Wednesday 5 July 2017

AUREN FANSA 16

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹16 🌹

http://MaryamSBello.blogspot.com


***

Tsaye take a gaban wardrobe tana gyara zaman skirt d'inta, duk da kayan dake jikinta sun mata kad'an hakan bai hana ta yin kyau ba, ji tayi an rungume ta ta baya, tasan baya wuce aikin Zarah.
"Auch! Haba mana Zarah so kike ki k'arasa ni ne?"
Zarah tasa dariya, tace
"To sarkin fad'a, yanzu dai maida wuk'ar albishir nazo miki dashi." Meenah ta juyo da murmushi saman fuskarta tace
"Ina jinki."
Zarah tace
"Fari ko ja?"
Meenah tace
"Fari k'al ma kuwa."
"Baba yace nayi WAEC d'ina yanzu idan naci mu tafi university tare!"
Zarah tace cike da murna. Meenah farin ciki ta rasa ina zata sa ranta, dama ta dad'e tana addu'ar su tafi university tare da Zarah, sai dai tasan Baba ne ya hana yace bazatayi ba sai ta kai SS3, amma yanzu ko ya akayi ya yarda? Meenah tace
"Amma ya akayi ya yarda?"
Zarah tace
"Wallahi ikon Allah, kuma fa ba tambayar sa nayi ba, shi da kansa ya kirani yace na shirya yin exam tare da ke."
Meenah cike da murna tace
"Lallai ikon Allah, Allah yasa kici."
Zarah ta rungume Meenah tana murna tace
"Amin sisi."
"Kai meye kun cika ma mutane kunne da hayaniya?"
Cewar Bilki daga bakin k'ofar d'akin tana tsaye, fuskarta ba yabo ba fallasa.
Sukayi tsit, ta kuma daka musu tsawa
"Ba da ku nake ba?"
Zarah tace
"Da... dama, Baba ne yace za... zan iya tafiya university tare da Meenah..."
Take ta washe baki kamar ba ita ba, tace
"Allah d'iyar Baba? Yaushe ya yarda?"
Tace
"D'azu kafin ya tafi wurin aiki."
Bilki tace
"Alhamdulillah, yayi daidai Allah ya bada sa'a sai ki dage, tun kafin ace bakida k'ok'ari, ko kuma ace wasu sun fiki."
Ta k'arasa tana ma Meenah wani irin mugun kallo. Duk sun san abinda take nufi kuma hakan ya sosa ransu.
"Ke! Meenah zo ki matsa man k'afa ta."
"Mami zan taya ta."
Wani kallo ta watso mata na irin kika k'ara magana sai na kakkarya ki sannan ta fice. Meenah ta dafa ta tana fad'in.
"Don Allah Zarah daga yau ki daina cewa zaki taya ni idan tasa ni aiki, wallahi fad'a kike ja man duk sadda kika fad'i haka."
"Uhm." Kawai Zarah tace, daga haka Meenah ta juya da sauri zuwa sashen Mami.

Da sallama ta shiga, zaune take kan wata
kujerar hutawa ta baje k'afafuwanta ma'ana ta mik'ar dasu saman kujerar, tana faman danne danne a wayarta k'irar iPhone 7plus, tana zuwa ta durk'usa har k'asa tace
"Gani Mami."
Sai data samu tsarabar harara sannan tace
"Meya tsaida ki tun d'azu nake zaman jiranki?"
Bata ce komai ba kanta na k'asa dai.
"Sai anyi magana kiyi sum sum da kai kamar mutuniyar arzik'i..."
"Kiyi hak'uri Mami, wallahi ban tsaya yin komai ba nan na taho."
Tayi tsaki gami da mik'o mata k'afa.
"Ni matsa man k'afata, kuma saura kiyi mani mugunta irin na rannan wllh sai na yi maganinki, don yau sai dai a kaiki asibiti don sai nayi miki lis!"
A hankali take matsa mata cikin lalla6awa, sai kuma ta sakar mata k'wanya a kai.
"Ke bakida hankali ne? Ya zaki dinga mani abu kamar susar k'adangare?"
Sai ta hau yi da d'an k'arfi, nan ma ta kai mata wanda yafi na d'azu zafi.
"Yau ga muguwa! Zaki 6alla min k'afa ne?"
Ta rasa yadda zatayi, mistake kad'an sai taji k'wanya mai shegen zafi a kanta.

Da daddare tana kwance ita dai abin duniya yabi ya dame ta, zuwa yanzu ta yarda ta amince ba Mami ta haife ta ba,  ta yarda Baba ne babanta amma sam ta kasa yarda Mami ce ta haifeta. To ina mahaiyarta? Ta rasu ne ko tana raye? Ko kishiyar Mami ce? Kullum ire-iren wad'annan tambayoyin sune suke mata yawo a cikin kai, kuma har yanzu ta rasa amsa. Daga k'arshe ta yarda ta amice mahaifiyarta ta rasu kuma kishiyar Mami ce kawai. Wasu zafafan k'walla suka zubo mata, ita kam batasan dad'in uwa ba, bata san ya ake ji ba idan mutum na tare da mahaifiyarsa.
Sama sama tayi bacci gudun makara saboda ga aikin gida ga kuma shirin makaranta.

Da asuba ta mik'e bayan ta gabatar da sallar asuba tayi wanka, ta yi aikin gidan kamar kullum, ta had'a kalaci, d'aki ta wuce ta sanya uniform d'inta da basu samu guga ba, bayan ta gama shirinta tsab ta fito don ta karya, tana bud'e kular abinci sai ta ganta wayam! Nan ta hau dube dube amma kaf ba komai a ciki.
Mami ce ta sauko cikin kayan bacci da d'aurin gaba tana zuwa tabi Meenah da mugun kallo, ta wuce kitchen. A ranar haka nan ta hak'ura da kalacin daman sun makara, sauk'inta ma Baba ya basu kud'in makaranta da batasan ya zatayi ba.


***

BAYAN KWANA BIYU

Da sallama ya shigo office d'in, yana zaune yana fama da aiki kamar kullum, d'ago da fuskarsa yayi yace
"Shigo mana Usman."
Sai da ya kammala abinda yakeyi sannan ya maida dubansa ga Usman dake zaune d'auke da wata babbar brown envelope.
"Yalla6ai daman akan aikin da kasani ne, to Alhamdulillah na kammala maka komai shine na kawo maka ka gani."
Da sauri ya d'ago yana duban Usman yace
"Da gaske ka kawo duk abinda nake buk'ata?"
Usman yana murmushi sosai yace
"K'warai kuwa gasu."
Ya sa hannu ya zazzaro wasu hotuna guda biyar ya dire a gabansa, sannan ya fiddo wani dogon paper mai rubuce rubuce a samanta....



MSB💖

No comments: