Thursday 27 July 2017

AUREN FANSA 31

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

 *_We don't just entertain we touch the heart of readers_*

PML

                 ๐ŸŒน31 ๐ŸŒน


http://MaryamSBello.blogspot.com

Komai tsab tuni ta kammala, ita da gida sun d'auki haske da k'amshi. Ta dafa masa Chinese rice with vegetable soup, sai salad. Bayan ta gama sai ta fad'a wanka ta kammala ta fito, yau ranar farko data bud'e 6angaren English wears, ta fiddo wani shegen tight wando kalar ash gashi marar tsawo da riga dark pink mai k'aramin hannu. Ta dad'e tana shawarar ta saka su, daga k'arshe dai tayi shahada ta sa duk da tana jin kunya amma dole ta yakice ta wuri d'aya. Bayan ta saka kayan sai ta taje kanta da mayuka masu k'amshi tayi parking d'inshi da pink ribbon daga can tsakiya sai jelar ta sauko bisa gdon bayanta. Tabi da turaruka masu dad'i.
Ta gama shiryawa da kusan minti goma idanunta na kan k'ofa har ta gaji da kallo, ta jawo laptop nata da Baba ya siya mata itada Zarah ta soma daddannawa, bata ankara ba sai taji charab an kamo ta. Ta mik'e zumbur cike da tsoro, sai data juyo suka kalli juna yayi murmushi.
"Ashe kinada tsoro haka baby?"
Ta zum6uro baki abinda ke birgesa tace
"A'a ba tsoro naji ba."
Yace
"Tsoro kika ji mana, bayan na gani da ido na."
Tayi dariya tace
"Sannu da zuwa."
Yace
"Yauwa."
K'irr! K'arar door bell ta shiga dodon kunnensu, ya dube ta yace
"Koma ciki Bala direba ne zai shigo da kaya."
Tayi ciki bata k'ara fitowa ba, ta wuce ta had'a masa ruwan wanka, da kanshi ya lek'o yace fito muyi fira. Tayi dariya tace
"Kai dai ka shigo ka watsa ruwa kaji dad'i."
Yace
"Angama baby."
Da taimakonta ta zare masa komai, ya shiga toilet, ta fiddo masa singlet da gajeren wando. Yana fitowa kuma yace
"Zo ki shafa man mai." Da mamaki kuma ya dubi kansa wanda baisan ya furta hakan ba. Ta sunkuyar da kanta k'asa tace
"Uhm bari naje na gyara dinning."
Da sauri ta fice inda shi kuma ya cigaba da kallon k'ofar data bi, ajiyar zuciya ya saki ya shirya tsab ya fito.

Suna tsakar cin abinci wayarsa ta fara ringing, ganin Jidda yasa gabansa ya fad'i, cikin sanyin jiki ya d'auka sannan ya dubi Meenah data tsare shi da idanu. Yace
"He...llo."
"Hello ya Faruk a gaskiya fushi nake da kai."
Yayi yak'e yace
"Menayi?"
Tace
"Har yanzu ko kazo wurina ko? Daman nasan baka sona."
Yace
"Ba haka bane zanzo..."
"To yaushe?"
Ya kalli Meenah har yanzu shi d'in take kallo. Sai ya mik'e sum sum ya shiga kitchen. Zuciyarta ta sosu, ko ba'a fad'a mata ba tasan da mace yake waya. Macen ma wadda zai aura, bata ankara ba hawaye suka zubo mata, jin alamun tafiya yasa tayi saurin goge hawayenta cikin dakewa ta k'ak'alo murmushi tana dubansa a lokacin da yake zama kan kujera. Ya d'an murmusa yana kauda fuska cike da kunya.
Sai da suka gama cin abincin ne ya mik'e yana aduba agogon hannunsa. K'arfe 8:44pm. Kallon Meenah yayi yace
"Zan fita bazan jima ba zan dawo."
Tace
"Yanzu? Ina zakaje?"
Yayi yak'e yace
"Ahh karki damu bawani dad'ewa zanyi ba."
Da sauri ya koma ciki ya sake shiri cikin light brown yadi mai matuk'ar taushi, har hular kansa kalar kayan, yayi kyau sosai. Kiss yayi mata a kumatu yace
"Sai na dawo baby."
Haka tana ji tana gani ya fita, sai k'amshinsa da ya bar mata a hanci, wanda ta tabbatar wurin budurwa zaije. Kuka ya k'wace mata ta yi d'akinta da gudu ta fad'a kan gado. Zuciyarta na tafasa kamar ruwan zafi.


***


Tsaye take a gaban madubi ta ci ado na k'in k'ari kai kace zataje tarbar matar gwamna, sanye take da wani french lace kalar ja da adon silver a jikinshi. Wardrobe nata ta bud'e, ta fiddo wani kwalli da turare da wata laya da k'awarta Luby ta bata.
"Wallahi idan kikayi amfani da kayannan Jidda kin gama da Faruk, sai yadda kikayi dashi, sannan ba abinda zai sa a gaba sai ganin ya mallake ki a matsayin mata, don haka ki tabbatar kinyi amfani dasu a daren da zai zo. Sannan wannan kuma a abinci zaki barbad'a masa ko lemo da zarar yasha yazo hannu!" Wannan shine maganar da Luby ta fad'a mata a lokacin da tazo ta kawo mata kayayyakin.
kwallin ta shafa ta fesa turaren, sai wata laya da akace ta rik'e a hannunta gam kar ta saki har sai ya tafi. Bayan ta kimtsa wayarta ta fara ringing, ganin mai kiran yasa ta saki murmushin mugunta sannan ta d'auka cikin kashe murya tace
"Hello my dear."
Yace
"Gani nan parlon Dada, da mun gama gaisawa zan iso main parlor ki jira ni a can."
Tace
"Angama honey."
Kashe wayar yayi ba tare da ya k'ara magana ba.
Dada ne yake shigowa, bayan ya k'araso ya zauna nan suka gaisa. Dada yace
"Ya gida ya iyali?"
Yace
"Alhamdulillah."
Dada yace
"Tunda nace ka nemi yardar matarka baka k'ara zuwa ba ko?"
Yace
"A'a Dada wallahi aiki ne yasa ni a gaba, nayi magana da ita ay ta yarda ta amince."
Dada yayi murmushi
"To kaga ka sauke nauyi, Allah ya tabbatar da alheri."
Yace
"Amin Dada, yanzu ma wurin Jiddar nazo mu fahimci juna."
Yace
"Madallah, babu matsala."
Daga haka ya mik'e ya fice.

A sadda Jidda ta fito Faruk na zaune kan kujerar zaman mutum biyu yana latsa waya, tun kafin ta k'arasa ya k'ura mata ido har ta iso yana kallonta.
Ta dube shi sosai ta zauna kusa da kujerarsa don ya shak'i k'amshin sosai tace
Sannu da zuwa."
A kasalance ya amsa a take yaji wutar sonta na ruruwa a ransa kamar ana kunna ashana. Ta dube shi sai taga ya tsare ta da idanu tace
"Yaya Faruk ina wuni ya gida?"
Ya kad'a kai tare da lumshe idanu, ji yake kamar ya kamota ya rungume, ita kam sai matsar layar takeyi tare da wani kad'a jiki tana wani fari da ido. Ya sake dubanta sai yaga tayi wani kyau ji yake kamar ba wacce tafita kyau...
Ta katse masa tunani da cewa
"Bari na kawo maka abin motsa baki."
Yace
"A'a da kin barshi ma bana jin yunwa."
Tayi wani fari da ido tace
"Ayi haka? Ay ko ruwa kasha kaida ba bak'o ba?"
Sai wani kashe murya takeyi. Yayi murmushi yace
"To kawo min ruwan dai ya isa, amma kar ki dad'e don ban gaji da kallonki ba."
Tace
"To yanzu zan dawo."
Ta mik'e cike fa yauk'i da yanga ta tafi, shi kuwa sai binta yake da ido har ta shige kitchen. Ya lumshe idanu kafin ya bud'e jira kawai yake yaga ta fito ko zaiji sanyi a ransa....



MSB๐Ÿ’–

Wednesday 26 July 2017

AUREN FANSA 30

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน30๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com

Mairo Gafai Allah ya baki lafiya yasa anyi a sa'a๐Ÿ˜

Daga d'an nesa yakejin kamar ana k'wala masa kira, hakan ya dakatar dashi daga bud'e motarsa da yakeyi. Hango Najeeb yayi yana k'arasowa cikin d'an gudu gudu, tun daga nesa yake hango sa kamar yana cikin damuwa. Sai da ya k'araso dab da shi sannan Najeeb yace
"Wai tafiya zakayi da wuri haka? Wurinka nazo fa."
Faruk yace
"To, kuma gashi har na rufe office zan wuce gida, amma idan maganar batada tsawo mu shiga daga ciki."
Najeeb yace
"No batada wani tsawo sosai, no need ma mu shiga daga ciki muna iya tsayawa  a nan."
Faruk yace
"Ok kafin nan ya gida ya k'anwata da fatan ana kula min da ita sosai?"
Najeeb yace
"Haba mana kai kason yadda nakeson Anisah ay, dole ma na kula da ita. Yawwa wata magana nake ji daga gida cewar zaka k'ara aure, shin gaskiya ne ko ba gaskiya bane ba?"
Faruk yace
"Wannan magana gaskiya ne, haka take."
Najeeb yace
"Amma ka bani mamaki Faruk, ta yaya zaka k'ara aure yanzu? Daga yin aurenku, baka bari nan gaba kad'an idan ma zaka k'ara sai ka k'ara. Haba Faruk..."
Faruk yayi murmushi yace
"Najeeb kenan, gani nayi fa ba haramun bane k'ara aurennan, sannan ba wata bare bace zan aura 'yar gida ce."
Najeeb yace
"Nasani mana, amma baka ganin Jidda bata dace da kai ba?"
Faruk sai ya kama dariya yace
"Ta yaya?"
Najeeb yace
"Haba Faruk, yarinyar nan kasani sarai batajin magana, kullum cikin yawo take, gata ta tara k'awaye a gida, baka ganin yadda su Dada ke fama da ita? Kai baka tunanin ta zame maka matsala a gidanka da kai da iyalinka nan gaba? Kuna zaman lafiya kaje ka jajibo ma kanka masifa har gida...?"
"Wa'iyazubillahi! Haba Najeeb ka daina kira min masifa a gida, insha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi. Kuma da kake batun Jidda bataji zan gyara ta, kai kanka zakayi mamaki."
Najeeb ya kad'a kafad'a alamun oho yace
"Well it's your choice not mine, don't say I didn't warn you to."
Faruk yace
"Yawwa kuma nagode da shawara, zamu iya tafiya?"
Najeeb yace
"Of course, ni zan tafi sai anjima a gaida gida."


***

A gajiye ya shigo gidan, tana zaune kan kujera ta zaman mutum uku, hannunta rik'e da remote tana chanza channel d'in da take muradin kallo.
Tunda ya shigo yake binta da ido, a tsawon rayuwarsa bai ta6a ganin Meenah cikin irin wannan ado haka ba.
Wani dark blue leshi ne a jikinta mai yarfin golding, ga wasu duwatsu dake rauraya daga gaban rigar, d'inkin an mata wanda ake cema da peplum sai skirt da ya kamata, d'aurin d'ankwalin kuwa kamar don ita akayi shi, tana sanye da 'yan kunne da sark'a kalar kayanta, yadda kasan wata matar shugaban k'asa ko wani gwamna saboda yanayin shigarta ya nuna hakan. K'amshin gidan ya had'u ya gauraye dana sanyin ac, hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba.
Bata ankara ba sai ganin mutum tayi tsaye a gabanta, murmushi ta sakar masa mai saurin fizge zuciya a yayinda ya mayar mata ba 6ata lokaci, sannan kuma ta tashi a hankali ta k'araso inda yake tana mai tafiya cike da nutsuwa. Shi dai yana tsaye yana binta da idanu, ta amshi briefcase d'insa tare da kama hannunsa tace
"My soul lafiya ka dawo da wuri haka?"
Ya dube ta cikin kulawa yace
"Wallahi kuwa na gaji ne, sannan yau bawani aiki sosai."
Tace
"Ok muje kayi wanka ko abinci zaka fara ci?"
Ya girgiza kansa alamun a'a yace
"Bari inyi wankan dai zai fi, sai inci abincin daga baya."
Hannunsa take ja yana biye da ita har d'akinsa sannan ta shiga ta had'a masa ruwan wanka kamar kullum, bayan ta fito ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa, sannan ta fice ta bashi wuri ya kimtsa.

Bayan sun gama cin abinci ne suna zaune a parlor suna hutawa Meenah ta soma magana.
"My soul don Allah na tambaye ka?"
Ya gyara zamansa yana fuskantarta yace
"Eh Allah yasa nasani."
Tayi murmushi tace
"Daman... nace ina kake ganin za'a samu 'yar aiki?"
Yace
" 'Yar aiki kuma? Me za'ayi da ita?"
Tace
"Mami daman keso, ni bansan inda ake samu ba shine nace bari na tambaye ka."
Hajir ta fad'o masa a rai, take kuma ya fara murmushi ganin wata dama ta samu da zaiyi amfani da ita kuma bazai bari ta wuce shi ba. Sai yayi saurin cewa.
"Haba indan wannan ne kar ki damu, Mama na da masu aiki, so samowa bazaiyi wahala ba, zan mata magana."
Cike da jin dad'i tace
"Kai nagode sosai my soul."
Ya d'an tsunkuli gefen kumatunta yace
"Anything for my baby."


****

Washe gari a office yasa aka kira masa Hajir, tana zuwa yace ta zauna, bayan ta zauna ya soma magana.
"Kamar yadda nayi miki bayani jiya zamuyi magana, to shine yanzu zan miki bayani. Da farko wani aiki zakiyi min, sannan don Allah ina buka'atar had'in kanki Hajir."
Hajir tayi dariya
"Insha Allah sir."
Yaji dad'i yace
"Da farko ina so ki chanza identity d'inki gaba d'aya."
Cikin rashin fahimta tace
"Bangane ba?"
Yayi ajiyar zuciya yace
"Ma'ana ina so ki tashi daga Hajir, 'yar gayu, mai ilimi, mai kud'i ki koma Atika bak'auya, marar ilimi, marar kud'i sannan kuma 'yar k'auye sannan Atika 'yar aiki, amma kar ki damu aikin naki bazai dad'e ba, sannan zansa a linka miki albashinki fiye da yadda ake baki."
Da mamaki tace
"Naji bayaninka, amma zan iya sanin dalili?"
Yace
"Yawwa, dalili kuwa shine, information nake buk'ata daga wurinki dangane da labarin dana baki jiya, dangane da mutuwar iyaye na. Abinda nake so dake zakije a matsayin 'yar aiki. So aikinki yana buk'atar hak'uri, dauriya, jajircewa, da fatan kin fahimta?"
Tace
"Na fahimta sir, kuma insha Allah baza'a samu matsala ba. Na farko taimako zanyi, duk da ban ta6a cin karo da aiki irin haka ba, amma na maka alk'awarin zaka same ni mai cika alk'awari. Sannan insha Allah zaka same ni mai hak'uri da kuma dauriya."
Yaji dad'i sosai ya cigaba
"Alhamdulillah, da farko zan d'an baki wasu kud'i kije kasuwa ki siyo 'yan atamfofi ki kai ayi miki d'inkin 'yan k'auye, sai ayi ta wanke su har su k'ok'e, daman ba masu tsada bane hakan bazaiyi wahala ba. Na biyu idan kin zama ready sai ki sanar dani sai nasa a kaiki inda zaki fara aikin. Na uku duk wani abu da kikaji ya zamanto kin rubuta shi inda hali ma ki mani vnote, ko kiyi duka biyun. Sannan zan siya miki k'aramar waya marar tsada ki saka sabon sim card yadda bawanda ya sanki da layin don kar a samu matsala. Aikinnan Hajir yana buk'atar lura da sa ido, ko wane motsi nata akanki, duk abinda kikaji ki rubuta ki kuma yi recording. Da munsamu muka had'a duk wani information da zamu buk'ata shikenan, sai na fad'a miki yadda za'ayi. Kar kiyi wani abu da zata gane ke ba 'yar k'auye bace, kar ki kuskura ki nuna kin iya turanci, kuma ki mata biyayya duk abinda ta saki kiyi. Shine kawai abinda nake buk'ata a wurinki."
Ta saki ajiyar zuciya tace
"Tabbas bazan baka kunya ba sir, insha Allah na maka alk'awarin taimaka maka wurin gano abinda kakeson ganowa, yanzu dana tashi daga nan zan wuce kasuwa sai na siyo abubuwan da nake buk'ata, ka bani nan da kwana biyu, zan zo sai ka kaini wurin aikin."
Yayi murmushi mai bayyana hak'ora yace
"Kai naji dad'i sosai wallahi, Allah ya bada sa'a, zan rik'a turo maki da kati lokaci zuwa lokaci, duk sadda kike buk'atar wani abu sai ki kirani. Ki tafi da babbar wayarki saboda recording d'in sai ya zamana kin 6oye ta yadda baza'a gane ta ba. Sai ki rik'a fiddo k'aramar kina amfani da ita. To make it more successful zaki iya rik'ayin wayar k'arya kamar kina kiran iyayenki kuna gaisawa a can k'auye."
Tace
"Babu matsala insha Allah."
Yace
"Yawwa."
Nan ya fiddo cheque ya rubuta mata kud'i masu tsoka sannan yayi mata godiya ta tafi.


MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 29

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน

Dedicated to Anty Zee and AishatFareeda❤️ nagode da k'auna๐Ÿ˜

          ๐ŸŒน29 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com

Bayan ya gama shirinsa yayi breakfast sai ya fara k'ok'arin fita, ba yadda Meenah batayi dashi ba akan ya hak'ura a gama ruwannan yak'iya yace aikin da zaiyi yana da mahimmanci sosai. Haka nan ya d'auki umbrella ya fice cikin ruwannan.
Bayan ya fita kuma ta hau aikin gida kamar kullum, ta kimtsa ko ina ta turara gidan da tuararen wuta ta bi da freshener ta fesa ko ina. Tayi kalacinta bayan ta gama tayi wanka ta shirya cikin wani simple lace kalar sararin samaniya (sky blue) da pink. Tana shirin d'aura d'ankwali wayarta ta fara ringing, ganin Zarah yasa tayi murmushi ta kara a kunne.
"Assalamu Alaikum..."
Zarah tayi murmushi
"Wa'alaikumusalam, ya kike?"
Meenah tace
"Uhm bansani ba bayan kin manta dani ma."
Zarah ta d'anyi dariya tace
"Haba sis, ni na isa ne? Gani nayi bai kamata na takura miki ba nasan kina can kina cin amarci yadda ya kamata, ba kya buk'atar takura..."
"To aku sarkin magana ya isa haka, ya garin ya su Mami?"
Tace
"Suna nan lafiya, daman kiranki nayi naji idan kina gida zan biyo, daga school nake ance admission ya fito shine naje na dubo mana..."
Cike da murna Meenah tace
"Haba don Allah? Munci?"
Zarah tayi dariya tace
"Oho sai nazo dai, amma ina fatan ango baya gida don wallahi idan yana nan zan wuce gida kawai."
"Haba mana Zarah wallahi baya nan kizo ina kewarki da yawa."
Zarah tayi murmushi
"Nima haka sai nazo."
Da haka sukayi sallama.


Minti sha biyar tsakani Zarah ta iso, rungume juna sukayi suna murna, Meenah ba k'aramin dad'in ganin Zarah tayi ba. Can ta shiga kawo mata kayan motsa baki su lemo da cake, su dambun nama da sauransu. Meenah tayi murmushi tace
"La Zarah kinga yadda kika jik'e kuwa? Meyasa kika fito cikin ruwa? Ki shiga d'akina ki cire wad'annan kayan ki saka nawa."
Tace "Tab kayanki sun mani kad'an ay."
Meenah tace
"Inji waye? Akwai wanda sukayi min yawa ay."
Zarah tace
"To."
Tunda Zarah tazo take bin Meenah da kallo, har dai Meenar ta tsargu a lokacin da take tsiyaya mata lemo a cikin glass cup, bayan ta gama ta koma ta zauna tana kallon Zarah tace
"Wai lafiya kike min wannan irin kallon haka?"
Zarah ta zuba mata idanu, kafin kuma ta saki ajiyar zuciya tace
"Meenah gani nayi kin rame sosai, akwai abinda ke damunki ne?"
Meenah tayi murmushin da bai kai zuci ba tace
"Babu komai me kika gani?"
Zarah tace
"Haba Meenah, tsawon shekarun da muka d'auka tare da ke nasanki, nasan idan kina cikin matsala ko akasin haka, kuma a matsayina na k'anwarki bai kamata ki 6oye min abinda ke ranki ba Meenah."
Meenah taja ajiyar zuciya tace
"Hakane, bawai na 6oye miki abinda ke raina bane, kawai abinda zan fad'a ne nasan zai rud'a ki had'e da mamaki marar misaltuwa."
Da mamaki Zarah tace
"Niko zanso inji menene wannan da zai rud'a ni haka zai kuma bani mamaki."
Meenah tace
"Uhm bari kedai, to ki nutsu kar ki rud'e dan Allah Zarah, to ba komai bane ba illa wai Faruk zai k'ara aure..."
Lemon da ta kai bakinta shi yayi sanadiyyar k'warewar da tayi hakan yasa ta dinga tari, da k'yar Meenah ta dinga bata ruwa har tarin ya tsaya tana ta faman yi mata sannu.
Sai da ta nutsu Zarah tace
"Wai wane Faruk d'in tukunna Meenah?"
Meenah ta d'anyi dariya tace
"Akwai wani Faruk da kika sani bayan mijina ne? Shi dai nake nufi Faruk da na aura a matsayin mijina to shine zai k'ara aure."
Salati Zarah ta shiga yi cikin tashin hankali sannan tace
"Faruk dai your soul Meenah? Wai aura fa kika ce? To kuma shine kika zauna kamar baki damu ba?"
Meenah tayi murmushi
"To ya kikeso inyi? Kashe kaina zanyi ne? Abinda Allah ya kaddara waya isa ya hana? Nidai na rungumi kaddara kuma ina fatan wadda zai aura mutuniyar kirki ce, sannan ina fatan bada tashin hankali zata shigo min ba, amma nidai idan mijina na sona banida matsala."
Zarah nata kallonta tana magana cike da mamaki, sai data gama Zarah tace
"Lallai an gaishe ki Meenah, kinyi k'ok'ari sosai, ba kowace mace bace zatayi abinda kikayi ba, ni gaskiya inda nice bazan yarda ba, sai anyi tashin hankali ba kad'an ba, tab kishiya fa lallai!"
Meenah tayi dariya.
"To Allah ya kyauta dai, kedai kiyi ta addu'a Allah ya baki miji na gari shine kawai.
Wai shin ina Nabeel kuna ta shan soyayya ko? Kuma yana zuwa zance ko kuwa?"
Zarah tayi dariya
"Han! Kin cika ni da tambaya wane zan fara amsawa?"
Suka d'ara su duka, Meenah tace
"Duka zaki amsa mana."
Zarah tayi murmushi mai bayyan hak'ora tace
"To Nabeel yana nan lafiya lau, yana ta zuwa wurina and kuma Baba yace ya turo iyayensa."
Cike da murna Meenah tace
"Masha Allah! Allah ya tabbatar da alkhairi Zarah."
Tace
"Amin... yauwa Meenah ina za'a samu mai aiki?"
Meenah tace
"Mai aiki kuma? Me za'ayi da ita?"
Zarah tace
"Mami mana, ta matsa ita 'yar aiki takeso, wai gwara ta samo don idan nayi aure nima babu kowa gidan."
Meenah tace
"To kin ta6a ganin na samo masu aiki ne? Amma zan tambayi Faruk ko yasan inda ake samu."
Zarah tace
"Yauwa nagode, batun result naga sunayenmu sun baki Business admin ni kuma Biology."
Cike da murna Meenah tace
"Alhamdulillah, kin anso admission letter?"
Zarah tace
"No sunce sai next week, so zamuje sai muyi registration."
Nan sukayi ta murna marar misaltuwa.
Kafin Zarah ta tafi sai da ta taya Meenah tayi abincin rana, shinkafa da miya sukayi da salad. Bayan sun kammala Zarah ta fara shirin tafiya. Nan sukayi bankwana akan Meenah zatazo gida ta gaida su Baba, Zarah kuma ta tuna mata batun mai aiki.


***

Tarin takardu ne da laptop a gabansa ya tasa gaba yana kallo, amma a zahiri hankalinsa baya wurin idonsa ne kawai ke kan takardun, tunanin Meenah yasa shi a gaba ya hana shi sak'at har ma ya rasa inda zai sa kansa. B'angare d'aya na zuciyarsa yana tunani akan yadda zai cimma burinsa, d'ayan 6angaren kuwa, Meenah ce tayi masa tsaye a rai duk yadda yaso yakice ta daga ransa abin yaci tura. Sai ma dad'a gaba abin yakeyi.
K'wank'wasa k'ofar akayi, ya bada izini aka shigo, matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru ashirin da biyar (25) a duniya, suna kiranta da young detective, saboda sabuwar shiga ce sannan gata yarinya.
"Sir wai kana nema na ko?"
Yace
"Yes ina nemanki, bismillah."
Tace
"Ok sir."
Bayan ta zauna ne yace
"Wani taimako zakiyi min Hajir, amma kafin nan bari na baki labarin komai tukunna."
Nan ya shiga bata labari tun daga farko har k'arshe sannan yace
"To yanzu kinji inda nakeson focusing, ina so kije kiyi tunani nima zanyi tunanin hanyar da zamu dinga samun information daga gidan, da naso muyi magana sosai but gaskiya na gaji kuma bana d'an jin dad'in jikina, so zan tafi."
Ya duba tima k'arfe 3:47pm. Yace
"La'asar ta kusa, zan je masallaci idan na tashi daga nan, sai na wuce gida, zuwa gobe idan nazo zamuyi magana."
Tace
"Insha Allah."
Yace
"Ya batun case d'innan da akayi assigning d'inki kin gama shi kuwa?"
Tace
"Na gama amma case d'in ya bamu wahala sosai, sai dai cikin ikon Allah munyi succeeding."
Yace
"Haka ake so ay, nima akwai cases masu bani wahala amma da mutum ya sa confidence a ransa da kuma jajircewa akan aikin sai kiga komai ya tafi yadda ake so."
Tace
"Haka ne."
Ya mik'e ya soma tattara komatsansa cikin briefcase yace
"Hajir zaki iya tafiya, sai goben insha Allah."
Tace
"To sir Allah ya kaimu."
Yace
"Amin."
Daga haka ta fice a yayinda ya kammala kimtsa kayansa sannan ya fice daga office d'in....


MSB๐Ÿ’–

Monday 24 July 2017

AUREN FANSA 28

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน


Wannan page d'in nakune members na MARZAH HAUSA NOVELS, nagode da k'aunar da kuke nuna min, Allah ya bar zumunci amin❤️

          ๐ŸŒน28 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com

Da sauri ya juya abin mamaki wai Meenah ce kwance kamar ba rai, a gigice yayi kanta ya shiga jijjiga ta, abin mamaki ko alamar motsi babu a tattare da ita. Tunda yake a rayuwarsa bayan mutuwar iyayensa bai ta6a tsintar kansa cikin matsanancin tashin hankalin irin wannan ba, ya rud'e ya shiga tashin hankali mai wuyar fassara.
Da gudu kuma yayi dinning ya d'auko robar ruwan sanyi ya shiga bud'ewa har wani kyarma yakeyi.
Yayyafa mata ya dinga yi amma ba alamar zata farka, hakan yasa ya juye mata shi gaba d'aya a fuska, aikuwa take ta saki ajiyar zuciya sannan ta bud'e idanunta wanda suka kad'a sukayi ja kamar garwashi, tarr take kallonsa kamar sabuwar halitta, shi d'in ma ita yake kallo babu ko k'yaftawa, a hankali ya sure ta in banda sannu babu abinda ke fita a bakinsa.
D'akinsa ya wuce ya shimfid'ar da ita kan gado sannan ya nemi wuri ya zauna gefen ta har yanzu ita yake kallo.
"Sannu Meenah... ya kike ji yanzu?"
Kauda fuskarta tayi daga kallon da take masa zuwa d'ayan 6angaren sannan kuma hawaye suka shiga kwarara daga idanunta masu zafin gaske.
"Meenah..."
Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa.
Hannunta ya kamo duka biyun yana murzawa, runtse idanunta tayi a take kuma wasu hawayen sukayi nasarar saukowa, tana cikin mawuyacin hali mai wuyar fassara, ita kad'ai tasan me takeji a halin yanzu.
"Tabbas nasan dole kiji ba dad'i, nasan kin fara tunanin bana sonki ko? Sheyasa nace zan k'ara aure ko Meenah? Ina so ki fahimce ni Meenah har yanzu ina sonki kuma ina k'aunarki babu abinda ya chanza, auren da kika ga zanyi yana d'aya daga cikin kaddara ta, ina so a matsayinki na musulma ki d'auki kaddara Meenah, kawo wata mace cikin gidannan bazai chanza son da nake maki ba, nidai fatana ki yarda kuma ki amince don bazan iya k'ara aureba ba tare da kin amince ba."
Fuskarta ya shafa ya cigaba
"Wallahi ko yanzu kika ce kar nayi aurennan na fasa kenan ko da kuwa yanzu za'a d'aura shi, kuma ko wacece zata shigo cikin gidannan zan zamo mijin da zai kare miki martaba da kuma mutunci, har abada bazan wulak'anta ki ba, nidai fatana inji ta bakinki a halin yanzu Meenah..."
Wani gumi ya ziyarce ta, wato dai da gaske kishiya zai mata kenan? Ita kam batada sa'a a rayuwa, ta taso tun tana k'arama tana d'and'ana bak'in ciki a koda yaushe ba kwanciyar hankali, tana tunanin auren da zatayi hutu ne a gareta ashe tayi kuskure. Sai dai kuma dole zatayi hak'uri tunda haka Allah ya kaddara mata ita kam.
Ta yunk'ura ta tashi zaune tana mai share hawaye duk da kuwa wani na bin wani amma dole ta share, kanta kuwa kamar ana sara mata guduma haka takeji. Cikin wata irin muryar data dishe tace
"Haba my soul, meyasa sai ka nemi izini a wurina sannan ka k'ara aure? Ka manta Allah ya halasta maka daga mace d'aya zuwa hud'u? Bana cikin irin matan da idanunsu ke rufewa da kishi har su fad'a halaka, Allah ya halasta maka aure ni wacece da zan hana? Ay ban isa ba ma."
Tayi murmushi mai ciwo ta cigaba.
"Ba k'arin aurenka ya fi d'aga min hankali ba, kasan me ya tada man hankali?"
Yace
"A'ah."
Tayi murmushi
"Wai ace aurenmu da ko sati ba'ayi ba amma ace zakayi aure, sannan kuma ina tsoron ka daina sona ne sheyasa ko kuma ka gaji dani."
Yace
"Haba my baby, kima daina irin wannan tunanin har yanzu ina sonki, kuma insha Allah zan cigaba har in mutu."
Tayi murmushi
"Na yarda da kai my soul, kuma ina alfahari da kai a matsayin mijina, a koda yaushe ina gode ma Allah da ya bani mai sona mai kuma k'aunata, idan aurennan alkhairi ne Allah ya tabbatar, idan ba alkhairi bane ba Allah ya za6a maka mafi alkhairi."
Gabansa yayi mummunan fad'uwa, ya lumshe idanunsa kafin ya bud'e, ya kalle ta cike da sha'awa!
Tunda yake a rayuwarsa bai ta6a cin karo da mace makamanciyar wannan ba. Matsowa yayi dab da ita yace
"A gaskiya kafin a samu mace irinki a wannan zamanin sai an tona Meenah. Nima ina so ki sani ina sonki ina k'aunarki sannan ina alfahari da ke a matsayin matata."
Duk da tana cikin wani hali hakan bai hanata yin murmushi ba, ta yunk'ura zata tashi jiri ya kwashe ta, da sauri Faruk ya taro ta sai kuma ta fad'a jikinsa haka ya rungume ta kamar wata jaririya. Wani shock ya kama ko wanensu, sannan kuma suka dubi juna cikin ido. Sun kai minti kusan d'aya a haka kafin Meenah ta fara kauda tata fuskar tana k'ok'arin tashi daga jikinshi.
Duk ya dabarbarce, kwanciya tayi sakamakon wani bacci da taji yana neman kwasar ta.
Duka duka batafi second goma ba bacci yayi awon gaba da ita.
Jikin Faruk yayi matuk'ar sanyi, sannan kuma take ya fara tsintar kansa cikin wani irin yanayin da bai ta6a tsintar kansa a ciki ba. Wani abu yaji yana bin dukkanin illahirin jikinsa tun daga kansa har zuwa tafin k'afarsa, take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr!
"Hasbunallahu wani'imal wakil." Shine abinda yake fad'i, sannan ya mik'e jiki a sanyaye ya fad'a toilet, a gaban sink ya tsaya tare da bud'e pampo ya shiga wanke fuskarsa, bayan ya gama sai ya tsaya yana kallon kansa kuma ta mirror, ba abinda idanunsa ke gani kamar fuskar Meenah, wani gurin tana murmushi wani gurin kuma dariya, tsintar kansa yayi yana mai murmushin shima. Da sauri kuma ya girgiza kansa ya fice daga toilet d'in yana ta faman maimaita "No."
Kwanciya yayi gefenta tare da rufe idanu yana jin wani bak'on al'amarin da bai ta6a ji ba a tsawon rayuwarsa ba....


Sassanyar iskar asuba mai k'unshe da ni'ima tare da tarin albarka shi ya daki fuskar Meenah kasaancewar tagogin d'akin a bud'e suke. Hakan yasa taja dogon numfashi tare da motsawa, tayi tsawon minti biyu a haka kafin a hankali ta fara k'ok'arin tashi zaune.
A natse ta juya tana maida kallonta kan Faruk da baisan inda duniyar take ba. Tuni abinda ya faru jiya ya fara dawo mata, nan ta yunk'ura cikin k'arfin hali ta mik'e duk da batajin k'arfin jikinta, kasancewar tana fashin sallah sai ta taka a hankali zuwa jikin window. Hadari ta gani sosai, iskar damina  had'e da yayyafi ya daki fuskarta, hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba, tayi ta shak'ar iskan gami da ware hannayenta don ya ratsa ta sosai, take taji ta samu k'arfin jikinta fiye da dah.
Ruwan saman ne ya sauko mai k'arfi, ta mik'a hannayenta duka ta tari ruwan.
K'arar ruwan saman ne ya farkar da Faruk, idanunsa k'yam a kanta, sai yau ya ta6a ganinta ba d'ankwali, gashin kanta ya zubo har bayanta hakan ya faru ne saboda cirewar ribbon d'inta jiya da daddare. Kanta a nannad'e yake kamar na jarirai gashj bak'i wuik!
Yayi zumbur ya mik'e tare da duba time ganin lokacin sallar asuba yasa ya mik'e da sauri ya nufi toilet.
Har ya gama sallarsa a d'aki Meenah batasan yanayi ba. Tana can tsaye tana kallon ruwa na sauka k'asa, abin burgeta yake tun tana k'arama, ita dai rayuwarta tana son ruwan sama yanzu haka ji take kamar ta shiga ciki tayi wanka.
A hakan ya cigaba da kallonta wanda baison yana yi ba.
"Ina kwana."
Ta fad'a gami da zama gefen gado. Yayi murmushi
"An tashi lafiya? Ya k'arfin jiki?"
Tace
"Alhamdulillah."
Har yanzu kallonta yake ganin ba wani yanayi na damuwa a tattare da ita dangane da maganar jiya ba.
"Lokacin dana suma jiya kasan me ya kamata kayi min amma ka kasa sai rud'ewa, ashe dai kana sona haka?"
Take gabansa ya fad'i, ya rasa dalili da ta ambaci yana sonta sai ya tsinci kansa da fad'uwar gaba?
Yana jiyo dariyarta har cikin kansa.
"Yanzu dai ina so ka fad'a min kai da ka ganni cikin wani irin yanayi ka rasa abinyi saboda kana tunanin ko mutuwa nayi? Ashe kana tsoron rasa ni?"
Ta k'arasa maganar tana dariya.
Yayi dum, sannan ya mik'e ya zauna gefenta tare da rik'o hannunta yace.
"Ay dole na tsorata tunda ina ganin zan rasa masoyiyata ta hak'ik'a."
A zahirin gaskiya baisan ya furta wad'annan kalaman ba...
Don haka sai yayi saurin tashi tsaye yana fad'in
"Bari nayi wanka yau zan fita office da wuri."
Da mamaki ta kalleshi
"Yanzu fa k'arfe shidda."
Yace
"Eh wurin bakwai nakeson barin gidannan."
Tace
"Ok bari na had'a maka breakfast kafin ka fito."
Da sauri ya tsaida ta
"A'a kar ki wahalar da kanki tunda bakyajin dad'i."
Tayi dariya
"Haba ba wani wahala bari yanzu zan gama."
Bata jira amsar sa ba ta fice da sauri. Ya dad'e tsaye a wurin kafin yayi saurin shigewa toilet.


MSB๐Ÿ’–

Sunday 23 July 2017

AUREN FANSA 27

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน

Hip!!!hip!!!hipp!!!
Hurray!!!!!!!
Wishing u long life in Islam and prosperity Faridat Allah k'aro shekaru masu albarka ya kuma k'ara basira da hazak'a Amin๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ˜๐Ÿ˜

          ๐ŸŒน27๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com


Gaba d'aya suka dube ta sadda take k'arasowa cikin parlon tare da zama gefen Dada sannan ta d'ora.
"A gaskiya Alhaji banga amfanin aurensa ba duka duka yaushe akayi aurennan da zai bijiro mana da zancen wani auren kuma? Haba me kake so duniya tace mana? Ko sati d'aya fa bakuyi ba da aure haba Faruk ka bani mamaki, me tayi maka? Me ta tsare maka? Yarinya salihar baiwar Allah zaka ce zakayi ma kishiya daga yin aure yanzu? To a gaskiya ban lamunta ba Alhaji, ya sake lala."
Dada bai ce uffan ba yana dai ta kallon Mama tana zuba har sai data gama sannan ya numfasa yace
"Wai da kike ta wad'annan maganganun kece zaki zauna masa dasu ne? Bashi yace yaji ya gani ba? Ba wanda ya masa dole ay, kuma ni bazan iya hanasa yin aure ba, amma abinda nakeso ka sani Faruk shine kasan shi aure ba abin wasa bane, sannan kuma kaji tsoron Allah idan har kayi aurennan tofa dole sai kayi adalci a tsakaninsu, idan kuwa bazakayi adalci ba gaskiya ban yarda ka sake aure ba kuma bada yawu na ba, sannan magana ta k'arshe   sai na tuntu6i ita Jiddar naji ta bakinta tukunna..."
"Ay Alhaji kar ma ka 6ata lokacin ka saboda Jidda ta dad'e da ciwon son Faruk a cikin ranta, don ma ina kwa6ar ta ay da tuni ta sanar maka tana sonsa, sai dai Alhaji dole fa sai mun tashi tsaye kasan halin Jidda bata jin magana ina gudun kar taje tasa d'iyar mutane a gaba kaga babu dad'i hakan."
Dada yace
"Haka ne, Faruk a gaskiya sai ka tsawatar ma Jidda sosai saboda duk wani abin tashin hankali ta guje shi, idan kuwa bazata iya kiyaya ba to a fasa auren. Hajiya kira min Jidda tazo ina nemanta."
"To Alhaji."
Bayan fitar Mama Dada yace
"Ina fatan ka sanar da ita Aminar batun k'ara aurenka? Kuma ta yarda ta amince da hakan?"
Yayi shiru, Dada ya ce
"Alamu sun nuna min cewa baka sanar da ita ba Faruk, to a gaskiya idan kaga ka auri Jidda sai da amincewar Amina, don haka kaje ka nemi shawarar matarka."
To kawai ya iya cewa ya mik'e, a daidai bakin k'ofa sukayi kaci6us dasu Jidda zasu shigo, bai tanka mata ba yasa kai ya fice, bayan sun shigo Dada ya soma magana.
"Jidda Faruk ne ya zo mana da wani zance wai yana son auren ki..."
Bai k'arasa ba ta mik'e cike da murna tace
"Dada? Da gaske kakeyi ko wasa? Da gaske Faruk zai aure ni? Mama da gaske kukeyi don Allah?"
"Ke meye haka wai!"?
Dada ya daka mata tsawa, zama tayi tana ta murna a yayinda Dada ya cigaba
"Kinga Jidda ki nutsu ki saurare ni da kunnen basira, kamar yadda na fad'a miki Faruk yazo man da zancen aurenki, amma inaso kisani kiji tsoron Allah Jidda, kar ki cutar da d'iyar mutane kinsan dai Allah na kallonki, sannan duk wani abin da zakiyi da bai kamata ba na samu labari to ki sani k'arshen zamanki gidan Faruk yazo kenan, don haka ki kama kanki. Hajiya kisa ido akanta sosai, tashi ki tafi."
Da gudu ta fice tana zuwa d'akinta ta fad'a kan gado cike da murna, har ma ta fara imagining wai gata can har sunyi aure da Faruk...



***


Da sallama ya shigo parlon tana zaune kan kujera tana kallo, tana ganinshi ta mik'e tana murmushi sosai ta k'arasa wurinsa tace
"Sannu da dawowa my soul." Ta fad'a tana amsar ledojin da ke hannunsa.
Ya kalle ta tana sanye da army green Indian  sari d'inkin riga da wando, kayan sun matuk'ar amsarta, fuskarta babu wata kwalliya don Meenah ba ma'abociyar yin kwalliya bace bata ma iya ba, hakan yasa kullum fuskanta take fresh gwanin kyau, d'ankwalin kayan kuwa yana d'aure akanta d'aurin ya zauna daram a kanta. Haka kawai kuma sai ta basa tausayi, ganin mummunna labarin da zai fad'a mata, yana tunanin yadda ma zata d'auki maganar.
"My soul inata magana kayi shiru."
Ya susa kai yana k'ak'alo murmushi yace
"Ohh sorry baby, banji ba me kika ce?"
Tace
"Nace muje na saka maka ruwan wanka kayi sai kaci abinci."
Yace
"Ok ok bismillah muje."

Tana gaba yana biye da ita, duk wani motsi nasa akan idonsa haka kazalika k'amshin turarenta duk ya cika masa hanci hakan ya haifar masa da kasala, jikinsa ya mutu.
Suna shiga d'akinsa yau a karo na farko data ta6a shiga, simple d'aki ne mai d'auke da black gado duka furnitures d'in dake d'akin black ne, hartta wasu 'yan kujerun hutawa guda biyu da table tsakiyarsu suma black ne, carpet black, sai paintin d'akin ne kawai yake fari k'al hakan ya haskaka d'akin. K'amshi gami da sanyin ac kuwa sun had'u sun mata sallama.
Kan gado ya zauna a yayinda da ta shige toilet nasa ta had'a masa ruwan wanka ta fito. Tana fitowa tace
"My soul ga ruwan can na had'a maka, idan ka fito ina parlor."
To kawai ya iya cewa shi duk jikinshi a mace yake ya rasa dalili.
Bayan ya fito ya kimtsa cikin kayan baccinsa kalar dark blue, ya fesa turare mai sanyin dad'i ya fito.

Tana zaune a parlor tana jiranshi, yana zuwa ta mik'e tana murmushi tace
"Har ka fito my soul? Ga abinci nan na girka maka."
Yayi yak'e yace
"Thanks my baby."
Tare suka zauna ta shiga zuba masa tuwon shinkafa miyar ku6ewa d'anya da k'ashin rago a ciki sai man shanu, bayan ta zuba masa da tsiyaya masa lemon kwakwar da tayi masa a glass cup, sai taja kujera tana fuskantarsa, a natse ya fara cin abincin sai dai gaba d'aya hankalinsa ba'a kwance yake ba. Ya kalle ta yaga hankalinta a kwance tana kallonsa, ya k'ak'alo murmushi yace
"Baby bangane ba ke bazakici abincin bane?"
Tayi murmushi tace
"Zanci amma ina so sai kaci ka k'oshi tukunna."
Ya kalleta cike da mamaki yace
"Sam ban yarda ba, idan bakici ba nima bazan ci ba."
Da sauri tace
"Haba dai? To zanci."
A tare suka ci abincin bayan sun kammala ta gyara wurin. Tana kitchen tana d'auraye plates ya kirata. Ta fito tana zuwa yace.
"Baby zauna ina son magana da ke."
Tace "to." Ta zauna. Ya had'iye wani miyau mai d'aci tukunna ya fara magana.
"Meenah kinsan dai ina sonki ko?"
Da mamaki tace
"Sosai ma my soul, nasan kana sona amma lafiya?"
Yace
"Kuma kinsan dai ina k'aunar ki ko?"
Tayi murmushi
"Nasani."
Yace
"Yawwa, kinsan kaddara mai kyau da marar kyau ko?"
Tayi dariya mai cike da mamaki tace
"Nasani mana."
Yace
"Kinsan kuma dai kowa da tasa kaddarar Meenah, maganar da zan fad'a maki tana da nauyi, amma ina so badan ni ba don Allah da kuma soyayyar da kike min ki fahimce ni."
Jiki a sanyaye tace
"Don Allah my soul ka fad'a min ko meye, sai kwana kwana kakeyi."
Yayi shiru cikin nazari, can yace
"Hakane zan fad'a maki amma ina so kiyi min alk'awari guda d'aya."
Tace
"Na me?"
Yace
"Bazaki d'aga hankalinki ba sannan bazakiga laifi na ba."
Gabanta yayi mummunan fad'uwa, tace
"Don Allah ka fad'a min my soul ka barni a duhu don Allah."
Tashi yayi tsaye yana mai juya baya don ya kasa ma had'a idanu da ita. Da k'yar ya iya tattaro kalamunsa wuri d'aya, yace
"Auren zan k'ara Meenah..."
A gigice take kallonsa, kanta yayi wani dum! Nuna sa takeyi da hannu tana fad'in
"Anya naji da kyau, sake maimaita mini."
Yace
"Kiyi hak'uri haka d'in dai nace, aure zan k'ara."
"Innalillahi wa inna ilahir raj'iun." Take kuma gumi ya dinga sassarfo mata ta ko ina, kafin kuma taji wani irin kuka ya taho mata cikin tashin hankalin ta fasa ihu sai dai yaji abu ya fad'i k'asa tim!


MSB๐Ÿ’–

Friday 21 July 2017

AUREN FANSA 26

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน26 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com

Bayan an kawo amarya masu ganin gida suka gama gani tare da fatan alkhairi, sai kuma suka soma tafiya, nan kuma aka bar 'yan matan amarya wad'anda zasu kwana saboda gobe walima.
Haka kuwa akayi washe gari aka gudanar da walima, aka k'are lafiya, bayan an gama aka maido amare gidanjensu, nan kuma su Zarah suka taya ta zama har dare haka sukayi jugum babu mai cewa uffan. K'arfe takwas, tara, goma har da rabi shiru babu ango babu alamarshi. Ganin sha d'aya saura yasa Zarah cewa.
Gaskiya nikam na gaji da zaman jiran ango Meenah."
D'aya daga cikin cousins d'in su Meenah mai suna Khadija tace
"Abinda za'ayi ko idan sunzo ki kar6a mana kud'inmu zan dawo gobe in amsa har ma da sauran kazar da kuka rage ta amarci."
Wannan karon Zarah bata tanka ba don takaicin rashin zuwan ango akan lokaci, haka sukayi ta mata bankwana suka bar gidan. Tayi shiru tana tunanin abinda ya hana shi zuwa har wannan lokacin, tayi tagumi. Har kusan sha biyu saura shiru, ta gaji ta yaye lullu6in tayi zaune ta zurfafa cikin tunanin babu ango babu alamarshi.
Gyangyad'i ta fara yi tun tana yi sama sama har ta kusa 6ingirewa k'asa. A tunaninta idan ta farka zata ganshi kan gadonta sai dai wayam ta ganta ita kad'ai.
Ta mik'e ta sauya kayan bacci ta duba agogo k'arfe 1:36am. Ta koma kan gadon ta kwanta cike da fargaba, sai kuma ta mik'e tana tunanin ko lafiyarsa k'alau don abin ya fara bata tsoro.
Wayarta ta d'auko ta kirasa amma abin mamaki wayarsa a kashe! Ta dafe k'irji tare da d'ora kanta bisa pillow tayi lamo. Can bacci 6arawo ya sace ta, a tunaninta zata farka ta ganshi ya dawo amma abin mamaki babu alamarshi. Ta duba agogo 4:50am, a sanyaye ta shiga toilet ta d'auro alwala tayi sallah. Sai da gari ya d'an fara haske ta fito don ta duba ina angonnata kuma taji dalilin da ya hanashi zuwa da daddare.
Bata san kan gidan ba haka tayi ta shiga tana fita amma ba alamun mutum a gidan. Ta cika da tsoro haka ta koma d'akinta tana tunanin ko ba'a gidan ya kwana ba?
Wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin ash material doguwar riga ta d'aura d'ankwalin kayan ta hau gado ta kwanta tare da lumshe idanu tana k'ok'arin tunanin meya faru da angonta haka har ya hana shi zuwa gareta duk da kuwa yana zakwad'in zuwan wannan rana.

K'arfe sha d'aya aka soma bubbuga gidan, ta mik'e ta fito har bakin k'ofa tare bud'ewa.
"Ina kwana?" Ta fad'a gami da kawar da fuskarta gefe.
"Lafiya lau, Bismillah."
Bata tanka ba kawai tabi ta gefenta ta wuce tana k'ok'arin had'iye kishinta.
Parlor suka zauna sannan tace
"Sunana Jidda, ni k'anwar Faruk ce abinci ne aka bada a kawo muku daga gida."
Ta fad'a tana matsar mata da kwandon gabanta. Meenah tayi murmushi
"Allah sarki, mungode Allah saka da alkhairi."
Tayi yak'e tace
"Babu komai, ina yayan ko bai tashi ba?"
Ta hau inda inda.
"Eh... a'a ya tashi ya shiga wanka."
Jidda ta sunkuyar da kanta k'asa tace
"Allah sarki ni zan wuce ki gaishe shi idan ya fito."
Meenah tayi murmushi tace
"Zaiji insha Allah a gaida Mama."
"Zataji." Ta fice.
Bud'e kular ta soma yi, soyayyar doya ce da k'wai da pepper soup sai k'osai da kunu.
Kasa cin abincin tayi don rashin zuwan Faruk gareta ya mata zafi duk da kuwa har yanzu batasan dalilin rashin zuwan nasa ba. Bata buk'atar komai a halin yanzu sai son ganin Faruk da kuma son jin dalilin da ya hana shi zuwa.
Ganin tunanin bazai mata ba yasa ta jawo kular abincin ta soma ci, kasa ci ma tayi sai kawai ta zuba kunun tasha ta koma kan gado.
Wayarta ta d'auko ta k'ara kiransa wannan karon a kunne taji ta amma har ta tsinke ba'a d'auka ba. k'walla suka cika mata ido, lallai al'amarin mai girma ne.

Sai da tayi kwana biyu a na ukkun ne taji alamar shigowar mota, da sauri ta lek'a shi d'inne yana sanye da suit kalar toka da wando kalar tokar shima.
K'in fitowa tayi don tana tsananin fushi da shi. Tana zaune taji alamun bud'e k'ofa, da alama d'akinsa ya shiga. Sai da ya d'auki akalla minti talatin sannan taji alamun fitowa, da sauri ta kwanta gami da rufe idonta kamar mai bacci.  Bud'e k'ofar d'akin yayi yana tsaye yana k'are mata kallo, daurewa yayi ya tako har bakin gadon gami da zama kusa da ita.
"My baby..."
Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa. Kamo hannuwanta yayi yana murza su a hankali cikin salo na k'warewa, bugun k'irjinta ya k'aru.
"Haba my baby shirunki yana iya haifar min da matsala babba idan baki amsa ni ba, kinji my baby please ki tashi kiji abinda zan fad'a miki."
Tsananin son da take masa shi ya hana ta yi masa musu, tashi zaune tayi fuskarta kuwa kamar an mata albishir da gidan wuta.
"Nasan ban kyauta miki ba, amma kiyi hak'uri babban dalili ne yasa kika ga ban zo ba a ranar da aka kawo ki..."
Ta kalle shi idanunta cike da kwalla tace
"Wane dalili ne ya hana ka zuwa? Wane dalili ne ya hanaka zuwa gareni duk da kuwa yadda kake zakwad'in zuwan wannan rana! Wane dalili ne yasa ka mance dani har kak'i d'aukar wayata a lokacin da nake nemanka? Wane dalili ne yasa a daren da aka kawo ni ka mance dani ka maida ni dani da bola duk d'aya suke a wurinka? Wane dalili ne ya hanaka kwana a gidanka ranar dana fara takowa a gidanka? Wane dalili ne...?"
Toshe mata baki yayi da hannunsa yana girgiza mata kai, take hawayen da take rik'ewa suka yi nasarar saukowa, sannan ta bishi da kallo na ina jiran amsa.
"Don Allah ya isa haka my baby, wallahi ba laifina bane, Dada ne bashida lafiya dole tasa muka tafi wurinsa..."
Ta girgiza kanta.
"Dada bashida lafiya meyasa da jidda tazo rannan da safe ta kasa sanar dani hakan, har tambayarka tayi ko kana ciki? Ta yaya mahaifinta bashi da lafiya ta kasa sani?"
Take ya hau inda inda.
"Eh ay ko ita kanta bata sani ba saboda bata gidan, amma banyi tsammani zaki zarge ni da yin k'arya ba Meenah."
Ya k'arasa yana k'ak'alo hawaye. Hankalinta ya tashi tace
"Ko kusa ba haka bane, na yarda da kai my soul, amma ka gane duk abinda ya shafe ka nima ya shafe ni, daka sanar dani ko addu'a dana yi masa, Allah ya bashi lafiya."
Yayi murmushi
"Yawwa my baby ko kefa? To yi murmushi mana."
Ya fad'a cike da shagwa6a, hakan ya bata dariya sosai. Kamo ta yayi yana fad'in.
"Zo muje na siyo maki abin dad'i."
Tayi murmushi suka fice.


***

Da misalin k'arfe 8:35pm yayi sallama, Dada na aiki a laptop nasa ya dakata gami da amsa sallamar sannan yayi murmushi.
"Ahh Faruk kaine tafe? Shigo mana."
Faruk ya shigo bayan ya zauna yace
"Dada an wuni lafiya?"
Yace
"Lafiya lau ya iyalin naka da fatan tana lafiya?"
Yace
"Lafiya lau Dada daman wurinka nazo."
Ya dube shi kafin ya cire gilashin dake idonsa na karatu yace
"To gani lafiya dai?"
Faruk ya sunkuyar da kai tukunna yace.
"Dada daman so nake na nemi izini wurinka zan k'ara aure."
A razane Dada ya dube shi gami da gyara zama yace
"Aure fa kace Faruk? Aurenku da ko sati ba'ayi ba sai kace zaka k'ara aure? Kaima kasan hakan bazai yiwu ba. Tukunna ma wacece zaka aura?"
Ya sukuyar da kai
"Dada daman Jidda ce..."
"Ban lamunta ba! Idan ma mafarki kakeyi to ka farka!"
Mama ta fad'a tana tsaye a bakin k'ofa daga ganinta kasan tana cikin 6acin rai.


MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 25

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน


Dedicated to Miss Hafsy and Aisha Ali Garkuwa❤️


          ๐ŸŒน25 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com

Da gudu ta fad'a jikin Mama tana kuka sosai, Mama dake had'a kayan wankinta a cikin kwando ta dakata tana kallonta cike da mamaki, sannan kuma tace
"Jidda lafiyarki haka zaki shigo kina kuka? Wani abin ne ya faru?"
Ta k'ara fashewa da wani kukan har tana shasheka. Hankalin Mama ya tashi matuk'a har ta fara tunanin ko batada lafiya ne ma.
"Wai bazakiyi magana ba, ni sa'ar ki ce ina miki magana kin min shiru?"
Cikin kuka tace
"Mama ki taimake ni! Mama idan na rasa shi kamar na rasa raina ne, bazan iya rayuwa bashi ba Mama ki taimake ni Mama!"
Taci gaba da kukanta. Da mamaki Mama tace
"Waye kuma idan kika rasa shi zaki rasa ranki? Ke bakida hankali ne? Akan namiji ki zauna kina wannan kukan, ni kin ma bani haushi. Wai waye ana miki magana kin ma mutane shiru?"
"Ya Faruk ne Ma..."
Ture ta Mama tayi daga jikinta tana kallonta galala sannan tace
"Wa kika ce? Wane Faruk d'in?"
Cikin kuka tace
"Na nan gidan, naji ance aure zaiyi, ni na yarda ya had'a mu ya auremu tare da wadda yake so..."
Buge mata baki Mama tayi hakan yayi sanadiyar katsewar maganar tata, ta dafa wurin tana cigaba da kuka.
"Lallai yarinyar nan ashe bakida mutunci? Kawai sai a shiga hak'kin yaro babu dalili? Shi baice yana sonki ba haka kawai sai a takura masa, to wallahi ahir d'inki! Kar na kuma jin magana makamanciyar wannan a nan gidan, tun wuri ki fitar da Faruk daga ranki kinji na gaya miki, ashe bakida wayau bansani ba? Tashi ni ki bani wuri."
Da gudu ta fice tana kuka, tsakanin d'a da mahaifi kuma sai Allah, take tausayin Jidda ya kamata don haka sai tabi bayanta.
Rarrashinta ta shiga yi da nasiha, har ta samu tayi shiru, nan dai tayi ta kwantar mata da hankali cikin hikima da dabara.


***

Ranar Juma'a magabatan Faruk suka gabatar da komai na auren d'annasu. Duk wata dukiya da ake buk'ata ta aure da kuma al'ada sun gabatar tare da sadakinsu. Bayan kammala komai aka saka bikin wata d'aya saboda Baba ya buk'aci hakan, don yace yafi so ta fara karatu a d'akin mijinta.
 Bayan Sati biyu da hakan kuma suka kawo lefe saitin akwati/jaka takwas da kit. Akwatinan sunyi kyau kalar purple.
Yanzu bikin ya rage saura sati biyu kenan.
To daga nan kuma aka cigaba da shirye shiryen biki, tun daga kan su dilka, gyaran gashi Baba ne yasa aka d'auko ta daga maiduguri mai suna Salima. Matar ta k'ware a gyaren jiki da gyaran amarya. Kwanan ta d'aya amma Meenah ta fara murjewa, ko wucewa tayi sai k'amshin jikinta ya bugo mutum.
Kayan d'aki kuwa Baba daga dubai yasa akayi mata order, gado set biyu masu matuk'ar tsada da kyau, sai set d'in kujeru suma biyu, kayan dining da kitchen ma duka a can akayi order komai da komai. Don Baba a shirye yake don nuna ma Meenah gata.
Hartta katin d'aurin aure daga dubai d'in aka bugo su, sheyasa ya fita daban ko kallon shi kayi kasan ya had'u!
Tun ana saura sati d'aya bikin Baba ya tafi Katsina ya d'auko Goggo. Nan itama aka fara hidimar biki da ita.

A 6angaren ango shima shiri sukeyi sosai, don su mutum hud'u ake ma biki, da Faruk da Najeeb da Yusra, sai Anisah, Nabeel da Jidda suka rage kasancewar basu fiddo wad'anda suke so ba. Don haka gidan ya kacame da hidima ba kad'an ba.

Events d'in da Meenah zatayi kamu ne kawai tasa sai yinin biki, sai d'aurin aure sai walima sai kai amarya sai ango zasuyi dinner shikenan.
Tun ana saura sati d'aya aka fara jere a unguwar Aso Villa, manyan gidaje ne jere guda uku amma kowa da katangarsa haka ma kowa da gate d'insa, babban gida ne ba laifi don yana da wadatar fili, gidan dai yaji shuka banda carpet grass dake shimfid'e a k'asa, ginin zamani mai d'auke da parlor biyu, d'akuna uku, kitchen da dinning. Gidan yayi sai dai fatan Allah basu zaman lafiya!

Ranar laraba ta kama ranar da ake ma Meenah k'unshi, nan fa aka zauna daga can garden aka shiga yaryara mata k'unshi. Sai wata kuma daban tana ma 'yan matan amarya da sauransu.
Ranar alhamis ranar da ake kamu k'arfe hud'u za'a fara a gama k'arfe shidda.
Amarya tayi shiri cikin ja da silver bridal gown wanda ya amshe ta ya kuma yi mata kyau! A yayinda da Zarah suke sanye cikin ashobi pink da black.
Bayan an gama shiri aka rufe mata fuska suka tafi wurin kamu.
Nan kuma aka shiga gabatar da kamun yadda ya kamata, tun a wurin kuma Nabeel yake ma Zarah wani irin kallon da har sai da ta tsargu, shikam tunda ya ganta yaji ta masa. Anyi taro lafiya, ansha hotuna. K'arfe shidda daidai aka kammala aka watse.

Bilki anata fama da jama'a, 'yan uwa, mak'ota, abokan arzik'i, 'yan cin arzik'i, da kuma k'awayenta don haka ko tana cikin 6acin rai ma bazaka gane ba. Hidima tasha kanta, gidanta a cike yake taf ba matsaka tsinke. Hartta dai Hajiya Laila da d'iyarta sunzo tun ana saura kwana biyu bikin.
Nabeel dai ya kasa hak'uri ya sanar da Najeeb yana son k'anwar Meenah, aiko yaji dad'in haka. Don haka ya sanar da Faruk, Faruk ya sanar da Meenah ita kuma Meenah ta tuntu6i 'yar uwarta taji ta bakinta. Batayi saurin amincewa ba sai daga baya, take kuwa suka kar6i number juna yanzu har sun fara gaisawa ta waya!

Ranar juma'a cikin garin Abuja dubban mutane suka shaida auren FARUK ADAM DA AMINATU HAMZA, NAJEEB DA ANISAH, YUSRA DA SADIQ.
Daga nan angwaye suka zarce walima a guest house d'in Dada dake can Asokoro.
Washe gari akayi wunin biki, tun safe jikin Meenah ya fara yin sanyi kuma, ko abinci tak'i ci, jinta take kamar wata marar lafiya. Gashi Bilki bata damu ba bare kuma ta tilasta mata taci. Zarah keta lalla6a ta har dai ta samu tasha ruwan tea.
Haka aka cigaba da gudanar da wunin biki cike da kwanciyar hankali.
K'arfe takwas na dare motocin d'aukar amarya suka iso.
Tun a sannan Meenah ta fara kuka, tun tana ganin zata rabu da 'yar uwarta sai kuma hankalinta ya tashi sosai. Take suka rungume juna suna ta kuka mai ban tausayi.
Da k'yar wata daga dangin Faruk ta janyota, bayan an kaita parlon Baba take kuma ta fara sabon kuka, shi kansa Baban idanunsa sunyi ja, su Goggo da Bilkin duk suna zaune a wurin, nan aka shiga mata nasiha mai ratsa jini da jijiyoyi, kuka kawai take, suka sassaka mata albarka da fatan zaman lafiya, sannan aka jawo ta wajen mota ana ta rangad'a mata gud'a. A kan hanyarsu ta zuwa hankalin Meenah yayi matuk'ar tashi, tunda zataje inda bata sani ba, bata ta6a rayuwa a ciki ba, zuwa cikin rukunin sabuwar rayuwa mai cike da garari, dad'i ko akasin haka....



MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 24

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน24 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com


Baba na zaune a parlonshi ya kira Bilki yace ta turo masa Meenah.
Tana d'akin Zarah a bakin gado tayi tagumi, Zarah kuma na jera kayanta cikin wardrobe da aka kawo daga wurin wanki da guga da safe.
Bilki ta shigo d'akin, da sauri Meenah ta d'ago fararen idanunta ta kalle ta, kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da tana cikin damuwa mai tsanani, take Bilki ta 6alla mata harara tace
"Taso muje."
Ta mik'e a sanyaye tabi bayan Bilkin har parlon Baba, jikinta yayi matuk'ar yin sanyi.
Baba na duba newspaper da idanunsa mak'ale cikin farin gilashi a lokacin da suka shigo.
Ya ajiye takardun gefe ya kuma cire gilashin yabi Meenah da kallo a lokacin da take zama kan carpet, sai ya saki murmushi yace
"Aminatu jiya wannan yaron Faruk yake sanar dani cewar yana sonki, kuma yana so in bashi izini don ya turo da magabatansa, k'warai na yaba da hankalin yaron da kuma nutsuwarsa, amma kinsan bazanyi saurin yanke hukunci kai tsaye ba, ina so inji ta bakinki tukunna. Shin Amina kin amince Faruk ya turo da iyayensa ayi magana, ko kuma baki amince ba?"
Farin ciki marar misaltuwa taji ya lullu6e ta har ta gaza 6oye hakan, take kuma ta sadda kanta k'asa fuskarta d'auke da k'ayataccen murmushi. Ta kai dubanta ga Bilki taga yadda ta had'e rai tayi murtuk.
"Amina." Ta d'ago ta kalli Baban tace
"Na'am Baba."
Yace
"Ke nake sauraro, shin kin amince Faruk ya turo magabatansa ko baki amince ba?"
Da k'yar ta bud'e baki saboda matsananciyar kunyar da takeji tace
"Haka ne Baba, kuma na amince."
Yayi murmushin jin dad'i yace.
"Alhamdulillah, idan yazo kice ya turo magabatansa, Allah yayi muku albarka."
Kanta na k'asa tace
"Amin Baba."
Yace
"Tashi ki tafi."
Tashi tayi ta  fita. Tana fita Bilki tace
"Alhaji!"
Ya dube ta yaga tayi kicin kicin da fuska yace
"Lafiya dai Bilkisu?"
Dama kamar jira take tace
"Haba Alhaji don me zaka biye wa yarinya daga tace tana son mutum sai ka d'auke ta ka bashi, sannan baka ganin yarinyar nan k'aramar yarinya ce duka duka nawa take da zakayi mata aure yanzu? Ko university fa bata shiga ba, gaskiya ni ban amince ba sam." Sai ya kalle ta yayi murmushi yace
"A lokuta da dama ku mata kuna bani mamaki, kina k'in auren Meenah ne saboda k'aramar yarinya ce? To ni banga k'ank'anta a tattare da ita ba, shekaru goma sha bakwai gareta idan baki manta ba wata mai zuwa shekararta goma sha takwas, a hakan ne kike ganin yarinya ce?"
Tayi shiru tana ciccin magani. Ya cigaba
"Babu wani abu da iyaye zasuyi alfahari dashi face suga sun aurar da 'ya'yansu, shine kad'ai kwanciyar hankalinsu saboda idan zaki auna karatu baifi aure ba, haka zalika zata iya cigaba da karatunta d'akin mijinta. Saboda haka nake gargad'inki da kiyi gaggawar kawar da wannan gur6ataccen tunaninki ki koma hanya madaidaiciya." Jiki a sanyaye tace
"Kayi hak'uri Alhaji, a had'o shayin ne ko sai anjima?"
Yace
"Bari sai anjima."

A ranar duk wanda ya kalli Meenah yasan tana cikin matanancin farin ciki.
Cike da farin ciki ta lalubo wayarta ta kira Faruk, bugu biyu ya d'auka.
"My baby." Ya fad'a yana murmushi. Tayi murmushin jin dad'i. Tace
"My soul." Sunan ta dake kiransa kenan.
"Albishirinka!"
Yace
"Goro."
"Fari ko ja?"
Yayi dariya
"In banda abinki ya ina ganin farin goro zan d'auki ja? Ay farin zan d'auka."
Tayi murmushi
"Haka ne, to Baba ya baka izini ka turo iyayenka my soul."
Yace
"Wow alhamdulillah! Gaskya nayi farin ciki insha Allah zan sanar da Dada, i love you so much my baby Allah ya nuna mana ranar auren mu lafiya."
Tayi murmushin jin dad'i tace
"Amin my soul love you too, bari naje Mami tana kirana sai anjima."
Yace
"Awwn kamar kar ki tafi, amma zan kiraki anjima, take care."
Sukayi sallama ta kashe wayan, yana cire wayan a kunnensa ya hango Najeeb tsaye a bakin k'ofa yana kallonsa. Ya hau susan kai yace
"Najeeb me kakeyi a nan? Ka k'araso ciki mana."
Najeeb yayi ajiyar zuciya ya k'araso ciki ya zauna gefen Faruk kan gado tare da dafa sa. Yace
"Faruk a gaskiya banga dalilin da zaisa ka yaudari yarinya ba alhalin ba itace tayi maka laifi ba."
Faruk yayi murmushi yana kallon Najeeb yace
"Don na yaudare ta shine me? Wannan shine first step da zan d'auka shine auren d'iyarsu!"
Najeeb yace
"Faruk da zaka ji shawarata da ka k'yale yarinyar nan akwai hanyoyi da dama da zaka d'auki Fansa ba dole sai ta wannan hanyar ba, she's too innocent wallahi dana ganta ta bani tausayi."
Nan take Faruk ya fara huci, bak'in ciki had'e da 6acin rai suka taru suka masa dirar mak'iya! Ya mik'e a lokacin ne kuma idanunsa suka sauya kala daga fari zuwa ja tsabar 6acin rai, shi kanshi Najeeb ya tsorata da ganin yanayinsa. Faruk ya soma magana cikin 6acin rai.
"Najeeb! Kar ka manta alk'awarin da na d'auka a baya, na k'watar mana 'yancinmu, auren Meenah shine abu na farko da zanyi, don gudanar da duk wani bincike na da zanyi. Idan har ban auri d'iyarsu ba ta yaya zan cimma burina na gano musabbabin yadda aka kashe mana iyaye? Dole sai na kusance su, sun yarda dani sun kuma amince dani, ta haka kad'ai zan sa ido sosai akansu. Bayan haka! Sai nasa sun raina kansu, sai sunyi dana sanin abinda suka aikata, ita kanta Meenah lokacin kad'an nake jira dana aure ta zan kuma wulak'anta ta, dole idan nayi haka abin zaiyi wa iyayenta zafi, to wannan kad'an ne daga cikin abubuwan dana tanada!"
Najeeb ya mik'e tsaye da sauri zuwa inda Faruk ke tsaye.
"Dan girman Allah ka sauke k'udurinka na wulak'anta d'iyarsu, bata ji ba bata gani ba, haba ya laifin iyayenta zai shafe ta?"
"Ya shafe ta! Kai harta karensu ko magensu laifin ya shafe su, na tsane su, na tsane su! Na tsane su! Wallahi duk sadda na kalli Meenah ko wani nata sai na ji kamar yanzu nake kallon gawar iyayena kwance cikin jini."
Ya runtse idanunsa gam gami da dunk'ule hannu, take jijjiyoyin kansa suka mik'e tar!
"Ka barni na cigaba da abinda na sa gaba, abinda kawai nake buk'ata daga gareka shine fatan alkhairi, amma idan ba wannan ba to bana buk'atar shawararka." Ya fad'a cike da 6acin rai
"Haba Faruk! Meyayi zafi haka? Kayi hak'uri don Allah ka kwantar da hankalinka, mubi komai a sannu, insha Allah zaka cimma burinka."
Take yayi murmushi. Rungume Najeeb yayi yana fad'in.
"Yawwa ko kaifa, haka ya kamata ka fad'a."
Najeeb ya k'ak'alo murmushi kurum.


*

Da daddare bayan Dada yaci abinci sai ya aika a kira masa Faruk, bayan ya shigo parlon Dada yana kallon tashar BBC, rage volume yayi yana kallon Faruk sadda yake zama kan carpet, bayan ya gaishe shi kamar kullum Dada ya soma magana.
"Faruk dalilin da yasa na kiraka shine, naji labarin daga wurin Hajiya cewar ka samu matar da kake so haka ne?"
Yace
"Haka ne Dada."
Dada yace
"To alhamdulillahi, daman abinda nake jira kenan Allah yasa albarka 'yar gidan waye?"
Faruk yace
"Sunan mahaifinta Alhaji Hamza, 'yan garin Katsina ne amma nan garin yake aiki baban nata."
Dada yace
"To yayi kyau, da fatan kayi k'wak'waran bincike kafin ka fara soyayya da ita?"
Yace
"Eh Dada, mahaifinta ma'aikacin banki ne, shine manager na First bank yanzu haka, kuma mutumin kirki ne, to yama ce na fad'a maka na tura magabatana a yi magana."
Dada yace
"To alhamdulillah, indai wannan ne babu matsala kar ka damu zamu je insha Allah, ni na d'auki nauyin komai kai da k'anwarka, zan shirya nida Alhaji Musa da Alhaji Sufyan (k'aninsa da yayansa) sai muje insha Allah. Jeka kira min Nabeel da Najeeb."
Yace
"To Dada."
Ya mik'e ya fita, ba'a juma ba suka shigo tare gaba d'aya, bayan sun zauna Dada ya fara magana.
"Kamar yadda nayi muku alk'awarin gina muku gidaje, to an kammala, ga ma makullen nan, kai Nabeel bazan baka ba sai ka samo wacce zaka aura, amma da Faruk da Najeeb su tunda suna da wad'anda suke so, sheyasa zan damk'a masu takardun gidajen da kuma mukallen. Sai kuma anyi maku order d'in motoci guda uku, zasu iso nan da sati d'aya insha Allah. Sai abu na k'arshe maganar lefenku Hajara (k'anwarsa) na damk'a mata ragamar yin lefe na kowanenku, abinda zakuyi list sai ku rubuta duk abinda kuke buk'ata, Allah yasa alkhairi yasa ayi damu."
Suka amsa da "Amin." Sannan kuma suka shiga jero masa godiya marar adadi tare da fatan alkhairi.
Sai yanzu Faruk ke tunanin anya zai iya cin amanar Meenah kuwa? Ko don albarkacin Dada wannan kaya da ya masa haka? Sai dai ya k'udiri a ransa ya zama dole ya d'auki Fansa kota wani hali ne! Jikinsa yayi matuk'ar sanyi a yayinda dayake fita daga  parlon.



MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 23

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน23 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com


Baba yayi murmushi yana dubansa yace.
"Faruk ka saki jikinka dani mana, ka d'auke ni a matsayin mahaifinka, ka bani amsar tambayar da nayi maka."
Ya daure yace
"Da...dama Baba, dama... dama... ina so mu lokaci ne, sannan na gabatar maka da kaina a cikin manaiman auren Meenah, duk da dai tace min batada wanda ta tsada, to amma... amma mun daidaita kanmu."
Baba yayi murmushi gami da lumshe idanu na 'yan mintina, sannan ya bud'e su a hankali kan Faruk.
"Haka ne, Meenah batada wanda ta tsaida, hasali ma kai ne mutum na farko da ta ta6a yin soyayya da shi, sai dai wani hanzari ba gudu ba, kafin na amince maka da auren Meenah, ina so kayi min alk'awarin rik'e ta bisa amana da gaskiya, kar ka ci amanarta kar ka yaudare ta, shine kawai abinda nake buk'ata daga gare ka. Duk da nasan dai mahaifinka mutumin kirki ne kuma ina da tabbacin tarbiyarsa gareku, kuma ina masa addu'a Allah ya jik'ansu da gafara."
Yace
"Amin Baba, indai wannan ne kar kayi haufi a kaina insha Allah babu matsala."
Baba yayi murmushin jin dad'i yace
"Alhamdulillah, amma kuma ina so ka bari in tuntu6i yarinyar tukunna inji ta bakinta, nafiso na tabbatar sai a sanar da kai don ka turo magabatan naka." Faruk yayi murmushi.
Yace
"To Baba babu damuwa insha Allah."
Baba yayi murmushi gami da mik'ewa tsaye.
Yace
"Kana iya tafiya Allah yayi muku albarka. Ya amsa da "Amin."
Baba ya yi gaba,  Faruk yabi bayansa yana jinjina al'amarin.


***


Abu k'arami na neman zama babba, tun tana ganin abin kamar wasa ta fara ganinshi babba. Cikin k'ank'anin lokaci Jidda ta fahimci Faruk soyayya yake, kuma wacce yake so d'in ta kame masa zuciya farat d'aya, duk wani observation nata akan Faruk ta gama gane komai, tausayin kanta ya kama ta. Anisah ce ta shigo d'akin tana tsaye a bakin k'ofa ta k'ura ma Jidda idanu, hannunta d'aya d'auke da cup d'in tea d'ayan kuma yana rik'e da wayarta k'irar Samsung galaxy S6, a hankali ta k'araso ciki tana murmushi. Zama tayi kan gadon da Jiddar ke zaune a kai ta dafa ta.
"Yaya Jidda..."
Firgit! Ta dawo daga duniyar tunani tana kallon Anisah, sai kawai ta k'ak'alo murmushin dole. Anisah tayi murmushi.
Meyake damunki?"
Tayi tsai kamar mai tunani kafin tace
"Babu komai."
Anisah ta girgiza kanta.
"Sam ban yarda ba yaya Jidda, na dad'e da ganin chanzawarki, gaba d'aya kin bi kin sussuce kin zama wata iri? Har Mama ta soma tambayarmu abinda akayi miki,a gaskiya yaya Jidda koma meyake damunki ki fito fili ki fad'a mana, k'ila da akwai taimakon da zamuyi miki..."
Har yanzu bata d'ago ba kanta na k'asa dai tana kallon wayarta.  Yusra ce ta lek'o tace
"Anisah ya Najeeb na kira, kuma yace kiyi sauri kiran nada mahimmanci."
Sai a sannan Jidda ta d'ago tana dariya tace.
"Kice dai za'a je a soye, wai yanzu Anisah har ta girma ta iya soyayya ko?"
Anisah ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi kafin kuma ta fice da gudu ganin zasu sakata gaba da zolaya.

Yana zaune a garden bisa kujera yana sanye da jar riga da ash wando (jeans). Kayan sun haska fatarsa da take kalar fatarsa chocolate mai haske, ta k'araso tana murmushi, tun daga nesa yake kallonta har ta iso inda yake. Yayi nisa a kallonta har bai san lokacin data zauna ba, sai data kira sunansa yayi firgit ya dawo duniyar tunani.
"Ya Najeeb."
Yayi sassanyar murmushi yace.
"Anisah kina lafiya?"
Tace
"Lafiya lau, ya naganka nan kai kad'ai?"
Yace
"Ke nake jira ki taya ni fira, ko baza'a ta ya ni ba?"
Tace
"Uhm, daman Yusra tace kana nema na, sheyasa na fito."
Yayi murmushi yace
"Hakane, ni nace ta kira ki, daman inji batun karatunku ina kukayi applying?"
Tace
"Nayi applying first choice d'ina a Base nida Yusra, sai second choice mukasa Turkish Nile. Sai last mukasa BUK."
Yace
"Ok yayi Allah ya taimaka."
Tace
"Amin."
Yace
"To ya batun maganarmu ina aka tsaya? Har yanzu fa baki bani amsa na ba, kullum dana miki maganar baki bani gamsashiyar amsa, amma yau ba inda zaki sai kin fad'a min."
Cike da kunya tace
"Wace magana ya Najeeb?"
Yace
"Kin fini sani."
Ta sunkuyar da kanta tana kallon k'asa, yace
"Ke nake saurare fa."
Tace
"Ya Najeeb, wai yanzu kake nufi za'ayi auren?"
Yayi dariya
"Eh mana idan har kin amince me ake jira? Bakiji me Baba yace ba? Yace mu dukkanmu zai had'a ya aura damu, yace mazan su fad'i matan da suke so, matan kuma su gabatar masa da wanda suke so, yace so yake yayi gaba d'aya ya huta. Kinga ni da ke sai ayi 'yar gida tuwo na maina. Ko ba haka ba?"
Tayi shiru bugun zuciyarta ya k'aru, tabbas tana son Najeeb kuma shima d'in yana sonta sosai. Tace
"To ya Najeeb Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Yaji dad'in kalamantanta sosai yace
"To Amin ya Rabbi, daman haka nake so naji daga bakinki."
Tayi murmushi.
Sai da suka kammala firar tasu ne kafin kuma su tashi su shige ciki.


MSB๐Ÿ’–

Wednesday 12 July 2017

AUREN FANSA 22

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน

Dedicated to Mrs Fawwaz, Sadnaf, Momyn Sultan, my sakwara, Maman Khady, Jannatuwa, Faridat Musa, Rufaida Yusuf. One luv guys❤️๐Ÿ˜

          ๐ŸŒน22 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com

Bilki ta soma magana cikin fushi.
"Kin bani mamaki Meenah, yanzu har yaushe idonki ya bud'e da kike neman k'wace ma 'yar uwarki saurayi? Ke ko kunya bakiji ace 'yar uwarki tana son wani kema kina sonsa? Fatima fa k'anwarki ce Amina, ay na d'auka ke mai d'auka ce ki sadaukar mata da wani idan ta kama, amma wai ke! Kece mai k'wacewa Meenah."!
Ta share hawayenta cikin tsantsan mamakin Mamin tasu, muryarta na rawa ta soma magana.
"Mami Faruk bai ta6a cewa yana son Zarah ba, ni yake so tun asali, ko ita Fatiman ba sonsa take ba, ni bansan ina kika ji cewar saurayin Fatima ne ba, idan ma kina tunanin cewar saurayin Fatima ne to ki daina tun wuri." Sai kuma ta juya mata baya gami da had'e hannayenta wuri d'aya tace
"A baya kinsha k'wace min kyauta a makaranta, amma gaskiya yanzu bazan yarda a k'wace min Faruk ba, hak'uri zakiyi ki sa mana albarka!"
Sai kawai Bilki tasa salati, yau tana fad'a Meenah na fad'a.
"Lallai wuyanki yayi k'wari ya isa yanka, akan nace kin k'wace wa 'yar uwarki saurayi kike neman ki fad'a min magana Meenah."
Ta fad'a tana nuna kanta.
"Bafa saurayi na bane Mami."
Duk suka d'aga ido tana tsaye bakin k'ofa idanunta sun kad'a daga fari zuwa ja! A hankali ta k'araso cikin d'akin tana share hawaye tace
"Akan me zaki mare ta akan maganar da bakida tabbas a kanta?  Mami! Ki sani Meenah 'yar uwata ce ta jini, ta yaya kike tunanin zata k'wace min saurayi? To bari kiji abinda baki sani ba, Faruk saurayin Meenah ne bani ba, ko don kinga ina zuwa muna fira dashi kikayi tunanin saurayina ne?" Tayi murmushi tace
"To ba haka bane, ni kawai mun saba ne sheyasa kikaga ina fita amma lokuta da dama ay tare da Meenah muke zuwa, duk randa kika ga naje ni kad'ai to Meenah ta tura ni akan in je kafin tazo." Ta kalli Meenah dake hawaye wani na bin wani, tasa hannu ta share mata tace
"Daina kuka 'yar uwata, kiyi hak'uri da abinda Mami tayi miki, sannan kisa a ranki Faruk naki ne ke kad'ai kinji?"
Suka rungume juna suna kuka.
Haushi ya kashe Bilku kafin kuma sum sum ta fice daga d'akin cike da kunya!
A wannan daren Bilki batayi bacci ba, yadda taga rana haka taga dare.

Washe gari Meenah taga fushin Bilki fiye da yadda ta saba gani, da Zarah take sabgoginta, itama sai ta kama kanta a d'aki tak'i fitowa tana karance-karancenta. Sai dai zuciyarta cike take da tsoron Mamin, data tuna marin da tasha jiya sai gabanta ya fad'i.


*

K'arfe goma na safe Faruk yazo, Bilki na zaune parlor tana chanza channel, tun daga jin sallamarsa tabi ta d'aure fuska yadda bata ta6a yi masa ba. Yana zuwa ya zube k'asa yana gaishe ta, sai kawai ta kafa masa ido bata amsa ba, k'arshe ma sai ta mik'e ta haye bene zuwa d'akinta ba tare da tace komai ba. Meenah na daga bak'in k'ofar kitchen tana ganin komai, ita kunya ma ta kamata ta kuma kasa k'arasowa ciki. Sai da ta d'auki akalla minti biyu sannan tayi ta maza ta shigo parlon kanta a k'asa. Dukkansu sunyi shiru aka rasa mai fara yin magana a cikinsu.
Da k'yar Faruk ya daure yayi murmushi cikin basarwa yace
"Munyi ma Mami laifi ko?"
Ta d'an d'ago suka had'a ido, ta lumshe idanu tace.
"Tun jiya take haka, mun rasa gane mata."
Yayi shiru cikin tunani, can kuma yace
"K'ila bata amince dani ba..."
Tayi saurin cewa
"Bakomai zata huce ne."

Baba ne ya ke saukowa daga mattakalar bene Bilkin na biye da shi tana rik'e da briefcase d'insa, ya hango shi a parlor zaune, da sauri ya mik'e cikin girmamawa yabi bayansa don yaga kamar parlonsa ya nufa daga can 6angarensa.
Baba nakan kujera Faruk na gefensa daga k'asa. Bayan sun gaisa kamar kullum cikin mutunci da girmama juna, can Baba yace
"Umar Faruk."
Ya d'ago da fararen idanunsa ya dube shi yace
"Na'am Baba."
"Meke tsakaninka da Amina?"
Faruk ya rud'e ya shiga inda inda saboda yadda yaga Baban ya masa kwarjini, take kuma ya sadda kansa k'asa.


MSB๐Ÿ’—

Monday 10 July 2017

AUREN FANSA 21

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน21 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com


Bayan kwana biyu da safe sai ga Baba ya diro garin wai da niyyar d'aukar su Meenah, hanakalin Meenah ya tashi don tasan da k'yar idan Mami zata barta tayi soyayya ba, tasan dai Baba baida matsala, amma Mami take ji. Aikuwa tana sanar da Faruk cewar gobe zasu koma Abuja yace shima zai tattara ya koma daman ya gama abinda ya kawo shi, sai ya koma zai cigaba da kawo mata ziyara.
Washe gari kuwa suka tattaro suka dawo gida.
Duk da hankalinta a tashe yake hakan baisa taji ko d'ar a zuciyarta game da son da takeyi wa Faruk Adam ba. A ganinta shi d'in yasan menene so, yasan darajar abinda yakeson, ya kuma iya tafiyar da shi ta hanyoyi daban daban, ya iya tarairaiyar mace da bata kulawa yadda ya kamata. Sheyasa son da take masa shi yake k'ara bata k'warin gwiwar fuskantar Mami.
Suna dawowa kuwa kusan kullum sai yazo, har dai ya zama d'an gida, yadda taga Baba ya amshi Faruk hannu bibbiyu ya sanya dole taja bakinta tayi tsit, kuma kullum yazo Zarah ke raka Meenah fira, hakan yasa ita kanta Mamin ta rasa gane wurin wa yake zuwa, amma tana fatan wurin Zarah yake zuwa, don a yadda take gani mutum ne mai kud'i sosai.


*

K'arfe takwas na dare kamar kullum Faruk ya isa gidansu Meenah, kasancewar ya zama d'an gida tsakanin Baba da Mami.
Bayan sun gaisa da Baba, a lokacin Baba yana da niyyar fita, haka ma Mami tana sama tana fama da lissafin kud'in kasuwancinta.
Yana nan zaune yana jiran Meenah. Aikuwa sai gata ta fito tayi kyau kamar kullum cikin material mai taushi silver da ratsin bak'i a jikinshi, d'inkin doguwar riga, d'inkin bai kama jikinta ba. Tun daga nesa suke sakarma da junansu murmushi mai sanyi. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa, centre table ne mai bak'in glass a tsakiya wanda aka d'aura kayan marmari cikin tray kala kala a cikinsa, irinsu Apple, grapes, banana, orange, pear da sauransu. Zamewa yayi ya zauna k'asa gami da rausayar da kai yace.
"Barka da hutu!".
Dariya ya bata sosai saboda yadda yayi maganar, tace
"Alhamdulillah, muna ta sha kam."
Yayi shiru zuwa wani lokaci sannan yace.
"Zuwa yaushe kike ganin za'a aurar da ke?"
Ita dariya ma ya bata tace
"Aure ay lokaci ne... sai lokaci yayi sannan."
Ya langa6ar da kai yace
"Haka ne, amma ni ko yanzu aka bani ke zan kar6a hannu bibbiyu, zan nuna maki k'auna ta ban mamaki, sai dai bansani ba ko ke zaki so ni kamar yadda nake son ki... sannan ina so idan Allah ya kaimu zan sanar da iyayenki cewar aurenki zanyi..."
Ta lumshe idanu cikin wata sabuwar k'auna dake k'ara mamayarta, ta kuma k'ara lallu6e mata zuciyarta, tace
"Kar kayi tantama a kaina ya Faruk, soyayyarmu had'in Allah ce, i respect you  and your values.. Faruk d'in da nake so bana ganin kowa sai shi, bana jin k'aunar kowa sai shi... haka ma banida buri a yanzu sama da mallakarka a matsayin mijin aurena na har abada..."
Sai bayan ta furta hakan kuma kunya ta kamata had'e da mamaki, yadda ta zauna tayi ta zuba kamar pampo, amma daga baya sai take ganin kamar su6utar baki tayi. Sai tayi saurin cewa
"Nidai fatana ka rik'e soyayya ta, kada kaci amanata, ka yarda dani, idan kayi min wannan to ni kuma nayi maka alk'awarin baka dukkan kulawa."
Sai ya rasa abin cewa kuma, murmushi tayi ta sauko k'asa ta shiga yanka masa kayan marmarin yana sha.


***

Bilki ta soma tsarguwa da yawan zuwan Faruk cikin gidansu, da yawan ke6ewa da sukeyi shida Meenah akan Zarah suna fira. Ga wata sabuwar al'ada da Meenah ta 6ullo da ita na yawan kwalliya wadda ta gama lura don Faruk take yinta. Ta gigice ta shiga damuwa sosai, neman k'arin bayani takeyi  tasan Zarah bazata ta6a fad'a mata ba saboda an ta6o 'yar uwarta haka bata ganin aibunta, su koda wani abin ne ba'ajin ta cikinsu kashewa sukeyi su rufe babu mai ji. Ko fad'a sukayi baya wuce yini d'aya idan kuwa sun dad'e to kwana d'aya ne sun shirya sun kuma manta komai. Don haka taga babu mafita illa ta tunkari Meenah tayi mata bayanin abinda take zargi.


K'arfe tara na dare ta raka Faruk ya tafi, tana dawowa ta taradda Mami tsaye gefen gadonta ta hard'e hanyayyenta wuri d'aya tana huci.
"Mami....?"
Ta dube ta sosai daga sama har k'asa tace
"Amina....!"
Bata amsa ba illa ta dube ta a yadda take kiranta cikin wata irin murya. Sai kawai ta jeho mata tambaya
"Meke tsakaninki da Faruk?"
Ta sunkuyar da kanta k'asa, batayi magana ba, sai da Bilkin ta daka mata uwar tsawa mai gigita k'wala.
"Bada ke nake magana ba?!"
Cikin sark'ewar murya tace
"Da...ma yace yana...so...na tun muna Katsina, kuma daman gobe ne Faruk d'in yake niyyar sanar daku muna son junanmu... mun yanke shawarar yin au..."
Ji kake tassa!!! Mami ta d'auke ta da wani irin wawan marin da har sai data ga giftawar wuta, ta nemi ji da ganinta ta rasa!



MSB๐Ÿ’–

Sunday 9 July 2017

AUREN FANSA 20

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน

Dedicated to each and every reader, you always support me, and i am grateful for that! Thanks alot!❤️

          ๐ŸŒน20 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com

Awa biyu tsakani ya diro cikin garin katsina, yana isa airport ya ciro wayarsa ya buga ma Meenah waya ya sanar da ita isowar tasa. Zarah bata gama shan mamaki ba sai da Meenah ta shiga kitchen don girka masa lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Coconut rice da miyar kaji, gefe kuma Russian salad ne, sai drinks kala kala. Banda su snacks da aka tanada. Goggo da k'amshi ya cika mata hanci ta fito daga d'aki ta lek'o tana fad'in.
"Kai lafiya me kuke dafawa?"
Zarah tayi dariya tace
"Ay Goggo surukinki ne zaizo, shine fa su Meenah ake ta shiri haka."
Meenah ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Goggo tayi dariya tace
"Ahh lallai kice munada babban bak'o, ay gara dai yayi yazo ko zamu huta hakan nan."
Bata gama komai ba sai da k'arfe bakwai harda rabi. Kasacewar yace mata da anyi sallar isha'i zaizo.

Tana gama wannan aikin ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin wani lace ruwan zuma (coffee brown) da light pink a jikinshi, d'inkin riga da skirt. Da taimakon Zarah ta d'aure d'ankwalin kayan irin na zamin da ake kira mai steps. Ga d'ankunne an sa kalar kayan. Tana gama fesa turare wayarta ta hau ruri da alama Faruk ya iso. A karo na farko taji ta gigice, kasancewar a yau zata ta6a fuskantar wani d'a namiji a rayuwarta da idanun soyayya. Bayan ta d'auka ya sanar da ita isowar tasa cewar yana bakin k'ofa. Ba yadda batayi da Zarah ba akan ta shigo dashi tak'i, harda zolayarta wai ay ba saurayinta bane ita. Hakan yasa ta d'auki waya ta tura masa da message akan yasa a shigo da shi bakin k'ofa (main entrance).

Tana bud'e mishi k'ofa suka bi juna da kallo mai kwantar da zuciya, kafin kuma dukkansu su saki murmushi mai d'auke da wani 6oyayyen sirri. Mamaki takeyi akan yadda yafi kyau a fili akan a hoto...
Ta kauce ta bashi hanya ya shigo, yanan sanye da shadda marar nauyi kalar sky blue sun kama jikinshi, idonshi mak'ale cikin farin glass wanda ya k'ara fito da cikar kamalarshi na cikakken namiji, wanda boko ya zauna masa sannan kud'i ma suka zauna  masa had'e da hutu, ga kuma uwa uba kyau, ba abinda ke tashi a wurin kamar k'amshin turarensa mai sanyaya zuciya.
Meenah fa tayi nisa a kallonsa yayi murmushi ya soma karkad'a mata key d'in motarsa, taji kunya sosai ta wuce ciki kanta k'asa, yabi bayanta. Suka zauna kan kujeru parlon Goggo, da k'yar ta ce
"Ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yayi k'awataccen murmushin dake fizge zuciya yace
"Alhamdulillah, ya gida ya hutu?"
Tayi murmushi still bata d'ago kanta ba tace
"Komai alhmdulillah, yasu Anisah?"
Yace
"Suna can lafiya lau, ina Goggo da Zarah?"
Kafin tayi magana Zarah ta fito da k'aton tray mai d'auke da lemo kala kala da cups d'in glass guda biyu. Sai data dire bisa center table d'in dake parlor sannan ta zauna suka gaisa a mutunce, yace
"Ga Zarah nan kenan? Itace sweet sister d'inki. Sannu Zarah ya kike? I've heard so much about you, gaskiya sister nan taki tana ji take."
Zarah tayi dariya
"Haka ne, nima ina ji da ita ay."
Tana gama fad'an haka ta mik'e tsaye ta fice. Ba'a juma ba kuma ta dawo d'auke da wani tray d'in mai d'auke da kuloli guda biyu, plate biyu sai kuma bowl na snacks da salad. Bayan ta dire sum sum ta fice saboda yadda taga sun kasa 6oye soyayyar da ke zuciyoyinsu a gabanta.

Ta lek'o don zuwa kitchen had'o tea, daman ita Zarah al'adarta ce duk dare sai tasha ruwan lipton (green tea) kafin ta kwanta, nan ta hango su suna cin abinci a plate d'aya, sai kuma sukayi mata kyau, kuma sun mugun dacewa da juna, abinda Faruk zai nuna ma Meenah shine haske fata don shi fari ne nesa ba kusa ba, Meenah kuwa bak'a ce (chocolate color). Suna cin abincin suna kallon juna, fatar bakinsu kuwa kad'an take motsi daga lokaci zuwa lokaci. Ta koma d'aki tana mamaki sai kace ba Meenah ba, gaba d'aya ta fad'a tarkon so.
Kafin ya tafi ya d'auko kyauta gift d'in turare da agogo ya bata, amma sam tak'i kar6a, sai da yayi da gaske har yana neman yin fushi sannan ta kar6a tana godiya sosai.

Soyayya tsakanin Meenah da Faruk kullum abin dad'a gaba yake cike da salo na ban mamaki, basu iya yini d'aya basuyi waya ba, haka ma kullum yana kan hanyar zuwa wurinta.
Tabbas zuwa yanzu soyayyar da Meenah ke ma Faruk bata misaltuwa, abin mamaki Faruk ya iya tafiyar da soyayya yadda ya kamata ya kuma son hanyoyi daban daban na yadda zai jawo hankalinta gare shi, ga yaci sa'a wannan shine karo na farko data fara sanin yadda ake soyayya, sheyasa a halin yanzu duk wanda zata so zata soshi ne da dukkan zuciya da kuma ruhinta. Faruk ya riga da ya saye zuciyarta farat d'aya, ko irin kalaman da yake furta mata kad'ai ya isa ya saye zuciyar Meenah, don haka sheysa bai sha wahalar yiwa zuciyar Meenah kamun kazar kuku ba!
Batada wani tunani sai na Faruk, batada wani ra'ayi sai nasa, sannan batada wani buri sai na mallakarsa a matsayin mijinta na abokin rayuwa na har k'arshen rayuwarta ba.



MSB๐Ÿ’–

Thursday 6 July 2017

AUREN FANSA 19

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน19 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com


Tun kafin ta kai ga d'auka haka kawai ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, ta kira sunan Allah don neman nutsuwa cikin zuciyarta. Cikin ikon Rabbi kuwa ta samu nutsuwa sai dai kafin ta d'auka tuni wayar ta katse. Ajiyar zuciya tayi, sai dai tana katsewa wani kiran na shigowa.
"AssalamuAlaiki yake ma'abociyar kyau, kwarjini da kuma nutsuwa."
Abinka da rashin sabon waya da maza, tuni ta rasa nutsuwarta, da k'yar ta amsa masa
"Wa'alakumsalam."
"Yau dai na taki sa'a tunda har aka d'auki wayata sannan aka d'aga lokacki d'aya, lallai ni mai babban sa'a ne. Ko ba haka ba 'yan mata?"
Ta k'ara kiran sunan Allah a karo na biyu, saboda rashin sabo da kuma muryar mutumin da bata san ko waye ba, sai dai me? Jin muryar takeyi kamar ana busa sarewa, bata ta6a jin murya mai dad'i ba irin ta wannan mutumin ba...
"Ya kikayi shiru Princess?"
Gabanta ya yanke ya fad'i, wai wannan mutumin kamar aljani? Da yayi mata magana sai gabanta ya fad'i.
"Nidai muryar nan taki ko dai zan biya ne don na lura tana tsada..."
"Ina wuni?"
Yayi murmushi, har tana jiyo sautin yana bugun dodon kunnenta, sannan a take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr!
"Kina lafiya?"
"Lafiya lau."
"To masha Allah, zan d'an baki dan gajeren labarina, bana so ki zo kina ce min bakisan ko da wa kike waya ba... ko ba haka ba?"
Tace
"Uhm."
Yace
"Yauwa, da farko sunana Faruk Adam, shekarata 26 kacal a duniya, iyayena sun rasu gaba d'aya tun ina k'arami, yanzu daga ni sai k'anwata muka rage, ina zaune gidan wani uncle d'ina a garin Abuja. Mahafiyata shuwa ce while babana fulani ne. Yanzu dai na kammala karatuna ina aiki. To kinji kad'an daga cikin tarihin rayuwata, ko zan iya jin naki?"
Tace "uhm, Allah ya jik'ansu."
Yace
"Amin, ina jinki fa."
Da k'yar ta iya tattaro nutsuwarta wuri d'aya ta soma magana mai cike da nutsuwa.
"Sunana Amina Hamza, mahaifina d'an garin Katsina ne amma yanzu aiki ya kai shi Abuja, na kammala karatuna na fita daga secondary ina jiran admission zan tafi university. Mu biyu ne kad'ai a gidanmu daga ni sai k'anwata mai suna Fatima."
Yayi murmushi
"Allah sarki Allah ya taimaka, to baki fad'a min shekarunki ba?"
Tace
"16."
Yace
"Wow, lallai ashe dai da sauranki yarinya."
Tayi murmushi mai cike da kunya.
Haka suka 6ata wannan daren Faruk na janta da fira, tun tana d'ari d'ari har ta d'an saki jikinta tana bashi amsa, idan akayi labarin dariya suyi dariya, daga k'arshe ganin har uku na dare ya sashi yayi mata sallama akan zai kirata da safe.
Koda ta kwanta kasa bacci tayi, muryarsa kawai takeji cikin dodon kunnenta kamar yanzu yake mata magana.

Daman bata sallah sheyasa ma bata tashi da asuba ba. Bacci takeyi har kusan goma da rabi na safe.
Juyi d'aya tayi akan gado tayi tozali da wayarta kamar had'in baki sai kuma ta fara ruri. Ganin number d'in jiya ya sata sakin murmushi ba shiri.
A kasalance ta d'auka gami da yin sallama.
"Good morning! Rise and shine, raina ya bani yanzun nan kika farka daga bacci, ko da yake laifi nane dana hana ki bacci da wuri tun jiya ko? To ayi min afuwa. Bazan sake ba."
Cikin ranta tace
"Wannan sai kace aku ko gajiya baiyi da magana?"
"Ina kwana?"
Yayi murmushi
"Lafiya lau da fatan princess d'in tawa ta tashi lafiya?"
Ta langa6ar da kanta gami da lumshe idanu tace.
"Alhamdulillah, thanks."
Yace
"Yauwa, to yanzu abinda ya kamata kije kiyi wanka sai kici abinci."
"To." Kawai tace gami da yi masa sallama ta kashe wayar. Ganin Zarah tsaye bakin k'ofa ya sa gaban Meenah ya yanke ya fad'i. Zarah ta k'araso tana dariya
"Love in the air, yanzu don Allah bakiji dad'i ba? Amma ace mutum ya takura ma kansa da rayuwar kad'aici haba!"
Murmushi tayi ta sauka daga kan gadon tace
"Bari nayi wanka."
Tana jin Zarah na d'aga murya tana fad'in
"Wai don dai kar ayi maganar zaki wani shige wanka."
Murmushi kawai tayi.
Wunin ranar zungur a d'aki tayi shi, har dare bata fito ba, ba abinda ke tashinta daga gado sai shiga toilet.

Washe gari kuma haka ta tashi sukuku. Zarah ta rasa gane kan yayar tata.
Haka dai komai ya cigaba da gudana a tsakanin Meenah ta Faruk, wuni sukeyi mak'ale a waya, zuciyarta  ta aminta da shi lokaci guda, ta yarda ta amince shi d'in takeso. Tun da ya turo mata hotunan sa taji yayi mata, lokaci guda ya sace zuciyarta ya kuma tafi da imaninta gaba d'aya, har ta soma cewa cikin ranta
"Anya ba surk'ullensu na fulani yayi mani ba?"

Wata rana da daddare yana ta kiranta ya sanar mata gobe zaizo wurinta, daman sunyi zaizo Katsina, idan yazo zai shigo su gaisa. A lokacin da yake ta kiranta tana bacci kuma wayar a silent take.
Washe gari da safe sai ta iske message d'insa ya turo mata.
"Just to say good night! With you in my mind... ?"
Sai tayi murmushi ta tura
"In both the soul and mind...."
A lokacin da ta tura masa sak'on bai gani ba saboda yana cikin jirgi don tahowa Katsina!


MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 18

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน18 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com


***

Kwanci tashi babu wuya wurin Allah har su Meenah sun gama zana exams d'in k'arshe. Ranar da suka gama Baba yayi musu kyauta mai tsoka sannan ya musu alk'awarin tafiya Katsina hutu. Murna a wurin Meenah ba'a magana, daman tafison can saboda can tafi sakewa tayi abinda takeso, babu mai takura mata.
Haushi Bilki kamar zata fashe, daman duk sadda zasu je Katsina hutu sai hankalin Bilki ya tashi a cewar ta mai mata ayyukan gidan bata nan.
Akan dole takeyi har sai sun dawo.
A tsarin hutun sati biyu zasuyi inji Baba, don haka tun ranar Meenah ta fara shirin tafiya. Ta wanke kayanta ta goge.

Ranar da zasu tafi tunda asuba ta tashi, bayan tayi wanka ta d'auko cikin sabbin kayanta na wata sallah ta saka, blue atamfa d'inkin riga da skirt, tayi kyau sosai.
A lokacin data sakko k'asa ta iske Baba da Zarah suna karyawa, yana ganinta yace.
"Maza zo kici abinci mu kama hanya."
Da saurinta kuwa ta taho tana murmushi.
Bayan sun kammala, Hassan mai gadinsu ya shigo ya fara fitar musu da kayansu yana sakawa boot.
Bilki ce ta sauko tana yak'e, tace
"Badai tafiyar bace?"
Baba yayi dariya yace
"Itace yanzu zamu kama hanya ma."
Ta had'iye 6acin ranta tace
"Wai tun yanzu Alhaji?"
Sai da yayi murmushi yace
"To idan bamu tafi yanzu ba sai yaushe zamu tafi? Katsina fa ba nan ba."
Tace
"Hakane kam, to Allah ya tsare ya kaiku lafiya."
Yayi murmushin jin dad'i yace
"Amin."
Bayan gama ban kwana, Alhaji ya d'auki hanya zuwa Katsinan Dikko.

Sai can yamma suka isa, da gudu su Meenah sukayi ciki suna zuwa suka haye 'yar tsohuwar dake zaune tana hutawa a parlor.
"Kai kai zaku 6alla ni ne?"
Sai kuma tayi murmushin jin dad'i
"Ahh Aminatu da Fatsima ne? Saukar yaushe?"
Meenah tace
"Yanzun nan muka iso, ina wuni Goggo?"
Tace
"Lafiya lau, ina Baban naku."
Meenah tace
"Yana waje yanzu zai shigo."
Bata rufe baki ba ya shigo.
"Lale maraba da Hamza."
Yayi dariya tare da zama k'asa yana kai gaisuwa zuwa ga mahaifiyar tasa.
"Mun same ku lafiya?
Tace
"Alhamdulillahi, ya aiki?"
Yace
"Alhamdulillah, ya k'arfin jiki?"
Tace
"Sai godiyar Allah."
Yace
"Allah k'ara lafiya, daman yaran suka kammala makaranta shine na kawo suyi maki sati biyu, naga sun kwana biyu basu zo ba, ni kuma gobe in Allah ya yarda zan juya."
Tace
"Kai masha Allah! Allah ya bada sa'a."
Suka amsa da "Amin."


BAYAN KWANA BIYAR.

Kamar kullum bayan Meenah ta sanya kayan baccinta riga da wando kalar dark pink, tana shirin kwanciya Zarah dake kwance tana latse latse a wayarta ta ajiyewa wayar gami da kiran sunanta.
"Meenah..."
Ta kalle ta gami da yin murmushi tace
"Na'am Zarah."
Jingina Zarah tayi jikin bangon gadon da take kwance tace
"Meenah wai meyasa kika k'i sauraron wannan mutumin? Nafa lura kamar sonki yake da gaske."
Take annurin fuskarta ya 6ace 6at! Ta d'aure fuska tamau gami da gyara zamanta kusa da Zarah.
"Wane mutumi kenan?"
A iya sanin Zarah babu wanda ke takura mata kamar wani wanda ke yawon matsa mata wai ya had'u da ita a Instagram!
"Haba mana Meenah, kinfa san wa nake nufi."
"Ay ni bai furta man cewar yana sona ba..."
Ta fad'a gami da jawo wani novel na turanci mai suna Behind the clouds ta soma bud'ewa tana k'ok'arin karantawa.
Zarah tayi ajiyar zuciya tace
"Bafa kyau wulak'anci, ki daure ko yaya ne ki sauarare shi."
Meenah ta ajiye littafin tana mai kallon Zarah tace
"Zarah duk duniya banida aminiya sama da ke, ke kanki kinsan cewa soyayya bata cikin ra'ayina a yanzu, ban iya bama bansan ya take ba, ban kuma san ta ina zan fara ba, nifa tun farko sheyasa nace miki kar ki bud'e min irin wad'annan abubuwan kika k'i ji Zarah, yanzu ga irin ta nan, daman abinda nake gudu kenan."
Zarah ta kalle ta da mamaki tace
"Me kike gudu?"
Meenah tace
"Samarin zamani mana, 'yan k'arya mayaudara, ina tsoron ayi min wasa da feelings d'ina, sheyasa ma kikaga ina tsoron yin soyayya..."
"Ay ba duka aka taru aka zama d'aya ba, idan kikayi sa'a sai kiga kin samu mai sonki da gaske..."
"Zarah da kinyi hak'uri kin k'yale ni bazan iya yin soyayya yanzu ba..."
Ta fad'a tana k'ok'arin cigaba da karatunta ranta idan yayi dubu to ya 6ace.
"Bazan tilasta miki ba, amma ina rok'onki ki bashi chance idan kikaga alamar mayaudari ne basai ki rabu dashi ba? Menene a ciki? Ni wallahi haka nan kawai yake bani tausayi kullum cikin damuwa yake da ke, ina laifin me sonka? Koda bai furta miki kalmar so yanzu ba, to na tabbata zai furta maki nan bada jimawa ba! Haba Meenah bansanki da wulak'anci ba..."
Ta d'aga mata hannu
"Ya isa Zarah, naji na amince zan bashi chance, shikenan?"
Zarah tayi murmushi
"Shikenan, kiyi karatunki sai da safe."
Tayi murmushi
"Allah ya kaimu lafiya."
Gajiya tayi da karatun ta d'auko wayarta gami da duba lokaci. K'arfe 12:53am, ajiye littafin tayi tana k'ok'arin kwanciya message ya shigo ta wayarta.
Tasan bai wuce d'an k'wak'war nan, ta fad'a a cikin ranta gami da sakin d'an guntun tsaki.
Dubawa tayi.
"Hello."
"Hey."
"No answer?"
"How are you dear?"
"Hmm."
"Are you sleeping?"
"Please talk to me mana."
Da k'yar tace
"Hi."
Yana kwance yana latse latse a laptop nasa message nata ya shigo, ya ware manyan idanunsa cike da mamaki, murmushi yayi ya rubuta mata.
"Thank God! Naji dad'i da kika man reply, i thought na maki wani laifi ne?"

"A'a bakomai..."

"So ya kike? Kin dai hanani number ki ko?"

"Hmm."

"Bakomai kina min rowan jin muryarki mai dad'i ko?"

"A'ah..."

"To ki bani mana, idan ba rowa ba."

Yau yaci albarkin Zarah, don haka sai kawai ta tura masa number d'in.
Minti biyu tsakani...
Kwance take lamo, zuciyarta na mata sak'e sak'e. Bata ankara ba wayarta ta fara ruri, bak'uwar number ta gani. Da k'yar tasa hannu ta d'auka....



MSB๐Ÿ’–

Wednesday 5 July 2017

AUREN FANSA 17

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน


Dedicated to Kiddies friends 4ever, thanks for the support you are special to me! Love you guys❤️


          ๐ŸŒน17 ๐ŸŒน


http://MaryamSBello.blogspot.com

D'aya bayan d'aya yake duba hotunan dake baje a gabansa, sai daya d'auki lokaci kad'an yana analyzing ko wanensu duk Usman yana kallonsa. Sai da ya gama sannan ya d'ago yana kallon Usman yace.
"Nagode, sai kayi min bayaninsu."
Usman ya gyara zama yace
"Yalla6ai ka duba wannan takardar na rubuta komai amma duk da haka zan maka bayani da baki.
"Da farko hotunan nan sai da nayi k'wak'waran bincike akansu kafin nazo nan."
Hoto d'aya ya d'auko ya mik'a masa.
"Wannan sunansa Alhaji Hamza Umar, haifaffan d'an garin Katsina ne kafin ayi masa transfer zuwa nan Abuja. Wannan kuma matarsa ce Hajiya Bilkisu, yaransu biyu kacal duka mata. Babbar itace Amina wadda suke kira da Meenah ga hotonta nan, sai k'aramar wadda babu wani tazara a tsakaninsu mai suna Fatima Zarah. Duk wad'annan hotunan sai da nayi bincike na gano account name d'in d'iyarsa mai suna Zarah duk a nan na kwaso hotunansu, ita Meenah a nata account d'in babu hoto ko k'wara d'aya, hartta handle d'insu yana nan a rubuce a jikin takardar.
Sai ita d'ayar mai suna Hajiya Layla ita tana Kaduna da zama da mijinta mai suna Alhaji Sambo, sai d'iyarta k'wara d'aya mai suna Yasmeen."
Gwauron numfashi Faruk ya sauke a lokaci guda kuma ya d'auko hotunan yaran nasu da akayi masa nuni dasu yana ta kallonsu yana juya hotunan. Aje hotunan kuma yayi yana kallon Usman tare da d'ora hannayensa saman table d'in yace.
"Good job, so anything else?"
Usman ya cigaba
"Yes, makaranta d'aya suke zuwa mai suna Turkish, ita babbar tana k'ok'arin kammala karatun nata ne while ita k'aramar wato Zarah tana SS2 a yanzu. Duk weekend suna zuwa Katsina wurin  mahaifiyar Hamzan mai suna Hajiya Fatima.
Idan suka je kamar misali ranar Juma'a zasu dawo ranar Lahadi, amma yanzu bincike ya nuna mani cewar sunyi akalla sati biyu basuje ba, sakamakon jarabawa da d'iyar Alhaji Hamza take shirin zanawa ta fita daga secondary.
Alhaji Hamza yakan d'auki yaranshi su fita yawon shak'awatawa duk ranar Alhamis da daddare."
Ajiyar zuciyar ya sauke yana kallon Usman ya kuma cewa
"Anything else?
"Yawwa, ka tambaya ina da ina suke zuwa, to a zahirin gaskiya yaran Alhaji Hamza basa fita yawo, daga makaranta sai islamiyya, amma daga nan basu cika zuwa ko ina ba. Amma kayi hak'uri a 6angaren Hajiya Layla sai na k'ara bincike don bansamu wani information sosai ba, na dai gano cewar tana yawan fita Dubai saro kaya."
Faruk yace
"Nagode, ka manta ka sanar dani aikin da sukeyi fa."
Usman yace
"Sorry sir, Alhaji Hamza ma'aikacin banki ne, amma matarsa bata aiki tana harkar kasuwanci, wanda naji ance tana da gidajen mai, shaguna, mall, tana da k'aton shagon saida saide, da sauransu.
Haka zalika Alhaji Sambo shi d'an kasuwa ne kuma yana aikin gwamnati."
Ya saki ajiyar zuciya yace
"Nagode da taimakon da kayi min duk da akan aikinka ne amma ni ka taimake ni ba kad'an ba, so nagode Allah saka da alkhairi."
Usman yayi dariya
"Haba yalla6ai menene na godiya? Ni keda godiya ay."
Faruk yace
"Bakomai Usman zaka iya tafiya."
Daga haka ya amsa da "To." Sannan yayi masa sallama ya fita.
Yana fita ya saki murmushin da shi kad'ai yasan mana'arsa.
Murd'a k'ofar akayi aka shigo, Najeeb ne, da murmushi Faruk yace
"Ka shigo mana."
Bayan ya zauna ne Najeeb ya soma magana
"Ka bani mamaki Faruk, ban ta6a tunanin haka daga gareka ba..."
Gaban Faruk yayi mummunan fad'uwa, yace
"Me akayi?"
Najeeb yace
"Yanzu daman abinda kake shiryawa kenan baka sanar dani ba? Inda banji me kuke cewa ba da bazaka ta6a fad'a min ba ko?"
Faruk yace
"Ko kad'an ba haka bane, naso ace sai na gama duk abinda ya kamata sai na sanar maka..."
Najeeb yace
"To tunda yanzu naji sai ka fad'a min komai."
Faruk yayi dariya yace
"Akan dai maganar nan ce ta kwanakin baya."
Najeeb yace
"Maganar iyayenka ko?"
Faruk yace
"Eh ita, so wani d'an bincike nasa aka yo mani akan mutanen kuma an kawo."
Ya k'arasa yana mik'a masa hotunan.
Najeeb ya duba bayan ya gama yace.
"Ok to menene next move naka?"
Faruk yayi murmushin nasa da ya saba yi masu ma'ana daban daban yace
"Zan sanar da kai komai, yanzu muje muyi sallah mu dawo."
Najeeb yace
"Ok muje."
A tare suka mik'e suka fice daga office d'in.


***

Yana shiga d'akin nasa ya jiyo k'amshin turaren wuta mai dad'i, ga sanyin ac gaurewa da d'akin. Yasan baya wuce aikin Jidda, don ya lura tunda suka dawo take faman d'wainiya dashi, bakin gado ya zauna ya shiga cire takalminsa da safa, bai kai ga gamawa ba ta shigo d'akin nasa, hannunta d'auke da tray d'in ruwa da lemon kwali 5alive, a d'an k'aramin table ta ajiye ta d'ago tana kallonsa cike da kunya, tace
"Sannu da zuwa yaya."
Yace
"Yawwa sannu da aiki."
Tace
"Yawwa, kana buk'atar wani abu?"
Ya d'an karkato gami da kallonta yace
"A'a nagode."
Daga haka ta fice daga d'akin a yayinda shi kuma ya fad'a toilet don watsa ruwa.


MSB๐Ÿ’–