Sunday 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 42

πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤
    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ
        πŸ’šπŸ’™
            πŸ’™


MSBπŸ’–


maryamsbellowo.wordpress.com



*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*



42


Bata amsa ba amma a zahiri zuciyarta tayi sanyi haka fuskarta ma ta nuna. Tun da suke bata ta6a kallonshi haka ba, ashe haka idanunshi suke manya masu yalwar gashin gira? Ashe wannan shine Adnan? Gwauron numfashi ya sauke sannan yaja hannunta zuwa sama, dakinsa suka fada, ya shiga yayi wanka ya fito daure da tawul, da sauri ta kauda kanta qasa kamar ta tsaga qasa ta shige don kunya, wani qayatacen murmushi yayi mata mai fitar da annuri mai yawa a kan fuskarsa da sabuwar soyayya danqare cikin qwayar idonsa, kamar wani almajiri mai neman abinci. Ya jawo stool na madubi ya zauna dab da ita yana fuskantarta.
"Wai meyasa kike jin kunya ta Khadija? Nifa mijinki ne wanda babu kunya a tsakaninmu"
Yadda yayi maganar kadai ya saukar mata da kasala balle yadda hucin sassanyan numfashinsa ke dukan fuskarta.
Nan da nan ta rikice tana ta faman sunne kai qasa, ita bata bashi amsa ba ita ta kasa hada idanu da shi.
Ya kuma cewa
"Ke nake saurao" ya fadi tare da daga yalwataciyar girarsa sama kadan, a hankali ta kai dubanta gareshi abinda ta gani cikin qwayar idonsa ya sanya ta mamakin anya wannan Adnan ne? Don kuwa yadda qwayar idonsa ta nuna mutumin da ke fama da azzabiyyar soyayya da qauna mai tarin yawa, nan da nan ta samu kanta da cewa.
"Ba kunyar ka nake ji ba..."
Yayi murmushi, murmushin da ke nuni da miji yana buqatar matarsa yace
"Wow idan kuwa haka ne yau zan tabbatar da zancenki"
Nan da nan ta fara karkarwa, ko wane sashe na jikinta na kaduwa, kaduwa mai ban mamaki.
Baiyi mamaki ba saboda yasan ita mace an halicce ta ne da kunya da kuma kawaici. Saboda haka sai ya miqa hannu ya kamo hannunta duka biyun ya miqar da ita tsaye, gabanta ya fadi ba kadan ba ganin yadda yake da fadi, ashe dama haka yake da ginuwar jiki?
Karo na farko tunda sukayi aure da ya jawo ta jikinsa a hankali ya rungume ta.! Yasa hannunsa cikin gashin kanta dake baje cikin salo na qwarewa da sanin duk wani weakness da lafiyayyar mace, in banda karkarwa ba abinda takeyi cike da tsoro da kuma rashin sabo. Sai dai duk wata ga6a ta jikinta ta amshi saqon da Adnan ke aika mata cikin gashin kanta har ta kai ta kawo lamarin ya wuce gona da irin yadda sam bazata iya hana shi ba.
Karo na farko a rayuwarta da ta tsinci kanta a wata duniya ta daban da bata ta6a tsintar kanta  aciki ba.

Ba abinda Adnan keyi sai hamdala da mata ta gari, yana rungume da matarsa. Wadda yake kallo tana baccin wahala ga idanunta da suka kumbura saboda kuka. Ya qara rungume matarsa gam hadi da qara godiya ga Allah tabbas wannan ta mallaki duk abinda yake so matarsa ta kasance tana dashi koma fiye. Ya yarda ya kuma amince da cewar Soyayya ba abinda ya kaita muhimmanci a cikin aure, akwai abubuwa bayanta.
Tayi juyi a hankali ta bude idonta wanda ke cike da bacci suka hada ido kunya ta kama ta, ta sunna kanta cikin fadadan qirjinsa majiya qarfi qasa a yayinda da hawaye suka gangaro mata, zuciyarta cike da so da qaunar mijinta.

Bayan ta gama wanka tayi sallar la'asar ba tare da ta cire hijabin ta ba ta miqe ta sauka qasa,  kacaniya taji a kicin, ta nufi kicin din yana sanye da gajeren wando da farar singileti, kanta a qasa ta qaraso tana fadin.
"Da ka barshi zanyi"
Ya aje kofin shayin da yake hadawa ya iso gare ta ya zagaye hannuwansa a kafadunta yana kallon qwayar idonta.
"Ya zan dora miki gajiya buyu? Ai wannan rashin adalci ne ma"
Cikin matsananciyar kunya tace.
"Na hutar da kai kaje zan hado maka"
Ta sauke hannuwansa qasa ta nufi inda yake hada tea din ta cigaba da hadawa. Yayi murmushi mai cike da shauqin so da qauna ya matso dab da ita yana kallon yadda take aikin.
Ta juyo suka hada ido har lokacin ya kasa dena kallonta.
Cikin shagwa6a tace
"Nidai gaskiya ka tafi idan kana kallona bazan iya yi ba zan iya qonewa"
Yayi dariya ya juya zai fita yana fadin.
"Afuwan rankishi dade"
Dariya tayi ta qarasa.

Kan dinning ta iske shi yana zuba musu abincin da basu ci ba na rana, ta qaraso ta ajiye amsa shayin inda yake zama sannan ta zo kar6ar cokalin yayi wuf! ya hana ta yana murmushi.
"Bazan baki ba ni zan zuba mana da kaina kedai iyakar ki ci"
Tana kallo ya zuba a filet daya ya jawo ta ya zaunar da ita kan cinyarsa yana mata wani irin kallo mai cike da sakkonni kala  kala.
Ta sunna kanta qasa tana murmushi kadan.
Ya debo abinci zai kai mata a baki, cike da kunya ta kasa ci, ya kalle ta yace.
"idan har bakici ba zan miki dure"
Yadda yayi maganar ya sanya tayi dariya. yadda take dariyar sai tayi masa kyau matuqa, ya yi tsai yana kallonta har sai data gama dariyar sannan ya bata abincin. Sai daya tabbatar ta qoshi tukunna ya qyale ta, tana so tace zata bashi tana jin kunya, Adnan ya kalle ta ya daure fuska yace.
"Ni baza'a ciyar dani ba kenan"
Ta sadda kanta qasa sa'ilin da take murmushi.
Da qyar dai Khadija ta dinga bashi abincin nan har suka kamalla, ya taimaka mata suka gyara wurin.

Bayan sallar isha'i ya shirya cikin qananan kaya yana taje sumar kansa ta shigo dauke da qaton tire taja tabur (table) ta dora masa tana satar kallonsa ta gefen ido. Tabbas yayi kyau matuqa ba qaramin burge ta yayi ba, dama Adnan mutum ne da yasan sirrin dressing, ba tun yau ba tun tana gidansu, ko na Hausawa ko kuma na qananan kaya ko wane yana masa kyau. Sannan kuma ko wane irin dressing yayi kar6arsa yake. Ya ajiye comb din ya juyo suka hada ido, tayi saurin dauke kanta da sauri ta juya zata fita ya riqo gefen hijabinta.
"Bafa inda zakije sai kin fada min me kike kallo?"
Cikin sarqewar murya tace
"Ni ba a...bi...nda  na...ke kallo"
Yayi murmushi
"Bawani nan Adnan kike kallo, mijinki, bakiyi laifi ba kalleni ki more ki kuma cire wannan burmemen hijbin na kalle ki da kyau, after all abinda ake ma kunyar Adnan ya kwashe gaba daya dazu"
Ya fadi yana kashe mata ido daya.
Kamar ta fasa ihu don kunya, kunyarta na burgeshi ainun, ya janyota ya rungume gaba daya, ya soma kissing karan hancinta yana fada mata kalamai masu nauyi da suka fi qarfin hannu ya rubuta, bayan ya gama ya sake ta yana fadin.
"Zan je asibiti bazan dade ba yanzu zan dawo insha Allah"


* * *
Tana waya dasu Umma jikinta na sauki sosai kusan kullum sai ta kirasu a waya.

To haka dai rayuwar ke cigaba da tafiya, a kwana a tashi ba wuya wurin Allah, yau saura kwana biyu kacal bikin Heenad, da qyar Khadija ta samu Adnan ya barta taje ta kwana har a gama bikin duk da bazaayi wasu event ba ba don Heenad tace batayi.
Kayanta ta soma hadawa cikin dan akwati qarami ta kammala duka akan idon Adnan. Ta dauko jakarta da gyalenta ta yafa tace.
"Na shirya"
Ya taso ya tako inda take tsaye yace.
"Naga sai wani rawar kai kikeyi kamar bazakiyi kewa ta ba ko?"
Tayi murmushi tana kallonsa.
Ya kamo hannunta ya sumbace su tukunna ya daukar mata akwatin suka fito waje, koda suka hau titi kalamai ya dinga fada mata masu dadi yadda zaiyi kewarta har suka isa.
Daidai bakin get yayi fakin, ya fito ya dauko mata akwatinta, ta fito tana kallonsa kamar kar ya tafi take ji, sukayi sallama ta shiga ciki, ya dade tsaye kafin ya ja motar ya bar unguwar cike da kewarta.



Maryam S belloπŸ’–

No comments: