Wednesday 30 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 30

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 30}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Dama ance duk abinda ka shuka tou shi zaka girba, Doctor din ne yayi kanta yana kokarin bata hakuri akan wannan kaddara ce kuma ay cuta ba mutuwa bace...kallonshi ta tsaya yi tana girgiza kai idanunta kuwa jajir wane garwashi ta daga masa hannu "Kar ka kuskura kazo inda nake! Nasan wannan result din ba gaskiya bane, bana dauke da wannan cuta don haka ban yarda da kai ba..." Mikewa ta fara kokarin yi Doctor din yace "I know da wahala ka yarda saboda wannan cutar ba abu bane me kyau, sannan ita survival rate dinta is zero percent amma idan har Allah yaso sai kiga kin warke, the best thing da zakiyi shine medication da gaggawa, in ba haka ba zata cigaba da kara yaduwa ko ina, hakuri zakiyi kizo ayi referring dinki to team of doctors don su fara baki taimakon gaggawa..." Wata irin tsawa ta daka masa "Tou ay sai kazo ka kasheni ingani! Komai zaka fada bazan taba yarda inada wannan cuta ba don haka kaga tafiyata!" Tana fadan haka ta fice daga office din, Doctor din tsaye yayi yana binta da kallo, adaidaita ta tsaida inda ta fada masa sunan unguwar su nan ya kaita, yanzu ita talauci zata koma tsundum? Saukinta ma tanada yan kudade a account dinta zata fara amfani dasu kafin tasan nayi, bakin lungun gidanta ya sauketa nan tabi unguwar da kallo ganin a can inda take ko kare gareta bazata kawo shi wannan unguwar ba, babu abinda ke tashi sai warin kwata, dod'e hanci tayi ta biya shi kudinsa sannan ta nufo ciki tun a bakin kofar gidansu taga dogarawa suna sauke mata kayanta babu abinda suke sai cilli da akwatinanta, da sauri ta karaso tana fadin "Kayan nawa ne aka wulakanta min su haka?" Babu wanda ya tanka mata a cikinsu sai bayan sun gama watsa mata kayanta tatas sannan suka kalleta "Mai martaba yace baya son ganin ko tsinkenki a gidansa sheyasa ya bamu umarni da mu kawo maki kayanki, bayanson ki sake taka masa koda kofar gida ne," suna gama fadan haka suka shiga mota suka tafi, kasa kwakkwaran motsi tayi, ta juma a tsaye kafin ta tako a hankali ta bude kofar gidanta wacce duk sha wahalar duniya, tana budewa ta dinga daukar kayanta tana shiga dasu bata damu da yadda yan unguwar ke kallonta ba, bayan ta kai ta shige ciki tana kare ma gidan kallo, anya zata iya rayuwa a cikinsa yanzu kuwa? Wannan gidan ko karenta bata iya kawowa, gidan wani dan kut dashi daga tsakar gida sai daki daya sai bandaki da kitchen sai kuma zaure, zubewa tayi kasan gidan tana zubar da hawaye, wayarta ta dinga jin alert tana dubawa taga transactions kala kala kamar an mata hacking account, kara dubawa tayi taga da gaske an yashe ta tas, hannu ta dora bisa kai ta fasa wani irin ihu kafin ta saki kuka mai cin rai....

Haka Karimah tayi hakuri ta cigaba da rayuwa cikin gidannan batada kudi gashi da kyar ma take samun cin yau dana gobe, yan unguwarsu kyamarta suke yi don bayan yan kwanaki sai ta fara ganin wasu kuraje na fito mata a jiki masu ruwa da wari, ga cikinta dake kumbura kamar wata mai ciki wata tara, gashi batada kudin zuwa asibiti abinci ma da kyar take samu ta ci sau daya a rana.

3 Months Later...

Daga dakinta ta fito tana faman jan kafa cikinta ya girma ya kumbura kamar wanda aka aje yaya goma a ciki, a bakin kofar dakin ta tsaya tana kokarin maida numfashi sabida yanzu ko taku biyu tayi sai ta dunga jin kamar zata suma, ta kai kusan minti goma tsaye tana numfashi sama sama, yau dai taga alama numfashin bata baida niyyar daidaita don kullum ta kanyi kamar minti goma zuwa sha biyu kafin ta samu numfashin ya dawo amma yau abin ya faskara, a dalilin haka ne zufa ta dinga tsatsafto mata ta ko ina anya ba mutuwa zatayi ba?Ta tambayi kanta, ganin dai abun bana karewa bane yasa taja jiki tana jin kamar cikinta zai fado tsabar yadda ya kumbure, bandaki ta shiga tayi wanka ta fito a tsakar gida ta zauna saboda wani irin zafi keda akwai a cikin dakin ga kurajen jikinta duk suk chabe suna mata kaikayi, jingina tayi da bango tare da numshe idanu nan da nan baccin wahala ya dauketa... tana kwance sai tayi mafarkin wai tana tafiya cikin daji a tsorace tana kalle kalle sai kyarma takeyi, wai sai tafiya takeyi hanyar dajin baya karewa ga wani bala'in duhu ga kishirwa tana ji, can dai sai taga wani pampo ta tafi da sauri har ta kusa zuwa wurin sai kawai taji kafarta zata fada cikin wani katon kabari wanda yake a bude, wasu hannaye masu zara zaran akaifa taji sun chafko mata kafa take ta fasa wani irin gigitaccen ihu, haka taji ana ta janta cikin kabarin nan har suka kai can cikin ramin mai zurfin balai, kawai suna zuwa sai kawai taga wata mata ta fito mata da fararen kaya duk jikinta haske ne daga kanta zuwa kafarta, a tsorace take ja baya ganin Ammin Hoodah, takowa tayi kusa da ita tace "Kadan daga cikin abubuwa da kika shuka ne suka fara tasiri akanki! Kin kasheni kin dauka kinci bulus? Kin zo kin bi bokaye kinbi malamai kinbi yan bori! Kin azabtar man da ya! Kin asirce sarki! Hahahaha! Tou kadan daga cikin abubuwan da kika fara shukawa ne kike girba!" Bat ta bace, kalle kalle ta farayi a tsorace. Tana tsaye sai ga wasu zombies sun taho kansu karkace badai kyan gani masu kama da aljannu, nufar ta sukayi gadan gadan suna fadan "Ki tuba ga Allah! Ki nemi yafiya ga wadanda kika cutar! Ki tuba kafin lokaci ya kure miki! Ki tuba, ki tubaaaa....." 

Suna gama fadin haka suka wani daga ta sama suka sake jefa ta cikin wani rami dake cikin kabarin, wata irin muguwar faduwa tayi ji kake tim! Kanta sukayi kuma gadan gadan suna fadin "This is your home in baki tuba ba!" Suka fada suna nuna mata wata wuta dake tashi mai shegen zafi, wadda tafi ko wace muni ce ta wani irin caka mata akaifa wata irin kara ta saki tana tura jikinta baya a tsorace, wata irin farkawa tayi jikinta babu inda baya kadawa zufa kuwa kamar an mata wanka, numfashi take ja tana faman zare ido "Sun kamani! Sun kamani!!" Abinda kawai take iya fada kenan tana faman goge zufa...

*******

Zarah ta riko mata hannu wasu sabbin hawayen na taruwa cikin idanunta tana girgiza kai itama haka Khadija ta tsaya tana kallonta cikin ido kafin Zarah tace "Kinyi gaganci da kika bari soyayyar wanda nakeso ta kama maki zuciya, meyasa kika bari zuciyarki ta yaudareki? Tou ki bude kunnenki da kyau ki saurareni da kunnen basira, Yaya Ashraf is mine and mine alone, babu abinda kika isa kiyi, ita soyayya ba'a forcing mutum yayita... ke baki isa kizo ki tursasa mashi dole sai ya soki ba, ko yanzu nasan am step ahead of you saboda ni yake so bake bake ba kisa wannan a ranki, ni yanzu hankali na a kwance yake saboda nasan bakya daga cikin kalar matan da Yaya Ashraf yakeso, sheyasa tun tuni nake nuna maki mace anasonta kamila mai al kunya, natsatsiya mai kamun kai ke ki fada man a ciki wanene kike dashi? Bakida ko daya baki iya komai ba sai hauka da shigar banza wallahi har mamaki nake yadda ma muka fito ciki daya dake, kwakakwata baki biyo halina ba, sannan magana ta gaba ni bazan taba yin fada dake akan saurayi ba bana fatan Allah ya nuna mun wannan ranar, kedai da kikaji zaki iya tou sai kije kiyi am not your mate, maganar yaya Ashraf kuma babu yadda zakiyi nan gani nan bari sai dai hange daga nesa, don haka ki kama kanki ke macece kar ki yarda kizubar da kimarki akan wani namiji." A fusace Khadija ta fizge hannunta daga na Zarah idanunta cike da hawaye ta shiga nuna Zarah "Kome zaki fada kije ki fada Zarah I don't care, yes baya sona for now amma zai soni a gaba, I told you sai na kwaci soyayyarsa kina ji kina gani, don haka sai ki shirya..." tana gama fadan haka ta juya ta fita nan Zarah ta tsugunna ta fashe da kuka mai ban tausayi....

**

Kafin ta kwankwasa sai taga kofar ma a bude take, a hankali take taku saboda tray din dake hannunta har ta aje shi saman table kafin ta dago tana kare ma dakin kallo, gyara dakin tayi tas tana tsakar linke bargo ya shigo motsinshi taji, fuskarsa alamun yana cikin damuwa ya zauna gefen gadon duk kokarinsa akan ya mata murmushi kasawa yayi, itace ma ta sakar masa murmushin "Abinci na kawo maka, amma naga alamar kamar kana cikin damuwa, please kaci abincin...." murmushi ya kakalo "Allah sarki kin kyauta kuwa thank you." Tray din ya jawo gabanshi yana budewa "Sannu kinji? Allah yayi maki albarka.." wani irin sanyi taji a cikin ranta, murmushi tayi kafin tace "Ameen." Kallon shi take yadda ya fara cin abinci cikin nutsuwa, kallonta ya dago yana yi ya kasa jurewa sai yace "Wai Zarah meyake damunki? Na lura gaba daya yau bakya cikin walwala meyafaru tell me?" Tsayawa yayi da cin abincin yana kallonta "Dan Allah kar ki boye man koma menene kinji?" Ta kakalo murmushi "Gajiya ce kawai kasan yau general cleaning mukayi ma gidan, is just stress that's all..." yayi shiru yana nazarinta "Tunda na fahimci kina cikin damuwa Zarah gaba daya nima sai najini cikin damuwa, kuma baza kice stress na saka damuwa ba, kinga yadda kika zama kuwa yau? Kin fada kin zama wata kala..."  tayi murmushi kafin ta tsiyaya mashi juice din data kawo mashi cikin glass cup "Ciwon so ne yake damuna na kosa na zama mallakinka kowa ma ya huta." Yayi dariya kafin yasha juice din "Kinji ki da wani magana, sai kace wacce za'ayi kwace? Tou nida ke wa ya kamata ace ya kamu da ciwon so? Kinsan yadda nake sonki kuwa?" Yar dariya tayi alamun jin kunya tace "Babu wanda zai mun kwace... nagode da son da kake mun." Tsayawa yayi yana kallonta "Ina so in bar kasar nan, ina ya kamata muje honeymoon bayan munyi aure? Saboda ni akwai mutanen da bana son gani yanzu gara mu gudu mu bar masu kasar..." dariya ta fashe da shi "Jishi don Allah kamar wanda ake kora ko ake masa wani mugun abu?" Yar dariya yayi yana kallon yadda take dariya kyanta na kara bayyana, ajiyar zuciya ya sauke "Zarah ina sonki, son da bansan adadinsa, I don't know how when where? But your love in my heart is deep..." karar abu sukaji suna daga ido sukaga Khadija tsaye tana binsu da kallo tray da cup din data dauko sun tarwatse a kasa, har glass ya fadan mata a kafa, da hanzari Ashraf da Zarah suka mike sukayi kanta take Khadija tace a shagwa6e "Yaya Ashraf am hurt...naji ciwo yana man zafi..." Zarah ta riko ta da sauri don ta fahimci attention din Ashraf kawai take so, janta takeyi da sauri tana tirjewa har cikin parlor, wani irin wurgi Zarah tayi da ita kan kujera sannan tace "What do you think you're doing?" Khadija tayi murmushi "What you think! Wai kin dauka wasa nake maki maganganun dana fada maki jiya? You must be joking!" Tayi wata dariya, Zarah tace "Ko me zakiyi bazaki taba cin nasara ba, our love is pure so dama ki kwantar da hankalinki Allah zai baki wanda ya fishi..." Mikewa Khadija tayi da hanzari "Babu wani wanda ya fishi, ke bari in fada maki, I told you before saina kwace Ashraf kota dadi ko ta tsiya! Ko aure aka daura maku saidai a kwance shi wallahi...!" Zarah batasan lokacin data dauke Khadija da mari ba tana nunata tace "So ba hauka bane, ki dawo cikin hankalinki tun wuri tun kafin wankin hula ya kaiki dare!" Dafe kuncinta Khadija tayi kafin ta dauko hannu zata rama taji ance "If you dare lay a single finger on her Khadija you'll regret ever been born!" Duk da yadda zuciyar shi ke mashi kuna haka nan ya daure ya fara magana cikin nutsuwa "Yau na tabbatar rawar kanki bata amfana maki da komai ba Khadija, bansan haka kike marar hankali ba sai yau! Duk naji conversation dinku tou bari kiji in fada maki Zarah nakeso baki isa kiyi forcing kanki a kaina ba! Ke dabbar ina ce da zaki fara kishi da yar uwarki? Har kike ikirarin sai kin aureni koda hakan na nufin ki kashe mata aure? A cikin dabobbi ke bansan wace specie bace kin taba ganin yan gida sun auri mutum daya? Are you mad? Duk wani abu da kike ji a game dani kiyi gaggawar fiddashi daga ranki in ba haka ba kece zaki wahala a banza a wofi! Hope kin fahimta...!" Shiru dukkansu sukayi. Zuciyoyinsu na bugawa, sai kawai ganin Khadija sukayi ta zube kasan gwiwowinta tare da riko wandon Ashraf ta fashe da kuka "Ko kasheni zakayi Ashraf Ina sonka! I still love you..." Cikin karaji Zarah tayo kanta gadan gadan tare da fincikota ta fara kokarin rabata daga jikin Ashraf hawaye na faman zarya a idanunta, Ashraf kuwa tsaye yayi kamar gunki komai nashi ya tsaya cak da aiki wannan wace irin masifa ce haka?




Kuyi hakuri da wannan ba yawa😆😆

Tuesday 29 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 29

 YAR AGADEZ



                 {Page 29}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



This page is for you Hafsat Kabeer your comments are always on point🔥❤️😅thank you🥰🥰



Wasu marukan ya sake sauke mata kafin ya fara maganar a fusace yana nunata da yatsa, "Wallahi kinyi karya! Kuma kazantar rayuwarki tayi kadan! Ke har kin isa ki bude baki ki kalli matata ki jefeta da wadannan munanan kalamai mafi muni? Kaskantacciya irinki ke har kinyi isar da zaki kalli matata ki kirata mai kisan kai? To wallahi baki isa ba kinyi karya don haka maza maza ki tattara kayanki da duk wani abu da kikasan dashi kikazo gidannan ki fice ki bamu wuri, wawuya butulu shashasha kawai!" Kafin sarki ya ida rufe baki Zubaida ta nufi wajen da kayanta suke, babban akwatinta ta dauko ta bude ta dinga jefa kayanta ciki, yanda zuciyarta ke tafasa da kuna kamar ranta zai fito tsabar bakin ciki, hakanan ta daure tama kasa tsaida kukanta don ta lura da wata dariya da Umma ke mata irin ta victory dinnan, bayan ta rufe akwatin ta dauko hand bag dinta ta saka wasu abubuwa da zata bukata, sauraren zagin da sarki ke mata takeyi kamar ta fasa ihu, tazo zata fita bakin kofa kenan taji ya tsaida ta "Tsaya malama! Ina zakije da wannan katon akwatin? Ko hand bag din dake hannunki a nan gidan kika sameta, da kayan dake ciki, abinda kawai kikazo dashi gidannan wasu tsummakora ne kwaya uku kacal tsabar talauci!" Wata dariyar takaici tayi ta juyo ta hada ido da Umma, "Ka tambayi matarka ita tasan duka kayan dake ciki da kudina na siya, i mean kudin da matan governors suke biyana ladar aikin da nake masu all thanks to your wife tasan manyan mata, i have the luxury by my self, and by the way Hajiya Karimah zan dauki motata da aka bani bayan na dawo da Japan don idan na sa kafa na fita bazan sake dawowa garinnan ba har abada, ranka ya dade rana da zuwa da duk zaka tuno da maganganun dana fada maka a lokacin ne na maku nisa ballantana ka nemi gafarata, all the same na yafe maka saboda ba laifinka bane tana juyaka ne son ranta amma akwai ranar kin dillanci, bissalam." Ko juyowa batayi ba ta fita daga dakin hawaye kuwa kamar an bude pampo, haka taje inda ake aje key din motoci ta dauki nata kafin ta fice daga gidan gaba daya.

Bakin wani daji tayi parking tana fitowa ta duka a nan ta fasa wani irin ihu ita matsakarta shine bakin paintin da Karimah ta goga mata, a hankali ta fara kuka tana dana sanin haduwarta da Karimah, ta kuduri zata gyara rayuwarta InshaAllah. 

Sarki kasa ta6uka komai yayi ya fito daga dakin duk ransa a dagule, tsayuwa yayi a balcony yafi minti talatin yana tuno da maganganunta, fita yayi daga balcony din ya nufi dakinsa direct ya rufe ya nemi privacy daga dogari, a ransa sai yake ganin kamar fa gaskiya Zubaida take fada don tafiye tafiyen da takeyi na menene tana baiwa? Yanzu daya koreta ina zataje? Kamar an dasa shi a wurin haka yayi jugum ya kasa kwakkwaran motsi. 

*****

Zarya takeyi cikin dakinta sai kai kawo takeyi ta rasa inda zata saka ranta abubuwan data fada a gaban sarki sunfi komai daga mata hankali, kawarta ce mai suna Larai tace "Haba Sarauniya Karimah ban taba tunanin zafin ranki ya kai har haka ba har kije ki aikata wannan abun ba, yanzu wane irin warning ke ban maki a kan wannan yarinyar ba? Tou yanzu danaje malamin cewa yayi in har kika bari tayi tozali da danginta asirin mu ya karye bama wannan kadai ba harda wannan kika yi wa sarki, asirinki tonuwa xaiyi tas, yanzu abunda mukayi ta mance ita wacece da ta tafi ta gano asalinta fa? Tou Wallahi sai kisan nayi nidai banida asara ke kika jiyo ma kanki." Tunda ta fara harkar nan bata taba ganin wanda ya kawo mata nasara ba kamar Zubaida yanzu in ta rasa ta ya zatayi? Don dole tabawa Larai kudi masu tsoka akan ta tsaida mata wannan gobarar dake neman tashi da ita, "Nasan InshaAllah ma babu abinda xai faru! Bazata hadu da kowa ba, ba kince Chad take ba? Tou nasan hankalinta bazai taba bata can ba saidai cikin Agadez ko Mali dai zatayi tunani ko tabar kasar gaba daya, yanzu nikam ya zanyi da her excellency? Sai kirana takeyi akan lallai lallai gobe in turota." Hankalinta duk ya gama tashi, wani irin tsakin takaici Larai ta saki, "Mts wannan ay duk mai sauki ne, kawai kice mata yarinyar ce batada lafiya, ta turo maki kudin jirgi da komai xaki turota da taji sauki." A haka sukayi sallama nan take Umma ta kira matar ta shaida mata, sam bata nuna rashin jin dadinta ba nan take ta turo wa da Umma da makudan kudade wai a kaita asibiti da kuma sauran kudin magani hade da siyayyar kafin tazo. Daya daga yaranta dake Mali ta tura ma ta tura ma hoton Zubaida wai a bincika mata ita. A bangaren Zubaida kuwa tunda ta bar gida gararamba takeyi ta rasa inda zataje a cikin mota take kwana, kuka kuwa babu irin wanda batayi ba ko kango ne gidansu zata je ta zauna a haka, saidai ta shiga wannan eatery taci abinci ta shiga waccan. Da daddare wajen 8pm ta tsaya wata eatery ta siya abinci amma kasa ci tayi ma, da kyar taci loma biyar ta mike ta biya ta fita cikin mota ta koma ta zauna don a nan ne gidanta. Nan tazauna ta dunga bin mutanen da kallo yadda suke annashuwa, wasu families ne wasu harda yara, wasu saurayi da budurwa wasu friends, take taji damuwa ta dawo mata cikin rai sabuwa fil take ta fara kukan bakin ciki.. duk tunaninta bai wuce inda zata samu matsugguni ba, tasan dai bamai taimakonta a wannan marra, idan tace ta kama gida ma bata tsira ba dama kowa kallon yar iska yake mata. Batada madafa haka zalika batada kowa a halin yanzu sai Allah, ana haka taji an haske tada fitila gabanta ya yanke ya fadi bata ta6a jin tsoro ba irin na yau, motar tayi parking ta gabanta, duhu bata ganin mai fitowa nan Zubaida tayi tsuru tsuru, knocking glass din window din akayi kamar bazata bude ba can dai ta bude, glass din ta sauke gaba daya a take sukayi ido hudu da yayarta Sadiya, wani irin kallon tsoro suka bi juna dashi, Sadiya ce ta fara girgiza kai tana kara damke hannun mijinta dake cikin nata, wannan ba Zubaida bace, Zubaida batada kudi, batada mota, Zubaida bata shigar yan gayu, tasan a matsayin baiwa aka kaita agadez gidan sarki how come? "Sadiya lafiya?" Mijijnta ya furta sai a lokacin hankalinta ya dawo jikinta kuka ta fara yi iya karfinta "Sadiq Zubaida ce! My one and only sister, ita kadai nakeda, amma anya wannan itace Zubaida? Taya ta xama mai kudi?" Bata jira amsar shi ba kawai taje ta bude motar inda Zubaida ke zaune kamar an dasata a wurin babu abinda ke motsi a jikinta, wasu fresh memories ne suka dawo mata kamar ana kunna mata tv tun daga lokacin da aka tura ta a matsayin baiwa har yanzu datake a gaban Sadiya har time din da suna yara ta hango cikin kanta, ta shekara ba iyaka tana kokarin tuna ko ita wacece amma yanzu tashi daya memory dinta ya dawo, mikewa tayi a hankali ita kuwa Sadiya cikin kuka ta fada jikinta sai a lokacin Zubaida ta saki wata atishawa mai karfi kafin tabi jikin Sadiya luu... da kyar Sadiq ya lallaba Sadiya kafin ya samu ta kama mashi Zubaida suka sata a mota, duk abinda ke cikin motar Zubaida sai da suka dauko shi ya kuma biya daya daga ma'aikatan wurin suka tuko masa motar. Tunda suka kama hanya Sadiya ke razgar kuka ya dade dajin labarin Zubaida wajenta kusan kullum sai tayi kuka akan itadai Zubaida bata san halin da take ciki ba tana so ta ganta, duk wani labari akan Zubaida ta masa so yasan how close they're, a lokacin da aka rabasu ta karfi aka tafi da Zubaida ita kuma Sadiya aka kaita aikatau, su marayu ne basuda uwa basuda uba. Bayan sun isa gida Sadiya ta kama ma Sadiq suka shiga da ita gida, tanaji ya gama shigo da kayan amma ko motsi Sadiya batayi ba, sai bayan kusan minti talatin Zubaida tafarka babu abinda bata gani ba cikin idanunta kuka ta fashe da shi saboda ta dauka duk mafarki ne, "Aunty Sady...." sunan da take kiranta dashi kenan, da kyar Sadiq ya lallabasu suka daina kukan nan, Sadiya ce tasa Zubaida ta shiga tayi wanka tasa kayan bacci, ta rama sallolinta sannan suka zauna don bada labarin bayan rabuwa "Wace irin rayuwa kikayi living? Naga kinyi aure kin auri mai kudi?" Sadiya ta gyada kai, "Bayan an kaini aikatau Allah ya hadani da mutanen kirki matar gidan na masifar sona ke in takaice maki labari dai itace ta hadani aure da danta..." Zubaida tace "Allah sarki kinyi sa'a fa, amma dama nan aka kawoki aikatau na dauka kina Chad?" Tace "Nan aka kawoni...."

She can't believe Aunty Sady tayi aure harda ciki, "Zubaida what happened to you? Don Ba Zubaidar dana sani bace ba." 

Numfasawa tayi "Ana kawoni  a matsayin baiwa na manta wacece ni Aunty Sady... Nadai san bayan nazo ta bani juice nasha tou daga lokacin na manta wacece ni, sunana kawai nasani amma bayan nan I don't remember who i really am...." tiryen tiryen ta fara ba Sadiya labari duk kasashen data je da kalar rayuwar da tayi, harda kayan data siyo kowane kala biyu take siya she just felt something is missing a part of her.... kuka sukeyi rungume da juna har karshe inda Sarki ya koreta, kuka sukeyi kamar ransu zai fita, sunsan ba komai bane ya jawo masu sai rashin iyaye amma sun dauke shi a matsayin kaddara, tun suna kuka har abun ya koma labari sunyi,  sometimes suyu dariya sometimes suyi shedding tears, karshe Zubaida ta kori Sadiya ta tafi wurin mijinta, share hawayenta tayi ta shiga bathroom ta wanke fuskanta kafin tazo ta kwanta cike da tunani kala kala...

*******

A hankali friendship dinsu ya rikede ya koma soyayya, tun lokacin da itama Khadija ta fahimce soyayyar Ashraf ya mata katutu a cikin ta fara neman hanyan da zata ja hankalinsa gareta, kuma a iya fahimtarta ta fahimci soyayya suke yi da Zarah, kullum sai ta rufe kanta cikin daki taci kukanta ta koshi, gashi ta kasa controlling kanta kishi take neman yi da yar uwarta ta jini wacce itama tayi nisa a soyayyar Ashraf, Zarah sam batasan me zuciyar Khadija ke ciki ba tadai fahimci idan ta gansu tare suna fira take mood dinta zai chanza koma ta tashi ta bar wurin. 

Wata rana da yamma Zarah ta dawo daga gidan friend dinta tana shigowa tsakar gida ta hango Ashraf zaune shida Khadija wacce ke faman son yi fira dashi amma da alama hankalinsa baya kanta kwatakwata, murmushi ta kakalo tace "Yaya Ashraf tun daxu fa nake ta faman yi maka magana amma ka gagara kulani, wai me nayi maka?" Hannu ya daga mata alamun ta dakata "Can you please keep quiet? Ina duba abu a nan ne kuma idan kina mun magana kina distracting dina." Wani kululun abu ya tokare mata makoshi, takun Zarah sukaji Ashraf ya daga ido ya kalleta "Assalamu Alaikum..." ta fada fuskarta dauke da kyakkywan murmushi, shima murmushin yayi mata yace "Wa'alaiki salam Fatima Zarah...." ledar dake hannunta ta aje bisa center table din dake tsakiyarsu ta fara kokarin fiddo abunda ke ciki, "Donut na siyo maku kuma glazed ne kaji dadinsa kuwa?" Yace "Da gaske? Thank you babe." Bude box din tayi tace "Am coming." Ta nufi ciki, can sai gata ta fito da cups da kwalin juice a hannunta, tana zuwa ta aje cups din guda uku ta zuba ma kowa nasa ta zauna tana kallon Ashraf "Yaa Yasir ya fita ne?" Yace "Ya fita zance tun daxu." Tayi dariya "Tou meyasa baka raka shi ba? Ya kamata ay kaje kaga masoyiyar tasa ko?" Shima dariyar yayi "Kinsan kishin Yasir kuwa? Ay bazan fara binsa ba..." tace "Har ya kaika?" Yace "Yama fini, saidai idan akanki ne tou fa nafisa kishin nan..." Khadija wacce keshan juice sai kawai suka ji ta fara tari alamun ta kware Zarah tayi saurin bubbuga mata baya "Subhnallah Khadija are you okay? Bari a kawo ruwa sorry." Tsaida ta tayi "A'a am fine bari na shiga ciki na sha...." ta fada tana kallon Ashraf wanda ke mata sannu ta mike tayi ciki sauri, ta window din dakinta ta tsaya tana binsu da kallo zuciyarta na tafasa kamar garwashi, wani irin nishi ta farayi ganin yadda Ashraf din ko kallo bata ishe shi ba yake bin da Zarah da kallon soyayya, kasa jurewa tayi take ta silale a tsakar dakin jikin bango ta hade gwiwarta ta saki wani irin kuka, "Innalillah wai meke shirin faruwa dani? Am I in love with my sister's boyfriend? It can't be! I can't do this to her, she's my sister I don't want to hurt her, amma kuma ina sonsa ni fa tawa zuciyar? Bazan iya controlling kaina ba, ya zanyi?" Kuka take bil hakki kamar wacce aka aiko ma da sakon mutuwa, ta kai awa daya a haka kafin ta mike ta shiga bathroom tawanke fuskanta ta fito, kamar daga sama sai ga Zarah ta shigo fuskarta ta kasa daina murmushi dauke kai Khadija tayi tana jin wani irin bala'in kishi na turnike ta, dafata Zarah tayi "Tarin ya tsaya? Meyasamu idonki Khadija? Did you cry?" Girgiza kai ta shiga tana share hawaye tace "Zarah tambaya nakeso na maki?" Zarah ta zauna gefenta tace "Ina jinki what's going on?" Khadija tace "Wata friend dina ce take tambaya na wai she's in love with a guy, tou Akwai sister dinta itama same guy dinnan takeso, shine take tambaya me zatayi shin ta bar ma yar uwarta saurayin ko kuma she should go for him?...." shiru Zarah tayi kafin ta numfasa "Wannan shi ake kira kwamacala, but in my own opinion they should let the guy decide a cikinsu wa yakeso, wacce baya so a cikinsu sai ta hakura dashi..." Khadija tace "Ni friend din tawa tace man bazata iya hakura dashi ba idan har ta rasa shi zata iya mutuwa..." Zarah tace "What if ita yakeso? Sai dayar ta hakura..." Khadija tace "Tace man dayar yakeso ba ita ba, and she can't lose him...." Zarah tace "Tou gaskiya I don't know, banida  amsar tambayar nan taki Khadija, abu daya zan iya cewa saidai daya zata iya sacrificing ta bar ma daya, tunda sisters ne..." Khadija tace "Put yourself in her shoes Zarah ke zaki iya yin haka?" Gaban Zarah ya wani buga tace "What do you mean? Meyasa xan alakanta kaina dasu? Ay mu bai faru damu ba so stop asking me that question Khadija, you're my blood sister bazaki taba son abinda nakeso ba, haka nima kuma bazan so abinda kikeso ba...." Khadija tace "Am saying what if a misali nake maki just answer me yes or no?" Zarah tace "Please stop it Zarah, this is not a joke..." Khadija ta mike tsaye "Amma yanzu kika gama cewa daya ta bar ma daya Zarah, now ke meyasa kika kasa amsa man tawa tambayar don nayi comparing dinsu dake?" Zarah tace "Saboda am not in their shoes, please stop it Khadija..." ta fada tana mikewa tsaye kirjinta na dukan tara tara... "Am in love with yaya Ashraf Zarah..." wata irin juyowa tayi tana  bin Khadija da kallo daka kalli kwayar idon Zarah kasan ba karamin girgiza tayi ba, "Me kika ce? You're in love with who?" Khadija tace "Yaya Ashraf, I love him so much don Allah ki taimakeni ki bar mun shi bazan iya rasa shi ba..." wani irin wawan duka kirjin Zarah yayi kasa tsayuwa tayi ta zube kan gado tana girgiza kai, da sauri Khadija ta zube gabanta tana zubar da ruwan hawaye "Ki taimakeni Zarah, nasan cewa kina sonshi kema, but wallahi nima am madly in love with him...." ta fada tana dafa kafafun Zarah, wani irin hawaye suka zubo ma Zarah, a hankali ta cire hannun nata ta mike tsaye da sauri tana goge hawaye "I wish zan iya hakura in bar maki shi but I can't Khadija, tun farkon zuwansa gidannan na kamu da kaunarsa duk da cewar lokacin he's heartbroken amma still na jure na raini soyayyarsa a cikin raina sai yanzu da ya fara accepting dina kawai sai kizo kice in bar maki shi Khadija? How is that even possible? I can't wallahi....I really can't am sorry..." tana gama fadan haka ko tsayawa kara kallon Khadija dake durkushe a kasa tana kuka batayi ba dakinta dake gefen na Khadija ta shiga tasa key da sauri ta silale a kasa, wani irin kuka ta fashe dashi mai ban tausayi "Why Khadija? Meyasa kika bari zuciyarki ta kamu da son masoyina? Kinyi ganganci gashi nima ina sonsa bazan iya hakura dashi ba, ya fara accepting dina I started enjoying his company, He's beginning to be happy around me, meyasa zaki bari zuciyarki ta yaudareki Khadija?" Kuka take harda shesheka yanzu wazata fadawa damuwarta? Gashi Mummy tayi tafiya kuma ko tana nan tasan zatace ta hakura ta bar mata shi, zatace ay kanwar tace, then what of her? A hankali taji ana bubbuga kofar dakinta "Zarah don Allah ki bude min kofar nan muyi magana, idan baki bari munyi magana ba zan rabu dake inje in kwaci soyayyarsa in rabaku don haka ki bude!" Zarah najin haka ta tsaida kukan da takeyi ta mike tsaye da kyar ta bude mata kofa, kallon Khadija tayi ta koma  kamar wata mahaukaciya kwalli duk ya bata mata fuska, rike shoulders din Zarah tayi pleading her tana kuka kamar ranta zai bar jikinta, "I love him Zarah, I love him so much, tun ina boyewa har yanzu na kasa banso na kasa jurewa ba amma ya zanyi? Abun yafi karfina! You are my only hope? Remember da muna yara? Kinsha bar man abubuwa kici girma kin tuna? Ko a school you always took care of me you loved me so much, yanzu ma meyasa bazaki iya bar man ba?" Hawaye suka cigaba da kwarara daga idanun Zarah "That was before Khadija, yanzu ba daya bane, I have no control over this, kiyi hakuri baya sonki ni yakeso, ke kadai ke sonsa shi baya sonki in return..." wani irin kuna zuciyar Khadija keyi kamar an zuba mata garwashi "Ki daina fada man baya sona it hurts! Na lura bazaki bar man shi ba ko? Do you want us to start a war?" Da mamaki Zarah ke bin Khadija da kallo "What are you saying Khadija? Bai kamata a kan saurayi kina fada mun haka ba! You're my sister for goodness sake, I beg you ki bar maganar nan ki aje makaman yakinki wannan fa ba doguwar magana bace! I told you he has accepted me mun fara relationship ta yaya kike zaton rana daya ya fara sonki? Karki bari soyayya ta rufe maki ido alakar dake tsakaninmu ta lalace a banza...." Khadija ta tsaida ta "Tou in bakiso ta lalalce ki rabu da Yaya Ashraf..." ta girgiza kai "I can't Khadija, I wish I could dana hakura amma kisani soyayya ba abu bane mai sauki da za'a ce ka cire ta a ranka rana daya ba...." daga mata hannu tayi "Well then, idan bazaki iya hakura ba then let the war begins! I can go to any length to get him and to love me you know I can do it, don't underestimate me Zarah, tunda bakiso ayita ta lalama then am ready to fight this war with you, mark my words sai na auri Yaya Ashraf no matter what it takes!" Tana gama fadan haka ta juya a fusace zata bar dakin da sauri Zarah ta riko mata hannu wasu sabbin hawayen na kuma taruwa a idanunta tana girgiza kai idanunta cikin na Khadija itama haka Khadija ta tsaya tana kallonta cikin ido, kafin Zarah tace....

*******

A 6angaren Umma kuwa tun ranar data kira Larai sukayi magana ta nufi gidan wata kawar huldarsu, a nan ta iske an kawo wata tsaleliyar budurwa tou yau aka kawo mata ita har gida, dalilin kenan data tabbatar da cewar sarki baya nan ya tafi farauta cikin daji, kuma ya kan dade a can wani lokaci har awa uku zuwa hudu bai dawowa, tunda taga tasamu dama sai kawai suka baje a dakinta suna sharholiyarsu, bayan kusan awa daya suna cikin alfasaharsu kawai taji an banko kofa, a duniya bata taba zaton zataji tashin hankali irin na yau ba, ganin da sarki yayi mata cikin Wanann siga ba karamin kidimata yayi ba, take ta fara kyarma tana mai tunanin kalaman malaminta "Sarauniya Karimah koda wasa karki bari ya kamaki cikin wannan siga, dan ke kinsan aikin da mukayi mashi shekara da shekara idan yau duniya zata taru a kanshi tace ga abinda kikeyi ina mai tabbatar maki bazai taba yarda ba! Ke ko ke da bakinki kika fada masa ba yarda xaiyi ba balantana ma a fada masa amma da zarar idanunsa suka gane masa zahiri toh illahirin asirin da kikayi ya karye har abada, sannan da sharadi zaki iya haukacewa ko ki kamu dawani deadly ciwo saboda ke kinsan aikin nan na aljannu ne karki bari ki ketara masu doka wallahi ki kula!" Da sandar dake hannun sarki, da wani littafi dake hannunsa yana nazari da kanshi sarkin tare suka fadi rigib kasa a bakin kofa, idanushi akan Umma ko kyaftawa baiyi, da sauri itada yarinyar suka suturta jikinsu kafin yarinyar tayi sum sum ta fice daga dakin, kamar wacce kwai ya fashe mawa a jiki haka ta silalo da rarrafe ta zo inda yake zaune rigib kasa hawaye kawai ke fitowa daga idanunta, "Karimah meyasa? Meyasa zakiyi man haka?." Ya fada hawaye na zuba daga idanunsa ji yake kamar ranshi zai fito ya huta da wannan bakin cikin da takaicin... giirgiza kai ta farayi ta fara bashi amsa "Jalal tun kafin na aureka nakeyi, bansan ya zanyi in daina ba na kasa hana kaina, kayi haku...." wani mugun kallo yake mata "Mena tare maki? Duk wani hakkinki dake kaina ina kokarin saukewa, ki rasa wanda zakibi sai mace yar uwarki? Dama abinda baiwarki take fada rannan gaskiya ne? You ruined their life, why did you do this to me? Why?" Da akwai yadda mutum zai fiddo zuciyar shi fa yau Jalal sai ya fiddo tasa komai ya tsaya masa cak, "Now tell me did you kill my wife?" Hannu ta kai zata tabashi yayi saurin janye jikinshi "Just answer my question did you kill her yes or no?" Da hanzari ta fara daga kai "Nina kashe ta years back, wallahi kishi ne kawai bawani abu ba, saboda kai nayi don ta bar man kai...." wani irin wawan mari ya dauke ta dashi hagu da dama cikin zafin nama ya shako mata wuya "So you're a monster as my daughter always told me, amma da yake bakin alkadarinki yana yawo a kaina na kasa gane komai, I always overlooked your mistakes and forgave you! Ashe da bakar muguwa nake zaune, kin rabani da matata mai kaunata tsakani da Allah ke ba sona kike ba, you are just after my sarauta and money!" Mikewa yayi har hannunshi kyarma yakeyi idanunsa jawur wane garwashi yace "Karimah kije na sake ki saki uku, ki tattara duk wani abu da kikasan naki ne ki bar man gida, na baki awa daya kacal ki kwashe kayanki ki fice man daga gida! Idan na dawo na iske shi cikin gidannan duk abinda nayi maki ke kika ja, bazan hukunta kiba amma kisani na bar komai a hannun Allah shi yasan yadda zaiyi dake!" Kuka take har wani shidewa takeyi tana wani irin ihu kai kace sabuwar mahaukaciya, fita yayi bai ko kara kallonta ba zuciyarsa na kuna, Karima na nan tsugunne inda ya barta tana kuka kawai sai jinta tayi tsamo tsamo cikin jini, da sauri ta mike ganin yadda jinin ke kwarara ba karamin tsoro taji ba "Innalillah wa inna ilahir rajioon, meke shirin faruwa dani? Kardai maganar malamin nan daya fada har ya saka man cutar?" Ganin jinin da gaske ba tsayawa zaiyi ba yasa ta samo pad ta saka ta gyara wurin da kyar take jan kafa sai binta da kallo mutanen cikin gidan sarkin sukeyi, bata damu ba itadai burinta taje asibiti, da isarta ta samu ganin wani Doctor ta masa bayanin abinda ta gani kuma tace masa ta wuce menopause sheyasa tayi mamakin ganin jinin, tests ya rubuta mata kala kala taje tayi da scans, bayan tayi ta dawo tana fuskantarsa gaba daya hankalinta a tashe yake ya soma warware takadar, kana hango tashin hankalin da Doctor din ya shiga yana bin takardar da ido, gabanta ya wani buga tace "Me aka gani a ciki?" Shiru yayi na dakiku kafin a hankali ya fura "Am sorry Hajiya result ya nuna mana kina dauke da Cervical cancer, tumor ce ta kasanki sheyasa ma kika fara bleeding, ta dade tare da ke baki farga ba sai yanzu data fara showing signs and symptoms...." mikewa tayi tana girgiza kai hawaye na shatata daga idanunta "No no it can't be, not me...." wani irin ihu ta kurma take ta zube kasa....

Monday 28 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 28

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 28}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




2 DAYA LATER

Stool Khadija ta jawo ta zauna gaban mirror wacce ke faman shafe shafe a fuskanta, wannan yarinya tana son makeup sai kace wata fashionista! Khadija ta daga ido ta hangota ta madubi tana kokarin shafa lipstick ta dakata tace "Lafiya kika kura mun ido haka? Ko na maki kyau ne?" Zarah tayi murmushi "Kyau? A haka? Duk kinbi kin painte fuskarki, Khadija kwalliyar nan tayi yawa, by the way you looked beautiful without makeup." Khadija ta turo baki "Kaji man bakin ciki! Zarah in har kwalliyar nan ta maki kyau kawai ki fada kema sai ayi maki ay." Zarah tace "No thank you please." Khadija ta cigaba da makeup dinta Zarah ta kuma cewa "Wai shin fita zakiyi ne?" Khadija tace "Yes salon nake son zuwa..." Zarah ta kwalalo idanu "Salon kuma? Malama kinsan karfe nawa ne yanzu? Karfe biyar fa harda rabi kice zaki tafi salon are you okay?" Khadija tayi dariya "I am perfectly fine! Salon kuwa zanje yanzu InshaAllah." Zarah ta tabe baki "Kekam kina bukatar addu'a gaskiya, kuma wai sai kinyi makeup kafin kije salon?" Khadija ta juyo a fusace "Wai kekam ina ruwanki? Haba ki kyaleni mana!" Shiru Zarah tayi ta cigaba da abinda takeyi. Bayan duk ta gama kimtsawa kai kace wacce zataje wani dinner party, turare ta feshe jikinta dashi ko ina har kamshin yayi yawa, chewing gum ta dauko ta watsa baki ta suri wayarta ta juyo ta kalli Zarah "Bye." Zarah tace "Wa zai kaiki? Ke zaki tuka?" Tana taunar chewing gum tace "Nah." Saukowa tayi bisa bene duk ta cika wurin da karar takalmi, hango Ashraf tayi bisa kujerar parlor yana faman danne danne a waya, ta gabanshi taxo ta wuce amma ga mamakinta ko dago kai baiyi ba bare ma ya kalleta, dakin Mummy ta wuce tana zaune kan gado da littafin hadith tana nazari Khadija ta shigo, gefenta ta zauna Mummy ta dago tace "Ina xakije haka kika ci wannan uwar kwalliyar?" Khadija a shagwa6e tace "Salon..." Mummy tace "Salon? Karfe 5:45?" Wayarta ta kunna ta kalli time ta dago tana kallon Mummy "Please Mummy wallahi kaina yana bukatar gyara, na dade ban gyara shi ba ji nake kamar bazan iya kai gobe dashi ba a haka..." Shiru Mummy tayi can tace "Ok karki dade kice wa Yasir idan yana nan ya aje ki mana." Ta turo baki "Baya nan fa yaa Yasir, sai yaya Ashraf kawai ke gidan." Mummy tace shi yasan gurin ne?" Khadija tace "Sai dai na masa kwatance," Mummy tace "No problem dauki key din motata bisa madubi kice nace don Allah ya taimaka ya kaiki." Da sauri ta mike ta dauko key din ta fice parlor yana inda ta bar shi dan sunkuyawa tayi tace "Yaya Ashraf ina wuni? Yaya Ashraf Mummy tace don Allah wai ka kaini salon." Bai ce mata komai ba kawai ya mike ya fice waje, kallon mamaki ta bishi dashi kafin a hankali tabi bayansa, waje ta iske shi tsaye harde da hannaye wurin mota yana ganinta ya kara hade rai, ta karaso ta mika masa key din, ko kallon inda take baiyi ba ya bude motar yace mata "Jeki kira Zarah ta raka ki." Hade rai tayi tace "Tace maka zata je ne?" Ya gyada kai "Zataje mana, kawai kije ki kirata." Shiru tayi kamar bazataje ba can dai ta juya kamar zata tashi sama ta nufi ciki, ta kai akalla minti sha biyar can sai gata ta fito itada Zarah wacce ke sanye da ash hijab abinta ba karamin birge shi tayi ba, gaba daya ya dinga binsu da kallo yana gani differences sosai tsakaninsu a halayya, tsarin rayuwa, nutsuwa da kuma kyau. Karasowa sukayi Zarah tace "Yaya Ashraf gani." Yace "Wai unguwa zaki raka Khadija." Tace "Don Allah ka rabu da ita kalli time fa yanzu ana iya kiran sallah muna can, yanzu salon dinne bazata iya hakura saida safe taje ba?" Tsaki Khadija ta saki da harara "Wai ina ruwanki? Ba Mummy tace inje ba dai?" Ashraf yace "It's okay ku shigo muje." Nan Khadija ta fara kokarin shiga gaba Ashraf yace "Koma baya Zarah zata shiga gaba ay itace babba." Ba karamin kule ta yayi ba yau, hade rai tayi ganin haka yasa Zarah tace "Bakomai fa zan shiga baya ni." Hade rai yayi yace "Nace ki shiga gaba ko?" Bude gaban tayi ta shiga Khadija ta shiga baya yana ayyanawa a ransa sai ya sauke mata rawar kan nan nata da wannan tunanin yaja motar suka bar gidan.

*****

Tana kitchen tana fama da girki kamar daga sama taji an rungomota ta baya, kamshin turarensa da taji shi ya tabbatar mata daya iso, fara ture shi tayi daga jikinta shi kuwa ya makalkaleta hade da rufe ido, "Sultan girkina zai kone please let me go." Peck yayi mata a wuya "Tou ya kone din, sai na girka mana wani." Shiru tayi, sai don kansa ya sake ta hade da juyota tana fuskantansa, kallonta yake cikin ido yana rike da waist dinta yace "Habibty, tun daga bakin kofa nake jin aroma na abincin nan na tashi, it sure gonna taste delicious." Tayi murmushi "Mhmm, tun kafin kaci har ka fara cika baki?" Ya rungume ta yace "Kome kika dafa dole yayi dadi indai daga hannunki ya fito." Tayi murmushi "Thank you, but first of all, go and freshen up then you can meet me at the dining later." Shagwa6e fuska yayi "Tou bazaki tayani ba?" Ta dan ware idanu "Girki nake fa amma next time." Yayi dariya "Naki wayon..." dariya yayi ya wuce daki zuciyarsa fes fes, Itama Hoodah cike da nishadi ta kammala girkinta, bayan yafito a haka suka kare cin abincin su suka tafi suka kwanta.

Kiran sallar farko ya tada Hoodah daga bacci wacce ke kwance a jikin Sultan ya nadeta da hannunsa, daga ido tayi ta kalleshi take kunya ta kamata tuna irin kukan data sha jiya, kallonshi ta tsaya yi bata taba kare masa kallo haka closely ba sai yau bacci yakeyi hankalinsa a kwance, bak'in sajensa take bi da kallo wanda ya nannade sai sheki yake kai kace na larabawa, yadda ya burgeta sai taji ta kasa hana kanta take ta dora hannu a kai ta dinga shafawa a hankali, wani irin santsi taji hade da taushi, haka ta cigaba da shafa shi, a hankali ta bi idanunsa dake rufe da kallo yadda lashes dinsa sukayi zara zara kamar a kitsa, tunani ta farayi wai ita dashi wama yafi tsawon lashes? Tayi nisa wurin kallon nasa ashe batayi aune ba ya tashi ya kura mata ido, "Da alama wata tana admiring kyawuna." Gabanta ya wani buga da sauri ta runtse idonta gam gam cike da kunya da sauri ta dauke hannunta daga kan fuskarsa yayi wuf ya riko mata hannun "Ay wallahi baki isa ba kuma, bazaki dauke hannunki ba sadda kika ga dama ba kuma," ya fada yana mayar mata da hannunta a wurin, "Ki barsu a nan Habibty." Kokarin tashi zaune ta farayi "Za..nyi salla...h." Ta fada tana kokarin janye hannun nata at the same time, yayi murmushi "Nima ay sallar zanyi, tare zamuyi sallar ma habibty." Hannunsa ya dora bisa hannunta yana motsa shi daga bisa sajensa "Naga alama wurin yana maki dadin ta6awa." Kunya duk ta kama Hoodah tayi maza tace "Kallo fa kawai nakeyi." Ta sauke ajiyar zuciya sai kai kace wacce tayi gudu don gaba daya yadda ya tsare ta da idanunsa sai taji bazata iya jurewa ba, tashi daga bisa gadon ta fara kokarin yi da sauri Sultan ya riko mata hannu, "Ina xakije?" Yace tare da kara rike mata hannunta cikin nashi yana murzawa shiru tayi tana sauraren bugun kirjinta, can tace "Uhm babu kawai xanje bathroom, I need to go please!" Murmushi yayi yace "Babu inda zakije mrs Sultan, ke kika tashe ni daga bacci, kuma  kika fara ta6ani sannan yanzu kice zaki gudu kuma?" Rufe ido tayi cike da kunya ya saki dariya ya mike tsaye ya kamo hannunta ya kaita har cikin bathtub ya kunna mata warm water, ba zato ba tsammani kawai sai ganinshi tayi ya shige wankan shima kusa da ita ay bata san sadda ta fasa ihu ba, dariya yayi suka yi wankan tare duk da ta kasa sakin jiki dashi, hade da alwalla. Da kansa yasa mata kayanta ya samata hijab, shima kayan ya sa yaja su sallah, saida suka gama sukayi addu'oinsu ya kalleta yace "Good morning my beautiful princess." Tayi murmushi ta rufe quranin data gama karantawa ta aje shi mazauninsa sannan tazo gefensa ta zauna hade da dora kanta bisa kafafarsa tace "Morning to you too my handsome prince." Hannunta taji ya kamo ya manna ma kiss sannan ya mikar da ita tsaye yana dago fuskarta "Look at me Hoodah." Ta kalleshi yace "I love you, you are the person who exactly knows how to put a smile on my face, kece mutum ta farko da nake so na fara gani da safe haka ma kece ta karse da nakeso na gani kafin nayi bacci, ever since I fell in love with you Hoodah rayuwata ta sauya, i will always be there for you no matter what." Hugging dinshi tayi sosai tace "Babu words din da zanyi amfani dashi wurin nuna farin ciki hade da godiya ga Allah (SWA) daya mallaka man kai a matsayin mijina I am really thankful." Zuciyar sultan kamar zatayi boasting tsabar farin ciki resting kansa yayi bisa shoulders dinta yace "I love you Hoodah, I promise to love and be with you duk rintsi duk wahala,  and this time around am not going to break my promises InshaAllah." Gyada kai tayi hawaye na kawo idonta, jawota yayi ya cire mata hijab dinta yace "Let's sleep." Kan gadon suka haye ni kuma na fito na basu waje....

******

"Ranki shi dade gaskiya nifa babu wata kasar da xan kara zuwa! Ni aure zanzo inyi na gaji da wannan kazantacciyar rayuwar da kika dora ni a kai, kiyi hakuri amma gaskiya bazanje ba!" Wani wawan riko Karimah tayi mata ta maidota ta gabanta kafin ta faska mata wani irin wawan mari, ranta a bace take kallon baiwarta wacce ta maida yar gayu tayi clean, har an kai lokacin da Zubaida zata kalli kwayar idonta ta fada mata magana? Kodai maganin da take amsowa ya fara daina aiki ne? Don a yadda sukayi maganar yace ko wani namiji yace yana sonta asirin zai karye shekara da shekaru tana wannan harkar sai yanzu wannan kazamar baiwar zata kawo mata cikas. Batasan ya zatayi ba gashi nan da kwana uku ya kamata ta tura Zubaida Paris yanzu ya zatayi? Zubaida batasan lokacin data fara kuka ba, "Nasan kin bani rayuwa kin tsamo ni daga cikin talauci a lokacin da nake tsamo tsamo a cikinsa, amma nagaji! Rayuwa ce me cike da kazanta da tarin zunubi! Rayuwa ce abar kyama ko nasani ko bansani ba nasan tabbas idan na dore akan wannan rayuwar babu abinda zai hana ta kaini zuwa jahannama, Umma ki hango yau da ace kinada ya ko da ake transferring dinsu daga wannan mace zuwa wata ko daga wannan namijin zuwa wani, kasa zuwa kasa ba don komai ba sai don alfasha da matan banza ko mazan banza! Ya zakije a ranki?" Kafin ta rufe baki Umma ta kara wanke ta da wani wawan marin, idanun baiwar Allahn nan har sun rine kumatunta yayi sawun mari, "Ke har kin isa ki alakanta nawa jinin da wanann maganar? Duka duka yaushe na dauke ki daga tsummar rayuwarki?" Abinda Umma ta fada kenan karshe ma sai ta fara dukan Zubaida, kuka take bawai zafin dukan ba sai don irin kunar da zuciyarta ke mata, wato ita bazataso ayi ma nata ba amma ita takeyi wa yayan mutane? Amma ji yadda ta dage tana dukanta? Ita wace irin alfasha ce ke bata aikata ba? Wallahi inda ace yau mai martaba zai gano kadan daga cikin abinda takeyi toh da ko kara second daya baxaiyi da ita a cikin gidansa ba... Dan halak din kuwa sai gashi ya shigo da sauri ya karaso yana fadin lafiya? "Sarki wai yau ni Zubaida ke fadawa magana, ni Zubaida take zagi ta uwa ta uba wai na mayar da ita baiwa ita ba baiwa bace da gatanta na dauko ina sata bauta!" Sai ta fashe da kuka, cikin tsananin bacin rai sarki ya damko Zubaida ya dauko yatsunsa biyar ya shatata mata a kunci, sannan yasa hannu ya shako mata wuya, babu abinda Zubaida keyi face girgiza kai tana gunjin kuka "Ke har kin isa ki fadawa matata haka? Idan kin mata bari na tuna maki cikin kazantarki na dauko ki na mayar dake mutum shine yanzu har wuyanki yayi kwari ya isa yanka ko?" Girgiza kai ta cigaba da yi tana kuka sosai tana kokarin cire masa hannu daga wuyanta da ya shake "Ranki ya dade wallahi ba gaskiya bane, sam banga laifinka ba Allah ya baka yawan rai! Sorry to say amma bakasan da wace irin mace kake tare ba, she's evil! She's wicked! She's a witch! She's a Murderer! And full of dirt!" Wani marin ta kara jin ya sauke mata, ko gezau batayi ba bata kuma bari ya fara magana ba ta tsaida shi "Ka tsaya ka saurareni! Ko mey zakace kace amma ka tsaya in gama magana! Kai kasan wace irin rayuwa tabani? Da kuma dubannan yan mata? Ta maida ni lesbian! Duk tafiye tafiyen da nakeyi ita ke tirsasa man! She sells me off to wives of ministers, senators, governors.... bani kadai ba duk wata da ka aje haka take maida su, ta saida mana mutuncinmu all in the name of son kudi and luxury! Bata tsaya a nan ba ta kashe matarka mahafiyar Hoodah kisan gilla...." wani irin wawan ihu da Umma ta kurma ta fara dora hannu bisa kai tana nuna kanta "Sarki kaga abinda mutum zai iya yi ko? Dan adam! Ka dauko shi daga rana ka maida shi inuwa amma shi sai ya tunkuda ka rana tsundum! Sarki a gabanka take alakantani da masu Wanann halayen?" Kuka Umma takeyi tana maganganu ta inda take shiga bata nan take fita ba, nan sarki ya fara binsu da kallo, daka ganshi kasan he's in shock ya kalli Zubaida ya kalli Umma ya rasa maganar wa zai dauka a cikinsu....

Sunday 27 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 27

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 27}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Shima same kallon data yi masa ya bita dashi sannan yace "Yawwa." Yana gama fadan haka ya bude mota ya shige yabarta nan tsaye, glass dinta ta maida Yasir ya zagayo yana mata wani mugun kallo yace "Wai ke yaushe zakiyi hankali? Gaskiya ki chanza hali." Yana fadan haka ya juya ya shige mota, kafada ta make alamun oho sannan ta bude mota ta shiga itama, nan ya tada motar suka bar airport din. Bayan yayi parking ko rufe motar bai ida yi ba Khadija ta bude motar ta fito da gudu tayi cikin gida, "Mummy!" Ta kwala mata kira tun daga bakin kofa aikuwa da sauri Mummy ta taso nan tayi hugging dinta, cike da murna Zarah ta fito itama jin hayaniya tace "Oyoyo mutan Turai!" Nan sukayi hugging juna, janta sukayi cikin parlor ta zauna tana cire jacket dinta tana wani fifita da hannu, "Mummy Nigeria zafi akeyi haka?" Mummy tayi murmushi "Sannu baturiya, kedai nan don kin saba da weather din can sheyasa amma ay babu zafi yanzu haka damina ta fara kawo kai." Shiru tayi ganin su Yasir sun shigo bakin kofa ya aje mata akwatinta yace "Ke bazaki iya tsayawa ki fito da akwatinki ba saboda kin rainawa mutane hankali ko?" Ashraf ya dafata "It's ok kaga ay tana murnar ganin Mummy ne dole ta manta akwati." Yasir yace "Toh idan kin gama sai kizo ki shiga dashi ciki." Yamutsa baki tayi alamun shagwaba "Kai yaaya na gaji fa." Tsaki yayi ya wuce dakinsa Ashraf na biye dashi a baya, Mummy ta mike tana fadin "Halinki dai na nan Khadija da lalalaci aikuwa dole ki dauke kayanki. Sai ki tashi kije ki watsa ruwa ga abinci nan kici." Tana fadan haka itama ta wuce dakinta, Khadija ta turo baki Zarah tayi dariya, Khadija tace "Yawwa wai wannan waye yake zaunen mana a gida?" Zarah tayi murmushi "Har kin manta yaya Ashraf? Wanda da suna karatu waje tare? In suna Niger ma ya kanzo nan garin har yayi kwanaki ya tafi? Yana da jinin sarauta kawunsa ne sarkin agadez...." shiru tayi alamun tunani can tace "Ohh na tuna sa, ay na dade ban ganshi ba sheyasa na manta fuskansa." Zarah tace "Sarkin mantuwa, tou yanzu dai ki tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci." Mikewa tayi tace "Don Allah ki taimaka ki hau mun da akwatina sama." Zarah ta maka mata harara "Wa? Wallahi baki isa ba uwar lalaci, ni inda nice yi mun zakayi ne? Ba saidai in mutu ba?" Zarah tayi dariya "Please please dear." Rolling eyes Zarah tayi tace "Naji." Ta fada tana mikewa ta nufi akwatin nan Zarah ta mata godiya ta kwashi tarkacenta ta hau sama, ruwa ta watsa ta fito Zarah na bisa gado tana latsa waya, shiryawa tayi cikin matsatsun kananan kaya, shekeke Zarah ke binta da kallo tace "Ke meye haka?" Khadija tace "Mey?" Zarah tace "Kalli shigarki nan fa Niger ne ba turai ba, ki chanza wannan shigar taki gaskiya batayi ba," ta wani hade rai "In chanza me? So kike inta fama da atamfa kayan zafi? I can't!"

Dariya taba Zarah tace "Ay bance dole sai kinsa atamfa ba, you just have to adjust nan Niger ne ba UK ba, kuma fa kinsan munada bako nan gidan bai kamata ya fara ganinki a haka ba, sam bai dace ba ga ya mace musulma." Tsaki ta saki tana gyara zaman rigarta tace "And so? Ni nace yazo mana gida? Kawai saboda shi sai in takura ma kaina? Sam bazai yuwu ba wallahi, this is bullshit! Idan har yaga shigar da nake zata takura masa yana iya kauda fuskarsa, hope u understood?" Zarah ta girgiza kai "Ke kam dai bakida mutunci Khadija, wai ina amfanin wannan mugun halin naki? Sai kace ke kadai kika taba karatu a kasar waje? Shikenan daga zuwa turai sai kibi ki chanza halayenki ki koma fitsararriya?" Wani mugun kallo ta watso ma Zarah "Toh sannu natsatsiya! Ni kinga yunwa nakeji bari na sauka kasa..." tana gama fadan haka ta fice tana tafiyar kasaita, girgiza kai Zarah tayi ta mike don dauro alwalla.

Yau dai gaba daya a dining suka zauna don cin abinci, Zarah ce karshen fitowa tana saukowa sukayi ido hudu da Ashraf sai ji tayi gabanta ya buga, daurewa tayi ta karaso ta zauna tana murmushi ta gaishe da kowa ta zauna gefen Zarah wacce ke kokarin bude warmer din dake gabanta, sai data bude gaba daya sai ta tsaya shesheke tana bin abincin da kallo, can tace "Mummy a rasa abinda za'a dafa mun sai shinkafa? Kinfa san na dade ban cita ba ta yaya kikeso in fara cinta a yanzu?" Mummy tayi murmushi "Khadija kenan, toh me kikeso a dafa miki in ba shinkafa ba?" Ta wani yamutsa fuska ita a dole yar gayu tace "Mummy nifa can na saba cin abincinsu sheyasa sai nake ganin shinkafan ta mun wani kala na daban..." Yasir yace "Ke! Rufe mana baki a nan! Mummy kike fadawa meyasa ta maki shinkafa? In banda rainin wayau in bazaki iya mata godiya ba ay ba'ace dole sai kin ci ba ko? Wai ke meye haka? Gaba daya halinki sake yin worst yakeyi ko wane hutu kikazo...!" Bubbuga kafa ta farayi tana kukan shagwa6a, nan kowa wurin ya bude baki galala yana kallonta, can ta mike tsaye "Wallahi bazanci shinkafar nan ba! Zanje nayi order din KFC ko Pizza!" Mikewa Yasir yayi a hasale zai tsaida ta Mummy ta daga masa hannu "Rabu da ita Yasir...." zama yayi yana jin kamar ya tashi ya bata shegen kashi kila zata natsu, Zarah ta mike ta fara masu serving fried rice da peppered chicken sai salad gefe da yaji kayan hadi, bayan ta zuba masu ta tsiyaya ma kowa zobo nan itama ta zuba nata ta fara cin abinci, every second take dagowa ta kalli Ashraf wanda baisan abinda takeyi ba. Bayan sun gama cin abinci suna kan dining din basu tashi ba Mummy ce kawai bata nan, sai ga Khadija ta shigo niki niki da ledoji a hannu, a bisa dining ta dire su ko kallon kowa batayi ba ta bude kazarta da katon robar pepsi ta zauna ta fara ci, Yasir ya mike Ashraf ma ya mike yana mamakin hali irin na Khadija, Zarah ce kawai ke bata tashi ba ta zuba mata ido tana cin kayanta, gefenta laptop ce ta kunna wani series tana kallo, Zarah ta numfasa "Yanzu tsabar karya kice baki iya cin shinkafa? Uban me kike ci a da kafin ki tafi uk din?" Tabe baki tayi "Wai nikam meyasa kika fiya sa ido ne? Sanin da kikayi mun a da tou yanzu na chanza nace bazan iya cin abincin nan ba ko dole ne?" Zarah tace "Da kyau, komin tsiyarki dai nan ne tushenki, muna nan dake zaki dawo kina neman abincin namu dole kici ba!" Tana gama fadan haka ta mike ta fara clearing wurin.

****

One week later....

Ashraf ya saki jikinsa sosai da Zarah sun zama friends duk da ita a bangarenta ba haka ta dauke shi ba tana matukar sonsa, amma dai Ashraf shi kawai ya kasa bude heart dinsa gaba daya amma dai suna friendship sosai, Khadija kuwa a nata bangaren rashin mutuncin yau daban na gobe daban, gaba daya halinta bai ma Ashraf ba, miss grumpy ma yake ce mata gashi ta tsani sunan, in kuwa ta bushi iska ta bar gidan yawo take tafiya Yasir yayi zagin yayi fadan amma duk a banza. 

**

Zarah tana zaune parlor tana cin apple at the same time tana kallo Ashraf ya shigo parlon yana kallonta yace "Wai bakya gajiya da kallon series dinnan ne?" Tayi murmushi "Bana gajiya dashi, ga apple bismillah." Daya ya dauka yana ci a hankali suna fira jefi jefi, Khadija ce ta shigo da sallama, tana sanye sa doguwar riga sai ta dora hola, kujerar da Zarah ke zaune akai ta zauna tana fuskantar Ashraf, kwana 2 sunyi noticing yadda ta chanza rawar kanta ya sauka sun rasa meya chanza ta haka gaba daya, Zarah tace "Wai meyake damunki Khadija?" Yamutsa fuska tayi ta dauko apple daya taci sannan tace "Me kika gani uwar sa ido?" Zarah tayi dariya "Kwari ma kuwa, naga kinyi sanyi ne." Ta kalli Ashraf da hankalinsa ke kan tv ta sauke ajiyar zuciya, "Tou babu abinda ke damuna sa idawa." Dariya taba Zarah tace "Haka akeso ay miss grumpy." Harara ta watsa ma Ashraf "Kagani duk kai kaja man wannan sunan yanzu gashi nan Zarah tana kirana dashi." Yayi murmushi "Tou ba gaskiya take fada ba miss grumpy?" Hade rai tayi "A'a bawani gaskiya wallahi."

*****

Da asuba bayan Ashraf ya gama sallah sai kawai yaji baya son komawa bacci fitowa yayi waje, shakar iskar asuba mai hade da ni'ima da kamshi dadi yayi, zama yayi a garden ya jingina da kujera ya lumshe idanu, "Good morning yaya Ashraf." Bude ido yayi ya ganta tsaye cikin kayan bacci riga da wando purple color sai tasa hula, "Good morning miss Grumpy!" Dan bata rai tayi "A'a am not nikam." Yayi murmushi "Toh how are you?" Tace "Alhamdulillah you seem to be enjoying the cool breeze today." Yace "Yes is a good feeling." Ta dade tana kura masa ido kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Tou bari na shiga cika bacci zanyi." Ok yace mata kafin ta fara tafiya a hankali tayi ciki.

Da rana Yasir da Ashraf sun dawo daga wata unguwa suka nufi kitchen jin hayaniya, Zarah da Khadija ne tsaye suna girki, Yasir ya leka ganin jollof rice ya sa yace "Tou mutan turai har kin fara cin shinkafar ne?" Zarah ta kyalkyale da dariya harda dukewa tace "Na nawa kuma? Ay yanzu karyarta ta kare saidai kuma idan komawa tayi can." Hade rai tayi tana cigaba da abinda takeyi, Yasir ya matso kusa da ita yace a hankali "Mufa mun gaji da ganin grumpy face dinki ya kamata ki saki ranki malama." Kara hade rai tayi ta kalli Ashraf da ya harde hannu yana binsu da kallo, "Zarah please miko mun curry." Ta fada hade da juya fuskarta gefe tana sauke ajiyar zuciya ita kadai tasan yadda zuciyarta ke harbawa, Zarah ta tsare ta da ido ganin yadda take sauke numfashi sannan ta kura ma Ashraf idanu har wani murmushi take saki, gaban Zarah yayi wani mummunan faduwa kar dai tunanin da takeyi akan Khadija gaskiya ne? Kar dai son Ashraf takeyi? Ji tayi ta kasa tsayuwa da sauri ta bar kitchen din har tana hada hanya, gaba daya suka bi Zarah da kallo....

Saturday 26 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 26

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 26}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



A gigice sukayi kanta babu abinda Mama keyi in banda rusar kuka, don dole aka bata gado aka sa mata drip nan Mama ta kira Baba ta sanar masa an kwantar da Khairy idan yazo zatayi masa bayanin komai, nan Mama ta zauna gefen gadon tana share hawaye, tashi tayi jin ana kiraye kirayen sallar magrib ta nufi bathroom ta dauro alwala ta gabatar da sallah, tana zaune nan har akayi sallar isha'i ta tashi tayi  tayi sallah, tana gamawa ta zauna a nan ta cigaba da azkhar dinta, tana nan a haka aka tura kofar aka shigo da sallama Baba ne yana dauke da ledoji Mama ta amsa sallamarsa ya aje ledojin a gefe ya nufi gadon Khairy har yanzu bata farka ba, ya dan dade a haka yana kallonta kafin ya kalli Mama yace "Ya jikin nata?" Mama tace "Da sauki bata farka ba har yanzu." Yace ok ya dawo gefen Mama bisa kujera ya zauna yace "Nasan kina tare da yunwa ga abincin nan na kawo maki..." Girgiza kai tayi take ta fashe da matsanancin kuka harda shesheka yayi shiru yana kallonta can ya numfasa "Komai kikaga ya samu bawa mukkadari ne daga Allah Turai, yanzu ba lokacin kuka bane ba, yanzu meye akace yana damunta har ta fadi haka?" Ta samu da kyar ta tsaida kukan nata tace "Malam tun ba yau ba nake fadan yawon Khairy amma bataji dama hausawa sunce ka haifi yaro ne amma baka haifi halinsa ba, Malam Khairy harda kanjamau ta kwaso ma kanta..." ta fada cikin gunjin kuka, salati Baba yayi cike da tashin hankali yace "Innalillah wa inna ilahir rajioon Allahumma-jurni fi musibati, wa akhlif li khairan minha, Allahumma Indaka Ahtasibu Musibati Fa’jirni Fiha Wa Abdil li Khairan Minha, Allah kayi mana maganin abinda yafi karfinmu, kiyi hakuri nasan da ciwo amma babu dadi amma haka Allah ya kaddara mana babu makawa sai ya faru, babu yadda muka iya saidai mu rungumi kaddara hannu biyu, kisani wannan jarabta ce..." bai karasa rufe baki ba sukaji mutsu mutsun Khairy da sauri suka nufi bakin gadon suna kallonta, idonta a rufe take fadin "Ni keda kanjamau? Ni nasan boka ne yasa man ba kowa ba, in bashi bane toh wadannan ne da sukayi man fyade! Mama da Baba ku yafe mun wallahi sharrin shaidan ne duk dan in raba Yarima da matarsa garin yin hakan naje na jawo kaina, naja maku abin kunya abun fadi, na kuma goga maku bakin fenti akan wata soyayyar da bata amfeni ba saima ta jefa ni cikin masifa... boka naje na sallamawa kaina yanzu ga irinta nan, na cuci kaina na jawa kaina..." sai kuma ta fashe da kuka, duk mutuwar tsaye su Baba suka yi, kasa tsayuwa Mama tayi nan tayi taga taga zata fadi Baba ya taro, kuka ta fashe da shi wane ranta zan fita "Abinda Khairy take fada gaskiya ne ko dai sambatu takeyi? Kuce man ba gaskiya bane!" Ta kara fashewa da kuka, farkawa Khairy tayi ta bude ido tangaram tana farkawa ta fara kokarin mikewa daga kan gadon, saida tayi tozali dasu Mama sannan ta ja baya ta jingina da bango ta rakube Mama tace "Khairy abinda kika fada gaskiya ne ko ba gaskiya bane? Wai wurin Boka kika je harda sallama masa kanki?" Baba yace "Kiyi hakuri Turai yanzu ba lokacin da ya kamata ki fara mata wadannan tambayoyin bane, ki danne zuciyarki har muje gidan sannan." Kuka Mama ta cigaba da yi zuciyarta na tafasa, ita kuwa Khairy tsit tayi tama kasa koda kallonsu. Sai can wajen karfe goma Doctor ya shigo nurse na biye dashi a baya, "MashaAllah patient namu ta farka, how are you feeling now?" A hankali tace "Alhamdulillah." Bude file dinta yayi yana rubuce rubuce "Kamar yadda na fada maku a baya ku gaggauta sanar da mijinta yazo yayi gwajin nan don a gani ko bai dauke da wannan cuta," ya kuma kalli Mama dake share hawaye yace "Hajiya kiyi hakuri wannan cuta ana shan magani kuma kiga mutum yana living normal life dinsa, ita dai kawai sai an daure an dinga zuwa karbar magani, kuma sai ta dinga kula da kanta...." Baba yace "Toh Doctor abinda nake so in tambaya shine shi yaron dake cikinta zai kamu da wannan cuta?" Yace "Ba lallai bane, saidai idan an haife shi za'a iya gwada shi agani, sannan kuma kanku sai kunyi taka tsantsan kunsan fa ba dole sai ta hanyar jima'i ake dauka ba, yanzu misali idan ta yanke akaifa da reza sai ta yanke jini ya fito wani daga cikinku ya dauka a haka yayi amfani dashi toh zaku iya dauka, sannan amfani da allura daya wajen daukar jini ma yana sawa kamuwa da wannan cuta, abubuwan dai gasu nan zan maku karin bayani InshaAllah, sannan zata fara shan magani babu bata lokaci sannan zata dinga zuwa ganin likita don kula da ita kanta lafiyar tata tare da abinda ke cikinta, da fatan kun fahimta?" Suka gyada kai, yace "Da safe zan sallame ku don naga ta farka kawai za'a ajeta for observation, duk zan rubuta mata maganin da zata dinga amfani dasu sannan don Allah kar a manta a kawo mijinta a gwada sa." A sanyaye suka amsa sannan ya bata medication ya fita, nan sukayi jugum jugum babu wanda ya iya koda kwakkwaran motsi.

Haka kuwa akayi sai da safe wajen karfe sha daya na safe aka sallameta, Doctor din ya masu kwakwaran bayani da kuma magungunan da zata dinga sha, a haka suka tafi gida, a sanyaye kowa yayi jugum suka shiga cikin gida, nan Mama ta sa tayi wanka ta bata abinci da magani, kafin Khairy ta basu labari kaf abinda ta aikata, tana magana tana kuka Baba ya numfasa "Hausawa sunyi gaskiya Ummalkhairy da sukace in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere in ba haka ba kaine zaka fada ciki, yanzu ina so ki fada man wace riba kika samu a duk abinda kika aikata? Nothing right? Babu abinda kika samu sai tarin wahala da bakin ciki da dana sani, yanzu ke akan namiji kika aikata duk wannan abun? Kece kulla mata sharri, kece bin boka, kece this kece that, wannan wace irin rayuwace kika daukar ma kanki? Yanzu wa gari ya waya? Yanzu ita Gimbiya da kikayi ma haka tana nan gidan mijinta bai rabu da ita ba tana nan daram, ke har kin isa ki wucewa hukuncin Allah? Allah ya kaddara bazaki aure shi ba amma kika kafe yanzu gashi nan, inda ace ke ta kirki ce Ummalkhairy da tun lokacin hakuri kikayi sai kiga kina zamanki Allah ya kawo maki chanji mafi alkhairi wanda zaki ji dadinshi, amma duk bakiyi ba, Nidai yanzu ina maki fatan wannan ya xama izina a gareki da duk masu aikata hali irin naki, kisani Boka ko Malami basu isa su baki abinda kikeso ba, babu wanda zai baki Allah kadai xaki roka ya baki ba wani boka ba ko malami, kinsan hukuncin wanda yayi shirka? Kin cuci kanki, kin kuma cuce mu Khairy amma ni bazan tsine maki ba addua zan maki yasa wannan shine sanadin shiryuwarki ya yafe maki kuskurenki, ki daure ki koma islamiyya inda ace kinada ilimin addini sosai da wani abun ma bazaki fara aikata shi ba, rayuwa da duk abinda ke cikinta a hannun Allah take don haka ki cigaba da istigifari sannan ya zama dole ki nemi gafarar wanda kika cuta, ki natsu Khairy ki daidaita rayuwarki kisan annabi ya faku, wallahi duk abinda ka shuka zai dawo maka ko alkhairi ko kuma sharri, da fatan kinji abinda na fada maki? Allah ya shiryeki ya saukeki lafiya ya baki miji na gari, inaso ki fita rayuwar su Yarima ki ji da taki rayuwar ki kyalesu suyi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da natsuwa, Allah shi kyauta..." Mama tace 'Amin, ina fatan kinji duk abinda mahaifinki ya fada maki? Wannan ya zama izina a gareki ya zamo shine sanadin shiriyarki." Tace "Amin." Bayan sun gama mata nasiha mai ratsa zuciya ta tashi da gudu ta nufi dakinta ta fada kan gado ta dinga rizgar kuka, kukan bakin ciki, kukan takaici da kunci, kukan dana sani, kukan nadama ji take inama a maida hannun agogo baya ta farka taga duk mafarki ne? Inama zata ga duk wannan abubuwan basu faru da ita ba? Inama zata koma baya ta gyara kuskurenta? Inama? Inama?....!

*********

Kafin asuba ya farka duk da yayi bacci late amma ya tashi da wuri, bathroom ya shiga ya dauro alwala ya fito ya gabatar da nafila yana tsakar karatun qurani Yasir ya farka nan bayan yayi alwalla sai suka tafi masallaci don yin sallah. Haka suka dawo suka kwanta bayan sun gama sallah shidai tunaninsa shin Zarah na sonsa? Batada wanda takeso? Nan ya kuduri a ransa zai gane indai bata sonsa toh sai ya san yadda aka dakatar da auren, in kuma tana sonsa zai kwantar da kai bori ya hau watakon ya kuduri zai sallama mata zuciyarsa da kuma ruhinsa!  Dafa shi akayi Yasir yace "What's wrong??" Ya juyo ya kakalo Murmushi "Bakomai me kagani?" Yasir yace "Naga tun dazu ka zurfafa a cikin kogin tunani, kar dai tunanin Hoodah ne ke dawainiya dakai?" Zaune Yasir ya mike "Look Ashraf, Hoodah yanzu matar wani ce dole zakayi hakuri ka manta da ita, kasani bai kamata kana tunanin matar wani ba...." zaune Ashraf ya tashi shima yace "Ko kusa ba tunanin Hoodah nakeyi ba, ina tunani ne akan Zarah...." Yasir yace "Have you fallen in love with her?" Ashraf yayi dariya da son kawar da zancen ayace "Ka tabbatar Zarah na sona? Zata zauna dani? Batada wanda takeso?" Yasir yayi murmushi hade da dafe kafadun Ashraf "Kamar yadda na fada maka Zarah is the most simplest girl you'll ever meet, wadda bana maka fatan ka hadu da ita shine kanwar mu wato Khadija, ita kwatakwata halinta yasha bambam dana Zarah, she's kind though but she got nerves...." Ashraf yayi murmushi "Allah sarki kasan sai kaga a gida daya kowa da halinsa, wai nikam tana ina Khadija? Kullum sai dai na dinga jin labarinta gun Zarah amma ban taba ganinta ba?" Yasir yace "Kar ka damu zaka ganta ay, ita Khadija karatu take tana 300 level tana UK, amma munyi waya tace mun tana nan zuwa very soon, zuwa jibi ma maybe..." Yasir ya kuma cewa "Kusan tsarararaki ne itada Zarah shekara daya ke tsakaninsu, amma fa suna mugun kama, saidai fa Khadija yar lele ce gaba daya Mummy ji take da ita, karfa kace ba'a ji da matarka amma dai tafi ji da Khadija." Ashraf yace "Allah sarki, toh wai ita Zarah ta gama karatunta ne?" Yasir yace "Ta gama kasan ita Khadija ta tsaya wasa da rawar kai sheyasa har Zarah ta kammala ita tana nan, saidai sa'ar ta daya Khadija dai yanzu ta kusa kammalawa don semester daya yarage ta shiga 400 lvl yanzu haka exams sukeyi." Ashraf yace "Ok, Allah toh ya dawo mana da ita lafiya." Yace "Ameen." 

Washe gari karfe tara da kusan rabi Zarah ta shigo da sallama dauke da tray din abinci, nan ta gaishe da Ashraf dake shanya towel din da yayi wanka ya amsa da murmushi saman fuskarsa, yace "Zarah nagode da dawaniyar da kike yi fa, nace maki ki dinga bar man a bisa dining zan dinga ci a can." Tayi murmushi zuciyarta na harbawa, binshi da wani asirtaccen  kallo tayi tace "Ba dawiniya bace yaya Ashraf karka damu, yanzu dai ina kwana?" Yayi murmushi "Lafiya lau Alhamdulillah ya kike?" Tace "Alhamdulillah, ga breakfast nan kaci, idan kagama zan dawo in dauke." Yace "A'ah karki damu zan kai da kaina ma." Tayi murmushi ta mike tsaye "A'a zan dawo in dauke kawai ka kirani." Tana gama fadan haka ta mike ta fita daga dakin tana murmushi. 

5 days later....

Tun safe ake shirye shiryen tarbar Khadija, rabonta da gida ya kai shekara daya da wani abu a cewarta ita bata cika son xama Nigeria ba it's suffocating her, karfe 12 na rana jirginsu zai sauka don haka Mummy ta umarce Ashraf da Yasir da suje su daukota, nan suka tafi lokacin karfe sha daya da minti kusan talatin, a mota ne Ashraf yace da Yasir "Lallai yau na gasgata zancenka Yasir wato dai Khadija yar lele ce haka?" Yasir yayi murmushi yana concentrating a titi yace "Ay bakaga komai bama." Karfe 12 da minti sha biyar suka isa, bayan sunyi parking ko fitowa daga motar basuyi ba sai ga jirginsu ya sauka, cikin farin ciki Yasir "MashaAllah sun iso, nasan nan da minti goma zata fito." Nan sukayi tsaye suna jiranta bayan minti kusan sha biyar Yasir ya hangota ta fito tana jan akwatinta, nan Yasir cikin farin ciki yace da Ashraf "Kaganta can tana sanye da kananan kaya." Daga ido yayi yana kare mata kallo, sanye take da bakin wando sai yar ciki da leather jacket, tana sanye da hula black color ta riko hand bag dinta da wayarta, tafe take cike da yanga da kaisaita kai kace diyar wani shugaban kasa ce ko gwamna, bakinta kuwa chewing gum ne take tauna in style, fuskarta na manne da bakin glass wanda ya rufe mata kusan rabin fuskarta, tun kafin ta karaso turarenta yabi ya cika masu hanci Yasir ya nufi inda take da sauri tana ganinsa ta saki akwatinta ta rugo da gudu ta rungume shi tana ihun murna, bayan sun gama hugs din ta sake shi ya dauko mata akwatinta suka soma takowa wurin motan, suna zuwa daidai nan ta bude mota zata shiga taji ance "You're welcome Khadija..." ta dago idanunta tana kare masa kallo, tana duban Yasir daya bude booth yana kokarin sanya mata akwatinta ciki tace "Bros who's he?" Yayi murmushi "That's my friend Ashraf, remember him lokacin muna school?" Ta dan yamutsa fuska "I can't remember...." Yasir yace "It's ok then, ki gaishe shi ko?" Ta kalli Yasir tana kokarin bude mota "But you know I don't talk to strangers..." ta fada tana kokarin bude kofar motan, Yasir yayi karaf ya rike mata hannu "Ashraf is not a stranger, mind you he's family now ki gaishe shi in ba so kike mu kwana a nan ba." Takowa tayi gabanshi ta tsaya dab dashi ta cire glass din idanunta tana kallonsa from head to toe sannan tace "Sannu."

Friday 25 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 25

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 25}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



A hankali yayi knocking kofar dakin  amma ga mamakinsa akayi shiru, tun yana sa ran xata bude har ya hakura ya daina knocking din, sam Hoodah bata nuna cewar ma taji knocking dinnan ba, yafi minti goma a haka har dai ya gaji, ajiyar zuciya ya sauke ya fice don tafiya masallaci don yaji ana kiraye kirayen sallar azahar, yana gamawa a hanyarsa ta dawowa ne yake ayyanawa a ransa cewar shifa ya gaji da zaman gabannan da takeyi dashi sai kace wasu enemies? All he knows is that he loves her yana sonta yana kaunarta har cikin ruhin zuciyarsa, saidai ya kudiri a ransa tilas yau zasuyi magana no matter what, dole zata kulashi kuma dole zai nuna mata yana kaunarta don haka dolenta ta yarda, idan ma ta kama ya balle kofar tou babu makawa zai balle ta. Yana dawowa ya shiga ya watsa ruwan dole don ba karamin zafi akeyi ba, dama dai kusan 2 weeks kenan bai tashi wanka sai azahar ta wuce, shin dama haka damuwa take? Shi tunda yake baisan meye damuwa ba sai yanzu da soyayya ta sako shi a gaba yasan ma'anar damuwa. Abinci ya fita waje yasa akayi masa order, daga can yayi tafiyarsa haraba shine bai dawo gida sai bayan sallar isha'i, sashen su Abbi yaje ya tafi dakinsu ya kwanta a nan ya samu yayi bacci, sai goma da kusan minti sha biyar ya farka tunda suka dawo daga agadez dama dai haka yakeyi kullum don indai sashensu ne toh fa bai iya baccin kirki saboda tunanin Hoodah dake sakashi a gaba. Yana shigowa sashen nasu dakin Hoodah direct ya nufa nan ya fara knocking don har yanzu rufe take kofar, tun yana yi a hankali har ya fara bubbugata da karfin bala'i wane zai balle kofan "Hoodah kizo ki bude kofar nan! Idan ba haka ba wallahi I will break it! Haba Hoodah wai ya kikeso inyi da raina? Sonki nakeyi kamar zan mutu tou wallahi kin wahalar dani enough, nace kizo ki bude min kofa Hoodah!" Shiru kakeji Hoodah batada niyyar tasowa ta bude, nan ya dinga magiya, yayi masifar da bala'in, yayi rarrashin ya bada hakuri amma duk a banza. A hankali ya silale a gurin ya dafe kai ya kai tsawon minti talatin a haka ya rasa meke masa dadi, ji yake kamar sonta zai halaka shi baki daya don wani iri bugu zuciyarsa keyi kamar zata huda kirjinsa ta fito, sai da ya gaji da xama a nan ya mike da kyar ya nufi kitchen, custard ya hada mata ya dawo dakinsa ya fara duba spare keys, dukkansu ya kwaso dan shidai baisan wane bane a ciki, daya bayan daya ya dinga saka su babu wanda ya dace dan babu key din a ciki, duk wanda yayi trying bai bude ba sai yasa hannu ya buga kofar da karfi akan tazo ta bude amma yadda kukasan yana magana da bango haka Hoodah ta koma, duka bayan ya gama tying ya rage saura key daya "Hoodah wallahi ko kizo ki bude man kofar nan ko kuma wallahi in balleta, kuma kika bari na balla duk bazamu kwasheta da dadi ba a cikin daren nan! Haba wai me kike maidani?" Yana fadan haka ya zura key din ciki sai gata ta bude! Wata uwar ajiyar zuciya ya sauke, ya buga kofar a zuciye ta bude da karfi daidai lokacin ne Hoodah ta taso zata bude don a tsorace take yadda yake buga kofar ya kuma bata tausayi matuka, yadda ya turo kofar shi yayi sanadin tunkudeta da yayi tayi baya zata fadi yayi sauri ya riko ta, ajiye cup din yayi kan drawer bai damu da masifar da zatayi masa ba...

Kokarin kwace kanta ta farayi daga rikon da ya mata, amma abin mamaki kanshi dake bisa wuyanta sai da taji kamar yana digar hawaye, hankalinta bai kara tashi ba saida taji yana sheshekar kuka yana magiya akan kar ta sake masa irin wannan ya horu horuwa mafi muni, "Hoodah nasan nayi maki babban laifi na aikata kuskure, na maki promises din babu wanda nayi fulfilling, but believe me I do love you so much! Bana tunanin akwai namijin da zai tsinci kanshi a halin dana tsinci kaina Hoodah, abinda nayi is uncalled for I shouldn't have did what I did the anger and everything! Ki yafe mun Hoodah... Hoodah bansan ina sonki har haka ba saida bakya tare dani, it was the worst days of my life, ki dauki duk abinda ya faru a matsayin kaddara mu sake bude sabon page na rayuwarmu, can you love me and trust once again?" Kuka yake har can kasan zuciyarsa, a nan sunfi minti sha biyar a haka while they hugged each other gaba daya zuciyar Hoodah ta kare tausayinsa ne ya cika ta, can tayi karfin halin goge nata hawayen kafin ta dago shi ta fara share masa nasa hawayen, "It's okay ka daina kuka, duk kukan na meye? Ba dan Habibty ta yafe maka bane? Ka manta ranar da ka ajiye ni a kofar gidanmu? Me nace maka? Na fada maka ranar nace zaka dawo kana rokona gafara akan na yafe maka what did I tell you? Ba nace zan yafe maka ba kuma zan fahimce ka ba? Nasan inda ace nice kai zan aikata fiye da abinda ka aikata ma because abubuwan ne gasu nan kala kala ance nayi, amma abinda duk yafi hurting dina da kaki tsayawa ka saurareni, karshe ma Sultan ka daukeni daga gidannan saboda extent din tsanar da kayi mun, shin wai dama haka zaman aure yake? Dama haka soyayyar take?" Hawayenta ta dakata ta share ta kirkiro murmushi tana kallonsa don ta kwantar mashi da hankali don da alama yau kukan nashi baida niyyar karewa, "Yes na taba soyayya I loved my cousin long ago, but bayan munyi aure komai ya chanza, soyayyarka ta shigeni, ba shigar sauki ta mun ba ko tausayi, inata denying amma I couldn't hold it, tausayinka a da sheyasa mun sonka a cikin raina, amma bayan ka chaza halayenka ka rikide ka koma monster nazo har shakkar ka nakeyi bana gabanka saboda kawai anaso a hadamu, amma kamar yadda na fada maka na yafe maka kuma na fahimce ka. Duk abinda na maka bayan mun dawo daga agadez ba'a san raina nake maka ba amma yaya zanyi? Inaso ka dandana abinda na dandana koda kadan ne, inaso kayi realizing how important I am in your life, so ka daina kuka komai ya wuce." Hugging dinsa tayi a hankali tana kuka mai ratsa zuciya, saida suka sha kuka suka gode ma Allah kafin ya saketa gaba daya dole sukaje suka hada wani sabon custard din suka sha sannan suka dawo daki. A hankali ta fara bashi labarin rayuwarta tun yarinta duk abinda tayi going through, da azabar da Umma ke gana mata har kawo yanzu da take a gabanshi, tana kuka yana kuka saboda dana sanin da yayi "Hoodah Habibty, I am truly sorry bansan haka kika taso ba cikin rashin mahaifiya yanzu Abba yana zaune da ita a haka? Anya haka ta barshi? She even killed your mom! Kai innalillahi wa inna ilahir rajioon, am sorry am sorry am sorry Hoodah this shouldn't have happen to you...." Girgiza kai takeyi tuna mata da wannan wound din na kisan Amminta ya dawo mata kamar yanzu take gani, hawayenta ya share mata yayi scooping fuskarta da hannuwansa biyu, "Hoodah look at me, today I am going make you a promise, zan daukar maki fansa she must be brought to justice she can't be roaming around scot free, you don't have to worry, zan daukar maki fansa I promise you Umma will regret ever been born!" Gyada kai takeyi tana gunjin kuka da sauri tayi hugging dinsa tana cigaba da kuka "Thank you thank you so much...." ya dago ta yana share mata hawaye "So where is this your cousin?" Ta share hawaye "Bansan ina yake ba, he left after Umma ta fada mana maganar aurena har yau maganar da nake maka ban sake ji daga garesa ba, ya kashe wayoyinsa ba'a samunshi." Ya share mata hawaye "It's okay, Umma is a cruel woman, amma karki damu sannan inaso kisa ma ranki kinga shifa komai mukaddari ne daga Allah, komai da kikaga ya faru a rubuce yake bawa bai isa ya guje wa kaddararshi ba, sai kiga abinda ka kwallafa wa rai kanaso ba shi bane alkhairi sai wanda bakaso, I even realized I have never loved Khairy before, sai da kika shigo rayuwata sannan nasan menene asalin so, Hoodah I love you so much,". Batasan lokacin datace "I love you too." ba... wani irin daukarta yayi ya dinga juyata tsakar daki sannan yayi hugging dinta ya dinga aika mata da sakonnin kisses ta ko ina yana nuna mata how much she means to him....

***

"Malam wallahi bazata sa6u ba! Kaji na rantse ko? To wallahi ko sama da kasa zata hade sai Ummalkhairy ta fita ta toya min awarar nan, ubana ne kai? jimun mutum kai! Sai ji kake kamar kai ka haifeni tou bazai yuwu ba! Na rantse maka da Allah ko? Tou ka fita idona tun ban maka rashin mutunci ba!" Yayi murmushi "Turai kenan, yanzu ni ban isa in fada maki magana ba kiji? A matsayina na uban Ummalkhairy nace kar ta fita toya awara kince sai tayi? Wai baki tausayinta ne? Ki duba fa halin da take ciki?" Tayi shewa da dariya "Aiko ya zama tilas sai tayi shi nima a matsayina na uwarta na kuma isa da ita nace sai tayi!" Juyowa tayi ta jefi Khairy da wani irin mugun kallo wacce duk ta lalace ta rame anya ma babu wani abu dake damunta banda ciki? Raku6e take gefe sai kukan fitan rai takeyi "Zaki daina wannan kukan munafuncin ko kuwa? Bari kiji in fada maki wallahi ko jini zai ringa zubowa daga idanunki sai kinyi tuyar awarar nan a kofar gidannan ko uban wa ya tsaya maki kuwa! Wannan shine horonki da dauko mana abun kunya don ubanki!" Sautin kukanta ne ya karu, Baba ya sa kai ya fita yana girgiza kai, wata irin mangara ta kai mata har saida ta kife kasa sannan ta kai mata kwanya "Zaki matsa ki bani wuri ko sai na kara mauje ki? Wallahi tallahi ki kiyayeni! Shi kuma uban naki sarkin tausayi ko tausayin uban wa ga yar iska irinki! Daga kawai zaki nema ma kanki sana'ar kanki? Tou kisani rayuwarki fa ta riga ta sauya, uban wa zai dinga biya maki kudin antenatal? Dama fita kikayi daga gidannan kisan nayi ki fara hura wuta, ke dan ubanki inda kinada hankali yaci ace kina taimaka man bakida aiki sai shegen yawo, yanzu yar suyar awara ce don ance kiyi kika bi kika tada hankalinki toh wallahi tallahi sai kinyi shi!" Tana gama fadan haka ta ja uban tsaki ta wuce ciki ta bar Khairy na gunjin kuka.

Tafi minti talatin a zaune tana kukan fitar rai, can dai ta mike da kyar ta dauko kaskon suya dama ta riga ta hada awararta ta dauko ashana da komai da zata bukata da kujerar zaman kasa, tana fitowa mutane suka fara binta da kallo wasu harda nunata, toh wai a haka zatayi cinikin awarar ma mutane na gudunta? Nan da nan ta zauna ta fara hada wuta mai yayi zafi, tafi awa zaune ko kallon arziki babu wanda yayi mata balle ma ta sa ran za'a siya, babu mai siya in ba almajirai ba suma bata wuce ta biyar ta goma, har bayan Isha'i tana zaune a wurin gaba daya cinikin da tayi na naira dari biyu da ashiri kacal, ita tsoron shiga gida ma takeyi. Can wurin karfe tara dai tayi shahada ta mike ta soma kwashe kayan, a bisa verandar tsakar gida ta iske Mama ta aje kujera tana azkhar, har kasa ta tsuguna ta mika mata kudin "Mama ga cinikin yau..." warce kudin tayi kamar zata balla mata hannu ta dubi kudin shekeke, "Me nake gani haka? Dan ubanki tun safe dari biyu da ashirin kadai kikayi? Kai amma anyi yal banza!" Hawaye Khairy ta kuma sharewa "Mama ina laifin dari biyun? da ban kawo ko sisi bafa?" Wani irin gigitaccen mari Mama ta dauke ta dashi fuskar nan daure murtuk! "Ni kike fadawa haka dan ubanki? Tou wallahi gobe kikawo man kasa da dari biyar sai na lahira yafiki jin dadi dan ubanki shegiya! Tashi ki bace man da gani! Kuma ki shiga ki fito ki zo kiman wanke wanke gashi nan ya taru!" Tashi tayi jiki na rawa ta shiga ciki tana kuka, kan gadonta ta fada ta dinga rera kuka ta mugun gajiya aikin da Mama ke sata ko yar aiki ta aje bazata dinga sanya ta irinsa ba. Numfashinta har wani sarkewa yakeyi kuka take kamar ranta zai fito, ji take gaba daya rayuwar ta fitan mata daga kai, gaba daya ji take a duniya babu wanda ya kaita shiga kunci da tsananin damuwa..

Washe gari tun karfe goma Mama ta hankado ta waje ta zaune kan kujera, ta hada komai da komai na suyar awara gaba daya kallon da ake mata cikin unguwar nan bata sonshi gani suke kamar wata dodo ce ta fito, a hankali ta fara tuya awarar nan don tanaso ta gama taje asibiti yau ne ranar farko da zata fara ganin likitan dan cikinta yanzu watansa biyu harda wani abu, har karfe biyu ta samu da kyar tayi dari bakwai, haka nan ta tashi ta kwashe kayan Mama na tsakar gida tana jiranta tace "Ke zo nan dan ubanki! Nawa kikayi yau?" Jiki na kyarma ta mika ma Mama kudin "Naira dari bakwai." Wata irin kwanya Mama ta sakar mata akai, wani irin ihu ta kurma kwanyar ta kuma ratsa mata kai "Sa'ar ki daya asibiti zakije yau da sai naci ubanki cikin gidannan! Tashi muje!" Da sauri ta mike har tana hada hanya suka fito tare karshe Mama saidai ta tasa niqab don saboda yadda ake binsu da kallo cikin unguwa. Da kyar suka samu mai adaidaita suka tafi asibiti, da isar su suka biya kudi suka fiddo kati nan suka bi layi don itace ta hamsin da hudu (54). Nan suka fara bin layi basu aka kira su ba sai karfe biyar na yamma, a gajiya suka shiga dakin likitan, yana zaune sanye da farin glass ya basu izinin zama, suka gaishe shi ya bude file dinta yana murmushi yace "Ummalkhairy right?" Ta gyada kai yace "Ok." Kwanciya yace tayi ta bude cikin ya daddana sannan ya kunna scan machine yayi mata scan saida ya gama ya kalli Mama yace "Akwai general test din da zatayi zata kawo mana idan an gama." Nan ya rubuta masu suka tashi suka fita suka nufi Lab, ba bata lokaci duk aka gidanar da duka tests din aka kammala suka basu results, nan suka koma wajen Doctor, yana duba wasu yace su dan jirashi minti kadan, sai bayan kusan minti biyar yace su shiga, bude paper din yayi ya fara dubawa "Your sugar level is normal, Bp is normal, no malaria...." shiru yayi yana kallonsu Mama gabanta ya fadi yace "But there's something...." Mama ta dafe kirji "Doctor mey?" Ya numfasa "Zan iya ganin mijinta, don dole shima sai an gwada shi aga ko bai dauke da kwayoyin wannan cuta..." a razane Mama tace "Wai wace irin cuta ce Doctor dan Allah ka fada mana!" Numfasawa yayi cike da alhini yace "Wato ummalkhairy tana dauke da cutar hiv aids!" Ay wani irin salati Mama ta rafka ta fashe da matsanancin kuka, ita kuwa Khairy gaba daya duniyar juya mata ta dunga yi kwalwarta ta tsaya cak da aiki, kallon likitan take ba kakkautawa daga bisani ta fasa wata razananniyar kara kawai sai gani sukayi ta fadi tim kasa!

Thursday 24 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 24

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 24}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Cak ya tsaya yana kallonta jikinsa kaf babu inda baya kadawa, abinda yake gani cikin idanun Hoodah ba karamin tsoro yaji ba da alama dai ta matukar zuciya, fushin da yagani bawai abu bane da zai iya kawar dashi lokaci daya yana bukatar lokaci. "Hoodah please listen to me, don't blame me for everything that has happened zuciyata zata iya daukar komai amma banda fushinki, will you listen? Wallahi bansan meya shiga kaina ba Habibty kamar wanda ake controlling haka na koma... like I have no control over me anymore."  Gaba daya ya rasa ma abinda zai ce mata anymore. Ko kula shi batayi ba ta fara kokarin sauka daga kan gadon, ta wani fizge drip din dake hannunta take ya fara digar jini ko damuwa batayi ba ta wani cire oxygen din very painful, saidai duk wani external pain din da take ji bai kai ciwon da zuciyarta ke mata ba ta shafe komai. "Ba sai kabani hakuri ba Sultan, I don't care anymore, idan kaso aljana ma zata iya controlling dinka I don't care." Tana gama fadin haka ta dafe gadon don biyu biyu take gani ta zura takalmanta ta fara tafiya tana hada hanya hawaye kuwa kamar an kunna pampo. Wani irin wawan riko yayi mata da tilas sai data fada jikinshi, ganin yadda take kokarin fizge jikinta daga gareshi tana wani irin gunjin kuka, yasa a tsorace ya kara riketa gam gashi daga gani ko karfin arziki bata dashi "Ina kuma zakije with this condition Hoodah? Can't you see you're sick and weak?" Ya fada cikin confusion don zuwa yanzu yama rasa abinda ke masa dadi ya rasa ta cewa "Zan tafi duk inda Allah ya kaini, meye amfanin zamana a asibiti? Ciwon da nakeji a jikina bai kai ciwon daka dasa man a cikin zuciyata ba Sultan, you hurt me deep it's damn painful, and kar ka damu I will be ok by myself you don't have to worry." Tana gama fadin haka tawani fizge jikinta daga nashi ta bude kofar fita baki daya a guje kamar wacce aka koro, cikin hanzari Sultan ya bita amma da alama dai Hoodah ta gudu tama fita daga asibitin, kudin asibiti ya biya yayi masu bayanin cewar Doctor ya maida marar lafiyar a gida zata karasa jinyarta a can, da gudu ya fito kamar wanda aka ce yazo yaga gawar Hoodah, nan fa ya hau dube dube babu inda bai duba ba kaf asibitin nan babu alamun Hoodah, har dai waje ya dinga bi yana dubawa amma bata nan, nan ya hau mota cikin hanzari ya hau titi, cikin sa'a ya hangota bisa mashin cikin go slow in banda kukan fitar rai babu abinda takeyi kuka take iya karfinta har mutanen dake bisa ababen hawa suna binta da kallo, babu damar da zai sauka haka ya dinga bin mashin dinnan, wani lokaci su bace masa ya bar ganinsu sai anzo wani junction din suke sake haduwa, ya dinga kallonta hawaye cike a idanunsa ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya surota daga kan mashin dinnan, kukan da takeyi ba karamin affecting dinshi yake ba haka yakejin kukan nata har kasan ransa, ji yake har wani sukanshi yakeyi cikin rai gaba daya hawayen nasa ma ya kasa rike su nan suka dinga saukar masa yana hade wani abu kamar madaci, ganin da gaske Hoodah duniya zatabi kamar yadda ta fada yaga an ajeta cikin wani daji, tana sauka taga babu wasu kudi a hannunta nan ta bar mai mashin tsaye yana jira ta bashi kudinshi, mamakinsa bai wuce yar sarki ba a haka saman mashin? Anya lafiya kuwa? Ita kuma a hankali ta juya ta fara tafiya cikin dajin nan gefen mai mashin dinnan Sultan yayi parking ya fito ya biya shi kudinsa, cike da tsoro da kuma fargaba ya fara binta a hankali kar dai ace kashe kanta zatayi? Take ya dinga binta a tsorace, wani wuri yaga ta tsugunna hade da rungumo gwiwarta, kuka takeyi irin wanda ke girgiza dan adam, ya kusa minti goma yana kallonta tana wannan kuka ita duk a tunaninta ita kadai ce a wurin, tasan yanzu ko tsafi takeyi bata isa ta koma gida ba, tasan halin Umma sarai ita yanzu ko fuskarta ma bata son gani, tasan idan ta koma to tabbas babu abinda xai hana Umma kashe ta, ganin kukan nata yayi yawa gashi bawani isassar lafiya gareta ba yasa Sultan ya matso kusa da ita sosai, bai tsaya wata wata ba kawai ya sureta tana shure shure tana dukan kirjinsa shi kuwa bai damu ba kawai ya bude mota ya saka ta a ciki, da sauri ya zagaya ya shiga ya danna lock driver ya jasu, ko tanka shi batayi ba don gani take ma yi masa magana bata baki ne, abubuwan da yayi mata ba karamin ciwo sukayi mata ba, gaba daya zuciyarta ciwo takeyi, tun tana ganin hanya sama sama har baccin wahala ya kwashe ta. 

Bata kara sanin inda kanta yake ba saidai ta farka tagansu cikin garin Niamey, bude ido tayi taganta cikin wata motar daban nan tafara kallon garin kamar yaune zuwanta na farko, da mamaki ta fara bin garin da kallo ganin har dare yayi da alama ma har isha'i angama, har suka iso gida babu wanda yace koda uffan ne a cikinsu, parking driver din yayi, yayi unlocking dinsu, Sultan ya fito ya zagaya ta gefenta ya bude mata kofa yace ta fito, wani irin mugun kallo ta watsa mashi ko gezau batayi ba ba ma tada niyyar fitowa, "Hoodah magana fa nake maki? Nace ki fito mu shiga gida." Hawayen da suka taru a idanunta ta maida "A lokacin da babu abinda nake so face zama gidannan me kayi man Sultan? Fitar dani kayi as if I mean nothing to you, don haka yanzu bana bukatar zama a gidanka, nasan banida inda zanje amma kuma bazan zauna gidannan ba anymore ka kaini hotel." Kallon mamaki ya bita dashi  "Hoodah nan fa gidan mijinki ne! Bakida inda yafi nan a halin yanzu, ki fito kishiga nace," tabbas zasu iya kwana a haka yanayin yadda yaga tawani kafe, "Kai bakaji kunyar cewa gidan mijina ba? Ashe dama zaka iya zama da wacce ka tsana! Wacce bakayi trusting ba kace mai bin maza, mazinaciya! I am indecent ko? Wato ka auro karuwa." Wani irin wawan numfashi yaja "Hoodah kar ki kara kiran kanki da wadannan munanan kalamai...." bai karasa magana ba ta tari numfashinsa "Saboda me? Saboda ina tsoronka? Har ka manta me kace mun? Lokacin da Umma tace maka nayi ciki meyasa ka yarda? Har kake ikirarin you can't accept it? Wai me ka daukeni ne Sultan? Yar iska? Ko karuwa? Ko kuwa rashin yarda dani ne yasa ko me akazo aka fada maka akaina sai kayi saurin yarda? Na fada maka ka kaini hotel ko in sauka inje in hau taxi."

Abinda ya lura dashi shine Hoodah meant every word she said, bai kara ce mata komai ba kawai ya sureta ta cak ya shige da ita ciki nan driver din gidan shine ya zo dama tuni ya fita daga motan kafin su gama ya fito masu da akwatinsu ya bama dogarawa suka shiga da shi ciki, bai ajeta ko ina ba sai cikin dakinta, kallon dakin yayi take wasu memories suka dinga dawo masa, itama dakin take kallo take sai hawaye, nadama marar iyaka Sultan yayi duk da yanada tabbacin abubuwan da ya aikata bada saninsa bane wani abin kamar baida control a kansa ne, kasa tsayawa yayi cikin dakinta yadda gabansa ke bugawa kawai sai ya juya ya fita daga dakin bai kara tanka mata ba. Ta jima a zaune tana share hawaye sannan ta mike tana tafiya da kyar saboda weakness ta shiga bathroom tayi wanka, tana fitowa ta kimtsa cikin kayan bacci marassa nauyi nan taji cikinta na kugi ta mike ta nufi kitchen a nan ta iske shi yana soya sausages gefe kuma indomie ce ya dora har ta kusa tsanewa daga shi sai singlet da boxers, tana shigowa ta wani hade rai ta kauda kanta gefe don ita ko ganinshi bata son yi balle ma har taji soyayyarshi ta kara yin tasiri a cikin ranta. Tana ji yana mata magana akan ita yake ma abinci amma ko kallon inda yake batayi ba, wanke kettle tayi ta zo ta zuba ruwa a ciki ta kunna ta hada custard ta fita. 

Haka suka cigaba da rayuwa kullum sai Sultan ya shigo dakin Hoodah yafi a kirga amma ko sau daya ba zataji tausayinsa ba balle ma har ta daga kai ta kallleshi, ko a parlor suka hadu it's either ta latsa waya, ko tv ko kuma ta kirkiri baccin karya. Satinsu biyu da dawowa amma tunda suka dawo magana bata ta6a hada su ba, in ba gaisuwa ba Hoodah bata tanka masa, babu irin roko da magiyar da bai mata ba amma duk a banza, kullum bai fi kalma uku ke hadasu ba daga ina kwana? Ina wuni? Sai kuma sai da safe. Gaba daya Hoodah ta dawo gidan kamar wata stranger tace toh meye amfani ta cigaba da nuna mashi kulawa bayan bai yarda da ita ba? Sannan babu abinda yafi mata ciwo yadda yace ta hada kayanta kiri kiri ya nuna baya bukatar cigaba da zama da ita tace toh ay ba amfanin ma ta cigaba da kula shi, abinda kuma yafi mata ciwo fiye da komai lokacin da Umma ta alakantata da mai cikin shege wai he can't accept it? Wato kawai tana fada har ya yarda kenan? 

Kullum aikinta kenan daga kallo, latsa waya, tunani, azkhar sai bacci. Ta daina girki ta daina cin abinci, in taga dama ta sha custard ko tea, ko yoghurt su kadai take sha, komai ya siyo ya kawo mata in zai shekara rokonta taci bazata ci ba sai dai ya hakura, ko kallon banza ma bata mishi ballantana ma yasa ran zataci. Tunda suka dawo kuwa yama daina fita haraba, duka duka baifi sau uku yaje ba. 

Yau ma kamar kullum tana zaune kan dining ta hada custard tana sha a hankali duk ta kara ramewa tayi wani fau da ita, Sultan ne ya shigo da ledar take away a hanunsa har wani duhu yayi shima duk ya rame, tana ganinshi kawai ta mike ta dauki cup dinta da niyyar shigewa daki taji ya riko mata hannu, rabon daya tabata tun ranar daya nemi yayi hugging dinta ta rufe ido ta karta masa wani irin rashin mutunci, yanzu ma wani irin juyowa tayi a fusace tana jefa mashi wani warning look hade da fizge hannunta cike da tsantsar masifa amma kafin ta kai ga magana taji yace "Hoodah ina sonki, san da bansan adadinsa ba, bansan ya kike so inyi da raina ba please ki daina fushin nan da kikeyi ki yafe mun Hab...." kalmomin kasa fitowa sukayi a sanadiyar wani wawan tsaki dataja harara ta watsa mashi ta wani shige daki ta buga kofar da karfin bala'i ji kake garam! Har dan firgita yayi data banko kofar kuma ta danna mata lock, shikenan yau yaga ta kansa yasan bazata yafe masa ba ya riga yasani, tsaye yayi a wurin kamar an dasa shi yana bin kofar da kallo cike da mamaki gashi kuma ya kasa wani kwakkwaran motsi, shifa ganinta kawai yakeso yayi baice dole sai tace tana sonsa ba, ta tsaya ma ta sauraresa ta kuma gasgata son ta yake mata, wai shin dama haka soyayya take? Ashe dama haka soyayya take da ciwo? Take wani irin bakin ciki ya mamaye masa rai, tun lokacin daya fahimce ya kamu da sonta amma ya kasa yarda shine yayi tunanin ya dauke ta daga gidanshi yayi zaton zai daina jin abinda yakeji in bata kusa dashi, amma daga ranar da ya maida ita gida rayuwarsa ta tsaya masa cak, ya lura rashin gani nata shine mafi azaba daya taba dandana a ransa mafi muni ma kuwa, a haka dai ya daure kuka ne kawai baiyi ba komai ya chakude

masa cikin rai. First ganinta da yayi bayan ya maida ita gidansu ji yayi kamar an sauke masa wani irin katon dutse a cikin zuciyarsa take yaji bata masa nauyin da take masa da bata tare da shi, bai taba jin dukan zuciya kamar yadda yaji a lokacin, baisan abinda yayi holding dinsa back ba lokacin da Umma take dukanta dama kana jin kakasa kwakkwaran tunani wani lokacin? Gashi yanzu sun dawo karkashin inuwa daya amma ko kallon arziki Hoodah batayi masa ba, he needs her more than anything else in the world wani dan guntun kwalla ya goge kafin a hankali ya taka yaje bakin kofar dakinta....

Tuesday 22 June 2021

YAR AGADEZ PAGE 23

YAR AGADEZ

 

 

              {Page 23}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



2 WEEKS LATER

Tun ranar da Sultan ya sauke Hoodah gida bai sake waiwayarta ba, bai kira ba baiyi text ba, gashi Abba yayi wata tafiya baya kasar ma, nan ita kuma Umma ashe babu abinda ya chanza, a wurin Kaka ne kawai take samun kulawa da nutsuwa, gashi Kaka ta dada tsufa ciwon yau daban na gobe daban batada lafiya, aikuwa Umma ta baje ganin Abba bai nan gashi Kaka batada lfy ta dinga gana ma Hoodah azaba. Wata rana tana zaune cikin dakinta tana danne danne a wayarta kawai sai ga Umma kamar an hankado ta, Hoodah ta mike a tsorace tana kallonta, Umma tace "Wai ke ina mijinki da zai zo ya aje ma mutane ke yayi tafiyarsa?" Inda inda ta fara "Zai zo ya daukeni yana wani aiki ne..." dungurinta Umma tayi ta juya ta rufe dakin gam yadda ko wani yazo kwatarta bazai iya shigowa ba, dan so take yau taji uban meye ya hada su da Sultan dan bata yarda da abinda Hoodah ta fada mata ba, so take taji abinda takeso taji wato ya wulakanta ta ya koro ta! Baya baya Hoodah ta fara yi ganin Umma ta nufo ta kamar wata yunwattaccen zaki "Don Allah Umma ki tsaya, karki dakeni! Wallahi abinda na fada maki iyakar gaskiya ta ce, don Allah karki dakeni." Kuka ta fara yi har ta kai bango ta runtse idanunta gam duk a tsorace take, wani irin mari ta dauke ta dashi har guda biyu a jere take ta kara rikicewa ta fashe da kuka har kyarma takeyi duk ta fita hayyacinta, "Wai ke mahaukaciyar ina ce? Dan uwarki nace ki fada man meya hadaku amma kike man karya ko? Ko ce maki akayi ni karamar yarinya ce?" Cikin kuka tace "Gaskiya na fada maki babu abinda ya hadamu, yana wani aiki ne sai ya gama zaizo ya daukeni!" Tace "Toh naji amma meya hanashi zuwa ko sau daya tunda ya ajeki!" Ta fara kyarma "Aiki ne ya masa yawa sheyasa...." shako ta tayi "Karya kike dan uwarki! Nace ki fada man uwar me kikayi masa? Ko iskanci kikayi masa ya koroki?" Tace "Ni ba yar iska bace ba!" Wayarta ta warce cikin sa'a taga ba password nan ta lalubo number Sultan ta fara kiranshi, tun yana rejecting, daga karshe ma sai ya barta tanata ringing. "dan uwarki nasan karya kikayi man yanzu gashi nan yaki dauka! Ki fada man nace me kikayi mashi ya koro ki?" Hoodah tace "Maybe he's busy ki gwada kira kigani ko zai dauka." Tsaki tayi ta sake dialing number din, cikin sa'a kuwa bugu biyu ya dauka Umma tasa ma Hoodah a kunne tana kyarma tace "Sul....tan!" Muryarta har wani daukewa tayi, jin muryarta yayi tun daga saman kanshi har tafin kafarshi, dama yana cikin hotel din daya sauka zaune shi kadai abun duniya duk ya ishe shi, ji yake kamar ya ganta gabanshi ya rungume ta amma ya dake, har zai danna ya kashe kawai yaji ta fara kuka "Sultan don Allah yaushe zakazo? Kazo kafin Umma ta kasheni don Allah ba don ni ba!" Bata ida magana ba kit ya kashe wayar, bata san lokacin da ta ture Umma ba ta bude kofar ta fita a guje, haka Umma ta bita da gudun itama har kofar gida nan Umma ta umarci bayinta da su bi bayanta su kamo mata Hoodah, sunkai tsawon minti ashirin suna zagaye cikin gidanan har daga karshe sukayi nasarar kamata mutum biyu ke rike da ita, suna tsaye bakin gate dinsu suna kokowa da Hoodah kawai taganshi tayi tsaye jikin mota ya juya yana magana da wani yaro alamun kiranta zai sa ayi, wasu hawaye suka gangaro mata kafin kace mey ta fara kukan fitar hankali kamar ance mata gawar Sultan ce aka kawo, yaron ne yace ay gata nan ma tafito a hankali ya juyo suna hada ido yawani sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, wani karfi yazo mata ta bankade su ta ruga a guje tayi hugging dinshi, kuka ta fashe dashi mai ratsa zuciya, take yaji zuciyarshi ta tsinke yayi hugging dinta back, saidai ta gaji dan kanta amma fa ko uffan bai ce mata ba, tausayi ta bashi ganin yadda ta koma kamar wacce ta shekara a kwance tana jinya, a hankali ta janye daga jikinshi tana faman share hawaye, a hankali yasa hannu yana share mata hawaye "Tou kukan ya isa haka, ba gani nazo ba? Menene ya faru waya taba mun ke?" A hankali yake maganar yana jin sonta na kara fizgarshi kamar ma sonta ne zaiyi ajalinshi, hannunta ta daga tana nuna mashi Umma da bayinta dake tsaye hannunta har kyarma yakeyi, Umma ta wani hade rai tace "Dan uwarki ba ciki kikayo ba ya koroki?" Da wani shock take kallon Sultan tana girgiza kai "Banida ciki, Umma haka take bata son ganin farin cikina ka yarda dani," ta fada a rude ganin yadda yake bin Umma da kallo baki bude can ya juyo yace "Ciki? No no I cannot accept this pregnancy! Am sorry I can't." Wani irin heartbreaking step tayi taking back tana kallonshi hawayenta ma sun kafe, "Karka hukuntani akan abunda baka da tabbas a kanshi, I know she's lying, abinda kayi man kadai ya isa na horu, ka yarda dani don't listen to her she's a witch!" Shiru yayi can ya furta "Anything can happen, ko a cikin gidan nawa ne." Ya fada cike da kokonta part of him ya yarda da ita wani part din  kuma  bai ma sani ba, wani kukan kura Umma tayi ta fizgo Hoodah bata tsaya wata wata ba ta fara dukanta, Hoodah tana ihu tana rokonta akan ta kyaleta, shi kuwa Sultan tsaye yayi kamar gunki kamar wanda aka dasa ya kasa motsi, wata irin tsawa Umma ta daka mata "Ni kike kira witch?" Take ta daga kafarta ta kai mata wani irin harbi a kirjinta da cikinta, wani irin gigitaccen ihu ta saki take ta silale a gurin, ta zube kasa idanunta na wani kakkafewa "You're going to loose me forever Sultan, I know you love me amma yau na tabbatar a yau that your love is weak tunda ka kasa cetona." A hankali take fada amma baiyi missing ko word daya ba a hankali idanunta suka dinga rufewa, idanunta kyam a kansa Umma na cigaba da jibgarta bata ma yi wani motsi ba ta barta ta cigaba da dukan nata, take jikinta ya saki, wani irin ihu Sultan ya fasa "Hoodaaaah!" ay baisan lokacin da ya rugo a guje ba yayo kanta ya zube kasa ya dinga jijjigata da karfi hawaye na zubo mashi babu abinda yake furtawa sai "I am sorry." Mikewa yayi yana kallon Umma dake ja baya ya wani damko ta a fusace, yana shake da ita ya ciro wayarshi ya sa aka kira mashi DPO yayi magana dashi ya kashe wayar. Ko cikkakken minti biyar ba'ayi ba sukaji jiniya da kugin yan sanda, yan sandan suka dinga durowa daga cikin motocin suka yo kan Umma yace suyi arresting din Umma da tayi mutuwar tsaye. Juyowa yayi ya kalli ogansu yace "Ku tafi da ita, zanyi magana da manyanku." Sultan a hankali kamar wanda kwai ya fashe mawa a jiki ya tako inda take kwance kamar marar rai ya sureta. Har ya turata mota ya rufe ya juyo kenan zai zagaya ya shiga shima kawai sai ganin Abba yayi kamar daga sama yana huci, "Maza ka kirasu su sakar man mata!" Ya juyo yana kallon Sultan cike da tsana, dan sunkuyawa yayi alamar girmanawa yace "Abba barka da wuni?" Yana fadan haka ya mike da sauri zai shiga motar don shidai tunaninshi bai wuce halin da Hoodah ke ciki ba, "Da ban wuni ba da ka ganni a nan? Sultan kake ko wa? Wallahi tallahi ka gaggauta fito man da matata a sako man ita tun muna shaida juna dakai! Dan ta d'an daki wannan yarinyar shikenan? itama ba kamar yar cikinta ta dauke ta ba? Kasani ko wani rashin kunyar tayi mata ta daketa? Ba uwarta bace? Ba ance nan ka barta wata da watanni ko waiwayarta bakayi ba ko ace maka bansani ba? Ohh sai yanzu ka damu da ita, ka sakar man mata na fada maka kasan ko ni wanene a garinnan zanfa sa a daure man kai! Ko kasheta tayi ina ruwanka? Yarka ce?" Baki sake Sultan ke kallon Abba in shock, so this is the what Hoodah has been telling him all along akan Abba da Umma? Ashe makircinta ya kai haka? What a life? Sai yaji ta kara bashi tausayi ya juya yaganta unconscious, "Amma Abba baka tunanin yanzu the most important thing to us shine rayuwar Hoodah? Zata iya rasa ranta fa kuma duk a sanadiyar your so called wife!" Bai taba tunanin akwai ranar xai wa Abba rashin kunya ba sai gashi ranar tazo. Ko kara kallon inda Abba baiyi ba ya bude mota ya shige, kofar motar Abba ya rike gam yace "Ina fada maka ka sakar man mata kana wani maganar marar lafiya! Yarinyar nan raki ne da ita baka santa bane, abinda ya fiye maka alkhairi shine ka sakar man mata!" Shiru yayi cike da mamaki "Abba kayi hakuri amma nidai xan wuce da ita asibiti, dama ni na kawota toh na dawo daukarta daga asibiti ma idan an sallameta bazan dawo da ita nan ba in ma kayanta ne idan tana bukata zan aiko a karbar mata." Yana gama fadan haka bai kara koda second biyar ba ya cire hannun Abba daga jikin motar ya rufe ya bar unguwar gaba daya, yana kallo ta mirror yadda Abba ke zazzaga masifa har dai kaka ta fito tana faman janshi su koma ciki abun kunya ne aga sarki a haka kofar gida yana masifa, shidai kawai girgiza kai yakeyii. Agadez Hospital ya nufa suna isa nurses sukayi gaggawar tafiya da ita emergency, zaune yayi a reception ya rasa wa zai kira ko yaji sassauci, sai a lokacin yaji hawaye ya kawo idonsa suka sauko mashi, mai ya aikata haka ya cutan da yar mutane? What has gotten into his dull brain? Wani irin haushin kansa ya dinga ji, sai can wajen la'asar kafin Doctor din ya fito yanata masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, ko gane fadan baiyi shidai kawai burinshi bai wuce yaje yaga halin da Hoodah take ciki ba, mikewa yayi tsaye dayaga doctor din baida niyyar yin shiru yace "Yanzu a ina zan ganta?" Don dama ya riga ya biya kudin baki daya "Room 12." Abinda ya fada kenan Sultan ya juya ya fita da sauri, duk taku daya dayake kusantar dakin da Hoodah take wani irin bugu zuciyarsa keyi kamar ta bulo kirjinsa, daidai dakin ya tsaya yana maida numfashi kafin a hankali ya murda handle din ya kutsa kai ciki, kwance ya isketa tana bacci fuskar nan tayi wani fau hannunta drip ne yana shiga cikin veins dinta, ganin yadda take numfashi ba karamin tsorata shi yayi ba kamar she's struggling to breathe duk da kuwa oxygen din da aka saka mata, wani pain yakeji a kirjinsa yanzu fa duk a sanadinsa hakan ya faru da ita ko babu wanda yaja mata in ba shi ba he's responsible for all that has happened to her, har bakin gadon ya taka yana kare ma fuskarta kallo, shidai abun ya masa yawa ga Hoodah ga iyayensa da wane zaiji? Zama yayi kan kujerar dake gefen gadon a hankali har yanzu bai daina kallon fuskarta ba, hannunta ya riko mai drip din very carefully yana dan murzawa. Bata farka ba sai can bayan sallar isha'i, ko bude ido batayi ba ta fara neman ruwa, shaf ya manta ana siyo abubuwa a aje, kamar zai tashi sama ya fita daga dakin yaje shop din cikin asibitin ya siyo ruwa da drinks da sauran abubuwan da za'a bukata ya dawo. Lokacin da yashiga ya sameta ta bude ido tangaram ga Doctor da nurses dake kanta suna examining dinta, yana shigowa ta daga ido ta kalleshi bata sake kallon wurin ba, kallo ne mai cike ma'anoni, kallo ne irin wanda ya maka babban laifi kake masa irinshi, saida suka gama dubata sannan suka fita, a hankali ya taka inda take ya bude ruwan ya mika mata kin karba tayi ta juya mashi baya, soyake yayi mata magana ko da hakuri ne ya bata yasan ya aikata babban laifi a gareta, rufe kwalbar ruwan yayi jiki a sa6ule ya haye gadon yayi hugging dinta, tana jin haka sai ta fashe da kuka baisan yadda akayi ba shima sai jin hawaye yayi suna sauko mashi, kuka sukeyi mai cike ma'anoni daban daban, "Habibty me ma zance miki? I just want to apologize please habibty ki saurareni." A hankali ta ture shi daga jikinta hannunta har wani rawa yakeyi "Don't ever call me that! Sultan din dana sani da bashi bane wannan Sultan din marar tausayi marar imani, ba kai bane mijina Sultan wannan mugu ne wanda baya tausayi na...." ta fada tare da juya fuskarta gefe tana cigaba da zubar hawaye....