Sunday 12 February 2017

TAGWAYE NE? Page 11 to 15

TAGWAYE NE? Na Maryam s bello {11 to 15}
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

11
* * *
Yau ta kasance asabar, su Ummi gaba 'dayansu sun tafi kano bikin wasu 'ya'yansu mata har su uku don haka dole suka tafi gidan babu kowa sai Adnan wanda aiki yasha masa kai har ya hana shi binsu.
Yana kishingi'de saman doguwar kujera sanye yake da farar singileti da ba'kin gajeren wando yana kallon tashar sports, yana cikin chanza tasha ta fa'do falon tare da yin sallama, kallonta yayi daga sama har 'kasa sanye take da purple skirt irin mai bu'dewar nan sai farar shirt marar hannu, sai ta na'de kanta da purple kashka 'karami, ya amsa sallamar tare da juyawa ga tashar da yake kallo.

Haushi ya kamata, tace a ranta.

"Wato wannan mutumin don yaga yanada kyau sheyasa yake wula'kanci"

 ta saki tsaki yanda ita ka'dai ke ji.
Ta tako kamar mai tsoron take 'kasa ta samu kujera daidai saitinsa ta zauna ta 'dora 'kafa 'daya kan 'daya, sai tayi pretending kamar kallo takeyi amma a zahiri satar kallonsa takeyi. Ya lura sarai amma sai ya basar saboda bata gabansa. Ta wani kashe murya cike da yaudara tace.
"Yayah dama shawarma da lemu na siyo maka don nasan kana tare da yunwa"
Haushi ya turnu'ke shi, batare da ya kalle ta ba yace.

Yace a ransa (wallahi da 'yar uwata ce da sai na kore ta)

Amma a zahiri sai cewa yayi.
"Nagode kije kici kayanki"
Ta rausayar da kai ha'de da shagwa'ba tace.
"Haba yayah ka daure kaci mana idan kuma bashi kakeso ba naje na dafa maka wani abin"
Ya kalle ta, ji yake kamar ya sha'ke ta ya huta amma sai ya daure ya mi'ke yace idan kin fita ki rufe min gidan sai da safe"



Daga haka ya wucewarsa ya barta nan cikin ba'kin cikin da tunda uwarta ta haife ta bata ta6a shiga ba.
Daga 'karshe ta mi'ke jiki babu 'kwari tana mai tunanin ko ta halin 'ka'ka ne sai ya aureta koda kuwa gawarta za'a kawo to a shirye take da ta aure shi.
* * *
Mami ce ta sauko daga stairs da shirin fita unguwa abinda taji Fatima da Abbanta suke tattaunawa shi yasa tayi saurin tsayawa tana sauraronsu.
"Daddy nifa idan na gama makaranta ba'a nan 'kasar zanyi karatu ba" ta fa'da cikin shagwa'ba.
Daddy yayi dariya.

"Diyar daddy ina kike so kije ko ina ne just say it, insha Allahu kina gamawa zan kaiki da kaina"
Heenad tayi dariyar jin da'di tace.

"Daddy ni nafison London"
Daddy yayi murmushi.

"An gama anything for my little princess"
"Haba Alhaji yanzu da hankalinka da komai zaka 'dauki 'diyarka mace ka fidda ta can wata uwa duniya wai da sunan karatu, duk makarantun da ke nan 'kasar basu ishe ta ba har sai ka fidda ta waje, haba Alhaji kadai chanza shawara gaskiya"
"To uwata zo ki fa'da min yadda zanyi, nace zoki fa'da min yadda zanyi" ya fa'da yana crossing hannunsa guda biyun.
"A'a nidai wallahi gaskiya nake fa'da maka a wannan zamanin ma 'danka na kusa da kai ya kuka 'kare ballantana baya kusa da kai yana can wata duniya shikenan ita duk yanda take so shi zakayi mata?"
"Eh haka zanyi mata..." in ji daddy
Mami tace "to wallahi indai ina numfashi babu inda Fatima zataje karatu"
"Sai ki hana ai" ya fa'da fuska 'daure.
Mami don takaici kawai ficewa tayi ta barsu nan.

Tana fita ya kalli Heenad yace.
"Rabu da ita ta gama haushin ta indai kin tabbata can kikeso an gama" ya fa'da yana murmushi.
Itama murmushin tayi tace.

"I know you won't let me down thank you daddy"
"You welcome my princess anything for you" yana gama fa'dan haka ya mi'ke ya fita.
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

12
* * *
    *2 weeks later*
Yau ma kamar kullum su Khadija na zaune da daddare tsakar gida, Inna ka'dai ke cikin 'daki tana sauraron radio.

Malam Sunusi ya dawo ri'ke da ba'kar leda, duk suka gaishe shi ya amsa fuska sake sannan ya shige 'daki, yana zama ya mi'ka ma Inna ledar yace.
"Tsire ne na siyo muku amma Khadija naga kamar batason shi shiyasa na siyo mata balangu yana nan zaki ganshi 'daurin shi daban"
Inna ta kalle shi da mamaki tace.

"Malam kasan Nabila ma batacin tsire amma baka ta6a siyo mata nata daban ba sai Hadiza?"
Malam Sunusi yace.
"In banda abinki Maria baki ganin ita Nabila babba ce? Ai sai tayi ha'kuri da abinda ta samu ko?"
"Ohhh ita Hadiza naga jaririya ce, wai shin Malam meke tsakaninka da yarinyar nan ne don naga sai rawar kai kakeyi a kanta?"
Malam yayi salati yace.
"Haba Maria yanzu ke kina tunanin wani abu ke tsakanina da Khadija?

 Ni ba abinda ke tsakaninmu sai tausayinta da nakeji, ke baki ganin halin da ta tsinci kanta a ciki ne?"
"Bana gani, kai dai Malam inda wani abu kawai ka fa'da basai an tsaya wani 6oye 6oye ba"
"To idan kina tunanin da wani abin kije kiyi tayi niba 'karamin yaro bane da zan tsaya ina miki rantsuwa" yana gama fa'din haka ya mi'ke ya shige ban'daki.
 Inna tace.

"Dama sai da Nabila tace min inbi a hankali, aiko gashi na fara gani, 'dan Adam butulu ka 'dauko shi daga rana ka maida shi inuwa shi kuma ya maida ka ranar tsundum"
Duk wannan abin da ke faruwa kaf yaran naji, Nabila ba abinda take sai dariyar mugunta can 'kasa 'kasa tana jin da'din nasarar data samu wajen wargaza tsakanin Khadija da mahaifiyarsu, yanzu abinda ya rage mata korar Khadija.
Ita kuma Khadija na can lungu ta takure tana kuka mai cin rai.
Daren ranar ko runtsawa batayi ba sai faman tunanin makomar rayuwarta take. Cikin kuka tace.

"Umma kina ina?

Anya zamanta zai yiwu a nan gidan kuwa? Ta tambayi kanta. Kodai na gudu?

 To idan na gudu ina zanje? Babu taba kanta amsa.
Koda asuba bata tashi ba kasancewar tana hutun sallah sai kawai ta kasa tashi, batason lokacin da 6arawo bacci ya saceta ba.
Washe gari tana tashi ta duba agogo, sha 'daya saura, ta mi'ke da sauri tana mamakin irin baccin da tayi.

Ta fito tsakar gida ta wanke bakinta da fuskanta sannan ta iska Inna tana linke kayanta tsakar gida kan tabarma, kayan wankinta ne da suka bushe take linkewa.
Har 'kasa Khadija ta tsugunna kamar kullum ta gashe ta, ba tare data kalle ta ba tace.

"Lafiya"

Taci gaba da abinda take yi.
Khadija tayi zaune zugum, dama tasan hakan zata faru, tana kyarma tace.
"Inn... inna ina su Nabila?"
Inna tayi murmushin takaici ba tare data kalle ta ba tace.

"Suna islamiyya"
Jiki a sanyaye ta mi'ke da nufin tafiya sai kuma ta dawo.

"Inna me za'a yi da rana?"
Saboda ta saba kullum ta kan tambayi Innar abinda za'a dafa.

Ba tare data kalle ta ba tace.

"Abinda duk kike so kije ki dafa"
'Kwalla suka cika mata ido. Wato Inna fushi take da ita akan abinda bata da tabbacinsa.

Tayi tsugunne nan ta kasa tashi sai 'Kwalla ke neman zubo mata amma tana maida su.
Cikin dakiya tace.

"Inna don Allah kiyi ha'kuri idan na 6ata miki rai wallahi..."

Sai kuma tayi shiru.
Inna tace "wallahi me? Ki 'karasa mana munafuka, wallahi kin bani mamaki Hadiza duk hallacin da nayi miki amma abinda zaki sake min dashi kenan?"
Kwakwata Khadija ta kasa fahimtar inda maganar ta dosa, amma kuma ta kasa magana don muryarta tayi rauni, sai kawai ta fashe da kuka dama 'kiris take jira.
A fusace Inna ta mi'ka.

"Naga dai nema kike ki raina min hankali to bari na warware miki, to magana dai ta baza gari cewar jibi za'a 'daura muku aure da Malam, uhm 'dan Adam butulu, Hadiza kin kyauta"
Khadija ta mi'ke a razane tare da dafa 'kirji tace.
"Ni?!!!
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

13

Tana fa'dan haka hawaye na kwarara daga idanunta kamar an bu'de famfo.

Tunda take a rayuwarta bata ta6a tunanin haka daga Baba ba, kuma shi bai ta6a nuna mata wani abu makamancin wannan ba, iyaka tsakaninta da shi sai gaisuwa.
"Anya ba sharri bane ba kuwa?"
Ta furta hakan a zuciyarta wanda batasan cewa ya fito fili ba.

Inna ta mi'ke a fusace tace.
"Sharri? Ni zan miki sharri, kinji kin kallame min miji da kalaman yaudara har ya amince zai aure ki, sannan kizo kice ana miki sharri iye?"
Khadija tayi shiru ta rasa kalmar da zatayi amfani da ita wajen fahimtar da Inna cewar wannan tunanin nata sam ba gaskiya bane, don kuwa babu alamar hakan a tattare da Malam Sunusi.
"Munafuki bayada kama, 'dan Adam butuli kin bani mamaki Hadiza" inji Inna. tana fa'dan haka ta shige 'daki.
Jiki a sanyaye Khadija ta mi'ke ta koma 'daki tana tafe tana jin kanta na juya mata ga wani azababbe ciwon kai, da 'kyar ta lalla6a ta kwanta kan 'yar katifar 'dakin.

Hawaye masu zafi da 'daci suka zubo mata. Ta runtse idonta hawayen na cigaba da zuba.

Itafa maganar kwakwata bata yarda da ita ba, ta yaya hakan zata kasance wai ita tayi kishi da Inna, matar da take kallo a matsayin mahaifiyarta ta yaya zata yarda ta ha'da miji da ita? Wai daga ina labarin nan ya fito, anya gaskiya ne?"

Haka tayi ta tambayar kanta amma bata samu amsa ba.
Ta runtse idonta sadda kanta ya sara mata, ji tayi kamar zai fa'do 'kasa.

Daga nan bata sani ba shin bacci ne ya kwashe ta ko suma tayi.
Can taji saukar ruwa mai 'dan karan sanyi a jikinta, a gigice ta farka tana salati, biji biji take gani kafin a hankali ta dawo daidai, Nabila ce tsaye, Jamila na gefenta ko wace ri'ke da 'kugu kai kace suna jiran dambe.
"Baccin munafunci kikeyi, hankalinki kwance kin bar mahaifiyar mu cikin 'kunci, shegiya hanci kamar bindin biri" cewar Jamila.

Abin ya bata mamaki ko kallon banza Jamila bata ta6a yi mata ba.
"Bar shegiya ai wallahi da ki auri Baba gwara ki fa'da rijiya ki huta don wallahi muddin kika yarda kika aure shi na lahira sai yafiki jin dad'i munafuka algunguma kawai" Nabila ta fa'di tana girgiza 'kafa.
Itadai Khadija tayi shiru tana sauraron su, to wai ma me zatace? Ai batada abin cewa.
"Tun muna shiri da ke ki tattara kayanki ki bar mana gida kar na illata ki, idan kuwa kika za'bi zama nan gidan har aka 'daura aurennan zaki sha mamaki" cewar Jamila.
Nabila abin nema ya samu na ganin Khadija cikin 'kunci da ba'kin ciki. Don haka a ranar Khadija taga rashin mutunci, zagi, cin zarafi, a ranar dai Nabila sai da ta na'da ma Khadija na jaki sannan suka taru itada Jamila suka dinga ran'kwashin ta a kai, sai da suka yi mata garga'di mai tsoratarwa na cewar kar ta yarda ayi aurennan sannan suka 'kyale ta zuciyar Nabila wasai.
Khadija ta dafe kai, tana razgar kuka, kuka take kamar ranta zai fita. Ga ciwon Jiki ga yunwa ko kalaci batayi ba gashi yanzu har uku da kwata. Abincin ma bata marmashin sa, ba'kin cikin da take ciki kuwa ita ka'dai tasan meke mata da'di.
Takwas da minti arba'in na dare Malam ya shigo gidan, Inna na daga bakin zaure tsaye tana jiransa. Yana shigowa tace.
"Ango kasha 'kamshi, angon Hudiza sannu da zuwa, yanzu ina zaka fara zuwa wurin amarya ko kuwa sai kayi wanka?"
Ya kalle ta cikin rashin fahimta yace.
"Bangane ba wace amarya wane ango?"
Inna ta kece da dariya.
"Sirrin 6oye ne ya fito fili, Allah ne ya tona asirinku, wai har zakayi aure Malam bansani ba kuma ka rasa wacce zaka auro sai yarinyar da nake kallo a matsayin 'diyar cikina, kai ko kunya ma bakaji ka auro tsarar Jamila, kai Allah ya kyauta dai"
Malam ya girgiza kai yace.
"Ke yanzu akace miki zan auri Khadija sai ki yarda? Da hankalinki da komai, to wai idan ma nace zan aureta kin isa ki hana ne? Abinda Allah ya halatta min ke kice zaki haramta min"
Inna tayi shewa.
"Ai dama nasani munafukai kawai Allah dai ya tona asirinku.
Malam ya kalle ta da mamaki.
"Yau ni kike kira da munafuki Maria?"

Ya fa'da yana nuna kansa.
Inna tayi shiru.
"To kinyi daidai"
Yana gama fa'din haka ya shige 'daki.
Yana jin sadda take cewa.
"Ga babbar munafuka nan ta 'kumshe 'daki, sai anyi magana ta saka maka na mujiya"
Iyakar abinda Khadija taji kenan, ta 'kara cusa kanta cikin cinya tana kuka mai ban tausayi.
"Zama na nan gidan ba zai yiwu ba tilas na bar gidannan shine mafi alkhairi"
* * *
A restaurant suke zaune itada Abida suna shan lemo, suna 'dan ta6a hira sama sama.



Kamar ance Heenad kalli can ta hango shi yana 'karasowa ciki da alama waya yakeyi. Fuskar da bazata ta6a mantawa da ita ba.

Batasan ya akayi ba sai ji tayi gabanta ya fa'di.

Gaba 'daya ta rasa nutsuwarta.

 Har Abida ta lura da hakan.
Sanye yake cikin 'kananan kaya, riga mai ratsin ja da blue da wando blue, yana waya yana murmurshin da ya 'kara bayyanar da fararen ha'koransa, yayi kyau har ya gaji.
Ya zauna yana duban abokinsa wanda Heenad batajin me suke cewa.

Shima baisan ya akayi ba ya hango ta, nan da nan ya rasa farin cikinsa haushi ya turni'ke, haka zalika shima bazai ta6a manta fuskar nan ba, yarinyar da ta tozarta shi, ta mare shi a a a gaban jama'a.
Ya mi'ke a fusace ya fice daga wurin, zuciyarsa na 'kuna.

"I hate that girl!"
Khalil ya fito da sauri yana tambayar lafiya.

Bai ce komai ba illa shigewa motarsa yayi yace masa.
"Muje na fasa cin abincin"
Itama 'bangaren Heenad haushin kanta taji
"Meyasa na kalle shi?" Ta saki tsaki tare da mi'kewa ta bar wurin, da sauri Abida tabi bayanta tana tambayar lafiya.
Maryam S belloπŸ’–
❤πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

14
Haka Abida ta dinga 'kwalawa Heenad kira har wurin mota, sai da suka isa jikin motor taja ta tsaya tare da lumshe idanunta jingine jikin motarta gabanta na dukan uku uku, Abida ta cimmata tare da dafata.
"Heenad"
Firgit ta bu'de idonta tana kallon 'kawar tata.
"Na'am"

Ta faďa a sanyaye.
"Meyake damunki ne?"

Abida ta fa'da tana kallonta.
"Babu, mu tafi kawai"
Abida zata sake magana kenan ta 'daga mata hannu.

Dole Abida tayi shiru suka shiga mota, bayan tayi dropping nata gidansu ta wuce gida.
Gidan ba kowa sai Hauwa mai aikin Mami, dama ta san Mami ta fita shi kuma daddy yana Lagos wani meeting.
A sanyaye ta zauna kan kujerar da ke 'dakinta, ta rasa meke mata da'di a duniya.

Bata da damar rufe idonta sai ta ga mutumin nan, haushi ya kama ta, ta saki tsaki. Ita a nata tunanin tsanarsa da tayi yasa take ganinsa haka.
Haka ta zauna jugum tana tunani har akayi isha'i. Ta tashi tayi sallah, tana shirin shiga toilet taji shigowar Mami.
Koda ta le'ko yanayin yadda taga Heenad tasan da wani abu. Amma sanin halin 'yar tata yasa bata zurfafa bincike ba.
*1:30 AM*
 Heenad na kwance tayi ta juye juye, sam bacci ya 'kauracewa idanunta, ta rasa yadda zatayi da tunanin mutumin nan wanda take 'dauka duk cikin tsana ce.

Daga 'karshe data gaji sai ta mi'ke zaune tana son yin ya'ki da zuciyarta akan lallai ba so bane tsana ce.
* * *
Khadija ta gama yanke ma kanta shawarar 'karshe cewar batada wata dabara illa ta gudu, saboda zamanta gidan bashida wani amfani, da wane zata ji?
Can 6angaren ga rashin ummanta, nan 6angaren kuma ga Inna da take shirin yin kishi da ita wanda har abada bata fatan hakan ta kasance a gareta Koda kuwa a mafarki ne.
 sannan ga uwa uba Nabila data 'daura mata karan tsana babu gaira babu dalili. Ta yaya ma zata yarda ta aurar musu uba, ta yaya ma zata yarda hakan ta kasance, ina! Abu mafi a'ala a gareta shine ta gudu kawai.

Wannan shine shawarar 'karshe data gama tsarawa kanta.
Don haka da sauri ta tashi dama kayanta a shirye suke cikin leda, ta duba 'yan ku'da'den da take dasu wanda tun Ummanta nan nan ta bata ajiyar su, ta duba taga kowa bacci yake dama 'dakinsu 'daya dasu Nabila, ta zura hijabinta har 'kasa, cikin sanďa ta tako bakin 'kofa tana kuka, ta fito sauri sauri, da cimma 'kofar zaure, ta zare sakatar a hankali ta fito.
Garin duhu sai hasken farin wata ke haskawa, kamar daga sama ta jiyo muryar Malam Sunusi yana fa'din.
"Waye nan...!
Da sauri ta bar wurin tare da toshe bakinta da hannunta kar sautin kukanta ya fito, ta 6uya bayan wani kwango, tana kuka a hankali.
Cike da mamaki Malam Sunusi ya fito yana mamakin wanda ya bu'de kofa da tsohon darennan.

Ya duba ko ina ya tabbatar da ba wanda ya shigo musu gida sannan yayi bismillah ya rufe 'kofa.
Khadija ta duba gabas, yamma, kudu da arewa tace.
"Ina na dosa?"
Ta fito da sauri ta bi gabas, ga tsoro ga fargaba amma a haka ta dake ta yi ta sauri ba tare data san inda ta dosa ba.

Tayi ta tafiya ga duhu ga ba ka jin motsin kowa sai tsuntsaye, sai da tayi tafiya mai nisa ta zauna don ta huta cike da tsoro dama Khadija badai tsoro ba.
Bayan minti kusan takwas ta dinga jin hayaniya da kamar mutane na tafiya, gabanta ya bada ras!

Sai zare idanu takeyi.
Samari ta gani irin 'yan iskan nan kusan su biyar majiya 'karfi.
Ta mi'ke da niyyar ta 6uya ashe sun hango ta bata sani ba, dayan ya kalli wani daga gani ogansu ne yace.
"Oga kaga wata 'yar 'kwaila?
Ogan cikin wata 'katuwar murya ta 'yan iska yace.
"A'ah ! Ina take?"
Mutumin yace.
"Oga ta ha'du fa amma cikin hijabi take daga gani ustaziya ce"
Ogan ya kece da dariya yace.
"Ba komai a kawo min ita"
Jin haka yasa gaban Khadija yayi mummunan fa'duwa koda Khadija ta sa6i jakarta ta cire slipas 'dinta ta kece a guje, gudu take suna gudu, ita tunda take bata ta6a sanin ta iya gudu haka ba.
Saida ta fito bakin titi taja tsaya tana shesheka, a gajiye gabanta ga na cigaba da fa'duwa.
A lokacin kuma taji an fara kiran sallar farko wato ta asuba kenan.

Ita kanta batasan iya adadin gudun da tayi ba.
Ganin ba mai binta yasa ta cigaba da tafiya a gajiye, can ta hangi wasu mutane suna alwalla, da sauri ta isa garesu.
Wani dattijo ne a tsugunne yana alwalla, sai data jira ya gama ta gaishe shi sannan tace.
"Baba don Allah ina tambaya ne, shin ina ne nan?"
Ya kalleta da mamaki yace.
"Yarinyar me kikeyi a waje da sanyin asuba kina mace?"
Ta yi shiru kamar me nazari can tayi saurin cewa.
"Tasha nike nema"
Ya numfasa yace.
"To, ga tashar nan gabanki amma sai 'karfe bakwai ake tafiya, shin ina zaki?"
Ta rasa me zatace.

Can dai ta sauke ajiyar zuciya tace.
"Ina suke zuwa?"
Ya maida dubansa gareta, kamar bazaiyi magana ba, can kuma ya mi'ke tsaye yana gyara hannun rigarsa yace.
"Kaduna da kuma Habuja, wane zakije?"
Da sauri tace.

"Habuja"

Ita kanta batasan meyasa ta za6i Abujar ba, hasali ma batasan ina ne haka ba amma tunda batada za6i dole ta za6i 'daya.
Ya numfasa yace.
"Shikenan ga wata 'yar rumfa can akwai mata a wurin, kije ki jira lokacin sallah yayi, sai ki jira gari ya waye sai mu tafi muma duk 'yan jiran Habujan ne"
A sanyaye tace.
"To"
Maryam S belloπŸ’–
πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ❤

    πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œ

        πŸ’šπŸ’™

            πŸ’™

MSBπŸ’–

Dedicated to Faty Mansur and Zainab Bapullo ILYSM

*(zeebee)*

*(Xarah)*

Sadaukarwa ga Rashidat A Kardam, Allah ya bar zumunci amin.

*πŸ’•Tagwaye ne? πŸ’•*

15

Khadija na zuwa cikin 'yar rumfar tayi tsaye saboda bataga wajen zama ba, mata ne aqalla zasu kai su goma sha uku yara da manya, wasu ma sai sharar bacci sukeyi hankalinsu kwance.
Ta russuna tare da takure jikinta wuri 'daya sakamakon wani sanyi da iska da suka bugo ta.

Ta runtse idanunta yayinda wasu hawayen suka gangaro mata a kunci, tuno da rayuwarta ta baya da kuma wadda zata fuskanta nan gaba, batasan me zata iske ba, da irin kalar rayuwar da zata fuskanta a gaba ba.

Ina zata dosa, ga ba dangin iya ba na baba, to ko dai ta fasa tafiya ne?
Kafin ta lalubo amsar taji an dafa kafa'dunta. Firgit ta dawo daga duniyar tunani, wata mata ta gani ba babba bace sosai zata kai kimanin shekara talatin da 'daya (31)
"Baiwar Allah ki tashi kiyi sallah naga lokaci har ya na neman wucewa"
Ta mi'ke da sauri tana fa'din.

"Subhanalillah, ban ankare ba"
Da sauri ta nufi wani 'dan kango nan taga matan na shiga akwai ban'daki daga baya, ta zagaya ta kama ruwa, sannan ta dawo ta tari ruwa ta 'dauro alwalla, tayi sallah.

Tana nan tana lazumi har gari ya waye.
Ta mi'ke ta koma 'dan nesa ta matan nan ta zauna ta cigaba da tunani.

Sun sha zama don kuwa suna nan har kusan takwas da minti sha bakwai (8:17 AM), sannan taga an fara taruwa ciki harda direbobin motocin da zasu kaisu.
Suna nan suka ji an fara kiran "Abuja! Abuja!! 'Yan Abuja su garzayo kafin tara zamu tafi. Haka nan taji gabanta ya fa'di, taji hawaye na neman zubo mata, da sauri ta maida su ta mi'ke ta kwaso kayanta, ta nufi motar da zata kaisu.

Bayan ta biya ta ajiye kayanta ta shiga ta samu wuri ta zauna jugum tana raba idanu karo na farko data ta6a shiga mota, mintinsu goma motar ta cika tap da mutane kowa ya gama shiga. Ba'a fi minti uku ba motar ta fara tafiya.
Tafiya tayi tafiya, tun Khadija na sa ran zasu isa har ta haqura, tayi bacci ta tashi, taga basu isa ba ga gajiya kamar ta kurma ihu taji da'di, kafafunta suka sage, ta rasa inda zata saka ranta, ga yunwa.
Sai yamma lis suka isa, kasancewar sunyi biye biye saboda sallah.

Bayan sun fito, ta 'dauki kayanta, sai raba idanu take, batasan kowa ba, bata san ko ina ba, ba dangi iya bana baba.
"Nayi ganganci meya kawo ni nan garin?"
Ta furta kamar zatayi kuka, yanzu abinda ya fi damunta yunwa, ko gani batayi.

A haka ta cigaba da tafiya, tana tafe tana har'de kafa, kamar zata fa'di.

Ita ko ruwa ne ta samu ta sha ko taji dama dama.
Ta cigaba da tafiya, sai da tayi tafiya mai nisa ta hango mai wani shago, da sauri ta 'karasa tana zuwa ta shiga da sallama.

Saurayin dake sanya lemon gwangwani cikin firij, ta gaishe shi da ladabi sannan tace.
"Don Allah ruwa zaka bani"
Ya kalle ta a wula'kance yace.
"Wane iri?"
Da mamaki tace

"Dama ruwa kala kala ne sai wanda ka za6a?"
Yace

 "Malama idan baki saye ki kama gabanki kar ki raina ma mutane hankali"
Da sauri tace

"A bani ko wane nagode"
Ya mi'ko mata kwalbar Faro yace

"Dari biyar kenan"
Ta zaro ido

"Dari biyar?

Ruwan?"
Ita ina taga 'dari biyar ku'dinta sun kare naira 'dari ta rage mata.

Ganin mutumin baiyi kama da kalar masu mutunci ba yasa ta ha'kura ta mi'ka mishi ruwan ta juyo.
Ta cigaba da tafiya tana waige waige ko zata samu inda zata wani ruwan.
Haka tayi ta tafiya duk inda taje ba ruwan 'kasa da naira 'dari biyu, haka ta gama wahalarta bata samu ba, daga 'karshe ta samu wata bishiya ta zauna tana maida numfashi.
* * *
Yanda Heenad taga rana haka taga dare sam bacci ya 'kauracewa idanunta.

Washe gari koda Mami tazo tashinta ta tafi makaranta cewa tayi batada lafiya bazata je ba, Mami tayi magiya tayi fa'dan amma fir Heenad tace batada lafiya bazata je, dole daga 'karshe Mami ta 'kyale ta.
Ta 'kyar ta 6a66aka ta yi wanka ta sanya kaya marassa nauyi ta sauko wajajen 'karfe na safe.

Lokacin Mami ta fita aiki sai Hauwa ke goge goge.

Hauwa ta gaishe ta, bata ko amsa ba, as always dama ba amsawa take ba, inda sabo ta saba.
Ta zauna don karyawa, farfesun naman kai ne da soyayyar doya da 'kwai da kuma plantain.

Ta zuba ta tsakura ta barshi nan.

 

Da sauri Hauwa ta dawo tace.

'Ya baki ci ba? Ko ayi miki wani abin?"



Ta girgiza kai tace

"No barshi kawai na qoshi"
Bayan ta gama ta koma sama ta cigaba da tunanin mafita.
* * *
Ya bubbuga 'kasa ya kallesu yace.

 

"Ga nasara nan amma sai kin dage saboda mutumin da taurin kai yake"
Hajiya Abu ta kalle shi da suri tace

"Yauwa Malam a taimaka ya sota kuma ya zamana bayajin maganar kowa sai tata ma'ana dai sai yanda tayi dashi hartta mahaifiyarsa"
Malamin ya she'ke da dariya yace

An gama kada ki damu wannan ba wani abu bane, amma da shara'di"
Ta gyara zama tace

"Menene shara'din? Fa'di kawai"
Ya kece da dariya yace

"Zaki iya kuwa Hajiya?"
Hajiya Abu tace

"Koma meye zanyi indai saboda Badiya ne"
Ya girgiza kai ya soma magana.

Maryam S belloπŸ’–

No comments: