Sunday 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 6 to 10

TAGWAYE NE? Na Maryam s bello {6 to 10}
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*
06
Abida ce ta fito da sauri ganin mutane sun watse, ta kamo hannunta suka koma gefen titi, tace mata.
"Lallai Heenad bakida hankali kawai daga ganin mutum bakisanshi ba sai ki kama marinsa? Sheyasa kullum nike 'kara gaya miki ki rage rawar kai, wata rana sai kin samu wanda zai miki shegen duka..."
Heenad ta daka mata tsawa.
"Abida please!!! Let me be! Haba ki 'kyale ni inji da abinda ya dameni, na tsani mutumin nan over, kuma wallahi ko yau muka sake ha'duwa da shi sai na gasa masa aya..."
Abida tayi dariyar takaici, tace.
"Allah ya shirye ki amma kuwa kar ki bari Mami taji maganar nan dan kinsan idan taji ranki sai ya 6aci"
"Taji mana ni ina ruwana, dalla ni kizo mu tafi kinbi kin cika min kunne da surutu haba!" Ta fa'di cikin isa da raini.
Abida tayi murmushi tace.

"Uhm ni kinga ina da karatun Biology da nakeyi saboda kinsan shi zamu fara yi don haka kizo muje gida don naga kamar yana baki matsala kinga sai na koya miki abinda baki fahimta ba?"
Heenad tayi tsaki tace.

"Ke karatu ya dama ni daddy zai biya a wuce mani"
Abida tace.

"A'ah Heenad hakan bashida wani amfani a gareki wallahi ki dage kiyi karatun shi yafi ko don saboda gaba kinji 'kawata?" Ta fa'da cikin sigar lallashi.
Heenad tace.

"Ai fa sai kiyi don ni ba karatun da zanyi"
Abida ta girgiza tace.

"Shikenan mu tafi"

Daga haka bata 'kara cewa komai ba kawai ta shige mota.
* * *
Tunda ya hau titi, ya kasa sukuni so yake ya gano wacece wannan yarinyar 'yar gidan marassa tarbiya.

"Tirr da wasu iyayen, rayuwar yanzu sam ba tsoron Allah, yanzu ji shigar da tayi tana 'yar musulma. Wacece ita? Ya tambayi kansa, wata zuciyar tace masa ka rabu da ita ka 'kyale ta mana, wata zuciyar kuma tace masa ina! Ai yadda ta tozarka, ta kuma wula'kanta a cikin bainar jama'a bai kamata ka 'kyale ta ba.

Wata zuciyar kuma tace masa abinda ya kamata ka fara yi shine sanin Wacece ita, daga nan sai ka 'dauki ko wane irin mataki ya dace da ita. Ya girgiza kai, alamun gamsuwa da shawarar tasa, daidai sadda ya karya kwanar layin gidansu, tun kafin ya 'karaso aka wangame gate, duk suka mi'ke "Welcome sir" ya amsa da kai tare da sakin murmushi mai 'kayatar da kyawunsa, yayi pakin ya shige sashensa.
Kallo 'daya zakayi masa ka tabbatar an 6ata masa rai don idanuwansa sun nuna hakan.
Ban'daki ya fa'da ya bu'de shower ya sakar ma kansa ruwa yana mai tuno marin da yasha 'dazu. Yana tunowa ranshi na 'kara 6aci, sheyasa yayi sauri kawar da tunanin daga kansa.
Bayan ya fito ya murza cream, ya 'dauko t-shirt mai dogon hannu mai ratsin sky blue da fari, ya sanya farin jeans kasancewar ana 'dan sanyi ko abinci bai nema ba ya fa'da kan gado ya kwanta rigingine.
Haka mahaifiyarsa ta shigo ta sameshi, saboda ta saba kullum ya dawo ta sashenta yake fara shiga ya gaishe ta sannan ya shigo nasa sashen, dama tunda taga ya dawo taji shiru bai shigo ba, tasan ba lafiya ba.
"Adnan"

Ta furta gami da zama gefen gadon.
A hankali ya juyo kasancewar ya bata baya, ya zuba mata manyan idanunsa sannan yace.
"Na'am Ummi"
Maman ta kalle shi kallo na 'kurilla tace.
"Lafiya dai Adnan?"
Yace "lafiya lau Ummi"
Tace "ka tabbata?"
Yace "na tabbata"
Tace "shikenan" tana kallonsha kamar mai son gasgata wani abu.
Can ta numfasa tace.

"Ka zo kaci abinci to, ko a kawo maka nan?"
Ya girgiza kai.

"A'a zanzo naci yanzu insha Allah"
Ta mi'ke gami da cewa.

"Shikenan sai ka shigo"
Tausayin mahaifiyarsa ya kamasa, don haka jiki a sanyaye ya mi'ke ya bi bayanta.
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

07
* * *
Takwas daidai na bugawa Alhaji Hamisu na sallamawa, daga bakin zaure ya shiga 'kwalawa Umma kira.
"Hasiya...! Ke Hasiya...!!! Wai bakiji ne ana ta faman kiranki?"!!!
A lokacin Khadija ta fito daga wanka, jin kiran yayi yawa yasa tayi saurin zura riga da hijabi ta fito.

Tana tafe tana tunanin ina Umma ta shiga ana ta 'kwala mata kira haka?
Tana le'kowa gabanta ya yanke ya fa'di, ko girman mutumin ka'dai ya isa ya tsorata ta.
Ta daure ta gaishe shi cikin ladabi.

yana huro hanci yace.

"Lokacinku ya cika, ayi maza a tattaro kaya a fito masu gidan na jira"
Khadija ta ha'diye wani yawu mai 'dacin gaske tace a ranta.

"Lallai mutane basuda imani musamman ma ga talaka marar galihu, in banda talauci an isa a wula'kanta mu?"
Amma a zahiri sai cewa tayi "To"

Ya bita da harara yana tsaye ri'ke da 'kugu yana jiran su kwaso kayansu.
Ta shige gida jiki ba 'kwari ta le'ka kicin don a nata tunanin Ummanta na ciki amma ga mamakinta babu Umma babu alamarta, bata kawo komai a ranta ba ta le'ka 'daki nan ma wayam.
"To wai ina Umma ta shiga?" Ta tambayi kanta ganin tsayuwar bazatayi mata sai ta tuno da gidansu Harira ma'kotansu ne, kuma suna mutunci dasu, don duk unguwar kaf babu wanda ke shiri dasu in banda gidansu Harira.

Da azama ta zura slipas 'dinta, ta fito tayi gidansu Harira.
Koda ta fito Malam Hamisu ya kama masifa yana cewa suyi su fito.

Ko bi ta kansa batayi ba ta shiga da sallama, Inna Maria na tuyar 'kosan kalaci Harira na dama kunu, suka juyo suka kalleta bayan sun amsa sallamar.
"A'a Hadiza ce?" Inji Inna Maria tana murmushi.

Khadija tayi ya'ke tace.

"Ni ce Inna, ina kwana?"

Inna ta amsa tana tambayar ya mamanta.



Nan da nan hankali Khadija ya da'da tashi gaba 'daya ta rasa sukuni, ta fara kuka.

Itama Inna hankalinta a tashe ta shiga tambayar ta abinda ya same ta. Kafin Khadija ta soma magana Malam Hamisu ya shigo babu ko sallama, nan da nan ya fara yarfa mata masifa.

Inna ta mi'ke a fusace tana cewa.
"Lafiya malam zaka shigo gidan matan aure babu ko sallama?"
Ko a jikinshi ya cigaba da masifa yana cewa su Khadija yake jiran su kwashe kayansu tun 'dazu suna neman raina mishi hankali.
Inna ta kalli Khadija tace.

"Hadiza me nike ji haka? Wannan wace irin magana ce haka malam, ina Hasiyar wai?"
Khadija ta 'kara fashewa da kuka tace.

"Nima bansani ba"
Da mamaki Inna tace.

"Bangane baki sani ba? Hadiza kiyi mani bayani mana yadda zan fahimta?"
Khadija na kuka tayi ma Inna bayanin komai tun daga farko har 'karshe.

Inna tayi salati gami da tafawa ta kamo hannun Khadija tana fa'din...

"Mu je gidan in gani"
Dukkansu suka fito kowa hankali a tashe, aiko suna zuwa suka duba gidan tas ba Umma ba alamar ta.
Abin mamaki abin al'ajabi wannan abu da 'daure kai yake shin ina Umma ta shiga tambayar da ni kaina bansan amsar ta ba.
Inna ta daure ta lallashi Khadija akan ta kwashi kayanta ta koma gidanta in yaso sai ta tayata neman Hasiya, ita tayi al'kawarin ri'ke ta tsakani da Allah, har Allah ya bayyana musu ita.
Khadija tayi na'am kuma ta gode ma Inna da taimakon da zatayi mata.
Nan da nan Inna ta taimaka mata suka fiddo kayansu tas, Khadija ta mi'ka mishi mukulli ya amsa yana fa'din.

"Na rabu da jarababbu Allah ya raka taki gona"
Khadija ta girgiza kai a yayin da wasu hawayen masu 'daci suka gangaro mata, "Allah kayi mana da kyau"

Ta fa'da a zuciya.
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™
MSBπŸ’–
Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*
Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.
*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*
08
Bayan sun shige gida suka tarar Harira ta gama kwashe 'kosan ta zuzzuba ma kowa nashi, kunun ma kowa ta zuba mishi nashi a kofi, Inna ta kali Harira tace.

"Ki ba Hadiza nawa nina 'koshi"

Khadija zatayi magana Inna ta 'daga mata hannun alamun ta zauna taci kawai, babu yanda ta iya don bazata iya jayayya da Inna ba. Ta kai 'kosan bakinta wanda takejinsa kamar madaci, ta tauna ta ha'diye da 'kyar daidai Lokacin da wasu hawayen suka gangaro.
Inna ta kalleta cike da tausayi ta dawo kusa da ita ta zauna, tayi ta lallashin ta da nasiha mai ratsa zuciya, har ta samu ta saki ranta har ma ta cigaba da cin abicinta.
Ana haka duk yaran suka fito cikin kayansu na islamiyya, kalar sararin samaniya (sky blue ), su shidda ne, mata hu'du maza biyu.

Babbar mai suna Nabila zata kai kimanin shekara goma sha shidda zuwa sha bakwai, sai mai bimata Jamila ita kuma shekarunta sha hu'du, sai masu bi mata 'yan biyu Hassan da Hussaini sai dai basu kama ko ka'dan hasalima Hassan yafi Hussaini haske, sai Amina mai shekaru tara sai auta Salima ita kuma tana da shekara shidda.
Duk gaba 'daya suka fito, Khadija ta kallesu sun mata kyau, sai ta dinga hango kanta cikin irin kayan, inama ita ce take zuwa makaranta?
Bugun farko kallon da taga Nabila ta watso mata na raini, dama tasani tun fil'azal Nabila bata 'kaunar ta, ko zuwa tayi ta dinga hararar ta kenan ko kuma ta bita da 'kananan maganganu tana kiranta mayya ko mai kama da aljana mummuna.
 Maganganun suna matu'kar 6ata mata rai, sheyasa kwata kwata bata 'kaunar Umma ta aike ta gidan ta ha'du da Nabila.

Ita ta rasa dalilin wannan tsana. Amma duk sauran yaran sun gaishe ta fuska a sake.
Lokacin Inna ta shiga 'daki ita kuma Harira (kanwar mahaifinsu) ta tafi gida da yake kusa suke tana yawan zuwa ko kuma ta shigo ta taya Inna aiki.
Khadija na nan zaure duk ta takura da kallon da Nabila ke watso mata, sai ta sadda kanta 'kasa, sadda zata 'dago sai sun ha'da ido, ita kuma Nabila ta watso mata harara, haka dai ta gama cin abincin a daddafe ta mi'ke ta kwashe wadanda aka gama amfani dasu ta tafi wurin wanke wanke don wankewa.
A lokacin Inna ta fito daga 'daki da shirin unguwa alamun fita zatayi, ta kalli yaran gaba 'daya har Khadija tace musu zataje barka ta dawo in sun gama su wuce islamiyya.
Bayan fitar ta da kamar minti shidda duk suka mi'ke suka 'kara shiryawa suka wuce makaranta, ita kuma Nabila ta matso dab da Khadija taja mata kunne tana fa'din.
"Uban me kikeyi a nan gidan, mayya kawai wallahi ki kiyaye ni kinji na gaya maki aljana kawai"

ta 'kara jawo kunnen da 'karfi har sai da Khadija ta saki 'yar 'kara, ta ran'kwashe ta a kai sannan taja tsaki ta fice ta barta nan.
Khadija ta sosa kanta yayin da wasu hawayen suka zubo, tana goge 'kwalla har ta samu ta kammala.
Ta dubo tsintsiya ta fara share gidan tas, ta gyara ko ina na tsakar gidan gwanin kyau kasancewar siminti ne sai wurin yayi 'kwal.
Ta gama ta 'dauko tabarma taja can gefe ta shimfi'da ta kwanta, tuno da Ummanta yasa tayi saurin tashi zauna, tana tunanin a wanne hali take ciki yanzu.
* * *
Mami na zaune saman kujera tana nazarin wani Hadith, taga Heenad ta shigo ba ko sallama as always, ita kam Allah yasani tayi iya 'ko'karinta na ganin yarinyar nan ta dawo kan hanya amma kullum kamar ana 'kara tunzura ta.
Don haka sai bata tanka ba, itama Heenad 'din bata ko kalli inda mahaifiyar tata take ba hasalima bata san da mutun a wurin ba.

Don ranta a matu'kar 6ata yake da jin haushin mutumin nan.
Tana shiga 'daki ta fa'da toilet tayi wanka ta fito 'daure da towel pink colour, ta zauna gaban mirror ta shafa mai da turaruka masu matu'kar 'kamshi, sannan ta gyara gashinta wanda ya sauko saman kafa'dunta, aka wani shafa mai aka tufke shi can tsakiyar kai da pink ribbon, Heenad ma'abociyar son pink ce.
Ta sanya riga da wando marassa nauyi sosai rigar pink da wandon 3qtr purple, tayi kyau sosai.
Ta hau saman gadonta ta bu'de wayarta, ta shiga Instagram tana kallon pictures kawai sai ta ci karo da wani picture, anyi tagging mutumin, sannan a 'kasa an rubuta "happy birthday bro".
Ta 'kura ma hoton ido sam ta kasa dena kallonsa, tace a ranta.

"Amma kam yana mani kama da wani" tayi ta tunani amma sam ta rasa inda ta sanshi.

Ba tare data San tayi ba kawai ta danna account 'dinsa sai dai kash private yake, tayi tsaki gami da fita daga Instagram 'din baki 'daya.
Amma sai me? Sai ta tsinci kanta da son 'kara ganin mutumin ta 'dauko wayar ta gami da shiga Instagram 'din sai dai  kaf ta duba bataga post dinnan ba, tayi tsaki gami da wurgar da wayar can gefe.
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*
09
* * *
Zaune yake a office 'dinsa yana duba time 'din da zaiyi surgery gobe, yaji an shigo masa office babu ko sallama.
Ya 'dago a hankali ya kai dubansa gare ta.

Sanye take cikin 'kananun kaya, body hug riga ba'ka da ba'kin wando skin tight, kannan yasha 'karin gashi, takalmin 'kafarta mai mugun tsini ba'ki, ya kai dubansa ga fuskarta ansha uban makeup da janbaki kai kace ba gobe, da sauri ya kauda face 'dinsa saboda shi a rayuwa ya tsani wannan shafe shafen yafiso yaga mace ta zama natural. Ya 'daure fuska cikin harshen turanci yace.
"Ki koma kiyi sallama har sai na baki izinin shigowa"
Ta kalle shi galala cikin mamaki, cikin ranta tace.

"Wanna guy 'din ya gama raina min wayau, sai dai yana iya tunda ni na kawo kaina"
Ta koma tana taku 'dai'daya duk illahirin jikinta motsi yake, sam bata burge shi ba sai ma 'kara tsanarta da yayi.

Ta fita wajen tare da kullo 'kofar ta 'kwan'kwasa, ya 'dauki tsawon minti 'daya yana waya sai da ya kammala sannan yace.

"Yes? Come in"
Ta shigo duk da ta 'kule sai da tayi sallama, ya amsa sallamar gami da nuna mata wurin zama.
Ta zauna tana mishi kallon yaudara irin na 'yan matan duniyar da idon su ya gama bu'dewa.
Ba annuri a fuskansa yace.

"Me kika zo yi a nan?"
Ta rausayar da kai tare da kallallama murya cikin sigar shagwa'ba ha'de da yaudara tace.

"Haba yayah banida damar shiga office 'din yaya na kuma? Tana wani kashe masa ido.
Da yake shima miskilin mutum ne sai kawai yace mata.

"Asibiti ba wurin zuwa bane anyhow, sai ki bari idan na koma gida sai kiyi yanda kikaga dama, don haka please leave"
Ya fa'da tare da nuna mata 'kofa.
Badiya ta 'kule iya 'kulewa ta mi'ke jiki babu 'kwari tana mai jin zafi abinda yayi mata.
Ta juyo zata sake magana yace.

"Please leave"

 Ta fice kamar zata tashi sama.
Ya girgiza kai gami da 'daga shoulders 'dinsa yace.

"Allah ya sauwake"
Daga haka ya cigaba da abinda yake.
Badiya na fitowa ta fashe da kuka tare da 'dauko waya don kiran yayar tata.
Basu ko gaisa ba ta koro mata bayanin cin kashin da tasha yau.
Hajiya Abu ta 'kyal'kyale da dariya tace.

"Sha kuruminki tawan, ai yayi ka'dan kuma wallahi tilas ya soki don haka ki kwantar da hankalinki ki sa a ranki Adnan naki ne ke ka'dai har abada.
Bayan sun gama wayar Badiya ta saki murmushi ta lumshe ido tana fa'din.

"I love you so much Adnan Allah ya nuna min ranar aurenmu"

Daga haka ta shiga mota tana mai jin da'din kalaman yayar tata.
* * *
'Karfe tara da minti hamsin Inna ta shigo gidan, Khadija na zaune saman tabarma idanunta sunyi luhu luhu alamun taci kuka, cikin tauyawa Inna ta kalle ta tare da zama kusa da ita ta kira sunanta.
"Hadiza, lafiya kuma bana hana ki kukan nan ba? Ki kwantar da hankalin ki, bi izininillahi ta'ala za'a ganta kinji?"
Ta girgiza kai tare da 'ka'kalo murmushi tace.

"Nagode Inna"
Inna tayi murmushin itama ta mi'ke da niyyar shiga 'daki mai gidanta ya dawo.

Da sauri ta tarbo shi tare da amsar ledar hannunsa tana mai sannu da dawowa.
Khadija ta mi'ke ta gaishe shi cikin ladabi sannan ta dawo ta zauna ta cigaba da sana'arta wato tunani.
Bayan sun shiga 'daki Inna ta kalli mai gidan nata da ke shan kunu tace.

"Mai gida dama akwai maganar da nakeso muyi"

Ya tattara hankalinsa gare ta yace.

"Na'am ina jinki Maria"

Nan Inna ta kwashe komai kaf ta fa'da masa ta kuma ce masa Khadija zata cigaba da zama dasu har Allah ya bayyana ta.
Ya jinjina kai cikin tausayin Khadija yace.
"Ha'ki'ka samun mace kamar ki a wannan zamanin da wahala don haka ba abinda zan ce miki sai Allah ya saka miki da alkhairi ya taya mu ri'ko, Allah kuma ya bayyana Hasiya"

Ta amsa da "Amin"
Ya mi'ke yana fa'din.

"Bari naje na sanar da mai gari ko da akwai taimakon da zasuyi mana"

Tace "haka ne Allah ya bada sa'a"

Yace "Amin"
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

10
Bayan fitar Malam Sunusi (mijin Inna Maria) da kamar awa 'daya Inna ta fito don girkin abincin rana, ganin Inna gaban murhu tana faman hura wuta ya sanya Khadija saurin mi'kewa taje ta kama mata.
Lafiyayyen tuwon dawa miyar ku'bewa 'danya ta sha kifi, Inna na tsakar kwashe tuwon yaran gaba 'daya suka dawo, suka gaida Inna da Khadija tare da yi musu sannu da aiki sannan suka shige ciki.

 Ciki kuwa harda Nabila ita har murmushi ta sakar ma Khadija, abin ya bata mamaki matu'ka koda yake ai duk rintsi bata nunawa a gaban Inna sai bayan idonta.
Bayan sun chanza suka fito lokacin ana kiraye kirayen sallar azahar, a lokacin su Khadija sun kammala tas har ma sun gyara wurin don haka kowa yaje ya 'dauro alwalla don gabatar da sallah, bayan sun gama aka ba kowa abincinsa.
Haka Khadija ta cigaba da rayuwa batada wata matsala sai ta tunanin Ummanta wani lokaci tayi ta kuka ita ka'dai idan ta tuna basusan halin da take ciki ba.

Kowa na nuna mata so, sun 'dauke ta tamkar 'yar uwar su ta jini, haka Inna da Malam Sunusi suka ri'ke ta tamkar 'yar cikinsu sam basu nuna wariya a cikin 'ya'yansu, kome zasuyi musu to harda Khadija suke ha'dawa.

 Kuma Malam Sunusu ya sanya ta islamiyya tare suke zuwa su dawo tare. Hakan ba 'karamin farin ciki ya sanya ta ba, don haka ta dage sosai tana karatu bil ha'ki, kullum addu'ar ta Allah ya saka ma mutanen nan da gidan aljanna, don sun mata 'kokari a rayuwa.
Matsalar ta 'daya bayan ta Ummanta sai Nabila, tsangwama, hantara na yau daban na gobe daban, musamman idan Inna ta fita nan zata dinga zaginta tana mata gori kala kala, ga wani irin mugun kishi tana yi idan suka fita bataso wani yace yana son Khadija sai ta san yadda tayi ta raba su tare da kulla ma Khadija sharri kala kala. .
Akwai ranar da suka dawo daga islamiyya da yamma suna cikin tafiya wani saurayi ya dinga bin Khadija wai yana sonta ita baiwar Allah ma batada lokacin wasu samari ko wannan ma ha'kuri ta basa akan an mata miji, nan da nan haushi ya kama Nabila ta kama cizon yatsa tana tunanin sharrin da zatayi mata. Aikau dabara ta fa'do mata.
Bayan Khadija da sauran yaran sun shige gida, Nabila ta tsaida saurayin nan ta ce.
"Bawan Allah bakasan matsalar dake tattare da yarinyan nan bane har kake binta?"
Yace.

"A'a wace matsala kuma?"
Tace.

"Cikin shege tayi"
Ya kalle ta a razane yace.

"Karya kike ban yarda ba wannan yarinyar natsatsa ce daga ganinta bazata iya aikata haka ba"
Ta she'ke da dariya tace.

"Naji na maka 'karya amma wannan 'yar uwata ce uwa 'daya uba 'daya ta yaya zan mata sharri?"
Ya jinjina cike da ba'kin cikin rashin Khadija da yayi don yarinyar ta masa dama shi yana son fararen mata marassa jiki masu kyau.

Don haka baice komai kawai ya tafi.
Bayan tafiyarsa Nabila tayi dariya ha'de da shewa tace.

"Ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, na tstane ki Khadija kuma wallahi sai kin bar mana gida"

Daga haka ta shige gida sai wani jin da'di take.
    *2 weeks later*
Wata rana da daddare Malam Sunusi ya dawo ri'ke da ba'kar leda duk suna tsakar gida ana hira, bayan sun masa sannu da dawowa, Inna ta kawo masa abinci tuwon masara miyar kuka yasha man shanu, bayan ya gama ya sha ruwa.

Inna ta kalle shi tace.
"Malam me aka kawo mana?"
Malam Sunusi yace.

"A'a 'yan atamfofi ne guda biyu nagani na siya ma Khadija saboda naga batada da kaya duk sun ko'de ko kuwa?"
Inna tace

"Haka ne Malam Allah ya saka da khairan dama kuwa nima ina ta so Ince Hadiza na bu'katar kaya to ka rigani ai shikenan ta gode wallahi"
Inna ta kalli Khadija da har ta soma bacci tace.

"Ungo nan Hadiza kaya ne Malam yace a baki sai ki 'dinka ko"
Khadija ta mi'ke tana mutsutsuka ido ta washe baki cike da jin da'di ta yi masa godiya sosai da fatan alkhairi addu'ar ta masu da'di sosai.
Banda Nabila dake can gefe ta takure ba'kin ciki kamar ya kashe ta.
"Wato Baba mu bazai siya mana kaya ba sai wannan shegiyar? Mu yaushe rabon da ayi mana kaya? Tilas sai na 'dauki mummunan mataki game da yarinyar nan idan kuwa ba haka ba Allah ka'dai yasan abinda zai mata nan gaba, itama Inna sai na fargar da ita don naga sai wani sonta take yi"

 Ta fa'di tana girgiza kai tare da shawarar matakin data 'dauka, daga nan ta saki dariyar mugunta.
Maryam S belloπŸ’–

No comments: