Sunday 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 43

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤
    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ
        πŸ’šπŸ’™
            πŸ’™


MSBπŸ’–


maryamsbellowo.wordpress.com



*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*


I want to use this medium to thank my people all over the world for the support and also thank you for reading my novel, i also want to dedicate this page to:
Asma'u Isa, Maryam Gafai, Bilkisu Ammani (chuchu), kdey, Faty Ladan, Fiddausi Abubakar, Hafsat Kabir, Zainab Bapullo, Asma'u Mashasha, Fatima Muhd Mansur, Asma'u Ammani, Fatima Bashir Musa, Sumayya Girei, Maryam Sayaya, Hauwee Bash, Meesha lurv. Word can't describe how grateful i am for all the love and support, Allah ya bar mana ku ya kara mana zumunci❤️❤️❤️❤️ thank you once again 😘😘  


43


Tun daga bakin qofa ta soma jiyo hayaniya, haka kawai ta tsinci kanta da faduwar gaba, ta dake ta kutsa falo, gaba daya kallo ya dawo kanta, wata mata daga cikin matan mai matuqar kama da Mami sai dai ta girmi Mami ta taso da sauri tana kallon Khadija, tayi tsai sai kuma can ta furta da qarfi.
"Wallahi itace" tana kallon Khadija tun daga sama har qasa, sai kuwa kowa ya taso yana tofa albarkacin bakinsa, rungumar da sukayi mata kamar zasu kada ita qasa, ita dai Khadija batace uffan ba sai ido, nan dai kowa ya gama tofa abinda zaice tukunna matar taja hannunta suka soma shiga ciki, dakin Mami taga tayi da ita, fitowar Mami daga wanka kenan, tana ganin Khadija ta fadada murmushi, wadda suka shigo tare ta furta a yayin da take zama kan gado.
"Wannan abin al'ajabi Safiyya ashe yar uwar Fatima nada rai tun ranar da kika sanar da ni a waya, ikon Allah kuma kinga yadda suke kama? Tabbas Allah da iko yake"
Mami ta juyo gami da zama kusa da matar tace
"Uhm bari kedai yaya kindai ganta"
Nan sukayi ta maida zancen ita dai Khadija tana ta murmushi, Mami ta kalli Khadija tace
"Kinga wannan? Yaya ta ce uwar mu daya uban mu daya, sunanta Anty Hafsa, yaranta na nan dakin Heenad idan kinje sai ku san juna, anjima da yamma ma za'aje jere can gidan amarya"
Anty Hafsa ta kalle ta da mamaki
"Dama bakuyi jere ba sai yau?"
Mami ta girgiza kai
"Wallahi laifin angon ne yaya sai jiya da daddare ya kawo mana mukullin gidan, so yau Alhaji ya tura aje a auna labulai a saya a asa kafin yamma zasu gama ku kuma sai kuje kuyi jeren"
Anty Hafsa ta girgiza kai cikin gamsuwa tace
"To shikenan Allah ya kaimu"
Anty Hafsa ta miqe ta kamo hannun Khadija
"Yata muje wurin yan uwanki suna daki"
Tare suka fita a yayin da Mami ta cigaba da shiryawa.

Tun kafin su shiga ta fara jiyo hayaniyar yan mata ana ta maida zance,  suka kutsa kai dakin da sallama, kallo ya dawo kansu, Heenad dake kan gado ta miqe da hanzari ganin yar uwarta ta taso gami da rungume ta cike da murna, Anty Hafsa tayi dariya
"Ja'ira sai kace ba ke bace kika gama kuka dazun nan?"
Heenad tayi murmushi hannunta cikin na Khadija  ta kamo ta suka zauna kan gado.
Anty Hafsa ta kalli yan matan da zasu tasan ma goma a dakin tace
"Gafa yar uwarku nan Khadija, sai ku jawo ta ajikinku ku saba" daga haka ta fita daga dakin
Gaba dayansu yan mata sukayi kan Khadija, wasu na yaba kanta wasu na yaba yadda suke kama da Heenad, kafin wani lokaci Khadija ta saba da yan uwanta sosai wanda ita din take mamakin yadda dangin Mami keda kirki haka.
 Abida ma tayi mamakin Khadija, ga muguwar kama sunayi.

Bayan sallar azahar, sunyi sallah sunci abinci, aka soma shiri, wata yar walima Mami ta hada da za'ayi cikin gida, after dress amarya tasa mai style dan kuwa ta hadu after dress din, mai kaloli jikinta, kwalliya aka yi mata marar nauyi, a yayin da yan matan suka sanya after dress baqa shine dress code din, Khadija ma irin ta Heenad ta sanya sai dai bambancin kowa da kalar tasa wadda duk Daddy ne ya siya musu, bayan sun kammala shiri aka fito tsakar gida inda  aka sanya kujeru masu kyau, sai na amarya daban, nan aka gudanar da walima anci an sha, sai bayan la'asar aka tashi.
Bayan anyi sallah Anty Hafsa da wasu yan uwan Mami guda hudu suka tafi jere, Anty Hafsa tayi mamakin gidan inda part biyu ne suna kallon juna, daya na mahaifyarsa, dayan kuma nan ne na Heenad din, gidan baida girma ko kadan,  gidan kam ya wuce ajin Heenad yadda ta taso cikin gata da kudi, (dama haka rayuwa take). Basu suka gama jeren ba sai bayan sallar isha'i. Don sun dan sha wahala duba da yadda gidan yake saboda kayan dakin Heenad komai manya ne ga gidan baida girma.
A gajiye suka koma gida.

Washe gari juma'a bayan sallah masallaci ya cika tap da jama'a ana shirin daura aure Daddy ya hango Abba, take kunya ta kama shi na farko ko katin gayya bai kai masa ba amma la'akkari da Khalil aminin Adnan ne ya sanya baiyi mamaki ba, na biyu abinda yayi masa ranar daurin auren diyarsa yanzu da wane ido zai kalle shi?"
Bayan an daura auren ne cike da kunya Daddy ya isa ga Abba dake zaune gu daya yana gaisawa da jama'a ya hango Daddy yana karasowa kansa na kasa, Abba ya bashi hannu yana murmushi suka gaisa yayi masa Allah sa alkhairi tukunna Abba ya tsugunna yace.
"Alhaji dama..."
Abba ya katse shi.
"Don Allah bana son ana tada maganar da ta riga ta wuce ni sam ban riqe ka a zuciyata ba"
Ya qarasa yana murmushi
Daddy ma yayi murmushi baice komai ba, Abba ne ma yake jansa da hira har ya saki jiki suka yi hira sosai kamar wani abu bai ta6a shiga tsakaninsu ba.
Ango kam ba'a maganarsa dan bakinsa yaqi rufuwa, Adnan sai faman zolayarsa yakeyi wai yanzu sun zama daya dama suna auren TAGWAYE.

Heenad na zaune tana razgar kuka a sakamakon jin an daura mata aure a yau dinnan, take zuciyarta tayi wani irin baqi, ji take ina ma bata yarda anyi auren nan ba, haushin Khalil kuwa baya kwatantuwa a cikin zuciyarta, hankalin Khadija gaba daya ya tashi ganin yar uwarta cikin wannan hali, take itama zuciyarta ta tsinke tayi ta kuka, nan aka shiga lallashinsu.

Qarfe takwas da rabi aka shirya amarya cikin qaton mayafi tana riqe da hannun yar uwarta tana kuka, falonDaddy aka shiga da ita, yayi mata fada sosai akan zaman aure Mami ma haka tayi mata fada sosai. Haka aka fita da Heenad tana gunjin kuka kamar wacce ake cire ma kai.
Bayan an kaita an watse, dakin ya rage daga ita sai Khadija, Heenad kanta na kife cikin cinya tana kuka, kukan dana sani, kowa ma haushinsa takeji. Khadija nata mata magana taqi kula ta har dai Adnan ya kira ta a waya ya sanar mata ta fito yana waje. Haka ta tafi jikinta yayi sanyi.

Ango an shigo sai zakwadi akeyi bakinsa har kunne, ya qaraso dakin da Heenad take cikin sauri, don jin kukanta da yakeyi, hankalinsa a tashe.
Ya zauna tare da dafa ta.
"Cutie kukan me kike yi? Yau ba ranar kuka bane ranar farin ciki ne fa"
Ya dafa kafadunta.
Ta dago a fusace dama qiris take jira, idanunta sun rine saboda kuka, ta kalleshi sai ta kauda kanta da sauri don ganinsa take kamar wani dodo, tace
"Kar ka kuskura ka ta6a ni"
Da mamaki yake kallonta.
"Heenad nine fa Khalil!"
A fusace tace
"Nafika sanin kowaye kai, ka tashi kar bar min daki, ka tashi nace!"
Ta fada cikin daga murya
Khalil yayi mutuwar zaune, ganin yaqi tashi yasa ta miqe cikin kuka tace
"Idan har baka fita ba ni zan fita wallahi"
Jiki a sanyaye Khalil ya miqe, wani qululun baqin ciki ya maqale masa a maqoshi, ya hadiye da qyar ya miqe.
"Naji zan fita amma dan Allah kici abinci kinji?"
"Bazan ci ba kwashe kayanka ka fice min nace"
Bai kwashe ba illa fita da yayi kamar yayi kuka yakeji, wannan abu da me yayi kama? Lallai mata sai dai a barku, ya fadi a lokacin a yake zama kan kujerar falo, yana hadiye kukansa.

Ganin yaqi fitar da abinci ya sanya ta kwaso ta jibgo masa bakin qofa sannan ta sa mukulli ta rufe qofar gam.
Haka ta kwana tana kuka, gashi ta bari shedan yayi galaba a kanta don kuwa kwana tayi tana tunanin Adnan wanda a yanzu haka yana can tare da yar uwarta.
"Sheyasa akeson bin umarnin iyaye, da nabi su da duk haka bata faru ba" ta fadi tare da qara fashewa da kuka.
Ranar sam bacci ya gagari amarya da ango musamman Khalil da baqin ciki ya hana shi runtsawa, haka ya kwana yana tunanin Heenad.


Washe gari Heenad na kicin tana hada kalacinta na cikinta ita kadai, wata yarinyar yar kimanin shekara sha bakwai kusan tsarar Heenad ta shigo dauke da dan kwandon abinci, ta gaida Heenad tukunna tace.
"Ga kalaci inji Goggo (mahaifiyar Khalil)
 Ta kalle ta daga sama har qasa tace
"Kije ki maida na qoshi"
Husna ta qule haushin Heenad ya kamata dama haka matar da yaya ya aure take? Ashe batada kunya dama?" Ta ambato hakan a ranta tana qare ma Heenad kallo.
Heenad ta kalle ta cike da jin haushi tace
"Nace ki je na qoshi ko?!" Ta fada cikin daga murya.
Husna ta fice a zuciya tayi sashensu, Goggo na kicin tana juye sauran kokon a flask Husna ta shigo a zuciya.
"Dan Allah Goggo daga yau kar ki qara kai ma yarinyan na abinci"
Goggo ta juyo da dubanta ga Husna tace
"Saboda me?"
Nan Husna ta bata labarin abinda tayi mata tare da ajiye kwandon qasa.
Goggo tayi murmushi
"Bazan dena kai mata ba, ki qyale ta wata rana zata gane gaskiya"



Maryam S belloπŸ’–

No comments: