Thursday 6 July 2017

AUREN FANSA 18

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹18 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com


***

Kwanci tashi babu wuya wurin Allah har su Meenah sun gama zana exams d'in k'arshe. Ranar da suka gama Baba yayi musu kyauta mai tsoka sannan ya musu alk'awarin tafiya Katsina hutu. Murna a wurin Meenah ba'a magana, daman tafison can saboda can tafi sakewa tayi abinda takeso, babu mai takura mata.
Haushi Bilki kamar zata fashe, daman duk sadda zasu je Katsina hutu sai hankalin Bilki ya tashi a cewar ta mai mata ayyukan gidan bata nan.
Akan dole takeyi har sai sun dawo.
A tsarin hutun sati biyu zasuyi inji Baba, don haka tun ranar Meenah ta fara shirin tafiya. Ta wanke kayanta ta goge.

Ranar da zasu tafi tunda asuba ta tashi, bayan tayi wanka ta d'auko cikin sabbin kayanta na wata sallah ta saka, blue atamfa d'inkin riga da skirt, tayi kyau sosai.
A lokacin data sakko k'asa ta iske Baba da Zarah suna karyawa, yana ganinta yace.
"Maza zo kici abinci mu kama hanya."
Da saurinta kuwa ta taho tana murmushi.
Bayan sun kammala, Hassan mai gadinsu ya shigo ya fara fitar musu da kayansu yana sakawa boot.
Bilki ce ta sauko tana yak'e, tace
"Badai tafiyar bace?"
Baba yayi dariya yace
"Itace yanzu zamu kama hanya ma."
Ta had'iye 6acin ranta tace
"Wai tun yanzu Alhaji?"
Sai da yayi murmushi yace
"To idan bamu tafi yanzu ba sai yaushe zamu tafi? Katsina fa ba nan ba."
Tace
"Hakane kam, to Allah ya tsare ya kaiku lafiya."
Yayi murmushin jin dad'i yace
"Amin."
Bayan gama ban kwana, Alhaji ya d'auki hanya zuwa Katsinan Dikko.

Sai can yamma suka isa, da gudu su Meenah sukayi ciki suna zuwa suka haye 'yar tsohuwar dake zaune tana hutawa a parlor.
"Kai kai zaku 6alla ni ne?"
Sai kuma tayi murmushin jin dad'i
"Ahh Aminatu da Fatsima ne? Saukar yaushe?"
Meenah tace
"Yanzun nan muka iso, ina wuni Goggo?"
Tace
"Lafiya lau, ina Baban naku."
Meenah tace
"Yana waje yanzu zai shigo."
Bata rufe baki ba ya shigo.
"Lale maraba da Hamza."
Yayi dariya tare da zama k'asa yana kai gaisuwa zuwa ga mahaifiyar tasa.
"Mun same ku lafiya?
Tace
"Alhamdulillahi, ya aiki?"
Yace
"Alhamdulillah, ya k'arfin jiki?"
Tace
"Sai godiyar Allah."
Yace
"Allah k'ara lafiya, daman yaran suka kammala makaranta shine na kawo suyi maki sati biyu, naga sun kwana biyu basu zo ba, ni kuma gobe in Allah ya yarda zan juya."
Tace
"Kai masha Allah! Allah ya bada sa'a."
Suka amsa da "Amin."


BAYAN KWANA BIYAR.

Kamar kullum bayan Meenah ta sanya kayan baccinta riga da wando kalar dark pink, tana shirin kwanciya Zarah dake kwance tana latse latse a wayarta ta ajiyewa wayar gami da kiran sunanta.
"Meenah..."
Ta kalle ta gami da yin murmushi tace
"Na'am Zarah."
Jingina Zarah tayi jikin bangon gadon da take kwance tace
"Meenah wai meyasa kika k'i sauraron wannan mutumin? Nafa lura kamar sonki yake da gaske."
Take annurin fuskarta ya 6ace 6at! Ta d'aure fuska tamau gami da gyara zamanta kusa da Zarah.
"Wane mutumi kenan?"
A iya sanin Zarah babu wanda ke takura mata kamar wani wanda ke yawon matsa mata wai ya had'u da ita a Instagram!
"Haba mana Meenah, kinfa san wa nake nufi."
"Ay ni bai furta man cewar yana sona ba..."
Ta fad'a gami da jawo wani novel na turanci mai suna Behind the clouds ta soma bud'ewa tana k'ok'arin karantawa.
Zarah tayi ajiyar zuciya tace
"Bafa kyau wulak'anci, ki daure ko yaya ne ki sauarare shi."
Meenah ta ajiye littafin tana mai kallon Zarah tace
"Zarah duk duniya banida aminiya sama da ke, ke kanki kinsan cewa soyayya bata cikin ra'ayina a yanzu, ban iya bama bansan ya take ba, ban kuma san ta ina zan fara ba, nifa tun farko sheyasa nace miki kar ki bud'e min irin wad'annan abubuwan kika k'i ji Zarah, yanzu ga irin ta nan, daman abinda nake gudu kenan."
Zarah ta kalle ta da mamaki tace
"Me kike gudu?"
Meenah tace
"Samarin zamani mana, 'yan k'arya mayaudara, ina tsoron ayi min wasa da feelings d'ina, sheyasa ma kikaga ina tsoron yin soyayya..."
"Ay ba duka aka taru aka zama d'aya ba, idan kikayi sa'a sai kiga kin samu mai sonki da gaske..."
"Zarah da kinyi hak'uri kin k'yale ni bazan iya yin soyayya yanzu ba..."
Ta fad'a tana k'ok'arin cigaba da karatunta ranta idan yayi dubu to ya 6ace.
"Bazan tilasta miki ba, amma ina rok'onki ki bashi chance idan kikaga alamar mayaudari ne basai ki rabu dashi ba? Menene a ciki? Ni wallahi haka nan kawai yake bani tausayi kullum cikin damuwa yake da ke, ina laifin me sonka? Koda bai furta miki kalmar so yanzu ba, to na tabbata zai furta maki nan bada jimawa ba! Haba Meenah bansanki da wulak'anci ba..."
Ta d'aga mata hannu
"Ya isa Zarah, naji na amince zan bashi chance, shikenan?"
Zarah tayi murmushi
"Shikenan, kiyi karatunki sai da safe."
Tayi murmushi
"Allah ya kaimu lafiya."
Gajiya tayi da karatun ta d'auko wayarta gami da duba lokaci. K'arfe 12:53am, ajiye littafin tayi tana k'ok'arin kwanciya message ya shigo ta wayarta.
Tasan bai wuce d'an k'wak'war nan, ta fad'a a cikin ranta gami da sakin d'an guntun tsaki.
Dubawa tayi.
"Hello."
"Hey."
"No answer?"
"How are you dear?"
"Hmm."
"Are you sleeping?"
"Please talk to me mana."
Da k'yar tace
"Hi."
Yana kwance yana latse latse a laptop nasa message nata ya shigo, ya ware manyan idanunsa cike da mamaki, murmushi yayi ya rubuta mata.
"Thank God! Naji dad'i da kika man reply, i thought na maki wani laifi ne?"

"A'a bakomai..."

"So ya kike? Kin dai hanani number ki ko?"

"Hmm."

"Bakomai kina min rowan jin muryarki mai dad'i ko?"

"A'ah..."

"To ki bani mana, idan ba rowa ba."

Yau yaci albarkin Zarah, don haka sai kawai ta tura masa number d'in.
Minti biyu tsakani...
Kwance take lamo, zuciyarta na mata sak'e sak'e. Bata ankara ba wayarta ta fara ruri, bak'uwar number ta gani. Da k'yar tasa hannu ta d'auka....



MSB💖

No comments: