hakan ta faru no never!!
Murmushinsa taji sai kuma yace
"Idan kina da abin cewa bismillah, idan kuma babu kiyi baccinki..."
Ko kallo bai ishe ta ba ta mik'e ta koma can k'arshen gado tayi kwanciyarta.

Toilet ya shiga, tana jin fitowarsa kamar ta make shi sai wani shafe yakeyi gaban madubi, da feshe feshen turaruka ya fesa kusan kala biyar, d'akin kuwa ya d'auki k'amshi mai dad'i. Ta d'an yi tsaki yadda ita kad'ai keji tace
"Ko wa zai burge da wani k'amshinsa? Ko da yake yana son k'amshi daman"
Ya rufe musu d'akin tare da kashe fitila, gabanta ya fad'i, tace a ranta
"Yau nice kwance gado d'aya da ya Khaleel?"
"Matso kusa dani Hanifah inji d'uminku"
Ya katse mata tunanin da takeyi.
Ta k'ara takure kanta wuri d'aya kamar mai bacci sai zare ido takeyi kamar tayi laifi, tana jinsa yana addu'ar bacci ya tofa musu addu'a, bifi minti biyu ba bacci yayi awon gaba dashi.
Ta saki wata uwar ajiyar zuciya, a yayinda wasu hawayen bak'in ciki suka biyo baya, ta d'ago kanta kad'an ta kalle shi a hankali tace
"Mugu kawai"
Daga nan batasan lokacin da bacci yayi awon gaba da ita ba.


*********

Da asuba Hanifah ta riga tashi, a hankali ta tura k'ofar ta fice don ma kar ya tashi, d'akinta ta koma tasa key gudun kar ya shigo, toilet ta fad'a ta d'auro alwalla sannan ta fito ta tada sallah, sai da gari ya d'an yi haske sannan ta tashi ta shiga tayi wanka, ta fito ta shafa mai tare da fesa turaren jiki kamar yadda ta saba, ta sanya wata atamfa maroon and ash ta fito tana dariyar mugunta, kitchen ta fad'a, a lokacin k'arfe bakwai da kwata, ta fera doya, tasan Khaleel baya son doya idan ba soyawa akayi ba, yasa ta dafa, bata soya ba kawai ta saka cikin warmers, kan dinning ta d'ora sannan ta dafa masa ruwan tea,  plate da cup kawai ta takwaso ta d'ora kan dinning d'in, ta kamalla a lokacin bakwai da minti hamsin da biyar.
Palo ta fito sai kuma taji tana sha'awar ganin gidan, sai kawai ta fito ta k'ofar kitchen, tsarin gidan yayi kyau don kuwa daga baya lambu ne ba kalar shukar kayan marmarin da babu, hakan ya k'ara k'awata wurin, ga tsuntsaye musamman geese da talo talo sai wasu guda biyu wanda bata sansu ba.
Ta ta6e baki tace "kilbibi kawai"
Ta fito gaban gidan, shima ya k'awatar sosai,  tsakar gidan nada girma sosai, don kuwa harda k'aton swimming pool da aka zagaye da grasses, gidan ma gaba d'aya grasses ne shimfi'de gwanin sha'awa, ga wasu kujerun hutawa nan guda biyu pink and blue da center table d'in rabin table d'in pink rabi blue. Tabbas idan akace wurin baiyi kyau ba anyi k'arya, daga gefen kujerun kuma irin rumfar nan ce zagayayya da akeyi da suminti, tsarin rumfar yayi kyau, can gefen swimming pool din kuwa swing ne (shillo) mai kamar kujera mai kyan gaske. Ta rik'e baki tana kallon gidan galala. Ga shukoki nan kala kala gaskiya gidan yayi kyau....
Sai kuma ta ta6e baki tace
"Wannan wurin dai baiyi kyau ba, kilbibi kawai, mtsw"
Ta fad'a tana k'are ma wurin kallo, wasu flowers ne suka d'auki hankalinta da akayi ma shapes kala kala.
"Yayi miki kyau halan?"
Ta jiyo da sauri tana k'are masa kallo....



MSB✍🏼

Thursday 23 February 2017

KHALEEL 29&30

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️


Wannan page d'in naku ne members na PWF, babu abinda zance muku sai dai nace Allah ya saka muku da alkhairi akan yadda kuke bada had'in kai don cigabanmu tare da taimakon juna, Allah ubangiji ya k'ara muku basira da zak'in hannu, i love you all so much❣πŸ’™❣


           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻29&30✍🏻✍🏻


K'arfe bakwai da kusan rabi aka shirya amarya cikin wani d'an ubansu fari da blue d'in bridal gown, sai dai bisa tarbiya ta Ammi baka cewa rigar amare ce, don kuwa ta rufe mata jikinta ruf, babu inda wani 6angare na jikinta ya bayyana irin na y'an matan zamani yadda zakaga an d'inka riga amma duk jiki a waje kamar ba y'ay'an musulmai ba, Allah dai ya shirye mu baki d'aya.
Ba'ayi mata wata kwalliya mai yawa ba, don Hanifah ba mai son kwalliya bace bata son wannan shafe shafen da ake yayi, aka d'auko mayafi aka lullu6e mata jikinta da shi kalar kayanta, y'an uwa da abokananta ma anko suka sanya kalar brown and cream, a lokacin da aka fiddo amarya an gama mata kwalliya kowa ya yaba kamar ba Hanifah ba.
Sai kusan takwas da rabi motocin d'iban mutane zuwa wurin dinner suka iso.
Khaleel na waje ya gama shirinsa cikin blue d'in shadda wadda ta yi masa kyau ba kad'an ba, kayan sun d'an kama shi haka ya k'ara fito k'arfi had'e da kumarinsa ta ko ina.
A yayin da Saif ke sanye cikin farar shadda sabuwa dal, cikin wad'anda Ammi ta d'inka masa.
Duk jama'ar wurin mutane ne daga garuruwa daban daban, inda yayi karatu ko yake da abokai da sauransu.
Wata daga cikin cousin d'in su Hanifah mai suna Surayya ta fito waje inda Khaleel da tawagarsa ke tsaye suna fira cike da nishad'i, gaishe su tayi tace.
"Ya Saif an gama shiri fa, mu taho a fara tafiya ne?"
Khaleel ya kalle ta yace
"Ina amaryar?"
Tayi murmushi tace
"Tana ciki itama an gama shirya ta"
Saif yace
"Ok ku fito na tafi da wasu a motata, sauran kuma wad'anda basu samu wuri ba, ga motaocin friends d'inmu nan sai su shiga"
Tace to, ta juya tayi ciki da sauri don kiransu.
Ba'a d'auki tsawon lokaci ba aka fara tafiya wajen dinner d'in, motar da aka shiga da ango da amarya babu kowa sai su kad'ai a ciki.
Khaleel ya kalli Hanifah yayi gyaran murya yace.
"Wannan kallon fa, yarinyar nan naga kamar kinfini zak'ewa ko?"
Ba shiri ta kalle shi, ta kuwa dank'ara masa harara ta kauda kanta. Ya rankwafo saitin kunnenta kamar yana mata rad'a yace.
"Gaskiya kin iya kallon love Hanifah, kinga yadda idanunki ke juyi kuwa"
Ta k'ule da maganganunsa wato yama raina mata hankali.
Haka suka isa wurin babu abinda Khaleel keyi sai tsokanar Hanifah, ita kuwa ko uhm ta dena cewa.
Wurin ya gauraye da hasken fitilu masu kyan gaske, motar da amarya da angon ke ciki ta tsaya, kafin su fito sai da suka yi minti biyu sannan Saif ya basu umarnin fitowa, tun daga bakin mota aka fara d'aukar su hoto da wayoyin flash, banda mai hoto da aka d'auko musamman domin d'aukar hotuna.
K'awaye masu anko suka fara shiga, sannan ango ya shigo shida amaryarsa cikin hall d'in.

Aka fara bud'e taron da addu'a, sannan Saif ya fito ya fara fad'in tarihin ango, kasancewar tsayin rayuwar Khaleel bashida wani aboki da zai kira da sunan amininsa sama da Saif, ya zayyano makarantar da yayi, tun daga nursery, primary da kuma secondary, da abinda ya karanta.
Ya gangaro da fad'in amarya da ango rainon gida ne, sannan shine mutum na farko da ta fara yi ma tumbud'i, aka k'yalk'yale da dariya.
Sam bai damu da dariyar ba ya cigaba da cewa.
"Akwai wata rana zamu tafi sallar juma'a ya d'auke ta yana mata wasa, kawai ta feso masa fitsari a fuska da jikinsa gaba d'aya, bata tsaya a nan ba kashi ya biyo baya, a wannan ranar sai da muka makara zuwa sallar juma'a don sai da ya sake wanka..."
Aka sake kwashewa da dariya.
Nan Saif ya cigaba da zayyano musu abubuwan da Hanifah tayi wa Khaleel d'in tana baby, Hanifah ta k'ule, kamar ta fashe.
Bayan ya kammala ya wuce ya samu wuri ya zauna, aka kira wata y'ar ajin su Hanifah a makaranta kuma k'awarta mai suna Sadiya, itama ta bada tarihin amarya da makarantar da tayi da sauransu. Ta kammala tayi addu'a ta koma mazauninta.
Bayan nan, aka fara ciye ciye da shaye shaye (abinci, drinks da sauransu), amarya da ango basuyi rawa ba sai y'an mata ne suka d'an taka, an dai kirasu akayi musu hotuna ba iyaka wanda za'a sanya a album.
Sai kusan sha biyun dare aka watse kowa ya nufi makwancinsa.
Ranar da k'yar Hanifah ta iya yin baccin kirki.


*******


Washe gari lahadi ba'ayi komai ba sai shirin d'aukar amarya da akeyi, jikin Hanifah duk yayi sanyi har wani zazza6i take ji, idonnan yayi jajir, ga anyi anyi taci abinci tak'i, Ammi har zare mata ido tayi amma tak'i cin komai, sai da Ammi ta had'o mata tea mai kauri ta shigo ta mi'ka mata tace.
"Tashi ki sha"
Ta d'ago daga kwance da take tace
"Na koshi Ammi..."
Ammi ta d'aure fuska ta fara fad'a
"Kar fa ki maida mu sakarkarin banza mana, don ma kinga ana lala6a kisha shine zaki fara yi mata mutane rainin hankali, aure kanki farau ne? Dama tun kafin kiga 6acin raina ki tashi kisha"
Hanifah ta fashe da kuka
Anty Ikilima (matar yayan Ammi) ta k'araso tace
"Don Allah kiyi mata a hankali, dama dole hankalinta ya tashi baki gani za'a raba ta da gida ne?"
Ammi tace
"To ita kad'ai ta ta6a yin aure a duniya?"
Anty Ikilima ta kalli Hanifah tace
"Y'ata tashi kisha kinji"
Ta'ki tashi ma k'ara tura kanta cikin pilo da tayi. Ammi ta kalli Anty Ikilima tace
"Kin dai gani ko? Yarinyar nan ta raina ma mutane hankali wallahi, ke kika sani idan kinga dama kar kisha ki zauna da yunwa, ai cikinki ne"
Daga haka tasa kai ta fice daga d'akin, Anty Ikilima ta kwanta da murya tayi ta lallashinta, da k'yar dai tasha rabin kofi, sannan kuma ta matsa matabdole ta tashi ta shiga wanka, a yayinda su Sadiya da sauran y'an uwa suka tashi suka fara harhad'a ma Hanifah sauran kayanta cikin akwati.


*******

Da yamma Ammi da kanta ta shirya Hanifah cikin atamfa d'inkin riga da skirt kalar green da dark pink, aka d'auko ALKYABBA aka sa sanya mata, a d'akinta Ammi tayi mata nasiha mai ratsa jini da zuciya, kuka kawai takeyi kamar ana zare mata rai.
K'arfe biyar daidai aka fito da ita daga d'akin Ammi wanda da k'yar aka 6an6are ta daga jikin Ammi, y'an rakiyar Amarya suka fito wad'anda mutane k'alilan ne sauran wad'anda basuje ba sai daga baya zasu je.
A mota ma kuka take sosai, Anty Ikilima sai Anty Hassan (itama matar brother d'in Ammi ce) suke gefen Hanifah suna aikin rarrashi har aka iso gidan.
Anty Hassana ce ta kamo hannunta ta fito da ita daga motar sannan ta sanya ta tayi bismillah, ta shiga gidan da k'afar dama...



MSB✍🏼

Tuesday 21 February 2017

KHALEL Page 27&28

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


Na sadaukar da page dinnan ga masu kaunar novel dinnan, me love you all so much....!!! 😘


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻27&28✍🏻✍🏻



            BAYAN SATI D'AYA


A k'arshen sati aka turo ma Khaleel da takardar shaidar aikinsa, dama kuwa yafara k'ananan zane, kowa ya taya Khaleel murna, ya shiga office d'insa cike da d'imbin nasara, da fatan alkhairi daga bakin Ammi da sauran y'an uwansa da duk wani mai k'aunarsa.
Khaleel ya soma aikinsa cikin k'warewa da kuma himma.
Aikin da ya fara ya d'an samu sauk'i a zuciyarsa, at least dai yanzu ya rage ganin Hanifah, amma koda yaushe tana nan mak'ale acikin zuciyarsa, ko laptop d'insa wani makaken hotonta ne da tasha kyau har ta gaji, office d'insa gaba d'aya ya k'awata shi da hotunan SANYIN IDANIYARSA.



*******


Hanifah ta gama yanke shawarar tayi wayar k'arya don ta k'ular da Khaleel, tasan muddin yaji to fa dole ranshi ya sosu, dan haka sai ta fito palo, tasan weekend ne Khaleel d'in na gida, hakan ya sanya ta gama tsara yadda zata k'ular dashi.
Kujera ta samu ta zauna na tsawon minti biyu, ba alamun Khaleel, amma still ta k'udiri niyyar 6ata masa rai kamar yadda ya watsa mata miyau rannan!
Tana nan zaune taji alamun mutum, bata san ko waye ba amma ta tabbatar baya wuce Khaleel don zuwa wannan lokacin Ammi na d'akinta tana hutawa.
Sai kawai ta kara wayar a kunne tayi ta zuba zance, tana kashe murya tana soyayyar k'arya. Ba zato ba tsammani taji saukar mari a kuncinta, a razane ta k'wala ihu, fizgo ta Ammi tayi ta shiga tsula mata wayar tv ta ko ina a jikinta. Tana tsula mata tana cewa
"Yanzu Hanifah tarbiyar da na baki kenan? Da ubanwa kike waya? Na ce da uban wa kike waya?"
Cikin kuka Hanifah tace
"Wallahi babu kowa Ammi"
Ina Ammi bata ma tsaya sauraronta ba ta cigaba da tsula mata wayar nan a jikinta.

Khaleel na kwance yana wasu ayyuka a laptop d'insa bacci ya fara surarsa, can cikin bacci ya jiyo kuka da ihu, a razane ya m'ike a tunaninsa ma ko mafarki yakeyi, sai da ya ji muryar Hanifah, zumbur ya mik'ke ya fito da gudu ganin ko lafiya?
Yana fitowa yaga aika aikar da Ammi keyi wa abar sonsa, da sauri ya k'araso ya tsaye a gaban Ammi yana fad'in.
"Ammi dake ni a madadinta, kalla kiga na fita k'wari Ammi"
Ammi tayi dariya ba shiri tace
"Kauce ko na had'a da kai Khaleel"
Ya'ki kaucewa dole Ammi ta dakata tana huci.
Jikin Hanifah yayi rud'u rud'u, abinka ga farin mutum!
Khaleel da k'walla taf idonsa yace
"Ammi meyayi zafi haka? Me tayi miki kikayi mata irin wannan duka haka?"
Ammi tace
"Khaleel Hanifah bataji, na rasa yadda zanyi da ita ta nutsu, duk yadda mutum yake da ita sai ta so ta 6ata masa rai haba!"
Khaleel ya sassauta murya yace
"Don Allah me tayi miki haka Ammi?"
Nan Ammi ta zayyano mishi abinda taji da kunnenta Hanifah nayi, Khaleel yayi shiru jikinsa yayi sanyi k'alau! Yace
"Hanifah bani wayarki"
Ba musu ta mik'a masa wayar ya shiga dubawa, amma kaf baiga komai ba, duk da baya da tabbacin ko gogewa tayi, amma ya duba babu lambar namiji sai shi da Saif, k'arewa ma batada lambar ko wane mahaluk'i sai su kad'ai, ya kalli Ammi yace
"Ammi anya da wani take waya? Banga lambar kowa ba a wayar"
Ammi ta harare shi tace
"To sarkin tausayi, ka manta wacece Hanifah ne?"
Sai kuma ta karkata kanta zuwa inda Hanifah ke kwance tana kuka sosai tace mata
"Daga yau koda wasa na k'ara kama ki kina waya da koma waye jikinki ne zai gaya miki"
Daga haka ta mik'e ta nufi d'akinta.

Ta dakinnata ya ya lek'a, a lokacin Halisa ta cikawa Hanifah ruwan zafi a bath ta sanya, wani magani ta d'iga mata mai yaji, ta dawo tace mata.
"Jeki gasa jikin ki ko zaki ji d'ad'i"
Hanifah wadda har lokacin kuka take, ta mik'e ta nufi toilet, Halisa ta fiddo mata doguwar riga ta material marar nauyi.
Ta dad'e a kwamin ruwan zafi na ratsa jikinta yana kuma rage zogi da rad'ad'i, bayan ta gama ta bud'e ruwan ya tafi, sannan ta tara wasu ruwan zafi tayi wanka da sabulu ta fito. Ta shafa mai a duka jikinta sannan ta sanya rigar da Halisa ta aje mata.
Halisa ta murza mata mantheleta a k'afufunta da hannunta inda bulalar da Ammi tayi mata ta kwanta, Khaleel ya kuma lek'owa yana kallonsu, sai ta bashi dariya, ya koma baya yayi dariya mai isarsa sannan ya shigo yana kallon Hanifah wacce idonta kamar an zuba yaji ko tarugu a ciki, ya sark'e hannayensa guda biyu tare yace.
"Haka kawai kinsa Ammi ta zabgar min ke?"
Hararasa tayi sannan ta kawar da fuskarta gefe, ya kai dubansa inda Halisa ke shafa mata a dogayen yatsunta na hannu, inda shatin ya tashi sosai, ya toshe bakinsa da hannu kada dariyar da yake rik'ewa ta fito, yace
"Hanifah ta Khaleel, kina zaman zamanki kin jawo wa kanki shan bulala, wai ke nan kina waya da sabon saurayinki da wani hancinki kamar tumaturi"
Sai da Halisa tayi dariya sosai har tana duk'ewa.
Haka yayi ta tsokanarta bata ce komai ba, cikin ran Hanifah kuwa cewa take
~<<"Nima dai waya kaini yin wayar k'arya a palo? Nima dai nayi wauta">>~


*****

Ana sauran sati biyu bikin su Khaleel Saif ya diro Nigeria, hidima tasha kansu duk basu zauna ba, Ammi na ta fama da jama'a, y'an uwanta na kusa da nesa duk sun zo, dama wad'anda ba'a samu kai masu katin gayya ba ta waya tasa Khaleel ya rubuta musu, gida ya cika tun ba'a soma sha'anin bikin ba, ga y'ayan y'an uwan Hanifah da k'awayenta suma duk sun fara zuwa. Su Khaleel baki har kunne, kullum cikin fara'a yake.
Dama lefe Saif ya hado wanda Khaleel ya dinga tura masa kudi yana siya a hankali, akwati shidda da d'an kit ya kawo, Ammi sun yaba masa da k'ok'arin da yayi, d'inki kuwa Ammi ce ta d'auki nauyin yin komai, tayi nata, Saif dana amarya da ango, sannan Halisa ma kala biyu aka yi mata.

Tun ana saura sati d'aya a fara biki aka soma jere a can gwamna road, gida ne flat mai d'akuna uku, palo biyu, kitchen da dinning area, tabbas Ammi tayi k'ok'ari don gidan ba k'aramin kyau yayi ba.
Kwakwata Hanifah bata nuna wata alama ta 6acin rai ko kuma ana tursasa ta ba, domin Ammi tayi mata warning mai tsoratarwa akan ta saki jiki ayi bikinnan lafiya, ba tare da wani tashin hankali ba.

Ranar asabar d'in k'arshe ta February dubban  jama'a suka shida auren KHALEEL DA HANIFAH, akan sadaki dubu hamsin, daga nan ango da tawagarsa suka zarce da walimar da Saif ya had'a a gidan saukar bak'i, a can unguwar jabi road!




      Ranar Dinner....!!!




MSB✍🏼

Monday 20 February 2017

KHALELL Page 25&26

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻25&26✍🏻✍🏻


Kai kawo yakeyi tsakanin dakinsa, abokinsa dake tsaye mai suna Fahad yace masa.
"Wai lafiya Deen? Meye haka?"
Ya dan dakata, sannan ya dunk'ule hannunsa ya naushi dayan yace.
"Ina yarinyar dana baka labari kwanaki?"
Fahad yace
"Wa kenan?"
Deen yace
"Yarinyar nan mana me sunanta ma?"
Ya dan tsaya kamar mai tunani, can kuma da sauri yace
"Hanifah!"
Fahad yace
"Oh! Nagane ta budurwarka da yayanta yayi maka duka saboda ka..."
Deen na huci yace
"Ya isa! Kar ka tuna min da mutumin nan, kasan me naji?"
Yace
"A'ah"
Deen yace
"Aure zatayi mana, yarinyar nan ni ta yaudara haka? Lallai batasan ko waye Zaharadeen ba"
Fahad yayi saurin katse sa.
"Yaudara kuma? Kana da bakin kiran wasu mayaudara, indai haka ne to kai me za'a kira ka kenan? Mata nawa ka yaudara? Mata nawa ka nuna kana sonsu daga baya ka yaudare su? Wallahi Deen kaji tsoron Allah, nasha fada maka hakan da kake bashida kyau..."
Deen yayi saurin daga masa hannu
"Da Allah dakata Fahad! Sheyasa ban cika sanya ka cikin harkoki na ba, da an fara magana sai ka sanyo min wa'azi, to dama kai nake tsoro ne da zakace min naji tsoron Allah, sheyasa nakeson Tboy da yana nan da ya bani shawara mai kyau, amma ba irin taka ba..."
Ya karasa yana huci da ka ganshi kaga tantirin dan duniya!
Fahad yayi murmushi mai ciwo yace
"Allah sarki! Ay daman nasan zakace haka, to kasani tunda ina tare da kai dole idan kayi ba daidai ba na fada maka gaskiya komai nacinta kana jina ko?"
Deen yace
"To baza'a dauki gaskiyar ba, idan ka isa ka sani naji, kuma wallahi kaj na rantse ko? To Sai na koya ma Hanifah hankali, da na fara nasara da cin ma burina akanta, amma lokaci guda 'dan iskan mijin da zata aura ya wargaza min plan dina"
Fahad abin ma ya bashi dariya saboda inda sabo sun saba haka dashi, indai akan gaskiya ne to Deen baji yake ba, amma tunda yana so Deen din ya shiryu sheyasa yake jure duk wani wulak'anci da zeyi masa. Don haka sai ya dafa Deen 'din yace
"Deen ka rabu da Hanifah, tunda dama bada niyyar aurenta ka fara nemanta ba, inda ma aurenta zakayi da sauki, wanda yake son aurenta zai aureta, it's high time ka nutsu, kaifa ba k'aramin yaro bane ba, yau da ace Abbanka nada rai da nasan bazaka dinga yin irin wadannan abubuwan ba..."
Deen ya furzar da iska da k'arfi yace.
"Fahad ya isa haka mana! Naji keep your wa'azi with you, am not interested, zan je na nemi Tboy shi ka'dai ne yasan shawarar da zai bani, amma kai kam banida lokacinka"
Daga haka ya fice tare da banko k'ofar dakin garam!
Fahad yayi murmushi yace
"Bazan gaji ba, insha Allah zaka dawo hanya madaidaiciya, Allah kabani ikon k'ara jurewa"
Yana fa'din haka ya fice daga d'akin yabi bayan Deen.



********


Wata ranar asabar da daddare duk suna zaune a palo ana kallo, Ammi ta mi'ke don ta fara jin bacci tace musu zata shiga d'aki ta kwanta.
Wurin ya rage daga Hanifah sai Khaleel, Khaleel ya kalli Hanifah yace
"Ya kamata ki rubuto abubuwan da kike buk'ata na hidimar biki ki bani, kinga lokacin sai matsowa yakeyi"
Tayi shiru, yace
"Wai badake nake magana?"
Tace
"Uhm"
Yace
"Ki ansa ni ba uhm ba"
Tace
"Ai naji kuma zan rubuto"
Yace
"Better, kiyi da wuri don ina so na fara rage abubuwa"
Ta kauda kanta zuwa kallon da takeyi. Cikin ranta tace
~<<"kai hidimar biki ta shafa sai wani rawar kai kakeyi">>~
Yayi murmushi yace
"Hanifah bani ruwa nasha please"
Wayyo kamar ta k'wala ihu takeji, mutumin nan ya takura mata a rayuwa.
Ya tamke fuska yace
"Dake fa nake"
Ta mike tana k'unk'uni, ta hade fuska kamar bata ta6a dariya ba, ta fice daga palon. Kitchen taje ta dauko masa ruwan roba na Swan da kofin glass, tana zuwa ta dire masa tayi hanyar waje sai wani cika take tana batsewa, k'iris ya rage ta fashe.
Sunanta ya kira, bata juyo ba amma ta dakata alamun taji kenan. Yayi dariya k'asa k'asa, sai kuma yayi saurin d'aure fuska yace.
"Dawo ki zuba min"
Tayi shiru still tana tsayen da take. Ya ce da dan k'arfi
"Ki dawo nace ki zuba min...!"
Ta dawo ta durk'kusa ta shiga bude ruwan. Kallonta yayi yanda idanunta suka kawo ruwa, sai kuma ta basa tausayi a ransa yace
"I'm sorry Hanifah, but i really have to do this, idan ba haka ba bazamu daidaita ba"
Saukar wani abu yaji a fiskansa daidai wurin hancinsa, ya runtse idanunsa, sai kuma ya bu'de, Hanifah ce tsaye tana 'kyal'kyaltar dariya. A razane yace
"Meye haka kika watsa min a fuska Hanifah?"
Ta dan 'daure tace
"Miyau na mana, wannan shine tukuicin k'aunar ka a gareni, wannan yana daga cikin abubuwan dana tanadar maka muddin ka bari mukayi aure, zaka wahala ne"
Yayi dariya
"Kina tunanin don kin sa min miyanki shine zanji haushi? Never Hanifah"
Sai kuma ya mi'ke tsaye yana fuskantarta.
"Son da nake miki bazai ta6a sa inji k'yamar miyanki ba baby, na gode da kika sa min ya k'ara min son da nake miki fiye da baya, kuma hakan ya k'ara min k'warin gwiwar cigaba da jiran ranar da zan mallake ki baby na"
Ta d'aure fuska a ranta tace
~<<"Maye kawai, naso yaji haushi gashi banyi nasara ba"~>>
Yayi murmushi yace
"Bari kiga wani abin mamaki"
Ya juya yayi dariya sanann ya juyo tare da watsa mata miyau a fuska, ita nata daidai bakinta, ta fasa ihu, ta shiga gogewa iya k'arfinta, ya kalle ta yace
"Gudumuwata ce nima, i love you so much Hanifah"
Yana gama fa'dan haka ya wuce yana murmushi yana fa'din.
"Hanifah kenan"
Ita kuwa da gudu tayi da'kinta tana kuka, toilet ta fad'a ta shiga wanke fuskarta ta soaps masu k'amshin dadi, a ranar da k'yar ta ta kasa bacci, data rufe ido sai ta tuna, wani irin haushi da tsanar Khaleel suka k'ara dirar mata lokaci daya, sannan kuma ta hau tunanin next move d'inta, ta mi'ke zaune daga kwancen da take tace
"Wallahi sai na rama don bazakaci bulus ba, sai na maka wanda yafi nawa!"


Kuyi hak'uri da wannan banda charge sai kuma anjima insha Allah....!❤️😌

MSB✍🏼

Sunday 19 February 2017

KHALEEL Page 23&24

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€





©PERFECT WRITERS FORUM
              (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻23&24✍🏻✍🏻


Ammi sai yamma ta dawo yadda tayi alkawari, a falo tayi kaci6us da Halisa tana dauke da kwanukan wanke wanke, tana ganin Ammi tayi saurin ajewa ta russina ta gaishe ta gami da yi mata sannu, Ammi ta amsa tana murmushi, sannan tace
"Ina mutan gidan? Naji gidan tsit"
Halisa tace
"Hanifah na dakinta, Khaleel kuma ya fita bayan sallar la'asar"
Tace
"To ga wannan a sanya fridge"
Halisa tace to tana mai amsar ledar daga hannun Ammi, sannan ta juya tayi kitchen.
Ammi ta nufi dakin Hanifah taji shi a rufe, ta kwankwasa, tazo ta bude, tana sanye da wata shirt ta polo pink color sai dogon wando baki wulik, ta matse gashin kanta daga tsakiya.
Ammi ta kalle ta tace
"Meye na rufe kofa da mukulli?"
Tace
"Haka nan"
Ammi tace
"To fito ki taya ni aiki, Gobe Halisa zata je ganin gida in ta tafi kuma dole ke zaki dinga taya ni, koma kiyi da kanki"
Tayi narai narai da idanu kamar zatayi kuka, tace
"Kai Ammi ni bana taya ki ne?"
Ammi ta galla mata harara tace
"Da yaushe kike taya ni? Kinga bana son dogon bayani muje kawai"
Ammi ta tasa ta gaba har kitchen tana cewa
"Idan ba Khaleel ba waye zai iya zama da ke, ga kuya ga shegen son jiki, bakida aiki sai kallo sai kuma karance karace litattafai, idan ma zaki gyara halinki tun wuri ki gyara kinji na gaya maki"
Ta rausaya da kai tace
"Kiyi hakuri Ammi"
Ammi tace
"Da anyi magana sai ki kwantar da kai kamar wata mutuniyar arziki, kina ma mutane kalar tausayi"
Tayi murmushi tace
"To Ammi kiyi hakuri dai"
Ta taimaka ma Ammi suka hada abincin dare mai rai da lafiya, suka jera kan dinning, sai zuba sauri take kar Khaleel ya dawo ya same ta a nan, dan halak din kuwa sai gashi kamar an jefo shi, ya shigo cikin takunshi na nutsuwa, ya shigo kitchen din.
Daga bakin kofa yaja ya tsaya yana kallonta kamar bai santa ba, sai kuma yayi gyaran murya yace
"Ammi me kuke dafa mana haka sai kamshi ke tashi a gidan, tun daga bakin kofa fa"
Tayi murmushi
"Duk naka ne Khaleel, nasan halinka da shiririta baka son ci abinci kwananan"
Yayi dariya kadan yana fadin
"Kin sangarta ni Ammi, kar fa na tafi inda banida gata inyi ta kewar ki..."
Tace
"Gashi kuwa Allah zai hada ka da makiwaciyar mata ya zakayi kenan?"
Ya dubi inda take tsaye, ta hade fuska kamar hadari sai wani hura hanci take.
Ya girgiza kansa yace
"Ya kuwa zanyi Ammi? A haka zanyi maneji (manage) ay, bahaushi yace da babu gwara"
Ta karasa masa
"Gara babu"
Hanifah bata tanka ba, ko inda yake bata kalla ba, ta kuma tsallake su zata wuce.
Ya sassauta murya, murya mai matukar sautin tausayi yace
"Kingani ko Ammi? Kingani zata koma daki ta kulle saboda aljaninta yazo"
Itama Ammi ranta babu dadi, tace
"Kar ka damu Khaleel, duk wani girman kan da takeyi zata aje shi ne tsab, kuma wallahi idan batayi a sannu ba sai na koya mata hankali"
Bai ce komai ba, ya shiga taya ta daukar coolers/warmers, har lokacin sallar magriba ta gabato, kai tsaye masallaci ya wuce don sauke farali.


*******

Bayan sallar isha'i Khaleel na tsakar tattara mahimman takardunsa da zai tafi dasu wurin daukar aiki gobe wayarsa ta fara ruri, ya dakatar da abinda yakeyi ya isa kan dressing mirror ya duba screen din wayar, ganin Saif yasa yayi murmushi gami da dagawa hade da yin sallama, Saif ya amsa yana dariya yace
"Yaya...!
Suka gaisa tare da tambayarsa karatu yace
"Alhamdulillah muna ta fama"
Khaleel yace
"Allah ya taimaka"
Yace
"Amin"
Saif ya gyara murya yace
"Yaya mutuniyar?"
Ya gane Hanifah yake nufi, Khaleel yace
"Alhamdulillah... "
Kamar ba Khaleel ba yadda muryarsa tayi kasa sosai, tabbas kowa da tasa kaddarar, in banda kaddara ma ace kamar Hanifah tana juya Khaleel son ranta?
Khaleel ya katse masa tunani yace
"Don Allah Saif a matsayinka na dan uwa na kuma kanina, na tabbata bazaka gaya min karya ba don inji dadi ba, kar ka 6oye min ka fito ga gaya min gaskiya tsakaninka da Allah, shin ina da wani aibu ko wani mummunar hali marar kyau ne da Hanifah ta kasa yarda ta so ni?"
Tausayin dan uwansa ya kama shi, yace
"Wallahi tallahi, kaji rantsuwar musulmi ko? Bakada ko daya daka lissafa min"
Saif ya runtse idanunsa tare da fito da sassanyar numfashi yace
"Ya Khaleel, shi So ba'a nan yake ba, kalli dai dan iskan yaron nan Deen da tace tana so, meya fika da shi? Amma tace tana sonsa, kawai dai Hanifah kanta na cikin duhu har yanzu, sannan tasan gaskiya take rufe ido ta take ta, wallahi yaya in banda kai ma da ka nace mata da nine kai da tuni na hakura da Hanifah, yarinya sai kace mai aljannu, haba!"
Ya karasa yana huci
Khaleel yayi murmushi mai sauti yace
"Kar ka damu Saif, yanzu idan har nace maka ina son wata mace a fadin duniyar nan, to nayi maka karya, Saif, So daban Kauna daban, ina kaunar Hanifah kuma zan cigaba har karshen rayuwata, ita wanda take ganin yana kaunar ta sonta yake hade da sha'awa, ta kasa ganewa, yanzu wahalarta mu kasance tare a matsayin ma'aurata, nidai a yanzu bazan tsaya ina lallashinta ba ta soni, ai sai ta raina ni"
Saif yayi dariya
"Ho! Ya khaleel! Son girma ko wane raini kuma tsakanin miji da mata?"
Khaleel yayi dariya, Saif ma dariyar yayi yace
"Kasan matsalar Hanifah? Batada nutsuwa, ma'ana taki nutsuwa ta fahimci ZAHIRIN KAUNAR da kake mata, ni na tabbata Hanifah tana sonka yaya, sai dai taki ta kwantar da hankalinta ta gane hakan, amma ina sa ran idan kukayi aure zata gane din, kasan mace da raini, sannan kasan halin mata basu iya nuna suna son namiji saboda sunanganin kamar zamu raina su, sunfi so namiji yafi nuna musu so fiye da yadda suke nunawa"
Khaleel yayi murmushi yana mamakin yadda akayi Saif yasan wadannan maganganun.
Haka sukayi sallama, zuciyar Khaleel babu dadi sam, ya ajiye wayar ya karasa hada takardunsa tsab.
Ya gama ya dan kishingida saman gado ya jawo wayarsa ya hau whatsapp, lambar Hanifah ya lalubo ya danna mata.
"Salam Beautiful"
A lokacin ta fito daga wanka tana taje gashinta taji shigowar message, ta dauka ta gane Khaleel ne sarai amma don ta kular da shi sai tayi masa reply da.
"Who is this please? Bansan mai number din ba"
Ya gyara kwanciyarsa yayi murmushi ya tura mata reply
"Kuma kina son sanin ko waye ko?"
Tace
"Yes of course mana!"
Da alama a kafule tayi masa reply din, yayi murmushi ya kai hannu cikin sumar gashinsa yana cakudewa, a yayinda numfashinsa ke harbawa da sauri sauri.
Ya dake ya kai hannu zaiyi reply amma sai yaji ya kasa, da kyar ya samu ya rubuta mata
"Ok"
Taga nema yake ya raina mata hankali sai ta kashe wayar gaba daya.

*****

Washe gari yayi wanka ya sanya wata orange  shirt mai ratsin baki, mai dogon hannu, da bakin bakin wando na jeans, ya taje sumarsa ta kwanta tayi luf luf, ya kammala shirinsa tsab, ya fito yana rataye da bakar jakar da mahimman takardunsa ke ciki, Ammi na palo, ya gaisheta, ta amsa tana murmushi, sun jima suna fira, daga karshe tayi masa fatan alkhairi da sa'a ya fito, motarsa ya tada, mai gadi ya bude masa gate ya fice.
Ammi tabi ta kofar dakin Hanifah, kamar kullum taji shi a rufe da mukulli, a zuciye ta shiga kwala mata kira.
"Amina! Ke Aminatu!!! Ki fito nan"
Tana budewa Ammi ta hau ta da masifa.
"Wai Hanifah wane irin hali ne da ke? Kashe kanki kike so kiyi? Ace mutum baida aiki sai zaman daki, gaba daya kin dena zama cikin mu ana firar arziki ina ma amfani?"
Bata amsa ba ta dai sunkuyar da kanta kasa
Ammai ta cigaba
"Ayi mutum sai shegen taurin kan tsiya da rashin tawwakali? So kike ki samu hawan jini haka kawai, me akayi miki? Yanzu ke Hanifah idan ma baki gode ma Allah ba,  bansan me zakiyi ba, ki dubi irin kaunar da Khaleel bawan Allah ke miki, ko wane irin wulakanci kikayi masa ya juri saboda yana sonki, duk wanda ya nuna yana son ka ay ya gama maka komai, to ki bude kunnenki da kyau kiji, auren da bakiso sai anyi shi, ko zaku mutu kuwa, in banda ma Khaleel din da ya nace ina zai kai halinki da bakar zuciyar nan taki, to idan kin ga dama ki gyara nidai na fita hakkinki"
Daga haka ta wuce ta barta nan tsaye, ta dade kafin ta koma daki ta haye gado ta fara kuka.
Khaleel yayi interview dinsa, sunce zasu neme shi idan lokaci yayi.
Bai tsaya ko ina ba, gida ya zarce yana cike da farin ciki.



MSB✍🏼

Saturday 18 February 2017

KHALEEL Page 21&22

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥


©PERFECT WRITERS FORUM
                (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻21&22✍🏻✍🏻


Washe gari koda Ammi ta kula da Hanifah tayi kuka sai kawai ta shareta ta cigaba da sabgoginta, zuwa yanzu abin nata ya zama rainin hankali, bayan sunyi kalaci da safe Ammi ta sauko cikin shiri da alama fita zatayi, Halisa ta iske a kitchen tana wanke cooker ta shaida mata zata je wata barka ta dora girkin rana, zata kai yamma bata dawo ba.
Haka ta sauko ko kula Hanifah batayi ba da ke zaune kan dinning tana hada tea, a bakin kofa ta hadu da Khaleel yana sanye da gajeren wando da riga marar hannu da alama jogging yaje, dama duk safiya ya kan fita yayi exercise, ya gaida Ammi yana murmushi yace
"Fita zakiyi Ammi?"
Tace
"Eh zan fita ne direba zai aje ni anjima zaizo ya daukeni"
Yace
"Ko na zo na kaiki?"
Tace
"A'a kayi zamanka Khaleel"
Yace
"To a dawo lafiya Ammi, dama nace zan siya ma Hanifah waya tunda waccan da na siya mata Saif ya ansa yana amfani da ita"
Ammi tayi shiru kamar mai tunani tace
"Anya Khaleel ka siya mata waya kuwa? Baka gudun ta koma tana waya da wannan tsohon saurayin nata?"
Yace
"Bazatayi ba Ammi, don zansa ido sosai insha Allah, gara a bata wayar saboda zama haka nan bai da dadi, don kinga yanzu ba makaranta take zuwa ba sannan kuma sai next year zata sake zana jamb ko"
Ammi ta girgiza kanta tace
"Shikenan amma don Allah kar kaje ka siyo mata irin masu tsadar nan wanda idan yaro yana rike irinsu sai ya dinga daukar kansa wata tsiya"
Khaleel yayi murmushi
"Insha Allah"
Daga haka sukayi sallama ta wuce mota shi kuma ya shige ciki, Hanifah na nan inda Ammi ta barta tana zaune kurum, ganin Khaleel zai wuce yasa ta hade rai tare da juya fuskarta gefe, murmushi yayi kawai ya wuce yana kallonta, kallon da yake mata ya sanya ta sakin tsaki mai kara har sai da Khaleel ya ji, ya juyo ya kalle ta sai bai nuna yaji ba sai ma yace mata
"Yan mata aje ayi wanka zamu fita"
Ta kalle shi tare da yi masa harara sannan tace
"Bazani ba"
Yana dariya yace
"Saboda me?"
Tace
"Bansani ba"
Yace
"To tunda baki sani ba kije ki shirya zamu fita"
Wannan karon sai baiyi dariya ba, ya daure fuska don ma kar ta dauki abin wasa.
Ta kalle shi haushi duk ya turnike ta tace
"Naji"
Yace
"Good girl"

Minti talatin ya shirya cikin wani dan karan yadi ruwan toka mai matukar santsi ta taushi, kamshi duk ya gauraye palon, tsaye yake bakin kofa hannunsa daya cikin aljihu, dayan kuma yana latsa wayarsa, ya gaji da jiranta hakan ya sa ya dawo saman kujera tare da kunne tv, ya sani sarai da gangan taki fitowa da wuri don dai yaji haushi, yayi dariya mai sauti yace
"Hanifah kenan"
Sai da ta kara 6ata akalla wata minti ashirin din sannan ta fito cikin doguwar hijabin da ta kusa kai mata kasa, kana hango dagon wando kalar baki ta kasan hijabin, fuskarta kuwa kamar an mata wahayi da gidan wuta, ko kallonsa batayi ba ta fice waje don bazata iya koda yi masa magana ba, girgiza kansa yayi tare da mikewa tsaye, ya kashe tv din da wutar gidan, sannan yasa key ya kulle gidan, sarai ta san ya hana ta zaman baya sheyasa ma ta bude gidan gaba ta zauna tana kallon taga, tana jin sadda ya bude kofar motar ya shigo amma bata ko kalle shi ba, shima kuma bai yi magana ba har ya murza key ya tada motar, sai da suka harba titi sannan ya kara gudu kadan.

 A tare suka jera cikin mall din, shima sai da yayi da gaske dan cewa tayi bazata shigo ba, kansa tsaye wurin saida electronics suka shiga, ita dai binsa kawai take da ido, wurin saida wayoyi taga sun tsaya, ya kalle ta yana murmushi yace
"Gimbiyata, gafa wayoyi nan ki za6i wadda tayi miki"
Ta daure fuska
"Wacece gimbiyarka?"
Yace
"Ke mana"
Ta harare shi tace
"Allah ya sauwake min na zama gimbiyarka"
Yayi dariya mai bayyana hakora yace
"To naji, ke gimbiyar wacece?"
Tace
"Ya Khaleel wai meye baka ne? Baka ganin cikin mutane muke?"
Yace
"Ina ruwana dasu, ni ke kadai nake gani"
Tayi tsaki
Yace
"Yanzu dai ki za6a da wuri idan ba haka ba zan cigaba da kiranki sunaye masu sanyaya zuciya"
Ta kalle shi tace
"Wai waye zai siya min waya?"
Yace
"Ina ruwanki? Kedai ki dauka mu tafi"
Tace
"Banso gaskiya"
Ya kyalkyale da dariya yace
"So kike idanu su dawo kanmu kenan?"
Tayi shiru cike da jin haushi, ta fara dubawa, can taci karo da wata waya fara kal mai suna HTC, ta nuna wayar, Khaleel yayi murmushi yasa aka ciro wayar yana dubawa a tsanake.
Ya kalleta yace
"Wannan tayi miki?"
Ta girgiza kanta a hankali.
Ya biya kudin wayar, har cover mai kyau ya siya mata, sannan ya biya ya siya mata kayan sawa, suka fito, basu dawo gida ba sai da ya tsaya ya siya mata layin MTN, sannan suka wuce gida, yana yin pakin ta fito da sauri tayi ciki, yayi murmushi bayan ya fito da ledar wayarta, yana zuwa ya iske ta bakin kofa tsaye, saboda mukullin gidan na hannunsa, yayi dariya ciki ciki, yana zuwa ya kalleta tare da sakar mata murmushi, ya bude gidan ya shige abinsa sannan tabi bayansa.
Dakinsa ya wuce ya jona mata charge, sannan ya shiga bayi don ya watsa ruwa.

Saida wayar ta cika sannan ya ciro harda charger din gaba daya, ya sanya mata lambar Ammi, data Saif, sannan ya sanya masa tata tare da saving sunansa don yasan ko ya sanya wani sunan chanja shi zatayi. Ya dauki tata sanann ya tura ma su Saif cewar wayar Hanifah ce.

Ya fito a lokacin tana kitchen tana dafa indomie, daga bakin kofa ya tsaya yana kallonta, sannan yayi sallama, ta amsa masa ciki ciki, ya matso dab da ita yace
"Ga wayarki nan"
Bata kalle shi ba tace
"Nagode"
Yaji dadin hakan, ya aje mata sannan ya fice, ta kura masa ido har ya 6ace sannan ta saki tsaki kadan tace.
"Zaka gane kurenka, wallahi sai ka gwammace dama baka sanni ba, sai kayi dana sanin aurena, na maka wanann alkwarin"
Ta karasa dafa indomie ta fito ta zauna kan dinning ta fara ci.
Wayar ta dauko tana juyawa tana murmushin da ita kadai tasan manufarsa.



MSB✍🏼

KHALEEL Page 21&22

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥


©PERFECT WRITERS FORUM
                (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻21&22✍🏻✍🏻


Washe gari koda Ammi ta kula da Hanifah tayi kuka sai kawai ta shareta ta cigaba da sabgoginta, zuwa yanzu abin nata ya zama rainin hankali, bayan sunyi kalaci da safe Ammi ta sauko cikin shiri da alama fita zatayi, Halisa ta iske a kitchen tana wanke cooker ta shaida mata zata je wata barka ta dora girkin rana, zata kai yamma bata dawo ba.
Haka ta sauko ko kula Hanifah batayi ba da ke zaune kan dinning tana hada tea, a bakin kofa ta hadu da Khaleel yana sanye da gajeren wando da riga marar hannu da alama jogging yaje, dama duk safiya ya kan fita yayi exercise, ya gaida Ammi yana murmushi yace
"Fita zakiyi Ammi?"
Tace
"Eh zan fita ne direba zai aje ni anjima zaizo ya daukeni"
Yace
"Ko na zo na kaiki?"
Tace
"A'a kayi zamanka Khaleel"
Yace
"To a dawo lafiya Ammi, dama nace zan siya ma Hanifah waya tunda waccan da na siya mata Saif ya ansa yana amfani da ita"
Ammi tayi shiru kamar mai tunani tace
"Anya Khaleel ka siya mata waya kuwa? Baka gudun ta koma tana waya da wannan tsohon saurayin nata?"
Yace
"Bazatayi ba Ammi, don zansa ido sosai insha Allah, gara a bata wayar saboda zama haka nan bai da dadi, don kinga yanzu ba makaranta take zuwa ba sannan kuma sai next year zata sake zana jamb ko"
Ammi ta girgiza kanta tace
"Shikenan amma don Allah kar kaje ka siyo mata irin masu tsadar nan wanda idan yaro yana rike irinsu sai ya dinga daukar kansa wata tsiya"
Khaleel yayi murmushi
"Insha Allah"
Daga haka sukayi sallama ta wuce mota shi kuma ya shige ciki, Hanifah na nan inda Ammi ta barta tana zaune kurum, ganin Khaleel zai wuce yasa ta hade rai tare da juya fuskarta gefe, murmushi yayi kawai ya wuce yana kallonta, kallon da yake mata ya sanya ta sakin tsaki mai kara har sai da Khaleel ya ji, ya juyo ya kalle ta sai bai nuna yaji ba sai ma yace mata
"Yan mata aje ayi wanka zamu fita"
Ta kalle shi tare da yi masa harara sannan tace
"Bazani ba"
Yana dariya yace
"Saboda me?"
Tace
"Bansani ba"
Yace
"To tunda baki sani ba kije ki shirya zamu fita"
Wannan karon sai baiyi dariya ba, ya daure fuska don ma kar ta dauki abin wasa.
Ta kalle shi haushi duk ya turnike ta tace
"Naji"
Yace
"Good girl"

Minti talatin ya shirya cikin wani dan karan yadi ruwan toka mai matukar santsi ta taushi, kamshi duk ya gauraye palon, tsaye yake bakin kofa hannunsa daya cikin aljihu, dayan kuma yana latsa wayarsa, ya gaji da jiranta hakan ya sa ya dawo saman kujera tare da kunne tv, ya sani sarai da gangan taki fitowa da wuri don dai yaji haushi, yayi dariya mai sauti yace
"Hanifah kenan"
Sai da ta kara 6ata akalla wata minti ashirin din sannan ta fito cikin doguwar hijabin da ta kusa kai mata kasa, kana hango dagon wando kalar baki ta kasan hijabin, fuskarta kuwa kamar an mata wahayi da gidan wuta, ko kallonsa batayi ba ta fice waje don bazata iya koda yi masa magana ba, girgiza kansa yayi tare da mikewa tsaye, ya kashe tv din da wutar gidan, sannan yasa key ya kulle gidan, sarai ta san ya hana ta zaman baya sheyasa ma ta bude gidan gaba ta zauna tana kallon taga, tana jin sadda ya bude kofar motar ya shigo amma bata ko kalle shi ba, shima kuma bai yi magana ba har ya murza key ya tada motar, sai da suka harba titi sannan ya kara gudu kadan.

 A tare suka jera cikin mall din, shima sai da yayi da gaske dan cewa tayi bazata shigo ba, kansa tsaye wurin saida electronics suka shiga, ita dai binsa kawai take da ido, wurin saida wayoyi taga sun tsaya, ya kalle ta yana murmushi yace
"Gimbiyata, gafa wayoyi nan ki za6i wadda tayi miki"
Ta daure fuska
"Wacece gimbiyarka?"
Yace
"Ke mana"
Ta harare shi tace
"Allah ya sauwake min na zama gimbiyarka"
Yayi dariya mai bayyana hakora yace
"To naji, ke gimbiyar wacece?"
Tace
"Ya Khaleel wai meye baka ne? Baka ganin cikin mutane muke?"
Yace
"Ina ruwana dasu, ni ke kadai nake gani"
Tayi tsaki
Yace
"Yanzu dai ki za6a da wuri idan ba haka ba zan cigaba da kiranki sunaye masu sanyaya zuciya"
Ta kalle shi tace
"Wai waye zai siya min waya?"
Yace
"Ina ruwanki? Kedai ki dauka mu tafi"
Tace
"Banso gaskiya"
Ya kyalkyale da dariya yace
"So kike idanu su dawo kanmu kenan?"
Tayi shiru cike da jin haushi, ta fara dubawa, can taci karo da wata waya fara kal mai suna HTC, ta nuna wayar, Khaleel yayi murmushi yasa aka ciro wayar yana dubawa a tsanake.
Ya kalleta yace
"Wannan tayi miki?"
Ta girgiza kanta a hankali.
Ya biya kudin wayar, har cover mai kyau ya siya mata, sannan ya biya ya siya mata kayan sawa, suka fito, basu dawo gida ba sai da ya tsaya ya siya mata layin MTN, sannan suka wuce gida, yana yin pakin ta fito da sauri tayi ciki, yayi murmushi bayan ya fito da ledar wayarta, yana zuwa ya iske ta bakin kofa tsaye, saboda mukullin gidan na hannunsa, yayi dariya ciki ciki, yana zuwa ya kalleta tare da sakar mata murmushi, ya bude gidan ya shige abinsa sannan tabi bayansa.
Dakinsa ya wuce ya jona mata charge, sannan ya shiga bayi don ya watsa ruwa.

Saida wayar ta cika sannan ya ciro harda charger din gaba daya, ya sanya mata lambar Ammi, data Saif, sannan ya sanya masa tata tare da saving sunansa don yasan ko ya sanya wani sunan chanja shi zatayi. Ya dauki tata sanann ya tura ma su Saif cewar wayar Hanifah ce.

Ya fito a lokacin tana kitchen tana dafa indomie, daga bakin kofa ya tsaya yana kallonta, sannan yayi sallama, ta amsa masa ciki ciki, ya matso dab da ita yace
"Ga wayarki nan"
Bata kalle shi ba tace
"Nagode"
Yaji dadin hakan, ya aje mata sannan ya fice, ta kura masa ido har ya 6ace sannan ta saki tsaki kadan tace.
"Zaka gane kurenka, wallahi sai ka gwammace dama baka sanni ba, sai kayi dana sanin aurena, na maka wanann alkwarin"
Ta karasa dafa indomie ta fito ta zauna kan dinning ta fara ci.
Wayar ta dauko tana juyawa tana murmushin da ita kadai tasan manufarsa.



MSB✍🏼

KHALEEL 19&20

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€



©PERFECT WRITERS FORUM (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻19&20✍🏻✍🏻


Ammi ta dawo hannunta dauke da katon tray, fuskarta dauke da murmushi tace.
"What a surprise? Ban yi tsammanin ganinka yanzu ba Khaleel, meyasa baka sanar dani zaka zo ba?"
Ya dan sosa keya yana dariya
"Wallahi Ammi tafiyar ce nayi ta ba shiri, kawai naji hankalina yayi gida, sannan kuma ai kinsan mun gama tun last week ban dai taho din bane"
Tayi murmushi
"Allah sarki, ai gida daban ne, kuma Allah ya sa anyi sa'a
Yace
"Amin, wallahi Ammi nayi missing girkinki yadda baki tsammani wallahi manegi {manage} nakeyi a can, sai muyi ta fama da na gwangwani"
Tace
"Khaleel kenan, nima nayi kewarka sosai"
Ammi ta aje tray din a gabansa ta shiga zuba masa lemon kwali (exotic), da ka kalle ta kasan tana cikin farin ciki marar misaltuwa, shi kuwa kallonta yakeyi zuciyarsa fes!

Halisa ta shiga dakin Hanifah da kayan guga da aka goge na Hanifah din ta tarar da ita tana sanya kayan bacci, da alama kwanciya zatayi.
Ta girgiza kai kurum ta bude wardrobe dinta tana jera mata kayanta ciki, ta dan dakata da sanya kayan tace.
"Wai nikam Hanifah bakiga yayanki yazo ba? Ai ko yar fira basai kije ki taya sa ba?"
Tayi tsaki a hankali tace
"Banida lokaci"
Halisa ta girgiza kanta ta karasa sanya kayan tare da kulle wardrobe din ta fito.

Tunda Khaleel yazo Hanifah bata fito daga daki ba, a takaice dai yau kwanansa hudu da dawowa amma Hanifah bata fitowa daga daki,
Zuwa yanzu ya kara yarda kiyayyar da Hanifah ke masa a cikin jininta take bata sonsa.
Idan har yana yi mata uzuri a da yanzu fa? Shekaruta goma sha bakwai ta isa ta fara bambance abinda takeso da wanda bataso, basai an tursasa ta ba, shi inda a son ransa ne da Ammi ta bari ta za6esa da kanta baya so ayi mata dole don muddin akayi aurennan akwai matsala.

Washe gari yana dakin Ammi suna fira tace
"In banda shirmen Hanifah da kuruciya ga dan uwanki na jini, wanda yasan darajarki da mutuncinki da kuma ciwonki, amman kirkiri ki nuna bakya sonsa"
Khaleel yayi tsai yana kallonta a nitse, duk da maganar Ammi ta ta6a masa zuciya amma sai ya dake tare da kakalo murmushi yace
"Ammi idan har Hanifah tana da wanda takeso ni sai inga hada mu aure bashida wani amfani..."
Ammi ta katse sa tare da cewa
"Kul na kuma jin kace haka Khaleel, hadin aurenka da Hanifah babu abinda ya kaishi amfani a wurina, da in dauke ta in bada ita ga wani can wanda bansan halinsa ba, gwara kai din da nasani, badai ka kammala karatunka ba, aikin ne kuma shima muna nan muna addu'a, ita kuma ta kammala karatunta na secondary to me ya rage? To bari ma kaji karshen zancen na kira yaya Hamza( yayan Ammi dake zaune a kano) na fada masa zancen auren naku, shima kuma yayi farin ciki sosai da hakan, ya sanar da ni karshen satin nan zasu zo ayi maganar auren naku in ta kama ma a sanya rana za'a sanya a ranar"
Ya rasa me zaiyi farin ciki ko kuwa akasin haka? Nan 6angaren yana fama da soyayyar Hanifah wanda burinsa yaga ya mallake ta, dayan 6abgaren kuwa tsanar da take nuna masa shi yake karya masa gwiwa.


******


Cikin ikon Allah kafin karshen satin takardar list din daukar ma'akaita ta iso ta cikin email dinsa, bai bude ba da wuri ba kasancewar tunda sassafe sakon ya shigo a lokacin kuma bacci yake, sai bayan ya tashi wauraren goman dare yayi arba da sakon, sunanshi ya shiga nema aiko shine layi na biyu a cikin list din, Parah-urbankonsuit-sabon_gari-kaduna, farin cikin da yaji baya misaltuwa, gashi yana tunanin yana kusa da gida baiyi nisa ba, lambar wayarsu suka sanya take ya kira, bugu uku suka dauka, ya sanar masu ya ga sunansa a list din daukar ma'aikata, suka ce masa eh zaizo interview ranar monday, yayi farin cikin sosai, take ya fita don sanar ma Ammi itama tayi farin ciki sosai ta sanya masa albarka, banda Hanifah da ko kallo bai ishe ta, bare ma yasa ran zata sa baki itama, wani mugun kallo Ammi ta watsa mata ba shiri tace.
"Congrats Allah sa alkhairi"
Yayi yalwataccen murmushi yace
"Amin lil sis godiya nake"
Harara ta watsa masa sannan ta tashi tayi dakinta da sauri.


*******

Karfe sha biyun ranar asabar su Yaya Hamza suka iso da shi da kaninsa mai suna Aliyu, dama su kadai ne yan uwan Ammi ita kadai ce mace, sai wani kawunsu wanda shine ya jagoranci tafiyar, bayan an kawo musu ruwa da abinci sunci, nan kuma aka soma tattaunawa da shawarwarin yadda za'a gudanar da shiirin bikin, karshe dai aka tsaida rana wata biyu masu zuwa, a ranar Hanifah batayi bacci ba, taci burin auren Deen wanda shi take so, amma Khaleel yayi mata katanga da hakan, ranar tayi masa Allah ya isa tafi a kirga, sannan tasa kuka, bata rintsa ba har garin Alalh ya waye.


MSB✍🏼

Thursday 16 February 2017

KHALEEL Page 17&18

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€




 ®TALENTED WRITER'S GROUP(TWG)✍🏻
©PERFECT WRITERS FORUM (P.W.F)❤️

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


This page is dedicated to all my fans, nagode da kaunar book dinnan da kukeyi much love 😍❤️


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻17&18✍🏻✍🏻


Hanifah tana kuka tana ba Saif hakuri, amma ina bai ma san tanayi ba, don ya riga yayi mugun fushi, Saif nada hakuri amma idan ransa ya 6aci ba kyau.
Kwarai tayi dana sanin abinda Deen yayi mata,
Sai dai ko kadan bataji ta tsane sa ba, tun daga bakin kofa kukan Hanifah ya karu, tana tsoron haduwarta da Ammi, tasan idan taji kashinta ya bushe. Da Khaleel suka fara cin karo ya fito da alama fita yake shirin yi, ganin haka ya rude yana tambayar abinda ya sami Hanifah haka, cikin fushi Saif yace.
"Bar yar iskar nan mana..."
"Subhanalillah! Haba Saif dena ce mata yar iska mana"
Cewar Khaleel a dan rude.
Saif yana huci yace
"Bakasan me tayi bane ba da baka ce komai ba..."
"Me tayi haka Saif? Meyafaru?"
Cewar Ammi tana karasowa a rude.
Saif ya soma basu labarin abinda ya ga Deen nayi mata a mota, salati Ammi tasa tana tafa hannuwanta, a yayinda da Khaleel yayi mutuwar tsaye, ga wani irin mugun kishi da yaji yana taso masa lokaci guda, kasa tsayuwa yayi ya koma baya ya zube kan kujera dafe da kai.
Saif na shirin kai ma Hanifah bugu da wayar
Cd Ammi tayi saurin hana sa, itama kanta ranta yayi mugun 6aci. Tace
"Kar kayi saurin bugunta Saif, ka barni da ita kawai idan tasan wata ai batasan wata ba"
Hanifah cikin murya kuka tace
"Kiyi hakuri Ammi na tuba bazan sake ba..."
Ammi ta doke mata baki tace
"Taso ki biyo ni"
Ta mike da kyar tana shasheka tana share hawayen fuskarta tabi bayan Ammi, kan kujera Ammi ta zauna, Hanifah da Saif suka zauna kasa. Khaleel ma a hankali ya zamo kasa ya kasa koda kwakwaran motsi.
Ammi ta numfasa tace
"Hanifah"
Ta dago da jajayen idanunta tace
"Na'am"
Ammi ta cigaba
"Keda waye Saif ya gani a mota?"
Tayi shiru
Ammi ta daka mata tsawa
"Nace waye?!"
Tace
"Deen sunansa, ya...yace yana so...na"
Da mamaki Ammi tace
"Saurayinki ne kenan?"
Bako kunya ta gyada kai a hankali tana zubda ruwan hawaye.
Khaleel ji yake kamar kirjinsa zai huje tsabar kishi, lallai Hanifah bata kaunata. Ya fada cikin ransa.
Ammi tace
"To kinyi daidai, amma idan kina tunanin auren wancan dan iskan bada yawu na ba, kin ta6a ganin saurayin arziki yana ta6a budurwarsa ba tare da an daura aure ba, wallahi dama da kinga irin haka to ba don Allah suke son mutum ba, yanzu ba islamiyya muka tura ki ba ? Dama ba zuwa kike ba Hanifah?"
Tayi shiru
"Kinsan Allah tun wuri dama ki fidda shi daga cikin ranki, don na yanke shawarar aura miki da uwanki dana yarda da shi Khaleel, zan fi samu kwanciyar hankali da nutsuwa idan shi ya aure ki, dama an dade ana 6oye miki kuma Saif ya sanar dani cewar shi da kansa Khaleel ya sanar da ke dangantar ku, to kinji kisa a ranki bakida miji sama da Khaleel..."
"Don Allah Ammi kar ki...." Cewar Khaleel
Ammi ta daga masa hannu
"Bana son jin komai daga gareka Khaleel, na riga na yanke hukunci kuma banida niyyar janyewa"
Daga haka ta mike tayi ciki, Hanifah kuka take na fitar rai, kafin ta tashi tayi dakinta da gudu tana kuka sosai.
Saif kuwa wani murmushin farin ciki yayi a yayinda Khaleel ya dafe kai, yana jin wani iri. Saif ya dafa shi, ya dago da idanunsa da suka kada sukayi ja. Saif yace
"Kar ka karaya yaya..."
Khaleel yace
"Ban karaya ba Saif, duk abinda Hanifah keyi yarinta ke dibar ta, nan gaba ko ance tayi bazatayi ba, amma kasan Allah banso Ammi ta yanke wannan hukunci ba haka da sauri ba"
Saif yayi murmushi
"Nikam na so hakan kuma naji dadi"
Khaleel yace
"Kayya Saif, Hanifah bata sona ko kadan"
Saif yayi murmushinsa mai kyau yace
"Zataso ka ne nan gaba, bakiji bature na cewa time heels ba?"
Khaleel yace
"Haka ne, Allah ya za6a mana abinda yafi alkhairi"
Saif yace
"Ko kaifa yaya, haka ya kamata kace, yaushe zaka tafi masters?"
Ya gyara zama yace
"Ina sa ran nan da sati biyu insha Allah"
Saif yace
"Allah ya kaimu"
Yace
"Amin"
Tare suka mike suka fice daga gidan gaba daya.



*******


A karshen wata takardar admission nashi ta kuma fitowa ta cikin email suka aiko mashi, inda yayi applying ya samu kuma, kuma a lokacin, kowa ya taya Khaleel murna banda Hanifah da ko digon farin ciki babu a digon farin ciki a cikin ranta, Shima kuma ya share ta saboda baya so yana yawan matsa mata, ya dan bata space.
Khaleel ya soma karatunsa cikin kwanciyar hankali.
Ita kuwa Hanifah tuni ta maida hankali kan karatunta kasancewar sun kusa fara zana jarabawarsu ta karshe, tun faruwar wannan abu bata kara ganin Deen ba, abin yana damunta sosai, ga koda wasa Ammi ta dena bata wayarta ba halin kuma ta kirashi taji ko lafiya.
Sannan yanzu ko Khaleel ya kira Ammi bai cika tambayar Hanifah ba kamar da, kuma bai cewa a bashi ita su gaisa, sai dai kawai yace a gaishe ta, banda haka ma abubuwa sun mashi yawa, karatu yakeyi bana wasa ba, ya kyaleta har lokacin da yake ganin ta mallaki hankalin kanta, itama ta soma fahimtar cewa Khaleel din ya share ta ba kadan ba, kenan yana nufin fushi yakeyi da ita?


*******



SOME TIME LATER! (Bayan wani lokaci)


A cikin jerinn masu saukowa daga matattakalar jirgi ciki harda Architect Khaleel  Usman, sanye yake da jibgegiyar dark blue din coat har gwiwa, idanunsa cikin bakin space, ya sanya dogon wando baki, saukarsu kenan a airpot din Ireland inda a yawancin passengers din a nan zasu sauka, sannan kuma a sake lodi masu tashi zuwa Nigeria.
Khaleel bai sanar da kowa zaizo ba.

Ammi na kicin itada Halisa suna fama da girki suka jiyo muryar mai gadi yana ma Khaleel sannu da zuwa. Da sauri ta fito adaidai lokacin da Yusuf mai gadi yake aje manyan manyan jikuna da Khaleel din yazo dasu
Yar mulkin na kwance a falo kan kujera da littafi a hannunta, wani irin sanyin kamshi da mutum daya tasani dashi a duniya, turarensa da yake so, a lokacin ya russuna daidai saitinta ya zare littafin.
Ta dago tana kare masa kallo da idanuwanta da suka kawo ruwa, don a ganinta mai takurawa rayuwarta ya dawo, shi kuwa murmushi yayi yadda Hanifah ta kara girma, ta kara kyau, Tsawo, da gogewa a tsayin watanni goma da yayi bai ganta ba, baiji muryarta ba.
Ammi ta shigo tana kallonsu, basu san ta shigo ba sai kawai ta koma kicin tana hamdallah, bata ta6a ganin miji da macen da suka dace da juna ba irin KHALEEL da HANIFAH ba, gashi dai kamar su daya haske kawai ya dan fita, Hanifah ce ta fara kauda tata fuskar sannan ta hade fuska kamar bata ta6a dariya ba ko sannu da zuwa da take mishi da, yau bai samu ba, karshe ma mikewa tayi ta bar masa falon.
Yayi dariya ganin yadda take hade rai kiris take jira ta fashe.






MSB✍🏼

Tuesday 14 February 2017

KHALEEL page 15&16

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€



 ®TALENTED WRITER'S GROUP(TWG)✍🏻


Dedicated to Cutie, Tafisuu, Xara bb, T.j auta, Faty Batagarawa, Sumy, Chuchu dear, Zainab Omar, Dainty, Ayusher, Zee bee, Xarah muhd, Suby and my pals Kiddies frnds forever one love ❤️😍❤️ {Ban manta da ku ba members na Hausa novels thanks for the love}😍😍😍

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻15&16✍🏻✍🏻


Kwakwasa kofar yayi hade da sallama, a razane ta mike zumbur gabanta na dukan tara tara, idanuwanta a waje alamar tsoro, tace
"Wa... waye?"
Yace
"Hanifa nine kizo ina son magana da ke"
Ta ce
"To" bayan ta kashe wayar da sauri ta dauko hijabinta da ta gama sallar isha'i ta fito, yana tsaye bakin kofar dakinta ya kalle ta yace
"Ina babban falo, ki zo ki same ni"
Bata tanka ba, sai ma harara da ta watsa masa bayan ya juya, sai da ya shiga falon tace
"Ko wace jarabar kuma zai kwaso min?"
Dakin Ammi ta fara shiga, bata dakin amma taji alamun watsa ruwa, hakan ya tabbatar mata da wanka take, sai kawai ta aje mata kan drawer ta kullo mata dakin ta wuce kiran Khaleel, sallama tayi ya amsa yana murmushi yace.
"Zo ki zauna mana"
Ba musu ta zauna dan nesa da shi. Ya numfasa yace
"Hanifah"
Bata amsa ba amma ta dago tana dubansa. Bai damu ba ya cigaba da magana.
"Akwai wani al'amari mai girma da bakisan dashi ba, ina ganin lokaci yayi da ya kamata ki sani"
Gabanta ya fadi uhm kawai tace
Yayi shiru ya rasa ta ina zai fara ma. Karfin hali yayi yace.
"Hanifah, a yadda kika dauke ni a matsayin yayanki ciki daya ba haka maganar take ba, ni ba Ammi ce haife ni ba, illa dai da mahaifinki da mahaifina sune suka fito a ciki daya"
A razane ta dago tana zubansa cikin rashin fahimta tace
"Ban...gane ba"
Yace "ma'ana dai ni cousin dinki ne, Hanifah ina so kisani ba tun yau ba nake miki son da bazaki ta6a iya sani ba, tun kina jaririyarki har kawo yanzu, don Allah Hanifah kar ki watsa min kasa a ido ki amshi kokon barata kar kice zaki juya min baya, kar ki kini zan iya rasa rayuwata"
Tunda ya fara magana take shatatar hawaye, jikinta har wani 6ari yakeyi, a hankali ta zamo daga kan kujera ta zube kasa tana cigaba da kuka, ganin haka yasa hankalin Khaleel ya tashi matuka, ba abinda yake ambato sai innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yace
"Nasan baki sona tun bakisan ainahin alakar mu da ke ba..."
Bata san lokacin da tace
"Dan Allah ya Khaleel ya isa haka! Kasheni kakeso kayi ne? Na roke ka kar kace zakayi min dole wallahi bana sonka, bana kaunar ka, nagode da fada min dangantakar mu da kayi, dama na dade ina ji a jikina akwai wani 6oyayen al'amarin da ba'a sanar da ni ba, ya Khaleel ina ganin girmanka to ka kama shi tun kafin ya zube kasa"
Da mamaki yake kallonta
"Hanifah yau ni kike fada ma magana haka? Menene laifina don nace ina sonki Hanifah?"
Bata tanka ba ta kara fashewa da kuka sosai.
Khaleel ya mike jikinsa yayi mugun sanyi yace
"Wallahi bazan ta6a miki dole ba Hanifah, zan baki lokaci kiyi shawara, idan kikace bakisona na miki alkawarin bazan tilaska ki ba, amma kisani bazan ta6a dena sonki ba"
Daga haka ya fice daga falon idanunsa sun kada sunyi ja! Dama abinda yake gudu kenan, gashi nan ya riga faru, ya yadda ya amince Hanifah bata kaunarsa, amma zai bata lokaci wata kila ta chanza ra'ayinta, ji yayi bazai iya tsayuwa ba, ya zauna gefen gado tare da dafe kansa dake sara masa, kirjinsa har wani bugawa yakeyi da sauri, duk yadda yaso daurewa, ya kasa, hannunsa yasa ya share hawayen fuskarsa yana jin wani irin radadi da daci a zuciyarsa, yau Hanifah ke fada masa magana son ranta?
Yafi minti goma zaune ya rasa meke masa dadi, karshe tashi yayi ya shiga ya watsa ruwa mai sanyin sosai, sannan ya dauro alwalla don baya jin zai iya bacci a wannan daren.

Hanifah kuwa da gudu ta shige dakin ta kullo, ta fada kan gado tana kuka sosai, duk da batasan meye so amma tanaji a jikinta babu wanda takeso a halin yanzu sama da Deen, ya riga ya sace zuciyarta lokaci guda!
Khaleel kuwa har gobe kallon dan uwa na jini take masa, amma babu ko digon soyayyarsa a zuciyarta, kwarai taso ta fada masa tana da wanda takeso amma bazata iya fada masa haka ba, ai ya zama cin fuska.
Haka ta kwana tana tunani kala kala.

Washe gari ta tashi da matsanancin ciwon kai, ga idanunta sun kumbura sunyi ja, koda Ammi ta tambayeta cewa tayi batayi bacci da wuri bane.
Suna kalaci Khaleel yaki fitowa, Ammi duk ta damu ta kalli Hanifah.
"Ina yayanki meyasa bai fito ba?"
Ta dan yamutsa fuska
"Wallahi bansani ba Ammi"
Ammi ta kalle ta tace
"Je ki kirashi"
Haushi ya turnike ta, ta mike a fusace tayi dakinnasa ta kwankwasa hade da sallama. Cikin wata irin murya yace
"Waye?"
Tace
"Hanifah ce kazo inji Ammi"
To kawai yace, ita kuma ta fice tana tsaki cikin ranta, mutum sai wani ji da kansa yake.
Sai da ya dauki tsawon minti uku sannan ya fito fuskarsa ba alamun annuri ko kadan, ya gaida Ammi, ta amsa tana mai kallonsa, kallo na kurilla tace
"Lafiya dai? Meyasame ka?"
Yace
"Bakomai Ammi, gani"
Tace
"Zo kayi kalaci"
Ya dan yamutsa fuska yace
"Bana jin yunwa"
Tace
"Me kaci da zakace bakajin yunwa?"
Yayi shiru
Tace
"Zo ka zauna nace"
Bai musa ba ya ja kujera yana fuskantar Hanifah ya zauna, ganin haka yasa ta mike, Ammi ta kalle ta
"Ina zakije?"
Tace
"Zan shiga wanka ne"
Ammi tace
"Ai baki gama ba"
Tace
"Na koshi ne"
Daga haka ta fice da sauri, Ammi da kanta ta zuba masa farfesun yan ciki da soyayyar doya. Da kyar yake hadewa, kamar yana cin madaci, duk akan idon Ammi, ta numfasa tace
"Khaleel"
Cikin wata dakusashiyar murya yace
"Na'am Ammi"
Tace
"Wai meke damunka?"
Ya kakalo murmushin dole yace
"Babu komai"
Tace
"Idan har baka fada min damuwarka ba, wa kake da shi da zaka fada masa?"
Yayi shiru
Tace
"Ina jinka"
Yace
"Da gaske Ammi babu komai"
Tayi murmushi
"Shikenan duk ranar da ka shirya ka sanar da ni ina jiranka"
Ta mike tana maganar zuci, tabbas tasan damuwarsa, kawai bazai fito fili ya fada ba, amma tana tausayin sa sosai.
Kasa cin abincin yayi, sai kawai ya hada ruwan tea ya koma dakinsa.



*******


Kullum da daddare sai Hanifah tayi waya da Deen a 6oye, tun Ammi na bata har ta fara hanata tace sai ta fadi mata wa take kira haka kullum, sai tayi karya tace ai yar ajinsu ce, ita dai Ammi tace ta gaji bata kara bata, gashi sun shaku sosai, Deen irin mazan ne da suka iya kalallame mace da kalaman soyayya,  da tilas budurwa sai ta nitse a kogin sonsa, Hanifah ta riga ta sallama masa zuciyarta.
Khaleel kuwa duk ya fita cikin hayyacinsa, tunanin yau daban na gobe daban, daka ganshi kasan yana cikin mawuyacin hali, shi kadai yasan meyake ji a cikin ransa.
Ammi kam abin ya ishe ta, hankalinta duk ya tashi ganin yadda Khaleel ya koma abin tausayi.

Ranar wata juma'a Ammi ta yanke shawarar samun Khaleel don ta nuna masa ta son damuwarsa, don bazata zuba ido tana ji yana ganin Khaleel dinta ya lalace a banza ba, bayan ga maganin matsalarsa nan cikin gida a kusa da shi.
Yana zaune falo ya kura ma katuwar tv din da ke makale a bangon falon ido, amma a zahiri sam hankalinsa baya wurin, Ammi tayi sallama a karo na uku, a lokacin yayi firgit ya dago yana dubanta bayan ya amsa tare da gyara zamansa. Zama tayi kan kujera, ganin haka yasa Khaleel ya zamo kasa ya zauna, tana kallonsa kallo mai cike da tausayawa tace.
"Khaleel"
Bai dago ba yace
"Na'am Ammi"
Tace
"Meke damunka? Kar kaso kaga yadda ka koma duk wanda ya kalle ka yasan ba lafiya ba"
Yayi shiru
Tace
"Ina jinka"
Yace
"Babu ko..."
Tace
"Kar kace min haka Khaleel, a matsayina na uwa na riga na fahimci matsalarka Khaleel, amma naga kamar baka dauke ni a matsayin mahaifiyarka ba..."
Khaleel ya dago a razane yace
"Ammi meyasa kika ce haka? Duk duniya banida mahaifiya sama da ke"
Tace
"Ban yarda ba inda ka dauke ni haka ai da ka fada min matsalarka"
Yayi shiru zuciyarsa ta raunana.
Tace
"Ni nasan Hanifah ce damuwarka Khaleel, ba tun yau ba na fahimci komai, bansan meyasa kake 6oye abinda ke cikin ranka ba, bakasan sai nafi kowa farin ciki idan hakan ta faru ba?"
Yayi murmushi kadan yace
"Nasani Ammi, amma don Allah kar kice zaki tilasta mata, nafiso ta amince da bakinta"
Ammi tayi tsai, can kuma ta numfasa tace
"Shikenan, ka nemi amincewarta ni kuma zan tsaya maka kai da fata har burinka ya cika insha Allah"
Yayi murmushi mai bayyana hakora. Koba komai ya dan samu sauki tunda Ammi ta bashi go ahead, kawai babbar matsalar yanzu Hanifah ta ina zai fara?
Har Ammi ta mike ta shiga ciki bai sani ba, don ya kara tsunduma cikin kogin tunani.


Saif sun shiga hutu don haka gida ya taho don ya jima rabonsa da gida, kowa yayi murna da ganinsa.
A cikin kwana biyu ya fahimci yadda Hanifah kema Khaleel, kuma ko kadan baiji dadi ba, amma yayi alkawarin shawo kan matsalar kafin ya koma.


*******


Yau ma kamar kullum bayan Hanifah tayi shirin islamiyya, ta leka tace ma Ammi ta tafi, tayi mata nasiha da addu'a kamar yadda ta saba, ta fito a falo tayi kaci6us da Khaleel yana shirin shiga ciki, ko kallonsa batayi ba ta fice, har cikin ransa bai ji dadi ba, wannan irin tsana haka?

Kamar kullum yayi fakin motarsa inda ya saba fakin yana jiranta, minti ashirin ta iso tana murmushi, ya kalle ta yana sosa sumar gefen bakinsa yace.
"Princess sai yanzu?"
Ta karaso tana kallonsa tace
"Sorry Deen wallahi na tsaya biya karatu ne"
Yace
"Its ok, zo ki zauna" ya nuna mata gefen kujerar motar, ba musu ta zagaya ta bude, nan hira ta 6arke tsakaninsu, Hanifah ta gama yadda da Deen, ta aminta da shi, shima din wani irin shu'umin murmushi yayi ya karkato da fuskarsa yana kallonta.
A hankali ya kamo hannuwanta cikin nasa yana murzawa, ta kasa hanasa duk da batason abinda yake mata amma gaba daya ta kasa kwakwaran motsi. Lumshe idanunta tayi kafin ta bude, ya shafi gefen fuskarta yace
"I love you Hanifah"
Tana shirin yin magana ta hango Saif wanda tsananin razana yasa ta kasa motsi, sai na shiga uku take kira, Deen yace
"Mekika gani haka da kika rude lokaci daya?"
Bata iya bashi amsa saboda tsananin rudanain da ta shiga ya sa ta rushewa da kuka, yadda Saif ya taho kamar kura taga nama, haka ya karaso yana huci ya bude inda Hanifah ke zaune tare da finciko ta, wata irin razananiyar kara ta fasa da tasa Deen ya rude.
"Dama wannan dan iskan ke hure miki kunne? Islamiyar kenan Hanifah?"
Kuka take sosai tana bashi hakuri. Ya juya yana kallon Deen da yake zaune babu alamun damuwa a tattare da shi, Saif cikin zafin nama ya finciko Deen.
"Dama kaine dan iskan da ke hure mata kunne?"
Ya dago hannu ya wanke Deen da mari, ya kara masa daya a 6angaren hagu, sannan ya soma naushinsa ta ko ina. Yana bugunsa yana masifa.
"Kai har ka isa Ammi ta dauki tsawon shekaru ba iyaka tana gina tarbiyyar diyarta, rana daya kace zaka rusa shi?"
Wani naushi ya kai masa da sai da bakinsa ya zudda jini, ga unguwar ba mutane sosai bare wani ya kawo dauki.
Sai da yayi masa jina jina a fuska, sannan ya finciko Hanifah dake kukan fitar rai yayi gida da ita.



MSB✍🏼

Monday 13 February 2017

KHALEEL Page 13&14

πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€

           πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️
   ♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€♥️πŸŒ€



This page is for you Aunty Yar Mitsia and Kdey❤️😍❤️one loveπŸ’ž



 ®TALENTED WRITER'S GROUP(TWG)✍🏻

           
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
                  *KHALEEL*
               πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com


 February 2017πŸ’Ž


              PAGE


✍🏻✍🏻13&14&✍🏻✍🏻


Saif yace
"Babban yaya yadai?"
Khaleel yayi dariya yace
"Meka gani ne?"
Saif yace
"Babu komai"
Daga haka bai kara ce masa komai ba, haka kuma Khaleel ya basar da zancen, aka cigaba da sabgar graduation.
Hanifah kuwa tunda tayi sababbin kawaye larabawa bata kara bi ta kansu ba.


******

Washe gari da misalin karfe tara da rabi na safe Khaleel yayi wanka ya shirya cikin bakin jeans da riga ruwan toka mai ratsin fari, ya fesa turare ya fito falon, Ammi da Saif  suna kan dinning suna kalaci, amma babu Hanifah a cikinsu, ya gaida Ammi yaja kujera gefenta ya zauna, flask ya jawo ya zuba ruwan tea, Ammi da kanta ta zuba masa plantain da dankali da soyayyen kwai, tana shirin zuba masa madara a shayin yace.
"Ammi don Allah ki bari na sa da kaina, wannan abubuwan fa mu ya kamata mu dinga yi muku shi"
Tayi murmushi
"Kar ka damu Khaleel, kome uwa tayi wa danta bata fadi ba"
Zata cigaba ya hanata
"Nidai dan Allah Ammi ki bari, wallahi kunya nakeji idan kina sa min"
Tayi murmushi kurum, ta zauna tana kallon dannanta. Ya juya da zagaye kwayar idonsa farare tas yabi table din da kallo, yana kallon Saif yace.
"Saif ina Hanifah?"
Yace
"Assignment takeyi a cikin dakinta"
Yace
"Saboda Assignment sai takiyin breakfast?"
Saif yayi murmushi kawai
"Ina zuwa"
Khaleel yace yana kokarin mikewa tsaye, babu wanda ya tanka masa sun dai bishi da ido. Ya doshi dakinta. Gaba daya kallon tausayi suka bishi da shi don zuwa yanzu sun fahimci abinda yake kokarin 6oyewa ya soma fitowa fili, Ammi har cikin ranta tausayin Khaleel takeji, ya akayi ya bari zuciyarsa ta kamu da son wannan kafaffiyar yarinyar da bata son ciwon kanta ba?"

Zaune take kan study table da katon dictionary, sai wasu manyan text books guda uku a gefe, ta bude daya tana rubutu bisa dogon exercise book, tana ta rubutu. A bakin kofa yaja ya tsaya yana kallonta, ko wane motsinta akan idonsa, bata ma san da mutum a nan ba, bazai iya cewa ga iya adadin lokutan da ya dauka a nan ba, kila jikinta ne ya bata ana kallonta, a hankali ta dago ta dube shi, bata ce uffan ba ta maida kanta kasa ta cigaba da abinda takeyi.
"Sorry... Na katse miki abinda kikeyi ko? Ki ajiye wannan aikin sai kinyi breakfast tukunna"
Ta yamutsa fuska ba tare data kalle shi ba tace
"Na koshi"
Bai ce komai ba yaja kujera kusa da ita ya zauna yace
"Shikenan nima bazan ci ba, kawo in taya ki"
Tayi banza dashi ta cigaba da abinda takeyi.
Ya numfasa yana kallonta a nutse yace
"Ki kawo na taya ki nace"
Wannan karon bata musa ba ta mika masa, aikuwa sai ya hada gaba daya ya rufe ya aje gefe, yana kallonta sosai a yayin da ta kawar da tata fuskar gefe.
"Oya ki tashi ki karya ba kyau mutum yana zama da yunwa"
Yayi maganar duniyar nan amma taki dagowa bare ma yasa ran zata kalle shi, ga ta turnike fuska kiris take jira tayi kuka, ransa yayi matukar 6aci, duk duniya babu mai yi mashi wulakancin da Hanifah ke masa, baisan lokacin da ya fizgo hannunta yana kokarin jawo ta daga kan kujerar.
"Zaka karya ni fa"
Yace
"Ai gara na karya ki in huta da wannan wulakancin da kikeyi min, Hanifah nifa yayanki ne, jininki, ko Saif dana girmeshi bakiyi masa wulakancin da kikeyi min, why Hanifah?"
Batasan lokacin da tace
"Kai yaya takura min kake, gaka mugu..."
Tayi saurin yin shiru tare da sa hannunta ta rufe idanuwanta tana jiran saukar bugu.
Murmushi yayi da yafi kuka ciwo yace
"Hanifah duk abuwan da kika ga ina yi miki is for your own good, taimakon rayuwarki nakeyi..."
Cikin muryar kuka tace
"Nidai ka sake ni"
Ya sake ta ba musu tare da fita daga dakin.
Allah sarki so! Dawowa yayi dauke da tray din kalacin ya aje mata har bisa table dinta hade da tsugunnawa gabanta, kukan da takeyi shi ya fi komai daga masa hankali, cikin murya mai rauni yace.
"Kisha ba don ni ba, kuma ba don na isa nasa ki din ba, kiyi hakuri kisha kinji yar kanwa ta?"
Ta dago ta dube shi duk sai ya bata tausayi kuma, wai ita me ke damunta ne? Meyasa kike wulakanta yayanki? Jininki ne fa, uwa daya uba daya ai ya wuce wasa. Wani 6angare na zuciyarta ya ce da ita.
Sai kawai ta mika hannu ta dauki cup din ta kai bakinta.
Ganin haka yasa ya mike ya fita zuciyarsa cike da tunani kala kala.

Wai sai yaushe zaka sanar da ita cewar bafa iyaye daya suka jefo ku duniya ba. Kara gyara kwanciyarsa yayi tare da juyawa gefe guda yana tunani mai yawa.
Sallamar Saif ce ta katse masa tunaninsa. Ya tako a hankali ya zauna kusa dashi yace.
"Yaya wata magana nazo muyi da kai idan bazaka damu ba"
Ba musu Khaleel ya mike zaune daga kwanciyar da yayi, ya janyo filo daya ya rungume yace
"Ina jinka Saif"
Saif ya gyara zama ya soma magana cike da damuwa.
"Yaya, kwana biyu naga kamar kana cikin damuwa, ya kamata ka sanar da ni koda akwai shawarar da zan iya baka"
Khaleel yayi shiru kawai. Saif ya numfasa yace
"Dana so nasa maka ido yaya, amma gaskiya naga hakan bamai yiwuwa bane, na san menene damuwar ka ba tun yau ba kallonka kawai nakeyi...!"
A razane Khaleel ya ce
"Ya...ya akayi kasani?"
Saif yayi murmushi
"Yaya kenan, ai sirrin da kake 6oyewa ne ya soma fitowa fili, soyayya ce mai matukar wahala take wahalar da ke, soyayyar wacce batasan kanayi ba, soyayyar yar uwarka kuma jininka HANIFAH....!"
Sunan har cikin kwalwarsa haka yaji shi, ya runtse idanunsa gam yana mamakin yadda akayi Saif har ya gano haka da wuri.
Saif ya cigaba da magana
"Yaya ya kamata tun wuri ka fito fili ka sanar da ita, idan ba haka ba nan gaba zakayi dana sani, a bari ya wuce shike sa da rabon wani..."
Khaleel ya katse shi
"Saif bana kin bin shawarka bane, a'a kai kasan halin Hanifah wata irin yarinya ce, yanzu ma bakaga irin tsanar da tayi min ba inaga idan na furta mata kalmar so, inajin tsoron rasa ta, idan na rasa Hanifah kamar na rasa rayuwata ne, besides yarinayar nan har yanzu batsan matsayina ba a wurinta"
Saif yace
"Haka ne, amma dai yaya kayi kokari ganin ka sanar da ita kota wane hali ne, ina guje maka gaba ne, saboda idan ka bari tayi maka nisa har abada bazaka iya kamo ta ba, amma yanzu da take kusa da kai ya kamata kasan me kuke ciki"
Khaleel ya girgiza kansa alamun gamsuwa da shawarar Saif.


******


Kwanansu biyar a Dubai suka dawo Nigeria, tun dawowarsu Hanifah bata kara bari sun hadu ba, shima bai matsa ba, amma ya kudiri a ransa cewar kota halin yaya ne zai sanar da ita matsayinsa a gareta, sannan ya fada mata irin dinbin kaunar da yake mata.

******

Karfe hudu da minti sha biyar ta fito sanye da kayan islamiya kalar toka, hijabin har kasa, sai jakar litattafanta da ta rataya a kafada, sauri takeyi kasancewar zata bada hadda a yau din, har ta kusa kaiwa wata mota kirar honda baka wulik, ta faka ta gabanta, hakan ya tsaida ta daga tafiyar da takeyi, cike da jin haushi ta bude baki zata fara masifa, aka bude kofar motar, matashin saurayi ne da bazai haura shekara asharin da hudu zuwa da biyar ba, ba fari bane, kalarshi chocolate color, yana da tsayi sosai, haka ma siriri ne sosai. Sanye yake da kananan kaya bakin wando da farar t shirt marar hannu.
Takowa yayi dab da ita yana fadin.
"Yan mata islamiyya za'a je haka?"
Tayi tsaki kadan tace
"Waye kai da zakazo ka wani sha gabana haka?"
Yayi dariya yana sosa sumar gashin kansa yace.
"Wani bawan Allah ne, dan Allah idan bazaki damu ba ara min lokacinki minti daya yayi yawa"
Tayi shiru alamun tunani, can kuma ta numfasa tace
"Yi sauri saboda na riga na makara"
Yayi dariya yace
"Nagode sosai Beauty"
Suka tsaya daga jikin motar yace
"Wallahi na jima ina ganinki kullum idan zaki wuce ta nan hanyar, wato idan zakije islamiyya, alfarma nake nema wurinki"
Ta dan zaro ido tace
"Ta me fa?"
Yace
"Yauwa, kamar yadda na fada miki nasha haduwa da ke ta nan hanyar, na juma da kamuwa da sonki, kuma komai sai dana gano game da ke tukunna kikaga na miki magana"
Tace
"Kamar yaya?"
Yace
"Ma'ana nasan gidanku da makantar da kike zuwa"
Ta dan saki fuska kadan tace
"Gaskiya ni yanzu bana soyayya har sai na kammala karatuna tukunna"
Yayi murmushi yana mata wani irin mayen kallo yace
"Naji baki soyayya, amma ya kamata ki fada min idan na samu kar6uwa yadda hankalina zai kwanta"
Tadan yi shiru tana kare masa kallo batace komai ba
Yace
"Wannan kallon ya tabbatar min da cewar na samu shiga kenan?"
Tayi murmushi a lokacin da ta gyada kanta alamun eh.
Wani irin tsalle yayi yace
"Yes!"
Ta kalle shi shekeke tana mamaki
Yayi dariya yace
"Nagode sosai ko zan samu number wayarki?"
Tace
"Kayi hakuri banida waya a halin yanzu, amma kana iya bani taka duk sadda na tashi zan kiraka"
Littafin makarantarta ta ta ciro daga jaka da biro ta mika masa, ya rubuta mata number din sannan yace
"Ina jiran kiranki"
To kawai tace tare da wucewa tayi hanyar makaranta, yayi saurin kiranta, juyowa kawai tayi.
Yace
"Baki fada min sunanki ba princess"
Tayi murmushi
"Sunana Aminatu, but you can call Hanifah"
Yace
"Nice name, ni sunana Zaharadeen, amma zaki iya kirani da Deen"
Tayi murmushi tace
"Ok Deen"
Daga haka ta wuce da sauri zuciyarta cike da tunani kala kala!
Kallonta yake har ta 6ace kafin yayi murmushin da shi kadai yasan ma'anarsa, sannan ya bude motarsa ya tafi.

Da daddare haka Hanifah tayi ta saka da warwarewa, ta yarda ta amince tana son Deen, sai kace wanda yayi mata asiri cikin rana daya har ta amince da shi ba tare da tasan ko wanene ba....?
Ta yanke shawarar aro wayar Ammi ta kirashi.
Ammi ma zaune tana zaune tana lazumi ta shiga da sallama, bayan ta gaishe ta tace
"Ammi dan Allah ara min wayarki zan kira wata yar ajinmu"
Ba tare da tunanin komai ba ta mika mata wayar.
Ta koma dakinta ta 6oye number din tare da kira, bugu biyu aka dauka.
Tace
"Hello?"
Daga kwance yace zumbur ya mike yace
"Hanifah kece?"
Tace
"Nice, Deen ne?"
Yace
"Nine my princess ya kike?"
Ta lumshe idanu tace
"Lafiya lau"
Yace
"Naji dadin kirana da kikayi, amma meyasa kika 6oye lambar?"
Tace
"Wayar mamana ce na ara zan dinga kiranka kafin a siya min wayata"
Yace
"Ok my princess menene labari?


Khaleel ne kwance a dakinsa ya kasa sukuni, tunanin Hanifah ya ishe shi, hakan yasa ya mike bayan ya yanke shawarar sanar da ita abinda ke zuciyarsa game da ita.
Jallabiyarsa doguwa ya zura ya fito da dakin.


(Sorry pls akwai inda nace Khaleel is 29 is a mistake he's 22 years😊)


MSB✍🏼