Sunday 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 54

๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ❤
    ๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ
        ๐Ÿ’š๐Ÿ’™
            ๐Ÿ’™


MSB๐Ÿ’–


maryamsbellowo.wordpress.com


®TALENTED WRITER'S GROUP (TWG)✍๐Ÿป


*๐Ÿ’•Tagwaye ne? ๐Ÿ’•*



54


Da tsakar dare naquda ta kama Khadija, nishinta ya tashi Adnan daga bacci, ya lalubo fitila ya kunna, ba qaramin razana yayi ba ganin yadda Khadija ke hada gumi ba, da sauri ya kamo ta yana tambayar lafiya, bata ko iya magana saboda azaba. Kamo ta yayi da qyar take tafiya a dudduqe suka fita har wurin motarsa, duk ya rude.
Kansa tsaye asibiti ya wuce da ita, yaci sa'a aka kar6e ta, sai yanzu ya tuna babu wanda ya sanar mawa, number Khalil ya lalubo cikin muryar bacci yace
"Hello"
A razane ya tashi zaune hade da kunnar wutar dakin, Heenad dake kwance gefensa itama ta miqe da qyar tana raba idanu.
Bayan ya kammala ya miqe a rude yana kokarin sanya jallabiyarsa, zumbur Heenad ta miqe itama ta fara nemo abayarta.
Ya kalle ta  da mamaki
"Ina zakije"
Tace
"Inda zakaje mana, wai meya faru?"
Nan ya sanar da ita aikuwa tace ina sai ta bishi.
Bayan Adnan ya sanar ma su Abba halin da ake ciki, ita ma Heenad a mota ta kira su Mami ta sanar masu.

Adnan na tsaye yana jiran likitoci wata nurse ta fito da sauri ta ce masa.
"Ka kawo kayan baby matarka ta kusa haihuwa"
Ya washe baki cike da farin ciki ya fita da gudu.
Koda ya dawo dauke da yar jakar kayan baby bata haihu ba, amma tana can tana ta fama. Nan ya iske su Heenad suma suna tsaye ko wane fuskarsa na nuni da yana cikin damuwa.

Minti biyu tsakani Khadija ta haifo kyakkyawar babynta katuwa mai koshin lafiya, kafin ta ankara wata ta biyo baya, tunda suka jiyo kukan jarirai suka san ta haihu.
A guje sukayi kofar dakin amma an hana su shiga. Adnan har qwallan farin ciki yayi, Heenad kuwa ji take kamar tayi tsuntsuwa ta gano su.

Can nurses biyu suka fito dauke da jarirai,  Adnan aka fara miqa mawa, ya qura musu ido, ko wace da kamarta hasali ma daya tafi daya haske, da sauri Heenad tasa hannu zata amshi daya amma fir Adnan yaqi bata, sai daya gama ganinsu yayi musu addu'oi sannan ya miqe ma Heenad daya don bazata iya daukar biyun ba.

A lokacin da Adnan ya shigo dakin an gyara Khadija, ya kalle ta cike da tausayin yadda ta kode lokaci daya saboda wahala.
Rungumo abarsa yayi tare da manna mata kiss a goshi, yace
"Maman yan biyu"
Murmushi tayi batace komai ba, nurse ce ta shigo tace za'a kaita dakin hutu.
Ko minti talatin Khadija batayi ba Heenad ta soma naquda itama, sai dai cikin ikon Allah minti goma kacal ta haifo danta qato mai qoshin lafiya. Haihuwa mai matuqar sauki Allah ya kawo mata.
Bayan an gyare mata danta dakin hutu aka kaita itama.

Washe gari asibitin har ta fara cika da yan uwa ganin jarirai. Sai da likita ya hana shigowa don abin ya soma yin yawa. Kafin goman safe Mami ta iso don an yanke shawarar tafiya da masu jegon gida daga asibiti, su Adnan ma sun amince da hakan.
Kafin sha dayan safe bayan likita ya gwada su aka basu sallama.
Daga nan su Adnan sukayi gida don dauko kaya a kai masu can gidansu. Bayan sun kai Khalil ya wuce gida don ya sanar ma Goggo.


* * *

A hankali Mami ke gasa ma Khadija jiki da tawul ta gama ta gasa ma Heenad nata jikin, sannan Anty Hafsa da ta iso tun safiyar ranar tayi wa jariran guda uku wanka, ta gasa musu cibi,  ta shirya su cikin kaya masu kyau da tsada, sannan ta nannade su cikin shawul mai dumi da nauyi, don ta kula garin hadari ne sosai.
Nama Daddy yasa a gasa musu, sannan aka damo musu kunu.

Da yamma yan uwa an hallara barka, sai dai bamai dadewa saboda hadarin da ya hadu garin yayi baqiqirin sai walqiya da akeyi akai akai.
Su Ummi da Hajiya Abu ma sunzo da yamma.
Washe gari sai ga Umma tazo itama, Khadija ta rasa inda zata ranta saboda murna. Nan Umma ke sanar mata aurenta da aka sanya wanda bayan auren Saudia zasu koma da zama, kowa ya taya Umma murna da fatan alkhairi.
Daga gidansu Adnan ma gaba dayansu sun zo ganin babies.

Ranar suna Matan sunci sunan Mami da Ummi wato Safiyya( Afra) da Halimatu Sadiya.(Haifah) a yayinda da babyn Heenad yaci sunan mahaifinta da Khalil ya jajirce a sanya masa ana kiransa da Adeel.
Ba'a wani yi bidi'a ba sosai, an ci dai ansha daidai gwargwado, anyi hotuna ba iyaka, masu jego anko suke tayi ga shi sunyi kyau masha Allah.

Sau uku ake musu gashin jiki sai gashi cikin wata daya Tagwayen sun miqe sun girgije, jariran sunyi 6ul 6ul dasu saboda isashen ruwan nono, da abinci mai rai da lafiya da mahaifansu ke ci kullum.


Maryam S bello๐Ÿ’–

No comments: